Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
na rasa mulkina,dukiyata da jama'ata face tsirarun wadannan dakaru da suka yi mini rakiya izuwa nan birnin Hirtoliya.Babu wani abu da yai mini saura a duniya face ke don haka dole ne nayi kokari na na tabbatar da cewar burinki ya cika tunda ni nasan cewa rayuwata yanzu gajeriya ce.A halin yanzu ni da tsirarun dakaruna babu abinda zamuyi a cikin wannan yaki face tsare rayuwar masoyinki yarima Uzaima har izuwa karshen wannan yaki.Zan baki wani kambu nawa na tsafi wanda indai kina tare dashi zaki iya tsallake kowanne irin hadari ba dai makiya su sami nasarar hallakaki ba.Lokacin da gimbiya Izaima taji wannan batu sai ta dubi sarki Rakalu cikin firgici da tsananin damuwa tace yakai Abbana to yanzu idan ka bani kambunka na tsaro kai kuma fa?Dajin wannan tambaya sai Sarki Rakalu ya dafa kafadar Izaima yace aini na manyanta kuma bani da sauran buri a wannan duniya ke kuwa yanzu ne ma kike kan tashen balaga da son cika BURIN RAYUWA don haka rayuwarki tafi tawa mahimmanci tunda ni ina daf da tafiya.Babban bakin cikina shine acr bayan bana nan babu abinda za'a kalla a tuna dani.Gama fadin hakan keda wuya sai sarki Rakalu ya ciro KAMBUN TSAFIn dake Damtsen hannunsa na hagu ya sanyawa Izaima a nata hannun na hagu.Tunda Izaima tazo duniya bata taba ganin abu mai kyalkyali da daukar ido ba tamkar wannan kambun tsafi.Abinda yafi bata mamaki shine ko kadan kambun bashi da nauyi kuma yana da tsananin taushi alamar cewa bada karfe akayi shi ba.Sarki Rakalu ya dubi Izaima cikin nutsuwa yace kinga wannan kambun shine rayuwata kuma shine dukkan abin dogarona wanda duk ya kasance tare da wannan kambu har abada bazai kaskanta ba a rayuwarsa kuma dole ne yayi sarauta sannan babu wani tsautsayi da zai hau kansa.Duk wuya duk rintsi kuma komai bala'in da akeyi da wuya sai maishi ya fita lafiya.Ki sani cewa asalin wannan kambun na kakana ne na arba'in da uku a cikin zuri'ar gidanmu.Kada kiyi wasa da wannan kambu kuma kada ki dankashi ga kowa face mutumin da kike tsananin KAUNARsa fiye da kaina.Idan kuwa kika yi kuskuren damkashi ga wanda ba kya sonsa sama da kanki lallai zakiyi babbar nadama irin wacce baki tabayi ba a rayuwarki.Koda jin wannan batu sai Izaima ta sake rungume sarki Rakalu duk su biyun suka fashe da kuka a lokaci guda.Kashe gari da sassafe wannan runduna tasu sarki Garzub suka kimtsa suka cigaba da tafiya ba sassauci ya zamana cewa basa tsayawa a ko ina face idan ta kama dole a tsaya din.Haka dai wannan runduna ta cigaba da keta dazuzzuka tana ratattaka duk abinda ta gani a gabanta.Saboda tsananin kwarjinin wannan runduna idan mutum ya hangota daga nesa kamar tazarar zira'i dubu sai yayi tsammani cewa gaba dayan halittun dake doron kasa ne duk suke tahowa.Kuma komai dakewar zuciyar mutum idan ya jiyo sautin sawayen dawakansu,rakumansu da alfadarnsu dole ne ya firgita ya nemi maboya.Bayan wannan runduna ta shafe kwana da kwanaki tana tafiya,da wani yammaci sai kwatsam suka hango wani abu daga can nesa kamar guguwa ya tokare sama yai bakikkirin ba kyan gani.Abinda ya dugunzuma hankalin su sarki Garzub shine gani suke kamar abin na shirin mamaye sama da kasa gaba dayanta.Yayi da abin ke kara kusantosu kuwa sai suka rinka jiyo wata irin dudufniya gami da sauti mai cika kunne tamkar kasa zata tsattsage abinda ke cikinta ya burtso waje.Nanfa dukkansu suka kasa kunne suna sauraro cikin firgici.Da yawa daga cikinsu sun zata ko girgizar kasa