Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
take domin gani take a koyaushe zata iya ganin Sadauki Sharkas a gabanta.Haka dai Sulaira tacigaba da tafiya a cikin daren janye da wannan saniya a cikin dajin ta durfafi hanyar da zata TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Daya (1) Part D Inda takai sarki Garzub ta boye.Saida ta shafe sa'a uku da rabi tana tafiya sannan ta iso wannan kogo ba tare da ta hadu da wani mugun abu ba.Cikin murna Sulaira ta shafi kofar kogon ta bude sannan ta shiga cikon kogon janye da farar saniyar.Suna shiga kofar ta bace bat.Cikin gaggawa Sulaira ta sawa Sarki Garzub wannan batta a bakinsa wacce ke cike da madarar shanu.Bisa mamaki kuwa sai taga ya kama kwankwadar madarar yana shanyewa ashe idonsa biyu ba bacci yake ba.Saidai Garzub yasha madarar ya koshi sannan ya bude idanunsa da kyar ya dubi Sulaira yayi mata wani guntun murmushi a lokacin da yake ciza lebensa saboda tsananin zogi da radadin da yake ji.Gashi yana bude baki kamar zaiyi mata magana amma ya kasa.A wannan lokaci ne Sulaira ta lura da wadanan manyan raunika guda biyu dake jikin Garzub ta fahimci cewa a kalla sai yayi kwana goma sha biyu a kwance kafin ya iya ma tashi zaune.Al'amarin daya dugunzuma hankalinta kenan domin bata ga yadda zasu iyayin rayuwa ba a cikin wannan kogo ita dashi da kuma saniyarta alhalin babu ruwa a cikin kogon babu isasshen abincin guzuri.Ida kuwa tace zata rinka yawan fita daga cikin kogon abokan gaba zasu iya ganinta su gano inda ta boye Garzub su biyosu su hallakasu gaba daya.Nanfa Sulaira ta zauna tayi tagumi ta shiga tunani mai zurfi tana kallon yanayin cikin wannan kogon dutse wanda ke cike da ciyayi da kananan bishiyoyi.Tana cikin wannan tunanin wata dabara ta fado mata kawai sai ta mike tsaye ta zare wata gajeriyar adda a kuibin cinyarta ta hagu ya kama tonan kasa da ita.Bisa mamaki saiga ruwa ya fara bulbulowa.Cikin tsananin murna ta cigaba da kwakule kasar wajen ta samar da yar karamar rijiya wadd ta ciko da ruwa.Al'amarin da yai matukar bata mamaki kenan."Abinda bata sani ba shine wannan dutse da suke cikinsa a saman wata korama yake." **** *** ** A can Sansanin yaki kuwa lokacin da gari ya waye sai kowanne bangare sukayi shiri aka fito filin daga aka tsaitsaya tsawon rabin sa'a ana tsaitsaye amma an kasa cigaba da yaki saboda kowacce runduna babu mai bata umarni sai kallon kallo ake ana muzurai kamar aci babu.Daga can sai wani babban barde daga cikin larabawa ya fara baiyana yana mai cewa yaku abokan gaba kuyi sani cewa mu daku duk muna cikin tashin hankali bisa rashin ganin shuganninmu saboda haka ina mai shawartarmu da mu tsaida wannan yaki har izuwa tsawon kwana bakwai in yaso mu zabi mutum bakwai bakwai su bazama cikin wannan daji don neman inda shugabanninmu suke.Ma'ana mu mu tafi neman namu shugaban kuma ku tafi neman naku.Idan wakilan namu suka dawo ko an gansu ko ba'a gansu ba sai mu cigaba da yaki wadanda ke da sa'a a tsakaninmu sai su sami nasara.Lokacin da wannan barde ya gama wannan jawabi sai wani dan uwansa balarabe ya fassara jawabin nasa a cikin yaren mutanen sarki Garzub.Koda jama'ar Sarki Garzub sukaji wannan batu sai suka aminta da hakan.Nan take kowacce rundunata zabo mutum bakwai daga cikinta kuma akayi alkawarin cewar wadannan mutane goma sha hudu ba zasu yaki juna ba a cikin daji har suje su dawo kuma dayansu ba zai cutar da wani daga cikin abokan gaba ba koda za'a yi kicibus mugun gamo a cikin daji.Bayan