Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
za'a sami ciyawa da ruwa domin dabbobinsu su sami abinci.Shugaban wadannan makiyaya ya kasance dattijo dan kimanin shekaru saba'in da 'ya'ya ana kiransa da suna Atiyar.Kallo daya mutum zai yiwa Atiyar ya gane cewa da can anyi GWARZON JARUMI,domin gaba dayan surar jikinsa irin ta sadaukai ce,amma tsufa ya sauya masa siffa ya tauye masa kwarjini.Shugaba Atiyar yana da 'ya guda daya,wata kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance mai suna Sulaira.Duk da cewa Sulaira ta kasance bakar fata amma kalar fatar jikinta ta bambanta data sauran bakaken mata,domin ita wankan tarwada ce,sannan tana da yalwar gashi mai santsi da sheki tamkar na mutanen kasar Hindu.Tana da dara daran idanu farare sol masu daukar hankali gami da dogon siririn hanci da dan karamin baki.Tana da kananan hakora a jere reras kuma masu haske wadanda duk sa'adda ta bude bakinta mutum yayi arba dasu sai yaji kamar ya kwashesu ya maida su nasa bakin.A duk sa'adda Sulaira tayi murmushi kuwa mutum na iya jin kamar an bashi SARAUTAR DUNIYA domin take zata zare masa dukkan bakin cikin dake cikin zuciyarsa.Kai kyawun diri kuwa a wajen Sulaira tamkar ita ta kera kanta,kwatance da baki bazai yiyuba sai abinda ido ya gani kawai.(Hmm Kyakkyawa).Gaba dayan mazajen wadannan makiyaya sun kasance zakwakuran mayaka masu dakawa maza gumba a hannu.Asalin wannan makiyaya dangine mai yawan zuri'a wadanda adadinsu yakai dubu uku,amma a yawon kiwon da sukeyi ne 'yan sumame ke kawo musu hari don rabasu da dabbobinsu aka rinka karkashe su har ya zamana saura su dari uku kacal.Fiye da shekaru goma baya ba'a sake kashe koda mutum daya daga cikinsu ba.A wannan shekarar ne shugaba Atiyar ya shirya gasar neman auren 'yarsa Sulaira a tsakanin samarin wannan zuri'a tasu,kuma an yanke hukuncin cewa sai anje dajin dake da iyaka da birnin Hirtoliya sannan za'a fara gasar.Yanayin gasar shine za'ayi kokawa ne a tsakanin samari ashirin da hudu ya zamana cewa kowa ya kara da kowa,wanda duk aka kasa kaishi kas har aka gama gasar shine zai auri Sulaira.Su Atiyar na cikin harhada kayansu kenan a lokacin da Sulaira ke taya mahaifinta debo kaya daga cikin bukka suna dorawa akan rakumansu sai kawai suka hango kura daga yamma ta turnuke sararin samaniya.Al'amarin daya dugunzuma hankalinsu kenan gaba daya.Nan take shugaba Atiyar ya yiwa jama'arsu tsawa yana mai basu umarnin a tusa dabbobi a gaba da gudu domin ya fahimci cewa wani gagarumin AYARI ne na yan sumame suka danno wadabda ba za'a iya tsayawa ba a tunkaresu har a fafata.Abinda ma bai sani ba shine abinda ke zuwa yafi karfin Ayari,RUNDUNA ce ta gaban hankali.Nan fa jama'ar Atiyar suka sa dabbobinsu akan gaba matansu a tsakiya suka sakarwa dawakansu kaimi suna masu tsala gudu.Koda suka waigo baya sai sukayi arba da rundunar mayakan su Sharkas sun taso su a gaba cikin matsanancin gudu suna neman kuresu.Babu abinda ya firgita Atiyar da jama'arsa face ganin tsananin yawan wannan runduna dake kokarin tarar dasu da kuma kwarjininsu.A wannan lokaci dakarun Sharkas ihu suke suna karawa dawakansu kaimi,suna cin burin su kurewa mutanen Atiyar gudu su ragargajesu su kama na kamawa su kashe na kashewa kuma su kwashe dukiyoyinsu.Saida su Atiyar sukayi gudun sa'a guda amma duk sa'adda suka waigo sai suga ABOKAN GABAR sun kusa cimmusu,kawai sai ya ja linzamin dokinsa yai turjiya ya tsaya cak,cikin tsananin razana sauran mazajen kabilar sukayi tirjiya suka tsaitsaya.Daya daga cikinsu ya dubi Atiyar cikin firgici yace