Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
ya farfado sai ya tsinci kansa a cikin jirgin ruwa ga marwatu da dakarunsa sun kewaye shi,yana daga kansa sama ya dubi gabas sai ya hango kurkukun Darul maut a nesa da su kadan,jirgin Na tafiya acikin teku,al'amarin da ya jefa Imhal acikin bakin ciki kenan have acikin zuciyarsa Yanzu mene ne amfanin wannan yunkurin guduwar da nayi?wai shin menene dalilin da yasa baki kashe kansa ba ya huta da wannan bakin ciki?yana cikin wannan tunanin zuci ne jirgin nasu ya I so kofar kurkukun Darul maut,nan take aka tsaida jirgi ya tsaya cak! sannan dakaru suka kama Imhal suka tashe shi tsaye aka fitar dashi daga cikin jirgin ,shi kuwa marwatu baki fits daga cikin jirgin ruwan ba sai ya dubi dakarun da suke rike da Imhal have dasu Kada Ku kaishi bangaren dakin fursunoni Ku kaishi dakin RIJIYA GABA DUBU Ku daure shi a jikin bango da sarkoki Ku barshi a haka,kuma kada a bashi ruwa ko abinci had sai Na dawo, .RIJIYA GABA DUBU Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 2D Na tafi gidan Sarki domin inyi masa albishir bisa nasarar kamo Imhal da mukayi,koda gama fadin haka sai marwatu ya juya ya umarci masu tukin jirgin da su juya akalar jirgin su nufi cikin gari,ba tare da gardamar komai ba kuwa suka bi umarninsa suka juya jirgin suka kama hanya akan ruwa. Su kuwa dakaru sai suka shigar da jarumi Imhal cikin kurkukun,suna shigewa aka mai da kofar Gidan aka rufe,tayi kara mai karfi tamkar an kulle kofar birnin gaba daya,yayin da aka zo wucewa da jarumi Imhal ta bangaren dakunan fursunoni suka kyalla I do suka hango shi sai suka kama ihu da shewa suna yi masa tafi da jinjina sabo da kasancewarshi fursuna Na farko da ya taba samun nasarar guduwa kuma ya tsira da rayuwarsa.Koda fursunoni suka ga an nufi dakin RIJIYA GABA DUBU da Imhal sai gaba dayan su jikin su yayi sanyi suka kamu da tsananin tausayinsa,ba komaine ya haddasa hakan ba face sanin cewar duk mutumin da aka shigar dashi cikin (ayya frnds ayimin afuwa wlh fefar littafin ta tsakiya banganta ba) . Koda Imhal yazo nan a zancensa sa aljani Sautil makatur ya bushe da dariyar mugunta a karo Na biyu yace, Sai kayi kokari ka fita daga nan din cikin hayyacinka yadda zaka iya bude idanunka ka kalli maharbi Imzanu. Koda gama fadin haka sai aljani Sautil makatur ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba acikin dakin,nan fa Imhal yaci gaba da jin tsananin zogi da radadin Harbin da kunamun nan suke masa har ya dinga jin kamar ya yanke duk wadan nan kurajen na jikinsa wadan da suka duri ruwa, gashi kuma a wannan lokacin yunwa da kishirwa sun addabe shi sai birgima yake yi a kasa yana mutsu- mutsu,kai komai rashin tausayin mutum idan yaga Imhal acikin wannan hali dole ya tausaya masa, haka dai Imhal ya kasance acikin wannan hali har sai da dare ya raba sannan aka bude kofar dakin RIJIYA GABA DUBU aka shigo aka baiwa Imhal wani irin ruwa mai tururin zafi acikin kwarya,Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce, Wanda yake cikin ruwa ko takobi aka mika masa kamawa zai yi, domin ana mikawa Imhal wannan ruwa a lokacin da yake fama da kishi sai kawai ya karbi kwaryar ya kafa a bakinsa ya fara kwankada duk da cewar ruwan yana kona masa harshe kuma yana mugun wari sannan bashi da dadin dandano,shi dai kawai burinsa ya jika makogwaronsa ya kawar da kishirwar da ta addabe shi. Hakika rashin Sani yafi dare duhu! Inda Imhal yasan abinda sai biyo baya da bazai sha wannan ruwan ba,gwara ya gwammace kishirwa ta zama ajalinsa domin yana gama shan ruwan da kamar dakika daya sai cikinsa ya murde matuka ya kama ciwo yaji kamar ana daddatsa hanjin cikinsa,bai San sanda yaci gaba da birgima ba a kasa yana rusa ihu,idanunsa