Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
yai tsartuwa daga cikin raunin.Sharkas ya zaro wukar ya sake daba masa ita a saman kirjinsa bangaren hagu.Garzub ya sake rusa ihu,shi kuwa Sharkas saiya bushe da dariyar mugunta ya dada zare wukar ya soka masa ita a saman kirjinsa bangaren dama a karo na uku.Nan take Garzub ya sume ya zama kamar gawa.A wannan lokaci Dakarun Sharkas na ta ragargazar dakarun Garzub tamkar suna sassabe a gona.Komai rashin tausayin mutum idan yaga irin kisan gillar da akeyi musu dole ne hankalinsa ya DUGUNZUMA.Sharkas ya tsaya akan Garzub har saida yaga ya farfado daga suman da yayi kawai sai ya sunkuyo da nufin yayi masa yankan rago.Ba zato ba tsammani sai yaga Garzub ya mirgina ta karkashin kafafunsa izuwa bayansa.Kafin Sharkas ya juya Garzub ya daka tsalle tamkar dan biri ya dira akan wuyansa kuma ya caka masa yan yatsunsa a cikin idanunsa.Take kwayar idanun Sharkas suka fashe jini ya kwararo daga ciki Sharkas ya fadi kasa yana birgima da kururuwa wacce ta cika dodon kunnen kowa a wajen tasa aka daina yakin akayi cirko cirko ana kallonsa.Kawai sai Garzub yazo kansa ya tsaya yasa takobinsa ya sare hannun Sharkas na dama hannun ya fice fit yai tsalle gefe daya.Sharkas ya kwarara uban ihu wanda yafi wanda yayi da farko a lokacin da jini ke malala daga cikin dungulmin hannun nasa.Koda ganin haka sai Sarki Garzub ya dubi Sarkin Yakinsa Zamud wanda ke tsaye daf dashi yana layi saboda jinin dake zuba a jikinsa sakamakon yawan raunika ya daka masa tsawa yace maza ka daure dungulmin hannun Sharkas ka tsaida jinin dake zuba don bana son ya mutu.Cikin sauri sarkin Yaki Zamud ya kwabe rigar jikinsa ya cika wannan umarni.A wannan lokaci shima Garzub layi yake kamar zai fadi kasa domin jini ne keta zuba daga cikin wadannan raunika nasa guda uku wadanda Sharkas yayi masa.Garzub ya nufi kan Sharkas yana tangadi kamar wanda yasha giya ya bugu sannan yasa kafa ya take kirjinsa ya dubeshi a lokacin da idanunsa ke rufeqa da budewa da kyar yace yakai Sharkas wakilin sarki Madarus ka koma izuwa kasarka ka gayawa sarkinku cewa ka kasa idda aikin daya turoka domin ka kamu da gamonka.Idan har yanason burinsa ya cika to yazo da kansa ya cika wannan aiki.Ina sauraron isowarsa a ko yaushe.Ka sani cewa kai taka ta kare domin na gama da rayuwarka,tunda na maishe dakai makaho kuma musaki,baka da idanu kuma naka da hannu guda.Ina mai matukar farin ciki da sa'a ta fado a kaina ka kasa idda mugun nufinka a kaina da matata.Gama fadin hakan keda wuya sai Garzub yaji Sharkas ya bushe da mahaukaciyar dariya.Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan a filin dagar.Daga can sai Sharkas ya hade fuska yace yakai wannan sarki mai taurin kai kayi sani cewa inda kasan irin sadaukantakar sarki da karfin mayakansa da bakayi wannan furuci ba.Tabbas zaka san cewa ka tsokano GUGUWAR ANNOBA wacce bata da magani,kuma ka shafawa sauran dukkanin kasashen dake makoftaka da kai kashin kaji.Ina tabbatar maka da cewa da zuwan sarkina wannan nahiya taku gwara a saukar da muguwar Annobar gobara daga sararin samaniya da kuma kasan kogi ta babbake ku gaba daya..Kafin Sharkas ya gama rufe bakinsa sai Garzub ya naushi fuskarsa da kafarsa ya baje kasa sumamme.Sannan Garzub ya juya ya nufi cikin dandazon mayakansa yana tafe jiri na dibarsa har zai fadi kenan akayi sauri aka rirrikeshi aka tafi dashi izuwa cikin tantinsa.Su kuwa jama'ar Sharkas sai sukayi sauri suka daukeshi suka shiga yi masa magani.Kafin cikar sa'a guda jama'ar Sharkas