Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
direban gidansu na nan yana jira amma gudun kada ta batawa kabir rai sai tace Bakomai mu hadu goben. To shikenan sai munyi waya kabir yace yana kallonta da murmushin yaudara. Zaka kirani awaya idan naje gida? Me zai hana Faridata cikin farin ciki farida ta nufi inda direbanta baba ali yake jira saidai kuma duk wannan farin kafin ta zauna abayan motar ne. Domin tana zama data kalli hannayenta saita nemi bakin zanen kunshin sama da kasa ta rasa. Na shiga uku na lalace. Farida ta fashe da kuka a tsorace. . Baki shiga ba matata keda nayi miki gata na fito miki da adonki agaban wanda kike so wata kakkaurar murya tace da ita daga sama. Wayyao Allah....waye ke magana? Farida ta tambaya tana waige waige abayan motar. Wa kikaji yayi magana? Direbanta ne baba ali ya tambaya yana kallonta cikin tsananin mamaki. . ** ** ** ** Washegari da safe misalin karfe goma da yan mintuna direba baba ali yakawo farida cikin jami'ar bayeron dan Allah Baba ali idan ka koma gida kace da mama sai wajen magariba zamu tashi kaji? Kace da ita kuma wata kawata ce zata dawo dani Farida ce ke fadi tana kallon dattijon tausashe. Basai na dawo ba kenan baba ali ya tambaya cikin sauri farida ta gyada kai Eh basai ka dawo ba kuma dan Allah idan baba yadawo da wuri koda yake dai nasan me yiwuwa jirgin yamma zai biyo daga abuja amma idan yadawo kafin nan sai ka nemeni awaya dan in sani kaji baba Ali? Baba ali ya danyi jim yana duban sitiyarin motar dake gabansa. . Saidai fa kinsan wayar tawa tafi sati biyu babu komai acikinta kwandala daya da yan kwabbai suka rage dasu nake flashing. Jin haka keda wuya farida ta fahimci abinda yake nufi cikin sauri ta bude jaka ta zaro naira dari biyar guda biyu sababbi kar ko kari babu ta mika masa Ga wannan kasa katin harma ka samu na goro. Yauwa 'yata ko kefa ai yana zuwa zan fada miki kuma ina ganin ma ba saina kira ki ba idan ya tambayeki zan iya cewa dashi sai wajen takwas zaku tashi zan koma a dauko ki nasan bazai damu ba. Yauwa baba ali na gode farida tace sannan saita bude kofar motar ta fice cikin sauri ta nufi inda dakin daukar darasinsu yake nan da minti arba'in zasu fara daukar darasi. . Dattijo baba ali yabita da kallo yana yabawa da abinda yagani azuciyarsa tun tana karama yake kaunarta aransa sannu ahankali tana girma yana kallonta har zuwa yanzu data girmewa duk wani mafalkin sa. Akaro na farko arayuwarsa sai baba ali ya fara tunanin ina amace saurayine shi dan shekara shirin da biyar ko talatin da babu abinda zai hana shi ya nemi Farida baba ali na tattare da masaniyar cewa duk watan duniya sai farida ta sauya sabon saurayi ya lura da hakane da irin samarin da kan rakata zuwa wajen motar yau in ya ganta da wancan dan tsololon bayan sati biyu ko uku kuma sai ya ganta da wannan dan lukutin to amma har kullum yafi ganin laifin samarin domin yayi imani da cewa da ace shi keda yan kananan shekaru kamar nasu da babu yadda za'ayi farida ta gagare shi. . Shekaru talatin da doriya da suka gabata Baba ali tsohon direban babbar motace ta daukar shanu daga arewacin najeriya zuwa kudanci azamanin da yake da sauran kuruciya mayen karfe abokansa direbobi yan bariki suke kiransa domin a