an gama wannan alkawari ne dakarun guda goma sha biyu suka hau dawakansu suka nausa cikin daji.Masu wakiltar bakaken fata sukayi gabas,su kuma masu wakiltar larabawa sukayi yamma.Wannan shine abinda ya faru a tsakanin rundunar mayakan biyu a rana ta biyu bayan an fara wannan yaki. *** *** *** Al'amarin Sadauki Sharkas kuwa lokacin da suka fado daga kan tsaunin nan shida sarki Garzub izuwa cikin kogi har kawunansu suka gwaru da duwatsu suka suma a cikin kogin har ruwa ya tafi da Sharkas,sai igiyar ruwa ta cigaba da tafiya dashi tamkar an dora takarda akan ruwa.Saida yayi tafiyar sa'a biyu da rabi akan ruwan bai fardado ba.Lokacin da ruwan ya kawoshi saman wani dutse dabam mai tsananin zurfin gaske ne ya farfado.Yana bude idanunsa yaga zai rikito izuwa kasan dutse mai tsananin zurfi saiya kwala ihu,ihun nasa ya cika dajin gaba daya yana amsa kuwwa.Saida yai dakika dari da tamanin sannan ya iso karshen dutsen ai kuwa sai ya fado akan wata bishiya reshenta ya cakeshi a kuibin cikinsa ya bullotso ta gadon bayansa nan yake ya sake sumewa.Sadauki Sharkas bai farfado ba sai bayan rabin sa'a.Yana farfadowa yaga jini na zuba daga cikinsa,yana shafawa haka yaji ice a cikin cikinsa kawai sai ya kama icen ya fara zareshi yana kwala ihu.(Kaji maza masu juriya da tsananin jarumta).Ai kuwa yana gama zare icen ya sake sumewa a karo na uku.Jim kadan saiya farfado yaga har a sannan jini bai daina zuba ba daga cikinsa.Cikin matukar karfin hali ya cire rawanin kansa ya daure cikin nasa sannan ya fado daga kan bishiyar ya tumu da kasa yana numfashi sama sama.Duk da cewar ya daure raunin cikin nasa da rawaninsa amma sai yaga har yanzu jini bai daina zuba ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan ya tabbatar da cewa idan bai dinke wannan rauni ba lallai zai iya zama sanadin ajalinsa a koyaushe.Koda gama aiyana hakan sai sadauki Sharkas ya rinka jan ciki ya isa gaban wani dutse ya jingina bayansa akan dutsen sannan ya cire jakar guzurinsa daga kafadarsa ya budeta da kyar ya dauki allura da zare irin wanda ake dinke rauni dashi ya shiga yiwa kansa likitanci.Duk da cewa yana jin mugun zogi da radadi a duk sa'adda ya soka allurar a cikin fatar jikinsa yaje zare amma sai ya daure baiyi ihu ba ya rinka ciza lebe kawai.A haka dai ya samu ya gama dinke raunin dake kuibin cikinsa wanda ke can gadon bayansa ne ba bu damar ya dinkeshi dole sai garin magani ya debo ya cusa a cikin ramin raunin har ya cikashi.Saida Sharkas ya kwana uku a wannan wuri yana jinyar rauninsa sannan ya sami saukin daya iya mikewa tsaye da kyar amma sai tafiya ta gagara dole ya karyo reshen wata bishiya ya rukeshi a matsayin sanda ya rinka dogarashi.Yana tafe yana rike da cikinsa kamar zai fadi kasa amma saboda naci bai fasa yin tafiyar ba.Babu abinda ke cikin zuciyar Sharkas face ya lalubo inda Sarki Garzub da Sulaira suke domin ya hanzarta kashe su sannan ya koma sansanin yaki yaga abinda ya kwana.Shidai Sharkas bashi da wani buri a ransa wanda yafi ya sami nasarar cika aikin da aka turoshi izuwa wannan nahiya ta bakaken fata,wato ya tattaro bayi da dukiya adadin da sarki Madarus ke bukata.Da yke Sharkas mutum ne mai nutsuwa,kaifin tunani da hangen nesa sai ya aiyana a ransa cewa babu inda zaiga su sarki Garzub face a can baya domin ya gani cewa sa'adda suka fado kasan tsaunin nan lallai suma yayi kuma ruwane ya janyoshi ya kaishi inda ya tsinci kansa yanzu.Koda gama aiyana haka sai ya juya da baya ya cigaba da