Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
yi mata aiyuka iri-iri, kwatsam! sai ta hango wata kuyanga ta taho za ta gifta ta gabanta,tana kallon fuskar kuyangar sai ta ga ai bakuwa ce domin bata taba ganin fuskarta ba.Al'amarin da yai matukar bata mamaki kenan domin babu yadda za'ayi a kawo bakuwar kuyanga cikin turakarta ba tare da an sanar da ita ba,Har kuyangar ta gifta ta zata wuce sai Shumaira ta Sha gabanta da sauri suka dubi juna,tsawon 'yana dakiku sannan Shumaira tace, Wacece ke kuma yaushe aka kawoki nan,muhallina ba tare da sani na ba?Koda jin wannan batu sai kuyangar tayi murmushi cikin alamun takama da yarda da kai tace,Ni ba kuyangar ki bace hanya ce ta biyo dani ta nan,bani hanya na wuce abina idan ba so kike ranki ya baci ba, Koda jin wannan batu sai ran Gimbiya Shumaira ya baci bisa ganin cewa tana matsayin'yar sarki amma kuyanga tayi mata rashin kunya, kawai sai ta daga hannu da nufin ta sharawa kuyangar mari,amma sai taji hannun nata ya makale a sama ta kasa sarrafa shi,kuma taji an matse hannun nata,wani irin mugun zugi da radadi na shigarta bata San sanda ta fara ihu ba,Abinda ya daure mata kai shine,duk ihun da take yi babu mai jinya,asalima babu wanda yaga abinda ke faruwa, nan take tsoro ya kama Gimbiya Shumaira ta fara tunanin cewa,lallai wannan kuyanga da ke gabanta ba mutum bace aljanna ce. Koda ta ayyana hakan a cikin zuciyar ta sai ta dubi bakuwar kuyangar cikin tsananin dauriya tace,Ki gafarceni banyi dai-dai ba,kafin ta gama rufe bakinta sai taji an saki hannun ta kuma ta daina jin zafin komai, kawai sai ta sake duban kuyangar tace,"Ya ya akayi kika sami damar shigowa gidan nan ,alhalin babu wani aljani da ya taba shigowa tun farkon gina shi? " sanda bakuwar kuyangar taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace,Ni ba aljana bace, mutum ce ni kamar ke,idan har kina so kisan ko ni Wacece ki kaini cikin turakar ki mu zauna muyi wata magana, bayan hakan ne za kisan ko ni wace ce kuma zan taimaka miki na kaiki har inda aka tsare bakon jarumi ki ganshi ba tare da kin fuskanci wata matsala ba,Koda jin wannan batu sai murna ta kama Shumaira nan take ta kama hannun kuyangar ta ka ta izuwa can cikin turakar ta,da shigarsu cikin kuryar dakin kuyangar ta zauna tana mai yin hamma alamar cewa tana jin yunwa da bacci, har Shumaira ta budi baki za tayi magana sai ta dakatar da ita da hannu tace,Kafin muyi maganar komai sai naci na koshi, maza kisa a kawo min abin kalaci,Koda jin haka sai gimbiya Shumaira ta kwalawa wata kuyangarta kira tace da ita,taje ta kawo mata abin kalaci,Koda jin wannan umarni sai mamaki ya kama kuyangar mai suna SALIFAT, Salifat ta sunkui da kai kasa tace,"ya shugabata me za kiyi da abincin kalaci yanzu alhalin dazu na kawo miki kika ce bakya bukatar?" Shumaira ta dakawa Salifat tsawa tace,"Ina ruwan ki,yanzu nake bukatar cin abincin, maza kije ki dauko mini kafin raina ya baci".Cikin hanzari kuyangar ta juya da sauri ta je ta dauko abincin bisa faranti a cikin manyan kwanuka guda biyu na dinare, kuyanga Salifat tazo ta ajiye farantin a gaban bakuwar kuyangar amma kuma ba ta ganta ba,bata ma