sun gama hada nasu inasu sun bar dajin gaba daya.Al'amarin sarki Garzub kuwa kafi a shigar dashi cikin tantinsa tuni ya suma,don haka cikin gaggawa shima likitan ya kama aiki akansa.Har likitan ya gama aikinsa Garzub bai farfado ba sai bayan sa'a uku.Yana bude idanunsa yaga Sulaira zaune a gabansa ta kura masa idanu tana zubar da hawayen farin ciki.Da kyar Garzub ya yiwa Sulaira guntun murmushi saboda tsananin zogi da radadin da yakeji a jikinsa.Saida suka shafe wata tara cif ana jinyar sarki Garzub a cikin wannan daji da akayi wannan bakin gumurzun yaki sannan ya warke.A ranar daya warke ne ya gamu da mummunan bakin ciki a rayuwarsa wanda bazai taba mantawa dashi domin a ranar ne matarsa Sulaira ta mutu sa'adda take nakudar haihuwa ta haifi santalelen jariri mai tsananin kyawun gaske.Saboda tsananin bakin ciki bisa ganin Sulaira ta mutu saida Sarki Garzub ya zamo kamar mahaukaci domin ihu yayi tayi da kuka DARE DA RANA.Sarki Garzub bai baro wannan daji ba da akayi yakin saida ya kara kwana arba'in kullum yana yini a gaban kabarin Sulaira yana kuka da begenta cikin rera wakoki masu baitoci na ban tausayi wadanda duk mahalukin dayaji su sai ya zub da hawaye.Bayan cikar kwana arba'in din ne su sarkin yaki suka lallameshi aka bar dajin aka nufin birnin Hirtoliya.Tunda aka fara tafiyar Sarki Garzub na rungume da jaririnsa baya rabuwa dashi face idan za'a shayar da jaririn madara,kuma da wannan farar Saniya ta Sulaira aka tafi ana tatsar nononta ana shayar da jaririn har aka iso birinin Hirtoliya.Duk sa'adda sarki Garzub ya dubi jaririnsa saiya tuno da Sulaira ya fashe da kukan bakin ciki.Wannan shine asalin tarihin rayuwar sarki Garzub da yadda yayi aure har ya sami dansa guda daya jal ya zauna a cikin shirin ko ta kwana yayi ta zuba ido yana sauraron martanin sarki Madarus na birnin Darul Nusur,amma har tsawon shekaru ashirin da 'ya'ya baiga komai ba kuma bai sami sakon komai ba.Lokacin da sarki Garzub ya gama tunanin wanann al'amari daya faru shekaru ashirin da biyar da suka gabata sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya fashe da kuka.Yana cikin wannan hali ne yaji an turo kofar turakarsa.Cikin sauri ya dago kai sai yaga ashe yarima Uzaima ne ya shigo idanunsa sunyi sharkaf da hawaye.Al'amarin dayai matukar baiwa sarki Garzub mamaki kenan ya mike tsaye ya tari Yarima Uzaima yana mai rike kafadunsa yace yakai dana ina dalilin zubar wannan hawaye a idanunka? Koda jin wannan batu sai Yarima Uzaima ya risina a gareshi yace yakai Abbana kayi sani cewa ba komai ne ya sani zubar da wannan hawaye ba face nayi nadama bisa bata maka rai da nayi a baya domin ka bukaceni da nayi aure amma naki.A dalilin haka ne na kamu da tsananin bakin ciki har ka daina zaman fada na tsawon yan kwanaki kuma kullum ka rinka kulle kanka a cikin turakarka kana kuka.Ina fatan zaka gafarta mini wannan laifi da nayi maka kuma ina tabbatar maka da cewa yanzu a shirye nake da nabi dukkanin umarninka don ganin farin cikinka.Sa'adda Sarki Garzub yaji wannan batu daga bakin Yarima Uzaima sai ya cika da tsananin mamaki gami da farin ciki sannan ya rungume Uzaima yana murna.Jima kadan saiya janye jikinsa daga cikin na Uzaima suka fuskanci juna,Sarki Garzub ya dubeshi yace yakai dana inason ka fada mini iyakar gaskiya,kai kuwa mene ne yasa kayi nadama bisa wannan ra'ayi nawa daka bijire masa?Dajin haka sai Uzaima yasa hannu ya share hawayen dake zuba a idanunsa yace ba wani abu bane yasa nayi wannan nadama ba face a jiya da daddare sarkin