tafiya yana dogara sandarsa yana dingishi kamar ma bazai iya doguwar tafiya ba.Haka dai ya cigaba da tafiya har rana ta take ya gaji likis yaje karkashin wata bishiya ya zauna yana hutawa sannan ya bude jakar guzurinsa ya fiddo abinci yaci ya sake zuba garin magani akan ciwon dake gadon bayansa ya mike ya cigaba da tafiya.Saida Sharkas ya shafe kwana uku yana tafiya a cikin wannan daji bai ga su Sarki Garzub kuma bai hadu da wata halitta ba.Abinda yafi daga masa hankali shine duk nisan tafiyar da yayi bai jiyo sautin alamar cewa ana yaki ba a cikin daji kuma baiga ungulaye suna yawo a sama ba bare ya gane cewa anyi gumurzu an sami gawarwaki.Koda ganin haka sai Sharkas ya yanke hukuncin ya koma can inda sansanin yaki yake,kawai sai ya cigaba da tafiya yana dogara wannan sanda kamar nakasasshe.Yana cikin tafiyar ne kwatsam yayi gamo da wadannan dakaru guda bakwai dakarun kabilar bakaken fata.Yana ganinsu sai ya zare makami don ya yakesu amma sai yaga ko motsi basuyi ba bare suyi yunkurin yin yaki dashi.Kawai sai suka ratse hanya suka falfala da gudu izuwa wata nahiyar daban suka barshi nan a tsaye cikin tsananin takaici domin inda lafiyarsa kalau sai duk ya kure musu gudu ya hallakasu.Abinda ya daure masa kai shine me yasa wadannan dakaru bakwai suka baro can sansanin yaki suka shigo daji?Ko kuwa GUDUN TSIRA sukayi bayan an gama yakin mutanensa sun sami nasara akansu?Nan dai Sharkas ya cigaba da tafiya har izuwa tsawon sa'a guda sannan ya sake kicibis da nasa mutanen wadannan mutane bakwan wadanda suka shigo cikin dajin domin nemansa.Koda Dakarun sukayi arba da Sharkas suka ganshi a cikin wannan hali sai sukayi turus suka kura masa idanu cikin matukar mamaki saboda a tarihin jarumtakar Sharkas bai taba samun rauni ba a wajen yaki amma yau gashi harma yana dogara sanda da kyar yake iya tafi.Sharkas ya dubi wadannan dakaru bakwai ya daka musu tsawa yace menene dalilin da yasa kuka baro sansanin yaki kuka shigo cikin wannan daji?Koda jin wannan tambaya sai daya daga cikinsu ya kwashe labarin duk abinda ya faru ya zaiyane masa a karshe ya shaida masa cewa sunga Sulaira a can bakin wani katon dutse amma sai ta bace bat suka nemeta sama da kasa suka rasa.Koda jin wannan batu sai Sharkas ya cika da murna ya tambayi hanyar da zaibi yaje wajen da sukaga Sulaira.Nan take sukayi masa nuni da hanyar.Cikin gaggawa Sharkas ya karbi dokin daya daga cikinsu ya hau ya zabureshi da gudu ya nufi wannan hanyar.Koda ganin haka sai wadannan dakaru sukayi sauri suka bi bayansa da gudu. TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Daya (1) Part E A CAN KOGON DUTSE kuwa,bayan Sulaira ta ga ruwa ya samu sai tayi tunanin ta dafa ruwan dumi domin ta dan gasa jikin sarki Garzub amma inda matsalar take shine babu tukunyar da zata iya dafa ruwan a ciki kuma babu busassun ice wanda zata iya dafa ruwan dashi domin koda ma tayi amfani da wutar tsafi ba zata sami biyan bukata ba kamar yadda takeso domin duk sa'adda zata yiwa mara lafiya magani bata amfani da karfin sihirinta.Bisa wanna dalili ne yasa Sulaira ta fita daga cikin kogon dutsen ta tafi neman tukunya da icen wuta. Da kyar da sidin goshi ta faki ido taje har can sansanin yakin ta dauko tukunyar kasa gami da icen girki ta dawo cikin kogon dutsen tayi sauri ta hada wuta a karkashin wadansu kananan duwatsu sannan ta dora tukunyar kasar akan duwatsun ta zuba ruwa a cikinta kuma ta zuba wani garin magani a cikin tukunyar sannan ta rufe. Saida