Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ZAYYANA 1 and 2 Littafin Nazir Adam salih (c) Nazir Adam Salih Created and design by :- Shuraih Usman . Daga Nazir Adam Salih 1- Kibiyar Ajali 2- Me Yafi Kudi ? 3- Ta Leko Ta Koma 4- Birnin Sarauniya 5- Naira Da Kwabo 6- Aci Bulus 7- Mutuwar Kasko 8- Alakakai 9- Wa Na Kama ? 10- Hindu 11- Ruhina 12- Dare Da Rana 13- Karya Linzamin Shaidan 14- Cuta Ta Dau Cuta 15- Iska Mai Kada Ruwa 16- Bindigar Kwali 17- Damisar Takarda 18- Aziza 19- Tsohon Alkawari 20- Kai Da Jini 21- Aljani Ya Taka Wuta 22- Sai Mutuwa 23- Kudi Da Maciji 24- Kisan Boko 25- Kura Da Kan Rago 26- Murmushin Alkawari 27- Zayyana. . DON Halima Umar Tudun Maliki. . ZAYYANA Copyright (c) Nazir Adam Salih 2008 . Hakkin Mallaka (H) Nazir Adam Salih 2008 . TARIHIN DAB'INSA An Fara Bugashi A Kamfanin KAMNAS PUBLISHERS Dakata Kano A Shekarar 2008. . GARGADI Ba'a Yarda Wata Qungiya Ba Ko Wani Mutum Ya Juyi Wani Bangare Na Wannan Littafi Ba Ta Hanyar Wasan Kwaikwayon Majigi Ko Kuma Wani Abu Daban Saida Izinin Marubucin. . ADIRESHI Abubakar Sadik Islamiyya Dakata Kano Akwatin Waya 4792. . ZAYYANA Nazir Adam Salih (NAS) . FADILA Wata dankareriyar mota jeep baka kirin kirar kamfanin marsandi tayi fakin akusa da wani munafikin lungu dake wata unguwa acikin birnin Kano. Ga wanda ke tsaye awaje bazai iya ganin wanda ke cikin motar ba domin gilasan motar masu duhu ne sosai anyi musu dare jim kadan da tsayawar wannan mota sai kofar gidan gaba ta motar ta bude ahankali sannan aka zuro wata santaleliyar kafa kyakkyawa fara sol da ita kamar kafar balarabiya daga cikin motar sannu ahankali takalmi mai tsini wanda ke dauke da santaleliyar kafar ya sauka acikin cabin ruwan saman da ake ta makawa kamar da bakin kwarya tun da garin Allah ya waye. Duk da yake ana kiran Sallahr Azahar ruwan yadan tsagaita amma har izuwa yanzu karfe uku na rana yayyafar kananan kwayoyin ruwan basu daina sauka akan doron kasa ba. Kofar motar ta dada budewa sosai sannan sai wata kyakkyawar halitta doguwa tafito daga cikin motar Zuwat. Tana rausaya kamar macijiyar data fasa kai kyakkyawa ce ta gaske ga duk wanda yasan me ake cewa KYAU haka nan kamar yadda kafafunta suke haka nan ma sauran jikinta yake fari sol kamar balarabiya me yiwuwa kuma ga wanda baiyi yawon duniya ba ya iya kuskurenta amatsayin shuwa arab, to amma agaskiyar al'amari iyayenta fulani ne gaba da baya. Kyakkyawar halittar tayi tsaye bakin kofar motar tana duban ciki lokaci guda kuma ta gyara dan yalolon gyalen dake dafe akanta kana ta dada jan damammiyar rigar silikin dake jikinta kasa sannan daga karshe saita zato wata farar lema daga cikin motar ta budeta akanta domin ta kare yayyafar ruwan dake zuba haryanzu akan doron kasa kyakkyawar ta dada gyarawa lemar tsayuwa a saman kanta sannan saita dubi wasu kyawawan yan mata su hudu dake cikin motar suma farare sol dasu kamar ya'yan larabawa fuskarta a murtuke amma kyawunta ya karu. Ku zauna anan kuyi jirana kada ku sake naga wata shegiya acikinku ta biyoni saura kuma ku koma gida ku fadawa mama munzo nan sainaci uban yarinya. Tana gama fadin haka saita rufe kofar motar da karfi a fusace sannan ta nufi munafikin lungun cikin sauri. . Sunan wannan kyakkyawa FADILA kuma adaidai wannan lokaci data nufi wannan munafikin lungu cikin sauri sa'o'i ashirin da