Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
barikin janguza suke motsa jiki basu fi ko mintuna uku da bacewa daga dutsen ba sai farida taji ihun baba ali ya ratsa dajin abin ya kada mata hantar ciki domin tun da take bata tabajin dan adam yayi irin wannan ihun ba. Har zuwa lokacin da sojojin suka kawota gida farida bata daina jin amsa kuwwar ihun baba ali acikin kwakwalwarta ba. . Washegari da safe ne take samun labari agurin mahaifinta cewa sojoji sun cirewa baba Ali idanunsa guda biyu yanzu haka yana asibiti kuma ya amsa cewa yayi kokarin yi mata fyade. Farida ta labartawa mahaifiyarta irin masifun dake faruwa akanta tun daga lokacin da akayi mata zanen kunshin nan. Ai kinga irinta in banda shaidancinku na ya'yan zamani ina ke ina zuwa ki budewa wani kato tsaraicinki wai yayi miki zanen kunshi gashi nan yanzu kin dauko jaraba in ba tashi mukayi tsaye ba ko aure ba zai barki kiyi ba. Mahaifiyarta ce ke fadin haka Rabi a fusace rabi a tsorace cikin tsananin kaduwa Awannan yammacin tayiwa mahaifin farida bayanin duk abinda ke faruwa akan yarsu ga mamakinta sai taga ya fashe da dariya. Wannan ai tatsuniyace haba TASALLAH haryanzu daman kina imani da tatsuniyoyin yaran zamani. . Kada kace haka Alhaji matarsa tasallah tace a tsorace domin tasan halinsa Alhaji ba karya bane kuma...... Bance dake Aljani karya bane amma saboda tsabar sake shine har ya zama mutum yakeyiwa mata zanen kunshin akan tsaraici haba Tasallah kada ki biye karairayin yaran zamani Wallahi sa kakiki su baro ki. Abin kawai daya kamata muyi shine mu aurar da yarinyar nan kawai mu huta. . Matar ta dube shi a rude tace bazasu barta tayi zaman aure ba. Dubi fa har baba ali suka cirewa kunne dayayi kokarin mata fyade. Alhaji Ilyasu ya fashe da dariya kada fa kema ki zama sokuwa kamar yarki in banda abinki ko jaki sojoji hudu suka jibga ai sai sun fitar masa da kunne ballantana mutum. Wannan duk yafaru ne watanni uku da suka wuce dan haka ayanzu da farida ta fashe da kuka sai mahaifiyarta ta dube shi tace. Dan Allah Alhaji nidai ina rokarwa yarinyar nan ahuwa abata nan da wata guda domin ta fito da wanda take so tun da dai samarin nan tana dasu bawai bata dasu bane. Alhaji ilyasu ya gyara tabaransa sannan ya dubi matarsa yace Bazan iya sabawa babban aminina alkawari ba kuma kada ki damu yaron nan kyakykyawa ne shima idan ta ganshi zata so shi dan gidan alhaji shu'aibu ne wanda muka zauna gida daya dashi a london. . Kamar jira ake ya iddar da zancensa kwatsa sai sukaji sallama wani kyakkyawan saurayi ne dogo ya shigo dakin farine mai manyan idanu farare. Baba Ina kwananku ya zube agaban su mahaifiyar farida ta dubi saurayin sannan ta dubi farida daga karshe kuma ta dubi mijinta baki na rawa tace. Shine wannan? Bata taba tsammanin saurayin zaikai kyawun haka ba. . Ba shi bane Wallahi shine. Farida tace da mahaifanta cikin karaji a tsorace mahaifan nata suka dubi saurayin a rude cikin rashin fahimtar abinda take nufi sannan ne to suka lura da cewa kafar kyakkyawan saurayin dake gabansu KOFATO Ce. . BABI NA SHIDA 6 Nayi zaton zamu kai magariba ashe da wuri ma zaki fito direban yace da mama sa'ar data fito daga gurin bokan ta shiga gidan baya. To ko tsayawa zamuyi mu kwana anan? Mama ta