Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
a gaban idanunsu sannan mu umarce su da abinda muke bukata kuma mu gargadesu cewa duk wanda ya tona asirinmu acikin su shima mutuwa zai yi,koda jin haka sai Zauwadu yayi dariyar farin ciki yace tabbas indai mukayi haka komai zai tafi dai-dai to amma fa kasani idan muka debo wadannan kudaden acikin sa'a daya asirinmu zai tonu don a sannan ne shugaban dakarun zai dawo,koda jin haka sai Imhal yayi tsaki ya mike tsaye zumbur a fusace ya dakawa ALZauwadu tsawa yace kada ka sake yimin tambayar komai har sai bayan mu samu nasararr fita daga gidannan.Gama fadin haka ke da wuya sai suka ji an kada kararrawar zuwa cin abinci nan take dakaru suka fara bude kofofin dakunan fursunonin,ana bude dakin su Imhal sai suka wuce da sauri suka zama akan gaba suka riga kowa zuwa inda masu dafa abinci suke suka shige har cikin dakin girkin ba tare da dakaru sunga lokacin da suka shiga ba,suna shiga suka iske masu dafa abincin akan aikinsu kawai sai Zauwadu ya kama kan daya daga cikin su ya murde ya yar da gawrsa a kasa,cikin tsananin tsoro sauran ma'aikatan suka zube a kasa suna rokon su ayi musu rai kawai sai Imhal ya dube su yace idan kuna so ku tsira da rayuwarku ayau ku zuba banju acikin abincin da za a kaiwa masu gadin shugaban dakarun gidannan idan kuma kuka gayawa wani wannan sirrin duk sai kun mutu lallai kuyi wannan aikin cikin dakiku kadan,koda gama fadin haka sai Imhal da Zauwadu suka fice daga cikin dakin suna fita kuwa suka yi arba da wani babban badakare akayi kallon-kallo nan take jikin badakaren ya bashi cewar da akwai abinda suke shiryawa. TO JAMA'A ANAN NAZO KARSHEN LITTAFI NA DAYA . Marubucin yace SHIN SU IMHAL ZASU SAMI NASARAR FITA DAGA CIKIN WANNAN KURKUKU . YAYA LABARIN TSOHO IMZANU DA MUZAIRA . SHIN SARKI GURZALU ZAI SAMU NASARAR HALLAKA IMHAL A GASAR JARUMTA NA BIRNIN KISRA . Marubucin yace domin jin wayannan amsoshi sai mu hadu a littafi na biyu . Nine Shuraih USman Inkiya Shuraih 99% dana kawo maku Nake cewa sai kun jini a Littafi na biyu gobe RIJIYA GABA DUBU Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani m gini Ebook creator Shuraih Usman Ebook publish by http://hausaebooks.cf . Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 2A . Da isar saiyaru cikin gidan kurkukun bayan ya wuce kofofi goma sha daya sai ya wuce kai tsaye izuwa dakin tuhuma yana ta murmushin mugunta,da isar sa kofar dakin sai masu gadin dakin suka rusuna suka gaishe shi,ko kallon su bai yi ba ya daka musu tsawa yace Maza ku budemini kofar da sauri na shiga,cikin hanzari daya daga cikin masu gadin yasa kuba ya bude kofar ya kunna kai,ashe wadannan masu gadin duk na bogi ne acikin shigar kayan dakaru suna daga cikin dakaru guda ashirin din da Imhal suka zaba domin su taimaka musu wajen samun nasarar guduwa daga kurkukun.Da shigar saiyaru cikin dakin sai yayi arba da Zauwadu zaune akan kujerar da aka saba dora masu laifi an daure hannayensa da kafafunsa da sarkoki ga badakare daya a tsaye akansa yana dukansa da kulki har ya fasa masa baki da hanci jini na suba.koda ganin haka sai saiyaru ya bushe da dariyar mugunta sannan ya dubi badakaren yace dakata haka