kuwa suka kumburo sukayi bulu-bulu kamar zasu fado kasa. Kurajen dake jikinsa kuwa sai suka cigaba da tsananin zogi suna kara kumbura, Daga can kuma sai Kurajen suka dinga fashewa da Kansu suna zubar da jini gami da wani irin mugunyar ruwa mai doyi, nan take kurajen Na gama fashewa gaba daya sai ya sume, bai sake farfadowa ba sai da sanyin asuba ya buga.A sannan ne aka sake bude kofar dakin aka kawo masa abinci loma daya da ruwa mukurwa uku acikin wani Dan karamin kofin kasa, Haka dai aka cigaba da ganawa Imhal azaba kullum, daga cikin azabobin da aka tanada na cikin RIJIYA GABA DUBU, har tsawon kwana goma sha hudu ya zamana cewa ya rame matuka ya lalace kuma ko ina a jikinsa duk ciwuka ne babu kyan gani,hatta fuskarsa ma sai da tayi muni amma duk wannan tsananin azaba da yunwar da ake yi masa horo da su bash sa ya mutu ba. A Ranar kwana na goma sha hudu ne da sassafe aka bude dakin RIJIYA GABA DUBU aka fito da jarumi Imhal a cikin matukar galabaice tamkar an dauko tsumma domin ko kadan babu kuzari a jikinsa da kyar ma yake iya taka sawayensa, da yawa daga cikin fursunonin Gidan ma da aka zo za a wuce dashi ta gabansu kasa shaida shi suka yi saboda yadda kamanninsa suka sauya da kuma yadda ya rame matuka, Koda fursunoni suka shaida shi sai suka kamu da tsananin tausayinsa harma wasu suka zubar masa da hawaye, nan dai aka fitar da Imhal daga cikin kurkukun gaba daya aka saka shi acikin jirgin ruwa a daddaure cikin sarkoki, kai kace wani katon goggon biri aka kamo, kuma suma dakaru DUBU ne suka kewaye shi acikin jirgin ruwan don kada yayi wani yunkuri na guduwa, nan take aka nufi Gidan sarautar birnin kisra da wannan jirgin ruwan,Wannan shine abinda ya faru da jarumi Imhal bayan ya gudu daga kurkukun Darul maut an kamo shi ansake dawo da shi. Al'amarin shugaban dakarun kurkukun Darul maut kuwa, wato sadauki Marwatu, lokacin da yaga sun dawo da jarumi Imhal kurkukun cikin nasara sai ya tafi izuwa gidan Sarki Gurzalu yana mai tsananin farin ciki. Da Isar sa gidan sarautar kuwa aka yi masa iso a wajen Sarki, take Sarki yayi masa izini ya shiga har cikin turakarsa inda ya iske shi tare da matarsa Muzaina a zaune acikin farin ciki da nishadi suna ciye-ciye da shaye-shaye, da isowar Marwatu kusa da kujerar da su Sarki suke zaune sai ya zube kasa kamar zai yi masa sujada ya kwashi gaisuwa sannan ya dago kai da nufin yayi bayani amma sai Sarki Gurzalu ya daga masa hannu yana mai yi masa muni da yayi shiru,Sarki Gurzalu ya mike tsaye ya tako har gaban Marwatu ya kama kafadun sa ya tashe shi tsaye sannan ya dube shi fuskarsa cike da annuri yace, ya kai Marwatu kayi sani cewa a iya tsawon aikin da kake yi mini a kurkukun Darul maut baka taba yi mini aiki mai kyau ba kamar wannan na kamo jarumi Imhal, domin inda ya samu nasarar tserewa da ya karya alkadarinmu gaba daya,kuma da ya rusa tarihin da mahaifina ya kafa akan kurkukun Darul maut, tabbas sakamakon da zai biyo bayanka shine mutuwa, to amma yanzu da ka samu nasarar kamo shi na baka kyautar dinare dubu dari biyar gami da Bayi mata da maza guda dubu, sannan kuma na baka gidan gona ta na birnin Saihur, Koda Marwatu yaji wannan bushara sai ya dimauce ya sake zubewa kasa yana sumbatar kafar Sarki yana mai yin godiya, Sarki Gurzalu ya bushe da dariyar murna yace, Tashi ka tafi abinka ya kai Marwatu, domin ka kamo min zakin da idan ya balle daga daji zai iya hallakani ya kawar da dukkan zuri'ata ta yanzu, Nan take Marwatu yayi sallama da Sarki ya mike tsaye da nufin ya juya ya fita,sai matar Sarki Gurzalu ta kirawo sunansa ya waigo sannan ta dube shi tace, Ya kai Marwatu kayi sani cewa nayi maka matukar farin ciki matuka da kasa aka kai wannan babban makiyi namu dakin RIJIYA