ya shugabana me yasa ka tsaya alhalin kasan cewa ba zamu iya da wannan muguwar runduna ba?Kafin Atiyar ya budi baki yace wani abu sai ya fara zare takobinsa sannan ya dubi wannan jarumi da yayi masa tambayar yace yakai Kufaru kayi sani cewa wannan gudu da mukeyi gudun banzane domin bamu isa mu tserewa wadannan yan sumame ba,dole ne su kure mana gudu kuma su karkashemu su wulakanta matanmu,su debe dukiyarmu.Da hakan ta faru salin alin gwara mu tsaya ko mutum dubu muka kashe daga cikinsu ai mun rage asara tunda dole ne su tafi da bakin cikin barnar da mukayi musu.Sa'adda Atiyar yazo nan a zancensa ne yaga 'yarsa Sulaira ta zuba masa ido hawaye na zuba a idanunta.Kawai saiya dubeta yayi murmushi yace yake 'yata yaune ranar da zan tafi izuwa inda mahaifiyarki ta tafi,saboda me zakiyi bakin ciki maimakon ki tayani farin cikin zan sadu da MASOYIYATA.Dajin Haka sai Sulaira ta zare takobinta sannan ta share hawayenta kuma ta yiwa Atiyar murmushi tace nima ina fatan na bika inda mahaifiyata ta tafi a yau domin banga amfanin rayuwa ba a duniya muddin babu MASOYI.Atiyar yace a'a yake 'yata bana fatan kema ki gushe,domin idan kika gushe shike nan babu sauran zuri'armu kenan.Na sani cewa abu ne mayuwaci wadancan yan sumame dake durfafarmu su kasheku a matsayinku na mata.Lallai inason ki rayu domin nan gaba kiyi aure har ki bar baya.Gama fadin hakan keda wuya sai Atiyar yaji gaba dayan sauran matan Ayarin nasu sun fashe da kukakn bakin ciki domin sun san cewa yaune ranar da zasu rabu da mazajensu.Adaidai wannan lokaci ne ya zamana cewa tazarar dake tsakaninsu Su Atiyar da da Rundunar bata da yawa sai ya daga takobinsa sama yace mu kare mutuncinmu mu bada jikinmu da jininmu ga kasa.Kawai saiya zaburi dokinsa da gudu ya tari abokan gaban.Koda ganin haka sai sauran yan uwansa mazaje suka rufa masa baya.Kaico!Kaji maza wadanda suka san hakkin zuri'arsu da dukiyarsu kuma suka sallama rayuwarsu domin su.Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda ko kadan babu wani tsoro ko fargaba a cikin zukatan su shugaba Atiyar duk da ganin tsananin yawan dakarun Sharkas,amma suka taresu,duk da sun san cewa ruwa ba sa'an kwando bane.Burinsu kawai shine a kashe su suna kokarin kare mutuncinsu in yaso a yiwa kasa ado da jikinsu da jikinsu.A cikin gaba dayan matan Ayarin su Atiyar Sulaira ce kadai ta bugi kirji ta shiga cikinsu Atiyar domin ayi wannan yaki tare da ita saboda itama tana da Jarumtaka ta ban mamaki domin barewa batayi gudu ba 'yarta tayi rarrafe.Koda aka gwamutse tsakaninsu Atiyar da dakarun Sharkas sai aka rincabe da AZABABBEN YAKI.Karar karafa gami da haniniyar dawakai da dudufniyar kofaton dawakan suka cika dodon kunne,kura ta tashi ta baibaye wajen gaba daya,sai gashi dan hakin da aka raina yana neman tsone ido,domin rukunin farko na dakarun Sharkas wadanda suka fara isowa gaban su Atiyar sun kasa aiwata komai,kaifi kawai suka sha saidai kaga sassan jikinsu na yawa a sama suna fadowa kasa.Jini kuwa ya rinka fantsamuwa.Koda sauran yan uwan dakarun Sharkas suka hango abinda ke faruwa ga yan uwansa sai suka karawa dawakansu kaimi suna ihi mai firgitarwa.Nan da nan kuwa suka iso kansu Atiyar sukayi musu rubdugu.Wayyo!Hakika sarkin yawa yafi sarkin karfi.Nan da nan aka fara yiwa dakarun Atiyar MUGUN KISA,saidai kaga an zabtarewa jarumi kafadarsa ko hannunsa ko kuma a filla masa kansa gaba daya ya bingire kasa matacce.Koda Atiyar da sauran sukaga irin barnar da ake yiwa yan uwansu sai suka ZAGE DAMTSE sosai suka cigaba da BAKIN ARTABU suna yaki suna