tambaye shi cikin gatse. Wani tattausan murmushi ya subuce daga bakin direban sa'ar daya sawa motar giya suka fara tafiya. Ni bance ba ranki yadade Allah yabaki hakuri Da Hakurin ta mutu nawa ka bayar kudin sadaka? Mama ta sake mayar da martani cikin tsiwa. Direban yayi shiru daga wannan bai sake cewa da ita kala ba har sa'ar daya ajeta a kofar gidanta. Mama na fitowa daga cikin motart bata jira sun sake sabon ciniki ba saita kirgo kudin data tabbata sun lunka kudin da sau biyu ta mika masa Jiki na rawa direban ya karba. Nagode ranki yadade yace da ita cikin murmushi Ga mamakinsa sai yaga mama ta sassauta fuska ta haskake shi da murmushi tace. Nima nagode suka danyi shiru na dan lokaci shi bai tafi ba ita kuma bata juya ba. Bani lambar wayarka kodon gaba idan kana da lokaci sai in kiraka kana kaini unguwa to ranki yadade direban yace yana rawar jiki lokaci guda kuma ya fadawa mama lambar wayarsa ta shigar atata wayar. To shikenan sai na kira mama tace sannan ta juya cikin sauri ta nufi kofar gidan. Adaidai lokacin ne tayi Turus. Sa'ar data hangi Mubarak saurayin da take mutuwar kauna tsaye ajikin wani dan kanti na katako dake dab da kofar gidan mama taji zuciyarta ta harba atsakankanin hakarkarinta numfashinta ya dauke yawun bakinta ya kafe tun da take aduniya bata taba kamuwa da ciwon son wani 'Da namiji ba sai Mubakar agurin mama maza tamkar kasuwa ne kashige su a lokacin dakaga dama ka sayi abinda kake so ka fice. Ayanzu data kalli mubarak sai mama ta gane kuskurenta a fili ashe dai maza sun wuce kasuwa saidai Gidan kwana. Sannunku mama tace dasu Mubarak da kuma mai tsawon kantin sannan saita dubi cikin kantin tace Kanada kwan wuta ne? Mama ta tambaya tana kallon kayan kantin lokaci guda kuma tana satar kallon Mubarak ta gefen ido Akwai naira hamsin. Mai tsaron kantin yace Ba musu ballamtana ta nemi ragi mama ta biya sannan saita kuya kamar zata tafi saita tsaya agaban Mubarak tace dashi a tausashe. Mubarak ko gaisuwa babu? Mubarak ya dubeta shekeke sannan ya shafi kwanjinsa yace Kin Ajeni anan ne domin kullum ina gaisheki? Mama taji kamar ya watsa mata wuta kunyar daya saurayin mai tsaron kantin ta lullubeta. Allah baka hakuri.... Ina kwana to ni na gaisheka Lafiya lau mubarak yace sannan cikin sauri sai yabar gurin ya nufi bakin titi. Mama ta bishi da kallo cikin kunan rai har saida ya bace sannan saita matsa jakarta daidai inda laya nan da boka ya bata kana tayi murmushin yake. Sai hakuri Mubarak dole ne saika aure ni tace da kanta sannan saita dada matsa layarta cikin jaka. ** ** ** ** Duk wannan al'amura sun faru ne kwanaki bakwai kafin honorabil sabo ya kori bebi daga gidansa. Awannan ranar yan yansandan ciki suka sa bebi cikin wata katuwar mota jeep kirar kamfanin Fodi bakikitin da ita kamar shuni suka nufi kanon dabo daga abuja su biyar ne acikin motar baya mutum uku ne babi da wasu karti biyu sanye da bakaken kwat da bakaken tabarau sun sata a tsakiya gaba kuma direba ne da wani katon shima sanye da bakin tabarau da shudiyar kwat. Motar nata kwarara gudu bebi na tsakiyar kartin tayi zuru da ita bata ko kwakkwaran numfashi da motsi domin ta lura suma mutanen dake zaune akusa da ita kyam suke basa motsi kamar busassun itatuwa abinda yafi