ruwan ya tafasa sannan ta dauko ganyen ta cire wani farin kyalle a jikinta wanda tayi damara dashi ta rinka tsomashi a cikin tafasasshen ruwan tana gasa sassan jikin Garzub.Kafin Sulaira ta fara wannan aiki Sarki Garzub bacci yakeyi amma tana dandana masa tsumman a karo na farko sai ya kwala ihu sakamakon wani mugun zogi da yaji sa'adda ruwan maganin ya ratsa cikin kofofin gashin jikinsa.Haka dai Sulaira ta cigaba da wanna aiki har ya zamana cewa ta gama gasa ko ina a jikin sarki Garzub.Bayan ruwan maganin ya ratsa ko ina a jikinsa sai idanunsa suka bude sosai a karon farko tunda aka shigo dashi cikin kogon dutsen tsawon kwana uku a sannan ne ya dawo cikin haiyacinsa sosai ya dubi gabas da yamma kudu da arewa ya fahimci a inda yake,sannan ya kurawa Sulaira idanu cikin matukar mamaki.Da kyar sarki Garzub ya budi baki yace da ita yake wannan MA'ABOCIYAR KYAWU yaya akayi muka zo nan cikin wannan kogon? Dajin wannan tambaya sai Sulaira ta kwashe labarin duk abinda ya faru a baya ta zaiyane masa tun daga lokacin da taga ya suma har izuwa sa'adda ta jashi a kas da kyar ta shigar dashi cikin wannan kogo ta shiga jinyarsa har izuwa sa'adda ta tafi neman dabbobinsu don ta samo madarar da zata bashi ya sha tayi sa'a kuwa ta gano inda dabbobin nasu suke ta taho da saniyarta.Daga wannan rana ta cigaba da jinyarsa har tsawon kwana uku.Lokacin da Sarki Garzub yaji wannan labari sai taga idanunsa sun ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa.Al'amarin dayayi matukar baiwa Sulaira mamaki kenan ta dubeshi tace yakai wannan sarki mai dara ta daya a cikin wannan nahiya,kai kuwa menene dalilin da yasa ka zubar da hawayenka yanzu sakamakon jin wannan labari dana baka? Da jin wannan tambaya sai Sarki Garzub yayi ajiyar zuciya sannan yace yake ma'abociyar kyawu kiyi sani cewa kece mace ta farko dana taba kadaita da ita a rayuwata sama da tsawon rabin sa'a gashi harma mun shafe kwanaki uku tare.A rayuwata in banda mahaifiyata babu wani mahaluki daya taba ceton rayuwata sai ke. Ita kanta mahaifiyata ta ceci rayuwata ne sa'adda ina yaro karami.Kece mace ta farko data taba jikina.Lallai al'amarinki ya bani tsoro kuma ya bani matukar mamaki.Shin zaki iya sanar dani labarinki da kuma dalilin da yasa jama'arku suka shigo cikin wannan daji har suka kafa wannan karamin kauye? Ba tare da boye komai ba Sulaira ta kwashe labarinta tun daga farko har karshe ta zaiyanewa sarki Garzub har da wasiyyar da mahaifinta yayi mata a karshe cewar kada ta kashe kanta lallai tayi aure domin ta bar zuri'arsu a doron kasa.Lokacin da Sulaira tazo nan a labarinta sai taga hawaye ya kara zubowa a idanun sarki Garzub saboda tausayinta,kawai sai taga ya yunkura da kyar ya mike zaune a karon farko tunda ta shigo dashi cikin kogon sannan ya kura mata idanu yace yake Sulaira kiyi sani cewa ni dake da iyayenmu sun barmana wasiya iri daya.Ki sani cewa a da can bani da burin yin aure amma duk sa'adda na tuno da wasiyyar mahaifina sai naga cewa bani da wani zabi wanda yafi nayi auren.Shin zaki iya yarda dani na zama ABOKIN RAYUWArki? Koda jin wannan batu sai Sulaira ta rungume sarki Garzub ta fashe da kuka tana mai cewa kaine 'da namiji dayafi cancanta dani domin a duniya ban taba jin naso wani ba ba sai kai. Dajin haka sai farin ciki ya kama sarki Garzub.Nan take ya kama hannun Sulaira ya yanki babban dan yatsanta yasa dan yatsan a cikin bakinsa ya tsotsi jinin daya fito. Itama Sulaira ta kama nasa hannun ta yanki dan