Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
sannan sai Ya mika hannu zuwa kan wani karamin teburi adab da gadon ya kunna wata irin fitila mai malafa nan da nan wani tattausan haske mara kashe idanu ya mamaye dakin. . Honorabil jatau ya mike tsaye a tsakiyar dakin sannan ya kurawa mama idanu wacce ke kwance akan gadon tana barci abinta cikin nutsuwa hakika nayi sa'ar yarinya jatau yace aransa sannan ya nufi bandakin dake fuskantar dakin kwanan domin mararsa tayi nauyi tun wajen karfe ukun dare yake jin fitsari amma yakasa tashi yaje yayi. Honorabil ya tura kofar bandakin ahankali ya shiga sannan sai yayi turus akofar cikin mamaki sa'ar dayaji zubar ruwa acikin bandakin. Mamaki da fargaba suka mamayi zuciyarsa lokaci guda kuma domin shi yasan su biyu ne kawai adakin haka nan ya tabbata bai bar famfo a bude ba. Shigo mana yaka tsaya anan nima fitsarin ne ya tashe ni naso in tabaka sainaga kamar kanajin dadin barcin wata MAMA ce tsaye acikin bandakin sanye da doguwar riga irinta waccan Mamar daya bari yanzun nan akan gado tana barci. Cikin tsananin firgici honorabil ya dubi mamar dake tsaye cikin bandaki yace bakinsa na rawa. Bake na gani yanzun nan a kwance akan gado ba? Mama ta girgiza kai cikin mamaki sannan ta haske shi da murmushi kodai tarin wannan katon bargon naka mai gashi ka gani kake zaton nice? Honorabil ya girgiza kai a tsorace sannan sai ya dubeta yace Jirani anan ina zuwa. Jiki na rawa ya nufi cikin dakin kwanansu tun kafin ya karasa bakin gadon sai wata Mamar ta mike zaune akan gadon tace. Wallahi harka bani tsoro inaka tafi na farka ban ganka ba? Honorabil jatau ya dubi kofar bandakin a tsorace sannan sai ya zauna akan gadon ya dubi mama yace a firgice. Bake nagani yanzun nan a bandaki ba? Mama ta girgiza kai sannan ta matso ta kwanta akan cinyarsa yan yatsunta akan katon tumbinsa tace. Kaifa baka rabuwa da abin dariya yaya gani anan tare dakai zakace wai ka ganni yanzu a bandaki. Mama ina ganin.......Kalmar ta makale a makwogwaron honorabil sa'ar dayaji wasu irin Farata masu kamar karfe sun nutse acikin tumbinsa. Honorabil ya bude baki zaiyi ihu amma sautin bai sami fitowa daga bakinsa ba. Aka kece da wata mahaukaciyar dariya sannan sai wani farin hayaki ya turnuke dakin. Waya fadama wani katon banza maci amanar iyalinsa yana taba min mata wata kakkausar murya tace daga sama. Mama tafito aguje daga cikin bandakin a tsorace sa'ar dataji mahaukaciyar dariyar tana zuwa bakin gadon sai tayi turus. Akwance akan gadon harshensa ya zazzago waje hanjinsa awaje jini ko ina akan gadon Honorabil Jatau Ne. ** ** ** ** ** Yaya zaka fita baka bada kudin yaran nan na zuwa makaranta ba. Wata katuwar matace uwar gidan Alhaji bilyaminu ke fada masa wannan kalma. Ke dai wallahi bakya gode Allah.... Yanzu kudin makarantar ma saina basu ke bazaki iya basu ba. Kaidai baka tsoron Allah alhaji yanzu tsakani da Allah aikin me nakeyi da zan sami kudin da zan biya dawainiyar makarantar yara haba alhaji wallahi ya kamata ka rage irin wannan mugun hali naka yanzu kadubi yarannan kanana sai yawo suke acikin tsumma kamar ya'yan almajirai? Ka dubi manyan ya'yanka nan duk abokansa da motocin hawa amma kai dan mugun hali da matsolanci ko dan lifan babur din zamanin nan ka kasa saya musu suna zuwa