yanzu kuma nine zanyi masa tawa azabar,ya kai Zauwadu kayi sani cewa yau ne ajalinka zai tabbata a hannnuna tunda har ka karya dokata ka sake haddasa fada tsakanin fursunoni,hakika yau gawrka rabon kifayen dake cikin teku ne.yana gama fadin haka sai ya daga kulkinsa ya nufi Zauwadu da nufin ya buga masa a kansa,ba zato ba tsammani sai kawai wannan badakaren dake tsaye ya shammaci saiyaru ya maka masa kulki akan kunnensa na hagu,take saiyaru ya sulalae kasa sumamme.Koda saiyaru ya farfado sai ya tsinci kansa a zaune akan kujera wacce ake dora fursunoni idan za a yi musu azaba an daure hannayensa da kafafunsa ta baya,Imhal da Zauwadu na tsaye akansa sanye da kayan dakaru,shi dai Zauwadu kayan saiyaru ya sanya sannan ya sanyawa saiyaru nasa na fursunoni.Koda saiyaru yaga haka sai ya tuntsire da dariyar mugunta kuma ya turbune fuska yace kun bata lokacinku a banza domin baku isa ku iya guduwa daga cikin gidan nan ba,nan gidan mutuwa ne gidan da babu wani fursuna da ya isa ya tsira da rayuwarsa koda kun gudu sai an kamo ku an dawo daku idan ma sanyin teku da halittun cikinsa basu hallaka ku ba.Koda gama fadin haka sai saiyaru yaci gaba da kyalkyala dariyar mugunta,cikin fushi Zauwadu ya daga katon kulkin nan na saiyaru ya maka masa shi a ka,take kan saiyaru ya fashe har kwakwalwarsa tayi fallatsi,koda suka ga saiyaru ya mutu sai Imhal ya dubi Zauwadu yace to fa yanzu duk nasarar mu tana hannunka duk yadda za a yi kada ka kuskura ka bari a gane cewa kai ba saiyaru banen,hatta muryarka sai ka karyar da ita irin ta saiyaru tunda daman can kuna kama da juna a fuska da yanayin jiki.Zauwadu ya risina ga Imhal yace yakai abokina kuma shugabana a wannan gida na darul maut,ina mai tabbatar maka cewa baza a taba samun wata matsala ba daga gareni sai dai daga sauran yan'uwanmu fursunoni guda ashirin wadanda muka janyo cikin wannan aiki,ni dai alkawari daya nakeso kayi mini,koda jin haka sai mamaki ya kama Imhal yace wane alkawari kakeso nayi maka?koda jin wannan tambaya sai Zauwadu ya sanya hannu acikin aljihunsa ya dauko wata sarka ta dinare ya damkawa Imhal a hannunsa yace,Wannan sarka ce ta matata wacce muke tsananin son juna fiye da hangen mai hange,a ranar da aka daura aurenmu da ita acikin birnin kisra dakarun sarki Gurzalu suka zo su dubu uku suka rufeni da masifaffen duka har sai da suka sumar dani,ina ji ina gani aka Rabani da amaryata SUHAILA aka sa mini sarka a wuyana,hannayena da kafafuna aka tafi dani suhaila tana kuka da ihu.Wannan shine asalin rabuwata da suhaila yau tsawon shekaru ashirin da bakwai kenan,suhaila na raye ko ta mutu ban saniba.ina son duk sanda ka dawo cikin birnin kisra komai dadewa ka nemi suhaila a unguwar Sharkas ka bata wannan sarka idan har na rasa rayuwata a kokarin guduwarmu daga nan,idan kuma na tsira da rayuwata to zan karbi sarkata domin nayiwa suhaila alkawarin cewar indai ina raye komai daren dadewa sai na dawo gareta ,amma idan ta ga an kawo mata sarkarta to bana raye.Koda Zauwadu yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa,Al'amarin da ya karya zuciyar Imhal kenan shima yaji ya kamu da tausayin Zauwadu har kwalla t acika masa idanu,nan take dai suka fito