damun bebi shine da bata iya ganin kwayar idanunsu. Suna nan tafe zuciyar bebi nata sake sake na gargadi mama. Bebi tace cikin zuciyarta tayi imani da cewa mama bazata taba iya kashe mutum ba bera ma tsoronsa takeyi ballantana har ta huda cikin mutum kuma ma me zaisa ta kashe honorabil jatau? Bebi ta tambayi kanta Yau da ace kudi sun bata adakin to da sai ace ko kudin tazo sata yakamata ai ta ya kuma ta kashe shi.... Kai bazaiyiyu ba ai mama ko kamata yayi tana satar kudinsa babazata iya marinsa ma ba ballantana har ta kasheshi to saidai kuma me yasa har tsawon wannan lokaci mama bata yi waya ba? Wadannan tarin tambayoyi su suke cunkushe kwakwalwar Bebi. . Ance ki kwantar da hankalinki. Daya daga cikin kartin yace da ita batareda ya dubi fuskarta ba. Babu laifin da kikayi mana so muke kawai ki kaimu gidan da take shikenan sai sai mu sallame ki. . Bebi tayi ajiyar zuciya sannan jikinta ya dauki rawa kamar wacce zazzabi ke shirin hawa. Ka... Kama ta zakuyi? Ta tambaye su cikin karfin hali Yan tambayoyi kawai zamuyi mata daya daga cikin karyin yace a takaice. Har yanzun nan bai jiyo ba ballantana ma ya dubeta akwai wani abu a tattare da yanayin mutanen dake baiwa bebi tsoro tabbas ayanzu tasan ya zama dole ta gargadi mama halin da ake cikin shin wai da tun farko ma meyasa batayi tunanin tayi kiranta ba. Kibar kaza acikin gashinta ki kaddara aranki cewa bakima taba haduwa da mama ba kada ki kirata idan kuma ita ta kira kice da ita kada ta sake ta dawo Abuja. Bebi ta tuna maganar honorabil sabo lokacin dayake fatan Allah yasa wani bai lura da shigarsu gidan honorabil jatau ba. Ashe ya maka masu gadi sun lura. Bebi ta muskuta abayan motar sannan ta takura lokaci guda ta dubi daya daga cikin kartin tace a tsorace. Zaku iya tsayawa nayi fitsari? Kwarai da gaske ki saki ranki dan Allah duk kinbi kin rude ba wani abu zamuyi miki ba. Bebi ta dubi mai maganar da wani busashshen murmushi sa'ar da direban motar ya tsaya dasu acikin dajin. Tsallaka can kiyi ga wata duhuwa can amma kada kiyi nisa kinsan dajin da macizai Bebi ta nufi bayan wasu dogayen ciyayi dake gefen kwaltar amma daga can ciki ta tsugunna abayan ciyawar. Saida ta tabbata babu mai ganinta Jiki na rawa ta bude jakarta ta dauko waya tafara daddanna lambobi wayar ta kwace ta fadi a kasa saboda rawar da hannunta keyi cikin sauri bebi ta sake rarumar wayar ta daddanna sannan ta kara a kunne tsahon dakiku masu kamar sa'o'i uku agun bebi sai mama ta dauki wayar acan daya bangaren. Mama.... Bebi ce..... Saurara da kyau ki ji bamuda lokacin gaisuwa......... *** *** *** *** FADILA ta dubi kan wayar tana mai shakkar abinda taji daga bakin mahaifiyar tata duk da an bata izini ta dauki wayar batayi hakan ba harda da tabbatar mahaifiyarta ta gama fita daga dakin ta kuma rufe kofar abayanta. Hannunta tareda duk wani bangare na jikinta na rawa fadila ta ganna abin amsa wayar sannan saita lumshe idanu ta kara a kunnenta. Fadila... Fadila ce? Don Allah kiyimin magana faisal yace acan daya bangaren bakinsa na rawa kamar zai fashe da kuka. Faisal.. Fadila ta kira sunansa da wata rarraunar murya. Acan daya bangaren faisal yaji kamar an kwarawa ruhinsa ruwan sanyi sa'ar dayaji muryar fadila. Yanzu kam ya tabbata duk