makaranta. Alhaji bilyaminu ya katseta ta hanyar daga mata hannu kinga dan Allah sauri nake ni ban tambayeki wa'azi ba na rediyo ma danakeji kullum kwanan duniya ya isheni yanzu dai ga naira dari hudu nan ki rarraba musu su tafi in sunje sacewa malamin gobe za'a kawo kudin makarantar. Matar ta dubi kudin daya mika mata cikin takaici. To in ka bada wannan yaya zamuyi da maganar abinci kuma? Na fa fada ma tun jiya bamuda ko kwayar shinkafa daya agidan nan waken ma yakare gashi ma jibi za'a mayar dasu MAMI DA HAFSAT makaranta... Zan turo yanzun nan akawo buhun masara dana wake dakuma fulawa yana gama fadin haka sai ya nufi gajeri inda motarsa take cikin sauri yana duban agogo. Karfe hudu da rabi na yamma. Matar ta share hawayen bakin ciki dake sartu akan kumatunta sannan saitace cikin sheshshekar kuka Allah idan munada hakki akan wannan mutumin dayake zaluntar mu Allah ka bi mana hakkinmu. . Acan cikin gareji Alhaji Bilyaminu ya bude motarsa yashiga sannan yafice aguje wani yaro mukhtar yazo da sauri ya rufe garejin. Koda yafara tafiya cikin motar saiya dauki wayarsa ya danna wata lamba sannan ya kara a kunne. Hello mama kina jina Eh ina jinka akace acan daya bangaren cikin sheshshekar kuka meya samiki naji kamar kina kuka? Kaina ne ke ciwo...Mama tayi masa karya Toh Allah ya sauwake Alhaji bilyaminu yace sannan saiya dada dacewa kije bankinki ki duba na turo miki da kudin sayen motar amma dubu dari biyar kawai aka samu. Da'ace jiyane da ba karamin farin ciki maganar zatasa mama ba amma abin daya faru adaren jiya yagama fitar mata da sha'awar komai aduniya. . Sa'ar da mama ta tabbata aljanin dayayi musu zanen kunshine ya kashe Jatau saita hada nata ya nata gari na wayewa ta baro abuja mama tayi sa'a domin ta sami wata gantalalliyar naira dubu acikin hular honarabil jatau dake falon gidan. Duka duka batafi sa'o'i hudu da sauka ba Alhaji bilyaminu ya bugo mata wayar. Saukarta keda wuya ta kunna rediyo domin jin labaran BBC na rana kamar yadda ta tsammata tun farko sun fadi labarin rasuwar honorabil jatau acewarsu ana zaton yan fashine suka kashe shi to amma haryanzu babu tabbacin iya adadin kudin da suka sata daga nan ba'a sake wani kwakkwaran bayani ba akan rasuwat tasa sai jifa jifan bayanai da aka dauka daga bakin wasu abokan aikinsa yan majalisu. Ayanzu haka da mama take zaune jira take taji kawarta bebi ta bugo mata waya ko kuma saurayinta honorabil sabo domin jin inda take amma ga mamakinta har yanzu shiru haka nan dataji wayarta ta dauki ruri ma ta dauka su ne sai kuma taga ashe saurayinta ne na kano Alhaji Bilyaminu. . Yaya naji kinyi shiru ko bakiji dadin abinda nayi bane? Naji. Mama tace dashi a takaice. Yauwwa ko kefa Alhaji bilyaminu yace baki na rawa. Yanzu sai yaushe zaki dawo din? Na dawo ma. Kina nufin yanzu kina nan kano? Eh ina gida gani nan zuwa yanzu Alhaji Bilyaminu yace sannan saiya karkata kan motarsa ya sauya hanya ya fasa zuwa bikin saukar karatun kur'ani da aka gayyace shi. *** Me ke damuna ne? Alhaji bilyaminu ya tambayi kansa sa'ar da yayi fakin da motarsa akofar gidansu mama dake Na'ibawa. Shi kansa abin na bashi mamaki irin yadda yaga ya damu da mama sosai a yan kwanakin nan. Adacan lokacin da suka fara alaka sam sam bata gabansa ya dai dauke ta ne kamar sauran matan da suke mu'amala