Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
mance ne ban tambayeki inda akayi miki wannan zanen kunshin ba. . Har zuwa lokacin da farida ta shiga farfajiyar dan daudu Amara idanunta basu daina nuna mata hannayen safiyya akan kafadar masoyinta ba. . Salamun Alaikum......sannunku farida tayiwa Fadila da mama sa'ar data shigo falon. Dan Allah anan ne ake kunshin nan? Fadila ta dubeta da murmushin yake domin haryanzu sanyi takeji. Eh nan ne kema saiki jira mu ma shi muke jira. Zaman farida keda wuya saitaji wata irin iska mai sanyi ta fara ratsa kashi da bargonta nan da nan taji jikinta ya fara rawa. Kai wannan wane irin sanyi ne? Mu ma haka muka tarar dashi mama tace cikin damuwa sannan saita dada da cewa ko waje zamu fita mu jira shi Ina ganin dai gaskiya zaifi fadila tace ta fara mikewa kenan. . Sai sukaga wani irin farin hayaki ya rufe kofar dakin sassanyar iska taci gaba da hurowa cikin dakin. . Me kuma zakuyi awaje bayan gani nazo ko bani kuke jira ba kanne na? Wata zazzakar murya tace dasu daga cikin hayakin. ** ** ** ** ** Matan uku suka dubi kofar dakin a tsorace cikin tsananin firgici sannan ga mamakinsu sai sukaga hayanin ya washe kamar ma ba'a halicce shi agurin ba. Sannunku da zuwa. Amara dan daudu yace dasu shine a tsaye akofar dakin maimakon farin hayakin. Nashiga uku mama tace tana duban amara a tsorace wannan wane irin hayaki ne amara duk kabi ka tsorata mu. Kuyi hakuri kannena dan daudu amara yace dasu. Wani sabon sinadari ne mai sanyin hayaki nake turara mutane dashi kafin nayi musu zane idan akayi haka yafi fitowa rangadadau. Da kuka shigo bakuji sanyi ko ina ba? Matan uku suka dubi juna sannan sukayi ajiyar zuciya munji suka amsa baki daya. Amara ya dube su da murmushi wacece tafara zuwa acikin kannen nawa? Fadila ta mike tsaye gamida duban agogonta har yanzu jikinta rawa yakeyi batasan abinda yasa ba amma har yanzu a tsorace take duk da yake wannan shine karo na kusan hudu da za'ayi mata kunshin sa'ar data dubi Amara saitaji gaba daya hankalinta bai kwanta dashi ba. Muje to nafara dake kanwata Amara yace da fadila sa'ar da yaga ta mike tsaye Suna nan zaune acikin Dakin Amara yagama zane kirjinta yadawo zuwa kan cinyoyinta. Yau naga kamar baka son hira Amara kamar ba kai ba ko baka ganeni bane? Fadila tace dashi yi hakuri yar uwata ai ina shigowa na ganeki....wallahi dan karin kudin sinadarin aikin nan ne aka samu duk yabata min rai. Bayan wani lokaci mai dan tsayi Amara yagama zane Fadila da mama wadanda suka dawo dakin jiran kusan jikinsu tsirara suka zauna akan wani kilishi mai taushi acan karshen falon domin su jira zanen ya bushe kafin kuma daga baya su wanke sannan sai a goga musu sinadarin Hydrogen wanda shike sa zanen yayi baki adaidai lokacinda amara yana can cikin daya dakin yana zane Farida. Ana cikin wannan hali ne kofar falon dake fuskantar waje ta bude sannan Fadila da mama suka yi duba I zuwa abunda ya dada sasu cikin firgici a tsaye abakin kofar dakin AMARA ne sanye da doguwar Jallabiya fara. . Sannunku da zuwa Amara yace dasu yana kallon zanen kunshin dake kan cinyoyinsu da kirjinsu. Mama ta dube shi cikin kaduwa tace Sannunmu da zuwa ina...yaushe ka fito daga dakin harka fice waje bamu ganka ba? Amara ya dubi mama cikin