Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
yazo nan a zancensa sai Imhal ya rungume shi suka fashe da kuka tare tsawon yan dakiku suna manne da juna sai daga can Imhal ya janye jikinsa daga cikin nasa ya dube shi yace Ya kai Abbana kayi sani bazan yi maka gardama ba bisa wannan shawara da kazo min da ita,sabo da nasan cewa ni bansan abinda kasani ba,domin duk wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi,yanzu sai mu koma bukkarmu mu debo kayanmu gaba daya,Imzanu ya gyada kai yace Ai na debo mana dukkan kudadenmu idan mun shiga cikin gari mayi guzuri,cikin alamun tsananin damuwa Imhal ya dubi imzanu a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah yace Haba ya kai Abbana ko ba komai na koma da baya ka nuna inda ka binne mahaifiya ta nayi mata bankwana tunda rabona da ita tun ina kankani,koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa Imzanu ya dubi Imhal yace ka gafarceni ya kai dana hakika naso nayi babban kuskure,zo muje na nuna maka kabarin mahifiyarka,ko da gama fadin haka sai tsoho Imzanu ya juya da baya suka koma izuwa can gaban bukkarsa suka cigaba da nausawa cikin daji suna bin wata hanya mai sarkakiya da yawa wacce shi kanshi Imhal a iya tasowar shi acikin daji bai taba sanin akwai wannan hanya ba,kawai sai tsintar kansa yayi acikin wadansu dogayen bishiyoyi masu manyan ganyaye wadan da suka sa dajin gaba daya yayi duhu,bisa dole suka kunna wuta a jikin itace don haska hanya,Imzanu ya cigaba da yiwa Imhal jagora sai gasu a bakin kofar wani kogon dutse mai girman gaske,da isowarsu bakin kofar kogon sai Imzanu ya haska cikin kogon yaga lafiyarsa sannan ya juyo ya dubi Imhal ya mika masa wutar itacen yace acikin wannan kogon na binne mahaifiyarka,ka shiga ciki zaka ga kabarinta sai kayi mata bankwana ni kam bazan iya sake kallon kabarin ta ba domin idan na gan shi zan tuno baya,kuma hakan zai iya jefani cikin mugun hali,cikin matukar sanyin jiki Imhal ya karbi wutar icen sannan uya kunna kai cikin kogon dutsen yana shiga kuwa ya hango kabarin na mahaifiyarsa,ka i tsaye ya tukari inda kabarin yake da isarsa gaban kabarin sai ya durkusa a gabansa ya kifa kansa akan kabarin sannan ya fashe da matsanancin kuka tsawon yan dakiku yana cikin wannan hali sannan ya dago ya kurawa kabarin idanu yace YAKE MAHAIFIYATA SABO DAME ZAKI TAFI KI BARNI LKACIN DA NAFI BUKATARKI FIYE DA KOMAI?ME YASA KIKA TAFI BAKI FADI KO WAYE UBANA BA?SHIN HAKA KIKE SO RAYUWATA TA KARE ACIKIN KADAICI, MARAICI GAMI DA TAKAICI KAMAR YADDA TAKI TA KARE?WANENE IMHAL?SUNAN DA KIKE AMBATA AKO DA YAUSHE? IDAN HAR BAZA KI IYA BUDAR BAKI KI GAYA MIKI AMSAR TAMBAYOYINA BA YANZU ZAN KASANCE MAI SAURARON FATALWARKI KODA ACIKN BARCINA,BAZAN TABA SAMUN SUKUNI DA KWANCIYAR HANKALI BA A RAYUWATA HAR SAI NA GANO ASALINA. Koda gama fadin hakan sai Imhal ya sake kifa fuskarsa akan kabarin ya dada fashewa da kukan bakin ciki. .RIJIYA GABA DUBU Littafi na daya 1 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 1C .Sai da ya jima yana kukan sannan ya mike tsaye ya fice daga cikin kogon dutsen yana waigen kabarin yana zubar da hawaye,har ya isa bakin kofar kogon zai fita sai ya waigo ya dubi kabarin yace Yake ummata nayi miki alkawarin