kuka saboda takaici da bakin ciki.Kafin cikar rabin sa'a an gama kashe gaba dayan dakarun Atiyar ya rage saura su biyu kacal,wato shida 'yarsa Sulaira suna ta namijin kokari.Gashi dai miliyoyin dakaru sun kewayesu suna kai musu hari ta ko ina,amma sun kasa kaisu kasa.Su kansu dakarun sunyi matukar mamaki bisa ganin irin jarumtakar wadannan mutane biyu.Ana cikin wannan bakin gumurzu ne sadauki Sharkas ya karaso wajen bisa dokinsa a sukwane.Koda ganinsa sai aka bude masa hanya,gaba dayan dakarun nasa suka ja da baya aka daina yakar su Atiyar akayi cirko cirko.A wannan lokaci baka jin sautin komai face sautin sawayen dokin sadauki Sharkas.Tun daga nesa kadan sadauki Sharkas ya kurawa Atiyar da Sulaira idanu yana mamakin yadda akayi har suka iya shafe kusan rabin sa'a suna fafatawa da dakarunsa ba tare da an kaisu kasa ba.Fuskarsa a murtuke ya kurawa Atiyar da Sulaira idanu.Koda ya gama nazarinsu yaga ma su biyu ne kacal kuma harma da mace a cikinsu sai ransa ya baci ainun.Atiyar da Sulaira kuwa suna hango Sadauki Sharkas sai jikinsu yayi sanyi suka tabbatar da cewa babu sauran wani kokari da zasu iyayi domin da gani ba tambaya,Kura zata ci Mutum!Tunda Atiyar yazo duniya bai taba ganin mutum mai fadi,tsawo da kirar karfi ba kamar Sharkas.Koda sarkin birnin Hirtoliya wato sarki Garzub da ake ta zancensa a nahiyar gaba daya yasan cewa baifi rabin wannan sadauki ba.Kafin Sharkas ya karaso garesu sai Atiyar ya dubi Sulaira yace da ita yake 'yata ki dubi gawarwakin yan uwanmu gasu nan birjik a kas.Ina murna nima zan bisu inda suka tafi.Kiyi mini alkawari bayan tafiyata daya daga cikin wadannan azzalumai bazai amfani jikinki ba.Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa Sulaira tayi jifa da takobin hannunta sannan ta zare wata sharbebiyar wuka daga jikinta ta dubeshi tace yakai Abbana nayi maka alkawari da zarar naga ka tafi nima zan tuta kaina inda ka tafi.Koda jin haka sai Atiyar ya yiwa Sulaira murmushin karshe sannan ya juya ya fuskanci sadauki Sharkas wanda saura kiris ya iso gabansa ya rike takobinsa da hannu biyu.Lokacin daya rage saura taku uku kacak sadauki Sharkas ya iso gaban Atiyar sai ya daka tsalle sama daga kan dokinsa tamkar an zukoshi da kugiya ya kawowa Atiyar mummunan sara.Atiyar ya kare saran da dukkan karfinsa amma saida takobin Sharkas ta raba takobin Atiyar gida biyu kuma ta tsarga kafadar Atiyar ya bingire kasa matacce.Koda ganin abinda ya faru sai Sulaira ta tsandara ihu ta daga wannan wuka dake hannunta da nufin ta caka a cikinta.Karar sukuwar dawakai ce mara adadi a bayansu tasa Sulaira ta fasa idda nufinta.Cikin firgici Sharkas da gaba dayan dakarunsa suka waiga sukayi arba da wata runduna mai yawan gaske ta durfafosu.Mayakan sun zare makamansu suna ihu suna haddasa karamar girgizar kasa a dajin gaba daya.Koda ganin wannan runduna sai Sharkas ya bushe da dariya duk da yaga cewa da kadan nasa dakarun zasu fi wadancan yawa.Ba komai ne yasa Sharkas yin dariya ba face ganin cewa dakarun dake zuwa gaba dayansu bakaken fata ne,shi kuwa rundunarsa duka ta sadaukan larabawa ce wadanda ya yarda da jarumtakarsu gami da bakin nacinsu da kwarewarsu a yaki.Ita dai wannan runduna dake zuwa ba tasu kowa bace face su Sarki Garzub wadanda suka fito domin kare kasarsu da dukiyarsu bisa jin cewa su Sharkas na nan tafe.Nan take Sharkas ya dakawa Dakarunsa tsawa yace maza su tari ABOKAN GABA.Ai kuwa sai duk suka sakarwa dawakansu linzami suka durfafi abokan gabar.Wohoho!Wanda duk bai ga sa'adda wadannan rundunoni biyu ke kokarin haduwa