uku kacal suka rage adaura mata a aure da sahibinta FAISAL. Mutumin da take kauna fiyeda kowa aduk fadin duniya zakuma ta iya tsallake maganar kowa domin ta farantawa faisal hakanan Fadila na iya bata ran ko wane in dai zai taba mata Faisal watanni tara da suka gabata watarana da yamma suna hira akatuwar farfajiyar gidansu Fadila acikin motar faisal sai faisal din ya kalli hannun fadila yaga duk an zane shi da kunshin zamani wasu irin surori ne na furanni da siraran ciyayi kamar na bakin kogi masu kyawun gaske. bakin zanen yayi matukar fitowa akan fararen hannun Fadil. Kai amma yau kin kara kyau Fadilata Faisal yace yana kallon bakin zanen dake hannunta Fadila ta lumshe idanuwa cikin farin ciki wani irin sassanyan dadi ya mamayi zuciyarta jin cewa ta farantwa Faisal Allah ko? To nagode tace tana wani farfarar da idanu Faisal ya mika hannunsa zai taba hannunta cikin sauri ta dauke hannunta cikin dariya tace Menene? Da Allah kawo hannunki na gani a ina akayi miki wannan zanen kunshin mai kyau haka? Cikin murmushi fadila ta mika masa hannunta ya rike yana kallon zanen kunshin Wata mata ce take.... Yi mana Fadila tayi masa karya domin abinda faisal bai sani ba shine wani katon dan daudu ne wai shi AMARA yakeyi musu wannan zanen kunshin da ace Faisal yasan gaskiyar al'amarin da ace yasan cewa zanen ya kamane tun daga kan kafafunta da hannuunta har zuwa kan cinyoyinta sannan daga kan cibiyarta zuwa kirjinta da wuyanta da babu abinda zai hana zuciyarsa bugawa domin yana tsananin kishin fadila wannan ce ma tasa tun da yake zuwa hira gurinta bai taba zuwa da aboki ba sai sau daya shima daga nan bai kara ba domin ya fahimci tun da sukazo idanun abokin akan Fadila yake. To My Faisal tace gamida hadawa da turanci dan haka ayanzu da fadila ta nufi munafikin lungun gidan dan daudun ta nufa domin ya zane ta da furanni tun daga sama har kasa domin burinta shine ta ruda faisal adaren amarcinsu na farko ashe kuwa bata sani ba wannan kunshin ba karamin Rudashin zaiyi ba. . Sannu ahankali fadila ta kawo izuwa kofar wani gida wanda shi kadai ne acikin lungun tayi mamaki sa'ar dataji kamar gidan shiru bata jiyo hayaniyar mata ba. Tayi sa'a yau ba layi tace cikin zuciyarta abinda daman take tsoro kenan domin Allah Allah take yi tazo agama mata ta koma gida kada ta dade mahaifiyarta ta tambayeta inda taje. Tuni mahaifiyarta tayi tofin Allah tsine da wannan kunshin kada in sake ganin kinyi wannan sakarcin shashashar banza shashashar wofi in banda wauta irin ta ya'yan zamani yaushe zanje gaban wani kato in bude masa cinyoyina da kirjina wai yayi min zanen kunshi kada ki karayi babu kyau ko macece yar uwarki bai kamata taga tsaraicinki ba ballantana wani katon banza munafikin dan daudu idan kika sake yin wannan kunshin Fadila to wallahi bada yawuna ba Fadila ta tura baki gaba kamar tsuntsuwa tana gunguni tundaga. wannan rana bata karayin wannan kunshi ba sai awannan rana tafito yiwa Faisal dinta kunshin da yake so ta riga ta kuduri aniyar ko mahaifiyarta bata amince ba sai tayi wannan kunshin tunda faisal dinta yana so. . Fadila ta shiga farfajiyar gidan sannan kai tsaye ta wuce wani falo inda anan ne tasan mata ke taruwa su jira kafin azo kansu duk wacce akazo kanta saita bi dan daudun abaya su shiga wani dan daki inda anan ne zata tube ya zaneta tun daga