daga cikin dakin tuhuma Imhal ya sanya sarkar suhaila a cikin aljihunsa suka kullo kofar dakin ,masu gadin dakin mutum biyu suka rufa musu baya. Duk ta inda su Zauwadu suka zo wucewa sai ka ga ana gaishe su sabo da ana zaton saiyaru ne,hatta muryar Zauwadu ta amsa gaisuwar sai ta zama iri daya sak da ta saiyaru,su kansu su Imhal sai da suka cika da tsananin mamaki bisa yadda suka ji Zauwadu ya iya mayar da muryar tasa haka,haka dai suka cigaba da tafiya har suka iso dakin da ake ajiye gawarwakin fursunonin mutum hudu da suka mutu a sanadiyyar fadan da akayi a dakin cin abinci,kawai sai Zauwadu ya bada umarni a debo gawarwakin a dora su akan amalanke domin a futar dasu gaba daya daga gidan a watsa a teku,nan take kuwa dakaru suka cika wannan umarni daya bayan daya fursunonin nan guda ashirin abokan aikin su Imhal suka dinga shigowa cikinsu suna take musu baya.dama su duka sunyi shigar dakarun gidan kurkukun,haka dai su Imhal suka cigaba da tafiya acikin kurkukun suna tura amalanken gawa ana bude musu kofofi,duk inda suka zo da zarar anga saiyaru akan gaba sai kaga anbude musu kofa da sauri har suka shige ta cikin kofofi goma sha biyu na kurkukun kuma duk kofar da suka fita sai an mai da ita an rufe. Suna fitowa daga cikin kofa ta karshe sai suka yi arba da dandazon dakarun dake tsaron gidan kurkukun,a gefe daya kuma ga jirgin ruwa da ma'aikatan kurkukun ke shiga idan zasu je karbo abinci ko wani kaya acikin birnin kisra.Su dai masu gadin kurkukun dakaru ne kimanin guda dubu arba'in,kuma ko yaushe acikin shirin yaki suke dauke da muggan makamai,koda suka yi arba da juna tsakanin su Imhal da masu gadin sai aka tsaya ana kallon-kallo,in ba don ma shugaban dakarun ya hango saiyaru akan gaba ba da tuni ya baiwa yaran nasa umarni su afka musu. Cikin karamar murya Imhal ya matso daf da Zauwadu yace dashi kada ka kuskura ka matsa kusa da dakarun can,domin sai shugabansu ya gane cewa kai ba saiyaru bane,daga nan zaka yi musu magana ka gaya musu cewa zamu tafi watsa gawar fursunoni ne teku.Koda jin wannan umarni sai Zauwadu ya daga murya ya dubi shugaban dakaru yace ya kai Murwatu kayi sani cewa yau an samu mutuwar fursunoni har guda hudu,sabo da haka ina son ku bani jirgi na zuba su a ciki sai na isa tsakiyar teku sannan na zubar dasu domin na tabbatar da cewa sun zama abincin kifayen ruwa.Koda jin wannan batu sai Murwatu ya turbune fuska ya dakawa saiyaru tsawa yace,Kai saiyaru sabo dame yau zaka zo mana da sauyin yanayin aiki? A aikin tarihin gidan nan tsawon shekaru arba'in da kafuwarsa ba a taba yin hakan ba,duk fursunan da ya mutu daga nan ake jefa gawarsa cikin tekun,idan baza ku iya jefa gawarwakin ba daga nan to fa sai dai ku hakura ku koma da gawarwakin ku,duk wanda yayi wani yunkuri cikin ku kuwa zamu far masa. Koda jin wannan batu sai hankalin su Imhal ya dugunzuma ,suka rasa abinda ke musu dadi domin ga dukkan alamu sun sha wahalar banza kenan bisa duk irin kokarin da sukayi suka samu nasarar fitowa har kofar karshe ta gidan kurkukun DARUL MAUT. Cikin tsananin damuwa da karayar zuciya Zauwadu ya dubi Imhal yace ya kai abokina yanzu mene abin yi? Imhal yace Bamu da abin yi face mu yaki su Marwatu