Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
fara kallon kallo tsakanin yarima Uzaima da Sadauki Kularu ya zamana cewa kowannensu yaji a jikinsa cewa ya gamu da gamonsa domin alamar karfi tana ga mai kiba.Sarki Garzub ya bushe da dariya sannan ya hade fuska yace ni nafi karfin na sakeyin fada dakai saidai nayi da ubangidanka sarki Madarus tunda mun gwabza a baya mun gama fitar da raini.Koda jin wannan batu sai sarki Madarus yayi murmushin mugunta sannan yace ai haka za'ayi.Yanzu ni,Sharkas da Sadauki Kularu zamu fara bude fagen yaki daku ku ukun.Bayan mun sami nasara akanku ko kuma kun samu sai acigaba da yaki.Sarki Garzub yace mun amince da hakan.Nan take Sarki Madarus ya sauko daga kan dokinsa ya cire alkyabbar dake jikinsa saiga damatsansa sun firfito fili.Koda yarima Uzaima yaga irin siffar jikin sarki Madarus yaga kuma da mahaifinsa zai gwabza yaki saiya firgita ainun ya matsa daf da sarki Garzub yace yakai Abbana ka kyaleni na tari sarki Madarus kai ka tari Sharkas,sarkin Yaki Zamud ya tari Kularu.Dajin haka sai sarki Garzub yayi murmushi sannan yace ai nafi shakkar Kularu kan sarki Madarus domin shi sarki Madarus ya fara manyanta kamar yadda nima na manyanta.Ko shakka banayi akwai iyakar lokacin da zai gaji.Zahiri nasan cewa sarki Madarus yafi ni sadaukantaka kuma yafi Kularu to amma zaifi kyau yaro ya tari yaro tsoho ya tari tsoho.Gama fadin hakan keda wuya sai shima Sarki Madarus ya sauko daga kan dokinsa yana mai zare takobinsa ya matsa daf da Garzub aka fara kallon kallo.Shima Zamud ya sauko daga kan nasa dokin saboda kasancewarsa musaki mai Hannu daya da kafa daya.Sarkin yaki Zamud ya zare takobinsa ya tari Sharkas.Koda yazo daf dashi sai Sharkas ya dubeshi yayi murmushin mugunta yace sarkinku ya tsorata da dana ya kasa tararsa yaje ya tari sarkinmu bai san cewa ajalinsa ya kirawo kusa ba domin masifar sarki Madaru ta ninka ta Kularu sau dari.Ina mai tabbatar maka dacewa a cikin dakika dari da tamanin zan maida kai abincin ungulu.Koda jin haka sai Zamud ya dakawa Sharkas tsawa yace kai wawa karyarka tasha karya domin ka hadu da daidai da kai.Tabbas zan baka mamaki zan nuna maka tsantsar kwarewata da sanin makama irin wacce kake takama da ita.A bangaren Yarima Uzaima da sadauki Kularu kuwa har suka zo daf da juna dayansu bai zare makaminsa ba.Sai kawai suka cigaba da kallon juna kowannensu zuciyarsa cike da sake sake da tunani kai da gani kasan cewa KAR TA SAN KAR ce.Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda tsawo,kaurin jiki da murdewarsu yazo daidai tamkar Hassan da Husaini tsakanin Yarima Uzaima da Sadauki Kularu.Hatta kwarjininsu iri dayane inda suka bambanta kawai shine a kamannin fuska.Shima Sadauki Kularu saurayi ne kyakyawa abin misali amma bai kai Yarima Uzaima ba kuma shekarunsa daidai dana Uzaima suke domin rana daya aka haifesu.Tun Kularu yana yaro karami dan shekara takwas yake tsananin son gimbiya Zarilaf har suka girma tare amma daidai da rana daya bai taba samun ganin murmushinta ba bare ya sami nasarar da zai iya furta mata abinda ke ransa.Saida takai cewa kowa a kasar yasan cewa Sadauki Kularu yana matukar son Gimbiya Zarilaf amma ita ko kadan bata sonsa.Kai ko sunansa bata son taji an ambata.comments TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Biyu (2) Part D . REAL RAYYANU SAEEd . Kai ko sunansa ma bata son taji an ambata.Babu irin abinda Kularu baiyi ba domin