GABA DUBU na kurkukun Darul maut, lallai acigaba da yi masa azabobin cikin RIJIYA GABA DUBU har tsawon kwanaki goma sha hudun nan kafin as tafi da shi birnin misra inda Sarki zai kashe shi a gaban miliyoyin jama'a a lokacin GASAR JARUMTA, Koda Muzaina tazo nan a zancen ta sai Marwatu ya risina yace,Angama ya shugabata sannan ya juya ya fice daga cikin turakar. .RIJIYA GABA DUBU Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 2E Faruwar hakan ke da wuya sai ga wata tsaleliyar budurwa ta kunno kai cikin turakar, Hakika wannan budurwa ta cika dari a fagen kyau domin sau tari idan ta fito cikin gari bata wucewa tabar mutane lafiya dole sai kaga hadari na faruwa, domin Wanda ke kan jaki ko doki zai bangaje masu tafiya a kasa bai sani ba,wadanda ke dauke da kaya a Kansu zasu saki kayan su zube bash sani ba,Kai bama maza ba hatta 'yan uwanta mata idan suka yi arba da ita sai kaga sun Wangame baki suna dalalar da yawu basu sani ba,sabo da tsabar kyawunta da burgesu da take yi,Ba wata bace wannan budurwa face Gimbiya LAMIRAT 'ya guda daya JAL! a wajen Sarki Gurzalu, A duniya babu abinda Sarki Gurzalu yake so sama da Gimbiya LAMIRAT, ba don komai yake tsananin sonta ba sai saboda halayenta sun zo iri daya da NASA,wato ko kadan lamirat bata son talakawa kuma sannan bata da imani da tausayi ko kadan,Laifi kankani bawa ko baiwa za su yi mata tasa a gaba musu azaba mai tsanani ko kuma tasa a sare musu hannaye, idan ma ranta ya baci sosai da kanta zata zare takobi ta sare musu kai,Gimbiya lamirat ta gado mahaifinta Sarki Gurzalu a tsananin Magunta da iya yaki sannan tana taba samun tsananta gaba akan makiyi, domin idan tasa shi a gaba sai taga bayansa, Bisa wannan dalili ne take yiwa 'ya'yan sarakai da 'ya'yan attajirai na birnin matukar kwarjini suke tsoron tunkararta da batun soyayya ko aure, Ita da Kanta Gimbiya lamirat ta dauke alkawarin baza ta auri wani namiji ba face Wanda ya fita bata,karfin damtse kuma ya cinye gasar jarumtaka ta nahiyar akan mahaifinta tunda mahaifinta shine ke rike da kambun gasar sama da shekaru ashirin ankasa samun Wanda zai karbe daga hannunsa. Lokacin da Gimbiya LAMIRAT ta shigo cikin turakar Sarki Gurzalu ta iske shi tare da mahaifiyarta Muzainat a zaune cikin farin ciki bayan fitar sadauki Marwatu sai ta karasa garesu cikin tsananin murna ta fada kan kirjin Sarki Gurzalu ta rungume shi tana mai cewa, Ya kai Abbana ina mai tayaka murna da aka samu nasarar kamo wannan babban makiyin namu bayan ya gudu daga kurkukun Darul maut kayi sani cewa naso ace ka bani dama naje har Darul maut na kashe wannan makiyi namu da hannu na domin ko sunan sa bana so naji an ambata bare kuma na ganshi da idanu na". bushe da dariya yana mai janye jikinsa daga cikin na LAMIRAT sannan ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar ya dubeta cikin nutsuwa yace,yake 'yata rabin jikina ki kara hakuri daga nan zuwa ranar da zamu hadu da wannan babban makiyi namu a filin gasar JARUMTA ta misra, zaki ga yadda zanyi masa kisan gillah ta hanyar yi masa mugayen sare-sare da takobi na,lallai sai na daddatsa shi kamar yadda ake daddatsa nama a mahauta, yanzu zan sanar daku wani babban sirri Wanda baku sani ba ke da mahaifiyarki, Ku sani cewa wannan jarumi Imhal Wanda nake so nayi gasar KAMBUN JARUMTA dashi ba wani bane face Dan marigayi Sarki Imhal na kasar nan Wanda na kashe shi na hau karagar mulkin da karfin tsiya,idan ban kashe wannan yaro yanzu ba nan gaba sai ya kashe ni ya karbi karagar mulkin sa,duk naga wannan al'amari ne a cikin madubin tsafi na bisa bincike da nayi a jiya da daddare. Koda Sarki Gurzalu yazo nan a zancen sa sai hankalin Gimbiya lamirat da mahaifiyarta ya dugunzuma ainun suka rasa abinda