tarihi ba'a taba ganin karuwar daya tsaya da ita bai dauki hankalinta ba koda bashida ko kwabo saita saurare shi domin allah ya hore masa iya zance yana dan shekara arba'in aduniya wani babban hadari ya rutsa dashi ahanyar ikko shi kadai ya rage bai mut ba acikin jama'ar motoci shidan da sukayi ta haduwa da juna amma dai ya tare a asibiti da karaya biyar saida yayi shekara biyu bata tuki bayan ya warke alokacin ne to wani babban amininsa tsohon direba andace shi nutsatstsene ba kamarsa ba ya hadashi da kwamishina Ilyasu Na Gamdo wanda ya ya kasance mahaifi agurin farida yau shekara goma sha biyu kenan yana aikin direban hajiya da ya'yanta. Baba ali na nan zaune cikin motar afilin fakin yana kallon farida har saida ta bace sannan saiya tuka motar ya nufi kofar fita daga cikin jami'ar cikin takaici. Me zai hana ka dawo daukarta in yaso sai kayi duk abinda kake so? wannan kururuwar shaidan ce cikin kunnensa yana dada karfafa masa gwiwa akan ya aiwatar da wani tsohon kudiri daya dade yana yawo cikin zuciyarsa tun sa'ar daya fahimci farida ta zama cikakkiyar mace. Akullum baba ali ya dubi farida sai ya fara tunanin me zai hana idan ya sami dama yayi mata fyade kawai ya gudu abinsa. Dama tuni wannan aiki ya isheshi domin dan abinda ake biyansa bai taba isarsa ba. Abinda yakamata inyi kenan Baba ali ya dada jaddadawa kansa. Tuni ya gama lissafin inda zai tsere domin anfi shekara uku wani tsohon abokinsa dake zaune a ikko nayi masa tayin sayar da kwaya. Wahalar banza kakeyi wannan sa'ar tamu tafi wannan direban hajiyar kanata wahalar banza yanzu da karfinka yagama karewa zasu sallameka shikenan kashiga uku. Baba ali yayiwa kansa murmushi sa'ar daya tuno kalaman tsohon abokin nasa tabbas wahalar banza nakeyi amma yau din nan zan karbi ladan aikina na karshe in bar musu tsiyarsu baba ali ya fadawa kansa. Abinda ya rage kawai yanzu shine idan magariba tayi nayi mata waya ince ta tsaya baba yace inzo in dauketa. Wani busashshen murmushi irin na yan duniya ya subuce masa cikin nishadi sai ya zura hannunsa aljihu domin ya dauko sigari abinda bai taba yarda yasha agaban uban gidansa kwamishina ba sa hannunsa keda wuya cikin aljihun sai yan yatsunsa sukaci karo da sababbin takardun kudin da farida tabashi ga mamakin baba ali saiyaji kudin sunyi sanyi sanyi karai adaidai lokacin ne ya kawo wani dan cunkoson motoci dake unguwar rijiyar zaki. Wannan kamar yanzu kuka futo daga inji baba ali yace sa'ar daya daga takardun kudin da hannunsa na dama yayin kuma da hannunsa na hagu yake tuki. Kamata yayi ace kunyi dumi ba sanyi ba baba ali ya kuma cewa da kudin cikin nishadi sannan sai ya mayar dasu cikin aljihu daga tafin hannunsa keda wuya saiyaga tambarin zanen dake jikin naira dari biyar din yafito rangadadau a hannunsa. Cikin mamaki sai baba ali ya goge tafin hannunsa ajikin riga da zummar ya goge fentin ga mamakinsa launin bai gogu ba baba ali yasake murmushi kana ya mayar da hankalinsa kan tukin da yake sannan yace. Yar banza yarinyar nan ko injin buga kudi sukedashi acikin gida? Naga wannan ko bushewa ma basuyi ba to duk tsiyarsu dai saina kashe su Da'ace dattijon mai cikakkiyar nutsuwa ne daya sha jikin jikinsa tun a wannan lokaci domin gargadi ne na