da juna ba yayi asarar kallo kuma baiga mummunan tashin hankali ba a rayuwarsa domin lokacin da dawakansu suka rinka kartar kasa suna azababben gudu kuma mazajensu dake kansu suka zare makamai suna ihu saida dajin gaba daya ya hautsine kamar sama zata rikito kasa.Ai kuwa ana haduwa aka kacame da masifaffen yaki tamkar mayakan duniya ne kaf suka hade.Nan fa wuri ya yamutse komai kallon kurillar mutum bai isa ya tantance bangaren da ke samun nasara ba,saboda jama'a gaba daya jikinsu da dawakansu ya rine da jini.Da zarar mutum ya daga kansa sama saidai yaga hannaye,kafafuwa da kafadun bil'adama na shawagi a sararin samaniya.Shi kuwa jini daya fara fantsamuwa yana zuba a kasa tamkar teku ta balle.Kai ko daga nesa mutum yaji ihun da mazaje sukeyi a wannan filin yaki dole ne ya kidime,mai karamar kwakwalwa ma zai iya zautuwa.Duk wannan bakin gumurzu da akeyi babu mutum biyu a ciki wato babu sadauki Sharkas da Sarki Garzub domin duk su biyu suna tsaye a gefe daya bisa dawakansu kowa ya zuba ido yana kallon bakin artabun da akeyi.Saboda bala'in wannan yaki da akeyi Sharkas ya manta ma da batun Sulaira wacce ke tsaye a bayansa kamar gunki. TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Daya (1) Part C Wacce ke tsaye a can bayansa kamar gunki tana kallon wannan azababben yaki da ake fafatawa.Sa'adda Sulaira ta fuskanci haka sai ta rinka ja da baya a hankali har tayi nesa dashi sosai taje can bayan wani katon dutse ta labe tana hangen abinda ke faruwa kuma tana kuka bisa tunowa da mutuwar mahaifinta da dukkan sauran zuri'arsu.Har izuwa wannan lokaci tana rike da wannan wuka kuma hannunta nata karkarwa tana shawarar ta kashe kanta ko kuma ta fasa.Lokacin da akayi yini ana wannan yaki ya zamana cewa ana ta asarar rayuka a kowanne bangare ba adadi kuma an kasa gane bangaren da ke samun nasara sai hankalin Sharkas dana Sarki Garzub ya dugunzuma suka rasa abinda ke musu dadi.Da yake duk su biyun sun hau kan duwatsu ne masu tudu suna iya hango juna kuma kowannensu yana yiwa kowa kallon shakka,duk da cewa Sharkas yafi Garzub kwarjini da cika ido.Ashe duk wannan abu dake faruwa Sarki Garzub ya lura da Sulaira wacce ta buya a can bayan dutsen da Sharkas ke bisa kansa.Shi kuwa Sharkas yama manta da al'amarinta.Lokacin da sarki Garzub ya fahimci cewa idan rana ta fadi duhu ya soma za'a iya tsayar da wannan yaki.Idan kuwa aka tsayar da yakin Sharkas zai iya tunowa da batun Sulaira yasa a farautota a duk inda take a cikin dajin.Tun sa'adda sarki Garzub ya kyallara ido ya hango Sulaira yaga irin tsananin kyawunta sai nan take yaji ya kamu da tsananin SONTA.Nan take Sarki Garzub ya kada linzamin dokinsa ya sauko daga kan dutsen da yake,kawai saiya zare takobinsa ya zaburi dokinsa da gudu ya nufi kan Sharkas yana ihu da kururuwa.Koda ganin haka sai shima Sharkas ya zare tasa takobin ya zaburi dokinsa.Dokin ya daka tsalle daga kan dutse ya duro kasa ya fita da gudu don haduwa da takwaransa wato Dokin Garzub.Sai gashi duk su biyun suna ihu da kururwa irin wacce ke firgita mazaje.Kai inda ace a lokacin da suke wannan dabbobin dajin na kusa da sai dukkaninsu sun dimauce,na rami sun kama fitowa,na waje na kokarin komawa rami su kuma na kan bishiya na tarwatsewa.Yayin da Sharkas da sarki Garzub suka kusan haduwa ya zamana cewa saura baifi taku biyar ba a tsakaninsu sai Sharkas ya daka tsalle sama daga kan dokinsa ya kaiwa Garzub mahaukacin sara irin wanda ya yiwa Atiyar mahaifin Sulaiara ya tsargeshi gida biyu.Cikin zafin nama Garzub ya goce kuma ya kare saran da