mamaki yace Ke Ja'ira kada kiyimin sharri ni rabona da gidan tun safe ina kasuwa ruwa ya rutsani sannan sai ya kalli zanen kunshin dake jikinsu yace. Wanene yayi muku wannan ku kukayi da kanku? Kada ka raina mana hankali mana ba kai ka gama yi mana zanen ba ina dayar da kakeyiwa? Inka gama mata ai gara kazo kasa mana Hydrogen din nan ko ma tafi mun dade anan mama tace. Ki rufamin asiri in mutu yan mata su kaini kinga ni tun da gari ya waye yau banyiwa kowa zanen kunshi ba. Jin haka keda wuya sai Fadila ta mike tsaye a tsorace ta dubi Amara tace. Kana da dan uwane yan biyu? Amara ya girgiza kai kafin tagama magana sai sukaji acan daya dakin Farida ta kwala ihu nan da nan su uku suka nufi dakin a tsorace suna shiga dakin suka tarar da Farida rabin jikinta tsirara an gama zaneta cinyarta dayace kawai ta rage babu zane. A ina yake mama ta tambaya a tsorace farida ta dubesu cikin kuka tace YA ZAMA HAYAKI. . Amara ya dubi sararin samaniyar dakinsa sai ya hangi sauran farin hayakin a makale. Na fada muku bani bane to in ba kaibane wanene? Fadila ta tambaye shi kamar zata fashe da kuka. Hahahahhaha wata kakkausar murya ta fashe da dariya sannan sai sukaji daga sama ance KUNYI KUNSHIN KARSHE YAN' MATA. . BABI NA DAYA 1 Hayaniyar biki gamida farin cikin ganin Faisal ya zama nata su suka mantar da Amarya Fadila rudanin daya faru agidan dan daudu Amara da farko sa'ar da aka shiga hayaniyar bikin duk kusan minti biyar sai gaban Fadila ya fadi idan ta tuna sa'ar da kakkausar muryan nan ta kece da dariya to amma daga baya sa'ar da kawaye da yan uwa gami da abokan arziki suka zagayeta sai zuciyar Fadila ta shagalta izuwa shagalin bikinta to amma fa duk da haka jifa jifa takan tuna kalmar Amara sa'ar da kakkausar muryar ta kece da dariya. Meye naga kunyi wani zuru zuru daku kamar kunyiwa sarki karya? Amara yace dasu sa'ar dayaga matan ukun sun dubi saman dakin a firgice. Kaga dan Allah amara idan wani ka boye yake bamu tsoro to kace ya bari ni wallahi bana son irin wannan wasan mama tace dashi. Yau na shigesu ni Amara kinjini da yan mata wai maganar me kuke ne? Kai kurma ne bakaji dariyar da akeyi a saman dakin nan ba? Duk abinda akeyi Fadila na gefe jiki na rawa kamar mazari ita ko magana bata iyayi jim kadan da gama maganar mama sai farida ta ruga aguje ta fice daga dakin ganin haka sai fadila da mama suma sukabi bayanta a gurguje suma suma fice daga cikin gidan. Yau Allah ya hadani da mahaukatan mata oh ni 'yasu in da ranka kasha kallo amara yace sannan ya taba cinya gami da shewa abinsa. . Kanwata. Mama tace Fadila a daidai lokacin da suka zo karshen munafikin lungun in ba damuwa ki bani lambar wayarki mana make gaisawa ba dan komai mama ta tambayi lambar wayar fadila ba sai don kawai taji aranta tana kaunarta domin tana son taga farar mace kyakkyawa domin wannan shine kawai abinda ya ragu a jarinta na karuwanci. Kawo wayarki nasa miki fadila tace da mama tana kallonta rabi a tsorace rabi kuma a yatsine tabbas mama bata kwantawa fadila azuciya ba domin tun sa'ar da mama ta shigo ta sameta a falon dan daudu fadila ta lura da tambarin bariki akan fuskar mama. In badan rudanin daya samesu tare ba da babu abinda zaisa fadila ta baiwa mama lambar wayarta. Nagode bari nayi miki Flashing