za'ayi.Sarkin yaki Zamud ya dubi sarki Garzub da yarima Uzaima yace anya kuwa wannan rawa da kasa keyi ba girgizar kasa za'ayi ba?Wancan gajimaren da muke hangowa kuma ba komai bane face fashewar dutsen karkashin kasa wanda ya dade yana cin wuta.Koda jin wannan batu sai Sarki Garzub ya dakawa Zamud tsawa yace baka da hankali ne?Ai wannan abinda kake hangowa mai kamar hazo ba hazo bane tsananin yawan abokan gabarmu ne,wannan sautin da kakeji kuwa a cikin karkashin kasa ba komai bane face karar kofaton dawakan ABOKAN GABA dana rakumansu da kuma kafafuwan dakarun dake tafiya bisa sawayensu.Koda jin wannan batu sai gaba dayan dakarun sarki Garzub suka firgita ainun domin tunda suke fita yaki basu taba karo da runduna mai tsananin yawa ba da kwarjini irin haka ba.Mutum uku ne kacal basu firgita ba daga shi kansa sarki Garzub sai sarki Rakalu sai kuma yarima Uzaima.Wani abu daya daurewa Uzaima kai shine Gimbiya Izaima na cikin dakarun dake kan gaba kusa dashi kuma ta rataya wata zabgegiyar takobi a bayanta,sannan sai ya lura da cewa gaba dayan dakarun da sarki Rakalu yazo dasu su da kuma shi Sarki Rakalu suna kewaye dashi.... TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Biyu (2) Part B Suna kewaye dashi duk inda ya motsa sai suma su motsa basa yarda suyi nisa dashi.Uzaima ya tambayi kansa a cikin zuciya yace waishin dama gimbiya Izaima ta iya yaki?Saboda me sarki Rafalu zai bar 'yarsa ta fito wannan yaki harma ta zamo akan gaba alhalin kowa na shakkar bala'in dake cikin wannan yaki?Sarki Garzub ya dubi Rakalu,Zamud da kuma Uzaima sannan ya gyada kai ya matsa daf da Uzaima yace yakai dana hakika naji a jikina cewa bamu da nasara a wannan yaki yanzu wace dabara ce dakai?Ta yaya kake ganin zamu fuskanci wannan runduna wacce ta ninka tamu sau uku ko hudu?Yarima Uzaima yayi ajiyar zuciya sannan yace yanzu dai mu jira muga karasowar wannan runduna kusa da mu sannan muyi shawara mu hadu wato ni da kai da sarki Rakalu da sarkin yaki Zamud.koda jin wannan batu sai Garzub ya jinjina kai yayi shiru baice komai ba kuma ya cigaba da kallon wannan gagarumar runduna dake tunkarosu wacce ta haddasa tashin gagarumar kura tamkar ana lokacin hazo.Sa'adda ya rage saura baifi zira'i hamsin ba tsakanin rundunonin biyu sai rundunar su sarki Madarus tayi turjiya suka tsaya cak kamar gumaka.Saida kura ta lafa sannan aka fara kallon kallo.Akan gaban tawagar Sarki Madarus ne wani shirgegen mutum wanda a gaba dayan filin yakin babu mai girmansa.Yana zaune akan wata katuwar gowa mafi girma daga cikin dukkan giwayen dake wajen,mutum ne mai tsananin kwarjini da ban tsoro,duk da cewa kuwa shekarunsa sun haura sittin,kallo daya mutum zaiyi masa yasan cewa ya cika gawurtaccen sadauki kuma jarumi.Gaba daya jikinsa a cike da guraye da layu na tsafi.Wata katuwar takobi dake ajiye a gadon bayansa tafi gaban misali domin dagata ma aiki ne wajen karti biyu majiya karfi sune zasu iya dagata.A kusa da shi sarkin yaki Sharkas ne mai hannu daya da kafa daya.Cikin tsananin mamaki sarki Garzub ya kurawa Sharkas idanu fuskarsa a murtuke babu sassauci har izuwa tsawon yan dakiku.Daga can sai ya bushe da dariyar mugunta.Adaidai wannan lokaci ne akaga tsakiyar dakarun sarki Madarus ya dare sai gashi an taho da wata KARAGAR MULKI rufaffiya,kai da gani kasan cewa akwai mutum a cikin karagar.Nanfa hankalin kowa ya koma kan wannan karaga har aka iso da ita daf da sarki Madarus aka ajiyeta.Kawai sai sarki Madarus ya sauko daga kan