Zarilat ta so shi amma abu ya gagara har saida ta kaishi ga kai ziyara ga bokaye a kasashen nahiyar su amma duk wajen bokan da yaje sai yace dashi babu abinda zai iyayi masa yasa Zarilat ta soshi.Da kyar ya sadu da wani takadirin boka wanda ya gaya masa cewa idan har yana son ya sami karbuwa a wajen gimbiya Zarilat dole ne yayi gagarumar bajinta a yakin da za'aje ayi a can nahiyar bakaken fata ya zamana cewa tafi kowa jarumtaka.Lallai idan yayi haka Zarilat zata soshi ainun harma ta aureshi.Bisa ga wannan dalili ne Sadauki Kularu ya ZAGE DAMTSE wajen baiwa kansa horon yaki dare da rana har tsawon shekaru bakwai ya zamana cewa yaji a jikinsa cewa zai iya tarar kowanne sadauki a duniya komai kwarjininsa da KARFIN DAMTSENSA.A bangaren tsafi kuwa sadauki Kularu ya tafi yayi nisa domin masu bincike sun gano cewa a gaba dayan nahiyarsu sarki Madarus ne kawai akan gabansa.A halin yanzu sadauki Kularu bashi da fargabar komai a zuciyarsa duk daya karewa Uzaima kallo ya fuskanci cewa sadauki ne shi na gaske wanda za'a fafata amma aby daya ne ya karya masa zuciya.Ba kuma wani abu bane face ya lura da lokacin da gimbiya Zarilat tayi arba da Uzaima tayi masa wani irin kallo mai dauke da ALAMAR TAMBAYA kuma ta kura masa idanu ko kiftawa batayi.Abinda Kularu ya tambayi kansa shine shin kwarjini Uzaima ne yasa Zarilat ta kura masa idanu ko kuwa kyawunsa ne ya ribaceta har ya burgeta?Nanfa Kularu ya kasa baiwa kansa amsar wannan tambaya.Abinda ya kudurce a ransa shine duk wuya duk rintsi saiya siye zuciyar gimbiya Zarilat a wannan yaki da za'ayi don haka yanzu zai fara wannan yaki ne da mugun nufi wato yana son duk wanda ya fara haduwa dashi yayi masa kisan gilla farat daya.Bayan jaruman shida sun tsaya daf da juna anyi kallon kallo na tsawon dan lokaci sai aka buga gangar yaki.Nan take aka ruguntsume da azababben yaki a tsakanin jaruman shida.Sadauki Sharkas ne kadai akan doki.Babu fadan da ya zama mafi ban tsoro face fadan manyan zakuna biyu,wato fadan sarki Madarus da sarki Garzub domin bambancin a baiyane yake wato karfin sarki Madarus da zafin namansa ya ninka na sarki Garzub sau uku.Tunda suka fara gumurzun ko sau daya sarki Garzub bai maida martani ba in ba don ma yana da matukar juriya da naci ba da tuni sarki Madarus yayi masa kisan farat daya.Babu abinda ya tsorata sarki Garzub sama da azababbiyar takobin dake hannun sarki Madarus wacce ta kasance sihirtacciya domin duk sa'adda sarki Madarus ya kawo masa sara da ita ya goce tofa ko kasa ya samu sai kaga ta dare kuma ko dutse ya samu sai ya rabashi gida biyu kuma ko dakushewa takobin batayi.Al'amarin daya dugunzuma hankalin sarki Garzub kenan domin yasan cewa idan aka sami koda tsawon rabin sa'a ne a haka sarki Madarus zai iya galabaitar dashi ya gaji da zarar ya gaji kuwa take zaiyi masa kisan farat daya.A bangaren Sarki Madarus kuwa shima yayi tsananin mamaki bisa ganin yadda ya kasa kashe sarki Garzub nan da nan domin a tarihin sadaukantakarsa da yake yaken da yayi bai taba haduwa da wani jarumi ba wanda ya kasa kasheshi a tsawon dakika sittin ba sai yau.Nanfa zuciyarsa ta kama tafarfasa ya kara zage damtse wajen kaiwa Garzub sara da suka cikin tsananin zafin nama.Shi kuwa Sarki Garzun zage damtse yayi waken kare kansa.A bangaren su Sharkas kuwa da sarkin Yaki Zamud yaki yayi tsamari a tsakaninsu.Shidai sadauki Sharkas dama yana kan doki.Sadauki Sharkas ya zaburo dokinsa da gudu