duniya babu wanda ya isa ya rabashi da Fadilarsa domin yanzu ne yake kaunarta fiyeda lokacin daya aureta ma. Na'am fadilata kina ina? Ya tambaya cikin wata tattausar murya. Ina gida Faisal. Me kike yi? Azaune nake ni kadai ina kuka ina tunaninka.... Muryar fadila ta karye ta fara sheshshekar kuka. Daina kuka dan Allah fadila kada kisa jinina ya hau. Toh faisal.... Na daina fadila tace a raunane haryanzu akwai alamu sheshshekar kuka a muryarta sukayi shiru na yan dakiku. Hello Fadila... Kina jina? Ina jinka Faisal. Kiyi hakuri don Allah ki yafemin abinda nayi miki. Fadila ta danyi shiru acan daya bangaren. Bazaki yafemin ba fadila? Aka sake shiru na dan lokaci. Na yafe maka faisal... Kaima kayi hakuri kaji? Bakiyi min komai ba fadila Ilove you... Kinji? Fadila ta dada lumshe idanunta acan daya bangaren cikin wani irin farin ciki da bata taba jin irinsa ba. Ina kewarka faisal... Yaushe zan ganka. Gani nan zuwa yanzu. Adaidai wannan lokaci sai kofar dakin Fadila ta bude mahaifiyarta ta shigo idan kun gama hirar saiki fito falo su malam sunzo zasu karasa miki addu'ar ki. Faidla ta gyada kai lokaci guda kuma tace da faisal acan daya bangaren. Kabari sai nan da awa biyu Tayi min tsayi faisal yace. Zan dai zo saina jiraki a kofar gida har sai lokacin ya cika. ** ** ** ** ** ** Dayake haryanzu fadila bata sa ko kashi daya daga cikin takwas na kayan lefenta ba sa'ar data fita daga wanka ta gama kwalliya saita kasa zaben irin kayan da zata tari tsohon mijin nata dashi saida ta shafe sama da rabin sa'a kafin daga karshe dai ta samu ta zabo wani bakin siliki siliki mai sheki wanda akayiwa dinkin riga da siket matsatstsu irin na wannan zamani tasa Tuni Faisal ya dade adakin shakatawa na musamman da aka ware dan manyan baki abokan mahaifinta. Fadila ta gama feshe feshen turare kenan sai mahaifiyarta ta shigo dakin sannan ta dubi irin kayan da fadila ta sa sannan ta girgiza kai tace. Oh Ya'yan zamani to daman yaya za'ayi ma ku rabu da aljanu? Saiki nemi gyale mai fadi ki yafa karki kije masa ahaka sinki sinkin kamar doya. Fadila ta fashe da dariya wannan itace dariyarta ta farko cikin wata uku rabonta da dariya tun yammacin da sukayi sallama da faisal dinta yatafi yiwa abokansa ban gajiya. Baba kenan kuma dan nasa wannan sai aljanu su fara bina. Keda Allah can rufe min baki har zaki fara kaudi dan kinga yazo. Kinga mama ni dai ki daina janyo min su Fadila tace cikin shagwaba Dazan janyo miki su ai da ban sa anyi miki addu'ar rabaki dasu ba mahaifiyarta tace sannanDa zan janyo miki su ai da ban sa anyi miki addu'ar rabaki dasu ba Mahaifiyarta tace sannan saita matsa kusa da yar tata tace a tausashe. Ina fatan dai yanzu kin warware babu matsala? Fadila ta gyada kai. Har yan gane ganenma yanzu bakyayi ko? Fadila takuma gyada kai mahaifiyarta tayi ajiyar zuciya sannan tace ai saikije yana jiranki. . A dakin karbar baki na musamman faisal ya mike tsaye cikin tsananin farin ciki sa'ar da masoyiyarsa tsohuwar matarsa fadila ta shigo dakin. Masoyan biyu suka zauna lokaci guda akan kujera guda sannan suka fuskanci juna da wani narkakken murmushi. Fadila daga yau babu wanda ya isa ya rabani dake Fadila ta lumshe ido cikin jin dadi tace kaidai fadi gaskiya. Gaskiyar kenan fadila