giwarsa ya bude wannan karagar Mulki da hannunsa sai ga wata tsaleliyar budurwa ta fito daga cikin karagar mai tsananin kyawun da yafi gaban kwatance.Gaba dayan mazajen dake wajen saida suka dimauce wasu suka kama dalalar da yawu basu sani ba.Kai wasu ma gaba daya mantawa sukayi cewar yaki suka fitoyi suka kura mata idanu kawai suna zaton a wata duniyar daban suke.Kyakkyawar budurwar ta kama hannun sarki Madarus ta sumbata sannan ta dubi rundunar sarki Garzub a wulakance tace yanzu da wadannan yan tsirarun mayakan zamuyi yaki?Ai ni ina ganin ma a cikin sa'a daya jal zamu gama dasu.Koda jin wannan batu sai sarki Madarus yayi murmushi sannan yace ai babu abinda zaisa ma har muyi sama da sa'a guda yake ZARILAF.Zarilaf tayi murmushi sannan tace kada ka manta da alkawarin da kayi mini tun kafin mu baro gida cewar ba za'a kashe mace koda guda daya ba daga cikin wadannan abokan gaba.Sarki Madarus yayi murmushi yace yake 'yata kin sani cewa a duniya babu abinda nake so sama dake,don haka duk abinda kika bukata daga gareni saina baki indai akwai shi a nan duniya.Na rantse da girman iyayena zaki sameni mai cika wannan alkawari.Kuma tun a gida na jaddadawa dakaruna cewa koda mun shiga cikin birnin Hirtoliya kada dayansu ya kuskura ya kashe mace idan kuwa ya aikata hakan a bakacin ransa.Yayin da Zarilaf taji wannan batu sai ta cika da tsananin murna ta juya da nufin ta koma cikin karagar mulkinta,a wannan lokaci Zarilaf ta rufe fuskarta da farin kyalle mai shara shara idanunta ne kadai a bude.A rayuwar gimbiya Zarilaf kullum kuma ko yaushe fuskarta a rufe take da wannan farin kyalle babu wani mahaluki daya taba ganinta ba tare da kyallen ba kuma ba'a taba ganin ranar data cireshi ba.Lokacin da gimbiya Zarilaf ta juya zata shiga cikin karagar sai idanunta suka kai kan can inda tawagar su sarki Garzub take ta hango yarima Uzaima.Kawai saita kura masa ido ta kasa shiga cikin karagar tata.Ba wani abu bane yaja hankalinta ba akansa da farko ba face ganin kyawun surar jikinsa da yadda yayi matukar kyau a cikin kayan yaki da kuma kwarjininsa.Duk da cewa daga nesane tana iya hango kyawun idanunsa da kuma dogon gashin kansa wanda ya zubo har gadon bayansa tamkar na mace.Tunda Zarilaf tazo duniya bata taba gani 'da namiji jinsin bakaken fata mai kyau ba kamar yarima Uzaima don haka bata san sa'adda ta cire wannan farin kyalle ba data rufe fuskarta ta cigaba da kurawa Uzaima idanu ba.Yayin da Uzaima yayi arba da kyakkyawar fuskar Zarilaf sai nan take yaji KIBIYAR SO ta soki kahon zuciyarsa kuma yaji kamar ya sakarwa dokinsa linzami ya tafi gareta.A daidai wannan lokaci ne Zarilaf taji an hankadata cikin wannan karaga tata.A fusace ta waigo don ganin wanda ya hankadatan sai taga she sarki Madarus ne da kansa yana mai daka mata harara.A firgice ta karasa shigewa cikin karagar tata ta zauna jikinta na bari domin a iya tsawon rayuwarta bata taba ganin ranar da sarki Madarus ya sauya mata fuska ba bare ma har ya harareta sai yau.Bayan dakaru sun dauke karagar gimbiya Zarilad sun kutsa ta cikin rundunar sun kaita can karshen baya sai sarki Madarus ya saki linzamin dokinsa ya fara tafiya a hankali cikin kasaita,izza da shan kamshi ya nufi inda rundunar su sarki Garzub suke.Har sarkin Yakinsa Sharkas da wadansu Zakwakuran mayakansa sun yunkura zasu bishi saiya daka musu tsawa tace kada dayanku ya biyo ni.Ba yaki zanyi ba magana zanje nayi da sarki Garzub kawai na dawo.Dajin haka sai duk suka ja da baya.Lokacin