farko a gareshi AMMA BAI SAN HAKAN BA. ** ** ** ** Kabir ya fito daga cikin motarsa shudiya kirar toyota ya mayar da kofar cikin burga da budawa ya rufe sannan ya nufi farfajiyar jami'ar yana tafiya yana wani tsalle kamar ansa masa dunkulen tamaula akasan takalmin sanye yake da wata damammiyar riga mai dogon hannu fara sol da ita kamar auduga sai sheki takeyi acikin dan abinda ya rage nadaga hasken ranar wannan yammaci agaban rigar an rubuta HUG ME cikin harshen turanci da wasu bakin zare mai sheki bakin wandon jeans din yayi matukar dacewa da farar rigar hakanan farin takalmin dake kafarsa gami da bakin tabarau din dake zaune daraf a saman doron hancinsa su suka kammala wannan kwalliya ta musamman dayayi domin ya samu damar karya zuciyar Farida. Kabir ya shafi gashin kansa wanda ke sheki sakamakon man da ya sha masa sannan ya gyara yan kanan sifikun dake cikin kunnuwansa wadanke ke dauko masa wani tattausan kidan zamani daga cikin wayarsa kirar Nokia dake aljihunsa yana tafiya yana bin kidan da bakinsa wata sa'ar kuma yana kwaikwayon wakar da fito babu abinda ya dame shi matsalar kudi babu duk abinda yake so hajiya zata bashi. . Mahaifiyarsa HAJJO HABIBA tsohuwa yar kano zuwa jidda ce hakanan ayanzu duk wani abu da zai kawo kudi tana ciki jita jita kuma nata yaduwa cewa wai yar damfara ce da yan daban take samun kudin domin ma'abota iya tsegumi na unguwarsu sunce basu taba ganinta cikin talauci ba hakanan duk bayan wata shida sai ta sayi motoci biyu sababbi daya tata daya kuma ta danta kwaya daya jal aduniya shima har yau ba'asan ubansa ba daga Allah sai ita sau da dama makwabtanta wadanda gulmarsu tafi karfin zuciyarsu sukan tambayeta wai shin waye uban kabir wannan tambaya bata taba batawa Hajjo habiba rai ba hakanan kullum amsarta dayace. Uban kabir yana sudan. . Sannu ahankali yana tafe yana fito kamar tsohon bature kabir ya karaso tagwayen dakunan daukar darasi anan ne sukayi kicibis da safiyya kabir baiji dadin ganinta ba domin yau ba ranarta bace kuma shi duk ya fara gajiya ma da ita domin tafiya naci. Safiyya duniya...daga ina haka? Kabir yace da faffadan murmushin karya lokaci guda kuma yana duban dan siririn wuyanta azuciyarsa yana cewa in banda shirmena ma ina ni ina wannan yarinya duk kashi duk zaman da suke da ita kabir bai lura da kashin ba sai jiya da farida ta matso kusa da shi ta rike hannunsa. Kai nake nema safiyya tace da murmushi gani kin samu...ya akayi? Mu tafi cikin motata ko motarka in fadama safiyya tace lokaci guda kuma ta kama hannunsa. Cikin sauri kabir ya girgiza kai sannan ya zare hannunsa daga cikin nata. Sauri nake zan koma gida hajiya ce ke nemana. Safiyya ta hade fuska. Haba kabir yaya zakayimin haka rabona dakai fa tun kusan jiya by this time ta karasa da turanci. Nace dake hajiya ce ke son ganina ki jirani zandawo na dauke ki in anjima da daddare sai mu tafi waje musha iska. Nan da nan fuskar safiyya ta washe cikin kwarkwasa ta dora hannayenta biyu akan tace a tausashe alkawari? Eh Promise kabir yace gamida gyada kai lokaci guda yana Allah Allah ta dauke hannunta daga kan kafadarsa kada Farida ta hangesu garinsa yayi kasa. Bari inje saina dawo kafin safiyya ta sami ta cewa tuni kabir yayi nisa safiyya