ko Aljanin nan ne zai sake dawowa bai isa ya rabani dake ba. Fadila ta dube shi cikin mamaki tace kana nufin yanzu ka yarda da abinda nafada wancan karon? Cikin murmushi faisal yace ai bake kika fada min ba agida na sami labarin a gurin MAMA Masoyan biyu sukayi shiru suna kallon juna cikin shauki na tsawon dakiku can sai faisal yayi ajiyar zuciya a tausashe yace Matata. Fadila ta lumshe idanu ta kuma bude su lokaci guda. Umhm Mijin Faisal ya mika hannu zai tabata sai fadila ta janye jikinta cikin sauri tana dariya tace. Kada ka manta ada nake matarka yanzu allura cikin ruwa ce mai rabo ka dauka. Faisal ya hade fuskarsa cikin wasa yace Dan Allah ki bari kada kisa jinina ya hau yanzu yaushe za'a mayar da auren namu? Fadila ta dube shi ido da ido tace Najisu mama suna cewa sai nan da shekara biyar. Faisal ya kai mata duka suka fashe da dariya cikin farin ciki. ** ** ** ** MAMA Tayi mika akan gadon sannan ta harba kafafunta har sau biyu kamar mai hawan bori sannan saita mike zaune a hankali ta dubi agogo karfe uku da minti ashirin na yamma. Tun karfe goma na safe data tashi ta wanke bakinta tayi karin kumallo saita koma ta kwanta abinta bata farka ba sai yanzu to me ya dameta? Daman aljanin nan ne gashi kuma yau kwanaki bakwa da bokan nan ya daukar mata sun cika. Dan Haka mama ta gama imani da cewa daga yau ta rabu da shegen aljanin nan. Cikin murmushi saita lalubi kanta tsakanin kitso ta shafi layar da bokan ya bata sannan ta fara tunanin ta inda zata bullowa Mubarak idan anjima. Idan har abinda bokan yafada mata ya kasance gaskiya babu abinda zai hanata auren Mubarak mama tagama yanke shawarar kawai ta auri Mubarak tun dai tana kaunarsa tuni ta gama yanke kauna da wannan harka ta karuwanci badon komai ba sai dan kawai tana kaunar mubarak hakanan kuma tasan in har ba garin kano zata bari ba cigaba da karuwanci zai yi wuya tunda dai labarinta ya watsa ko ina gashi wani abin kara tonon silili har masu sayar da hotuna da kalandu ne ke yawo da hotunanta a kalanda da kuma na likawa a kasan hoton an rubuta MATAR ALJAN. Zuciyar mama cike da wannan sake sake ta shiga bandaki ta fesa wanka kana ta dawo ta zauna agaban dogon madubin dake dakinta ajikin bango ta fara goge goge da shafe shafe irin na kwararriyar yar duniya bayan tsayin mintina tagama sannan ta kalli surarta ajikin madubi mama tayiwa kanta murmushi danjin dadin abinda tagani haryanzu nan ashe dai fuskarta na nan dauke da TSOHON ALKAWARI kyawu nan nata duk da yake dai yawan bilicin datake yafara samun tasirin sauya launin kudukukinta amma fararen idanunta da dan bakinta faffada gwanin iya shan (Ice Cream) Madarar kankara su suka kara mata kwarin gwiwa tabbas babu abinda zai hana Mubarak kamuwa da sona idan ya ganni. Mama ta fada cikin sauri dauke da nishadi sai mama ta nufi bakar akwatinta mai kaya ta fara lalube laluben irin kayanda yakamata tasa. Ta bude can ta leka can ta bincika can daga karshe dai hannunta yakai kan wata bingilalliyar riga tsawonta baifi iya cibiya ba shudiya ce kusan rabin kirjin rigar duk a wawake yake hakanan rigar tana da doguwar siket wacce idan mamatasa har kasa take ja. Mama tayi murmushi sannan ta dauki rigar. Har ta fara sa rigar saikuma ta tsaya kai da wahala mubarak