da Sarki Madarus yaje kusa dasu sarki Garzub ya zamana cewa tsakaninsa dasu baifi taku biyar ba saiya linzamin dokinsa ya tsaya cak akayi kallon kallo tsakaninsa da sarki Garzub na yan dakiku sannan ya bushe da mahaukaciyar dariya.Lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa ya dubi sarki Garzub yace yakai wannan sarki ma'abocin taurin kai da rashin biyayya a garemu.Kayi sani cewa kimanin shekaru ashirin da biyar baya kayi matukar kona mana zuciya tamkar an soyata da garwashin wuta.Babu yadda banyi ba akan nazo na murkusheka na baje birninka na kama matayenku da yayayenku kuma na kwashe dukiyarku amma sai tsafina ya hanani ya tabbatar mini da cewa bazan sami nasara ba akanku har sai bayan shekaru ashirin da biyar.Babu irin bakin cikin da banyi ba bisa wannan lalura amma da yake komai yana da lokacinsa yanzu gashi lokaci yayi halinsa.Yakai wannan sarki ka dubi yawan dakaruna da irin mugayen MAKAMAN YAKIn da muke dauke dasu kai kasan cewa ruwa ba sa'an kwando bane kuma ko ba'a gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza.Na rantse da darajar tsafi da girman iyayena sai na cika burina akanku saina kashe dukkan mayakanka kai ma nayi maka KISAN GILLAH,Wato kisan wulakanci irin wanda ba'a tab yiwa wani mahaluki ba.Sannan na kame sauran jama'ar dake cikin birninka mazansu da matansu a matsayin bayina,kuma na kwashe dukkan albarkatun dake cikin kasarku nayi tafiyata bayan na kone dukkanin gidajenku.Sa'adda sarki Madarus yazo daidai nan a zancensa sai sarki Garzub ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace yakai wannan azzalumin sarki kayi sani cewa karyarka tasha karya domin ni sarki Garzub ba kanwar lasa bane kabar ganin cewa ka take sauran kasashen dake bayan tawa kayi zaton cewa nima zaka iya gamawa dani farat daya.Ai kowa yaci zomo dole ne yaci gudu.Ina tabbatar maka da cewa ba'a sanin maci tuwo sai miya ta kare kuma inda babu kasa anan ake gardamar kokawa.Lallai sai an gwada sannan akan san na kwarai.Na rantse da darajar abin bauta ta Larratu baka isa kayi mini irin cin kashin da kayiwa sauran kasashen dake bayanmu ba.Tabbas yau zaka san cewa KARO DA DUBU sai dubu ta taru,kuma GUGUWAR ANNOBA bata da magani sai kallo.Kafin sarki Garzub ya gama rufe bakinsa sai sarki Madarus ya fara tsuma,gaba daya jikinsa ya kama karkarwa,zuciyarsa ta kufulo yaji kamar ya zare takobinsa ya afka musu shi kadai.Sarki Madarus ya kara matsawa da dokinsa gaba sannan ya zare takobinsa ya dagata sama ya tsaya cak akan dokinsa bai motsa ba.Koda ganin haka sai gaba dayan dakarun sarki Madarus ma suka zare nasu takubban,karar zare takubban ya cika dajin gaba daya har yana amsa kuwa.A wannan lokaci ne sarkin Yaki Sharkas ya matso kusa da sarki Madarus ya tsaya sannan saiga wani garjejen saurayi mai murdadden jiki ma'abocin kirar sadaukai shima ya fito ya tsaya daf da sharkas.Kallo daya mutum zai yiwa saurayin ya gane cewa ya kasance jinin Sharkas domin kamanninsu iri daya ne sak tamkar an tsaga kara.Shakas ya dubi sarki Garzub ya kyalkyale da dariya sannan yace yakai wannan sarki mai taurin kai kuma babban abokin gabata kayi sani cewa a rayuwata nayi yake yake sama da gudu dubu uku amma ko sau daya ba'a taba yi mini rauni ba amma sai gashi kai ka sare mini hannuna da kafata guda daya a wancan yakin da mukayi shekaru ashirin da biyar baya.Inason ka sani cewa a tsawon wadannan shekaru ashirin da biyar babu abinda nake face tanadi akan yadda zan dauki fansa a kanka.Bana