Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
gareta shine kyawun fuskarta. Bebi ta sake zubawa fuskarta idanu cikin kaduwa domin ta lura duk ta lura fatar ta fara saki kamar fatar dadadden mangwaro duk da yake dai bebi tai imani da cewa ta gama kama ruhin honorabil sabo amma abin ya bata tsoro domin ta sani idan batayi hanzari ba honorabil sabo na iya sauya aniyarsa ta aurenta dayafara yi duk da yake dai tasan cewa ba ra'ayin kansa bane ya aure ta malaman tsibbunta da bokayenta ne ke ta aiki akansa amma yanada kyau ace idan kanada kyau ka kara da wanka wannan tunanin shiyasa bebi ta sake kallon kanta ajikin madubi akaro na uku sannan saitace da kanta cikin takaici. Haba fuskata... Ya zakiyi min haka? Tana gama fadin haka sai bebi ta lalubi wayarta akasan matashin kai ta daddanna wasu lambobi sannan ta kara wayar a kunne acan jimawa saitace. Hello.... Malam ina kwana? Lafiya lau. Akace adaya bangaren kudin nan dana turo ma yazo ko? Kwarai kuwa yazo masha Allah Allah yasaka da alkhairi aka amsa adaya bangaren shiru na dan lokaci. Dan Allah malam sai akuma dage min kaga haryanzu dai zancen auren nan namu shiru kwata kwata ma ya daina zancen rabon da yatada zancen tun kafin mutuwar abokinsa honorabil jatau kaga yau kusan wata uku kenan fa Malam. Kada ki tashi hankalinki 'yata. Akace da wata kakkausar murya acan daya bangaren nafada miki tunda mukayi wannan aikin na farko babu abunda zai hanashi aurenki. To ai malam ni abin ne da ban tsoro kaga fa da ba'a sama da kwana biyu banganshi ba amma yanzu tunda abokin nan nasa ya rasu sai inyi kwana goma ban ganshi ba ya ajiyeni kawai sai kiwatani yake kamar akuya kullum yana shagwaba ni da jin dadi amma ni duk wannan bashine agabana ba nidai burina shine ya aureni kuma idan da hali ma so nake matarsa uwar ya'yansa tabar gidan. Kada ki damu babu abinda ya gagari malam. Aka danyi shiru acan daya bangaren yanzu yaushe rabon da ku gana dashi? Ido da ido dai yau anfi kwana shida amma kullum muna waya kamar sau uku zai tambaya idan kayan abincina ya kare sai a karomin akwai wanda yake aikowa. To shikenan Allah rufa asiri yanzu ina ganin wani aikin zamu sake. To malam bebi ta amsa cikin gaggawa zamu bukaci bakaken tinkiyoyi guda goma wadanda babu sofaren fari a jikinsu To malam nawa ne kudin saina kawo ma gobe da kaina. Yan kanana dai basa wuce dubu shida shida.... Kada ka damu zan kawo ma dubi dari gobe sai ayi duk abinda yakamata nidai burina shine...... Bebi tayi shiru sa'ar dataji motsi da surutun Jama'a a farfajiyar gidan. Zan kiraka in an jima bebi tace da malamin kafin ya amsa ta kashe wayar. Lokaci guda kuma ta koma kan gadon ta kwanta lamo kamar tashinta kenan daga barci batayi minti guda da kwanciya ba aka banko kofar dakin da karfin tsiya aka shigo bebi ta dago kai a firgice cikin mamaki sai taga honorabil dinta sabo tsaye a tsakiyar dakin kallo daya tayiwa fuskarsa tasan cewa tabbas ba lafiya jiki na rawa ta tashi zaune akan gadon ta dube shi amma batace uffan ba. Tashi kisa kayanki ina san magana dake akwai alamun karkarwa acikin muryarsa haka nan bebi ta lura da fuskar honorabil sai naso take da gumi Lafiya..... Me yayi zafi haka? Bai amsa mata ba sai ya