ko mu ko su! Cikin firgici Zauwadu yace Baka da hankali ne,ta yaya mu ashirin da biyu zamu iya yakar dakaru dubu arba'in? Imhal yace bamu da wani zabi wanda ya wuce hakan,ko dai mu yake su ko kuma mu jefa kanmu acikin tekun nan mu hallaka shine kadai gatan da zamu yiwa kanmu,ya kai abokina kai sani cewa faduwar gaba asarar namiji ce,yau ne za muyi yaki da dukkan karfinmu na jiki da karfin zukatanmu,ko mutuwa mukayi mun bar abin fadi.Ko kuwa ka zabi ka koma cikin darul maut a cigaba dq gana maka azaba har ka mutu tunda kasan cewa ko kadan baza ayi mana sassauci ba tunda mun kashe saiyaru?koda Zauwadu da sauran fursunonin suka ji wannan batu sai nan take suka ji dukkan tsoro ya kau daga cikin zukatan su. Friends kuyi hakuri fa 2days kun jini shiru wallahi mkaranta ne ya boyeni kuma makarantan ma boarding Yanzu haka yaune na dan dawo gida Shiyasa nace bazan dan yi maku post Ammafa ban dauki alkawarin na gobe baRIJIYA GABA DUBU Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 2B . Lokaci guda su duka suka daga kulakensu,sannan suka ruga izuwa kan dandazon dakarun suna masu kurma uban ihu,ai kuwa suma wadan nan dakaru su dubu arba'in sai suka zare takubban su suka ruga gare su.ana haduwa aka kacame da azababben yaki. a kofar gidan na darul maut.Kaico hakika idan mutum yaga mutuwa muraran to fa sai inda karfinsa ya kare,duk da cewar su Imhal yan kalilan ne a cikin wadannan dakaru sai gashi suna ragargazarsu don duk inda suka sa gaban su sai dai kag maza na zubewa kasa alokacin da jini ke feshi da fantsama,kuma ihun mazaje da karafkiyar karafa ta cika dodon kunne.Koda aka samu dakika dari biyu ana wannan gumurzun sai labari ya sauya sabo da sarkin yawa yafi sarkin karfi,nan fa dakaru suka fara samun nasarar saran jikin fursunonin nan,jikinsu na darewa suna ihu amma sabo da naci gami da taurin rai sunki su fadi kasa,a hakan suke cigaba da yaki.Sai dai kaga jikin fursuna yayi kaca-kaca da sara da suka tamkar yayi wanka a kogin jini amma shima bai fasa ragargazar maza ba,wani lokaci ma har faduwa suke kasa sakamakon jiri dake dibarsu amma sai kaga suna mikewa tsaye suna cigaba da yakin. Koda shugaban dakarun ya ga ana ta ragargazar yaransa kuma ya kasa fahimtar bangaren dake samun nasara a tsakanin mutum ashirin da biyu kacal da kuma mutum dubu arba'in sai ya fusata ainun ya kutsa cikin fursunonin nan da karfin tsiya cikin tsananin kwarewar yaki ya dinga fillewa fursunonin kawuna suna zubewa kasa matattu. Kafin Zauwadu da Imhal su ankara da abinda yake faruwa tuni ya kshe musu mutane goma sha biyu ya zamana cewa saura goma kacal,koda Imhal ya juyo yaga gawarwakin jama'arsu a kasa a lokacin da gaba daya jikinsa ya rine da jinin dakarun da ya kashe sai ya kwarara uban ihu ya kara kaimi yana mai cigaba da sara da suka cikin tsananin zafin nama mara misaltuwa sai gashi yana yiwa dakarun mummunar barna. Shima Zauwadu da yaga Imhal ya kara zage damtse sai shima yayi koyi dashi suka haukace suna ta daukar rayuka,Koda shugaban dakaru Murwatu yaga haka sai ya daka tsalle sama kamar an cilla shi daga cikin kibiya ya dira a gaban Zauwadu ya tare shi suka ruguntsume da azababben yaki. Wohoho! idan tsagwaron