yayi kan Zamud da niyar da danneshi.Wohoho!Hakika karfi yana da ranarsa domin in badon Zamud ya kasan kakkarfan gaske ba da tuni dokin ya danneshi.Idan mutu yaga yadda kwanjin Zamud ya kumbura dole ne yasan cewa ya cika Sadauki.Ba zato ba tsammani sai akaga Zamud yayi jifa da dokin Sharkas,take Sharkas ya wantsulo kasa suka baje a kasan tare da dokin nasa.Cikin zafin nama Sharkas ya dogara sandarsa ya mike tsaye da kafarsa daya ya sake daga takobin tasa ya fuskanci Zamud.Koda Zamud yaga zaiyi yaki da mai kafa daya da hannu daya saiya bushe da dariya uace ai dama dokin kane ya ceceka a dazu don haka yanzu karyarka tasha karya mutuwarka tazo.Sharkas ya dubi Zamud cikin murmushi da raini sannan yace ai fada ba cikawa bane lallai sai an gwada akan san na kwarai.Ina sauraron ka nuna mini iyakar jarumtakarka da kwarewarka na gani.Ka sani cewa sarkinka ma baiji da dadi ba a wancan karon da muka gwabza tsananin sa'a ce tasa ya sami nasara a kaina kawai.Gama fadin hakan keda wuya sai Zamud ya daga takobinsa sama ya kwarara uban ihu ya ruga izuwa kan Sharkas.Sharkas ya tsaya cak a inda yake ko motsawa baiyi ba suka kacame da sabon azababben yaki.A bangaren sarki Garzub kuwa da sarki Madarus al'amura sun sauya salo domin tuni sa'a daya ta shafe da fara gumurzunsu,a sannan nefa ido ya raina fata a wajen sarki Garzub domin ya fara gajiya har takai cewa da kyar yake iya tare mugayen hare haren sarki Madarus.Suna cikin haka ne sarki Madarus ya shammaceshi ya dankara masa sara a saman cibiyarsa.Duk da Garzub yayi kokarin kare saran saida takobin Madarus ta yankeshi wajen ya dare jini yai tsartuwa.Sarki Garzub bai san sa'adda ya kurma ihu ba yai tsalle ya fadi kasa.Madarus ya kawo masa wawar suka a ciki da tsinin takobinsa ya goce takobin ta nutse a cikin kasa gaba dayanta.Kafin ya zaro takobin ne Garzub ya dage iya karfinsa ya kirba masa naushi a fuska.Saboda karfin naushin saida Madarus yayi taga taga da baya kamar zai fadi.Take idonsa guda ya lunkume fuskar ta kumbura.Wannan shine karon farko da sarki Garzub ya sami nasarar taba jikin Madarus tunda suka fara yaki.Shi kuwa Madarus dama tuni ya hadawa Garzub jini da majina saboda yawan naushi.Cikin tsananin fusata sarki Madarus ya sake zaro wadansu gajerun adduna guda biyu dake jikin cinyoyinsa a daure ya ruga inda Garzub ke kwance da nufin ya daddatsashi tunda ya kaishi kasa.Yayin daya rage saura taku uku kacal ya iso kansa sai kawai yaga Garzub ya yunkura cikin bakin zafin nama ya mike tsaye zumbur tamkar sifirin sannan ya yagi suturar jikinsa yayi gammo da ita a zagayen cikinsa wato ya daure raunin da ita don tsaida jini ya tari Madarus suka cigaba da bakin artabu.Wannan karon dai sai gashi kowannensu yana iya kare hari da maida martani.A bangaren zaratan matasa biyu kuwa wato yarima Uzaima da Sadauki Kularu abin ya zama ba kyan gani.Hatta sauran dakaru na kowannen bangare dake tsaitsaye suna kallon abinda ke faruwa kowa hankalinsa ya dugunzuma ainun domin kare jini biri jini suke saboda karfi yazo daya.Da farko saida suma suka shafe sa'a guda cur suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta,ya zamana cewa dayansu bai sami nasarar koda lakutar jinin abokin gwaminsa ba.Da kansu suka ja da baya sukayi cirko cirko suna kallon juna suna haki.Daga can sai suka rugo da gudu suka sake kacamewa da yaki amma a cikin sabon salo na tsalle tsalle da kwance kwance.Abinda ya baiwa kowannensu