nufi bakin gadon ya zauna sannan ya dubeta . Abinda Nake Gudu Ne Bebi Shiya Faru Honorabil Yace Yana Girgiza KaiMaganar kawarki ce mama gashi nan yanzu ita jami'an tsaro suke nema. . Bebi taji gabanta yafadi kana nufin kace dani ita ta kashe shi? Honorabil ya girgiza kai cikin damuwa babu tabbas amma sunanta ne a shafin zargi na farko honorabil ya danyi shiru sannan sai ya dago fuska ya dubi bebi ido da ido yace. Nayi Nadamar haduwa dake bebi da nasani daban dora idanuna akanki ba Bebi gashi yanzu kin sani acikin masifa bebi ta dafe kirji cikin kaduwar jin bakaken kalaman dake fitowa daga bakinsa. Haba darling me yayi zafi haka sai kace ni na kashe shi ni meye laifina acikin wannan al'amari ? Da bansanki ba da bazan taba mu'amala da mama ba abinda baki sani ba shine masu gadin gidan marigayi jatau ne suke bada shaidar sun ga mun shiga mu uku sannan mun fito nidake sun tabbatarwa da jami'an tsaro cewar acan gidan mama ta kwana. Akan dole aka takura ni na amsa cewa eh lallai haka akayi... Honorabil sabo yayi shiru ga mamakin bebi saitaga hawaye ya fara sartu akan fuskarsa. Kin cuceni bebi kin zamo sanadin barin kujerata domin idan wannan abun kunya yafito fili idan ya tabbata cewa mama ce ta kashe shi dole ne a tsigeni daga kujerata. . Mama bazata iya kashe mutum ba.... Wallahi nasan ko bera mama bazata iya kashewa ba. Honorabil sabo ya mike tsaye a fusace ya dubi rabi saikifito ki fada musu haka dan suna dakin shakatawa suna jiranki. Bebi taji gabanta ya fadi. Su wanene? Ta tambaya a tsorace. Jami'an tsaro zasuyi miki tambaya ki kuma kaisu inda zasu sami mama yana gama fadin haka saiya lalubi aljihunsa ya zaro naira dubu biyu ya jefa mata akan gadon sannan yace. Na baki minti goma ki hada kayanki gaba daya kifito ki bisu daga yau bana kara son ganin kodaddiyar fuskarki agidan nan Bebi ta fashe da kuka haba.... Darling kai da kace zaka aure ni yanzu duk zaman da mukaiyi da wannan zaka sakamin dubi fa wai da dubu biyu ma zaka sallameni. Honorabil jatau ya dubeta da murmushin yake sannan saiya sunkuya ya dauke dubu biyun daya bata. Sannan yace Idan bakyaso ni inada bukata domin banzan abinda gobe zatayi ba saikiyi sauri kada su gaji da jira yafice daga dakin cikin gaggawa. . BABI NA BIYAR 5 Fadila ta kalli fuskar wayar tafi da gidanka dake gabanta sannan saita rufe idanu ta fashe da kuka wayar taci gaba da ruri gashi dai tana ganin Faisal dinta ne ke kira amma batada ikon ta amsa wayar. Umarni ne na mahaifanta. Kada ki kara amsa wayarsa har sai mun gama aikin da zamuyi akanki.... Bakida lafiya fadila tabbas kin hadu da lalura babba. . Fadila ta tuno da maganar mahaifiyarta sa'ar da wayar taci gaba da ruri agabanta hawaye na zuba akan kyakkyawar fuskarta hannu na rawa ta dauko wayar ta danna gurin amsawa amma batace kala ba sai kawai ta kara a kunne tasan yanzu haka wani yana labe akusa da kofar yana sauraro datace Hello mahaifiyarta zatashigo ta hauta da fada dan haka sai fadila ta lumshe idanunta tana sauraron tattausan muryar faisal dinta acan daya bangaren kamar zai fashe da kuka yana cewa. . Fadila... Fadila yanzu bazaki amsa min ba nasan kina sona nima ina sonki Wallahi kuskure ne fadila... Hello dan Allah