ta bishi da kallo cikin mamaki me ke faruwa ne? Wannan baiyi kama da kabir din dana sani ba tace cikin zuciyarta. Yana tafe yana waige waige ko zai hangota kabir ya nufi inda motarsa take ya riga ya sani babu abinda zai hana farida zuwa domin yasan ta gama kamuwa dan haka yana zuwa saiya bude kofar gidan gaba na motar ya zauna yana yabar kofar a bude kafafunsa awaje sannan ya kunna rediyon dake gaban motar kidan zamani yafara tashi a tausashe sannan sai wani mawaki mai katon makwogwaro yafara wani abu mai kamar ihu matsayin waka. Baifi ko minti biyar da zama ba ya hangota ta nufo inda yake. Numfashinsa ya dauke cak sa'ar dayaga irin shigar da tayi. Saura kadan na cuci kaina ashe bebin nan haka tayi bala'in haduwa. Daga can nesa dashi Farida ta hange shi farin ciki yaso ya mamayi zuciyarta amma rufanin datake addabar zuciyarta shiya dakushe dukkan wani digo na farin cikin dake zuciyarta. Yanzu kam farida ta riga ta gama yarda da cewa batada lafiya matsala ta sameta tabbas tasan ta gamu da aljani tasha ji abakin kawayenta cewa aljanu suna hawa kan mata suyi ta wahalar dasu mahaifiyarta ma tasha yi mata fada akan barin gashin kanta awaje kokuma zama tsirara tsirara domin acewar mahaifiyarta wadannan abubuwa suke baiwa aljanu sha'awa har su hau kan mace suyi ta bugeta acikin jama'a. Farida tayi ajiyar zuciya a tsorace sa'ar data fahimci cewa idan ba wani ikon Allah ba itama kwanan nan aljanin zai fara bugeta tuni ta fara nadamar zuwa gidan dan daudun nan domin yi mata zanen kunshi akan tsaraicinta farida ta riga tasan wannan kunshi shine sanadiyyar wannan bala'in dake faruwa akanta daman mahaifiyarta tashafada mata cewa yawan fito da tsaraici a fili na cikin abinda ke sa aljanu su hau kan mata. . Farida ta dubi tafin hannayenta dakuma bayansu batayi mamaki ba sa'ar dataga zanen kunshin yadawo rangadadau kamar ma yanzu aka zana shi duk kuwa da cewa ta tabbata har lokacin da baba Ali ya sauketa hannunta babu zanen kunshin. Farida tayi matukar kyau awannan yammaci ita kanta ta sani domin inka dauke yan littattafan dake hannunta duk abin dake jikinta sabo ne tun daga kan riga da siket din da mahaifiyarta ta sayo mata a landan zuwa ga takalmin dake kafarta da yan kunnayenta da sarkoki kai hatta alkalamin rubutun dake hannunta sabo ne domin dazun ta saye shi. In banda farida ta riga tasan zanen kunshin dake hannunta na aljanu ne da sai tace shima ya taimaka wajen fito da kyawunta a fili. . Kai gaskiya yau kinyi bala'in haduwa. Kabir yace sa'ar da farida ta karaso inda yake lokaci guda kuma ya rage sautin kidan dake tashi. Nagode farida tace a tausashe. Naji dadi da kwalliyata tayi maka kyau Ah gaskiya tayimin zagayo ki shigo ciki kabir yace sannan ya mika hannunsa ya bude mata daya kofar. Ahankali farida ta shigo cikin motar ta zauna sannan ta rufo kofar, shima kabir ya rufe kofar ya kunna na'urar sanyi kana ya dubeta farida ta lura da irin kallon dayakeyi mata dan haka cikin bin umarnin shaidaniyar kawarta Asma'u saita dan bude gaban rigarta kadan domin kabir ya sami damar hango tsakanin kirjinta sannan saita dan matsa kusa da jikinsa ta dora kanta akan kafadarsa. Ilove You Kabir. Kabir yaji kama ta watsa masa ruwan sanyi azuciya a wannan dan