Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
kansa horon yaki har ta iso daf dashi sannan ya dubeta yace,"Yake 'yata,ina dalilin fitowarki a wannan lokaci, kuma a cikin shigar yaki? " Koda jin wannan tambaya sai lamirat tayi murmushi tace,"Ya kai Abbana kayi sani cewa Yau kusan shekaru uku kenan rabon da mu wasa jini ni da kai,don haka ina son mu dan fafata domin na gani ko na samu cigaba a koyon yaki na fiye da abinda ka koya mini a baya tunda a kullum a cikin neman Karin ilimi nake." Koda jin haka sai sarki gurzalu yayi murmushi yace, "Wannan ba laifi". Nan take ya gyara tsayuwarsa, ita ma sai ta tsaya a nesa kadan dashi ta gyara tsayuwarta suka fuskanci juna,Daga can kuma sai suka fara zagaya juna, Kamar hadin baki sai suka ka da baya a lokaci guda sukayi taku uku kacal, sannan suka rugo da gudu izuwa kan juna suka kacame da masifaffen yaki, ya zamana cewa suna kaiwa juna SARA DA SUKA cikin azababben zafin nama,juriya da bajinta, suna neman hallaka juna da dukkan karfinsu tamkar sun kasance tsofaffin abokan gaba, Tunda suka fara wannan gumurzu sarki gurzalu ya cika da tsananin mamaki, domin a saninsa Sam gimbiya lamirat bata da zafin nama irin na yanzu, kuma kwarewarta a yaki ba ta kai hakan ba. Abu dai kamar a mafarki sai gashi karfinsu ma yazo daya,an rasa wanda zai iya cutar da dayan. Sai da suka shafe rabin sa'a suna fafatawa a cikin wannan hali, Al'amarin da ya fusata sarki gurzalu kenan, ya sauya salon yakin ya hada da kai mata bugu da naushi hannu da kafa. Kawai sai yaga ita ma ta koma irin salon da ya koma kuma ya kasa cutar da ita,da kyar da sidin goshi ya shammaceta ya daka wawan tsalle sama ya doketa da kafa a fuska, Tana faduwa kasa a lokacin da lebenta ya tsage, jini ya dan zubo, sai ita ma ta kwarfi kafafunsa yai sama ya rikito kasa,amma sai ya duro bisa kan tafin hannunsa guda cikin bajinta ya doki kasa da tafin hannun nasa yai sama ya dawo kasa bisa kafafunsa. A dai-dai wannan lokaci ne suka ji ana yi musu tafi, suna waigowa baya suka ga Ashe sarki taryan ne tare da 'yarsa Gimbiya Shumaira suka durfafo inda suke, cikin hanzari lamirat ta mike tsaye tana mai goge dan jinin da ke kan lebenta da tafin hannunta. Sarki taryan ya dubi Gimbiya lamirat yace,"Hakika wannan 'ya ta gaji ubanta a jarumtaka, lallai yanzu ne nasan cewa kin cancanci ki shiga.,...." Kafin ya karasa fadin abinda ke bakinsa sai Gimbiya lamirat ta tari numfashinsa don kada ya tona ma ta asiri tace,"Ai barewa ba ta gudu danta yayi rarrafe. Ya shugabana me yasa kazo ka katse mana wannan horon yaki da muke yi?" Koda jin wannan tambaya sai sarki taryan yayi ajiyar zuciya yace, "Ai wani gagarumin abin mamaki ne ya faru yanzu shine nace lallai sai nazo na sanar da Ku, yanzun nan na kaiwa jarumi Imhal ziyara a dakin da aka tsareshi, ina zuwa sai na iske likitana yana cire zaren da aka dinke wannan rauni na kirjin sa,ina mai tabbatar muku da cewa raunin ya hade ya warke sumul tamkar ma bai taba yin sa ba". Koda jin wannan labari sai sarki gurzalu da Gimbiya LAMIRAT suka kallo junansu cikin fargaba da tsananin mamaki. Sarki taryan yaci gaba da cewa," A halin