karfi ya hadu da kwarewa akwai tashin hankali,kai koda ga dan kallo ma cikin firgici da tashin hankali zai iya kallon wannan gumurzun.Sai da Marwatu da Zauwadu suka shafe dakiku masu yawa suna kaiwa juna mugayen hare- hare na sara da suka basu samu nasarar komai ba. A wannan lokaci kuwa Imhal ya samu nasarar bazar da dakaru dubu ashirin a kas,ragowar dubu ashirin din ma sun razana dashi ainun sun fara ja da baya duk da cewa wasun su ya sassare su amma sabo da naci sun ki hakura dada yi masa kawanya suke domin suyi masa rubdugu A bangaren Marwatu da zauwadu kuwa,lokacin da suka fafata ainun suka ga babu wata nasara sai suka ja da baya sukayi cirko-cirko suna haki da kallon juna kamar wadan su zakaru,kowannensu na tunanin irin dabarar da zai sauya don ya samu nasara akan abokin yakinsa.kamar hadin baki suka zare takubbansu suka daga sama lokaci guda suka rugu izuwa kan juna suna kururuwa,koda ya rage saura bai fi taku uku ba su hadu sai kowannensu ya daka tsalle sama suka kaiwa juna mummunan hari.Cikin sa'a Murwatu ya sokawa Zauwadu takobi a kahon zuciyarsa,shi kuwa Zauwadu ya soka masa a gefen cikin sa,suka rikito kasa a matukar galabaice jini na zuba a jikin su. Zauwadu ya baje a kasa wanwar ya kasa tashi yana aman jini da karkarwar jiki,shi kuwa Marwatu sai ya mike tsaye ya yage rigar jikinsa ya daure raunin cikin nasa don tsaida zubar jini. Koda ya dubi Zauwadu yaga yana kakarin mutuwa kuma ya waiga yaga shima Imhal ya fara gajiya ainun tsabar naci ne da tsananin juriya yasa yake cigaba da yakin sai ya bushe da dariyar farin ciki ya dubi zauwadu yace Ai babu yadda za ayi ku samu nasarar guduwa daga nan har ku tsira da rayuwarku,shekaru arba'in baya haka muke gadin gidan nan ku duka sai kun zama gawa,saura Imhal shi kadai a tsaye shima kuma yanzun nan zan koma na gama dashi kamar yadda na gama dakai. Koda jin wannan batu sai hawayen bakin ciki ya zubowa zauwadu ya dubi gawarwakin 'yan uwansu fursunoni dake kwance a kasa,kawai sai ya yunkura cikin matukar karfin hali ya bushe da dariya ya dubi marwatu yace,Tabbas mutuwa zanyi amma ko ba komai na jagoranci fursunoni mun karya alkadarin gidannan tunda gashi har mun samu nasarar fitowa daga cikinsa alhali babu fursunan da ya taba fitowa,ko ba komai kai marwatu zan mutu na barka da tabon yankan takobina a cikinka. Gama fadin haka keda wuya sai suka ji karar bude kofofin kurkukun guda goma sha biyu gami da gudun sawaye alamar cewa dakarun da ke cikin gidan sun faarga da mutuwar shugabansu saiyaru wanda aka bar gawarsa a dakin tuhuma don haka fitowa za suyi waje su kawowa su marwatu dauki. Koda Imhal ya jiyo sautin gudun dakarun daga cikin kurkukun sai ya zabura ya falfalo da azababben gudu izuwa inda su marwatu suke ya buda dakarun nasa da karfin tsiya yana saransu da banke su kai kace tamkar bai taba gajiya ba ko kuma a sannan kuma a sannanne ma ya fara yakin. Kafin marwatu ya juya ya tari Imhal tuni Imhal ya dako tsalle a sama ya doki gadon bayansa,sabo da karfin dukan sai da marwatu yayi tsalle sama ya bar kan tsuburin gaba daya ya fada cikin tekun,koda ganin haka sai ragowar dakarun nasa gaba daya suka ruga zuwa bakin tekun domin su ceto rayuwar