San cewa akwai wani mutum a cikin dakin ba face Gimbiya kadai,Koda kuyangar ta ji kamshin abinci ya doki hancinta sai ta fado kasa Daga kan kujera ta bude kwanukan abincin ta duma hannu a ciki ta kama ci kamar wacce ta shekara da yunwa, kafin a jima ta cinye kusan rabin abincin dake cikin kwanukan biyu wanda a ka'ida mutum shida ne ke iya cinye shi,tana gamawa ta dauki tambulan din ruwan ta shanye shi tas ya zama ko digo daya bata rage ba sannan tayi wata katuwar gyatsa,kai da gani kasan cewa bata saba cin abinci mai daraja ba irin wannan, A sannan ne bakuwar kuyanga ta mike tsaye ta koma kan kujerar ta zauna sannan ta fuskanci Gimbiya Shumaira ta dubeta cikin nutsuwa tace,"sunana MUZAIRA, kuma ni 'yar uwar matar sarkin Kisra ce na da,wanda sarkin yanzu ya kashe ya hau karagar mulkinsa. "Koda jin wanne batu sai Shumaira ta mike tsaye zumbur! cikin alamun tsoro da mamaki, kuma jikinta ya kama tsuma tana mai nuna MUZAIRA da dan yatsa bakinta na rawa tana so tace wani abu amma sai ta kasa,Koda ganin haka sai MUZAIRA tayi murmushi tace," kwantar da hankalin ki ya ke Gimbiya Shumaira, ban zo nan dan cutar da ke ba,sai domin na taimake ki kamar yadda nayi alkawari,kuma kema ki taimake ni,wannan bakon jarumi da kika kamu da son sa wato jarumi Imhal da ne a waje na,domin MAHAIFIYARSA yayata ce,uwar daya uba daya,kuma na biyo shi ne izuwa birnin misra domin na ceci rayuwar sa a cikin GASAR JARUMTAKAR da ake yi,Tabbas a dazu sanda ya fafata da sadauki Darwaz, in ba don na kawo masa dauki ba da tuni Darwaz ya hallaka shi da karfin sihiri, inda kin lura za kiga cewar jarumi Imhal ya tsaya cak a waje daya sanda Darwaz ya rugo da gudu izuwa kansa a wannan lokaci wata guguwar sihiri ya jefo masa ta kanannadeshi ya kasa Koda motsa hannayensa,nice na kawar masa da guguwar a lokacin da saura kiris Darwaz ya gama dashi. Yanzu zan gaya miki wani babban sirri wanda ba ki San shi ba,kuma labarin zai girgiza kwakwalwarki, da farko dai nice barauniyar da ake ta nema a cikin garin nan da kewayensa wacce tayi wa sarki gurzalu sata, kuma ba wani abu na sace masa ba face wani GURU na TSAFI indai yana tare da wannan grun tsafi babu wani mahaluki da ya isa ya samu nasara a kansa,ko ya iya cutar dashi, yanzu gashi Gurun ya dawo hannu na, koda MUZAIRA tazo nan a zancen ta sai ta yaye rigar da ke jikinta, take Shumaira tayi arba da gurun tsafin zagaye a kugun MUZAIRA, MUZAIRA ta saki rigar ta rufe gurun sannan ta cigaba da cewa, Albarkacin wannan guru ne na samu damar shigowa gidan nan ba tare da kowa ya ganni ba,kuma abinda sarki gurzalu bai sani ba shine, tun kafin su shigo cikin garin nan na sace gurun a wani lokaci da suka ya da zango a cikin daji ya fita daga cikin tantinsa yaje yayi wanka a wani rafi.RIJIYA GABA DUBU Littafi na uku 3 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 3D . Dama ina biye dasu tun daga can birnin kisra a cikin siffar wata tsuntsuwa basu sani ba,A lokacin na shiga cikin tantin nasa,kuma nayi sa'a na iske akwatinsa a bude, ya manta bai kulle ta ba bayan ya dauki mayafin da zai tsane ruwan jikinsa bayan yayi wankan, Bai taba mancewa da kulle wannan akwati