ki amsa min ko naji muryarki na sami saukin kunan zuciya.. Halo... Fadila. Fadila taji kamar ta amsa masa amma maimakon haka saita lumshe idanunta taci gaba da sauraron muryarsa tasan yasan tana sauraronsa kuma tasan tana son itama tayi magana dashi amma tasan baisan abinda ya hanata amsa masa ba. Idanunta a lumshe yanata surutunsa har kudin wayar suka kare. Maimakon fadila ta bude idanunta saita kara runtsesu zuciyarta tafara dawo mata da majigin rudanin da suka biyo bayan watanni uku da suka shude masu kama da shekaru uku agurin fadila. . Watanni uku sun shude kamar wasa abubuwa dayawa sun faru acikinsu harda takunkumin magana da ake sawa fadila. . Kin cuceni Fadila na sake ki saki biyu taji amsa kuwwar muryar datafi kauna fiyeda komai aduniya tana ruri cikin kwakwalwarta. Fadila bata taba ganin masifa irin ta wannan safiyar ba domin faisal dinta na gama furucin sakinta saiya rubuta a takarda ya jefa mata sannan ya fice abinsa fitarsa keda wuya aka fara tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya sai da fadila ta shafe sama da sa'a guda tana kuka daga karshe dai ta fahimci cewa koda fa kukan jini zatayi saidai jinin jikinta ya kare dan haka jiki na rawa zuciya na kuna ido na yararin ruwan hawaye fadila ta dauki yar karamar jala irin ta mata sannan ta kwashe duk hotunan da suka dauka ita da faisal dinta tun farkon soyayyarsu har zuwa daurin aurensu ta zuba acikin jakar daga wannan jakar bata dauki komai ba sai lemar faisal saboda ruwan da ake makawa. Ruwa na dukan rabin jikinta lemar dake hannunta kuma na kare wani bangaren a haka ta iso bakin titi neman mota duk kuwa da cewa filin fakin din katon gidansu na alfarma akwai manyan motoci sama da guda uku. Titunan babu kowa sai jifa jifan motoci da kuma yan kabu kabu da ruwan yagama jikawa ba'a dade ba fadila tayi sa'a wani dan mashin mai rumfa da taya uku launin rawaya ya tsaya agabanta jikinsa an rubuta ADAIDAITA SAHU wani bawan allah mai siffar kamala da dan gemu tsurut kamar jelar dawisu shike tuka wannan mashin. Tun kafinma fadila tagama bayanin inda zata mai mashin din yace ta shiga domin ya lura tana cikin matsanancin hali. Lokacin da fadila ta shiga babban dakin shakatawar gidansu ba karamin kaduwa tasa mahaifanta da kuma yan uwanta ba domin kannenta da wasu yan uwanta guda hudu sunci kwalliya jira sukeyi kawai a dauke ruwa akaisu gidan amarya kwatsam sai gata acikin dakin shakatawar ta jike shakaf da ruwa kamar algarar goro idanunta sunyi luhu luhu saboda kuka tana zuwa saita wuce gurin mahaifiyarta aguje ta fada akan cinyarta ta fashe da kuka. . An dauki sama da awa guda kafin ashawo kanta daga karshe dai mahaifiyarta da wata kanwar mahaifinta suka shiga da ita wani daki inda ta ZAYYANA musu wannan labari mai kama da Almara matan suka kwashi salati sa'ar da tagama basu labarin. Ba'afi sa'a biyu da zuwanta gida ba saiga mahaifin faisal da wani abokinsa sunzo gidan abubuwa suka dada rincabewa to Amma sa'ar da sukaji wannan labari sai suka baiwa iyayen fadila hakuri akan cewa shashanci ne irin na yaran zamani acewarsu duk da yake dai akwai matsala bai kamata dansu ya saketa ba to amma sun bada shawarar lallai adage mata da addu'a daga karshe