marwatu. Damar da Imhal ya samu kenan ya sunkuya ya dauki zauwadu ya saba shi ae kafada ya ruga da baya izuwa inda jirgin ruwa yake ya daka tsalle ya dirga acikin jirgin ruwan ya warbar da zauwadu a ciki sannan yasa takobinsa ya sare igiyar da ta daure jirgin,aikuwa sai igiyar ruwa ta kada jirgi sai gaba. a dai dai wannan lokaci ne dakarun cikin kurkukun suka karaso kofar gidan a guje suna da yawa kuma a sannan ne aka tsamo marwatu daga cikin tekun aka dawo dashi kan tsibirin. Koda marwatu ya kyalla ido ya hango su Imhal acikin jirgi nesa kadan da tsibirin sai ya kwarara uban ihu yace A ruga a debo karnukan gidan,nan take kuwa aka je aka debo karnukan,Marwatu da karnukan tare da wadansu dakaru kimanin mutum dari biyu suka shiga wani jirgin dabam suka bi bayan jirgin Imhal. Lokacin da Imhal yaga igiyar ruwa ta kada jirginsu yayi gaba sa ya dawo inda ya warbar da Zauwadu ya iske shi yana ta kakarik mutuwa bai mutu ba,Imhal ya durkusa daf dashi ya kama hannayensa ya rike a lokacin da hawaye ya zubo masa ya dube shi yace "Haba ya kai abokina,sabo dame zaka tafi ka barni alhalin gashi mun sami nasarar guduwa daga kurkukun darul maut?" koda jin wannan batu sai Zauwadu yayi kakin jini ya tofar sannan ya dubi Imhal cikin karfin hali yace"ya kai abokina ina mai farin ciki da ya zamana cewa kai kadai ka tsira da rayuwarka daga cikin mu ba don komai ba sai don nasan cewa ka samu damar da zaka cika alkawarin dake tsakanin mu, duk ranar da ka riski matata suhailat ka bata labari irin rayuwar da mukayi a cikin kurkukun darul maut da yadda ka zama babban abokina kuma masoyina alhalin da farko mun kasance makiyan juna,ka sanar da ita yadda akayi muka samu nasarar guduwa daga wannan masifaffen kurkuku har izuwa sanda ajalina ya riskeni,ya kai Imhal idan kayimin haka ka gama yimin komai,kuma cikin kabarina zanyi bacci acikin kwanciyar hankali batare da bakin ciki ko nadamar komai ba,sabo da ko ba komai matata tasan cewa na mutu a filin daga a matsayin gwarzon jarumi,ka sani cewa ba wani laifi nayi baaka kawoni kurkukun darul maut face kawai na hana dakarun sarki Gurzalu zalunci a watavrana sanda suka shigo cikin gari suka kashe wani attajiri suka kwashe dukiyar gidansa kaf,suna shirin kashe iyalinsa ne na afka musu na ragargaje su suka gudu,nan take na taimaki iyalan attajirin na kaisu tashar jirgin ruwa suka hau jirgi suka bar garin gaba daya,tun daga wannan rana sarki Gurzalu ya dinga farauta ta ina buya har izuwa ranar da tsautsayi yasa aka zo aka kamani ranar da na auri suhaila" kodaZauwadu yazo nan a zancen sa sai yayi wa Imhal murmushin karshe sannan idanunsa suka kafe gaba daya jikinsa ya sandare ya zama gawa.Koda ganin haka sai Imhal ya kwanta akan gawar zauwadu ya rungumeta yana mai fashewa da matsanancin kukan bakin ciki kamar ba zai taba dainawa ba, sai da Imhal yayi kuka har ya gaji barci ya dauke shi bai sai ba,a lokacin da igiyar ruwa ta ci gqba da kada jirgin acikin teku yayi ta tafiya ba sassauci. . RIJIYA GABA DUBU Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 2C Al'amarin su marwatu kuwa,wadan da suka hawo wani jirgin tare da mugayen karnuka kimanin guda arba'in sai suka nemi jirgin su Imhal