yanzu dai jarumi Imhal yace a shirye yake ya cigaba da wannan gasa gobe, don haka na sanar da duk Alkalan gasar tuni ma an cigaba da shirye-shirye." Koda sarki taryan yazo nan a zancen sa sai sarki gurzalu yayi ajiyar dogon numfashi yace,"Wace irin magana kake yi haka kamar Almara? Ya za ayi ace mutum ya samu irin wannan babban rauni, kuma ace ya warke a cikin kwanaki uku kacal? " Sarki taryan yace ai kada kayi mamaki da hakan, domin akwai mutane masu baiwar saurin warkewa daga ciwo, idan baka manta ba ai har a cikin RIJIYA GABA DUBU ta kurkukun DARUL MAUT aka sa jarumi Imhal ana yi masa azaba har tsawon kwanaki, amma aka fito dashi a cikin kwanaki kadan duk raunin dake jikinsa suka warke, kuma ya samu lafiyar jikinsa. Koda jin wannan batu sai sarki gurzalu da gimbiya lamirat suka kalli juna cikin alamun damuwa da takaici, sannan lamirat ta dubi sarki taryan tace,"Wanene wannan jarumin da zai fafata da Imhal gobe? " Sarki taryan ya jinjina kai yace "Wani bakin jarumi ne shima daga birnin Askandariyya,nima ban taba ganinsa ba,sai gobe a filin gasar za muga ko wane ne". Koda gama fadin haka sai sarki taryan ya kama hannun gimbiya Shumaira suka juya suka nufi inda suka fito. Suna cikin tafiya ne Gimbiya Shumaira ta juyo ta kalli sarki gurzalu da Gimbiya lamirat ta ga ko kadan babu annuri akan fuskokinsu, tamkar an aiko musu da sakon mutuwa, kawai sai tayi musu wani irin guntun murmushi wanda suka kasa fahimtar ko na mene ne tsakanin na mugunta ko na alhini. Shi kuwa sarki taryan sai ya dubi Shumaira yace, Hakika yanzu na fara yarda da zargin da nake yi akan sarki gurzalu, domin ban ga dalilin da yasa suka tsananta kiyayya ba akan jarumi Imhal,bisa binciken da nayi ma tun farkon haduwar Imhal da sarki gurzalu laifin da yayi masa bai kamata ayi masa hukuncin dauri a kurkukun Darul Maut ba balle har a sanyashi a cikin RIJIYA GABA DUBU a azabtar dashi na tsawon kwanaki ba,tabbas an zalunceshi, ni kuwa a rayuwata bana son zaluntar mutumin da yake kasa dani,musamman wanda ya kasance talaka na". Koda Gimbiya Shumaira taji wannan batu daga bakin mahaifinta sai farin ciki ya lullube ta domin ta fuskanci cewa hakanta zai cimma ruwa a kokarin da take yi na raba alakar da ke tsananin sa da sarki gurzalu, tunda gashi shi da kansa ma ya fara gano irin zaluncin sarki gurzalu. A daren wannan rana aka cigaba da shela a cikin birane da kauyukan kasar misra ana sanar da cewa, "Lallai gobe da safe za a cigaba da gasar kambun JARUMTA. Ai kuwa tun a cikin daren 'Yan kallo suka dinga tururuwa a cikin filin gasar don kada su rasa inda za su zauna suyi kallo. yayin da gari ya waye kuwa sai ya zamana cewa duk inda mutum ya duba a filin gasar babu masakar tsinke, ko ina kawunan bil'adama ne rututu. Kai! har kan katangar filin gasar mutane ne a zazzaune maza da mata,a tsakiyar filin ne kawai aka bar hanyar da za a wuce don shigowar sarakai gami da jaruman gasa da alkalai. Sai da aka shafe kusan rabin sa'a ana jira sannan aka ji tambura na tashi gami da bushin Algaita alamar cewa sarakai za su shigo filin gasa,Nan fa filin gasar ya rude da shewar jama'a suka kamu da tsananin murna