takin dakikar saiyaji kaunarta ta mamaye zuciyarsa amma a iya lokacin nan kawai kafin shaidan ya maye gurbin da sha'awa. Daga nan idan mun tashi ina zamu? Kabir ya tambayeta yana wani lumlumshe idanu sannan ya kama hannayenta biyu yana kallon zanen kunshin dake jiki. Farida ta dubeshi cikin mamaki tace Gida mana ba gida kace zaka kaini ba? Kabir ya dubeta ido da ido ya girgiza kai yace, sai mun fara biyawa ta gidan wani abokina kafin nakai ki gidan domin can zamufi samun sake. Farida taji gabanta ya fadi bata dauka abin zaikai ga haka ba yaushe za'ace ta bishi wani gidan aboki. Ina ganin muyi hirarmu anan dai zaifi kyau... Farida tace a tausashe zuciyarta na harbawa tana tsoron kada ta batawa kabir rai. Kabir ya kamo tafukan hannayenta guda biyu ya dorasu akan fuskarsa yace. Ina kaunar ki ne farida shi yasa na nemi ki bini domin in nuna miki yadda nake kaunarki. Farida taji gabanta ya fadi ahankali ta zame hannayenta a wayance daga kan fuskarsa. Haba farida bakya.... Kalmar ta makale a fatar bakin kabir sa'ar dayaga yanayin fuskar farida ta sauya nan da nan da kabir ya kalli fuskarsa a jikin madubi alokacin daya hangi irin zanen kunshin dake tafin hannunta rangadadau a zane akan kumatunsa kamar yi masa akayi. . Kada ki damu idan bakya son zuwa yanzu maje watarana kabir yace da ita cikin sauri shi a haukansa ya dauka abinda yace ne ya birkita kamanninta. Farida ta gyada kai babu magana idanunta zuru akan zanen fulawar dake kan kumatunsa. Ganin haryanzu batayi fara'a ba sai kabir ya rankwafa jikinta yana cewa haba farida....kiyi min murmushi mana konaji dan dadi dadi yana gama fadin haka sai ya zura hannayensa ya tallafo kanta sannan ya tura bakinsa gaba da nufin zai sumbaceta anan ne to wani abu mai kamar hannu ya zuro cikin motar kamar daga sama ya kifawa Kabir Mari. Wayyo Allah... Kabir yasa ihu sa'ar da yaga wani haske kamar wuta ya gifta akan fuskarsa. Wayyo... Wayyo dan Allah ki taimakeni za'a kasheni kabir ya sake kwala ihu sannan a rude sai ya bude kofar motar ya fada kasa yana birgima afilin ajje motoci na jami'ar bayero. Daga yau ka sake lalata ya'yan mutane dan banza lalatacce an fadama matata irin matan da zaka iya tabawa ce. Wata kakkausar murya tace daga sama sannan sai aka kece da kakkausar dariya. Tsananin kaduwa da tsoro su suka hana farida yin motsi tana nan zaune akan kujerar motar kamar gunki tana hangen kabir yana ta murkususu adaidai lokacin ne to ta lura da wasu fararen abubuwa masu kama da kashi akan cinyarta hannunta na rawa farida ta dauki fafaren abubuwan. Saida ta kura musu idanu sannan ta gane ashe Hakoran mutum ne guda uku wannan shiya sata bude kofar motar ta fice aguje sannan tasa kabir agaba ta fara Ihu. Nan da nan gurin ya cika da dalibai hadiman jami'ar masu gadi da shara aka zagaye kabir an rasa mai taba shi can sai wani kakkarfan dattijo mai shara ya matso ya tashi kabir da kyar daga kan fuskarsa jini na zuba nan da nan daliban dake zagaye dashi suka rike numfashi a razane sa'ar da sukaga bakin Kabir ya karkace ya koma baya gashi babu hakoran gaba. Ku kamamin mu shiga dashi cikin makaranta ayi masa addu'a ina zaton aljanu ne suka shafe shi. Dattijon yace. . BABI NA UKU 3 Abayan katuwar sakatariyar gwamnati