takobinsa.Saboda karfin saran da kaifin takobin Sharkas wacce ta kasance tsafaffiya saida takobin Garzub ta rabe biyu,takobin Sharkas ta datsa bayan dokin Garzub ya rabe biyu tamkar an yanka lemon bawa a tsakiya,dokin ya zube kasa matacce.A lokacin da Sharkas ya duro kasa bisa kafafunsa,shi kuwa Garzub ya mike zumbur da sauri.Maimakon Garzub ya fuskanci Sharkas sai kawai ya falfala da matsanancin gudu gaba ya nufi wannan dutse wanda Sulaira ta buya a bayansa.Koda ganin haka sai Sharkas ya cika da mamaki ya bishi da kallo kawai yana tunanin ko guduwa yake so zaiyi bisa ganin abinda ya faru ga takobinsa da dokinsa.Wata zuciyar kuma sai tace da Sharkas haba ya za'ayi sarki guda kuka GWARZON MAYAKI kamar Garzub wanda aka bashi labarinsa ace zai gudu a filin yaki alhalin ya jagoranci wadannan miliyoyin mayaka kuma gashi har yanzu yakin ake ta fafatawa wanda babu alamar nasara ga kowanne bangare.Sadauki Sharkas na cikin wannan tunani ne ya hango Sarki Garzub ya isa inda wannan dutse yake kawai sai ya sake hango Sulaira ta mike tsaye zumbur.A tsorace bisa ganin Garzub ya taho gareta.Nan take Garzub ya gaya maya wata maganar tunda Sharkas nacan nesa baya jiyo abinda suke tattaunawa.Kawai sai yaga sun kama hannun juna sun kara falfalawa da gudu izuwa cikin daji.Koda ganin hakan sai Sharkas ya juya da sauri da nufin ya kamo dokinsa ya hau ya bi sawunsu amma sai yaga ma dokin nasa nacan baya don haka zai bata lokaci kafin ya isa inda dokin yake,kawai sai shima ya falfala da gudun tsiya domin ya cimma su Garzub.Duk da cewa sun bashi tazara mai dan yawa sai gashi yana neman ya cimmasu saboda azababben gudun da yakeyi ya wuce nasu.Adaidai wannan lokaci ne Sulaira ta fafi kasa.Kafin Garzub ya sunkuya ya tasheta tsaye tuni Sharkas ya dako tsalle ya dira a gabansa.Kawai sai yasa kafa ya naushi Garzub a kirji.Tamkar ya daki tamoka haka Garzub yai sama ya fado kasa a galabaice,amma saboda naci da juriya irin ta mazajen kwarai sai sarki Garzub ya mike tsaye zumbur yayi sauri ya zare wadansu tsofaffun Adduna guda biyu dake jikinsa suka fara kallon kallo suna zagaye juna.Ita kuwa Sulaira sai ta koma gefe daya kawai ta zuba musu idanu jikinta nata kyarma saboda tsoro.Sharkas ya dubi sarki Garzub cikin kallon raini sannan ya budi baki cikin harshen larabci yace yakai wannan sarki mai taurin kai kayi sani cewa baka isa ka gujewa balai na ba.Ina tabbatar maka da cewa kafin gari yayi duhu mayakan sun gama karkashe gaba dayan mayakanka.Kai kuma yanzu zanyi maka kisan gilla a gaban wannan Kyakkyawar yarinya irinka BAKAR FATA sannan itama nayi mata fyade na kasheta kamar yadda na kashe ubanta.Daga nan bazan tsaya a ko ina ba nida dakaruna sai a cikin birninka na Hirtoliya.Da zuwa zmuje mu baje birnin gaba daya mu kame jama'arka a matsayin bayinmu sannan mu kwashe dukiyoyinmu kuma mu tona kasa mu debe albarkatun cikinta wadanda aka kabarta mana.Lokacin da Sharkas yazo nan a zancensa sai yaga sarki Garzub yana duru duru alamar cewa baya jin yarensa.Kwatsam!Ba zato ba tsammani sai sukaji Sulaira ta fara fassara bayanin da Sharkas yayi a cikin nasu yaren na bakaken fata.Koda Sarki Garzub yaji jawabin sai zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone kawai saiya ruga izuwa 8 hours ago kan Sharkas suka ruguntsume da azababben yaki suna masu kaiwa juna SARA DA SUKA cikin tsananin ZAFIN NAMA,juriya da bajinta.Bisa mamaki sai Sharkas yaga takobinsa ta kasa lalata addunan Garzub.Nan take ya gane cewa suma addunan tsafi ne.Duk da cewa Garzub yana matukar kokari wajen