yaki Zamud ya bani labarin yadda akayi ka hadu da mahaifiya har kukayi aure aka haifeni bayan kun fafata gagarumin yaki da mutanen Kasar darul Nusur sa'adda kayi jarumtakar da baka taba yin kamarta Ba.Yakai Abbana me yasa ka boye mini wannan labari tuntuni?Na rantse da darajar kaunar da kake yiwa mahaifiyata inda nasan da wannan labari da tun farko bazan taba bijirewa umarninka ba na son nayi aure.Koda sarki Garzub yaji wannan batu sai ya sake rungume Yarima Uzaima a kirjinsa ya fashe da kukan farin ciki.Kashe gari da sassafe sarki Garzub ya tashi manzo ya aikeshi izuwa wata kasa da ake kira Karyabu inda sarki Rakalu ke mulki.Sarki Rakalu aminin sarki Garzub ne kuma yanada wata kyakkyawar 'ya wacce babu kamarta a gaba dayan nahiyar,ana kiranta da suna Gimbiya Izaima.Sakon da sarki Garzub ya aikawa sarki Rakalu shine ya hanzarta ya taho birnin Hirtoliya a gobe tare da yarsa Izaima domin ayi baikon 'yarsa Gimbiya Izaima da yarima Uzaima.Tsakanin Birnin Hirtoliya da birnin Karyabu tafiyace ta kwana uku kacal.Lokacin da manzon sarki Garzub ya isa fadar sarki Rakalu ya isar da sakon sia sarki Rakalu ya cika da tsananin farin ciki mara misaltuwa.Ita kuwa gimbiya Izaima sai da tafi mahaifin nata ma farin ciki ta rinka tsalle da rawa domin ta dade tana begen yarima Uzaima a zuciyarta kuma babu abinda batayi ba domin ta sami soyayyarsa amma bata samu ba.Duk sa'adda Gimbiya Izaima takai ziyara birnin Hirtoliya sai ta bukaci ta gana da yarima Uzaima ko sau day bai taba yarda sun kebe ba bare suyi hira.Kai tun Gimbiya Izaima tana yarinya karama mahaifiyarta ke zuwa da ita gidan sarki Garzub kuma tun a sannan ne tahi tana son yarima Uzaima amma ko magana bai taba yi mata ba,idan ma tazo kusa dashi saiya tashi ya ruga da gudu ya bata wuri.Har suka girma akan haka al'amuran ke tafiya.Gimbiya Izaima tayi kuka sau ba adadi akan yarima Uzaima saboda tsananin son da take masa yana wulakantata.Shi kansa Yarima Uzaima saida takai cewa yana tausaya mata amma a zahiri bai taba nuna mata yana tausayin nata ba.Cikin gaggawa Sarki Rakalu yasa aka shirya masa tafiya izuwa birnin Hirtoliya tare da 'yarsa Gimbiya Izaima ya debi dukiya nai yawa gami da makada da mawaka,dakaru dubi dari uku sukayi masa rakiya.A cikin kwana uku daidai kuwa suka isa birnin Hirtoliya.Tun kafin su shigo cikin garin labari ya riski sarki Garzub yayi hawa da kansa yazo ya tarbesu cikin farin ciki suka dunguma gaba daya izuwa gidan sarautar.Abinda ya baiwa Gimbiya Izaima mamaki shine yarima Uzaima bai biyo sarki taryarsu ba amma sai ta aiyana aranta cewa wani uzuri ne ya hanashi zuwa.Har su Izaima suka isa gidan Sarautar aka kaisu masaukinsu bataga Yarima Uzaima ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalinta kenan taji babu abinda takeso sama da ganinsa.A wannan lokaci da suka iso birnin Magriba tayi don haka sai sarki Garzub ya gaya musu cewa su bari sai gobe da safe ayi wannan shagalin biki na baikon Yarima da Gimbiya.Domin har a sannan ma bakin da ka gaiyato basu gama zuwa ba.Har dare ya raba gimbiya Izaima bata sami sukuni ba kuma sau bakwai tana aikawa ayi mata iso wajen yarima Uzaima amma duk sa'adda akaje sai a tarar yarima Uzaima baya nan yana can turakar mahaifinsa suna ganawa.Haka dai Izaima ta hakura ba don taso ba taje ta kwanta amma sai bacci ya gagara saboda Farin ciki da dokin ganin gari ya waye anyi baikonta da Yarima Uzaima.Ai kuwa tunda duku dukun safiya Izaima ta tashi tayi wanka ta kure adaka.Sa'adda ta tsaya a gaban madubi tana ado saida