yaso rigar nan dan naga ustazu ustazu ne mama tace da kanta cikin murmushi. Duk da yake dai tasan takadiri ne wasu ma nayi masa kallon dan daba amma mama nada yakinin baya harka da mata. Mintina ashirin suka shude daga karshe dai da kyar mama ta zabo wata doguwar riga launin zuma da dishi dishin fari kamar fatar damisa rigar na da wando me dauke da wata beza beza ta farin leshi daga can kasa kamar kafar namijin tattabara. Karfe biyar saura yan mintuna mama ta gama shirinta tsaf sai kamshi take yi tun daga sama har kasa domin ta feshe jikinta da turare sama da kala biyar mama tayiwa kanta kallon tsaf na karshe ajikin madubi sannan saita dauki farar jakarta ta nufi kofar gida inda Dabar su Mubarak take. . Mubarak na zaune shi kadai akan wani benci karyayye agindin wata bishiyar darbejiya saiyaji kamshi ya buhi hancinsa kamshin ya dadada masa hanci matuka cikin sauri ya dago kai ahankali domin yaga daga ina kamshin ke tashi dago idanunsa keda wuya sai sukayi ido biyu. Sannu da hutawa mubarak dama Sannu da hutawa mubarak dama gurinka nazo. . Mubarak zuciyarsa ta harzuka wai shin dan uban karuwar nan meyasa ta rainani ne? Mubarak ya tambayi kansa rashin duka ne shaidaniyar zuciyar ta shawarceshi nan da nan kamshin turaren dake tashi yakoma kamar warin mushe agurin mubarak domin aduk matan duniya babu wacce ya tsana irin mama duk da yake dai daman shi mata basu dame shi ba abinda ke gabansa shine kallon kwallo da yawon farauta idan ta samu. . Kikazo kiyi min me? Mubarak ya tambaya yana kallonta a fusace yana ciccije baki. Mama taji zuciyarta ta harba tsakanin hakarkarinta bata tsammaci irin wannan daga bakinsa ba dan haka saita sa hannu kamar zatayi susa ta shafo layar dake tsakanin kitsonta awayance sannan ta dubi Mubarak ido da ido Gani nayi kamar gurin babu kowa shiyasa nazo in tayaka zama. Mubarak yaji zuciya ta tuke shi. . Kebace kar in barar dake an fada miki ni abokin kazamai ne irinki? Wannan kalma itace mafi muni da mama ta taba ji arayuwarta abinda ya harzukata mama bata bari ya bayyana a fuskarta ba. Maimakon hakan sai mama ta dada shafar layar a karo na biyu sannan babu zato babu tsammani sai ta matsa inda mubarak yake ta zauna akan bencin bata kura dacewa bencin gurgu bane tana zama sai nauyinta ya rinjayesu nan da nan suka fadi da baya. Wasu yara acan gefe na wasa suka fashe da dariya harda sowa. Mubarak ne yafara tashi a fusace sannan ya zare bakin BELT din dake kugunsa. Kayi hakuri mubarak bansan a..... Kafin ta karasa mubarak ya hauta da duka da farko mama ta dauka abun wasa ne daga karshe kuma saitaga Mubarak yasa kafa yayi bal da ita harsada ta fada KWATA. Wayyo na shiga uku mama tasa ihu sannan ta mike ta ruga aguje Mubarak ya rakata yana duka sai saida ya rakata har kofar gida. Akace bakya jin duka wai kina da aljani yanzu uban wa na daka? Mubarak yace yan ciccije baki sannann saiya juya yana bubbudawa lokaci guda kuma yana mayar da belt dinsa cikin wandonsa ya nufi inda mai dan kantin nan na kusa da gidansu Mama yake. Bani sigari yace da mai kantin yana muzurai. Acan cikin gida mama tafada cikin daki tayi rub da ciki akan gado ta fara rusa kuka. Ba kukan zafin dukan da mubarak yayi mata ba takeyi ba kukan wulakanci da nuna mata kyamarta