Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
sarkin karfi,saiya hakura bisa dole ya juya da baya ya cigaba da yaki.Yana yakin yana dada lura da yanayin yadda yakin yake kasancewa.Abinda ya daure masa kai shine duk da cewa mayakansu sun ninka na sarki Garzub sau uku amma gashi har a sannan sun kasa karar dasu.Kuma komai zuba idon mutum bai isa ya iya gane bangaren dake samun nasara ba domin duk bangaren da ka duba sai kaga jama'arsu nata zuba a kas tamkar sharesu akeyi da tsintsiya.Gaba daya filin yakin ya cika da gawarwaki fululu babu kyan gani.Kofaton dawakai da kafafun mutane sai taka jini suke yana dada fantsamuwa.Filin yakin ya yamutse ga ihun mazaje,ga karafkiyar karafa kuma ga kura da jini sun gallabi al'umma.Wani lokacin saidai kaga kasa ta hadu da jini ta hade tamkar kwabar gini za'ayi da ita.Lokacin da Yarima Uzaima ya sami nasarar kai sarki Garzub cikin tantinsa sai na da nan likitocinsa suka taru a kansa suka shiga aikinsu.An shafe lokaci mai dan tsawo sannan ya farfado.Koda ya bude idanunsa ya dubi inda yake sai ya yunkura da nufin ya mike tsaye ya fita daga cikin tantin yaje ya cigaba da yaki.Cikin hanzari da matukar damuwa Uzaima ya rike kafadunsa ya dubeshi yace ya kai Abbana kayi sani cewa idan ka fita yaki a haka za'a iya hallaka ka cikin kankanin lokaci domin a halin yanzu babu kuzari a jikinka domin ka zubar da jini mai yawa.Lallai kana bukatar isasshen hutu.Cikin fushi sarki Garzub ya dubi Uzaima yace saboda me ka ceci rayuwata?Me yasa baka bari sarki Madarus ya hallakani ba in yaso ka tareshi ku cigaba da yakin ko ka kashe shi ko ya kasheka?Ka sani cewa yanzu haka yana can yana dada ragargazar mutanenmu.Shin ka mantane cewa idan suka gama damu anan can birninmu zasu karasa suje su kama kowa da kowa a matsayin bayi su kwashe arzikinmu kuma su kone birninmu yadda har abada za'a manta da tarihinmu.Mu ne kadai masu iya taka musu birki bisa wannan mugun nufi nasu.Idan muna nan su suna can filin yaki nan da kankanin lokaci zasu karar da dakarunmu,mene amfanin rayuwarmu da numfashinmu a yanzu?Uzaima yace yakai Abbana aini yanzu zan koma filin daga kuma na tabbatar yanzu haka sarki Rakalu da sarkin Yaki Zamud suna can sun yiwa abokan gaba mummunar barna.Haka kuma sauran sadaukanmu,wannan karon suna yaki ne da DAKAKKIYAR ZUCIYA domin nayi matukar mamaki bisa ganin irin namijin kokaron da sukeyi a filin yaki.Sarki Garzub yayi ajiyar zuciya yace duk na gani da idona amma inason ka sani cewa ganin irin jarumtakar da mukeyi ne tasa suma sadaukan namu suka taso.Baka tunanin cewa rashinmu a filin yaki zai iya janyo musu karayar zuciya?Shin yanzu menene tabbacinka cewar sarki Rakalu da sarkin yaki Zamud har yanzu suna nan a raye?Bazan yi hutun jaki da kaya ba maza ka tashi mu koma filin daga tunda dai harka sami nasarar kawoni nan kuma anyi mini magani kayi babbar jarumtaka.Ka sani cewa karo da sarki Madarus ba karamin bala'i bane.Koda mu biyu zamu taru a kansa bana zaton zamu iya hallakashi.Koda gama fadin haka sai Sarki Garzub ya diro kasa daga kan gadon karfen da aka kwantar dashi ya gyara damararsa ya nufi kofar fita daga cikin tantin.Cikin hanzari babban likitansa yasha gabansa yace ya shugabana idan ka