a hadu ayi harka a watse babu wata dangantaka mai tsayi. Ayanzu da Alhaji yayi fakin da motar a kofar gidan ji yake yi kama ma zai iya auren mama saboda irin kaunar da yaji tana kwarara acikin zuciyarsa. Alhaji bilyaminu yafito daga motar ya rufe sannan ya nufi cikin gidan kai tsaye abinka da wanda ya saba shiga. Ya riga yasan mata biyu ne kawai acikin gidan daga Mama sai wata inyamura wacce ke aiki a kamfanin magani. Mafi yawan lokuta baifiye isketa agidan ba amma duk sa'are da akayi dace ya sami inyamurar agida in zai fito sai ya jefe ta da dari biyar badan komai ba sai don kawai yana son ya burge mama. Kwan...kwan kina ciki ne Alhaji bilyaminu yace sa'ar daya shiga farfajiyar gidan yana wani bubbudewa waishi ga dan duniya ina nan shigo ciki mama tace jikinsa na rawa gamida dokin ganinta alhaji bilyaminu yashiga dakin sannan ya zauna akan gado kusa da mama Kai yau ana zafi ki kunna AC mana jiki ba laka kamar kazar da kwai ya fashewa aciki mama ta mike sannan ta nufi makunnin na'urar sanyaya dakin ta kunna. Tun da yanzu mun gama da maganar mota kamata kuma yayi ace na saya miki gida Alhaji bilyaminu yace yana kallon irin kirar da Allah yayi mata sai yaga kamar ta kara kyau. Azuciyarsa yana cewa idan na rabu da mama bazan sake samun wata mace aduniya kamarta ba. Mama ta dawo kusa dashi ta zauna. Kai din ne zaka iya sayawa mutum gida? Wannan ma sa'a akayi kasa kudin shima saida ka Kwangemin naira dubi dari Alhaji bilyaminu ya cire babbar riga gamida hularsa ya ajiye agefen gadon sannan ya shafi dogon sankonsa daidai lokacin da sassanyar iskar ta fara fifitashi Da'ace hajiya mai gidan nan zata amince da wannan gidan da kike ciki zan saya miki. Allah sa. Mama tace a yatsine sannan ta dubi wayarta tana mai mamakin abinda yasa haryanzu su bebi basu nemeta ba anya kuwa yan sanda ba nemanta sukeyi ba tasan babu abinda zai hana ace ita ta kashe shi. Tunanin me kikeyi naga kinyi shiru? Alhaji bilyaminu ya bukata Tunanin rayuwa mana Haba mama kedai kin fiye damun kanki wallahi menene yayi zafi haka da har ya gagari ruwan sanyin da zamu zuba masa? Mama tayi shiru bata bashi amsa ba lokaci guda kuma tana dan wasa da yan yatsun hannunta zamansa adakin tuni ya gama gundurarta domin duk hankalin ta yana abuja. Saidai babu yadda ta iya tunda dai ya zuba mata naira dubi dari biyar a asusunta in banda wannan da tuni ta fatattake shi nan da nan saita sami kanta tana mai addu'ar inama dai ya gaggauta yayi abinda zaiyi ya fice ko ya kyaleta da abinda ke damunta. Na dade banga murmushin ki ba dan Allah ki saki fuskarki mana ko ayi mana ruwan sama. Mama ta saki wani busashshen murmushin yake ta dubi Alhaji mai dogon sanko tace Kaidai Alhaji baka girma Alhaji bilyaminu ya kwanta ajikinta sannan ya kama hannayenta yace in har zan tsufa da wannan harka to kuwa ina tabbatar miki cewa harshe ma zai tuba da yawan surutu. . Amma kuwa kayi asara mama tace cikin zuciyarta in banda sha'anin karuwanci mace batada zabi da babu abinda zaisa ta mu'amala da dattijo kamar wannan dan kusan shekara sittin shi yasa a kullum ta tuna da tarihin da ake ta fada mata tun tana karama saita jinjinawa mahaifinta domin akalla dai shi bai yarda sunyi zaman banza da mahaifiyarta ba aurenta yayi. . Kai amma fa zanen kunshin nan naki yayi kyau