da yayi takeyi. Mama ta tashi zaune akan gadon hawaye sharaf shafar ta lalubi kanta tsakanin kitson da niyyar ta dauko layar nan da boka ya bata tayi jifa da ita adai wannan lokaci sai wayar tafi da gidanka dake gefenta ta katse mata hanzari sakamakon ruri data fara. Da farko mama batayi niyyar amsa wayar ba dan haka saita dauki wayar a fusace da niyyar ta kashe sai kuma tayi turus sa'ar da taga sunan kawarta BEBI ya bayyana a fuskar wayar. Nan da nan mama taji duk damuwar dake tattare da ita ahalin yanzu an zare mata ita kamar cirar kaya sannan alokaci guda wata sabuwar damuwa ta maye gurbin wanccan. Cikin sauri mama ta share hawaye sannan ta danna abin amsa waya tace cikin wata malalaciyar murya. Hello. Mama bebice saurara da kyau kinsan bamuda lokacin gaisuwa..... Ki tattara naki ya naki kibar kano kafin mu karaso nan da awa biyu zamuzo da yan sanda wai zasuyi miki tambayoyi akan mutuwar honorabil.... Dan Allah mama fadamin gaskiya ke kika kashe shi? Mama taji wani zazzafan gumi ya fara sartu akan gashinta tuni dama kukan dukan da tasha ya wanke kwalliyar data shafe sama da sa'a guda tanayi. Haba Bebi.... Wallahi bani na kashe shi ba... Ke kinfi kowa sani na Nida bera ma tsoroyake bani tayaya zan iya kashe mutum..... Amma dai nasan ta yadda...mama ta danyi shiru. Kinsan me? Bebi tace acan daya bangaren cikin kaduwa, bani na kashe shi ba.... Amma akwai labari dai me tsayi akan..... Kinga mama saurara bebi takatse ta acan daya bangaren. Koda bake kika kashe shi ba idan kinsa bakida gaskiya kigudu kawai kuma amatsayin kawa domin na rama irin mutuncin da kika nuna min lokacin dana fara zuwa kano ke kika fara bani sababbin kaya kyauta.... Sai wataran kawata. . Layin ya katse daga can daya bangaren cikin tsananin firgici zuciyar mama ta kankame gawar wayar a kirjinta domin numfashinta ya fara daukewa tsahon mintina tana nan azaune kwakwalwarta ta kasa tunanin komai sai bayan mintina goma sannan ta fuskanci halin da take ciki ta riga tasan har kullum daman wannan al'amari kandarsu acikin ranta amma matsalar wannan aljani dake addabarta su suka dauke tunaninta daga kan duk wani hadari dake iya samunta a sakamakon katuwar honorabil jatau. Da farko mama ta yanke shawarar tayi zamanta kawai ta jira zuwansu bebi tunda dai ai ba ita ta kashe shi ba Jimawa kadan kuma sai wata zuciya tace da ita idan suunzo kuma kuma kice dasu me? Kice dasu wani aljani ne yafito atsakiyar dare ya kashe shi kina kwance? Mama tayi ajiyar zuciya tasan wannan zance ba mai yiwuwa bane duk duniya wanene zai yarda da wannan tatsuniya? Mama tasan tana fadin haka zata fada hannun hukuma domin har yau din nan ita kanta gani takeyi kamar mafarki. Jikinta na rawa mama ta mike tsaye cikin zafin nama naban mamaki ta hada duk suturarta cikin jakankuna guda biyu sannan ta nufi bandaki ta wanke fuskarta tana dawowa saitaci gaba da laluben sauran abubuwan da take tsammanin zasuyi mata amfani agaba da wannan karon mama bata damu da ta shafa koda farar hoda ba ballantana ta tsaya doguwar kwalliya tuni tagama yanke shawarar inda zata gudu garin da aka dade ana bata labari aka kuma dade ana shawarartar ta data tafi tun lokacin da aka kaddamar da shari'ar musulunci a kano. Ai saikiyi ta zama baki