son ka mutu yanzu amma inason na rabaka da hannunka guda da kafarka guda kamar yadda ka rabani da nawa.Yanzu gashi nazo maka da dana Kularu uban sadaukai.Lallai shine zai Dauki FANSAr abinda kayi mini.Lallai na umarceshi daya cire maka hannu da kafa daidai kada ya kuskura ya kasheka domin burina shine ka gani da idanunka yadda zamu shiga har cikin birninka mu kashe mutanenka mu kame mata da yara kuma mu kwashe dukiyarku.Kafin Sharkas ya gama furta wanna jawabi sai sarki Garzub ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace kai tsohon azzalumi bakin annamini kayi sani cewa kamar yadda kake takama kana da 'da nima ina dashi.Nan take sarki Garzub ya kira Yarima Uzaima yazo kusa dashi ya tsaya.Sai aka fara kallon kallo tsakanin yarima Uzaima da Sadauki Kularu ya zamana cewa kowannensu yaji a jikinsa cewa ya gamu da gamonsa domin alamar karfi tana ga mai kiba.Sarki Garzub ya bushe da dariya sannan ya hade fuska yace ni nafi karfin na sakeyin fada dakai saidai nayi da ubangidanka sarki Madarus tunda mun gwabza a baya mun gama fitar da raini.Koda jin wannan batu sai sarki Madarus yayi murmushin mugunta sannan yace ai haka za'ayi.Yanzu ni,Sharkas da Sadauki Kularu zamu fara bude fagen yaki daku ku ukun.Bayan mun sami nasara akanku ko kuma kun samu sai acigaba da yaki.Sarki Garzub yace mun amince da hakan.Nan take Sarki Madarus ya sauko daga kan dokinsa ya cire alkyabbar dake jikinsa saiga damatsansa sun firfito fili.Koda yarima Uzaima yaga irin siffar jikin sarki Madarus yaga kuma da mahaifinsa zai gwabza yaki saiya firgita ainun ya matsa daf da sarki Garzub yace yakai Abbana ka kyaleni na tari sarki Madarus kai ka tari Sharkas,sarkin Yaki Zamud ya tari Kularu.Dajin haka sai sarki Garzub yayi murmushi sannan yace ai nafi shakkar Kularu kan sarki Madarus domin shi sarki Madarus ya fara manyanta kamar yadda nima na manyanta.Ko shakka banayi akwai iyakar lokacin da zai gaji.Zahiri nasan cewa sarki Madarus yafi ni sadaukantaka kuma yafi Kularu to amma zaifi kyau yaro ya tari yaro tsoho ya tari tsoho.Gama fadin hakan keda wuya sai shima Sarki Madarus ya sauko daga kan dokinsa yana mai zare takobinsa ya matsa daf da Garzub aka fara kallon kallo.Shima Zamud ya sauko daga kan nasa dokin saboda kasancewarsa musaki mai Hannu daya da kafa daya.Sarkin yaki Zamud ya zare takobinsa ya tari Sharkas.Koda yazo daf dashi sai Sharkas ya dubeshi yayi murmushin mugunta yace sarkinku ya tsorata da dana ya kasa tararsa yaje ya tari sarkinmu bai san cewa ajalinsa ya kirawo kusa ba domin masifar sarki Madaru ta ninka ta Kularu sau dari.Ina mai tabbatar maka dacewa a cikin dakika dari da tamanin zan maida kai abincin ungulu.Koda jin haka sai Zamud ya dakawa Sharkas tsawa yace kai wawa karyarka tasha karya domin ka hadu da daidai da kai.Tabbas zan baka mamaki zan nuna maka tsantsar kwarewata da sanin makama irin wacce kake takama da ita.A bangaren Yarima Uzaima da sadauki Kularu kuwa har suka zo daf da juna dayansu bai zare makaminsa ba.Sai kawai suka cigaba da kallon juna kowannensu zuciyarsa cike da sake sake da tunani kai da gani kasan cewa KAR TA SAN KAR ce.Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda tsawo,kaurin jiki da murdewarsu yazo daidai tamkar Hassan da Husaini tsakanin Yarima Uzaima da Sadauki Kularu.Hatta kwarjininsu iri dayane inda suka bambanta kawai shine a kamannin fuska.Shima Sadauki Kularu saurayi ne kyakyawa abin misali amma bai kai Yarima Uzaima ba kuma shekarunsa daidai dana Uzaima suke domin rana daya aka haifesu.Tun Kularu yana yaro karami dan shekara takwas yake tsananin son gimbiya Zarilaf har suka girma tare amma daidai da rana daya bai taba samun ganin murmushinta ba bare ya sami nasarar da zai iya furta mata abinda ke ransa.Saida takai cewa kowa a kasar yasan cewa Sadauki Kularu yana matukar son Gimbiya Zarilaf amma ita ko kadan bata sonsa.Kai ko sunansa bata son taji an ambata. TSIRA DA HALAKA!!! Littafi Na Biyu (2) Part C . Suna kewaye dashi duk inda ya motsa sai suma su motsa basa yarda suyi nisa dashi.Uzaima ya tambayi kansa a cikin zuciya yace waishin dama gimbiya Izaima ta iya yaki?Saboda me sarki Rafalu zai bar 'yarsa ta fito wannan yaki harma ta zamo akan gaba alhalin kowa na shakkar bala'in dake cikin wannan yaki?Sarki Garzub ya dubi Rakalu,Zamud da kuma Uzaima sannan ya gyada kai ya matsa daf da Uzaima yace yakai dana hakika naji a jikina cewa bamu da nasara a wannan yaki yanzu wace dabara ce dakai?Ta yaya kake ganin zamu fuskanci wannan runduna wacce ta ninka tamu sau uku ko hudu?Yarima Uzaima yayi ajiyar zuciya sannan yace yanzu dai mu jira muga karasowar wannan runduna kusa da mu sannan muyi shawara mu hadu wato ni da kai da sarki Rakalu da sarkin yaki Zamud.koda jin wannan batu sai Garzub ya jinjina kai yayi shiru baice komai ba kuma ya cigaba da kallon wannan gagarumar runduna dake tunkarosu wacce ta haddasa tashin gagarumar kura tamkar ana lokacin hazo.Sa'adda ya rage saura baifi zira'i hamsin ba tsakanin rundunonin biyu sai rundunar su sarki Madarus tayi turjiya suka tsaya cak kamar gumaka.Saida kura ta lafa sannan aka fara kallon kallo.Akan gaban tawagar Sarki Madarus ne wani shirgegen mutum wanda a gaba dayan filin yakin babu mai girmansa.Yana zaune akan wata katuwar gowa mafi girma daga cikin dukkan giwayen dake wajen,mutum ne mai tsananin kwarjini da ban tsoro,duk da cewa kuwa shekarunsa sun haura sittin,kallo daya mutum zaiyi masa yasan cewa ya cika gawurtaccen sadauki kuma jarumi.Gaba daya jikinsa a cike da guraye da layu na tsafi.Wata katuwar takobi dake ajiye a gadon bayansa tafi gaban misali domin dagata ma aiki ne wajen karti biyu majiya karfi sune zasu iya dagata.A kusa da shi sarkin yaki Sharkas ne mai hannu daya da kafa daya.Cikin tsananin mamaki sarki Garzub ya kurawa Sharkas idanu fuskarsa a murtuke babu sassauci har izuwa tsawon yan dakiku.Daga can sai ya bushe da dariyar mugunta.Adaidai wannan lokaci ne akaga tsakiyar dakarun sarki Madarus ya dare sai gashi an taho da wata KARAGAR MULKI rufaffiya,kai da gani kasan cewa akwai mutum a cikin karagar.Nanfa hankalin kowa ya koma kan wannan karaga har aka iso da ita daf da sarki Madarus aka ajiyeta.Kawai sai sarki Madarus ya sauko daga kan giwarsa ya bude wannan karagar Mulki da hannunsa sai ga wata tsaleliyar budurwa ta fito daga cikin karagar mai tsananin kyawun da yafi gaban kwatance.Gaba dayan mazajen dake wajen saida suka dimauce wasu suka kama dalalar da yawu basu sani ba.Kai wasu ma gaba daya mantawa sukayi cewar yaki suka fitoyi suka kura mata idanu kawai suna zaton a wata duniyar daban suke.Kyakkyawar budurwar ta kama hannun sarki Madarus ta sumbata sannan ta dubi rundunar sarki Garzub a wulakance tace yanzu da wadannan yan tsirarun mayakan zamuyi yaki?Ai ni ina ganin ma a cikin sa'a daya jal zamu gama dasu.Koda jin wannan batu sai sarki Madarus yayi murmushi sannan yace ai babu abinda zaisa ma har muyi sama da sa'a guda yake ZARILAF.Zarilaf tayi