Alhaji bilyaminu yace lokaci guda kuma ya tura mama ahankali ya kwantar da ita akan gadon sannan ya sake duban hannunta yace kai kunshin nan naki ya zanu ZIZI. . Yana gama fadin haka sai yasa hannunsa ya shafi zanen dake hannunta awannan lokacin ne to yaga kakkauran hannunsa ya zuke yakoma kamar lawurjen wando. Kai-Kai meye haka? Alhaji Bilyaminu yace a tsorace yana kallon hannunsa. Mama ta tashi zaune a tsorace domin tariga tasan abinda ke shirin faruwa tashinta keda wuya sai taga hannun Alhaji Bilyaminu ya shanye yakoma kamar maburgi sannan ahankali sai na hagun ma ya zuke nan take. Wayyo Allah... Wayyo na shiga uku Alhaji bilyaminu yasa ihu agigice sannan ya mike tsaye zaifito aguje daga dakin. Taku uku kawai yayi sai ya zame ya fadi kafafunsa ma sun shanye bazasu iya daukar nauyinsa ba. . Aka kece da mahaukaciyar dariyar nan sannan sai kakkausar muryar tace Daga yau bazaka sake shafar hannun matar kowa ba ballantana tawa. . BABI NA HUDU 4 Faisal yayi fakin da motar akusa da sauran motocinsu guda uku ya bude kofar motarsa yafito da lema ahannu domin ruwan saman ya dada kecewa kamar da bakin kwarya Tabbas laifina ne faisal ya fadawa kansa sa'ar daya nufi inda ginin gidan yake agaggauce yana tafiya iska na dawo dashi baya sakamakon lemar dake hannunsa kodayake dai lalura ce ta kawo haka. Faisal ya kuma fadawa zuciyarsa idan ba rashin lafiyar mahaifiya ba me zaisa na in tafi nabar sabuwar amarya ta kwana daya kacal da tarewa har kusan goma sha biyun dare ban dawo gida ba gashi nan yanzu na barta ana neman a tsorata min ita yaya zatace wai nine kwance kusa da ita? Ahaka yana wannan tunani har ya shiga cikin dakin kwanansu. Sannan ne to yayi turus yana kallon Fadila wacce ke zaune akan matashin kai ta takure ajikin bango daga can kuryar daki tana sharbar kuka. . Daina kuka gani nadawo... Fadamin duk abinda ke faruwa fadila ta dubi fuskar mijinta a rude tasan abin kenan da yakamata tayi ta fada masa dukkan abinda yafaru tun daga ranar da sukaje kunshi gidan dan daudun har zuwa yanzu sai dai tambayar anan itace anya kuwa faisal zai iya amincewa da wannan labari mai kamar tatsuniya. Faisal ya matsa kusa da amaryarsa ya zauna sannan ya mika hannu zai janyota jikinsa sai yaga ta janye jikinta cikin sauri. Meye kuma haka wai meke damunki ne ki fadamin mana. Fadila ta dubeshi cikin sheshshekar kuka wani aljani ne ke damuna faisal shine yazo min a siffarka. Faisal ya dubi fadila a rude azuciyarsa yana cewa anya kuwa yarinyar nan ba tabuwa tayi ba. Aljani fa kikace mai siffanta a kwance akusa dake to yanzu yana ina? Faisal ya tambayeta akwai alamun zargi karara akan fuskarsa. Ya bace... Kanayi min waya ya bace Faisal ya girgiza kai sannan ya dubeta da murmushi yace Kinga fadila kin kwantar da hankalinki kawai babu wani abu da zai sake faruwa tunda gani na dawo ina ganin tsorata kawai kikayi ganin bana nan shine kika fara gane gane. Daman na sani wannan ma bai yarda ba to yaya kuma idan na bashi labarin gidan kunshi fadila ta fada aranta. Come On fadilata zo nan ki kwanta faisal yace yana nuna mata kan cinyarsa cikin lallashi Cikin sauri fadila ta dada janye jikinta ta dada mannewa da bangon kamar zata huda bangon ta shige ciki Faisal ya dubi amaryarsa cikin tsananin mamaki sannan saiya mike tsaye akan gadon