saikiyi sebin din lambata mama tace sa'ar da fadila tasa mata lambar wayar. Mintuna uku da faruwar haka fadila shiga cikin Jeep dinta ta wuce mama tsaye abakin titi tana jiran tasi. Mama ta dagawa fadila hannu amma fadila bata damu da ta rama mata ba. . Duk wannan al'amura sun zama tarihi a gun amarya fadila anyi biki lafiya an tashi lafiya an kaita dakin mijinta babban masoyinta Faisal mutumin da take kauna fiye da kowa aduniya. Adaren amarcinsu na farko bayan kawaye da abokan ango sun tafi sun barsu su kadai daga fadila sai angonta faisal wanda shima mahaifinsa na da abin hannu amma bai kai mahaifin Fadila ba. Awannan dare ne to abinda Fadila ta dauka tamkar wani shudadden mafarki kokuma wata binnanniyar gawa ya fara FATALWA. Zaune suke a dakin kwanansu akan wani fankadeden gado na alfarma wanda akalla zai iya daukan mutum biyar batareda kowa yaji hucin dan uwansa ba. Fadila ta dubi faisal sannan faisal ya dubi fadila sai suka fashe da wata tattausar dariya lokaci guda cikin farin ciki. Dariyar me kakeyi? Ke dai zan tambaya dariyar me kikeyi? Masoyan suka sake yiwa juna murmushi Faisal barci nakeji. Fadila tace dashi tana lumshe idanu cikin wata shagwababbiyar murya. To ki kwanta mana ko so kike na kwantar dake Uhm fadila tace gami da gyada kai. Faisal ya matso kusa da ita ya dora hannayensa akan kafadarta cikin murmushi sannan yafara kokarin kwantar da ita. Uhm Uhm ni ba anan zan kwanta ba Fadila tace tana wata girgiza cikin shagwaba. To fadila a ina kike son kwanciya? Anan fadila tace gamida nuna cinyoyinsa. Faisal ya fashe da dariya fadila kenan duk fadin gadon nan ki rasa inda zaki kwanta sai akan cinayata. Nidai anan zan kwanta fadila ta kuma fadi cikin shagwaba faisal yayi ajiyar zuciya sannu ahankali sai fadila ta kwanta akan cinyarsa ta yadda fuskokinsu zasuke kallon juna fuskar faisal dauke da faffadan murmushi ya kamo santala santalan hannayenta Fadila. Ya kallesu sannan sai ya dubeta cikin mamaki. A ina zanen kunshin da nace inason kiyi min duk ranar da za'a kawomin ke? Fadila taji gabanta ya fadi ras da faisal yasan abinda maganar zata janyo da baiyi ta ba. Nan da nan sai wani zazzafan gumi ya fara sartu akan dogon wuyan fadila hankalinta ya tashi tunaninta ya yamutse lokaci guda kuma ta fara tunanin irin karyar da zatayiwa faisal domin tasan haryanzu akwai shatin zanen da aljanin nan yayi ajikinta to saidai bai fito sosai ba domin ba shafa masa sinadarin hydrogen ba sa'ar da gayyar ta watse gashi kuma bata san ta sabawa faisal dan tasan yanada zafin zuciya idan ranshi ya baci. . Yaya naji kinyi shiru? Faisal yace da ita cikin murmushi da kuma mamaki domin ya lura kamar yanayin fuskarta ya sauya haka nan ta sandare ajikinsa shagwabar da takeyi baki daya ta bar jikinta. Nayi ma laifi my darling fadila tace cikin wata sassanyar murya alokaci guda kuma kwakwalwarta na kokarin nemo abin fada. Haba fadila laifin me kikayi min? Kisan fa ance wai amarya bata laifi koda ta kashe dan masu gida. Kunshin da kace nayi ma ne ba'a gama ba muka baro gidan an gama zanen kenan za'a sa hydrogen sinadarin dayake sa shi yayi bakin nan sai mama tayi min waya tace nayi maza na koma gida ana jirana duba ka gani zaka ga ma shatin zanen Fadila tace lokaci guda kuma ta mika