mahaifin faisal yace zai dawo da magariba domin su tattauna yadda za'a shawo kan wannan al'amari don alokacin mahaifin Fadila baya nan haka nan mahaifin na faisal ya dada da cewa kada a sake a dauki koda Allura daga gidan yaran. Washegari aka tura malamai sukayi ta addu'o'i akan fadila baji bagani tun daga wannan rana kullum sai anyi mata addu'a watan farko daya biyo bayan faruwar al'amarin anso a mayar da auren faisal da fadila amma sai wani malami yabada shawarar abari tukunna agama yi mata addu'o'i domin in bahaka ba sai aljanin yaci gaba da wahalar da ita. Yaran zamani saidai hakuri amma suna da sakaci malamin ne ke yiwa mahaifin fadila bayani. Kaga yara ne idan zasu kwanta barci basusan suyi addu'a ba gashi Ayyatulqursiyyun nan duk kusan yaron dayan taba zuwa islamiyya ya haddaceta amma bazasu iya karantata ba idan sunzo kwanciya saidai suyita kallace kallacen fina finan banza su raba dare suna yi kuma da zarar sun tashi kwanciya kawai zasuyi babu wata addu'a. Wai to Allah gafarta malam meke faruwa ne matanmu ke fama da matsalar aljanun nan yanzu fa duk acikin mace goma baka rasa akalla guda biyar masu fama da matsalar aljani? Mahaifin fadila ya tambayi malamin. Wato Alhaji mafi yawan matan da jinnu ke hawa kansu sakaci ne kaga na farko da akwai zama da sukeyi cikin kazanta da rashin tsarki sun iya shafa mai da hota da turare amma jikinsu babu tsarki na biyu kuma akwai bayyana tsaraicinsu a fili wasu ma tsirara suke kwana wasu ko suyi ta yawo da kaya rabinsu tsirara ga barin gashi a waje duk wannan suke janyo hankalin aljanu su sami damar shiga jikinsu.... Wato abin dai Alhaji saidai addu'a yanzu in ba lalacewar zamani ba yaushe ne za'a ce wai ZAYYANA na kunshi ta wuce tafin hannuwa da kafafuwa ta kai har tsaraici kai Allah yayi mana tsari da wannan shaidanci. Ameen malam... Amin wannan duk ya farune watanni uku da suka shude. A tsayin wannan lokaci kullum sai anyiwa fadila addu'a da yan rubuce rubuce nasha. Mako guda da faruwar al'amarin ne watarana da yamma sai faisal ya bugowa fadila waya alokacin suna tare da mahaifiyarta fadila ta dubi wayar cikin tsanancin mamaki domin bata taba tsammanin bayan abinda yafaru faisal zai nemeta ba. Faisal ne tace da mahaifiyarta baki na rawa. Kada ki amsa... Rabu dashi dan banza marar mutunci sukayi shiru a dakin na nyan dakiku wayar nata ruri. Kada ki sake inji kin amsa wayarsa in ba rashin mutunci ba ko kwarto ya kamaki dashi a daki ai ya shawarci na gaba dashi kafin ya sakeki amma kwana daya kacal agidan ya sake mana ke dan wulakanci rabu dashi yayi tayi ko za'a mayar da auren nan saiya san darajarki tukunna dan banza mai manyan kunnuwa. Tun daga wannan rana har zuwa yanzun nan da fadila ke zaune tana tuna baya bata amsa masa waya ba. Sau daya dai hana rantsuwa ta taba kokarin ta amsa wayar sai mahaifiyarta ta kamata. Bakiji abinda nafada bako? To wallahi duk ranar da kika amsa saina kwace wayarki kin daina magana da kowa ma kuma babu inda zaki fita ko nan da kofar gidan har sai an gama yi miki addu'o'in nan uwar shegen taurin kan tsiya babu yadda banyi dake ba akan wannan shegen kunshin tsaraicin amma saida kikayi yanzu gashi nann kin hada mu da wahala da ganin