ba sai a wannan lokaci, don haka bayan na sace gurun tsafin sai na datse kwadon akwatin ,shi kuwa dan mabudin kwadon akwatin dama ko da yaushe yana jikin mazagin wandonsa. Lokacin da ya dawo cikin tantin nasa ya iske akwatinsa a rufe bai iya tunawa cewa a bude ya barta ba,Bayan na mallaki gurun tsafin ne jiya na shiga har cikin turakarsa na bude akwatin da karfin sihiri, kuma na barta a bude domin nasa shi zargi cewa a nan ne aka sace Gurun. Yanzu zan baki labarin abinda yasa na sace wannan Guru. Nan take Zumaira ta bawa labarin duk yanda akayi aka yanka mahaifiyar Imhal aka kaita daji aka yar ana zaton ta mutu har tsoho imzanu ya ganta ya ceci rayuwar ta kuma ta cigaba da rayuwa a cikin hauka har izuwa sanda ta haifi jarumi Imhal, a karshe ta mutu ta barshi a hannun tsoho imzanu ya cigaba da rainonsa har ya girma, kawo izuwa sanda sarki Gurzalu ya tura a kashe tsoho imzanu a kamo Imhal har izuwa cikin gari inda suka fada cikin gidan ta ta taimake su. Koda MUZAIRA tazo dai-dai nan a labarin ta,sai taga hawaye na zuba a idanun Shumaira sakamakon tsananin tausayi da ta ji bisa jin tarihin rayuwar Imhal da yadda aka yiwa iyayensa kisan gillah, Nan take Shumaira taji ta tsani sarki gurzalu don jin mugun zaluncinsa, kuma ta kudurce a ranta cewar lallai sai ta raba alakar dake tsakaninsa da mahaifinta sarki taryan, Koda Zumaira taga Shumaira na kuka,sai itama zuciyar ta ta karaya ta fashe da kukan aka rasa wanda zai rarrashi wani har izuwa tsawon 'yan dakiku sai daga can Shumaira ta nutsu ta daina kuka ta dago kai ta dubeta tace,Yanzu wane irin taimako kike so nayi miki? Koda jin wannan tambaya sai Zumaira ta nutsu tace,Ba wani taimako nake so kiyi mini ba face ki ajiye duk abinda na fada miki sirri a cikin zuciyar ki har izuwa ranar gasar Imhal ta karshe, wato ranar da zai fafata da sarki gurzalu domin idan kika gayawa Imhal cewar sarki gurzalu ne ya kashe iyayensa ya hau karagar mulkin a yanzu duk shirin mu ya watse baza mu iya daukar fansa ba akan sarki gurzalu, domin Imhal zai hau kace ne yace yanzu-yanzu zai dauki fansa,kinga kuwa ba zai iya ba,tunda sarkin yawa yafi sarkin karfi,karfi. Inda dai ace nasan sirrin yadda ake amfani da wannan gurun sihirin ne na sarki gurzalu da nayi amfani dashi wajen hallaka shi, abinda zan iya yi yanzu kawai shine, nacigaba da boye wannan gurun tsafi a waje na har izuwa ranar da zasu fafata shi da Imhal ya zamana cewa ta kowane hali bai bar hannuna ba,domin indai gurzalu baya tare da gurun tsafin, bazai iya samun nasara ba akan Imhal,sirri daya na sani na amfani da wannan gurun, wato sirrin bata,duk wanda yake tare da wannan gurun da wanda ke tare dashi ba a ganinsu, kuma ba a jin muryarsu Koda kuwa za suyi ta tsandara ihu, su kwana suna yi,yanzu sai ki tashi kiyi mini jagora izuwa inda aka tsare Imhal domin na ganshi ko ma samu 'yar nutsuwa, amma baza muyi masa magana ba ,don ko munyi ma bazai ji ba ,ba tare da gardamar komai ba Shumaira ta mike tsaye ta kama Zumaira ta ka ta suka fice daga cikin gidan sarautar suna ta ratsawa ta cikin lunguna da sakuna, suna tafe suna hira abin su,kuma gashi duk inda suka ratsa akwai dakaru