sama har kasa. Salamu alaikum kwan kwan fadila ta kuma cewa shiru ba'a amsa ba me yiwuwa ya fita sayen sinadaran kunshin ne Fadila tace aranta domin tariga ta sani wata sa'ar ana cikin kunshin sinadarin ke karewa sai AMARA yafita ya sayo musamman lokaci irin na bikin sallah, dan haka sai fadila ta nemo kujera daya ta zauna sannan ta dauko daya daga cikin mujallun kasashen turai dake warwatse akan wani tebur dake tsakiyar dakin ta fara karantawa domin ta raka lokaci kafin Amara ya dawo . Adaidai wannan lokacin ne wata sassanyar iska mai sanyin gaske ta fara ratsowa cikin dakin nan da nan fadila taji jikinta ya dauki rawa domin sanyin iskar cikin bargonta yake shiga ko kusa ko alama iskar batayi kama da iskar damuna ba jikinta na rawa fadila ta dago kai daga kan Mujallar da take karantawa ta dubi kofar falon inda take tsammanin tanan iskar ke fitowa ga mamakinta sai taga duk da wannan sassanyar iskar mai karfi dake shigowa labulayen taga da kofar falon basa motsi kai hatta takardar mujallar dake hannunta bata motsi gashi kuma haryanzu iskar na kadawa. . MAMA Karfe uku da minti goma daidai wata tsohuwar tasi ta nufi munafikin lungun tana tafiya tana kara rukukuku kamar tsohon keken shanu tana tafiya tana bulbular da farin hayaki kamar jirgin kasa. Kai wannan wace irin mota ce anya kuwa ba kamawa tayi da wuta ba? Wata doguwar mata dake zaune abayan motar ce take fadawa direban ba'a bakinki nafara jin hakan ba 'Yan mata sau uku kenan yau ana cewa in tsaya in kashe wuta basu san ba motarce ahaka so nake idan kin sauka na wuce gurin gyara direban yace dan tsatstsama ne busashshe mai tarin gashin baki kamar ciyawar bakin kogi sanye da doguwar riga da hula amma samanta ya cizge kamar bera ya gwagwiya saboda yawan shekarunta a duniya. Ni wannan mota da nasan haka take da wallahi ban shiga ba ga tsada ga babu sauri ga kuma shegen hayaki. Direban ya shafi gashin bakinsa sannan ya juyo da kansa ya dubeta. In banda tsohuwar motace yaya zan dauko ki shata tun daga Na'ibawa har nan a naira tamanin kema dama ai san banza ne yasa kika tsayar dani. Kaga juya can ka isheni da surutu lura da gabanka Wallahi ga kwanan nan agabanka Matar tace dashi cikin Karaji. Direban ya juya da sauri adaidai lokacin ne to ya hangi katuwar Jeep din baka agabansa. Saukeni anan matar tace. Dan tsatstsaman direban ya daddage ya taka birki yana ciccije baki dakyar gamida kama sandar giya ya samu ya tsayar da motar adab da gindin Jeep din. Yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi matar da murmushi yace. Dana bugawa danyen kwannan dake gabana ai da zurawa zanyi aguje na barki acikin tsohuwar motar nan. Matar ta harare shi sannan ta zaro naira dari ta dungura masa a kasan hanci gashi nan ka rike sauran chanjin ashirin din ka cika ka sayi sabon inji. Kafin direban ya sami damar mayar da martani tuni har matar ta bude kofar ta fice abinta. Shegiya Kilaki direban yace yana kallon bayanta. Cikin sauri doguwar matar ta nufi cikin munafukin lungu tana tafiya tana girgiza bangarorin jikinta kamar wata bishiyar kanya lokacin iskar hunturun sanyi doguwar matar farace amma farin dan kanti ne baza a iya kiranta kyakkyawa ba amma tana da daukar hankali Allah ya hore mata kyan kirar jiki wanda ke tattare da wani mayen karfe mai karfin gaske wanda ke fizgo hankalin mazaje izuwa