wulakanci. . Fadila tayi ajiyar zuciya sa'ar data gama wannan dogon tunani adaidai lokacin ne kofar dakin ta bude mahaifiyarta ta shigo dauke da wani dan kofin tangaran a hannunta kamar jira ake ta shigo. Wayar ta sake daukar ruri Fadila ta kalli fuskar wayar Faisan ne ke kira. Shi din ne? Mahaifiyar ta tambata tana kallon yarta tausayinta ya kamata yau saura kwana biyu a gama mataaddu'o'in Da Akeyi. Wayar Taci gaba da ruri fadila taci gaba da zubar da hawaye. Amsa masa. Mahaifiyarta tace da yarta a tausashe sannan saita fice daga dakin. ** ** ** Safiya ce mai dauke da kurar hazo ga iska abin babu dadi ga sanyi kamar ya tsaga kashi jama'a sai korafi sukeyi kamar yadda suka sabayi akowane irin yanayi duk da cewa dai sanyin ya uzurawa kowa ya hana kowa sakat amma akwai wasu tsirari da suka dage akan cewa sufa har yanzu suna nan akan bakarsu cewa sunfi jin dadin sanyin nan akan zafi. Mama bata yarda da wannan ra'ayi ba domin katuwar rigar sanyi mai gashi kamar buzun malam data rufa akan damammun kayanta sun nuna hakan. Abakin titi take tsaye tana jiran tasi akan titin na'ibawa kanta boye cikin wata irin hular gashi haka nan kafafunta ma boye suke cikin takalmi sau ciki irin na mata hatta hannayenta boye suke cikin bakaken safa ka karamar kaduwa Mama tayi ba sa'ar dataga wani dan cuwa cuwar Mai abakin titi ya dauko jarkan mai daga shi sai gajeren wando da wata yar jeleliyar riga singileti mai kamar hanci yana tafe abinsa yana fito kai kace abakin kogi yake lokacin zafi. Oh... Inda ranka kasha kallo mama tace azuciyarta tana kallon saurayin cikin mamaki sannan saita dawo da hankalinta kan matsalar dake gabanta ba'afi mintina biyu da faruwar hakan ba dan tasi ya tsaya agabanta mama ta fada masa inda zai kaita dan tasi ya cajeta kudi da yawa domin inda zai kaita mota bata zuwa gurin domin gindin wani dutse zai kaita gurin wani BOKA dake bayan wani kauye ahanyar Wudil. Mama ta shiga bayan motar ta zauna bata damu da yawan kudin daya cajeta ba domin kudi ayanzu ba matsalarta bane tun da dai haryanzu akwai sama da naira dubu dari hudu acikin asusunta kudin da Alhaji Bilyaminu ya bata domin ta sayi mota abinda yafi damunta ayanzu shine ta kubuta daga hannun mugun aljanin daya sata gaba tuni kasuwarta ta gama mutuwa a jihar kano duk wanda kaga ya kulata to rashin sani ne shima da an fada masa zai tsere ya barta. Jikin mama ya dauki rawa abayan motar sa'ar da tuna wannan muguwar rana watanni uku da suka wuce Ta tuno sa'ar da Alhaji bilyaminu ya fadi a tsakar dakinta yana ihu hannu da kafafunsa duk sun shany sun koma kamar maburgin miya. A lokacin mama tasan abinda ke faruwa musamman ma sa'ar dataji an kece da mahaukaciyar dariyar nan acikin firgici sai mama tasa kururuwa sannan ta fito daga cikin dakin aguje ta nufi kofar gida tana ihun akawo mata agaji kafin kiftawa da bisimilla gidan ya cika da jama'a wasu ko sukace bazasu motsa ko nan da can ba dan daman rashin kunyar mama ta gama isarsu. Aranar da daddare a filin INDA RANKA na gidan radio Freedom suka yayata wannan labari mai kamar almara harma sun sami damar zantawa da mama wacce tayi bayanin wannan masifa data sameta daga yin wannan kunshi na zamani jama'a sukayita