a dudduke ya nufi inda take zai janyota jikinsa lokaci guda kuma yana cewa zo nan mana kefa wallahi kin cika rudewa da yawa. Kada ka tabani dan Allah fadila ta roke shi cikin karaji yanzu kam ta riga ta sani rayuwarta data mijinta suna cikin hadari. Me kike nufi ba zan tabaki ba fadila? Faisal ya tambaya akwai alamun sosuwar zuciya akan fuskarsa. Nidai nace kada ka tabani dan Allah zanyi ma bayani cikin fushi sai faisal yakai mata cafka ya fizgota jikinsa tana fadowa zai zanin dake jikinta ya fadi sannan ne to faisal yayi sororo yana kallon abin mamaki tun daga kasanta har zuwa kan kirjin amaryarsa fadila zanen furanni ne kunshin zamani irin wanda yace tayi masa kafin akawota batayi ba. . Tambayar farko data fara zuwa zuciyarsa itace yaushe har farida ta fita akayi mata wannan zanen ita da aka kawota gidan jiya jiyan nan faisal ya dubi amaryarsa fadila wacce ke kwance rub da ciki akan cinyarsa tana kuka. Yaushe kika fita akayi miki wannan? Ya tambayeta akwai alamun zargi karara a yanayin sautin muryarsa. Fadila tayi ajiyar zuciya ta riga tasan an rutsata bata da mafita dolene ta fada masa gaskiyar al'amarin ko ya yarda ko kada ya yarda. Kayi hakuri Faisal.... Wallahi agidan wani dan daudu mukaje yayi... Me faisal ya daka mata tsawa cikin kaduwa gidan dan daudu....kai amma fadila kin cuceni yanzu daga kawo min ke jiya shine har kika fita unguwa batareda kin fadamin ba kikaje kika budewa wani katon banza tsaraicinki yanayi miki zane Wallahi kin cuceni yana gama fadin haka sai ya turar da ita gefe guda ya tashi tsaye. Fadila ta fashe da kuka tsaya kaji dan Allah faisal bari na karasa maka abin.... Babu wata magana da zan sake saurara daga bakin kifaisal yace bakinsa na kumfa saboda tsabar zafin zuciya. Shine da kika fake da aljani zakiyi masa karya.... Waya sani ma ko dan daudun kika kawomin gida kikace wai aljani ne a kwance kusa dake... Allah ya isa tsakanina dake fadila. . Fadila ta kife kai akan gadon ta fara rusa kuka Ahaka suka wayi gari ita tana cikin dakin kwanansu tana rusa kuka shi kuwa yana falo zaune akan kujera hawayen bakin ciki na zuba akan kumatunsa gari na wayewa ya mika mata takarda. NA SAKE KI SAKI BIYU 2. ** ** ** ** ** Farida na zaune agefe guda tana sheshshekar kuka yayinda dalibai keta tururuwa daga dakin kwanan dalibai zuwa kallon kabir wanda ke kwance akan wani daben siminti wasu tsofafaffi uku sun zagaye shi suna tofe shi da yawu daga baya bayan cincirindon daliban wasu masu karancin kunya sun fara gunaguni me zai hana a tafi dashi asibiri tunda dai ga bakinsa nan har jini yakeyi. Duk wannan rudani da akeyi farida na can gefe nesa dasu bama kowa yake lura da ita ba domin hankalin jama'a na kan kabir wanda ke kwance yana murkususu gashi kuma daman ma duhun dare tuni ya gama shigowa dan haka su kansu tsofaffin dakeyi masa addu'a saida wasu samari suka taimaka wajen haske gurin da fitilolin dake jikin wayarsu. . Ana cikin wannan rudani sai farida taji wayarta ta fara ruri ajakarta hakan shi yadawo da ita cikin hankalinta akaro na farko tasan cewa daga gidane meyiwa ake nemanta jiki na rawa ta zaro wayarta daga cikin jaka sannan ta kara a kunne. Hello tace da wata malalaciyar murya Farida...Farida nine baba ali Alhaji yadawo na fada masa abinda kikace na fada shine yace in taho