ta tarayya abuja jama'a ne jingim maza da mata kowa nasha'anin gabansa wasu nata sunturi daga can zuwa nan suna kokarin neman kwatancen ofishin wanda suke nema domin neman aiki ko kuma maula hakanan agefe guda lemomin masu wayar haya acikin rana sunyi sahu sahu jama'a har jerin gwano sukeyi suna sayen katin waya da kuma buga wayar haya don su sami zantawa da wadanda suka zo nema. Acikin wadannan mutane masu waya hardasu MAMA. Mama tayi tsaki sa'ar data danna lambar kawarta Bebi a karo na ashirin ana cewa wayar a kashe. Yaya bebi zatayimin haka? Mama ta tambayi kanta acikin damuwa. Mama tazo sakateriyar ne badon takira wayar haya ba sai dan anan ne bebi tace idan tazo ta kirata zatazo ta sameta agurin daga nan kuma su wuce gidan da nata honorabil din ya ajiyeta aciki. Mama ta sake danna lambar wayar bebi akaro na ashirin da daya cikin damuwa domin idan har bata samu bebi ba tashiga cikin matsala dan ko kudin da zata koma kano batadashi adaidai wannan lokacin ne wayar dake hannunta ta dauki kara cikin sauri mama ta dubi lambar dake fuskar wayar ta dauka bebi ce Mama tayi tsaki sa'ar da taga ashe lambar ALHAJI BILYAMINU ce matsolon saurayinta na kano Hello menene? Mama tace dashi a fusace kuma fada- fada, bi ahankali kada ki fasa min dodon kunne Alhaji Bilyaminu yace acan daya bangaren kina inane? Nazo gidanku ance min wai tun da sassafe kika fita. Nayi tafiya ne mama tace a yatsine Eh naji kinyi tafiya kina ina nace? Ni ganinki nake sonyi. Bazaka sami ganina ba ayau jibi ma albarka dan ina abuja Alhaji bilyaminu ya rike numfashi acan daya bangaren haba mama yaya zakiyi tafiya batareda kin sanar dani ba? A'a yau kajini da mutum mama tace cikin wayar da karaji aurena kakeyi kokuwa zaman daduro muke dakai? Duk da babu ko daya dai acikin abinda kike fada ai yakamata kisanar dani. To banyi niyya ba kai ni kaga nafa gaji da hulda da marowatan mutane irinka yar motar nan ma ka kasa sayamin sai ka bushi iska kazo ka uzuramin. Haba mama meye yayi zafi haka? Ba nace zan saya miki motar acikin wannan watan ba? Haka dai kace amma wa yaga sayen mama tace gamida tsaki sannan sai tayi kamar zata katse wayar da sukeyi kada ki kashe wayar dan Allah mama yanzu yaushe zaki dawo? Idan naga kidin mota cash acikin bakina. Babu komai Alhaji bilyamin yace cikin sauri ki dawo gobe sai in saya miki bazan dawo gobe ba domin ayanzu haka ma kofar Nikon Hotel nake inajiran wani darling dina ya fito dan majalisa ne wanda yasan abinda akeyi da kudi ba irinka ba. Alhaji bilyaminu yaji wani matsanancin kishi ya tuke zuciyarsa kai kace wata matarsa ce ta aure. Amma agaskiya mama baki kyauta min ba yanzu duk irin wahalar da nakeyi miki sai kinbi wani mutum har zuwa abuja. Idan kaji haushi ka ajjeni daduro mana ko kuma ka aureni idan zaka iya. Alhaji bilya ya dauke wuta na yan dakiku sannan saiya tausasa murya yace. Allah baki hakuri mama...yanzu yaushe zaki dawo. Nan da sati guda idan naga dubu dari shida kudin sayan mota acikin bankina idan kuwa naji shiru me yiwuwa har abada bazaka sake ganina ba. Har abada fa kikace? Kwarai kuwa angaya ma kano garin mu ce ko ka manta ni yar gombe ce? Zan turo miki da kudin gobe kiyimin text din lambar asusun bankin naki yanzu kuma dan