fadil ra'ayoyinsu akan wannan al'amari wasu suka tausayawa mata wasu ko sukace Allah ya kara ai yanzu ta daina karuwanci tunda aljani fara buge manemanta saida aka shafe sama da sati guda jama'a na sunturi zuwa gidan mama domin su ganta. Dan haka saida takai idan mama tabar gidan da sassafe bata dawowa sai tsakar dare mama tariga tasan in badan kudin da Alhaji Bilyaminu ya bata ba da sai zaman kano ya gagareta watanni uku da suka shude ko kuda baya sunsunata idan kaga dan duniya ya kulata to bako ne. Wannan al'amura su suka taru suka dami mama domin ta riga tasani bata da wata sana'a data wuce karuwanci takuma riga tasani duk namijin daya rabeta ya shiga uku shin kudin dake hannunta kwana nawa zasuyi kafin su kare idan kuma sun kare din tayaya zata sake samun wasu? Wannan sune tambayoyin da suka addabi zuciyar mama da farko ta yanke shawarar tun da yanzu tanada yan kudi ta samo dan yaro kawai ta aura ta huta da wannan masifa Nan da nan wannan tunani ya rushe kamar yadda ruwa ke rusa tubalin toka tabbas idan har ba Aljanin nan aka rabata dashi ba mama tasan wani namiji bazai kara rabarta ba. Wannan shiya tashi hankalin mama ta tashi tsaye wajen neman magani. To saidai kuma a tunanin mama bokaye ne kawai zasu iya rabata da wannan aljani wata kawarta ta taba cewa da ita wai bokaye da aljanu suke kwana a dakunansu wai har da akwai bokan da yake kwana da aljanu miliyan guda hakan kawar mama ta dada cewa wai boka na iya kiran kowane irin aljani ne ke damunta ya tsawatar masa cewa kada ya kuma damunta idan aljanin yayi gardama wai za'ayi zane shi. Imani da wannan tatsuniya su suka sa mama bin bokaye wannan boka da mama ta nufi gidansa ayanzu shine boka na goma sha daya da zataje gurinsa acikin watanni uku da suka wuce tuni mama ta sayi saji sama da guda dari biyu. . Karfe sha biyu saura suka isa gindin dutsen tsaya nan ka jirani mama tace da direban ma'abocin tarin gashin baki kamar tsohon soja zaki dade acan ne? Meya shafe ka kaidai ba aikin kudi kakeyi ba? Direban ya dubeta da murmushi cikin jin dadin cewa tata Fadi Gasassa. . Gaskiya ne ranki ya dade ina nan ina jira nasan dai ai ma tafi nan da magariba ko? Waya sani ko anan zamu kwana mama tace cikin gatse sannan ta nufi gindin dutsen cikin sauri Tuni mama ta riga ta gama yanke shawarar cikin zuciyarta cewa idan har wannan boka bai rabata da wannan aljani ba to kasar nijar zata shiga me yiwuwa ko zata dace acan tun da dai gashi yau kusan sati uku kenan babu ko saurayi daya daga cikin tsofaffin samarinta daya mata waya. Wannan abu na tada hankalin mama domin ada kullum ba'a kirata ba a kirata sau saba'in sai gashi yanzu ko flashing ya gagara. . Sannunki da zuwa tun jiya daman na ganki tafe.... Yar mitsitsiya ce ta kawomin labarinki ta fada min abinda ke tafe dake amma duk da haka dai zanso inji matsalar daga bakinki. Bokane ke fadin haka. Mama ta zube agaban bokan kamar zata fashe da kuka tace cikin karyayyar murya. Malam... Boka wani aljani ne ke damuna kwata kwata ya hana maza su saurareni mama taci gaba dayi masa dogon bayanin abubuwan dake faruwa akanta kamar yadda ta saba yiwa sauran bokayen da taje gurinsu abaya. Baibayau ne.... Dan banza tabbas Dabaibayau ne