a tsaitsaye suna rangadi amma babu mai ikon ganinsu ko jin muryarsu, duk inda suka je kuma suka iske kofa a rufe basa bukatar su bude sai dai kaga sun ratsa ta cikin karfen kofar sun wuce, tamkar yadda danshi ke tsatstsafowa daga cikin kasa,Albarkacin wannan gurun tsafin dake daure a kugun MUZAIRA hakan ke faruwa, A haka dai suka iso kofar dakin da aka sa jarumi Imhal a ciki. da yake kofar dakin anyi tane da sandunan karfe sai suka ganshi kwance a kasan dakin ko shimfida babu yana ta faman shara baccin wuya, Koda suka ga halin da yake ciki ,kuma suka ga katon raunin dake kan kirjin sa sai suka fashe da kuka, Tabbas duk wanda ya dubi Imhal a wannan yanayin da yake dole ne ya tausaya masa domin numfashinsa ma yana fita ne da sauri-sauri kamar ba zai rayu ba,sai da suka dade a tsugune a wajen suna kallon sa sannan MUZAIRA ta zura Kanta ta cikin sandunan kofar da hannun ta guda ta shafa kan Imhal, a lokacin da hawayen idanun ta ya zubo akan kumatunsa, shafa kan nasa ke da wuya ya farka daga bacci, Koda ya ji danshi a kumatunsa sai ya shafo shi ya duba, Koda ya fahimci cewar ba ruwa bane,hawaye ne,sai ya mike tsaye zumbur! ya kama waige-waige amma bai ga kowa ba,A lokacin ne Shumaira tayi sauri ta kama hannun MUZAIRA ta janye ta suka bar wajen. Nan take Imhal yaji a jikin sa cewar lallai wata ce tazo wajen sa har tayi kuka hawayen ta ya zuba akan kumatunsa, Amma abin tambayar shine,Shin Wacece wannan mai zubar da hawaye saboda tausayinsa? Amsar da ya kasa baiwa kansa kenan, shi dai a sanin sa bashi da kowa a wannan duniya wacce zata zubar da hawayen ta saboda tausayinsa, nan dai jarumi Imhal ya fada kogin tunani inda ya tuno da abokin sa MARIGAYI ZAUWADU kuma ya tuno da wasiyyar da ya bar masa sanda ya bashi wata sarka yace dashi, lallai komai dadewa yaje unguwar sharkas a cikin birnin kisra ya nemi masoyiyarsa SUHAILA ya bata wannan sarka, kuma ya bata labarin rayuwar su a cikin kurkuku har izuwa lokacin da ajali ya riske shi,Koda yazo nan a tunaninsa sai hawaye ya zubo masa yaji yana fatan ya rayu ya sake kubuta Daga sharrin sarki gurzalu domin yaje ya sauke wannan alkawari da ya daukarwa abokinsa Zauwadu. Wannan shine abinda ya faru tsakanin Gimbiya Shumaira da Zumaira kanwar mahaifiyar jarumi Imhal wacce itama take da burin daukar fansa akan sarki gurzalu. Al'amarin sarki gurzalu kuwa, lokacin da su Gimbiya LAMIRAT suka sake shafe wuni guda suna neman barawon sa a cikin birni da kauye suka dawo babu nasara, sai sarki gurzalu ya zama kamar mahaukaci ya dinga buge-buge da iface-iface, da kyar!LAMIRAT ta shawo kansa ya dawo hayyacinsa, sannan ta dube shi tace,Ya kai Abbana yanzu mene ne dalilin da ya hana ka tashi na garzaya izuwa can birnin kisra domin kar shiga dakin halwar tsafin ka ka binciko wanda ya sace maka gurun nan?Koda jin wannan tambaya sai sarki gurzalu yayi aniyar zuciya yace, Abinda yasa naki komawa birnin kisra shine tunda nake zuwa wannan gasa tsawon shekaru talatin baya ban taba komawa gida ba a lokacin da aka gasar ba,idan na koma mutane za su iya cewa na tsorata ne da abokin gwamina ko kuma na karaya na koma gida don nayi sabon shiri, kinga