don sanin cewa yanzun nan za a fara gasar. Ai kuwa sai ga sarki taryan, sarki gurzalu, da 'ya'yayensu mata tare da sauran manyan sarakuna na nahiyar sun shigo cikin filin gasar dakaru na biye da su a gaba da baya, gefe da gefe, ana cigaba da buga tambura, har sai da suka isa inda mazauninsu yake suka zauna. Zaman su ke da wuya sai mai gabatar da gasar ya mike ya fara jawabi yana mai yiwa manyan baki barka da zuwa, sannan ya sanar da cewar jarumin da ya fara wannan gasa,wato jarumi Imhal ya warke daga raunin da ya samu a cikin kwanaki uku kacal,kuma da shi za ayi wannan gasa ta Yau kamar yadda dokar gasar ta tanadar cewa,duk jarumin da ya samu nasarar lashe gasar ba zai yi fashin wasa ba face baya numfashi a doron kasa,kuma komai yawan raunikan da ke jikinsa indai zai iya warkewa sai an jira shi ya warke har izuwa tsawon mako biyu, idan ya wuce mako biyu ne bai warke ba an cire shi daga cikin jaruman gasar, Lokacin da jama'a suka ji cewar jarumi Imhal ya warke daga ciwon sa a cikin kwanaki uku kacal sai kowa ya kamu da tsananin mamaki aka shiga yi masa jinjina da kirari tun kafin ma ya fito filin gasar,nan fa filin ya rude da shewa gami da hayaniyar mutane har sai da aka buga gangar fara gasa sannan aka yi tsit! tamkar mutuwa ta fado filin gasar. A sannan ne mai gabatarwa ya kirawo sunan bakon jarumin da yazo daga birnin Askandariyya wai shi ZAMBARU IBINI KULSAS. Kawai sai aka ga wani bajimin katon mutum mai tsawon kamu ashirin da bakwai ya fito daga cikin dakin jaruman gasa wanda ya kasance mai kauri da fadin kirji, inda za a yanke kafarsa guda a dorawa mutum dakon ta a kansa,ji zai yi kamar an Dora masa cinyar katuwar giwa. Koda jama'a suka yi arba da wannan narkeken kato mai kirar mutanen farko, sai suka firgice suka dimauce ainun, domin gani suka yi kamar zai baje filin gasar gaba daya ya mutsittsike kowa da komai da ke filin. Nan fa jama'a suka kama mikewa tsaye domin su ruga da gudu izuwa wajen filin gasar,sai da dakaru suka hau daka musu tsawa sannan kowa ya nutsu ya koma mazauninsa. Duk sanda Zambaru yayi tafiya taku daya sai a ji birnin gaba daya yayi girgiza kamar kasa za ta tsage komai da ke samanta ya rufta cikin ta, Kai hatta sarki Gurzalu da ya kasance jarumin da ke rike da KAMBUN JARUMTAKA sai da ya firgita bisa ganin Zambaru, Ya Sha jinin jikin sa,ya ayyana cewar lallai babu tabbacin shi kansa zai iya hallaka wannan basamuden kato Koda kuwa da karfin sihirin tsafi ne. Bayan Zambaru ya iso tsakiyar filin gasar sai ya tsaya ya daga kansa sama yayi wata irin kururuwa mai tsananin kara da firgitarwa wacce ta cika cikin birnin misra da duk kauyukan da ke kewayensa da amsa kuwwa, kuma ta firgita mutane da dabbobi har ma da aljanun dake kawayen wajen. Al'amarin da ya janyo hargitsewar birnin kenan, mutane suka dinga guje-guje da iface-iface, matan dake dauke da tsohon juna biyu kuwa ba shiri suka kama yin nakuda ta ba zato suka dinga haife abinda ke cikin duba tare da lokacin haihuwar yayi ba,Har sai da Zambaru ya tsuke bakinsa sannan komai ya lafa, mutane suka dawo cikin hayyacinsu. A wannan lokaci ne mai gabatarwa ya kirawo jarumi