ta bata sa'a biyu tana kwalliyar.Duk abinda tayi sai taga baiyi mata kyau ba sai ta sakeyin wani. Al'amarin Yarima Uzaima kuwa ko kadan baya farin ciki da zuwan wannan rana domin a rayuwarsa bai taba ganin wata 'ya mace data burgeshi ba bare har yaji yana son ya aureta.Yanzu ma ya amince ayi masa baiko da gimbiya Izaima ne don kawai ya farantawa mahaifinsa rai kuma ya kwantar masa da hankali ya daina yawan kuka da begen matarsa marigayiya Sulaira.Lokacin da fadar sarki Garzub ta cika da batse da manayn baki da sauran jama'ar gari sai makada da mawaka suka fara aikinsu ya zamana cewa fadar ta cika da hayaniya anata shagali.Jim kadan saiga sarki Garzub da Sarki Rakalu sun fito daga cikin gidan sarautar suna rike da hannun juna suna tafe suna ta hira cikin nishadi da farin ciki,Gimbiya Izaima na biye dasu a baya.Kai tsaye suka nufi inda karagar sarki take suka zauna,nanfa Izaima ta kama hange hange da waige waige domin taga Ta inda Yarima Uzaima zai fito.Ai kuwa jim kadan da zamansu sai ga Yarima Uzaima ya shigo fadar yana sanye da tufafi koraye masu tsananin kyau irin na sarakai.Abinka da mai kyau kuma ya sanya mai kyau sai gashi Uzaima ya zamo tauraro mafi haske a cikin taurari wato ya fita daban a cikin dukkanin samarin dake cikin fadar sai haske yake da kyalkyali.Mata kuwa basu san sa'adda suka wangame baki ba suna kallonsa kawai kamar su ruga su daukeshi.Cikin murmushi Yarima Uzaima ya nufi inda gimbiya Izaima take zaune.Koda ta hangoshi ya nufota saita cika da tsananin murna ta kasa nutsuwa ta rinka muskuce muskuce jikinta nata tsuma.Koda Uzaima yazo daf daita sai ya kama hannunta ya sumbaceshi yace lale marhaban da ABOKIYAR RAYUWATA.Koda jin wannan batu sai hawayen farin ciki ya subutowa Izaima bata san sa'adda ta sumbaci goshin Uzaima ba tayi masa rada a kunne tana mai cewa lale marhaban da rabin jikina abin begena dare da rana.Uzaima yayi murmushi baice komai ba sannan ya zauna a kusa da ita suka fuskanci tsakiyar fadar inda wadansu yan mata su goma sha biyu keta faman tika rawa sunyi wata shiga irin ta siffar dawisu mai ban sha'awa suna debewa kowa kewa a fadar.Saida masu rawar suka shafe rabin sa'a sunata aikinsu sannan aka sallamesu suka fice daga tsakiyar fadar.A wannan lokaci ne sarki Garzub ya mike tsaye cikin farin ciki yayi jawabin barka da zuwa ga manyan baki kuma yayi bayanin dalilin wannan gagarumin taro da aka shirya.Bayan ya gama wannan jawabi ne aka kirawo Gimbiya Izaima da Yarima Uzaima domin yi musu baiko.Lokaci guda duk su biyun suka taso daga inda suke zaune suka nufi tsakiyar fadar.Nan take fadar ta rude da shewa da tafin jama'a.Bisa al'adar mutanen birnin Hirtoliya inda akayiwa mace da namiji baiko to har abada dayansu bai isa yayi aure ba da wani daban idan dayansu ne ya mutu.Yanayin yadda akeyin baikon shine za'a zuba zuma ne da madara a cikin kasko sai masoyan su sa cokali su rinka diba suna sha har sai zumar da madarar sun kare sannan sai a fasa wannan kasko.Nan take aka kawo wannan kasko wanda ke cike da madara da zuma aka ajiye akan wani tebur dake tsakiyar fadar.Uzaima da Izaima sukazo suka tsaya agaban Kaskon suka sashi a tsakiya suna masu fuskantar juna.Ba tare da bata lokaci ba aka kawo musu cokali na duma suka fara diban wannan madara da zuma ta cikin kaskon suna sha.Sannu a hankali suka kusan shanye madarar ya zamana cewa saura baifi cokali uku ba.Kwatsam sai ga wani bafade wanda ya kasance daya daga cikin dakarun da suka kewaye bayan gari don tabbatar da tsaro ya shigo cikin fadar