masa hannayenta tana daga kwance. Faisal ya dubi hannayenta cikin murmushi yana nazarinsu Fadila kenan ke dai in bakiyi ba kawai shikenan ba sai kinyimin karya ba ni banga sanen komai ahannunki ba. . Jin haka keda wuya sai fadila ta bar jikinsa ta tashi zaune. Haba Darling yaya zanyi ma karya bayan ga.....kalmar ta makale acikin fatar bakinta domin ta lura ko sama ko kasa Allah masani amma zanen dake hannunta ya bace baki daya kamar ma ba'a taba zana shi ba. Faisal ya dubeta cikin murmushi sa'ar dayaga kamanninta sun sauya ta firgice cikin sauri ya janyota jikinsa yana cewa. Haba Fadila me yayi zafi haka da har zaki tashi hankalinki adaren amarcinmu na farko? Dan bakiyi kunshi ba ai ba wani laifi bane nan gaba idan inaso basai muje duk inda kike so ayi miki ba. Fadila ta kankame shi gamida ajiyar zuciya ta tabbata mintuna biyu da suka gabata kafin ta kwanta akan cinyarsa ta lura da zanen ahannunta tayaya kuma za'ace ya bace cikin mintina biyu? Tambayar kenan datayiwa kanta babu Amsa. ** ** ** ** Washegari da la'asar sakaliya misalin karfe biyar da rabi amarya fadila ta fito daga wanka daure da wani farin tawul tattausa ajikina tana tafiya tana yauki kamar zata tsinke ta zauna akan waata doguwar kujera dake gaban wani kyakkyawan madubi na musamman da akayi mata shi don Kwalliya. Tun da garin Allah ya waye fadila ke tare da angonta suna ta wasanni na soyayya bashi ya fita ba sai karfe hudu acewarsa abokai zaije yiwa bangajiya. Kada ka dade don Allah.....ni banason zama ni kadai awannan katon gidan fadila tace dashi sa'ar daya shirya zaifita kanta akan kafadarsa. Bazan dade ba my....karfe takwas ina gida. To shikenan fadila tace cikin shagwaba kataho min da wani abu mai dadi karkiji komai idan zan dawo zan zo miki da TUBANI. La.. Me zanyi dashi fadila tace cikin dariya tubani ba shine wanda na karanta a littafin KARYA LINZAMIN SHAIDAN wai wani tsoho yanaci ba. Ko bashi kake nufi ba? Shi nake nufi mana my darling faisal yace cikin dariya. Cab. So kake kenan in mutu idan na hadiyi wannan abin ai sai ankaini asibiti. Suka fashe da dariya lokaci guda da haka suna tafiya suna hira hannayensu kamar zasu shafi juna ta rakashi har farfajiyar gidan inda motocinsu na hawa guda hudu ke tsaye sunyi jerin sahu faisal ya zabi wata karama kirar honda ya hau. Fadila na tsaye a farfajiyar gidan tana daga masa hannu har saida ya fice. Lokacin data dawo fankacecen dakin shakatawar na alfarma saitaji duk kadaici ya lullubeta hakanan duk saitaji gabanta nata faduwa hakan shiyasata kunna talabijin sannan ta kamo tashar kasar larabawa wata balarabiya yar masa masar ce mai katon baki take cashewa amma katon bakinta bai hana makwagoronta feso waka mai dadi ba. Fadila ta lume cikin daya daga cikin kujerun alfarma da suka zagaye dakin kofin tangaran dauke da tacaccen lemo ahannunta na hadun taci gaba da kallon wake waken larabawan wannan shiya dauke mata damuwa har zuwa sa'ar da taga yakamata ta tashi ta sake wanka domin taren mijinta faisal tana fitowa daga wankan sai saita nufi Madubi. . Daga inda take zaune ayanzu tana fuskantar madubin fadila na iya jiyo rugugin aradu sakamakon hadarin dake lillibe da sararin samaniya hakanan amaryar na iya hangen shuke shuken alfarma da furanni na zamani