kaiwa Sharkas hari gami da kare nasa harin amma yaji a cikinsa cewa ruwa ba sa'an kwando bane domin Sharkas ya fishi zafin nama nesa ba kusa ba kuma karfin saransa ya ninka nasa sau uku.A duk sa'adda Sharkas ya kawowa Garzub sara ya kare sai yaji kamar zai fadi saboda karfin saran.In badon Garzub ya kasance mai tsananin juriya ba da naci da tuni Sharkas yayi masa kisan farat daya.Lokacin da aka sami rabin sa'a ana wannan gumurzu tsakanin Sharkas da Garzub ya zamana cewa babu wanda ya sami nasarar komai sai Sharkas ya fusata ainun ya sauya salon yaki ya zamana cewa ya hada da kaiwa Garzub NAUSHI DA BUGU da hannu da kafa.Da yake yana da matukar zafin nama sai kawai ya shammaci Garzub ya gabza masa wawan naushi a kumatu.Saboda karfin naushin saida wani gudan jini yayi fitar burgu daga cikin bakin Garzub ya kife kasa rub da ciki.Kafin ya yunkura ya tashi Sharkas ya soka masa takobi a bayan kafadarsa.Garzub da Sulaira suka tsandara ihu a lokaci guda.Shidai Garzub ihun da yayi na tsananin jin zafi da zogi ne.Ita kuwa Sulaira ihu ne na firgita bisa ganin an sami lagon wanda ke kokarin kare rayuwarta.Sarki Garzub ya sake mirginawa kasa a matukar galabaice lokacin da jini ke bulbula a kafadarsa.Sharkas ya tsaya a kansa yana kyalkyala dariyar mugunta.Duk da cewa idanun Garzub sun fara lumshewa yana gani dishi dishi sai ya tuno da bakin jawabin da Sharkas yayi dazu wanda Sulaira ta fassara masa.Nan take ya yunkura da dukkan karfinsa ya mike zumbur suka cigaba da fafatawa.Ai kuwa suna farawa ne Sharkas ya sami nasarar sake cakawa Garzub takobi a gefen kirji.Take takobin ta lume a cikin kirjin ta faso ta gadon baya.Sharkas na zare takobin jini yai tsartuwa.Saida Garzub yayi katantanwa a tsaye sau uku ya tafi kasa luu!Zai fadi amma saboda tsananin juriya saiya daka tsalle sama kamar sufurin ya zabgawa Sharkas naushi a fuska iya karfinsa.Saboda mugun zogin da Sharkas yaji bai san sa'adda ya saki takobinsa ta fadi kasa ba kuma yayi taga taga da baya kamar zai fadi,amma da yake giwa ba wasa bace saiya mike zumbur ya cafi wuyan sarki Garzub ya rinka jera masa naushi a ciki kamar ana doka tabarya a cikin turmi.Nan da nan ya lugui-guitashi,Garzub ya zamo tamkar tsumma.Sharkas ya warbar dashi a kasa tamkar yayi jifa da gawa.Kawai sai ya juya izuwa inda takobinsa ta fadi da niyyar ya daukota ya gididdiba Garzub.Har ya sunkuya yakai hannu zai dauko takobin sai idanun Garzub suka bude ya hango abinda ke shirin faruwa.Daga kwancen Garzub ya dafa kasa da hannayensa biyu kawai yayi tsalle tamkar an cillashi daga cikin kwari ya fada kan Sharkas suka kife kasa tare suka rukunkume juna da kokawa gami da naushi suna murgin murgin.Ai kuwa basu ankara ba suka tsinci kansu a sama wani tsauni mai matukar tsawo.A firgice Sulaira ta bisu da gudu izuwa kan tsaunin amma kafin ta riske su sun sallamo kasa izuwa kasan tsaunin dukkaninsu suna masu tsandara ihu domin sunsan cewa dukkaninsu karshen su yazo.Ai kuwa suna fadowa kasan tsaunin sai kowannensu kansa ya bugu da dutse duk suka sume,amma sai ruwa ya tafi da Sharkas,shi kuwa Sarki Garzub sai wani dutse ya tokareshi.Yayin da Sulaira ta leko kasan tsaunin ta hango Garzub a baje kamar gawa sai ta jua da baya da gudu ta gangaro izuwa kasan tsaunin tayi kundunbala ta daka tsalle ta fada cikin kogin ta kama iyo har ta isa inda sarki Garzub yake.Da kyar da sidin goshi ta janyoshi daga cikin kogin izuwa gaba.Koda ta kara hancinta daidai nasa sai taji yana numfashi kadan kadan,amma data dubi mugun raunin dake kirjinsa da bayansa sai ta