mamaki shine salo iri daya sukeyi.A wannan karon ne Kularu ya sami nasarar yankar Uzaima a gadon baya wani irin dogon yanka.Uzaima ya kurma ihu saboda mugun zafi da zogin da yaji amma saboda juriya da naci irin na Uzaima bai fadi kasa ba sai ya daka wawan tsalle sama bayan ya dafa kasar da tafin hannunsa tamkar an cillashi daga cikin baka.Kularu bai ankara ba sai ganin Uzaima yayi a sama ya shallakeshi.Kularu ya juya da sauri domin ya kawo masa wani harin amma sai yaji tuni Uzaima ya dankara masa dogon sara a kirji.Kularu ya kwalla ihu sakamakon jini da yai tsartuwa a kirjin nasa yayi baya taga taga kamar zai fadi amma saiya tsaya cak.Kawai sai ya rike takobinsa da hannayensa biyu a lokacin da jiri ke dibarsu su biyu.Koda suka fahimci halin da suke ciki sai kowannensu ya tsaya ya daure raunin jikinsa don tsaida jini sannan suka sake ruguntsumewa da masifaffen yaki.Saida suka sake shafe rabin sa'a a haka sannan Kularu ya sami nasara a karo na biyu ya sari Uzaima a gefen cikinsa.Kafin Kularu ya dauke takobinsa tuni Shima Uzaima ya rama saran da yayi masa kuma shima a gefen ciki.Lokaci guda suka fadi kasa tare kowannensu ya kasa tashi.Adaidai wannan lokaci ne Uzaima ya juya ya dubi bayansa inda ake fafatawa tsakanin sarki Garzub da sarki Madarus,kawai sai ya hango Madarus ya lumawa Garzub takobi a cinya ta hudo ta baya.Yana zare takobin Jini yayi tsartuwa.Garzub ya kurma uban ihu.Madarusi bai kyale Garzub ba sai yasa kafa ya doki kirjinsa yai tsalle sama ya fado kasa ya baje a cikin mugun hali,Madarus ya ruga izuwa kan Garzub yana kururuwa cikin mugun nufi.Yana isowa daf dashi ya daga wannan sihirtacciyar takobi tasa da nufin ya tsargeshi gida biyu kawai sai akaga Uzaima ya sake dako tsalle daga inda yake ya doki kirjin sarki Madarus da kafafunsa biyu.Saboda karfin dukan saida Sarki Madarus yai sama sosai sannan ya rikito kasa a matukar galabaice.Kofa dakarun sarki Madarus sukaga abinda ya faru ga sarkinsu sai suka yunkura gaba dayansu suka afkawa dakarun sarki Garzub.Nanfa filin yakin gaba daya ya hautsine aka bar batun fidda raini a tsakanin sadaukan shida.Aka ruguntsume da azababben yaki cikin zafin nama.Uzaima ya suri mahaifinsa Sarki Garzub ya goyashi a bayansa sannan ya cigaba da yaki a haka yana ragargazar maza yana kutsawa ta cikinsu da karfin tsiya yana sare na sarewa kuma yana banke na bankewa,kokarinsa kawai shine ya koma can baya inda farkon dakarunsu suke wato inda tantin sarki yake domin ayi masa magani a ceci rayuwarsa daga hallaka sakamakon jinin dake ta zuba a jikinsa mai yawa.Tunda Uzaima yazo duniya hankalinsa bai taba dugunzuma ba sama da na wannan rana kuma ransa bai taba baci ba kamar haka domin yana yakin ne da dukkan karfinsa a lokacin da zuciyarsa ke tafarfasa.Gaba dayan dakarun dake filin yaki saida suka cika da mamakin irin wannan gagarumar jarumtaka da Uzaima keyi musamman da akaga an rasa wanda zai sha gabansa ya tsaidashi.Duk ta inda aka kawo masa hari walau gabas da yamma ko kudu da arewa sai aga ya tare harin.Wanda zai iya tarar tasa a wannan lokaci mutum biyu ne kacal daga sarki Madaru sai Sadauki Kularu.Su kuwa duk sun haukace akan daukar rayukan dakarun sarki Garzub duk inda suka ratsa saidai kaga mazaje na zubewa.Shima sarkin yaki Zamud haka ya rinka ragargazar dakarun Madarus.Kuma duk sa'adda ya hango Sharkas na kokarin hawa kan dokinsa saiya ruga inda yake ya kashe dokin su cigaba da