fita yaki a haka ba zaka iya koda rabin sa'a ba zaka yanke jiki ka fadi.Cikin harara da tsawa sarki yace da likitan kauce ka bani hanya kona sareka da takobina.Kawai sai ya juyo ya dubi Uzaima yace koda mutum daya jal zan sami nasarar kashewa a wannan fita da zanyi nima a kasheni na samu babbar nasara domin na mutu namiji ba rago ba.Gama fadin hakan keda wuya sai sarki Garzub ya fita da sauri daga cikin tantin Uzaima ya bishi.Lokaci guda aka kawo musu dawakai suka hau suka zaburesu da gudu izuwa cikin sansanin yaki.A tsiyace sarki Garzub da Yarima Uzaima suka afkawa abokan gaba aka cigaba da bakin gumurzu ya zamana cewa sun haukace kuma basa ji basa gani face saran mutane saidai kaga sassan jikin bil'adama na shawagi a sama yana zubowa kasa.Sarki Madarus ma yana can bangare guda yana ta ragargazar maza,kawai sai ya hango gawar sarkin yakinsa Sharkas data abokin gwaminsa Zamud a waje daya.Koda ganin wannan gawa sai ya fusata ainun shima ya haukace akan saran abokan gaba ya zamana cewa a lokaci guda idan ya kai sara damansa sai kaga sama da mutum arba'in sun zube kasa matattu.Haka ma hagunsa,gabansa da bayansa.Nanfa ya cigaba da mummunar barna domin duk inda ya durfafa saidai kaga yana tarwatsa cinkoson dakarun dake wajen suna bajewa a kas tamkar manoma sunyiwa gona rubdugu suna yi mata sassabe.Yana cikin wannan mummunar barnar ne ya dubi bangaren da Sadauki Kularu yake ya ga shima yana ragargazar maza saiya cika da farin ciki kuma ya rinka hange hange da waige domin har a sannan baiga duriyar su sarki Garzub ba.Kwatsam!Sai ya hangosu a can nesa dashi suna ta ragargazar dakarunsa kamar yadda shima yake ragargazar nasu.Nan take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone ya sake zaburar dokinsa izuwa inda Kularu yake.Tun daga nesa Kularu ya hango sarki Madarus yana mai yi masa nuni da hannu cewar su kai dauki izuwa can inda su sarki Garzub keyi musu barna.Nan take kuwa Kulara ya fahimci inkiyar Madarus ya tarwatsa dakarun dake gabansa ya sukwani dokinsa izuwa inda sarki Garzub da Uzaima suke yaki.Tuni sarki Madarus ya rigashi nufar wajen don haka Uzaima na hango sarki Madarus ya nufosu saiya yunkura don ya tareshi.Cikin hanzari sarki Garzub ya rukeshi yace ai ba abokin gwaminka bane ka kyaleni dashi,ga sa'anka can a bayana yana tahowa shi zaka tara nika kyaleni da wannan babban shaidanin.Cikin alamun tsoro da matukar damuwa Uzaima ya dubi sarki Garzub yace yakai Abbana shin ka mantane cewa ka jarraba tarar wannan mutum amma baka sani nasara ba?Sarki Garzub yace ka kyale ni dashi.Take sarki Garzub Ya tunkari sarki Madarus Suka runguntsume da azababben yaki.Shi kuwa Yarima Uzaima saiya tunkari Sadauki Kularu.Lokacin da sarki Madarus da sarki Garzub suka fara wannan gumurzu a karo na biyu sai labari yasha bamban domin wannan lokacin kowannensu yana yakine a fusace da dukkan karfinsa kuma da dacin zuciya.Al'amarin daya janyo karfinsu da zafin namansu ya kusan zuwa daya.Suka wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin bajinta.Saida suka jima a haka babu nasara ga kowannensu har ya zamana cewa takubbansu nata zubar da tartsatsin wuta da hayaki saboda yawan haduwa.Dukkaninsu sunyi kokarin amfani da karfin