kenan yanzu duk zabi biyun da nake dasu akan matakin da ya kamata na dauka duk sun rushe, muna ji muna gani kenan makiyanmu za su iya samun nasara akan mu. Koda jin haka sai lamirat ta gyada kai tace, Haba ya kai Abbana, hanyar kashe makahon kare yawa gareta, ina da wata dabarar, cikin mamaki da zumudi sarki gurzalu ya dubi lamirat yace, Ya ke'Yata wace irin dabara kike tunani? lamirat ta numfasa tace,Ni ina ganin cewa ka saka sarki taryan ya kirawo maka gaba daya bokayen kasar nan su dukufa akan binciken gano barawon ka,indai bokayen kasar nan suka hada karfi da karfe, lallai zasu iya gano barawon ka a cikin kwanaki kadan kafin Imhal ya sami lafiyar da zai iya cigaba da wannan gasa har haduwarka dashi tazo, Koda jin wannan shawara sai farin ciki ya lullube sarki gurzalu yace, ina alfahari dake 'yata tabbas kinyi dogon tunani mai kyau, to amma fa dole ne muyi la'akari da irin raunin dake jikin Imhal mu kiyasce iya tsawon lokacin da muke ganin zai warke, idan kuma yazo dai-dai da sanda Bokayen za su samu nasarar gano barawon shikenan bamu da sauran damuwa,amma idan har Imhal ya samu lafiya kafin su gano barawon akwai matsala babban,Lamirat tace, kada ka damu ya Abbana, duk zan kula da hakan, kuma a Yau dinnan za a gama komai, Koda gama fadin haka sai Gimbiya lamirat ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin,bata zame ko ina ba sai turakar sarki taryan, bayan anyi mata iso ta shiga inda yake sai ta risina ta gaishe shi sannan tace, ya shugabana, Abbana ne yace nazo na nemi alfarmar zuwa ganin jarumi Imhal, Koda jin haka sai sarki taryan ya girgiza kai yace,Ai bazan iya baki wannan dama ba domin yana daga cikin dokar wannan gasa ba a barin abokin gasa yaje ya gana da dan'uwansa,idan har kika je kika gana da Imhal kamar sarki gurzalu ne yaje tunda kin kasance 'yarsa,Lamirat tace,na yarda ka hadani da amintattun Hadimanka su rakani gareshi, idan ana zargin ko zanje na cutar dashi ne,,Koda jin haka sai sarki taryan yayi shiru yana tunani, daga can kuma sai yayi aniyar zuciya yace,shikenan na amince, Take lamirat tayi godiya, ba tare da bata lokaci ba aka hadata da wadansu amintattun Hadimai su hudu gami da dakaru dari suka tafi izuwa dakin da aka kulle jarumi Imhal. Da isarsu suka iske jarumi Imhal a kishingide a jikin bango yana con abinci dakyar kamar zai yi amai ko Riga babu a jikinsa sakamakon katon raunin da ke kirjin sa. Tun daga nesa jarumi Imhal ya hango Gimbiya lamirat tare da dakaru sai ya kura mata idanu yana mai yi mata murmushi. . .RIJIYA GABA DUBU Littafi na uku 3 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 3E . Ita kuwa Koda taga yana yi mata murmushi sai ta murtuke fuskarta tamkar taga bakin kumurci(Bakin maciji mai masifa da mugunta) kuma sai ta dinga satar kallon raunin da ke kan kirjinsa, tana nazari da tunanin adadin kwanakin da take ganin cewar ciwon zai iya warkewa har ya iya cigaba da yin wannan gasa. Lokacin da Gimbiya lamirat suka iso daf da kofar dakin sai suka tsaya cak! Akayi tsit! ana kallon-kallo tsakaninta da jarumi Imhal, kawai sai Imhal ya dubeta fuskarsa cike da annuri yace,"Mene ne ya kawoki wajena,ko kuwa kinzo ne ki karasani saboda kina tsaron karona da mahaifinki? " Koda jin wannan tambaya sai murmushi ya subucewa Gimbiya lamirat bata sani ba,ta dubeshi cikin gadara tace, "Ai matsoraci baya kusantar abokin gaba,nazo ne domin naga lafiyar abokin gaba, domin idan ka mutu yanzu sai nafi kowa bakin ciki, saboda bani da burin da yafi na sare kanka da hannun nan nawa". Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama jarumi Imhal yace," Wai shin menene dalilin da yasa keda mahaifinki kuka tsananta kiyayya a kaina,alhalin babu wani mugun sabani da ya taba shiga tsakanina da Ku? shin ta yaya Zaki samu damar sare kaina da hannunki alhalin bakya cikin wannan gasa ta KAMBUN JARUMTA? Koda ma kina cikin wannan gasa ni bazan iya kashe ki da hannu na ba,domin a cikin fadin duniya kaf a yanzu babu abinda nake kauna sama dake". Koda jin wannan batu sai lamirat da gaba daya dakaru da hadiman dake bayan ta suka cika da tsananin mamaki, lamirat ta fusata ainun, ta dakawa Imhal tsawa tace,"Kai talaka, makaskanci! ka sani cewa wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa,kuma RUWA da WUTA basa haduwa, batun soyayya a tsakani na dakai babu har abada sai kiyayya! Nayi maka alkawarin cewar wannan karon baka isa ka kubuce ba daga sharrin mu face munga karshenka!!" Koda jin wannan batu sai jarumi Imhal ya bushe da dariya, lokaci guda kuma ya hade fuska yace,"Ni kuwa nayi miki alkawari sai kin nemi gafarata da murya mai taushi, kuma kin rokeni na So kind......!!!" Kafin jarumi Imhal ya rufe bakinsa tuni lamirat ta tofa masa yawu a fuska tace,"Da dai na SO ka har na furta maka kalmar SO gwara na rasa rayuwata, kuma ka saurari ranar da za kayi gasa ta uku, nice abokiyar gwaminka ". Tana gama fadin haka sai tayi sauri ta juya cikin fushi zuciyar ta na tafasa tamkar zata kone, cikin hanzari hadimai da Dakaru suka bita a baya. Shi kuwa jarumi Imhal sai yasa hannun sa ya lakuto yawun da lamirat ta tofa masa a fuska ya shanye shi yana murmushi yace, " Ba a soyayya da karya... kuma ba a kiyayya da karya, na kamu da tsananin sonki Gimbiya lamirat, kuma bazan daina sonki ba Koda Zaki zamo sanadin ajalina! Yana gama fadin haka sai ya koma ya kwanta a kasa, kansa yana kallon Rufin dakin yana murmushi gami da mamakin yadda akayi radadin SO ya sa shi ya bayyana soyayyarsa a fili a Yau ba wadda ta tsane shi kamar yadda ta tsani ajalinta, kuma ya cigaba da wasu-wasi a cikin zuciyarsa akan cewar; "Wai shin da gaske ne Lamirat ce abokiyar gwaminsa ta uku a cikin wannan Gasar Jarumtaka?" Abinda baiwa sani ba shine, shi kansa sarki gurzalun baiwa San cewa Gimbiya lamirat ta shiga cikin wannan gasa ba,don tun kafin su iso birnin ta aiko da wasika mai dauke da hatiminta da sa hannunta ba sarki taryan tace lallai a sata a matsayin jarumar da zata fafata a karo na uku da bakon jarumin da za su zo dashi ". Koda sarki taryan yaga wannan wasika sai ya cika da dimbin mamaki, amma da yaga hatimi da sa hannun ta sai yasa aka rubuta sunanta a cikin jaruman gasar. Wani iko na Allh kuma sai ya manta ya tambayi sarki gurzalu dalilin da yasa ya bar Gimbiya lamirat ta shiga cikin wannan gasa. Bayan