gareta musamman wadanda shaidan yafi karfin zuciyarsu. Wannan doguwar mata mai kyakkyawar jiki ma'abocin sinadaran mayen karfe sunanta MAMA akalla dai hakanan yan uwanta karuwai yan duniya suke kiranta a bariki to amma wani tsohon dan bariki wanda ya dade da saninta tun tana karama a mahaifarta GOMBE ya taba cewa da Babbar kawarta BEBI. Wai kinsan sunan kawarki kuwa na gaskiya Bebi ta girgiza kai menene sunanta na gaskiyar ZULAIHAT Uhm bebi tace dashi a yatsine wannan kai ta shafa tsohon munafiki meye na fada min sunanta na gaskiya kuda bakwa rabuwa da munafurci. . Ayanzu haka da mama tashigo layin tana rausaya sai ka kira sunanta Zulaiha akalla sau hudu kafin ta iya tunawa ma da sunan ne domin rabon da akirata da wannan suna tun tana garinsu Gombe yau kusan shekaru shida kenan da suka gabata. Zulaihat ko kuma Mama yar gidan wani tsohon direban jirgin kasa ce wanda Allah yayiwa rasuwa tun tana karama Mahaifiyarta talatu tsohuwar yar duniya ce tana yawonta suka hadu da mahaifin mama a tashar jirgin kasa dake garin GURU sa'ar daya tsaya sauke fasinjojin jirgin kasan basufi wata biyu da fara harkar bariki ba suka auri juna sa'ar da mahaifin mama yakai mahaifiyarta Gombe jama'a....... jama'a sunyi mamaki da akace dasu karuwa ce ya auro akayita surutu wasu sukace wai asiri tayi masa ya aureta wasu ko sukace a'a wai cikin shege sukayi dan haka suka auri juna abinda jama'a basu sani ba shine dalilin auren mahaifan ma dalilai ne masu sauki na farko dai mahaifin mama ya auri mahaifiyarta ne saboda kyawun jikinta kuma bazai iya ganin kowane namiji yana mu'amala da ita ba itako mahaifiyar mama ta auri mahaifinta ne saboda ta fahimci akaluum kwanan duniya baya rasa kudin kashewa ya sai musu tsire suci kasu su sha nono ya kuma dinka mata duk irin suturar da take so. . Mutuwar mahaifin mama keda wuya sai ungulu ta koma gidanta na tsamiya to saidai kuma awannan lokacin tsohuwar ungulun tsufa ya risketa batareda ta sani ba dan haka sa'ar da mahaifiyar mama ta dawo barikin ma babu riba domin babu mai kulata sai dattijan banza wadanda dayawansu matsiyata ne wadanda suka dorawa kansu masifa sa'ar da mama takai shekara goma sha tara sai tabi sahun mahaifiyarta domin abinda ta gani kenan tanayi nan da nan sai bakar kasuwa ta bude mata ba'afi shekara guda ba ta baro Gombe zuwa kano to saidai kuma tazo arashin sa'a domin tazo ne alokacin da aka kaddamar da shari'ar musulunci a kano karuwanci ya zama babu riba in ma za'a yi saidai a boye sannu ahankali shekaru hudu suka shude mama tana kano to saidai abubuwa sunja da baya matuka domin mama ta lura duk da kyawun jiki irin nata ta sami wadanda suka damata suka shanye hakanan saita fahimci kamar karuwan ma anfi son farare dan haka sai mama ta fara bilicin nan da nan ta kwaile ta koma fara jajuz duk da wannan ungulu da kan zabo da mama tayi hakanta bai cimma ruwa ba domin haryanzu a cikin kawayenta ita kadaice bata da motar hawa ana cikin wannan haline to kwatsam rannan da rana sai babbar kawarta dake abuja wai ita Bebi ta bugo mata waya. Hello kawata kina ina. Maza ki hada naki ya naki ki taho nan abuja muci karenmu babu babbaka babu wanda zai tsangwamemu da zancen shari'a kinga daga zuwana har wani dan majalisa yabani mota Ke ki bari don Allah. Mama tace cikin kaduwa. Wallahi kuwa kawata ai kema kina kan