sihirin tsafi wajen ganin sun hallaka juna amma sai sihirin yaki yayi tasiri saboda kowannensu sihirin nasa mai karfi ne.Da kansu suka soke takubban nasu a cikin kufe suka tsaya suna kallon juna suna haki kamar zakaru ko sauraron abokan gaba basayi saidai duk wanda yasha gabansu sai kaga sunyi masa naushi daya ya kife kasa matacce.Dakaru nata saransu da takubba suna sukarsu amma kamar duwatsu ake sara domin makaman basa tasiri a jikinsu saboda karfin sihiri.Nanfa Madarus da Garzub suka cigaba da kusantar kuna har ya zamana cewa tsakaninsu bai wuce taku biyar ba sai gashi sarki Madarus ya zama shirgege a gaban Garzub tamkar giwa a gaban kura.Sarki Madarus ya dubi Garzub cikin tsananin fishi yace yanzu kuma karfin damtsenka ne zai ceci rayuwarka daga sharrina baby batun iya yaki ko sihiri.Tabbas yanzu zanyi maka KISAN GILLAH irin wanda ba'a taba yiwa wani ba domin yanzu a fusace nake bisa ganin gawar sarkin yakina wanda sukayi RAGAS da na sarkin yakin.Koda jin wannan batu sai idanun sarki Garzub suka ciko da kwalla yace nayi matukar bakin ciki da ya zamana cewa sarkin yakinka shine ajalin sarkin yakina domin kusan ya dauki fansa ne a kansa bisa maisheshi musaki da nayi,so nayi ace nine na raba sarkin yakinka da ruhinsa.To amma duk da haka sarkin yakina ya mutu cikakken namiji ina alfahari da haka.Ina tabbatar maka da cewa koda zaka sami nasarar hallakini nima saina bar maka babbar shaida a jikinka wacce harka bar duniya da bakin cikinta a zuciyarka.Inason ka sani cewa bani da wata nadama idan na mutu a wannan yaki domin tun kafin na fito yakin nayi bincike a hallarar tsafina naga cewa bani da nasarar a wannan yaki amma kuma kuma koda kun sami nasara sai kun koma kasarku da bakin cikinmu da tashin kwanciyar hankali.Kafin Garzub ya gama rufe bakinsa tuni Madarus ya daka masa tsawa yace karyarka tasha karya yakai wanna sarki.Tabbas sai mun biya dukkan bukatarmu dake kanku.Lallai sai mun sami nasarar yaki daku kuma sai munje har can birninka Hirtoliya mun kama matayenku,yayayenku da tsofaffinku kuma mun kwaso dukkan dukiyarku.Koda gama fadin haka sai sarki Madarus ya shammaci Garzub ya shaki wuyansa da hannu daya kuma ya dagashi sama sai ga kafafun Garzub suna wutsil wutsil yana reto a sama a lokacin da idanunsa suka kumbura kuma suka kada sukayi jawur ya fara kokarin mutuwa.Garzub yayi ta kokarin ya cire hannun Madarus daga wuyansa amma ya kasa.Nanfa Madarus ya fara kyalkyal dariyar mugunta domin ya tabbatar da cewa nan da yan dakiku kadan Garzub zai sheka Barzahu a hannunsa.A wannan lokaci ne sauran dakarun Sarki Garzub da suka ga halin da sarkinsu yake shiga sai suka yanyame Madarus masu saransa nayi masu sukarsa nayi.Kai harda ma masu cizonsa amma duk a banza domin babu wanda ya sami nasarar koda yakusar fatar jikinsa.Kawai sai ya rinka makesu da daya hannunsa suna zubewa kasa matattu.Duk wanda ya cafka da hannunsa kuwa idan yai jifa dashi sai kaga kamar da takarda yai jifa,domin sai mutum ya luluka sama sannan kaga ya fado kasa cikin cinkoson jama'a ana takeshi.Kwatsam!Ba zato ba tsammani sai sarki Garzub ya naushi Madarus a al'aurarsa da kafa.Ba shiri Madarus ya saki An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7