murmushi sannan tace kada ka manta da alkawarin da kayi mini tun kafin mu baro gida cewar ba za'a kashe mace koda guda daya ba daga cikin wadannan abokan gaba.Sarki Madarus yayi murmushi yace yake 'yata kin sani cewa a duniya babu abinda nake so sama dake,don haka duk abinda kika bukata daga gareni saina baki indai akwai shi a nan duniya.Na rantse da girman iyayena zaki sameni mai cika wannan alkawari.Kuma tun a gida na jaddadawa dakaruna cewa koda mun shiga cikin birnin Hirtoliya kada dayansu ya kuskura ya kashe mace idan kuwa ya aikata hakan a bakacin ransa.Yayin da Zarilaf taji wannan batu sai ta cika da tsananin murna ta juya da nufin ta koma cikin karagar mulkinta,a wannan lokaci Zarilaf ta rufe fuskarta da farin kyalle mai shara shara idanunta ne kadai a bude.A rayuwar gimbiya Zarilaf kullum kuma ko yaushe fuskarta a rufe take da wannan farin kyalle babu wani mahaluki daya taba ganinta ba tare da kyallen ba kuma ba'a taba ganin ranar data cireshi ba.Lokacin da gimbiya Zarilaf ta juya zata shiga cikin karagar sai idanunta suka kai kan can inda tawagar su sarki Garzub take ta hango yarima Uzaima.Kawai saita kura masa ido ta kasa shiga cikin karagar tata.Ba wani abu bane yaja hankalinta ba akansa da farko ba face ganin kyawun surar jikinsa da yadda yayi matukar kyau a cikin kayan yaki da kuma kwarjininsa.Duk da cewa daga nesane tana iya hango kyawun idanunsa da kuma dogon gashin kansa wanda ya zubo har gadon bayansa tamkar na mace.Tunda Zarilaf tazo duniya bata taba gani 'da namiji jinsin bakaken fata mai kyau ba kamar yarima Uzaima don haka bata san sa'adda ta cire wannan farin kyalle ba data rufe fuskarta ta cigaba da kurawa Uzaima idanu ba.Yayin da Uzaima yayi arba da kyakkyawar fuskar Zarilaf sai nan take yaji KIBIYAR SO ta soki kahon zuciyarsa kuma yaji kamar ya sakarwa dokinsa linzami ya tafi gareta.A daidai wannan lokaci ne Zarilaf taji an hankadata cikin wannan karaga tata.A fusace ta waigo don ganin wanda ya hankadatan sai taga she sarki Madarus ne da kansa yana mai daka mata harara.A firgice ta karasa shigewa cikin karagar tata ta zauna jikinta na bari domin a iya tsawon rayuwarta bata taba ganin ranar da sarki Madarus ya sauya mata fuska ba bare ma har ya harareta sai yau.Bayan dakaru sun dauke karagar gimbiya Zarilad sun kutsa ta cikin rundunar sun kaita can karshen baya sai sarki Madarus ya saki linzamin dokinsa ya fara tafiya a hankali cikin kasaita,izza da shan kamshi ya nufi inda rundunar su sarki Garzub suke.Har sarkin Yakinsa Sharkas da wadansu Zakwakuran mayakansa sun yunkura zasu bishi saiya daka musu tsawa tace kada dayanku ya biyo ni.Ba yaki zanyi ba magana zanje nayi da sarki Garzub kawai na dawo.Dajin haka sai duk suka ja da baya.Lokacin da Sarki Madarus yaje kusa dasu sarki Garzub ya zamana cewa tsakaninsa dasu baifi taku biyar ba saiya linzamin dokinsa ya tsaya cak akayi kallon kallo tsakaninsa da sarki Garzub na yan dakiku sannan ya bushe da mahaukaciyar dariya.Lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa ya dubi sarki Garzub yace yakai wannan sarki ma'abocin taurin kai da rashin biyayya a garemu.Kayi sani cewa kimanin shekaru ashirin da biyar baya kayi matukar kona mana zuciya tamkar an soyata da garwashin wuta.Babu yadda banyi ba akan nazo na murkusheka na baje birninka na kama matayenku da yayayenku kuma na kwashe dukiyarku amma sai tsafina ya hanani ya tabbatar mini da cewa bazan sami nasara ba akanku har sai bayan shekaru ashirin da