yatsansa tasa a bakinta ta tsotse jini. Wannan itace al'adar mutanen birnin Hirtoliya.Indai mace da namiji sukayi haka sun zama miji da mata.Faruwar hakan keda wuya sai sukaji sukuwar dawakai a kofar kogon da suke ciki. Cikin firgici Sulaira ta mike zumbur ta zare makaminta amma sai Sarki Garzub yayi caraf ya rukota ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi.Nan take ya gani a cikin idanunsa cewa Sadauki Sharkas ne da dakarunsa mutum bakwai sukazo gaban kogon dutsen bisa dawakai sukayi turjiya.Nan take Sadauki Sharkas ya sauko daga kan dokinsa ya dubi wannan kogon dutse kawai sai wani irin haske ya fito daga cikin idanunsa ya dira a daidai inda kofar kogon dutsen take.Hasken ya fara kokarin bude kogon.Cikin hanzari sarki Garzub ya cigaba da karanta wadansu dalasimai na tsafi sai gashi duk su biyun sun fara yin zufa kuma jikinsu na karkarwa.Gaba dayan kogon dutsen ya kama girgiza kamar zai nutse izuwa karkashin kasa.Saida rabin sa'a ta shafe a haka ya zamana cewa Garzub da Sharkas sun jike sharkaf da gumi sannan duk su biyun suka fadi kasa suna numfashi da kyar.Jim kadan sai Sharkas ya mike tsaye zumbur ya kama doki ya haye ya dubi wadannan dakaru nasa yace ku zo mu koma can sansanin yaki mu karar da sauran abokan gaba sannan nayi sabon shiri mu dawo nan a hallaka wadanda ke cikin kogon.Koda gama fadin hakan sai Sharkas ya zaburi dokinsa da gudu ya durfafi inda sansanin yakin yake.Su kuwa wadannan dakaru nasa sai suka bishi a baya da gudu suna karawa dawakansu kaimi. Tafiyarsu Sharkas keda wuya sai Sarki Garzub ya yunkura ya mike tsaye da kyar yana tangadi sakamakon raunikan dake jikinsa ya zare takobinsa ya nufi hanyar fita daga kogon.Koda ganin haka sai Sulaira ta ruga da gudu tasha gabansa ta rike kafadunsa a sa'adda idanunta suka ciko da kwalla tace kada ka fita yaki yakai mijina,domin ko kadan babu kwari a jikinka,ba zaka iyayin komai ba.kuma abokan gaba zasu iya samun lagonka nan danan.Sa'adda Garzub yaji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi Sulaira yace yake matata kiyi sani cewa idan ban fita ba yanzu za'a gama karar da dukkanin sauran jama'ata a kama na kamawa a kashe na kashewa sannan abokan gaba su karasa izuwa birnina su bajeshi su kwashe dukiyarmu su debi bayi.Sanin cewa ina nan a raye yanzu shine yasa su Sharkas basu tafi izuwa birnin nawa ba domin sun san cewa idan suka tafi kamar sun bar BAYA DA KURA ne. Ki sani cewa idan muka cigaba da zama anan har Sharkas ya dawo ni dake duk ba zamu tsira ba.Lallai yanzu bamu da wani zabi face mu fita mu tunkari abokan gaba domin komai zai iya faruwa.Kodai mu tsira ko kuma mu hallaka.Gama fadin hakan keda wuya sai Garzub yayi nuni da hannunsa izuwa ga kofar kogon.Take kofar ta wanzu suka fice daga ciki Sulaira na rike da kugun Garzub yana takawa a hankali da kyar. Ai kuwa suna fitowa daga cikin kogin sai wannan saniya ta Sulaira ta biyota.Kwatsam kuma sai ga dakaru bakwai na jama'ar sarki Garzub sun iso bakin kogon dutsen bisa dawakai.Koda wadannan dakaru sukayi arba da Garzub suka ganshi a raye sai suka cika da matukar farin ciki suka zube kasa a gabansa suka kwashi gaisuwa.Sarki Garzub ya dubesu yaga har da SARKIN YAKINsa wato sadauki Zamud. Garzub yayi murmushi sannan ya dubi su Zamud yace kuyi gaisuwa ga gimbiya Sulaira domin a yaune ta zama MATATA.Dajin haka sai su Zamud sukayi sujjada ga Sulaira suka kwashi gaisuwa sanna suka dago a lokaci guda suka fuskanci sarki.Garzub ya dubi Zamud yace