wadanda ke jere sahu sahu a farfajiyar gidan abin gwanin ban sha'awa sunata rangaji cikin iskar daminar kamar yan amshin shata. Fadila ta dawo da hankalinta kan madubin ta fara nazarin hannayenta da kafafunta da kuma kirjinta cikin mamaki da fargaba domin ko kusa ko alama duk shacin zanen nan da akayi mata ya bace babu alamunsa ko da kankane. Na rabu da jaraba fadila tace gamida ajiyar zuciya kana saita shafi goshinta ga maminta saitaga kamar ta fara gumi sannan ne to ta lura shema na'urar sanyaya dakin ba'a kunne take ba gashi kuma garin ya daure babu iska sakamakon bakin dake ta haduwa. Fadila tasa wani farin mataji ta korashi tsakanin siraran gashinta sannan ta mike ahankali ta nufi inda makunnar na'urar sanyaya daki take ta kunna sannan ta dawo gurin zamanta ta zauna taci gaba da shafe shafe irin na mata batafi k minti guda da zama ba saitaji iskar na'urar ta fara sanyaya dakin fadila tayi ajiyar zuciya sa'ar da sassanyar iskar ta fara ratsata lokaci guda kuma taci gaba da nazarin surorin jikinta a fuskar mudubin tana yabawa da abinda ta gani ita kanta tasan kyakkyawa ce wata sa'ar tana kwalliya ne kawai saboda dai wai ance sabo da tayi wai gawa da yatsine amma fadila tasan ko batayi kwalliya ba ita kyakkyawa ce. Iskar na'urar sanyaya dakin taci gaba da fifita fadila ganin ruwan wankan dake jikinta yafara bushewa sai fadila ta matso wani tattausan mai fari daga cikin wata doguwar roba mai kamar jallo ta fara shafawa ahannunta daga nan sai kirjinta sai kuma kan cinyoyinta zuwa sangalalin kafadunta bayan ta gama saita dago ta sake nazarin jikinta a fuskar madubin sannan ne to taga abinda yasa numfashi da yawun bakinta daukewa. A zane radau radau tun daga kan hannayenta da kirjinta zuwa kan cinyoyinta zanen kunshin nan ne na surorin furanni baki sidik ya bayyana a fili abin gwanin ban sha'awa saidai kuma fadila bata san daga inda zanen ya bullo ba. . Na shiga uku fadila tace a firgice gami da dake kirji lokaci guda kuma ta dauke fuskarta daga kan madubin a tsorace ta dubi sassan jikinta a zahiri har yanzu zanen kunshin na nan randagagu ajikinta ba wai madubin ne ke fada mata karya ba. Na shiga uku....wayyo Allah fadila tace cikin karaji sa'ar data fara ja da baya da baya a tsorace tana barin jikin madubin. . Baki shiga uku ba matata.... Ki kuma bi ahankali kada ki takani don gani nan tsaye abayanki ina yabawa da abinda na aura. Wata busashshiyar murya ce ke fada daga bayanta fadila ta rufe baki domin ihun ma yakasa fita daga makogwaranta ta juya ta dubi bayanta cikin tsananin firgici wayam bataga kowa ba. Wanene? Fadila ta tambaya cikin wata murya data kasa ganewa amatsayin tata. Wani mai sha'awar surar jikin ne.... Zanen kunshin nan ya karbe ki bazan taba daina kaunarki ba muddin ina kallonsa. Aka sake kecewa da kakkausar dariya sannan sai farin hayaki ya turnuke dakin. Acan wani bangare na sararin samaniyar birnin kano aka saki rugugin aradu mai karar gaske fadila ta toshe kunnuwanta sannan ta fadi rub da ciki akan tattausan kilishin dake daben dakin. ** ** ** ** Fadila ta farka agigice daga nannauyan barcin rudanin daya dauketa sannu ahankali ta mika hannu ta dauko wayarta dake ajje akan gadon kusa da ita ta duba lokaci. Karfe takwas da minti arba'in nan da