biyar.Babu irin bakin cikin da banyi ba bisa wannan lalura amma da yake komai yana da lokacinsa yanzu gashi lokaci yayi halinsa.Yakai wannan sarki ka dubi yawan dakaruna da irin mugayen MAKAMAN YAKIn da muke dauke dasu kai kasan cewa ruwa ba sa'an kwando bane kuma ko ba'a gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza.Na rantse da darajar tsafi da girman iyayena sai na cika burina akanku saina kashe dukkan mayakanka kai ma nayi maka KISAN GILLAH,Wato kisan wulakanci irin wanda ba'a tab yiwa wani mahaluki ba.Sannan na kame sauran jama'ar dake cikin birninka mazansu da matansu a matsayin bayina,kuma na kwashe dukkan albarkatun dake cikin kasarku nayi tafiyata bayan na kone dukkanin gidajenku.Sa'adda sarki Madarus yazo daidai nan a zancensa sai sarki Garzub ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace yakai wannan azzalumin sarki kayi sani cewa karyarka tasha karya domin ni sarki Garzub ba kanwar lasa bane kabar ganin cewa ka take sauran kasashen dake bayan tawa kayi zaton cewa nima zaka iya gamawa dani farat daya.Ai kowa yaci zomo dole ne yaci gudu.Ina tabbatar maka da cewa ba'a sanin maci tuwo sai miya ta kare kuma inda babu kasa anan ake gardamar kokawa.Lallai sai an gwada sannan akan san na kwarai.Na rantse da darajar abin bauta ta Larratu baka isa kayi mini irin cin kashin da kayiwa sauran kasashen dake bayanmu ba.Tabbas yau zaka san cewa KARO DA DUBU sai dubu ta taru,kuma GUGUWAR ANNOBA bata da magani sai kallo.Kafin sarki Garzub ya gama rufe bakinsa sai sarki Madarus ya fara tsuma,gaba daya jikinsa ya kama karkarwa,zuciyarsa ta kufulo yaji kamar ya zare takobinsa ya afka musu shi kadai.Sarki Madarus ya kara matsawa da dokinsa gaba sannan ya zare takobinsa ya dagata sama ya tsaya cak akan dokinsa bai motsa ba.Koda ganin haka sai gaba dayan dakarun sarki Madarus ma suka zare nasu takubban,karar zare takubban ya cika dajin gaba daya har yana amsa kuwa.A wannan lokaci ne sarkin Yaki Sharkas ya matso kusa da sarki Madarus ya tsaya sannan saiga wani garjejen saurayi mai murdadden jiki ma'abocin kirar sadaukai shima ya fito ya tsaya daf da sharkas.Kallo daya mutum zai yiwa saurayin ya gane cewa ya kasance jinin Sharkas domin kamanninsu iri daya ne sak tamkar an tsaga kara.Shakas ya dubi sarki Garzub ya kyalkyale da dariya sannan yace yakai wannan sarki mai taurin kai kuma babban abokin gabata kayi sani cewa a rayuwata nayi yake yake sama da gudu dubu uku amma ko sau daya ba'a taba yi mini rauni ba amma sai gashi kai ka sare mini hannuna da kafata guda daya a wancan yakin da mukayi shekaru ashirin da biyar baya.Inason ka sani cewa a tsawon wadannan shekaru ashirin da biyar babu abinda nake face tanadi akan yadda zan dauki fansa a kanka.Bana son ka mutu yanzu amma inason na rabaka da hannunka guda da kafarka guda kamar yadda ka rabani da nawa.Yanzu gashi nazo maka da dana Kularu uban sadaukai.Lallai shine zai Dauki FANSAr abinda kayi mini.Lallai na umarceshi daya cire maka hannu da kafa daidai kada ya kuskura ya kasheka domin burina shine ka gani da idanunka yadda zamu shiga har cikin birninka mu kashe mutanenka mu kame mata da yara kuma mu kwashe dukiyarku.Kafin Sharkas ya gama furta wanna jawabi sai sarki Garzub ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace kai tsohon azzalumi bakin annamini kayi sani cewa kamar yadda kake takama kana da 'da nima ina dashi.Nan take sarki Garzub ya kira Yarima Uzaima yazo kusa dashi ya tsaya.Sai aka

Chapter 5 of 7