zan rayu acikin wannan duniya komai RINTSI DA TSANANI har izuwa lokacin da zan gano asalina na dawo har nan na sanar dake,koda gama fadin haka sai ya juya ya fice daga cikin kogon yana fitowa ya iske tsoho Imzanu a zaune ya kishingida da jikin kogon har ya fara bacci sabo da gajiyar yaar tafiyar da yayi,motsin takun sawun Imhal ne yasa ya farka daga baccin cikin yanayin damuwa,Imzanu ya dubi Imhal yace yakai dana kayi sani cewa na gaji ainun kuma gashi tsufa yana tabani ina ganin cewa yanzu bazan iya takawa da kafafuna ba yanzu sai dai mubarwa gobe da safe amma yin hakan yana da hadari,domin ina ji a jikina cewar sarki zai iya turowa a kamaka domin ya tsareka a kurkukunsa,don kada ka gudu kabar garin,kafin tsoho Imzanu ya gama rufe bakinsa sai suka jiyo sautin takun sawu daga can nesa,alamar takun sawu ne ta mutane da yawa kuma inda suke aka durfafo,koda jin haka sai Imhal yayi wuf ya suri tsoho Imzanu ya goyashi a bayan sa ya daure shi tamau,sannan ya ruga izuwa kan wata bishiya mai tsawon tsiya wacce can karshenta ganyayene manya manya masu duhuwa,kamar kadangare na hawa bango haka Imhal ya dinga hawa kan bishiyar da gudu kai kace ba sama yake hawa ba,cikin dakiku kadan ya isa karshen bishiyar yayi lambo akan wani reashe,shi kansa Imhal idan ya leko kasa baya iya jiyo motsin komai sabo da nisa,A dai dai wannan lokaci ne dakaru acikin bakaken kaya kimanin su dubu suka iso dai dai kofar kogon dutsen da gudu,dukkanninsu suna rike da tagobi tsirara kuma sun rufe fuskokinsu,koda tsoho Imzanu ya hango wadannan dakaru sai ya sai zuciyarsa ta buga da karfin gaske ya firgita ainun ya fara kokarin tuno da wani al amari wanda ya faru a shekarun baya,amma sai kwakwalwar tasa ta kasa tuno komai.Dakarun masu bakaken tufafi na isowa suka tsaya cirko cirko suna kallo kallo da waige waige,nan dai shugabansu ya rarraba su izuwa gabar da yamma kudu da arewa,suka bazama neman inda su Imhal suke,har cikin kogon dutsen inda kabarin mahaifiyar Imhal yake sai da suka shiga.A dai dai wannan lokacine Imhal yayi kundunbala ya sallamo kasa daga kan doguwar bishiyar,karar dirar kafafunsa kasa ne yasa dakarun suka farga suka baro inda suke da gudu,amma kafin su iso inda suka bari tuni Imhal ya falfala da azababben gudu goye da tsoho Imzanu,Wohoho!kafa me naci ban bakiba?idan zan ta tarar da muje mu sai abinda hali yayi,duk tsananin gudu irin na Imhal sai gashi wadannan dakaru suna rufa masa baya har ma suna nema su cimmasa amma sun kasa,koda dakaru suka ga an shafe dakiku masu yawa sun kasa cimma Imhal duk da tsananin nacinsu gami da horon da suka samu na juriya sai suka fara zaro kibiya suna danawa akan baka suna harbawa Imhal,Imhal na cikin gudu sai yaji kibiyoyi suna wucewa ta samansa da gefensa,har ma sai da wata kibiya ta karci gefen kunnensa jini yayi tsartuwa,al amarin da yayi matukar girgiza hankalinsa kenan ya kara karfin gudunsa,amma abinda ya kara tayar masa da hankali shine,tunowa da tsoho Imzanu wanda ke goye a bayansa wanda ako da yaushe bisa tsautsayi kibiya zata iya zuwa ta soke shi,koda ya aiyana hakan sai yasa hannayensa ya juyo da tsoho Imzanu daga bayansa ya dawo dashi gabansa ya ci gaba da falfala gudun da haka,kaico! Tsautsayi ba a yi