nan sai fadila ta mike zaune zumbur a tsorace tana waige waige akan faffadan gadon. Ina faisal me ya hanashi dawowa haryanzu shida yace karfe takwas zai dawo. Tambayar kenan data farayiwa kanta sannan ne to abubuwan da suka a yammacin suka fara dawowa kwakwalwarta. Ita kanta fadila batasan ta yadda akayi ta kawo kanta cikin dakin kwanansu daga falon gidan ba. Abinda kawai da zata iya tunawa shine bayan farin hayakin ya washe ta tallaba a tsorace ta fada kan gado ta fashe da kuka batasan sa'ar da barci ya dauketa ba. . Fadila ta muskuta akan gadon a tsorace adaidai lokacin ne to taji an sake sakin wata katuwar tsawa sannan saitaji saurin ruwan sama ya fara sauka ajikin tagogin dakin fadila ta sake kallon lokaci ajikin wayarta. Tara saura minti biyar sannan ne to fadila ta yanke shawarar karshe aranta. Tabbas in har taran dare tayi faisal bai dawo ba to ko me zai faru kome aljanin nan zaiyi mata saidai yayi amma ficewa zatayi daga gidan gara ta koma gidansu. Wani zazzafan hawayen takaici ya fara sartu akan kumatun fadila yaya kwana daya kawai agidan masoyinta duk wannan bala'in zaiyita faruwa akanta ta tambayi kanta sannan ta dauki wayarta ta fara buga lambar faisal kwata kwata tsoro da fargaba sun raunana tunaninta abinda ya kamata fa ace tayi kenan tun dazu ta neme shi awaya domin tasan inda yake. Tafara danna lambar kenan saitaji an kwankwasa dakin sannan aka fara turowa zuciyar fadila ta harba tsakanin hakarkarinta nan da nan ta jefar da wayar ta nufi kofar dakin aguje. . Gani nan darling bari na bude maka. Fadila tace muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka fadila tayi tsalle ta rumgume faisal sa'ar data bude kofar cikin kuka faisal ya dauketa kamar yar tsana ya ajjeta akan gado sannan ya dubi fuskarta a tausashe Kukan me kikeyi? Kadan ya rage fadila ta fada masa abinda ke faruwa to sai kuma tayi tunanin me yiwuwa ma in ta fada masa yace ko zautuwa tayi adaidai wannan lokaci kuma sai fadila ta tuna da zanen kunshin daya dawo jikinta gabanta ya kuma faduwa shin yanzu idan faisal ya tambayeta inda akayi mata kunshin tace dashi me? Ita dai tasan bazai yiyu ba tace dashi bayan yafita itama ta fice domin ayi mata zanen kunshi ba. Wannan na iya harzukashi domin tasan zuciyar faisal. Kinyi shiru kina kallona kukan me kikeyi? Faisal yace da tattausan murmushi lokaci guda kuma ya dubi hannunta kamar zai kama koda fadila ta dubi hannayenta sai taga zanen kunshin ya bace babu shi babu alamarsa jikinta ya dauki rawa sannan saitayi ajiyar zuciya ta kalli faisal tace a tausashe. Rashinka ne yasani kuka don me zaka tafi ka barni kaida kace dakayiwa abokanka bangajiya zaka dawo karfe takwas dubi agogo yanzu karfe nawa? Am Sorry faisal yabata hakuri cikin harshen turanci sannan sai ya janyo amaryarsa ta kwanta a kirjinsa . Ango da amarya na kwance abinsu cikin kwanciyar hankali bugun zuciyoyinsu na bugawa lokaci guda da dakikar katon agogon dake magale a bangon dakin adaidai lokacin da agogon ya buga karfe goma sha biyun dare wayar Fadila dake gefen gadonta ya dauki ruri. Fadila ta farka a firgice kirjinta na harbawa gamida tsaki da kuma nadamar ma meyasa tun farko bata kashe wayar ba Fadila ta dauki wayarta ta kara a kunne. Hello wanene? Fadila ta tambaya Hello