suka rasa a cikin tekun domin ya bace musu sakamakon iskar da ta ie kadawa mai karfin gaske ce gami da hazon da ake yi mai duhun gaske,amma sai suka cigaba da tuka jirgin nasu a haka,sai da suka kwana uku suna tafiya a cikin teku sannan suka iso bakin gaba a wata sakaliyar safiya,ai kuwa suna isowa suka yi kicibis da jrgin su Imhal a gefen tekun,cikin hanzari murwatu yasa aka saki wadan nan karnuka suka ruga izuwa cikin jirgin Imhal suna nemansa suna shinshine-shinshine,A lokacin ne murwatu da dakarunsa suka iso gaban jirgin suka caje cikinsa kaf amma basu ga Imhal ba sai alamar jinin zauwadu da ya zuba a kasa wanda har ya bushe,Kawai sai marwatu ya dago kai ya dubi dakarunsa yace Duk yanda akayi Imhal yana nan cikin dajin nan bai yi nisa ba amma abokinsa zauwadu ya mutu domin babu mutumin da zai zubar da jini mai yawa haka ya rayu,yanzuzamu bazama cikin wannan daji duk inda Imhal yake sai mun riske shi mun kashe shi,sai na cire kansa na tafi dashi izuwa darul maut domin sauran fursunonin gaba daya su gani ya zama gargadi a gare su don kada wani yace zai kara yunkurin gudu anan gaba,kuma nasan cewa sai sarki Gurzalu ya daukaka ni ya bani dukiya mai yawan gaske sakamakon wannan gagarumin aiki da zanyi kai inda hali ma a araye nake so na kamo Imhal domin na mayar dashi cikin darul maut mu sake tsare shi sabo da sarki ya fi son su sake haduwa a gasar jarumtaka wacce za ayi a birnin misra nan da cikar kwana goma sha daya,maza ku saki karnukan nan subi sawun Imhal domin suna iya jin kamshin mutum komai tazarar da ya basu kuma suna da karfin gudun da bai isa ya tsere musu ba.Koda jin wannan umarni sai dakarun dake rike da karnukan suka sake su suka sake rugawa izuwa cikin dajin suna masu haushi da falfala azababben gudu su marwatu suka bi bayan karnukan da gudu.Marwatu na cikin yin gudu sai raunin da ke gefen cikinsa ya motsa yaji wani azababben zafi da zugi ya shige shi,bai san sanda ya fadi a kasa ba,nan da na dakaru suka yanyame shi,koda ya kwaye rigarsa sai yaga ashe dinkin raunin ne ya farke,cikin tsananin takaici marwatu ya kwarara uban ihu ya dubi dakarun yace Maza ku tafi farautar Imhal kada ku dawo nan sai tare dashi,nan take kuwa suka bi bayan karnukansu da gudu shi kuwa marwatu sai ya bude jakar guzurinsa ya dauko zare da allura gami da garin magani domin ya sake gyara rauninsa. Al,amarin Imhal kuwa,a ranar da jirgin ya kawo shi gabar teku sai ya dauko gawar zauwadu ya fito da ita daga cikin jirgin ya nausa da ita izuwa cikin daji,sai da yayi tafiya mai nisa ya iso gaban wani katon dutse sannan ya sauke gawar ya haka kabari ya binne ta.A sannan ne ya kurawa kabarin idanu yana tuno duk abubuwan da suka faru a baya tsakaninsa da zauwadu a cikin darul maut,kawai sai hawaye ya fara zubo masa,yana cikin wannan hali ne ya jiyo sautin haushin karnukan nan na darul maut,da yake yasan irin haushin nasu kuma ya san tsananin gudunsu da irin mugun horon da aka basu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun,kawai sai ya mike tsaye zumbur! ya falfala da azababben gudu izuwa cikin dajin. Imhal ya dage iya karfinsa da iyawarsa har yana tashi sama yana shallake duwatsu da karyayyun bishiyoyi da