masa barci!Imhal na cikin wannan azababben gudu ne kibiya tazo ta soke shi a duga duginsa na kafar hagu take kibiyar ta ta nutse ta hudo waje,Imhal ya kwarara uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da yaji,yayi taga taga kamar zai kife kasa amma sai ya yunkura cikin zafin nama da tsananin juriya ya take kafar a haka tana zubar da jini yaci gaba da gudu.Naci damben kuturu!koda dakarun nan suka ga Imhal yaki faduwa kasa yaci gaba da gudu duk da cewar kibiyar ta soke shi a kafa sai suma suka ci gaba da falfala gudu suka dada zubo masa ruwan kibbau ba sassauci,Har Imhal ya iso daf da kafar cikin gari dakarun basu cimmasa ba kuma babu wata kibiya data soke shi amma fa yana jin mugun zugi acikin kafarsa tamkar ya sare kafar da hannunsa ya yar da ita.koda dakaru suka ga an iso cikin gari sai suka samu lokuna suka shiga suka buya suka sauya tufafin jikinsu suka sa irin na mutanen gari suka bude fuskokinsu,sannan suka rarrabu suna masu dada ci gaba da farautar Imhal.Imhal na shigowa cikin birnin kisra goye da Imzanu sai ya fara sarewa yana jan kafa da kyar,cikin hanzari ya doki kofar wani gida dake rufe da hannunsa guda, take kofar ta balle ya kunna kai ciki ya yunkura zai kwance Imzanu daga jikinsa sai yaga ashe ya suma sakamakon wata kibiya data soke shi a gefen wuyansa,cikin tsananin dimaucewa Imhal ya sauke Imzanu kasa ya wangame baki zai rusa ihu don a zatonsa Imzanu ya mutune,sai kawai yaga wata tsaleliyar mata ta rugo da gudu daka can cikin gidan ta dube shi tana mai yi masa inkiyar yayi shiru. Sai da tazo daf da shi sannan tayi masa rada a kunne tace tsohonka bai mutu ba,zan iya ceto rayuwarsa ni likita ce,bari nayi sauri naje na batar da shaidar da zata sa a gane ka shigo nan,maza ka shigar da tsohon can cikin dakina ka kwantar dashi kada ka taba shi,tana gama fadin haka sai ta dauki wani tsumma ta ruga waje,cikin sauri Tsaleliyar matar taje ta goge duk jinin kafarsa,daya zuzzuba a kofar gidan,sannan ta sake rugawa izuwa cikin gidan ta mai da kofa ta saka sakata.Faruwar haka ke da wuya sai ga wadannan dakaru da suka biyo Imhal sun iso wajen da gudu,gaba dayansu sai suka tsaya suna yin duru duru suna waige waige da hange hange,suna jiran karasowar shugabansu domin ya basu umarni bisa abinda za suyi Al'amarin Imhal kuwa,lokacin da ya kinkimi tsoho Imzanu ya shige dashi izuwa dakin wannan tsaleliyar mata a dimauce sai ya shimfide shi akan wani babban teburi na katako,a sannan ne ya dubi ko ina a cikin dakin nan take ya gamsu cewa daki ne na likita,don babu komai acikinsa face tarkacen kayan likitoci,kawai sai ga matar ta shigo cikin dakin da gudu,ko kallon Imhal batayi ba ta ruga izuwa kan tsoho Imzanu ta shiga yi masa aiki,nan take ta cire kibiyar dake wuyan nasa,ta zuba wani garin magani akan raunin nan take jini ya daina zuba,duk wannan abu da take Imhal yana tsaye a gefe daya ya zuba mata idanu kawai cikin tsananin mamaki,domin bai san dalilin da yasa ta taimake shi ba alhalin gashi ma yayi mata laifi ya karya mata kofar gida da karfin tsiya,kuma gashi bata taba ganin shi ba sai yau,Bayan gama shudewar dakiku dari da ashirin da gama yiwa Imzanu magani sai ya farfado ya bude idanunsa,koda ganin haka sai farin ciki ya