yakai dirkar Hirtoliya me ake ciki acan filin yaki? Zamud yayi murmushi sannan yace ya shugabana damu da abokan gaba kowanne bangare sunyi asarar miliyoyin rayuka musamman bangarenmu domin ka sani cewa sun fimu yawa.Lokacin da muka nemeka muka rasa sai hankalinmu ya dugunzuma kuma muka sami karayar zuci domin mun tabbatar da cewa indai babu kai a wannan yaki cikin kankanin lokaci abokan gaba zasu sami nasara akanmu. Ya shugaba yanzu ina dabara take tunda gashi kana cikin yanayi na matukar rashin lafiya? Ina ganin cewa bazaka iya yin yaki a haka ba.Dajin wannan batu sai sarki Garzub yayi murmushi sannan ya hade fuska yace ai duk NAMIJIN KWARAI ba'a sanshi da karayar zuciya ba.Idan har abokan gaba zasu fito wannan yaki lallai nima zan fita yanzu muyi sauri mu koma can sansanin yaki don kada a fara yakin muna nan.Koda jin haka sai daya daga cikin dakarun ya baiwa Sarki Garzub nasa dokin.Cikin hanzari gimbiya Sulaira ta hau kan dokin sannan ta mikawa Garzub hannunta ya rike ta janyoshi shima yahau kan dokin ya zauna a bayanta.Zamansa keda wuya sai Sulaira ta saki linzamin dokin ya fita da gudu,ai kuwa sai wannan saniya tata tabi bayansu da gudu sannan dakaru suka rufa musu baya wanda ya baiwa Sarki Garzub dokinsa kuwa a kasa ya falfalo da gudun tsiya bisa kafafunsa.Lokacin dasu sarki Garzub suka isa nasu sansanin yakin inda jama'arsu suke sai suka iske mutane a zazzaune suna hutawa babu wani yaki da akayi.Al'amarin dayayi matukar basu mamaki kenan.Kawai sai sukaga an harbo wata wasika a jikin KIBIYA.Kibiyar tazo ta cake a gaban dokin sarki Garzub.Cikin hanzari sarkin yaki Zamud ya sunkuya ya zare kibiyar daga cikin kasa sannan ya warware wasikar ya soma karantawa a fili kamar haka:-Takarda daga sadauki Sharkas sarkin yakin birnin Darul Nusur zuwa ga sarki Garzbu na birnin Hirtoliya.Ykaia wannan sarki ka sani cewa mun fafata yaki nida kai a karo na farko bakaji dadi ba kuma ka tabbatar da cewa ruwa ba sa'an kwando bane.In badon kayi sa'a ba mun rikito kasa tare daga kan tsauni duk mun suma ba da tuni na cire maka kai.Ina maiyi maka mugun albishir da cewa gobe da safe zamu cigaba da wannan yaki na ganin ido,a sannan ne zanyi maka KISAN GILLAH a gaban jama'rka.Dama na sani cewa kai mai kishin jama'arka ne da kasarka don haka dole ne ka fito daga cikin wannan kogon dutse da kuka buya kai da sabuwar matarka Sulaira.Lallai a gobe bayan na kashe ka zan yiwa matar taka fyade sannan itama na sassarata gunduwa gunduwa.Koda jin wannan jawabi sai zuciyar sarki Garzub ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda fishi.Gaba dayan jikinsa ya kama tsuma ya yunkura da nufin ya zare takobinsa ya ruga izuwa sansanin su Sharkas sai su Zamud sukayi sauri suka rirrikeshi suna masu bashi hakuri da tausasa zuciyarsa. Da kyar da sidin goshi suka shawo kansa in badan ma Sulaira ta rungumeshi ta fashe da kuka da basu isa su hanashi zuwa inda sadauki Sharkas yake ba. Lokacin da Sarki Garzub ya shiga cikin tantinsa sai ya iske Sulaira a zaune ta kifa kanta bisa guiwoyinta tana ta faman rusa kuka.Al'amarin daya matukar DUGUNZUMA hankalinsa kenan ya karasa gareta da sauri ya durkusa a gabanta ya dago da habarta da hannunsa suka dubi juna sa'adda hawaye ke shatata bisa kumatunta ya dubeta cikin alamun matukar damuwa yace yake matata ina dalilin wannan kuka naki? Dajin wannan tambaya sai Sulaira ta rungume sarki Garzub ta sake fashea da matsanancin kuka kamar bazata daina ba.Daga can sai tayi