yanzu yanzun nan na mayar dake gida kina ina? Farida ta lumshe idanu tana sauraron sa har sa'ar daya gama sannan sai ta kuma cewa cikin malalaciyar murya Taho mu tafi zan jiraka a filin fakin. Gama fadin haka keda wuya saita zagaye taron jama'a tabi duhun dare ta wuce kai tsaye zuwa filin fakin. Ayanzu duk abubuwan da suke faruwa sun fara dawowa cikin zuciyarta garai garai tabbas tasan da kabir bai matsanta mata ba daya bari sun zauna hirar arziki batareda yayi kokarin turo bakinsa izuwa sumbatarta ba to da yanzu yana nan lafiyarsa kalau. Kabir shi ya janyowa kansa... Ba laifina bane farida ta kuma jaddadawa kanta amma duk da haka dai ta tausayawa kabir musamman da taga bakinsa ya koma baya. Tana nan tsaye ita kadai a tsakankanin daidaikun motocin da suka rage a filin fakin din zuciyarta lullube da duhun rudanin dake tattare da rayuwarta ta kasa tunanin komai ahaka direbanta baba ali ya sameta. Tunanin me kikeyi ne? Ya tambayeta cikin mamaki sa'ar daya tsaya akusa da ita domin yaga hon dinsa uku bata juya ba farida tayi firgigit kamar wacce ta tashi daga wani nannauyan barci ta dubeshi sannan ta juyo tayiwa inda kabir ke kwance ganin karshe. . Kace baba ya dawo? Ta tambaya batareda ta kalli baba ali ba lokaci guda kuma ta bude gidan baya na motar ta shige ta zauna Tun dazu ya dawo...misalin biyar da rabi na dauko shi a filin saukar jirage ya tambayeni ke sainace dashi jarrabawar gwaji kikeyi ba zaku tashi ba sai karfe takwas baba ali ke fadin haka amma bai yarda sun hada idanu da ita ba. Uhm abinda farida tace kenan azuciyarta tana mamaki domin bata taba ganin mahaifinta yadawo karfe biyar da rabi ba. Dattijo baba ali ya tuka motar ahankali ya nufi kofar fitar daga sabuwar jami'ar bayero ta kano lokaci guda kuma ya gyara madubin gaban motar na sama ta yadda zaike iya samun damar satar kallon fuskar farida shirun da tayi da kuma irin yanayin fuskarsa awannan lokaci yafara damun zuciyarsa duk da yake dai har yanzu nan zuciyarsa bata karaya ba tun da dai daman kome zai faruma ai ba'a son ranta za'ayi ba. Sannu ahankali suka kawo kofar fita daga sabuwar jami'ar bayaro direba baba ali ya mikawa mai gadi balgacaccen jar roban da ake baiwa duk wanda zai shiga jami'ar amatsayin shaida yana fitowa daga kofar jami'ar sai ya karkata hannun dama yabi hanyar da zata kaishi Gwarzo maimakon yabi wacce zata dawo dashi cikin birnin Kano. Ina kuma zamu? Farida ta tambaya cikin mamaki. Baba ali ya shafi doguwar hular dake kansa mai kamar ribabbiyar dankali yace ranki yadade yimin afuwa muje nan gaban jan guza musha mai. Haba baba ali duk man dake cikin gari bai isheka ba har sai munje gaban wani jan guza? Baba ali ya karawa motar giya daga daya zuwa biyu sannan ya kaiwa wani nacaccan kuda duka dake ta faman zarya agefen kunnensa na hagu Mai yafi araha awajen gari shiyasa nake neman ki rufa min asiri kamar yadda nima na rufa miki kinga dan ragin da muke samu da shine muke dan rage zafin garin nan. Baba ali yadanyi shiru yana satar kallonta cikin madubin dake saman motar. Shikenan farida tace dashi sannan ta dauke kanta gefe guda tana kallon korayen ciyayi da tafasa da sukayi sahu sahu agefen hanya abin gwanin ban sha'awa daga inda take zaunen acikin hasken fitilun motocin dake ta wuce su tana iya hango koramu inda