hanya kuma mota kamar kin samu domin jiya muna tare dasu wani honorabil abokinsa yaganki a hotunan da muka dauka aruwan tiga yace lallai saina kawo masa ke..... Saboda haka duk abinda kikeyi saiki bari ki taho abuja amma fa sai kin gyara jikinki da kyau kizo musu a hade. Wannan kalma ta karshe ita tasa mata shigowa munafukin lungun cikin sauri domin tazo Amara ya zaneta tun daga sama har kasa irin yadda zata ruda honorabil din da kawarta Bebi zata hadata dashi. Gobe har wahaka na rabu da wannan jaraba anbi an hanamu rawar gaban hantsi da wata shari'a sai inga uban da zai bimu abuja ya hanamu abinda muke so Mama tace aranta sa'ar data karaso farfajiyar gidan Amara dan daudu mai zanen kunshin zamani. . Sannunki mama tace da fadila ayatsine sa'ar data shigo falon mama taja kujera ta zauna sannan ta kalli kyakkyawar surar fadila nan da nan saita sami kanta tana mai fatan inama itace Fadila Da ko babu kunshi sai na sace zuciyar honorabil. Mama tace cikin zuciyarta. Yana ciki ne? Mama ta tambayi Fadila nima ban same shi ba inajin dai kasuwa yatafi sayen kayan hadi fadila tace bakinta na rawar sanyi. Baiwar Allah lafiya naga kina rawar sanyi? Naga kamar ai zafi akeyi ko? Mama ta girgiza kai aini da'ace da fanka ma kunnawa zanyi mama na rufe bakinta sai taji sanyin ya soki cikin kashinta. Kai Wallahi nima nafara ji wannan wanwe irin sanyi ne? . FARIDA. Da wani dattijo da wata budurwa yar makaranta suka shigo munafukin lungun cikin wata mota honda kirar Ali dari tara da casa'in da takwas dattijon shike jan motar budurwar na zaune abaya da yan littattafanta da takardu agefenta akan kujerar motar jakarta ajje akan cinyarta. Dattijon direban yayi fakin akusa da katuwar jeep din sannan ya dubi budurwar da tun tana yar kankanuwa yake tuka takata a mota direban gidansune. Ko ba nan bane lungun da kike fada? Nan ne budurwar tace da dattijon to saidai fa na jiraki anan kinga mota bazata iya shiga lungun ba kuma dan Allah kiyi sauri kinga ina mayar dake zan koma dauko yan uwanki. Budurwar ta bude kofar motar lokaci guda kuma tana kokarin bude jakarta. Dan Allah idan munje gida kada kace munzo nan kaji BABA ALI Dattijon ya dubeta cikin mamaki me zakiyi anan din? Kunshi ne za'ayi min ka gane to amma hajiya bata so na tafi ko ina indai yayi nesa da gida to ni kuma agaskiya irin wannan kunshin sai anan kawai za'a iyamin irin shi. Zaki dade kenan Baba ali yace yana dubanta cikin damuwa Gaskiya zan dade tun da idan da akwai layi ma dole saina jira. A'a kinsan bazata yiyu ba idan muka koma gida amakare banje dauko yan uwanki ba me kike tsammanin zan fadawa Hajiya? Budurwar ta dubeshi cikin damuwa haba baba ali kaifa nawa ne kasan ai bama haka dakai nasan bazaka rasa abinda zaka fadawa hajiya ba ta danyi shiru sannan saitaci gaba dacewa cikin sauri kokuma me zai hana kaje yanzu ka dauko su salima din ka mayar dasu gida nasan kafin kadawo ko ba'a gama min ba kadan zai rage. Kuma idan hajiya ta tambaye ni kina ina ince mata me? Budurwar ta dubi dattijon da murmushin wasa tace Haba Baba Ali basai kace da ita ina makaranta bamu tashi ba.... Uhm Uhm ko kuma dai kace da ita wani malami ne yasa mana Lecture darasin da bamu san dashi ba sai kace Sai biyar zamu tashi tana gama fadin haka saita zaro naira dari biyar daga cikin jakarta ko lankwasa babu ta mika masa. Ga