Allah ina jiranki din idan zi yiwu ma ki dawo nan da kwana uku. To shikenan saika turo din mama tace a yatsine sannan batareda ta sake bashi damar cewa kala ba saita kashe wayar sannan ta dira kafa akasa cikin murna lallai abin da malamin tsibbun nan ya fada min gaskiyane daman saida yace shi maganin kadan kadan yake ci na fi wata shida ina zuba mai magani a abinci yanaci amma shegen ya kasa yimin koda kyautar dubu arba'in sai gashi yanzu a banza zai saya min mota. Duk da ya rude ya dauka bazai sake ganina ba mama ce ke fadin haka cikin zuciyarta sannan saita kudiri aniyar in har alhaji bilyaminu ya saya mata mota saita sayawa malaminta mashin. Mama taci gaba da lallatsa lambar bebi yanzu kam damuwar dake tattare da ita ta ragu domin tasan in babu nan akwai can idan hagu taki saita koma dama tasan ko bata sami ganin bebi ba tana iya yin waya Alhaji Bilyaminu ya turo mata koda katin waya ne ta sayar domin ta sami kudin mota. Wayar mama ta sake daukar ruri akaro na biyu awannan karonma mama tayi zaton ko bebi ce amma data duba fuskar waya sai taga ashe bakuwar lambace yanzu haka ma wani wahalallan ne mama tace gamida tsaki sannan ta kara wayar a kunne. Hello wanene? Nice bebi dan Allah mama kiyi hakuri wallahi wayata na jefar yanzun nan wata wayar na aiaka aka sayomin kina ina? Mama tayi ajiyar zuciya ina nan Federal secretaria inda kikace na tsaya nafi awa daya da sauka. Oh kiyi hakuri kawata gamu nan zuwa yanzun nan ai gidan babu nisa da inda kike. Mintina goma da wannan sai gasu bayan mota kirar fijo wata dunkulalliya mai kamar kwai wani dogon direba mai dogon sanko kamar titin mota ne ke janta. Fara tafiyarsu keda wuya sai direban motar yakunna na'urar sanyi nan da nan sassanyar iska ta fara fifita su. mama tayi ajiyar zuciya sa'ar dataji sanyin iskar ya fara busar da guminta. . Kina hutawa kawata mama tace da bebi. Toh ya muka iya haka nan hali yayi bebi tace sannan ta kalli hannun mama tayi kasa kasa da murya yadda direban bazai iya jinsu ba tace. Shegiya kawata tsumma makunshin cuta mage mai kwanciyar daurar rai a ina akayi miki wannan hadadden zanen kunshin. Mama ta dubi hannunta cikin mamaki sannan ne to taji kamar na'urar sanyin ta fara huro mata zafi mama tayi imani dacewa har sa'ar data shiga cikin motar babu wani zane a hannunta amma sai gashi yanzu ya bayyana rangadadau kamar ma yanzu aka gama zana shi. Meye naga kin hade rai? Shegiya wallahi da gaske nakeyi ba tsokanarki nake yi ba wannan idan nayi wasa ai saiki kwace har nawa honorabil din bebi ce ke fadi sa'ar da taga yanayin fuskar mama. Mama ta feso murmushin karfin hali tace aina dauka tsokanata kikeyi kokusa wallahi kai zanen naki yayi kyau idan muka koma kano sai kin rakani inda akayi miki wannan bebi tace lokaci guda kuma ta kama hannun mama tana dubawa. Kai yaya naji hannunki sanyi karau kamar kankara lafiyarki kuwa? Mama ta dubi kawarta da murmushin yake tace Lafiyar kenan me kika gani? ** ** ** ** ** HONORABIL JATAU ya kurawa mama idanu baya ko kiftawa kamar wani tsohon maye tabbas ya yaba da abinda yagani. Acikin wani katon dakin shakatawa suke a tsakiyar wani gida wanda ke boye abayan wani munafikin lumbun shakatawa su hudune acikin dakin daga bangaren gabas