ruwan damuna ke taruwa wasu kananan kwari sai sunturi sukeyi a saman ruwan acikinsu har dani dan tsololin kwaro mai siffar jirgi mai saukar ungulu. Wata kawar farida ta taba cewa da ita siffar wannan kwaron nasara ya kwaikwaya lokacin da zai kera jirgi mai saukar ungulu. . Na fuskanci kamar kina sha'awar ganin korayen ciyayi acikin hasken fitilu direba baba ali ya tambaya sa'ar daya lura da cewa tunda suka baro kofar jami'ar idanunta waje suke kallo. Uhm suna burgeni musamman da yamma likis kafin rana ta gama faduwa Harzuwa lokacin da farida ke wannan batu zuciyarta bata daina hasko mata jifa jifan hoton al'amarin daya faru akan kabir ba. To amma tafiyar da suke yanzu ahankali ta fara samun saukin kaduwar dake dabaibaye da kwakwalwarta musamman ma lokacin da ta sauke gilashin motar daddadar iskar damuna mai dauke da kamshin kasa da tsirrai ta daki fuskarta. Haryanzu bamu karasa gidan man bane? Farida ta tambaye shi ganin cewa tafiya ta mike har sun wuce kwanar jun guza yana nan gaba kadan awani dan kauye dattijon direban yace batareda da ya dubi fuskarta ba. Sannu ahankali suna tafiya har mintina biyar suka shude adaidai lokacin ne dattijon direban ya ragewa motar wuta adaidai wasu dogayen duwatsu dake gaban wani gulbi ma'abocin tarin ciyayi masu tsaye baba ali ya karkata kan motar lokaci guda ya kutsa ta cikin ciyayin zuwa bayan dutsen sannan ya tsayar da motar. Me....me kuma zamuyi anan? Farida ta tambaya a tsorace akwai alamun firgici karara akan kyakkyawar fuskar budurwar Dan Allah baba ali ka fitar damu daga cikin wannan kungurmin dajin..... Ya zaka shigo damu nan acikin wannan duhun dare Baba ali ya dubeta da wani kekasasshen murmushi lokacin bada umarninki ya rigaya ya wuce yanzu nike da ikon bada umarni. Ban...ban fahimce ka ba? Farida tace a tsorace lokaci guda kuma tana duba izuwa cikin duhun daren da kuma dogayen duwatsu da ciyayin dake zagaye dasu. Tuni ta fara tunanin mafarki takeyi tabbas wannan ba gaskiya bane awata duniyar dai take. Abinda nake nufi shine duk abinda nace kiyi sai kiyi baba ali yace lokaci guda kuma ya bude gidan gaba na motar ya fito waje sannan saiya bude gidan baya na motar inda farida take zaune ya zauna akusa da ita cikin sauri kamar wacce maciji ya rabeta ta matsa can jikin daya kofar motar a tsorace. Kaga baba ali wannan in wasa ne ni bana so dan Allah ka fitar dani daga cikin dajin nan. Ba wasa bane farida wannan al'amari gaske ne na dade ina fatan samun wannan dama ban samu ba sai yau.... Me.... Kake nufi farida ta tambaye shi a fusace kuma rabi a tsorace Abinda nake nufi shine ki cire kayanki ahankali tun kafin na cire miki su. Haba... Baba ali ya zakayimin haka ? Kamar yaya na cire kayana? Nace ki cire kayan jikin mubi abin nan ahankali ko so kike na takura ki da karfin tsiya? Na shiga uku farida tace cikin shashshekar kuka dan Allah ka rufa min asiri....wallahi ni ban tabayin abinda kake nufi ba. Yau zaki fara cire kayanki kigani baba ali yace sannan ya matsa kusa da ita ya dora hannunsa akan kafadarta. Cire mana yar 'yata yanzu zamu gama farida ta rike numfashinta cikin tsananin kaduwa hannun dattijon direban dake kafadarta tamkar wani kan bakin maciji take jinsa. Kada ka tabani dan Allah... Matsa daga kusa dani farida takuma mannewa ajikin kofar motar