a guje yana haki rike da wata wasika a hannunsa.Da zuwansa gaban karagar sarki saiya zube kasa ya kwashi gaisuwa ya mika wannan wasika ga sarkin yaki Zamud.A wannan lokaci gaba dayan mutanen fadar sun kame kamar gumaka sun kasa kunne su ji sakon da aka zo dashi.Yarima Uzaima da Gimbiya Izaima ma sai suka tsaya ga barin cigaba da shan wannan madara.Cikin sauri sarkin yaki Zamud ya warware wannan wasika ya fara karantata a fili kamar haka:-Takarda daga hannun SARKIN SARAKAN duniya mai daraja ta daya wato sarki Madarus na birnin Darul Nusur.Zuwa ga makaskancin sarki Garzub na birnin Hirtoliya.Yakai wannan sarki kayi sani cewa TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Daya (1) Part G Ya kai wannan sarki kayi sani cewa ba'a ramuwa ranar gaba.Idan baka manta ba kimanin shekaru ashirin da biyar baya da suka shude na aiko sarkin yakina Sharkas ibini Tauwab domin yazo nahiyarku ku bashi bayi da dukiya mai yawa amma saika bijirewa umarninmu ka shirya mayaka ka fita ka kashe mana dakarunmu kuma ka maishe da sarkin yakina makaho kuma musaki.Kayi sani cewa a iya rayuwata duniya babu wanda ya taba yi mini irin wannan wulakanci dacin mutunci sai kai.Naso tun a wannan lokaci na fito da kaina nazo na rushe kasarka na kwashe komai naku amma danayi bincike a tsafina sai naga babu nasara a sannan dole sai bayan shekaru ashirin da biyar.Tofa!Yanz u lokaci ya cika daidai wato shekaru ashirin da biyar,yanzu haka maganar da nake maka saura kwanaki uku kacal na iso birninka tare da dakarun yaki guda miliyan Tamanin wato ninkin wadanda na turo a wancan karon.Ina mai sanar maka da cewa gaba dayan kasashen dana iske akan hanyata duk na cisu da yaki na sami fiye da adadin bayi da dukiyar da nake bukata.Zan karaso kasarka ne kawai saboda kawai nayi ramuwar gayya wacce tafi ta gayya ciwo.Na rantse da girman mulkina da daukakata ko beran birninka ba zan barshi da raiba,sai an kashe dukkanin mazajenku manya da kanana,yara da tsofaffi.Gava dayan matatenku saina kamasu a matsayin bayi bayan anyiwa dukkaninsu fyade.Duk wani abu na dukiyarku koda tsinke ne sai mu kwashe shi sannan mu bunkawa birnin naku wuta har sai komai ya kone ya zama toka.Ko ku shirya ku fito ku taremu ko kuma mu iso mu riskeku,Mune GUGUWAR ANNOBA kuma GOBARA DAGA KOGI wacce bata da magani!.Sa'adda sarkin Yaki Zamud ya gama karanta wannan wasika sai hankalin kowa ya dugunzuma a fadar masu kuka suka kama kuka,masu ihu suka kama ihu,masu gudu suka kama gudu.Nan da nan fadar ta yamutse,ita kuw la gimbiya Izaima saboda firgitar da tayi gami da bakin ciki domin tasan cewa har abada burinta ba zai cika ba.Cikin tsananin fishi sarki Garzub ya mike tsaye ya daka tsawa kowa ya shiga taitayinsa sannan ya dubi sarkin yaki Zamud yace aje a shirya mini sulken yakina ni da kaina zan jagoranci mayakanmu mu fita mu tari wadannan abokan gaba.Koda jin haka sai Zamud ya dubi sarki Garzub cikin matukar tsoro yace ya shugabana ka tuna da irin tsananin masifar da muka shiga a wancan karon da mukayi yaki da wadannan mutane.A sannan nefa da miliyan goma kacal suka fimu yawa.Yanzu kuwa ina tabbatar maka da cewa sun fimu yawa da adadin miliyan arba'in da biyar.Babu yadda za'ayi mu sami nasarar wannan yaki.Bugu da kari da da yanzu fa ba daya bane.Ni da kai yanzu duk girma ya fara kamamu.Jarumtakar da mukayi a da yanzu ko rabinta ba zamu iyayi ba.Tabbas ba zamu tsira ba a wannan yaki,gaba dayanmu sai mun hallaka.Kafin Zamud ya gama rufe bakinsa sai yarima Uzaima ya tari numfashinsa yace idan ku kun