artabu.Ba abinda zai baiwa mutum mamaki a wannan yaki face yadda sadaukai ke nuna tsantsar jarumtaka domin sai kaga sadauki da raunika manya a jikinsa yana ta zubar da jini amma yaki zuwa kasa yana dada ragargazar maza.Kaico!Yau fa ranar cinikin rayuka,ga inda aka baje kolin gawa kuma ga inda kogin jini yake ambaliya.Kowa ka gani a filin yaki sai kaga anyi masa wankan jini.Hatta fuskokin jamaa sun shafe da jini saidai kaga suna share idanunsu don kada jini ya hanasu gani.Duk wannan jarumtaka da Uzaima keyi ashe gimbiya Zarilat na hangowa daga can karshen baya inda tantin sarkinsu yake.Koda Zarilat taga irin gagarumar bajintar da Uzaima yayi sai nan take taji yayi matukar burgeta.Nan take Sonsa ya shiga zuciyarta ya mamaye amma data tuna cewa makiyi ne a gareta sai ta fara tunanin yakice shi daga cikin zuciyarta.Kularu na cikin ragargazar dakarun Garzub sai ya hango can tsakiyar filin yakin inda Uzaima keta tsala gudu yana dauke da mahaifinsa a baya yana kutaswa ta cikin miliyoyin abokan gaba har yaje tsakiyar.Tabbas nan da wasu dakiku kamar dari uku da doriya zai iya zuwa inda tantin sarki Garzub yake a sami damar yi masa magani cikin gaggawa.Koda ganin haka sai Kularu ya daka tsalle sama ya rinka gudu akan kawunan mutane ya durfafi inda Uzaima yake.A wannan lokaci ne Kularu ya nuna tsantsar zafin namansa domin duk sa'adda ya taka kan Abokan gaba sai kaga sun kawowa kafafunsa sara amma babu wanda ya tabashi har ya dira a gaban Uzaima yasha gabansa.Bisa dole Uzaima ya tsaya cak a waje daya yana mai sara abokan gaba masu afko masa kuma suka fara kallon kallo shida Kularu.Shima Kularu bai fasa saran dakarun su Uzaima ba tunda filin yakin a yamutse yake gaba daya.Duk mai tsautsayin da yazo ta gabansu ko ta bayansu ko ta gefe take yake zama gawa.Bisa dole akatarwatse daga kusa dasu aka cigaba da yaki a nesa kadan dasu domin sun zama dodanni a fili dagar.A sannan ne Kularu ya dubi Uzaima ya kyalkyale da dariyar mugunta sannan yace kana zaton zaka sami nasarar kai mahaifinka can tantinsa ne alhalin ina nan a filin wannan yaki? Tabbas kayi babban kuskure da kake tunanin zaka sami nasarar yin hakan.Tabbas kayi dabara daka ceci rayuwar mahaifinka daga sharrin Sarki Madarus saidai kayi gudu ne na banza wanda babu wajen zuwa.Ko shakka banayi yanzu zan kashe mahaifinka nayi masa KISAN GILLAH a gaban idanunka sannan kaima na kasheka.Hakika idan nayi haka na gama cika burina domin na gama siye zuciyar abar begena.Cikin tsananin mamaki Uzaima ya dubi Kularu yace wace kuma abar begenka?Maimakon Kularu yace wani abu sai yayi nuni da takobinsa izuwa can inda sansaninsu yake wato inda suka kafa tantuna.Uzaima ya dubi can wajen saiya hango Gimbiya Zarilat tsaye akan wani dogon dutse ta rufe fuskarta da farin kyalle mai shara shara kuma ta kura masa idanu.Kularu ua dubi Uzaima yana mai cigaba da bayani yace kai kadai ne sadaukin da yayi gagarumar jarumtaka a bangaren abokan gabarmu.Lallai idan na kasheka a yanzu na nuna cewa jarumtakata tafi taka.Adaidai wannan lokaci ne sarki Garzub ya budi baki da kyar yace yakai dana ka ajiyeni ka tari wannan yaro domin ni tawa ta kare bazan iya tsinana komai ba a wannan yaki.Koda jin haka Sai Uzaima ya girgiza kai yace Yakai Abbana kayi sani cewa ba zan iya ajiyeka ba makiya su hallaka.Lallai ta kowane hali sai na kaika tantinka.Kularu bai isa ya hanani ba.Kafin Uzaima ya gama rufe bakinsa tuni Kularu ya daka