lullube Imhal ya kama yiwa matar godiya,A dai dai wannan lokaci ne suka ji ana kwankwaso kofar gidan da karfi,Al'amarin da ya tayar da hankalin Imhal ya yunkura zai zare tagobinsa,sai matar tayi masa nuni da kada ya zare tagobin,ta dube shi tace ka bani yardarka ina mai tabbatar maka da cewa komai dadewa zaka dawo ka iske mahaifinka a cikin koshin lafiya,maza kayi sallama da tsohon naka zan nuna maka hanyar da zaka bi ka fice daga cikin gidan nan ba tare da wani ya ganka ba,cikin tsananin mamaki Imhal ya dubeta yace wacece ke kuma sabo dame kika ce ci rayuwarmu nida wannan tsohon nawa?matar tayi murmushi mai taushi ga Imhal tace Ni na sanku fiye da shekaru bakwai baya,kune baku san ni ba,kuma na dade ina bibiyarku a duk sanda kuka shigo garinnan,tana gama fadin haka ne suka ji anci gaba da buga kofar gidan da karfin gaske,A guje matar ta kama hannun Imhal ta jashi izuwa cikin wani dakin daban yana waigen tsoho Imzanu yana hawaye,shima Imzanu ya bishi da kallo yana zubar da hawaye,domin duk su biyun sun san cewa abu ne mai wuyar gaske idan har zasu sake saduwa da junansu,da shiga su Imhal cikin wannan daki na biyu sai sukayi arba da wata rijiya a bude wacce ta ciko da ruwa har baki,kai sai matar ta dube shi tace kayi nitso izuwa can kasan rijiyar zaka samu hanya wadda zata kaika har izuwa kogon Ishmal dake can bayan gari,daga nan sai ka nausa daji kayi kokarin ficewa daga nahiyar nan gaba daya,kada ka kuskura ka dawo garinnan sai bayan anyi gasar Jarumta a birnin misra koda gama fadin haka sai matar ta juya da baya,cikin sauri Imhal ya ruko hannunta,ta waigo ta dube shi cikin mamaki yace mata mene sunanki? Matar yai murmushi tace mishi sunana ZUMAIRA IBINI IMHAL.Koda jin wannan suna sai idanun Imhal suka zazzaro ya kasa sakin hannunta kuma a sannan ne suka ji anbugo kofar gidan da karfi ta fadi rikica gaba daya,koda ganin haka sai matar tasa kafarta ta doki kirjin imhal ya fada da baya cikin rijiyar,kawai sai ya nutse izuwa karkashinta,cikin hanzari matar ta juya ta koma baya da gudu.Tana isowa falonta ta iske tsoho Imzanu zaune akan teburin cin abinci yana shan ruwan Inibi kuma har ya sauya tufafin jikinsa,kuma ya sauya kamanninsa domin ya shafe gemunsa da sajensa da shuni kamar bashi ba,wadansu karti kimanin su arba'in na tsaye a gabansa daya daga cikinsu nayi masa tambayoyi,kawai sai Zumaira ta dakawa kartin tsawa ta dube su tace,su waye ku akan wane dalili zaku karya mana kofar gidanmu ku shigo?koda jin haka sai Dakarun suka waigo izuwa kan zumaira suna muzurai kamar saci babu har sun zare takubbansu zasu afka mata sai daya daga cikinsu ya daga musu hannu suka dakata sannan ya matsa daf da Zumaira ya dubeta a fusace yace muna neman wani saurayi da wani tsoho mai furfura a gemunsa ki gaya mana gaskiya idan sun ahigo gidannan kun boye su domin idan kuka yi mana karya kuma mukayi bincike muka gansu sai mun kasheku,koda jin haka sai Muzaira tayi guntun murmushi tace ai sai ku duba ku gani,nan take katti suka bzama ko ina amma basu ga kowa ba,sannan suka fice daga gidan gaba daya. . . RIJIYA GABA DUBU Littafi na daya 1 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 1D .Muzaira ta dubi tsoho Imzanu kawai sai taji ya fashe da