tsufa ai mu yanzu muke kan ganiyar kuruciyarmu kuma mun gaji komai naku.Uzaima ya dubi sarki Yace yakai Abbana kayi mini izini naje na jagoranci mayakanmu.Koda jin wannan batu sai sarki Garzub yayi murmushi yace da kyau 'dana tabbas yanzu nasan cewa banyi asarar komai ba duniya tunda na haifi kamata.Tabbas kai NAMIJIN DUNIYA ne wanda bai san tsoro ba.Hakika matsoraci bashi zama gwani kowane ne.Na yarda da jarumtakarka kuma nasan zuciyarka a dake take.Ka tafi da albarkacinmu data mai girma Larratu,nylayi maka izini ka jagoranci wannan yaki.Koda jin haka sai Yarima Uzaima ya juya ya fice daga cikin fadar.A wannan lokaci ne sarki Rakalu ya lura da halin da 'yarsa gimbiya Izaima ke ciki,wato ya ganta kwance a kas a sume sai ya rusa ihu ya kara firgicewa dama tuni ya rude bisa jin cewa sarki Madarus ya ratso ta cikin birninsa ya gama da birnin.Cikin gaggawa sarki Garzub ya bada umarni aka dauki gimbiya Izaima aka shigar da ita izuwa cikin gidan sarautar kuma aka ruga domin a kirawo likita ya dubata.Nanfa aka fara shirye shiryen yaki aka rinka fito da makamai,dawakai da guzuri.Kafin rana ta fadi tuni an gama shiri tsaf.Idan kowa yaga irin shigar da yarima Uzaima yayi ta yaki a wannan rana dole ne ya firgita dashi domin daka ganshi kaga mahaifinsa,bambancinsu kawai shine shi matashi ne mai ji da SAMARTAKA.Shi kuwa sarki Garzub ya fara manyanta domin shekarunsa sun haura hamsin.Lokacin da yarima Uzaima ya gama shirinsa tsaf ya fito filin fada inda miliyoyin dakarun yaki ke tsaye suna jiransa sai kawai yaga sarki Garzub,Sarki Rakalu da sarkin Yaki Zamud a cikin mayakan.Al'amarin dayai matukar bashi mamaki kenan ya dubi sarki Garzub cikin tsananin mamaki yace yakai Abbana saboda me kuka fito wannan yaki alhalin yanzu lokaci ne daya kamata ace kun zauna a gida kun huta bautar da kukayi a baya,in yaso mu mu wakilceku?Koda jin haka sai Sarki Garzub ya dubi Uzaima yayi murmushi sannan yace yakai dana kayi sani cewa wannan yaki da zaka fita ya wuce dukkanin tunaninka,kuma ina tabbatar maka da cewa ba'a taba yin gagarumin yaki irinsa ba duniya a baya kuma har anan gaba ma baza'ayi irinsa ba.Kai kadai ba zaka iya jagoranci ba.Basirarka,tunaninka da hangenka sunyi kadan dole ne ka bukaci gudunmawa irin tamu ta tsofaffin hannu.Tabbas wannan yaki da za'a fita ne na TSIRA KO HALAKA.Uzaima ya jinjina kai domin wannan bayani ya ratsa shi sosaimsannan ya dubi sarki Rakalu yace yakai sirikina kai kuma saboda me ka fito wannan yaki? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa sarki Rakalu yace yakai Yarima Uzaima kayi sani cewa a halin yanzu babu wani abu daya rage mini a duniya face 'yata gimbiya Izaima domin a halin yanzu nasan na rasa kasata,mulkina da jama'ata.Idan har . ban fita wannan yaki ba na taimaka maka an sami nasara ba,indai ka mutu tabbas 'yata zata kashe kanta domin a duniya babu abinda take so sama dakai.Ni kuma babu abinda nake so sama da ita.Indai ka hallaka a wannan yaki tabbas nima zan kashe kaina.Koda jin wannan batu sai hankalin Yarima Uzaima ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi a duniya.Cikin sanyin jiki ya zaburi dokinsa ya fita da gudu.Nan take kuwa su Sarki Garzub suka rufa masa baya suka nufi kofar fita daga birnin Hirtoliya gaba dayansu.Idan mutum yaga adadin dawakan wadannan mayaka da mahayansu wadanda suka kasance ZARATAN JARUMAI masu kamar zasu ci babu dole ne ya firgita. WANE IRIN AZABABBEN YAKI ZA'AYI IDAN RUNDUNAR SU SARKI GARZUB TA HADU DA RUNDUNAR SARKI MADARUS? KUMA WANE BANGARE