karaya ta fara tunanin abune mayuwaci ya rayu.Har izuwa wannan lokaci tana iya jiyo ihun mazaje daga inda suke a can inda aka wannan bakin yaki kuma a sannan ne gari ya fara yin duhu.Sulaira ta dubi Garzub taga kato ne ba zata iya daukarsa ba kawai sai ta kama jansa a kas tayi ta jansa har saida tayi nesa da wannan kogi ta kaishi har cikin wani kogon dutse mai zurfin gaske.A sannan ne ta juyo an buga gangar tsaida Yaki.Kamar daukewar ruwan sama haka ta daina jiyo karar MAKAMAN YAKI da ihun mazaje.Nan take Sulaira tayi tsafi sai kofar wannan kogon dutse ta rufe ruf da dutse tamkar babu wata kofa data taba wanzuwa a jikinta.Ta sake yin tsafi ta kunna wuta a jikin itatuwa kogon ya haskake da haske.A sannan ne ta bude jakarta ta guzuri ta debo garin magani ta rinka cusawa a cikin ramin raunikan Garzub har saida ta cike ramukan jini ya daina zuba.Har izuwa wannan lokaci numfashin Garzub baya fita daidai akwai lokacin ma da numfashin ya dauke gaba daya tayi zaton ya mutu sai daga can kuma numfashin ya dawo.Cikin matukar farin ciki ta cigaba da sa masa magani a kansa inda ya sami rauni lokacin da suka rikito kasa shida Sharkas daga kan tsauni.Bayan Sulaira ta gama sawa Garzub magani sai ta sake bude jakar guzurinta ta dauko wani abinci ta ci ta koshi ta daga salkar ruwanta wacce ke cike fal ta kwankwada.Gama shan ruwan keda wuya sai ta bingire ta kama bacci saboda tsananin gajiya.Wannan shine abinda ya faru tsakanin Sarki Garzub da sadauki Sharkas bayan sunyi bakin gumurzu har Sulaira ta ceci rayuwar Sarki Garzub. *** *** *** A can filin yaki kuwa ana buga gangar tsaida yaki sai kowanne bangare suka ja da baya.A sannnan ne aka lura da irin mummunar barnar da akayi.A bangaren bakaken fata kuwa,wato dakarun sarki Garzub an kashe sama da mutum miliyan ashirin,wato wadanda sukayi saura basu kai miliyan goma ba.A bangaren fararen fata kuwa wato labarawa Dakarun Sharkas mutanen da aka kashe sun kai miliyan goma sha biyar,wato suma wadanda suka rage basu fi miliyan ashirin da biyar ba.Nan take kowanne bangare suka kwashe gawarwakinsu kuma aka baiwa juna tazara mi yawa sannan aka kafa tantuna.Har sai bayan an gama binne gawarwaki sannan kowannen bangare suka fahimco cewa basu ga shugaban su ba,wato larabawa basu ga Sharkas ba,suma bakaken fata basuga sarki Garzub ba.Nan fa hankalin kowanne bangare ya DUGUNZUMA aka fara shawarwari akan a tafi neman shugabannin.Amma kuma da aka fahimci yin hakan yana da matukar hadari tunda gari yayi duhu kuma yakin zai dade kaurewa ayi tayinsa ba tare da an fahimci inda aka dosa ba sai kowanne bangare suka hakura da batun tafiya neman shugabansu har sai gari ya waye ido na ganin ido. *** *** *** A can cikin kogon dutse kuwa tunda Sulaira ta bingire ta kama barci bata farka ba sai da dare ya raba.Tarin Sarki Garzub ne ya tasheta yana mai ambatin ruwa.A firgice Sulaira ta farka,koda taji Garzub na ambaton ruwa sai ta ruga da gudu ta dauki salkar ruwanta tasa masa a baki yayi kurba uku da kyar sai tari ya sake turnukeshi.Al'amarin daya dugunzuma hankalin Sulaira kenan ta fara kokarin ciccibar kafadunsa domin ta tayar dashi zaune amma sai taji yayi kara saboda zafin da raunikan jikinsa sukayi masa.Cikin sauri Sulaira ta mayar dashi kwancen a lokacin da idanunsa ke lumshewa.A sannan ne tayi tunanin cewa Garzub na bukatar abinci.Amma inda matsalar take shine ba zai iya cin irin abincin guzurinta ba dole ne ta samo masa abu mai ruwa musamman ma madarar shanu.Koda gama aiyana hakan sai Sulaira ta tuno da dubunnan shanunsa da ragunansu