kuka,al amarin da ya karya zuciyarta kenan ta kamu da tsananin tausayinsa don haka sai ta dube shi tace Ya kai Imzanu ka kasance mai gaskiya da juriya acikin duk irin yanayin da ka tsinci kanka aciki,koda jin haka sai Imzanu ya dago kai ya dubeta cikin mamaki yace Ya akai kika san sunana?yayin da muzaira taji wannan tambaya,sai nan take idanunta suka ciko da kwallah sannan ta dubi Imzanu tace Mahaukaciyar da kayi jinya acikin daji har ta haifi wannan saurayi da kuke tare yayata ce uwarmu daya ubanmu daya,kuma ita ce babba a wajen mahifinmu wanda shine sarkin kisra na da,kafin azzalumin sarkinmu na yanzu ya kashe shi ya hau kan karagar mulkinsa.Gaba daya zuri armu sai da sarki GURZALU ya kashe su,nice kadai nayi saura,nima albarkacin karfin sihirin tsafin da nake dashine yasa na tsira da rayuwata,Ba wani abune yasa yar uwata ta haukace ba face a gabab idanunta aka kashe mijinta Imhal aka yi masa yankan rago,sannan aka yanka iyayenmu da dukkan zuri'armu,tana ganin wannan al'amari ne ta haukace nan take,amma duk da haka sai da aka yi mata yankan rago akasa dakaru sukayi badda kama suka dauki gawarta suka kai daji suka yar,Abinda yasa aka dauki gawarta aka kaita daji shine,Ramin da aka haka aka saka gawar mijinta da ta sauran zuri'armu ya cika.Duk abinda ya faru da yar'uwata Shulaira na gani a madubin tsafina,kuma duk naga irin dawiniyar da ka sha da ita shi yasa yanzu na taimake ku na kubutar da Imhal,ina mai tabbatar maka da cewa Imhal ya kubuta daga sharrin sarki Gurzalu domin zai fice daga cikin garin nan gaba daya ta cikin wata rijiya dake cikin gidannan.koda Muzaira tazo nan a zancenta sai tsoho Imzanu ya cika da tsananin mamaki gami da tsananin bakin ciki,daga can kuma sai ya dubi Muzaira cikin alamun damuwa yace Ke kuwa mai yasa tun yar'uwarki na raye a wajena a daji baki ziyarce ta ba,kuma me yasa yanzu baki gayawa Imhal cewar ke kanwar mahaifitarsa bace?Muzaira tayi ajiyar zuciya tace Ai ina fita daga cikin garinnan sihirin tsafina zai karye sarki Gurzalu ya gano inda nake ya turo a kashe ni,dalilin da yasa ban sanar da Imhal ni uwace a garshiba shine,idan na gaya masa bazai tafi ba yanzu kuma idan yaki tafiya ni dashi halaka zamuyi,koda jin haka sai hankalin tsoho Imzanu ya tashi fiye da ko yaushe ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Lokacin da Imhal ya nutse izuwa cikin karkashin wannan rijiya ya isa can kasanta sai ya kama laluben hanya,nan da nan ya fara fita daga hayyacinsa sakamakon rashin numfashi,amma cikin sa a sai yaga wani kifi yas shigo cikin rijiyar ta cikin wata kofa,cikin sauri ya kunna kai cikin kofar sai ya ganshi akarkashin wani katon kogi,ciin sauri ya taso sama domin ya shaki numfashi,aikuwa yana dagowa sama yaji an gabza masa duka da kulki a fuska,take jini yayi feshi daga cikin bakinsa da hancinsa nan take ya baje a saman ruwa sumamme. Sa'adda Imhal ya farfado sai ya tsinci kansa acikin wani matsatstsen daki kwance a kas,gefensa ga wani garjejen saurayi a zaune ya kura masa idanu,cikin dimaucewa da mamaki imhal ya mike zaune zumbur ya karewa dakin kallo tsaf,sannan ya dubi garjejen katon saurayin dake gabansa yace,Ina ne nan?Yaya akayi nazo nan?koda jin wannan tambaya sai katon ya bushe