suka fadi kasa amma koda ya waigo sai ya hango wadan nan karnukan suna neman cimmasa sai kawai ya kara kaimin gudun,Ba zato ba tsammani sai yaga wani katon rami mai tsananin zurfi a gabansa,kafin ya iya sarrafa kansa ya cije sai karfin gudun nasa ya rinjaye shi ya fada cikin ramin yana mai kurma uban ihu. Sa'ar da yayi kawai kawai kasan ramin cibiya ce ta ruwan teku amma yana tsunduma a cikin ruwan sai kansa ya bugu da wani dutse ya sume. Su kuwa karnukan suna isowa bakin ramin sukayi tirjiya suka fara haushi,sautin haushin nasu ya cika dajin gaba daya,wanda hakan ne ya janyo hankalin dakarun Marwatu suka rugo sashin da suke jin haushin cikin matsanancin gudu,suna cikin gudun ne suka hango karnukan sun kewaye wani rami suna ta haushi,don haka suka kara azama don nufar inda ramin yake. Lokacin da dakarun marwatu suka iso bakin ramin wanda Imhal ya fada sai suka iske karnuka a tsaye a wajen suna ta haushi sai suka leka kasan ramin,ai kuwa sai suka hango Imhal a kwance akan ruwa kuma ruwan yana tafiya dashi ko motsi bayayi kamar gawa. Cikin gaggawa wasu daga cikinsu suka gangara kasan ramin suka shiga cikin ruwan suka tsamo Imhal,suna fitowa dashi sai suka ga yana numfashi don haka sai suka yi sauri suka turmushe shi suka daure hannayensa da kafafunsa da sarkoki sabo da sun san cewa in har ya farfado baza su iya kamashi ba. Nan take suka daure shi suka kai shi can inda Marwatu yake zaune,da zuwan su suka iske Marwatu a kishingide ya gama dinke raunin dake cikinsa ya saka magani,koda Marwatu yaga dakarunsa sun dawo dauke da Imhal a daure cikin sarka sai ya kamu da tsananin farin ciki mara misaltuwa ya mike tsaye zumbur!ya kwarara uban ihu irin wanda manyan barade ke yi afilin yaki yayinda suka samu nasara akan abokin gabar su,kawai sai yasa aka warbar da Imhal gefe daya a kasa aka kyale shi har sai da ya farfado daga suman da yayi. Koda Imhal ya bude idon sa yayi arbuna da marwatu zaune a gabansa yana yi masa murmushin mugunta sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya yunkura da nufin ya gudu amma sai ya kasa sakamakon sarkokin da suka daure kafafuwansa da hannayensa Nan take yaji wani irin bakin ciki ya lullube shi,ya ayyana a ransa cewar da ma ya mutu a kokarin wannan guduwa da yayi daga kurkukun Darul maut da ya fiye NASA alheri. Kawai said yaji marwatu ya bushe da dariyar mugunta yana mai nuna shi da yatsa,daga can sai marwatu ya fara yiwa kansa kirari yana cewa Nine sa gudu maganin ki gudu,kuma nine sarkin darul maut mai RIJIYA GABA DUBU,ya kai wannan takadarin jarumi,kayi Sani cewa inda ba muyi nasarar kamoka ba da sai Na kashe kaina sabo da Kaine kadai jarumin da ya karya alkadarina,ya sami nasarar guduwa daga kurkukun darul maut Wanda Na shafe shekara da shekaru INA gadinsa,ban taba samun rauni ba a rayuwata said wannan karon don haka idan muka koma darul maut sai Na dandana mama azabar da bantaba dandanawa wani fursuna ba sai Na shigar da kai RIJIYA ta azaba mai GABA DUBU.Koda gama fadin haka sai marwatu ya mike tsaye yaje inda jarumi Imhal yake zaune ya shammace shi ya gabza masa wawan naushi a fuska ,nan take Imhal ya sulale a kasa sumamme. lokacin da Imhal

Chapter 3 of 7