wannan ka sayi goro....saika dawo din inajiranka. Eh to kema fa kinzo da dabara tabbas haka zan fada mata. Baba Ali yace a daidai lokacin da budurwar ta fice daga motar sannan ta nufi MUNAFIKIN LUNGUN cikin sauri. Koda dattijo baba ali ya tuka motar sai ya murza sabuwar naira dari biyar din da budurwar ta bashi sannan yace wai dole dai sai ya'yan zamani sun sa dattijo yayi karya to da sauki ma tunda da karyar banza zanyi ba. . Budurwar ta mike zuwa cikin layin tana tafiya tana yan waige waige a tsorace domin ta fahimci lungun babu mutane aciki me yiwuwa ruwan saman da aka wuni ana shekawa kamar da bakin kwarya ne duk ya kori mutane. . Wannan budurwa sunanta FARIDA ILYASU yar gidan wani tsohon kwamisha ce awannan lokacin daliba ce a jami'ar Bayero ta kano kuma tana shekarar karatunta ta karshe ne a bangaren tsimi da tanadi. Farida gajeriya ce amma kyakkyawa ta gaske ma'abociyar iya kwalliya dasa sutura tayi daidai ajikinta kamar dama da ita aka halicceta bayan karatun tsimi da tanadi da takeyi ahalin yanzu babu wani abu da farida ta kwarance akai irin tsabar ruwan ido. Kullum acikin sauya samari take bata zama da saurayi daya yau in ka ganta da wancan gobe saika ganta da wannan. Saurayi agurin farida ba wani aiki bane kamar yadda sauya rigar dake jikinta bai zama aiki ba. Duk da yake dai bata samari biyu ko lokaci guda amma duk wanda ta hadu dashi an fara soyayya rimi rimi ba'a fin sati biyu ko uku sai su rabu duk saurayin kuwa dayayi wata guda tare Farida ba karamin mai hakuri bane. Watarana farida tana kwance sai irin yadda take sauya samari kamar riga ya fado mata dan haka sai ta fara lissafin adadin samarin datayi soyayya dasu daga lokacin data shiga jami'a kawai ba karamin kaduwa tayi ba sa'ar dataga sun doshi hamshin da wani abu. Watarana da safe ana dab da za'a fara jarrabawa farida na zaune akan faffadar matattakar dakin karatu na sabuwar jami'ar Bayaro cikin damuwa domin ta shiga dakin karatun ta tarar ya cika da dalibai babu gurin zama dan kowane dalibi fama yake da karatun jarrabawa gashi kuma ita in ba'a dakin karatun ba bata iya karatu a ko ina ba. Tana nan zaune sai taji agefenta na dama ance Sannunki. Juyawarta keda wuya sai sukayi ido biyu da wani saurayi dan kwalisa mai matsaikacin tsaye sanye da damammiyar riga fara ta kama jikinsa kamar fata da kuma wando na jeans baki. Yauwwa sannunka dai Farida tace a yatsine sannan ta dauke kai gefe guda. Saurayin ya zauna akusa da ita yace a tausashe kema baki samu guri bane? Uhm wallahi ni na rasa ma inda zani farida tace tana dubansa akwai wani abu a tattare dashi dake sawa idan ta kalleshi bata iya hakuri saita sake juyowa. Muje zuwa na baki guri saurayin yace da ita yana satar kallon siririyar girar idonta. Kai ka tashi daga karatun ne? Farida ta tambaye shi cikin mamaki saurayin ya girgiza kai. Yanzun nan nafara amma tunda ke baki samu ba saina hakura na baki gurina domin da ganinki nasan bazaki iya karatu ako ina ba sai a dakin karatu kinga ni kuwa ako ina agindin bishiyar can ma sai inyi zamana nayi karatuna ban damu ba. Ya kake magana kamar wani malamin duba? Farida tace cikin murmushi domin tafara jin dadin hira dashi. Kamar kin sani idan kina so ma yanzun nan sai in fada miki abinda kike ci kafin kifito daga gida. Ah rufa min asiri bawan Allah saikace wani tsohon