my darling mijinki ne faisal dan Allah kiyi hakuri yanzu zan dawo Wallahi gida naje na tarar mama batada lafiya shine muka kaita asibiti amma gani nan yanzu zanzo. Fadila taji kamar wata katuwar katanga ta fado mata a tsakiyar baya Fadila ta dubi mijinta dake kwance a kusa da ita sannan ta dubi kan wayar a tsorace. Kaga Malam nifa matar aure ce ga kuma Faisal dina kwance kusa dani. Aka kyalkyale da wata tattausar dariya acan daya bangaren Haba darling na dai fahimci haryanzu fushi kikeyi dani kiyi hakuri gani nan zuwa. Fadila taji kamar tasa ihu tabbas muryar faisal dinta takeji acan daya bangaren yawun bakinta ya kafe sa'ar dataga sunan Faisal din ne a saman wayar. Faisal dan Allah da gaske kaine? Fadila tace a tsorace tana kallon daya faisal din dake kwance a kusa da ita. . Kun hanani barci da shegen surutu wai ku masoya an fada miki shi kadai yake sonki idan ba barin dakin nan nayi ba bazaku barni nayi barci. Faisal din dake kwance akusa da ita ne ke wannan bayani cikin kakkausar murya yana gama fadin haka sai farin hayaki ya turnuke dakin. Wayar dake hannun Fadila ta Subuce. . BABI NA BIYU 2 . Adab da babban dakin karatu na sabuwar jami'ar bayaro agindin wata yar dukurkusar bishiya dake fuskantar tagwayen dakunan darasi daga gabas FARIDA ce zaune tana kallon ikon Allah zuciyarta kamar zata fashe ta fito ta tsakanin hakarkarinta. Daga inda take zaune tana iya hangen Kabir dinta zaune akan wani benci na farin dutse SAFIYYA zaune akusa dashi suna hira abinsu jifa jifa kuma saita bude baki kabir ya jefa mata alawa aciki duk sa'ar da hakan ta faru sai Farida taji kamar sun watsa mata wuta a fuska. Tun karfe hudu na yamma direbanta Baba Ali ke zaune a filin fakin yana jiranta amma har zuwa karfe shida na yamma farida na nan zaune domin ta gama rantseewa yau ko me za'ayi saita yiwa kabir magana. Farida na nan zaune kusan dakika ashirin saita dubi agogo sannan saita dago kai ta dubi kabir tabbas maganar Asma'u gaskiya ce da dai bata yarda ba amma ayau ta yarda domin duk da yake abinda Asma'u ke bata shawara tayiwa kabir nau'i ne na shaidanci to amma shine kawai mafita in har tana so ta kwato kabirunta Farida ta fadawa kanta sannan saita dada da cewa cikin zuciyarta ai shima kabir din shaidani ne domin idan bahaka ba yaushe ne za'ace wai sai nayi shaidanci zai damu dani. Farida na nan zaune tana kallon ikon Allah duk kusan daliban dake gurin sun tafi gida sai jifa jifan wadanda ke kwana a makaranta dake yar zirga zirga nan da can. Karfe shida da rabi daidai lokacin da farida ta fara tunanin ko anan zasu kwana sai taga su kabir sun mike tsaye safiyya na kokarin kama hannayensa biyu duk da yake farida bata iya jin abinda safiyya ke fadawa kabir amma ga yadda motsin bakin da yanayin fuskarta ya nuna tabbas kalamai masu dadi take fadawa kabir. Farida taji zuciyarta tayi kuna ana cikin hakane saitaga kabir ya tashi ya nufi hanyar da zata kaishi zuwa dakin kwanan dalibai yayinda ita kuma safiyya ta nufi hanyar da zata kaita filin da aka tanada dan ajiye motocin dalibai Suna tafiya suna waige suna waige suna dagawa juna hannu. . Cikin sauri tana tafiya gabanta na faduwa kafafunta na hardewa fadila tabi kabir abaya. Kabir farida takira sunansa cikin wata rarraunar murya adaidai