da tumakansu wadanda aka kadasu cikin daji sa'adda aka hango dakarun Sharkas sun kawo harin Sumame.Nan take Sulaira ta mike ta nufi bakin kofar kogon ta shafeta da hannu sai kofar ta sake budewa ta fice.Tana fita ta sake yin tsafi kofar ta sake shafewa.Cikin sanda Sulaira ta nausa cikin dajin tana hange hange da waige waige cikin alamun tsoro.Haka dai ta cigaba da tafiyar har ta hango inda rundunar mayakan biyu suka kafa sansanisu suna makotaka da juna.Sulaira ta ratsewa hanyar da zata kaita izuwa inda sansanin rundunonin biyu suke ta falfala da gudun tsiya izuwa wata hanya daban wacce dabbobinsu suka bi tana gudu tana duba sawun dabbobin nasu.Saida Sulaira ta shafe sa'a uku cur tana gudu a cikin daji ko alamun dabbobin nasu bata gani ba,a sannan ne kuma taji ta gaji likis yayi data iso gaban wani katon dutsw mai tsawon gaske da madaidaicin fadi.Sulaira ta fadi gaban dutsen tana haki cikin alamun karayar zuciya.A wannan lokaci ne ta tuno da mahaifinta Atiyar da sauran zuri'arsu.Kawai saita fashe da matsanancin kuka tana mai aiyanawa a ranta cewa menene amfanin rayuwarta a duniya tunda bata da kowa.Nan take Sulaira ta zare wannan sharbebiyar wuka tata ta daga sama zata kirba a cikinta sai ta tuno da batun sarki Garzub wanda ta kaishi can cikin kogon dutse ta barshi a cikin mayuwacin hali wanda rayuwarsa ke tsakanin RAI DA MUTUWA.Nan fa Sulaira taji bai kamata ace ta kashe kanta ba ayanzu,zaifi kyau ta koma kogon dutse tayi iya kokarinta wajen ceto rayuwar Garzub.Ita kanta Sulaira sai ta cika da mamaki bisa dalilin da yasa ta damu da rayuwar Garzub alhalin ta rasa ma mahaifinta.Wata zuciyar sai tace da ita ai dole ne ki ceci rayuwar Sarki Garzub domin inba don shi ba da tuni yanzu an miki fyade kuma anyi miki KISAN GILLAH.Ashe kuwa dole ne kiyi masa halacci kuamar yadda ya siyar da rayuwarsa ya tari sadauki Sharkas don kubutar da taki.Lokacin da Sulaira tazo nan a zancenta sai tamike tsaye da nufin ta koma da baya.Ba zato ba tsammani sai kawai ta jiyo kukan shanu a bayan wannan katon dutse da take.Cikin sauri ta ruga izuwa bayan dutsen ai kuwa sai tayi atba da dukkanin dabbobinsu a bakin wata katuwar korama suna ciki ciyawa da shan ruwa.Saboda farin ciki Sulaira batasan sa'adda ta bushe da dariya ba.Duk da cewa dare ya raba a wannan lokaci kuma duhu yayi amma akwai hasken sararin samaniya kadan don haka sai Sulaira ta ruga izuwa inda dabbobin suke.Wani abin mamaki daya faru shine dabba daya bata gudu ba daga wajen har Sulaira ta karaso cikinsu ta tsaya tana dube dube tana neman wata farar saniyar mahaifinta wacce tayi matukar sabo da ita.Kawai sai Sulaira taji an dungureta ta baya,a tsorace ta waiga da sauri sai taga ashe wannan farar saniya ce.Cikin matukar farin ciki Sulaira ta rungume saniyar ta fashe da kuka.Tsawon yan dakiku Sulaira na rungume da saniyar tana kuka.Daga can sai ta shiga karkashin saniyar ta fara tatso nononta tana zubawa cikin battar ruwanta har saida ta cika battar sannan ta mike tsaye ta juya da baya domin tabar wajen.Ai kuwa sai taga wannan saniya ta biyota a baya.Sulaira ta kora saniyar baya domin ta daina binta amma taki.Abinda ya daurewa Sulaira kai kenan musamman dataga cewa gaba dayan sauran dabbobin babu wanda ya biyota sai wannan farar saniya.Tun Sulaira na dada cigaba da korar saniyar har ta gaji ta kyaleta suka jera tare sukayi tafiya a cikin dajin ya zamana cewa Sulaira ta kama wata karamar igiyar dake wuyan saniyar ta cigaba da janta suna tafiya.Duk wannan tafiya da sukeyi Sulaira a tsorace

Chapter 2 of 7