tsalle ya dira a gabansa ya kawo masa wawan sara da nufin ya tsarge kafadarsa gida biyu,cikin zafin nama ya goce suka ci gaba da artabu sai gashi Uzaima yana yin gagarumar jarumta ta gaban kwatance wadda ta shallake tunanin shi kansa Kularu,domin Uzaima yana yaki dashi kuma yanayi da sauran dakarun su Kularu yana kutsawa ta tsakiyarsu da karfin tsiya.Kiri kiri Kularu ya kasa taba jikin Uzaima duk da cewa yana kai masa SARA DA SUKA ta ko ina kuma shima a hakan yana yakar dakarun su Uzaima.Ba zato ba tsammani sai Kularu yaga Uzaima ya zabura ya falfala da azababben gudu ta cikin dakaru yana bankesu da karfin tsiya yana samarwa da kansa hanya.Ana saransa jini na tsartuwa amma yaki ya fadi kasa kuma gashi yana goye da mahaifinsa sarki Garzub yaki yarda ya yar dashi.Kularu yabi Uzaima da gudun tsiya domin ya sake shan gabansa ya hanashi kaiwa can karshen inda dakarunsu suke wato inda tantin sarki Garzub yake,amma sai ya kasa cimmasa domin inda Uzaima ke shiga wuri ne inda Dakarunsu sukafi tsananin yawa don tabbatar da tsaro ga tantin sarki don haka sai dakarun suka rinka lullube Kularu.Tunda sarkin yawa yafi sarkin karfi dole ya rinka komawa da baya da karfin tsiya domin ya ceci rayuwarsa saboda indai ya cigaba da kutsawa ta cikinsu tabbas sai ya gaji da yaki sun kaishi kasa.Ashe duk wannan jarumtaka da Uzaima keyi Gimbiya Zarilat na kallo domin ta sake sulalowa daga can inda take ta dawo tsakiyar filin yakin tana more idanunta bisa ganin yadda ake RAGARGAZAR MAZA.Koda Gimbiya Zarilat taga irin wannan jarumtaka da Uzaima yayi sai taji duk duniya babu mutumin da yafi dacewa da ita face Uzaima.Kuma a sannan ne ta tabbatar da cewa Kularu bazai taba zama abokin rayuwarta ba domin yau gashi taga jarumin daya fishi tsananin juriya da jarumtaka.Nanfa Gimbiya Zarilat ta cigaba da kutsawa ta cikin turmitstsin mutane ba tare da fargabar komai ba tana karawa gaba da gudu domin ta sami damar hango irin jarumtakar da Uzaima keyi.A iya rayuwar Gimbiya Zarilat bata taba zuwa filin yaki ba kuma ta kasance mai tsananin tsoro domin ko yaya taga jini ya zuba a jikin mutum sai ta kama kuka saboda tausayi da razana,amma ya gashi ana gididdiba bil'adama,sassan jikinsa ma take tattakawa tana wucewa amma bata tsorata ba.Ba komai ne ya janyo hakan ba face kawao son ta cigaba da kallon jarumin daya burgeta a cikin filin yakin wato yarima Uzaima.Ba komai ne yasa Zarilat ta sami damar sulalowa ba daga inda ake tsare da ita ba face yadda filin yakin ya hargitse ya zamana cewa yakin yayi tsamari ainun kowanne bangare sun firgice sun dimauce an koma neman TSIRA.Duk da cewa dakarun su sarki Madarus sunfi yawa ainun amma sai gashi ana KARE JINI,BIRI JINI domin kowanne bangare yana gane kurensa,mazaje nata zubewa kasa matattu.A can tsakiyar filin yaki kuwa sarki Rakalu ya hakura da bin bayan Uzaima don bashi tsaro na musamman saboda bala'in yakai bala'i.A wannan lokaci comments and like TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Biyu (2) Part E Al'amarin Yarima Uzaima da Gimbiya Izaima kuwa suma kai tsaye suka wuce izuwa nasu sansanin.Da zuwa sai dakaru suka rugo da gudu suka sauke sarki Garzub daga kan doki aka shigar dashi cikin tantinsa aka kwantar dashi akan gado.Wannan karaya ta yan yatsun hannunsa aka fara gyarawa sannan aka cigaba da duba sauran jikinsa.Koda babban likitan nasa yaga wannan kashin baya ya karye sai hankalinsa ya dugunzuma ainun,domin