NE ZASU SAMI NASARA? SHIN INA LABARIN SHARKAS WANDA SARKI GARZUB YA MAYAR MUSAKI KUMA MAKAHO? SHIN WANE IRIN AZABABBEN KARFIN DAMTSE DANA SIHIRI SARKI MADARUS YAKE DASHI? SHIN YARIMA UZAIMA ZAI DAWO GIDA A RAYE HAR YA AURI GIMBIYA IZAIMA? Mu Hadu TSIRA DA HALAKA littafi na Biyu don jin cigaban wannan kasaitaccen kayataccen labari. End Of Book 1. TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Biyu (2) Part A. LOKACIN DA UZAIMA ya jagoranci mayakan su gaba daya suka fice daga cikin birnin sai suka wanzu suna tafiya ba sassauci.Saida suka yini suna tafiya har rana ta fadi sannan Uzaima yaja linzamin dokinsa ya tsaya ya bayar da umarnin a yada zango.Nan take kuwa aka shiga kafa tantuna da kokarin dafa abinci.Wannan karon ma ba'a fita wannan yaki da mace ko guda daya ba kuma yarima Uzaima ne ya kaddamar da dokar hakan yayi koyi da mahafinsa bisa yadda yayi wancan yaki dasu Sadauki Sharkas wato shekaru ashirin da biyar baya da suka shude.Hadimai Hudu kadai sarki ya taho dasu,daga mai dafa masa abinci sai mai kula da shimfidarsa sai kuma shamakinsa sannan kuma liktansa daban.Bayan an kafa tantuna har an kawowa Uzaima abincinsa yana shirin fara ci kenan sai ga wani badakare ya shigo.Bakadaren ya zube kasa ya kwashi gaisuwa sannan ya shugabana sarki ne yace kaje ka sameshi a cikin tantinsa domin kuci abinci tare.Koda jin wannan batu sai yarima Uzaima ya cika da tsananin mamaki domin shi a rayuwarsa kuma a iya saninsa bai taba cin abinci ba tare da sarki ba,to menene dalilin da sarki keson cin abinci tare dashi a yau?Haka dai yarima Uzaima ya mike zumbur yabi wannan badakare suka fita tare.Da zuwansa kofar tantin sarki Garzub sai wannan badakare yaja gefe daya ya tsaya a kusa da yan uwansa dakaru wadanda suka yiwa tantin kawanya don tabbatar da tsaro.Dama sun riski shamakin sarki a tsaye a kofar tantin.Tun kafin su karaso bakin tantin shamaki ya shiga ciki yayi busharar zuwa yarima sannan ya fito.Kai tsaye yarima Uzaima ya kunna kai cikin tantin.Ai kuwa yana shiga yayi arba da mutum uku a zaune.Cikin tsananin mamaki da fishi Yarima Uzaima ya tsaya cak!Ya kura musu idanu kawai yaji kamar ya koma da baya.Ba komai ne ya haddasa hakan ba face Yarima yaga sarki tare da abokinsa sarki Rakalu da 'yarsa gimbiya Izaima.Cikin tsananin damuwa yarima Uzaima ya durkusa a gaban sarki Garzub yace yakai Abbana kai da bakinka ka gaya mini cewa mai girma Larratu ya goyi bayan dokar dana kafa cewar baza'a fito wannan yaki tare da mace ba koda guda daya.saboda me yanzu aka taho tare da gimbiya Izaima?Koda jin wannan batu sai sarki Garzub yayi murmushi kuma ya mike tsaye ya kama kafadun yarima Uzaima yace yakai dana hakika duk abinda ka fadi gaskiya ne amma ka sani cewa Izaima ba haifaffiyar birnin Hirtoliya bace dama dokar tana aikine akan macen data kasance haifaffiyar birninmu.Abu na biyu na yanke shawarar a taho da gimbiya Izaima ne domin idan muka barta a gida zata iya shiga wani mugun hali bisa tunani da fargabar halin da muke ciki gwara dai ace tana kusa damu.Ina tabbatar maka da cewa kasancewar Izaima tare damu bazai haifar da wata matsala ba facema karin guiwa.Akwai karin bayani idan mun kadaita ni da kai.Sa'adda Yarima Uzaima yaji wannan batu sai jikinsa yai sanyi bai kara cewa komai ba kawai saiya koma gefe daya ya zauna.Nan take gimbiya Izaima ta mike tsaye taje ta zubawa sarki Garzbu da sarki Rakalu abinci sannan ta zubawa Uzaima nasa daban taje ta ajiye a gabansa.Izaima taje ta debi nata abincin itama ta koma gefe daya ta