da dariyar mugunta,maimakon ya baiwa Imhal amsar tambayarsa sai ya mike tsaye ya damki makoshin Imhal da hannu daya ya daga shi sama tamkar ya daga sillan kara,sai gashi Imhal ya fara kakarin mutuwa,kawai sai garjejen katon yaci gaba da kyalkala dariyar mugunta sannan ya daga kansa sama yana duban Imhal yace,Kai yaro yau ka shigo kurkukun darul maut na birnin kisra,kurkukun da ba a fita sai dai gawa ta fita kuma gashi kayi rashin sa a ka shigo dakin dodon kowa a gidannan ZAUWADU,a dai dai wannan lokacine sauran fursunonin dake cikin sauran dakunan gidan suka kama lekowa dakin Zauwadu domin suga mai karar kwanan da aka kawo,ashe duk fursunan da aka kaishi dakin Zauwadu kawai so akeyi a kashe shi,Ba zato ba tsammani kawai sai Zauwadu yaji Imhal ya gabza masa mugun duka a fuska da kafarsa guda,Sabo da karfin dukan sai da Zauwadu yaga taurarin wuya bai san sanda ya dimauce ba ya saki wuyan Imhal ya fado kasa yana tari,koda Zauwadu ya shafa fuskarsa yaji jini sai ya fusata ainun ya juya bayansa inda Imhal ke kwance yana mai yin kururuwa kuma yakai masa mugun taku da kafa,cikin bakin zafin nama Imhal ya goce ya mirgina can gefe daya ya shammaci Zauwadu ya buga masa kafa akan marenansa,take Zauwadu ya sulale kasa sumamme,koda ganin abinda ya faru sai gaba daya fursunonin gidan suka daina shewa da dariya suka kame kamar gumaka sabo da tsananin mamaki,Ba komai ne ya jefa fursunonin cikin tsananinb mamaki ba face ganin yadda aka samu jarumin da ya sumar da Zauwadu.Gaba daya fursunonin dake cikin kurkukun suna tsananin tsoron Zauwadu,kai ba ma fursunoninba su kansu dakarun dakaru dake tsaron fursunonin shakkarsa suke domin mutum goma basa iya ladaftar dashi sai dai ashirinb zuwa sama,duk da cewa dakarun kartine majiya karfin gaske wanda sai da aka zabo su,ko ya ya wani abu ya hada fursuna da Zauwadu to fa sai dai a sanya sunansa acikin matattu don ansan cewa Zauwadu ya kashe shi sabo da zaluncinsa,karfinsa da rashin imaninsa.Lokacin da Zauwadu ya farfado daga dogon suman da yayi yaga Imhal a zaune acan gefe daya kan shimfidarsa ya harde kafafu tamkarma ba fada sukayi ba sai ya fusata ainun musamman da ya waiga baya yaga gaba daya sauran fursunonin dake cikin sauran dakuna sun zubo idanu suna kallonsa,nan take zauwadu ya yunkura zai sake afkawa Imhal kawai sai gani yayi Imhal ya daka tsalle sama kamar dan biri ya dirga akan wuyansa ya shake shi,duk da tsananin karfi irin na Zauwadu sai gashi ya kasa kwacewa kuma idaninsa sunyi bulu-bulu sunyi jawur sai gashi yana dukushewa kasa yana kakarin mutuwa.Koda Imhal yaga Zauwadu na neman mutuwa sai ya sake shi ya zube kasa magashiyan yana numfashi sama-sama,take imhal ya nuna Zauwadu da dan yatsa ya dubeshi yace idan ka kara kawo miki wargi a karo na uku sai na kashe ka,Tun daga wannan rana Imhal ya zama shugaban fursunonin gidan gaba daya ya zamana cewa kowa yana shakkarsa ana yi masa ladabi da biyayya.A bangaren shugaban dakarun dake dake tsaron kurkukun kuwa,sai ya dauki kiyayyar duniya ya dora aka Imhal ya zamana cewa haka kawai sai yasa a kama Imhal a daureshi a tsaye da sarkoki ai ta dukansa da itatuwa har sai ya suma kamar gawa sai dai fursunoni su zo su dauke shi suyi masa magani,wani