ai dan banzan aljani sa'a ma kikayi ai da kika zo nan amma da kin kara wata guda baki zo ba gurgunta ki zaiyi tunda kikace har cinyoyinki ya taba lokacin da yakeyi miki Kunshin. Mama ta rike numfashi a tsorace gurgunta ni fa kace? Kwarai kuwa... Amma kada ki damu ai kinyi sa'a tunda kikazo gurina rufe idanunki bokan ya umarce ta Jiki na rawa mama ta rufe idanunta Bude su bokan ya sake umartarta mama ta bude sake rufewa Mama ta sake rufe idanunta akaro na farko. Sake budewa mama ta sake bude idanu ga mamakinta sai taga wani katon koko agabansa cike da layu iri iri wasu kamar kuli kuli wasu kamar ya'yan barkono wasu kuwa manya manya masu siffar makani. Sake rufe idanunki ki dauki daya bokan ya umarce ta cikin karaji. Jiki na rawa mama ta rufe idanu sannan ta tura hannunta cikin kokon ta dauko laya daya. Bude idanunki ki bani ita mama ta bude idanu lokaci guda kuma ta mika masa layar. Tsawon dakiku bokan ya jujjuya layar a hannu can sai yayi ajiyar zuciya ya dubi mama. Kin hadu da dan banzan aljani mai nacin tsiya amma daga yau din nan kin rabu dashi. Bokan ya danyi shiru yana kallonta. Zamu bukaci ayanka fararen zakaru goma jajaye goma bakake goma dole ne kuma ayankawa aljani dabaibayau burgun gafiya biyar da zomaye uku. Mama tayi ajiyar zuciya ta dubi bokan baki na rawa tace Ko nawa ne zan biya sai asaya in dai zan rabu da wannan jaraba. Ungo rike nan bokan ya mika mata yar karamar layar data zabo mai kamar barkono. Idan kinji gida yanzu kisa ayi miki kitso da wannan layar a tsakanin gashinki kada ki sake ki tsefe sai bayan kwana bakwai alokacin ne zanyi miki duk aikin da kike bukata idan muka yanka duk abubuwan dana lissafa miki abaya aljani dabaibayau zai shanye jinin shikenan kun rabu dashi har abada in dai kina tare da wannan layar. Kana nufin da layar zanyi ta yawo akaina har abada ? Boka ya girgiza kai zaki iya cirewa bayan kwana bakwai amma ki tabbata duk inda zaki kina tare da wannan layar. Na fahimta mama tace baki na rawa sannan saita bude jaka ta kirgi wasu adadin kudi masu yawan yan dubu dubu ta mika masa. Ajje anan bokan yace da ita sannan saiya dubeta ido da ido yace. Idan kwanaki bakwan nan sun cika kina iya kiran duk namijin da kikayi niyya zaizo kuma idan kin nemi aurensa ma zai yarda. Adaidai wannan lokaci sai MUBARAK yafadowa mama arai kana nufin kowa nace ya aure ni sai yayi? Kwarai kuwa dan dole mutum ma sai ya aureki domin ai aljanin ne ke hanasu zuwa shi yake dabaibaye su. Mama ta lumshe idanu cikin jin dadi duk duniya babu wanda take so kamar wani takadirin saurayi alayinsu waishi Mubarak to saidai kuma ya tsaneta domin ko gaida shi tayi mubarak baya amsawa. Wani busashshen murmushin mugunta ya subuce a gefen bakin mama. Shege uban girman kan tsiya shi zan aura mama tace da kanta. *** ** ** ** Acikin wani katon dakin shakatawa ma'abacin yalwa wanda ke dauke da kujerun alfarma sunyi sahu sahu kamar a filin fareti wani tsohon kwamishina ne zaune daga shi sai farar singileti da farin wando na shadda mai tazuge jarida a hannunsa yana dubawa ta saman dan siririn tabarau fari wanda ke zaune daraf a saman dogon hancinsa mai kamar na aku. Lokacin da yana saurayi kafin zamani da tsufa su cimmasa