yasan cewa kashine wanda koda an dorashi har abada mutum ba zai iya mikewa ba tsare bare har yayi tafiya.Saidai ya cigaba da rayuwa a kwance har izuwa lokacin da rayuwarsa zata kare.Lokacin da aka fara yiwa sarki Garzub gyaran wannan karaya ta kashin bayansa saida ya suma sau shida saboda tsananin zafi da zogin da yakeji.Bayan an gama gyaran ne aka bashi maganin bacci yasha.Bai farka ba sai bayan sa'a hudu.Kafin sarki Garzub ya farka sai Yarima Uzaima yaja babban likitan gefe daya ya dubeshi yace yaya jikin mahaifina?Nan da wane lokaci kake ganin zai samu lafiyar jikinsa sosai ya mike tsaye ya cigaba da yaki?Sa'adda babban likitan yaji wannan tambaya sai hankalinsa ya dugunzuma fiye da ko yaushe ya sunkui da kansa kas ya kasa cewa komai.Cikin fishi yarima Uzaima ya cakumi rigar likitan yace maza kayi mini bayani ko yanzun nan na shakeka ka mutu.Jikin likitan na karkarwa yace ya shugaban mahaifinka har abada ba zai iya mikewa tsaye ba bare ya iya cigaba da yaki.Koda jin wannan batu sai Uzaima ya kurma uban ihu mai firgitarwa sannan ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa ya fashe da matsanancin kuka.Gimbiya Izaima dake can nata tantin a zaune tana kuka tana tunanin nata mahaifin da ta rasa sai ta jiyo ihun Uzaima,bata san sa'adda ta mike zumbur ba ta ruga waje da gudu ta nufi inda Uzaima ke durkuseh.Da zuwa ta tsuguna a gabansa tace yakai burin zuciyata ina dalilin wannan kuka naka? Uzaima ya dago kai da kyar ya dubeta a lokacin da dukkaninsu suke zubar da hawaye yace yake Izaima kiyi sani cewa har abada mahaifina bazai mike tsaye ba ya nakasa.Koda jin haka sai Izaima ta rungume Uzaima suka sake fashewa da kuka a tare.Ita dai Izaima dalilin kukanta guda biyu ne.Dalili na farko tsananin bakin ciki ne bisa ganin cewa mahaifinta ya mutu,kuma shima mahaifin Uzaima ya shiga mummunan hali don abu ne mayuwaci aurenta da yarima Uzaima yayiwu.Dalili na biyu kuwa tsananin farin ciki ne bisa ganin a yau kuma a karo na farko ta sami damar kusantar Yarima Uzaima gashi ma harta rungumeshi a kirjinta.Tsawon yan dakiku Uzaima da Izaima na rungume da juna,daga can saiya janye jikinsa daga cikin nata sannan ya mike tsaye ya kira babban likita yazo gabansa ya tsaya.Uzaima ya dubi babban likitan yace dashi abinda nake so da kai shine kada ka kuskura ka gayawa mahaifina cewa ba zai mike ba.Lallai ka sanar dashi cewa nan da wani lokaci zai warke sumul ya mike.Idan ka kuskura ka saba wannan umarni nawa hukuncin kisa ne a kanka.Koda gama fadin haka sai Uzaima ya dubi sauran gaba dayan dakarun dake sansanin yace dasu.Kuma abinda nake so daku shine kada dayanku ya tona wannan sirri ga mahaifina wanda duk ya tona kuwa hukuncin kisa ne a kansa.Abu na biyu ku zuba ido sosai wajen tabbatar da tsaro a wannan sansani namu domin a ko yaushe makiya zasu iya kawo mana hari.Yanzu dole ne mu saurara izuwa lokacin da sarki zai farka daga bacci domin muji umarnin da zai bamu.Sa'adda Uzaima yazo nan a zancensa sai wani sadauki mai suna Ukazu wanda shine mataimakin sarki yaki ya dubeshi cikin alamun karayar zuci yace ya shugabana kayi sani cewa zamanmu anan sansanin yana da matukar hadari domin a halin yanzu mun rasa dukkan manyan jarumanmu kuma kaso biyu cikin uku na mayakanmu duk sun mutu saura kaso daya.A cikin kaso dayanmu da muka rage rabi sun afka cikin jeji sun buya.Duk da cewa mun kashe da yawa daga cikin abokan gaba har yanzu fa sun ninkamu