ajiyar zuciya cikin shasshekar kuka tace yakai mijina kayi sani cewa ba wani abu bane yasa kaga nake wannan kuka ba face sanin daga gobe shike nan mun rabu har abada ba zamu sake saduwa ba.Ina ji a jikina cewa bamu da nasara a wannan yaki da za'ayi gobe.kai kanka ka sani cewa Sharkas yafika karfi,jarumtaka da zafin nama.Tabbas ba zaka iya hallaka shi ba.Idan kuwa har baka hallakashi ba lallai sai ya hallakamu da dukkan mayakanka sannan ya cika mugun nufinsa a kaina.Daga nan kuma ya wuce izuwa birninka ya cika babban burinsa.Kaga kenan ni da kai duk bamu cika wasiyayyar iyayenmu ba.Sa'adda Sulaira tazo nan a zancenta sai sarki Garzub yasa hannunsa ya share mata hawaye sannan yace yake matata ina son ki sani cewa takin dake tsakanin TSIRA DA HALAKA dan kankani ne.Mai rai baya cire tsammanin samun rabo koda kuwa a bakin kura yake. Na sani cewa kin karaya bisa yakin da za'ayi gobe kuma kin tsorata ainun,Abinda nakeso dake shine idan har kinyi imani da son da kikeyi min a cikin zuciyarki na gaskiya ne to ki dauka cewa tabbas sai na sami nasara akan wannan yaki koda kuwa bayn nasarar zan hallaka.Inason ki sani cewa tun kafin na fito wannan yaki na gana da abin dogarona ubangiji Laruta ya tabbatar mini da cewa bazan hallaka ba wannan yaki amma akwai wani abu wanda zai sameni wanda yaki sanar dani ko menene.Ni kam naji a jikina cewa bazan mutum ba'a wanna yaki kuma ke ma ba zaki mutu ba kuma da izinin Larruta sai mun cika burin iyayenmu.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Sulaira ta kara kankame Sarki Garzub a cikin kirjinta ta shiga Shasshafa jikinsa.Nan dai suka wanzu a cikin SOYAYYA irin ta ma'aurata har suka gusar da bukatar juna. Washe gari da sassafe sa'adda hasken rana ya hudo aka buga tambarin cigaba da yaki aka rinka busa algaita.Nan da nan dakarun yaki suka fito filin daga bisa dawakai a sahu sahu. Bangaren sarki Garzub suna sanye da bakaken tufafi gaba dayansu.Su kuwa bangaren su Sharkas fararen tufafo suke sanya.Idan daga nesa mutum ya hango wannan dandazo guda biyu na mayaka sai yayi tsammnin cewa fari ne da tururuwai sukayi cinkoso.Nan take sarki Garzub ya tsaya a gaban tasa rundunar sanye da bakin sulke a jikinsa na karfe sama da kasa hatta kansa ya rufeshi da hular karfe kuma yana rike da zabga zabgan takubba guda biyu bisa farin ingarman doki. Tsayuwar sarki Garzub keda wuya sai akaga dakarun Sharkas sun buda hanya a tsakiyarsu saiga Sharkas ya ratsa ko riga babu a jikinsa daga sai wani dogon wanda na fata sai kuma dogon takalimi karfe yana rike da wannan tafkekiyar takobi tasa.Hakika duk inda kato yakai Sharkas ya cika abin misali domin ya kasance dogo kuma kakkaura wanda duk jikinsa a murde yake tamkar dutwasu aka jera.Kallo daya mutum zaiyi masa yasan cewa sadauki ne shi na gaban kwatance.Idan yana tafiya ita kanta kasa rawa takeyi saboda nauyinsa,shi kadai sai kaji yana wani huci kamar na rikakken zaki.Koda Sharkas ya iso gaban dakarunsa sarki Garzub yayi arba dashi kuma ya kare masa kallo sama da kasa sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi domin bai san cewa haka surar jikin sharkas take,domin wancan karon ba'a tube ya ganshi ba.Nanfa ya gane kurensa ya tabbatar da cewa yau fa ya taro abinda yafi karfinsa.Nan da nan aka fara kallon kallo tsakanin Sharkas da sarki Garzub.A wannan lokaci Sulaira nacan baya cikin tsakoyar dakarun Garzub tana hango filin yakin zuciyarta na ta daka tamkar zata faso kirjinta ta fado kasa don tsananin