lokaci guda muka ta rufe hancinta da tafin hannu domin duk lokacin da dattijon yayi magana sai taji bakin sa na hamami kamar bakin kura tabbas tasan kowane lokaci daga yanzu zata iya fara amai. Zan lissafa miki uku baba ali yace kana yayi wuce ya kama gefen rigarya da busassun hannayensa masu kamar itace. Idan baki cire ba ni zan cire miki. Farida ta kwalla ihu a razane sa'ar dataji ya fara ja mata riga har wuyan rigarta ya sauko zuwa kafada duwatsun dake zagaye dasu suka amsa kuwwar datayi wani kurege ya ruga aguje ya shige cikin raminsa a tsorace sakamakon ihun. . Duk wannan bazata kaiki ba fitananniya ai ba akaina kika fara ba yana fadin haka sai ya cafko hannunta da zummar ya janyota jikinsa ga mamakinsa sai yaji kamar ya cafko tubakin kankara nan da nan yaji hannunsa ya sandare sannan sai jinin jikinsa yafara tafiyar hawainiya acikin jijiyoyinsa adaidai lokacin da wata sassanyar iska mai karfin gaske ta fara fifita su acikin Motar. Baba ali yaji hannayensa sun dada sandarewa cikin gaggawa ya saki hannayen a tsorace kana ya dubeta Me kikayi min naji hannuna kamar zai tsinke? Kafin ya rufe bakinsa sai yaji wani abu kai karfin gaske kamar kofaton doki ya daki tsakiyar fuskarsa. Wayyo Allah Wayyo Allah. Farida tayi sororo ciki rudani tana kallon ikon Allah tabbas yanzu tasan abinda ke faruwa abin nan mai kamar kofaton doki ya kuma dungurowa ta cikin tagar motar ya daki gefen fuskar baba ali. Wayyo Allah... Na shiga uku. Sai ka shiga talatin ma idan ka kara tabamin matata kakkausar murya mai amsa amo tace adaidai wannan lokacin ne to farida taji lema lema ajikin sangalalin hannun tatana tabawa sai taji wani abu mai laushi laushi dago shi sama keda wuya saita jefar dashi sannan cikin tsananin razana sai hannunta ya kai izuwa mabudin kofar motar farida ta bude sannan ta nufi hanyar da take tunanin zata kaita izuwa bakin titi aguje tana ihu kamar mahaukaciya. Abinda yasata wannan firgici abinda yasata wannan gudu tana ihu shine kunnen direbanta Baba Ali datagani akan sangalalin hannunta yana mots kamar kosai mai rai. ** ** ** ** Bebi ta wangame baki tana hamma babu kalmar shahada sai wani dan ihu da tayi kamar tsuntsuwa sannan taja wata doguwar mika akan tattausan gadon alfarmar ta mirgina kamar yadda jaki yakeyi idan yana wanka acikin toka. Kai ashe rana tayi haka. Tace da kanta sannan cikin lalaci acikin tattausan kilishin dake mamaye da tsakar dakin. Ahankali kamar kazar da kwai ya fashewa aciki bebi ta nufi gindin tagar dakin dake fuskantar koren lambun shakatawar gidan honorabil sabo dake bayan dakin ta zuge labulen sannan ta bude tagar dakin sassanyar iska tsabtatacciya daga cikin lambun ta bugi fuskarta. Bebi tayi ajiyar zuciya domin taji sanyin iska yafara yawa Da gaske dai sanyin za'ayi kenan? Ta tambayi kanta da kanta ganin cewa har kusan biyu amma kamar goma sannan saita bar jikin tagar ta dawo kan gado ta zauna tana tunanin makomarta lokaci guda kuma ta dubi fuskarta acikin dan madubin dake daf da gadon ba karamin kaduwa tayi sa'ar dataga fuskarta ta fara tauyewa hakanan baki baki shudi shudin tambarin Bilicin yafara bayyana a fuskarta. Na shiga uku bebi tace a tsorace ta riga tasan bayan kyan kirar jikinta da take takama dashi abu na biyu dake fizgo hankalin mazaje izuwa

Chapter 4 of 7