bebi ce da kawarta mama kowannensu sanye da wata irin doguwar rigar Alatsine mai shara share kamar buhun algarara. Abangaren yamma na dakin honorabil jatau ne zaune da babban abokinsa HONORABIL SABO wanda shine saurayin Bebi. Tun sa'ar da mama ta sauka agidan shakatawa na honorabil sabo saurayin bebi basu sami ganinsa ba sai washegari da misalin karfe goman dare yashigo gidan acewarsa in dai har ba karya yake ba wai tun jiya suke gurin taro basu fito ba sai yanzu wannan bata dami bebi da mama ba domin sun huta sun wala abinsu katon gidan na alfarma babu kowa aciki sai su da wani dan dukurkushin kare mai yawan gashi irin na turawa da kuma masu dafa musu abinci idan sunci abinci sai suyi kwanciyarsu suyita barci idan sun farka su kunna talabijin suyita kallon fina finan da ake watsawa a kasashen turai. Babu abinda ya dame su duk abinda suke bukata magana kawai zasuyi sai akawo musu. Sa'ar da honorabil sabo ya dawo ne da misalin karfe goma sai suka gaisa da mama shi kansa ya yaba da abinda yagani to saidai kuma bai isa ya nuna hakan a zahiri ba tun da dai ga bebi manne akusa dashi kamar cingam bayan yayi wanka ya huta sai ya bugawa abokinsa honorabil jatau waya domin ya sanar dashi cewar bakuwarsa ta sauka kuma gasu nan zasuzo gidansa yanzun nan. . Sannu da zuwa mama honorabil jatau yace yana dubanta da yan mici micin idanunsa kamsu kama dana maciji tabbas ayadda yaga mama azahiri har tafi yadda yaganta a hoto burgewa. Ina ganin saimu tafi ko? Tun da mun hadaku. Honorabil sabo yace sannan ya mike tsaye gamida yiwa bebi alamar ta mike tsaye to kawata sai yaushe kenan mama ta tambayi bebi. Zamuyi waya bebi tace gamida kashe mata idanu. Da haka suka fice daga dakin fitarsu keda wuya ko motarsu basu tayarba honorabil jatau ya dawo kusa da mama ya zauna sannan ya dora hannayensa biyu akan kafadarta yace. Naji dadin zuwanki mama hotonki ya burgeni to ashe azahiri ma har kinfi haka burgewa inason ki sani cewa bazaki yi nadamar zuwan da kikayi ba. Mama ta lumshe idanu irin na kwararriyar karuwa sannan ta kwanta ajikinsa tace. Kaima bazakayi nadamar gayyatata da kayi ba. . Abinda basu sani ba shine wani acikinsu yayi kuskure. . Tashi mu shiga daki naga dare yayi sosai ko? Babu musu mama ta mike tsaye sannan saita bishi abaya zuwa cikin wani dakin kwana da bata taba ganin irinsa ba koda acikin mafalki lokacin sanyi. Lokacin da duk wannan ke faruwa karfe biyu saura ne na dare. . Dare yayi dare birnin tarayya yayi shiru bakajin komai sai jifa jifan haushin karnuka nan da can dakuma kukan tsuntsaye shima jifa jifa haka nan da mutum zai kasa kunne da kyau bazai rasa jin rurin dubban na'urorin sanyaya dakunan dake ta famar aiki ba'a acikin birnin. Dan haka ba dole bane wadannan yan kananan sautuka su dami honorabil jatau da mama ba wadanda ke kwance abinsu akan gadon alfarma barci har da munshari sannu ahankali dakiku na wucewa lokaci na matsowa har dai dan gajeren hannun dake fuskar wani kyakkyawan agogo na azurfa dake ajiye a gefen gadon ya nuna karfe hudu na asuba. Honorabil jatau ya matso adaidai wannan lokacin sannan ya tashi zaune akan gadon daga shi sai gajeren wando yana mutsutstsuka idanu. Bayan wasu yan dakiku idanunsa suka washe

Chapter 3 of 7