lokacin kuma ai ta gana masa bakar azaba iri-iri wacce duk fursunan da akayiwa ita sai ta zama sanadin ajalinsa amma sai gashi imhal yana jureta,duk da tsananin juriya irin ta Imhal sai da ya dinga ramewa yana yawan ramewa yana yawan rashin lafiya sabo da tsananin wahalar da yake sha,kai in ba don ma fursunonin suna matukar kaunarsa ba kuma suna gadin rayuwarsa ba,da tuni dakarun gidan sun kashe Imhal,komai rashin tausayin mutum idan yaga irin halin da imhal ya shiga sai ya tausaya masa,ba komai ne yasa fursunonin gidan suke matukar kaunar jarumi Imhal ba face zuwansa ya kawo adalci a tsakaninsu ya zamana cewa mai karfi ya daina zalunta mara karfi,a da,ko abinci fursuna ya karbo ya zauna zaici sai kaga wanda ya fishi karfi yazo ya kwace ya hada da nasa sai dai wancan ya kwana da yunwa,haka kuma akwai fursunoni masau mugayen dabi'u na yin luwadi ga wadan da sukafi karfi amma duk sai da Imhal ya hana yin wadannan mugayen abubuwa,Zauwadu da ya kasance babban makiyin Imhal sai da ya zamo babban amininsa kuma abokin shawararsa. . RIJIYA GABA DUBU Littafi na daya 1 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 1E Wata rana bayan an kama Imhal an kai shi wani daki na musamman inda ake yiwa fursunoni azaba,anyi masa dukan kawo wuka,sai aka dawo dashi dakin su aka warbar dashi a kasa jina-jina yana numfashi sama-sama kamar zai mutu,cikin dimaucewa Zauwadu ya shiga yi masa magani,da kyar ya samu ya tsayar da jinin da yake zuba a jikinsa,koda Imhal ya farfado ya dawo cikin hayyacinsa sai ya bude idanunsa dakyar ya dubi zauwadu yace Gobe idan na samu karfin jikina da cikin dare zan gudu daga cikin kurkukun nan,idan zaka iya bi na kazo mu gudu tare mu tsira tare,koda jin wannan batu sai idanun Zauwadu suka zazzaro ya kamu da tsananin tsoro ya dubi Imhal cikin damuwa yace Ya kai abokina kayi sani cewa tunda aka gina kurkukun nan tsawon shekaru arba'in a baya ba'a taba samun fursunan da ya samu damar guduwa ba daga cikinsa,ta ya ya kake tsammanin kai zaka iya?ka dubi katangar gidannan wacce ta kasance mai tsananin tsawo da kauri,Ta ya ya zaka iya haurata ko fasata ba tare da anzo an kamaka ba?ka dubi yawan dakarun dake rangadi a harabar gidan nan a duk dare da rana,sannan ka dubi mugayen karnukan da suke gadin ko ina wadan da suka kasance manya tamkar kuraye sannan gashi sun samu da horo na musamman na iya kama mai laifi gami da tsananin karfin gudu gami da juriyar su.Idan baka sani ba to ka sani cewa gaba dayan kurkukun nan akan tsibiri yake,kuma shi tsibirin akan tsakiyar teku yake,idan ma ka samu nasarar fita daga cikin kurkukun nan ta yaya zaka iya ketare wannan teku har ka tsira da rayuwarka?Ai dabbobin dake cikin tekun nan ma kadai da sanyin teku sun isa su hallaka ka.Tabbas wannan kurkukun yaci sunansa DARULMAUT wato gidan mutuwa,duk fursunan da ya shigo gidan nan ya san cewa ya shigo gidan ajalinsa.Lokacin da Zauwadu yazo nan a zancen sa sai kawai yaji Imhal ya bushe da dariya al'amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan ya kura masa idanu kawai ya kasa cewa komai,daga can sai Imkal ya nutsu ya dube shi yace Babu wani abu da bazai yiwu ba a doron kasa,kawai abinda nakeso dakai shine ka nemo mana kudade masu yawa wadan