firgita.Ba zato ba tsammani sai akaji Sharkas ya bushe da mahaukaciyar dariya wacce kararta ta cika dajin gaba daya da amsa kuwa. Lokaci guda Sharkas ya murtuke fuskarsa ya nuna Garzub da dan yatsansa yace yakai wannan sarki Mai Taurin Kai kayi sani cewa yaune ranar kure karya,kuma yau ne ranar da za'a bambance tsakanin aya da tsakuwa.Tabbas kayi ganganci da rayuwarka data jama'arka domin inda kabi umarninmu da tun farko kai da jam'arka kun tsira daga masifarmu amma yanzu lokaci ya kure dole ne ku fada cikin hallaka.Ka yi sani cewa nida kai ne zamu fara bude fagen wan yaki.Da zarar na gama hallaka ka sai mu fadawa jama'arka na kamo matarka da hannuna na idda bakin burina a kanta.Kafin Sharkas ya gama rufe bakinsa sai aka ga sarki Garzub ya diro daga kan dokinsa cikin zafin nama da kunan rai ya falfalo da matsanancin azababben gudu izuwa inda Sharkas yake tsaye yana mai daga takubbansa biyu sama yana tsala ihu da kururuwa. Ai kuwa yana riskarsa suka kacame da azababben yaki wanda ya dugunzuma hankalin kowa wajen domin yaki ne irin wanda ba'a taba ganin kamarsa ba. Sharkas da Garzub suka rinka kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama,juriya da mugun nufi. Nima ganin wannan azababben yaki da ake gabzawa yasa na tsaya cak domin na kalla. TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Daya (1) Part F Cikin tsananin zafin nama,juriya da mugun nufi. Duk sa'adda takubbansu suka hadu sai kaga har tarwatsin wuta ne ke tashi.Wannan karon dai saida suka shafe sa'a guda suna gumurzu dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba duk da cewa karfin saran Sharkas da kaifin takobinsa ya ninka na Garzub sau uku.Shi kansa Sharkas yayi matukar mamaki bisa ganin irin kokarin da Garzub yayi a wannan lokaci ya rinka kare hare harensa yana jure karfinsa.Koda Sharkas yaga Garzub na bata masa lokaci saiya fusata yayi jifa da takobinsa ya tsaya cak a waje daya ya dunkule hannayensa kawai.Koda Garzub yaga haka sai ya cika da murna ya ruga garesho cikin mugun nufin ya daddatsa shi da wadannan takubba nasa guda biyu.Tun daga nesa tazarar taku shida Garzub ya dako tsalle sama ya kaiwa Sharkas mugayen sara guda biyu da nufin ya fille masa kai kuma ya raba masa allon Kafadarsa gida biyu.Kawai sai akaga shima Sharkas ya daka tsalle sama tamkar an harbashi da kibiya kuma ya gocewa dukkan harin Garzub ya danki makoshinsa sai gashi Garzub yana wutsil wutsil a sama da kafafunsa kamar yaro ya rike jelar dan tamilo.Suna durowa kasa Sharkas ya dunkule hannunsa ya gabzwa Garzub naushi aka.Saboda karfin naushin saida hular karfen dake kan Garzub ta tarwatse ta kakkarye tayi filla filla.Garzub ya sulale kasa zai fadi cikin mugun hali mai kama da suma,sai Sharkas ya sake cafo makoshinsa ya cigaba da gabza masa naushi a ciki da fuska yayi ta jera masa naushin sai gashi Garzub na aman jini ta baki da hanci.Koda Sulaira ta hango wannan al'amari dake faruwa sai ta kwala ihu ta sulale kasa sumammiya.Gaba dayan dakarun Garzub sai dukkaninsu suka kama koke koke suka fara tunanin neman hanyar gudu.Kamar dakarun Sharkas sunsan abinda ke shirin faruwa sai suka ruga da gudu izuwa kansu filin ya hautsine aka ruguntsume da azababben yaki.Lokacin da Sharkas yaga ya luguiguita Garzub matuka sai ya sakeshi ya fadi kasa ya take kirjinsa da kafarsa gudu.Nan take ya zaro wata sharbebiyat wuka ya cakata akan tsohon raunin Garzub.Garzub ya kwala ihu sakamakon mugun zafi da yaji kuma jini

Chapter 3 of 7