sau uku a yawa,ko a yanzu idan suka afko mana nan zasu iya murkushemu a cikin kankanin lokaci.Yayin da Uzaima yaji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya yace tabbas duk abinda ka fada gaskiya ne yakai Ukazu amma abinda nake so ka fahimta shine suma abokan gabar tamu yanzu a cikin mummunan tashin hankali suke tunda abin dogaron nasu ya zama nakasasshe tunda ya rasa kafa daya da ido daya.Sun rasa sarkin yakinsu da kuma manyan sadaukansu wanda ya rage musu yanzu sadauki Kularu ne kamar yadda nima na rage a cikin manyan sadaukanmu.Abune mayuwaci suyi yunkurin kawo mana farmaki a yanzu dole sai sun tsaya sun yi tunani da shawara.Na tabbata shima sarki Madarus bayan likitocinsa sunyi masa magani dole ne su bashi maganin bacci kuma bazai farka ba sai nan da tsawon yan sa'o'i kusan lokacin da namu sarkin zai farka.Ina tabbatar maka da cewa a yau dai babu wani yaki da za'a cigaba dayi saidai gobe.Koda gama fadin haka sai Uzaima ya tafi ya leka cikin tantin sarki Garzub ya ganshi kwance yana ta shara bacci.Cikin sanyin jiki ya juya da baya ya tafi izuwa nasa tantin.A wannan lokaci ne dakaru suka shiga hidimar daga abinci.Yarima Uzaima ya zauna a cikin tantinsa yayi tagumi kuma ya fada tunani mai zurfi.Yana cikin wannan hali ne yaga an shigo cikin tantin nasa koda ya daga kai sai yaga ashe Gimbiya Izaima ce dauke da abinci.Jikinta a sanyaye tazo daf dashi ta ajiye abincin sannan ta koma gefe daya ta zauna tana mai sunkui da kanta kas.Koda Uzaima ya dago kai ya dubeta sai yaga hawaye na zuba a idanunta.Al'amarin dayai matukar dugunzuma hankalin Uzaima kenan ya dubeta cikin tsananin mamaki yace yake gimbiya ina dalilin zubar da wannan hawaye naki? comments and like to be continued TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Biyu (2) Part F Alhalin gata a tsaye a gabansa.A sannan ne ya fahimci cewa tana da tsarin tsafi mai karfin gaske a jikinta wanda babu mai iya cutar da ita a filin yakin gaba daya.Koda fahimtar hakan sai sarki Madarus ya rabu da Izaima ya ruga izuwa cikin abokan gaba ya cigaba da yaki,Izaima ta fada kan gawar mahaifinta ta rungume gawar a kirjinta ta fashe da matsanancin kuka.Abinda ya kara daure mata kai shine gashi dai mutane suna ta yaki a kanta suna ta dudufniya amma ko kadan babu wanda ya taba jikinta.A sannan ne ta tuno da maganar da mahaifin nata ya gaya mata cewa muddin tana tare da wannan Kambun tsafi daya bata babu wani tsautsayi da zai sameta.Koda ta tuno da wannan batu saita dada kankame gawar sarki Rakalu a kirjinta ta kuma rushe da kukan bakin domin tasan cewa son da yakeyi mata yafi wanda yake yiwa kansa tunda har ya iya bata wannan kambun tsafi ya sallama rayuwarsa domin tata.A bangaren sarkin Yaki Zamud da sarkin Yaki Sharkas kuwa lokacin da yaki ya sake yin nisa sai suka sake hadewa suka ciga da masifaffen yaki sai gashi kowa ya baiwa kowa mamaki domin karfi yazo daya domin dukkaninsu sunsan cewa yaufa sun gamu da gamonsu.Duk wanda ya sami nasarar yiwa dan uwansa rauni sai kaga nan take shima wanda aka yiwa raunin yayi ramuwar gaiya.Kafin cikar rabin sa'a sun yiwa junasu muggan sara da suka sunyi fata fata da jikinsu.Lokaci guda duk su biyun suka zube kasa matattu dayansu bai sake shurawa ba.Al'amarin Kularu kuwa lokacin daya fahimci cewar idan ya cigaba da bin yarima Uzaima izuwa inda tantin sarki Garzub yake zai iya rasa rayuwarsa tunda sarkin yawa yafi

Chapter 6 of 7