wata kyakkyawar budurwa ta taba cewa dashi. Wallahi kana burgeni... Saboda dogon hancin nan naka. Ai kuwa kya yi kya bari an ni ko burge ni bakyayi. Ya mayar mata da martani a takea agurin mutum ne mai son gwale mutane sam sam ba'a yi masa daidai gashi baha'i murdadde duk lokacin da jama'a suka karkata dama shi sai yayi hagu idan akayi gaba shi sai yayi yamma. Wannan fa duk mai sauki ne idan aka kwatanta da halayarsa ta muguwar gardama domin idan ya tsaya akan ra'ayi babu wanda ya isa ya sauya masa tunani koda kuwa abinda ya tsaya akai ba daidai bane. Wannan tsohon kwamishina sunansa Alhaji Ilyaskuma shine mahaifin Farida. . Mutumin ya dago kai daga kan jaridar da yake karantawa sannan ya dubi inda farida take a takura agefen wata kujera tana sharbar kuka tun idanunta na zubar da hawaye har sun kafe babu komai sai majinar datake zuba daga hancinta. Ko kukan jini zakiyi sai kin aure shi tunda kin raina mutane. Farida ta sake fashewa da kuka. Adaidai wannan lokacin ne mahaifiyarta tashigo dakin fuskarta a murtuke yar gajeriyar mata ce fara kyakkyawa tana dauke da zanen kalangu agefen fuskarta hagu da dama. Alhaji ni dai wallahi abin nan ba sonsa nake ba kai kuma idan ka kafe akan abu ka kafe kenan saikayi amma in ba haka ba kasan lalurar dake kan yarinyar nan ka bari ayi mata magani kaki kuma gashi sai kokari kake ka hadata da wanda bata so mutumin da ko ganinsa bata tabayi ba. Alhaji Ilyasu ya ajje jaridar dake hannunsa ahankali agefen kujerar ya dubi matarsa sannan ya dubi yarsa cikin kunan rai Idan ma bata taba ganinsa ba yau zata fara zaman da nake yanzu shi nake jira su gana dan ko tana so ko bata so nan da sati guda za'a daura musu aure. Mahaifiyar farida ta rike numfashi cikin kaduwa. Rana ita yau fa kace? Haba alhaji wannan abu kamar kasha kwaya yarinyar da...... . Alhaji ilyasu ya katseta ta hanyar daga yan siraran hannunsa masu kama da muciya babu wanda ya isa ya saura min ra'ayina kinaji ko? Daman ai ke kike daure mata gindi take duk iya shegen da taga dama kullum tana tara mana yan iska a kofar gida to wallahi ko mutuwa zatayi saina daura mata aure rana ita yau Aljanin karyar da take baki labari saidai ya kasheta karyar banza karyar wofi in ba ta raina mutane ba ke kintaba ganin inda Aljani yayiwa mutum Kunshi? Farida dake zaune agefensu ta fashe da kuka kasa kasa sannan ta runtse idanunta kana ta rufe kunnuwanta da tafin hannayenta ko kusa ko alama bata kaunar kalaman dake fita daga bakin mahaifinta dan me zaice labarinta karya ne kodon baiga abinda ya samu kabir bane kuma baiga abinda ya sami baba ali ba. . Zuciyar farida ta hasko mata bakin titin gwarzo watanni uku da suka wuce sa'ar data rugo aguje zuwa bakin titin. Wayyo Allah dan Allah ku taimakeni farida ta kwalla ihu sa'ar data hangi wasu mutane hudu suna gudun motsa jiki nan da nan mutanen hudu suka dawo izuwa gareta. Ke menene? Wani daga cikinsu ya daka mata tsawa da wata kakkausar murya. Shine... Yana ciki. Fadila tace a rude tana nuna bayan dutsen cikin duhun daren. Tsaya nan muna zuwa katon mutumin yace da ita sannan sai suka ruga aguje zuwa bayan dutsen abinda Farida bata sani ba shi kartin mutanen wasu sojoji ne daga

Chapter 5 of 7