lamirat ta baro wajen Imhal sai ta koma izuwa turakar sarki gurzalu ta gaya masa cewa," Dole ne Bokayen da za su kira suyi musu wannan bincike su kammala a cikin kwanakin da basu wuce bakwai ba,saboda na tabbatar da cewar kafin Imhal ya warke har yaji karfin da zai iya fitowa filin gasa sai ankai kwana bakwai ". Sanda sarki gurzalu yaji wannan batu sai fuskar sa ta fadada da murmushi, yace," Ai faduwa tazo dai-dai da zama, domin tuni na gana da shugaban bokayen kasar nan a Yau bayan na rabu da ke, kuma har ya tabbatar mini da cewar nan da cikar kwanaki bakwai dai-dai za su gano mini Barawon,tabbas aikin ki yayi kyau. Da jin haka sai farin ciki ya lullube Gimbiya lamirat tayi godiya kuma sai fuskarta ta sauya yanayi izuwa matukar damuwa ta sunkui da Kanta kasa tana mai yin shiru,Al'amarin da ya tayar da hankalin sarki gurzalu kenan ya dubeta shima cikin damuwa yace, "Ya ke 'yata me ya faru,kuma naga fuskarki ta sauya yanayi daga farin ciki zuwa kishiyarsa?" Sanda ta ji wannan tambaya sai ta dago kai a lokacin da idanun ta suka kada suka yi jawur kamar hawaye zai zubo mata tace,"Ya kai Abbana a iya sanina a cikin tarayya ta dakai ban taba yi maka karya ba kuma ban taba yi maka laifi ba,ko ba haka bane?" Cikin mamaki sarki gurzalu ya gyada kai yace,"Tabbas tun daga kuruciyarki kawo izuwa girmanki baki taba yi min wadannan abubuwan biyu ba". Lamirat tace,wannan karon nayi maka wani laifi tun kafin mu baro gida, kayi hakuri bazan iya gaya maka wannan laifi ba sai bayan an kammala wannan gasa ta khango JARUMTA, amma ina rokonka da ka yafe min wannan laifi tun kafin ka San shi" Koda Gimbiya lamirat tazo nan a zancen ta sai sarki gurzalu ya sake kamuwa da tsananin mamaki, yayi shiru yana tunani da nazari har izuwa tsawon dakiku, daga can sai ya dubeta cikin murmushi yace, "Na yafe miki wannan laifi'Yar Lele,kuma ko bayan na San laifin na rantse da girman abin bautarmu bazan yi fushi da ke ba" Koda jin haka sai farin ciki ya kama lamirat ta rungume sarki tana mai yi masa godiya, nan dai lamirat tayiwa sarki gurzalu sallama ta tafi izuwa masaukin ta,wato dakin Gimbiya Shumaira. Tana shiga dakin sai ta hango Shumaira zaune tana sarrafa hannayen ta alamar cewar tana yin magana ne da wani. Amma da lamirat ta karaso cikin falon sai taga Ashe babu kowa a cikin falon, Shumaira ce kadai a zaune. Al'amarin da yayi matukar bata mamaki kenan, ta dubi Shumaira tace,Shin akwai wani aljani da yake zuwa wajen ki kuyi hira? Cikin mamaki Shumaira ta dubi lamirat tace,Ai babu wani aljani da ya isa ya shigo cikin gidan sarautar nan domin iyaye da kakanni sun gama shirya gidan da tsari na musamman. LAMIRAT tace,"Wannan gaskiya ne,domin mahaifina ya tabbatar min da haka, amma yanzu da na tunkaro wannan falon naki naga kina sarrafa hannayenki alamar cewa kina yin magana ne da wani " Koda jin haka sai Shumaira tayi murmushi tace,A'a babu wanda nake hira da shi ,kawai dai ina tunani ne gami da zancen zuci , Cikin sanyin jiki Lamirat ta zauna a gefen Shumaira suka yi shiru tsawon'yan dakiku kadan. Duk wannan abu dake faruwa MUZAIRA na zaune a gefe daya tana hararar lamirat, kuma jikinta