gaji da wahala bane kullum ana binki ana takura rayuwarki kamar barauniya ance kizo mu tafi inda zamu fantama babu mai rakura mana. Wata kawarta ce ke bata wannan shawara. Wai wane gari ne wannan? Mama ta tambayi kawar. Wani garine tsakanin bodar najeriya da nijar harka agarin ba magana kizo kawai muyi tafiyarmu can inda babu tsangwama. Ayanzu da mama ta dauki jakankunan ta cikin sauri can ta yanke shawarar guduwa babu abinda mama ta tsana irin karuwancin kauye to amma yanzu batada zabi akalla dai zan bace na dan lokaci kafin kura ta lafa waya sani ma ko aljanu basa iya tsallaka boda ballantana su dameni. Mama ta fadawa kanta domin ta dada samun kwarin gwiwa abinda yafi damunta ayanzu shine kudadenta dake banki kodayake tuni mama tasan idan ta kwashe kudinta gaba daya daga bankin zata iya damkasu a hannun wani dan canji a wafa wanda take canjin kudin kasashen ketare agurinsa tasan duk inda take zai iya tura mata da kudinta. Mama ta dubi agogo sa'ar data fito kofar gidan karfe biyar saura tasan idan tayi sauri zata iya samun banki ba'a rufe ba. Mutane suka zuba mata idanu sa'ar da sukaga ta fito da jakankuna a tunaninsu dukan da mubarak yayi mata ne yasa zata tafi. Mama ta isa bakin titi kafin ta tsayar da dan tasi sai ta dandanna wasu lambobi awayarta. Sannan ta kara a kunne tace Hello.. Mu'azu... Nice mama dan Allah mu hadu yanzun nan a OCEANIC BANK zan baka wasu kudi da zakayi min sako dasu ta danyi shiru sannan saitace. To shikenan amma kayi sauri don tafiya zanyi. . Wani da adaidaita sahu ya tsaya akusa da ita da mashin mai kafa uku mama ta jefa jakankunanta biyu aciki sannan ta shiga tace da direban Oceanic bank zaka kaini daga nan kuma zamu wuce tasha kofar ruwa. Direban yaja mashin din ahankali. Koda suka fara tafiya sai mama ta hangi mubarak tsaye abakin titi kusa da wasu sayar da bakin Mai. Batasan abinda yasa ba sai kawai ji tayi bakinta ya subuce Yace. Mubarak Mubarak ya juyo sai yaga mama tana daga masa hannu cikin mashin mai taya uku. Kai yau na hadu da mayya mubarak yace sannan ya tsartar da yawu. . FARIDA Dakin shakatawar yayi shiru bakajin motsin komai kamar anyi ruwa an dauke. Alhaji Ilyasu ne yafara magana cikin karfin hali yana kallon kyakkyawan sauri me kafar Kofato. Bawan Allah daga ina kake? Farida acan gefe guda a takure ta dada runtse idanunta da kunnuwanta bata son ji ko ganin abinda ke faruwa idan su basu san kowanene saurayin ba ita tasan shi. NINE MIJIN FARIDA. Kyakkyawan saurayin yace dasu sannan sai ya fashe da wata kakkausar dariya mai kamar aradu wata iska mai karfi da sanyin gaske ta fara fifita cikin dakin sannan sai wani farin hayaki ya turnuke dakin. Mahaifiyar Farida ta dauki satali a razane nan da nan taji kafafunta bazasu iya daukar nauyinta ba cikin sauri ta lalubi daya daga cikin kujerun ta lume aciki domin bata iya ganin komai sai farin hayaki. Tsahon lokaci kafin hayakin ya washe . Na shiga uku..... Yau mun hadu da jaraba Alhaji kaga abinda nake fada ma ko? Mahaifiyar farida ce ke magana Alhaji Ilyasi yayi kasake na tsahon mintuna cikin tsananin mamaki da fargaba yan mici micin idanunsa suna kallon bangon dakin da wani yabashi labarin abinda yafaru yanzun nan agabansa da babu abinda zai hana

Chapter 6 of 7