zauna.Ba tare da bata lokaci ba duk su hudun suka kama cin abincin.Duk sa'adda Yarima Uzaima ya daga kai sai yaga ya hada idanu da gimbiya Izaima tana yi masa wani irin TATTAUSAN MURMUSHI.Ko kau da kai batayi kuma bata jin kunyar su sarki ma.Al'amarin dayai matukar baiwa Uzaima mamaki kenan a lokacin da kunya ta isheshi ya kasa sakewa yaci abincin sosai.Abinda Uzaima bai sani ba shine tsananin farin ciki ne ya jefa Izaima a cikin wannan hali saboda wannan ne karo na farko data taba samun dogon lokaci tare da Uzaima a iya rayuwarta dashi.Hakika idan mutum yayi zurfi a cikin son wani tofa baya ganin laifin wanda yake so din.Shekara da shekaru Izaima tasan cewa Yarima Uzaima bai damu da ita ba kuma bai taba nuna mata wata alama ba wacce ta nuna cewar yana sonta amma duk da haka bata taba damuwa ba.Abinda tayi imani dashi shine duk ranar data mallakaeshi ya zama mijinta to da sannu shima zai sota saboda tsabar kulawar da zata ta nuna masa da TSANTSAR SOYAYYA.Haka dai su Uzaima suka gama cin abinci har suka kare gaba daya.A sannan ne Yarima Uzaima ya mike yaje ya wanke hannunsa a cikin wata kwatarniya da aka tanada sannan ya dubi sarki ya nemi izinin tafiya.Sarki Garzub ya mike tsaye ya kama hannun yarima Uzaima ya jashi suka fice daga cikin tantin suka koma can gefe daya domin tattaunawa.A wannan lokaci dakaru da yawa sun yiwa sansanin KAWANYA don tabbatar da tsaro.Sarki Garzub ya dubi Uzaima yace yaka dana ka sani cewa in badon wannan yaki ya taso ba da tuni yanzu kai da Izaima kun zama MIJI DA MATA.Na sani cewa baka son Izaima amma yanzu zaka sota ne don kawai ka faranta mini rai.Lallai ka sota saboda ni don domin bani da wata bukata a wajenka wacce tafi hakan.Lallai nasan cewa zaka so Izaima anan gaba da sannu.Bani da tabbacin wannan buri nawa zai cika kafin ganin karshen wannan yaki tunda dole sai bayan yakin ne burin nawa zai cika wato ganin aurenka da Izaima.Yakai dana inason a yanzu kayi mini alkawarin cewar ko bayan raina zaka auri Izaima indai kai da ita kun rayu.Sa'adda Yarima Uzaima yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma,nan take idanunsa suka ciko da kwalla ya dubi Garzub yace yakai Abbana ka sani cewa ni mai ladabi ne da biyayya a gareka saboda haka babu yadda za'ayi na ketare umarninka har abada.Lallai na dauki wannan alkawari indai ina raye bayan wannan yaki kuma Izaima ta rayu lallai zan cika maka burinka.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarki Garzub ya rungume Uzaima cikin tsananin murna a lokacin da duk su biyun hawaye ke zuba a idanunsu saboda tunanin cewa abu ne mayuwaci duk su biyun su rayu a karshen wanna gagarumin yaki wanda basu san yadda karshensa zai kasance ba.A cikin tanti kuwa bayan sarki Garzub da Yarima Uzaima sun fita sai Izaima ta ruga da gudu izuwa wajen mahaifinta ta fada kan kirjinsa tana ta kyalkyala dariyar farin ciki.Cikin matukar mamaki Sarki Rakalu ya kama kafadun Izaima suka fuskanci juna yace yake yata ke kuwa menene dalilin wannan farin ciki naki haka?Izaima tace yakai Abbana kayi sani cewa hakika yanzu ne na fara ji a jikina cewar burina zai cika.Mafarkin dana dade ina faman yinsa dare da rana yana daf da tabbata gaskiya.Koda jin wannan batu sai sarki Rakalu yayi ajiyar zuciya sannan yace yake yata hakika abinda kika fada gaskiya ne in ba don wannan yaki daya taso ba bakatantan ai da tuni yanzu buri ya cika.Ina so ki sani cewa ban fito wannan yaki ba don kishin kasata ko jama'ata ba sai domin ke kadai.Ki tuna cewa a halin yanzu

Chapter 4 of 7