na tsuma, ji take kamar ta mike zumbur! ta je ta shake Gimbiya lamirat har sai ta kasheta saboda kiyayya. Ita kuwa lamirat gashi dai tana fuskantar kujerar da MUZAIRA take zaune a kai amma ba ta iya ganinka,Shumaira kadai take iya gani a cikin falon. Daga can sai lamirat ta katse shirun da suke ciki ta dubi Shumaira tace,Ya ke kawata ina son zan baki wata shawara guda daya, shawarar kuwa ita ce,Kada ki so saurayin da ba shine ya fara nuna soyayyarsa ba a gareki, domin watakila kiyi SON MASO WANI. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Gimbiya Shumaira tace, Ke kuwa mene ne dalilin da yasa kika fada mini wannan magana alhalin ban taba gaya miki cewar ina son wani saurayi ba? Koda jin haka sai lamirat tayi murmushi tace, Tun da dai nayi miki hannun ji mai sanda baki gane ba bari na fito fili nayi miki baro-baro watakila za ki fi fuskantar inda nasa gaba. Idan za ki iya tunawa, a ranar da aka fara gasar kambun JARUMTA tsakanin jarumi Imhal da sadauki Darwaz sai da kowa ya gane cewar kin kamu dason jarumi Imhal sakamakon nuna matukar tashin hankali bisa ganin zai hallaka da kuma yadda kika nuna farin ciki lokacin da ya samu nasara, to ina mai tabbatar miki da cewa jarumi Imhal yana da tsananin so da bege a cikin zuciyar sa,kuma har ya fito fili ya bayyana mata sirrin zuciyar sa,sai dai kashe! Anyi rashin sa'a,domin wacce yake so din ta tsane shi kamar yadda ta tsani mutuwarta, bisa wannan dalili ne na gaya miki cewa ki taka a hankali, kada kiyi SON MASO WANI wanda hausawa suke cewa KOSHIN WAHALA. Na baki wannan shawara ne a matsayinki na tsohuwar kawata da muke tare tun kuruciya,sannan idan kunne ya ji jiki ya tsira,shawara kuma ta rage ga mai shiga RIJIYA. Koda gama fadin hakan sai Gimbiya lamirat ta mike tsaye ta shige cikin dakin bacci ta kwanta domin ta huce gajiyar da tasha a ranar SAKAMAKON yawon da suka Sha na farautar barawon mahaifin ta. Ita kuwa Gimbiya Shumaira sai taji zuciyarta ta buga da karfi, tunani da wasu-wasi suka cika mata ranta bisa kokarin gano ko Wacece budurwar da jarumi Imhal ya kamu da tsananin sonta haka? Koda MUZAIRA taga hankalin Shumaira ya dugunzuma ainun sai ta mike tsam! Daga kan kujerar da take zaune ta koma wajen ta ta dafa kafadunta ta dubeta tace,"Kwantar da hankalin ki ranki ya dade,a matsayina na uwa a gun jarumi Imhal in dai ina numfashi a doron kasa sai na siyo miki soyayyars Imhal,domin kece kika dace dashi fiye da kowace budurwa a wannan duniya, domin soyayyarki a gareshi, soyayya ce ta gaskiya, wacce babu algus! a cikin ta". Koda jin wannan batu sai hankalin Shumaira ya kwanta ta rungume MUZAIRA tana mai yi mata godiya gami da fatan samun nasara akan makiyansu. . . RIJIYA GABA DUBU Littafi na uku 3 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 3F . Kwana Uku cur!da Faruwar wannan al'amari ne sarki gurzalu na tsalle-tsalle gami da yin wasa da takobi a wani babban fili dake cikin harabar gidan sarki taryan don baiwa kansa horon yaki, sai ga 'yarsa Gimbiya LAMIRAT ta durfafoshi sanye cikin shigar yaki kuma rike da takobi, Al'amarin da ya bashi mamaki kenan, ya tsaya cak! ga barin baiwa

Chapter 6 of 7