lokacin dasuka kawo kusa da wata yar rumfa da dalibai ke hutawa kabir ya juyo cikin mamakin jin muryar mace tayi kiransa. Oh farida kece haryanzu baki tafi gida ba? Kabir yace sa'ar daya juyo. Ina nan ban tafi ba farida tace gamida danyin shiru domin ta lura kallonsa yatafi izuwa hannayenta. . Kai nake jira tun dazu ina can azaune farida tace lokaci guda ta nuna karkashin bishiyar data baro haba farida amma kuma kika ki yi min magana wallahi banganki ba. Farida ta sunkuyar dakai naga kuna hira mai dadi ne shine nace bari na jira dan kada na bata muku hirarku haba dai ai dama kinzo ba wata hirar kirki mukeyi ba maganar jarrabawa mukeyi. Farida ta dago kai a yatsine ta dubeshi tace Au jarrabawar bana hardasu sa alewa abakin budurwa? Lallai bana makin din jarrabawa sai a barwa su Shazumamu. Kabir ya fashe da dariya Kai lallai farida yau kin samin idanu farida ta waiga hadu da dama bata hangi kowa akusa dasu ba sai daga can bangaren shiga dakin kwanan dalibai take iya hango kawunan jama'a jifa jifa hakan ita ta kara mata karfin gwiwar matsowa kusa da kabir ta yadda har yana iyajin numfashinta fuskarta dab da tasa ta dubeshi ido da ido tace. Kabir me yasa kake guduna ko dan kaga na mutu akanka? Kabir ya dago kai ya dubi farida cikin mamaki da kaduwa amma da yake kwararren mayaudari ne bai bari kaduwa ta nuna a fuskarsa ba. Abinda ya bashi mamaki shine kama hannunsa da yaga farida tayi yasan cewa wannan ba al'adar farida bace ita dai ka barta da sauya samari kamar riga amma shashanci ba aikinta bane. Tsahon lokaci suna tsaye ahaka kabir yayi ajiyar zuciya kana idanunsa sukayi duba izuwa hannayenta akaro na biyu. Ba gudunki nakeyi ba farida. In ba guduna kakeyi ba me yasa ka daina kirana awaya kuma sai in nemeka in rasa amma dana ganka sai in ganka tare da safiyya farida tace sannan sai ta dafa hannunsa. Kabir yaji wani irin sanyi ya ratso daga hannun farida ya soki hannunsa kamar an rike shi da hannun kankara. Ke yaya naji hannunki sanyi karau haka? Sanya fa kace? Farida ta dube shi cikin mamaki kaga ni hannuna dumi ne dashi saidai ko in hannun safiyyarka ne keda sanyi kabir yayi murmushi yace kinga ga dan Allah mu bar wannan zancen ya wuce daga yau in Allah yaso kin zama tawa my only one. Kaidai fadi gaskiya safiyya fa? Kada ki damu da wannan shirmenta kawai take. Kabir yace azuciyarsa kuma yana cewa wannan ma rabo na minallahi ce wai tsuntsu daga sama gasashshe. . Kai amma fa zanen kunshin nan naki yayi bala'in kyau a ina akayi miki kabir ya fada a fili. Gaban farida ya fadi cikin sauri ta dubi hannayenta a iya saninta zanen dake hannunta ko baki baiyi ba amma sai gashi yanzu rangadadau yayi baki kamar yanzu aka zana shi. Wata...wata kawata ce tayimin farida tayi masa karya a tsorace kabir ya lura da sauyin yanayi na lokaci guda akan fuskarta dan haka cikin sauri sai ya saki hannunta azuciyarsa yana cewa bi ahankali dan samari wannan farin shigace ba irin su safiyya bace. Yanzu yaushe zamu sake haduwa mu tattauna sosai? Farida ta dubi zanen dake hannunta a tsorace tace. Duk lokacin da kake so mu hadu gobe a filin fakin idan mun tashi daga karatu saina kaiki gida. Tunda farida tazo jami'ar bayero bata taba bari wani saurayi ya kaita gida ba domin kullum

Chapter 2 of 7