da zamu iya siyan ma'aikatan gidan nan,babu abinda kudi bazai iya yi ba.Koda jin wannn batu sai jikin Zauwadu yayi sanyi ya sunkui da kansa kas ya fada kogin tunani,Daga can sai ya dago kai ya dubi Imhal yace Ya kai abokina ko na bika ko ban bika ba mutuwa zanyi acikin gidan nan don haka gwara ma na bika din tunda babu wanda yasan abinda zai faru gobe,naga misali akan haduwa ta dakai,ban taba zaton za'a iya samun fursunan da zai zo gidan nan ba har ya iya kaini kas sai gashi ma kai ka kaini kas har da sumar dani alhalin babu wan "DA" mai karfina kowa tsorona yake,dukkan fursunoni da ma'aikata amma sai gashi andawo andaina tsorona kai ake tsoro ana yi maka ladabi da biyayya.Ko da jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Imhal ya rungume Zauwadu suka bushe da dariyar murna tare.Daga can sai Zauwadu ya janye jikinsa daga cikin na Imhal ya dube shi cikin nutsuwa a karo na biyu yace Ya kai abokina kayi sani cewa da dangari akan ci gari,a matsayina na fursuna da ya shekara ashirin da uku a cikin gidan nan nafi kowa sanin sirrin kurkukun nan acikin fursunoni domin babu wanda yayi dadewata kuma nafi kowa sanin irin ma'aikatan da ya kamata mu hada kai dasu wajen samun nasarar wannan gagarumin aiki da mukeyi,Ina nufin dole ne mu zubo ma'aikatan da na tabbatar da cewa suna da kwadayin abun duniya,to amma inda matsalar take shine ta yaya zamu iya samo kudaden da zamu biya ma'aikatan su bamu hadin kai?Abu na biyu shine,har yanzu baka gaya min yadda zamu iya ketare tekun da ya zagaye gidannan bayan mun sami nasarar fita wajensa ba?Sa'adda Imhal ya ji wannan tambayoyi sai yayi murmushi yace abinda nakeso dakai shine ka bini a sannu zamuyi komai daki-daki da idanunka zaka ga amsoshin duk wadannan tambayoyin da kayi min yanzu. Abu na farko da nakeso mu farayi shine ina so mu hada baki da masu dafa abincin gidan nan,su zuba banju acikin abincin dakarun da suke gadin dakin shugaban dakarun gidan nan,domin mu samu damar shiga mu balle akwatin da yake ajiye kudin hidimar gidannan aciki,na sani cewa akalla baza mu rasa dinare dubu dari ba acikin wannan akwatin wadannan kudade sun isa mu siye duk mutanen da mukeso suyi mana aiki,Zauwadu ya gyada kai yace tabbas zasu ishe mu,amma ta yaya zamu samu amincewar ma'aikatan da suke dafa abinci su zuba banju acikin abincin?Imhal yace baza mu iya yin wannan aiki mu biyu kacal ba,dole sai mun nemi hadin kan yan'uwan mu fursunoni akalla mutum goma,cikin tsananin firgici Zauwadu yace idan muka gayyato mutane cikin wannan aiki namu za a iya samun rashin sirri a ciki,acikin mu za a iya samun munafikin da zai zagaye ya tona asirin mu,Imhal ya gyada kai yace ai ba kowa zamu tabo ba sai wanda mukasan ya gari da zaman gidannan kuma yana da taurin rai gami da sai da rai,haka kuma duk wanda ya shigo cikinmu zamu gaya masa idan har ya tona mana asiri aka kamamu hukuncin kisa ne akan sa,koda jin wannan batu sai Zauwadu yayi murmushi yace hakika kwakwalwarka tana aiki sosai to idan muka samu mataimakan ta yaya zamu samu hadin kan masu dafa abincin?Imhal ya sake murmushi a karo na biyu yace ka sani cewa masu dafa abincinnan fursunoni ne yan'uwanmu dole ne mu firgita su mu kashe daya daga cikinsu

Chapter 2 of 7