Imhal, kawai sai aka ga jarumi Imhal ya fito da gudu daga cikin dakin jaruman gasa rike da takobi da garkuwa cikin shigar yaki ba tare da shakkar komai ba. Koda ganinsa sai filin gasar ya rude da shewa aka kama yi masa jinjina da kirari, mawaka na yi masa lakabi da SABON JARUMI MAI ABIN AL'AJABI, Koda Zambaru ya hango jarumi Imhal ya nufo cikin filin gasar a guje rike da wata takobi sai ya zura hannun sa izuwa bayan sa ya fiddo wata lafceciyar takobi wadda inda za a ajiye ta a kasa karti ashirin majiya karfi basa su iya dagata sama ba. Maimakon jarumi Imhal ya tsaya a sake buga tambarin fara gumurzu, kawai sai ya cigaba da gudu ya tunkaro inda jarumi Zambaru yake tsaye. Shi kuwa Zambaru sai ya fara wulwula takobinsa a sama yana jiran isowar Imhal. Yayin da ya rage saura bai fi taku shida ba kacal Imhal ya iso inda Zambaru yake sai ya daka wawan tsalle sama kamar an cilloshi daga baka sai gashi ya iso dai-dai wuyan Zambaru. Ai kuwa sai ya dankara masa Sara a wuya, take takobin ta makale a jikin wuyan Zambaru tamkar a jikin bishiya mai kauri ta nutse. Imhal ya finciko takobinsa da hannayensa biyu da dukkan karfinsa amma sai ya kasa Ciro takobin. Kafin ya sake yin wani yunkuri tuni Zambaru ya mako shi da hannun sa na hagu wanda baya rike da makami, take Imhal ya fado kasa ba shiri ya duro akan kafarsa ta hagu,ai kuwa sai kafar tasa ta karye ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da ya ji ya sulale kasa a matukar galabaice ya kasa mikewa tsaye. Koda ganin abinda ya faru sai Zambaru ya bushe da mahaukaciyar dariya ta mugunta, sannan yasa hannun sa na hagun ya zare takobin Imhal wacce ta makale a wuyan sa, jini yayi tsartuwa daga jikin wuyan nasa,amma ko a jikinsa. Kawai sai yayi jifa da takobin ya nufi jarumi Imhal wanda ke zaune a kasa, yana mai daga lafceciyar takobinsa. Gaba daya 'Yan kallon da ke cikin filin gasar sai suka dafe kai suka fara ihu da kururuwa domin sun San cewa lallai Imhal ya zama gawa tasa ta kare. Su kuwa attajiran da suka zabi Zambaru a matsayin jarumin gasar su suka sa kudin su na caca a kansa sai suka fara yin tsalle da murna suna kida da rawa don sun San cewar kakarsu ta yanke saka, sun gama zamowa manyan attajirai. Wadan da suka zabi jarumi Imhal kuwa a matsayin jarumin gasar su sai suka fara kuka suka kamu da tsananin bakin ciki sabo da sun San cewa lallai karayar arziki ta zo musu!!! YAYA KARSHEN WANNAN GASA ZA TA KASANCE TSAKANIN JARUMI ZAMBARU DA JARUMI IMHAL? TA YAYA JARUMI IMHAL ZAI TILASTAWA GIMBIYA LAMIRAT TA KAMU DA SONSA? SHIN IMHAL ZAI RASA RAYUWARSA NE A CIKIN WANNAN GASA TA KAMBUN JARUMTA KO KUWA ZAI LASHE GASAR NE HAR TA CIKA BURIKAN DA KE GABANSA?INA LABARIN TSOHO IMZANU KUMA A CIKIN WANE HALI YAKE YANZU A CAN BIRNIN KISRA? Mu hadu a RIJIYA GABA DUBU 4 don jin cigaban wannan kasaitaccen labarin. . Toh jama'a gashi mun kawo gargada na wannan littafi Amma kuma an samu tsaiko a dalilin bani da littafi na Hudu Don haka nake baku hakuri . Izan kuwa acikin members ko Admins an samu wanda yake da shi sai ya taimaka ya kawo maku .Shuraih Aka 99% . . An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7