maye. Suka fashe da dariya sannan ta bishi a baya suka shige dakin karatun. Aranar da dare farida ta sallami saurayinta na hamsin da uku 53 acikin shekara uku sannan ta maye gurbinsa da sabon saurayinta KABIR. To saidai kuma tun daga ranar dayazo gidansu na farko farida bata kara ganinsa ba. Ga mamakinta saitaji ta kasa samun sukunin zuciya kullum a neman kabir take gashi bai ma fada mata abinda yake karantawa ba ballanata taje tsangayarsu nemansa haka nan ko lambar wayarsa bata karba ba. Rannan da safe sai sukayi Kicibis dashi a kofar dakin karatu ''Ka Kyauta kabir wato har guduna ma kakeyi ko? Farida tace muryarta a raunane. Ba haka bane farida kin gane wato abubuwa ne sukayi yawa....kuma ina dan tsoro. . Tsoron me? Tsoron ki farida bazan boye miki ba ance bakya iya zama da saurayi duk yadda kuke dashi sai kin jefar dashi kinga kuwa ai bazai yiwu in kai kaina makasa ba ko? Farida ta matso dab dashi cikin takaici sannan tace daga kanka na gama saurayi kabir nayima alkawari baka ganin wadancan samarin su suke sona kai kuwa ni nake..... Tayi shiru bata karasa ba cikin kunya. Tun daga wannan rana alkadarin farida ya karye akaro na farko a tarihin farida ta shafe.ta shafe sama da wata shida da saurayi daya kuma abin bakin ciki da takaici shine haryanzu nan kabir bai damu da farida ba sosai ba watarana saitayi sati biyu bata ganshi ba amma duk da haka ko gaisawa da wani saurayin batayi dan kada kabir ya ganta ransa ya baci rannan sai farida takai kukanta gurin wata kawarta adakin kwanan dalibai. . Kwata kwata bai damu dani ba ASMA'U na rasa yadda zanyi in shawo kansa kinga rannan ma tare da SAFIYYA na ganshi cikin mota suna ta hira Asma'u ta dubi kawarta tace wacce irin hira kukeyi dashi? Ban fahimce ki ba farida tace cikin mamaki kina nufin hira...wacce hira zamuyi data wuce irin wacce kowa keyi hirar fatar baki. To anan kuskurenki yake yanzu ke ko dan irin kissing sumbatarsa din nan ma bakyayi? Farida ta girgiza kai haba Asma'u yaya zan bar mutumin da ba mijina ba ya taba jikina. Aikuwa sunanki sorry dan wallahi safiyya kwace miki shi zatayi kinaji kina gani haka fa Rukayya sani taso ta kwace min usman dina saida na dage da kyar da yan dabaru na kwatoshi kinga ma wannan saboda shi nayi Asma'u tace lokaci guda kuma ta yaye cinyarta a gaban farida babu kunya babu tsoro sannan ta da daga mata rigarta ta fito da kirjinta a fili. Farida ta dubi kyakkyawan zanen kunshin zamanin dake kan cinyoyin Asma'u da kirjinta baki na rawa tace. Gaskiya ni kunya nakeji yaushe zan bari har kabir yakawo nan. . Asma'u ta fashe da dariya ai kuwa kinaji kina gani za'a rabaki da dan Darling dinki ni kinga nawa Usman din da zarar munyi Graduation zamuyi aure. Kaini dai bazan iyaba Wallahi da haka farida tabar kawarta Asma'u. . Fitowarta keda wuya kamar cewa fito muna jiranki sai farida ta hangi kabir dinta zaune agindin wata bishiya dake gefen dakunan kwanan dalibai shida safiyya ta dora santala santalan hannayenta akan kafadarsa suna hira da shewa cikin farin ciki. Farida taji kamar an watsawa zuciyarta garwashin wuta ba zata yiyu ba tace cikin zuciyarta sannan sai SHAIDAN yaci karfin tunaninta hannunta na rawa ta dauko wayarta daga cikin jakata ta bugawa Asma'u Hello Kawata yaya akayi ne ko mantuwa kikayi? Asma'u ta tambaya acan daya bangaren. Na

Chapter 1 of 7