yake musu dadi,cikin alamun tsananin damuwa lamirat tace,Ai kuwa tunda haka ne yanzun nan zan he kurkukun Darul maut na kashe jarumi Imhal da hannu na in ba haka ba ina cikin zulumi da fargaba tunda ance Ka kashe makashinka karfin ya samu damar kashe ka,Koda gama fadin haka sai Gimbiya lamirat ta mike tsaye da nufin ta fice daga cikin turakar amma sai Sarki Gurzalu yayi wuf ya ruko hannun ta yana murmushi ya dubeta yace,Haba yake 'yata ai kin sani cewa duk irin kiyayyarki da Imhal bata kai tawa ba amma sai gashi nayi hakuri ina jiran lokaci ya cika Wanda ya dace da zan kashe wannan yaro, kin sani cewa dake zanyi wannan tafiya izuwa birnin misra a gabanki zan kashe wannan yaro, abinda nake so dake shine, lallai ki danne kiyayyarki ga Imhal a yayin wannan tafiya tamu, kada ki kuskura ki sanar dashi cewa nine na kashe mahaifinsa da dukkan zuri'arsa domin idan ya gano hakan burina na kashe shi a filin gasar JARUMTA ba zai cika ba,Koda Sarki Gurzalu yazo nan a zancen sa sai zuciyar Gimbiya lamirat tayi Dan sanyi ta dube shi tace ,shikenan ya kai Abbana zan cigaba da hakuri har izuwa wannan rana amma fa ka sani cewa ba zan iya danne zuciya ta ba akan nunawa Imhal kiyayya gami da cin zarafin sa da azabtar dashi kafin mu isa birnin misra, Sarki Gurzalu yace A a bana son ki taba lafiyarsa domin ina so ya murmure kafin mu isa can din ramar dake jikin sa ta bace kuma ya samu isasshiyar lafiya don kada mutane suga cewar da nakasasshe zanyi wannan gasa, Koda jin wannan batu sai Gimbiya lamirat ta ciza yatsanta cikin tsananin takaici domin ba haka taso ba,tabbas taci buri ta kara azabtar da Imhal ainun bayan da ma ya Sha azabar RIJIYA GABA DUBU. wannan shine abinda ya faru a gidan Sarki Gurzalu kafin cikar kwanaki goma Sha hudun da za a fito da Imhal daga cikin kurkukun Darul maut. Al'amarin Jarumi Imhal kuwa bayan Angama yi masa wannan azaba ta kwanaki goma Sha hudu da kayan masifun dake cikin RIJIYA GABA DUBU an fito dashi an kai shi gidan sarautar sarki Gurzalu a matukar galabaice kuma a daddaure cikin sarka sai aka watsar da shi a cikin rana yayi ta gasuwa a cikin harabar gidan sarautar har tsawon kimanin sa'a guda sannan sarki Gurzalu tare da 'yarsa Gimbiya LAMIRAT suka fito Daga cikin gidan sarautar a cikin gagarumar shigar yaki gami da kimtsawar tafiya, tun daga nesa Gimbiya LAMIRAT ta kurawa Jarumi Imhal idanu Wanda ke kwance a kasa magashiyan ya jike sharkaf da gumi yana faman nishi kamar Wanda ransa zai fita. duka da cewar Imhal ya rame matuka amma surar jikinsa irin ta manyan sadaukai tana nan kuma babu abinda ya taba lafiyar kyakkyawar fuskarsa, koda tayi arba dashi a karon farko sai taji zuciyar ta ta buga da karfin gaske kuma ta kasa sanin dalilin haka, Yayin da sarki Gurzalu da Gimbiya lamirat suka iso akan jarumi Imhal suka tsaya sai sarki gurzalu ya sa kafarsa ya dunguri wani ciwo dake hakarkarin Imhal,Imhal yayi Dan ihu sakamakon mugun zafin da ya ji, shi kuma sarki gurzalu sai ya dube shi ya bushe da dariya yace Ya kai yaro, ka sani masu iya magana suna cewa, Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,Yau gashi ranar yin gasar mu ta JARUMTA ta so kamar yadda na shaida maka, ko da gama fadin haka sai sarki ya kirawo wadansu hadimansa yace, Ku dauki wannan fursunan kuje kuyi masa wanka kuma a kirawo likita na yayi masa magani sannan a bashi kayan yaki yasa azo dashi bakin kafar gari inda za muyi wannan tafiya tare dashi, Koda gama fadin haka sai wadannan hadimai suka ciccibi Imhal suka tafi dashi dakaru kimanin guda dubu na kewaye da su don tabbatar da tsaro, saboda kar Imhal yayi yunkurin guduwa duk da cewar yana daure cikin sarkoki, Bayan an tafi da jarumi Imhal ne sarki gurzalu ya juyo ya dubi Gimbiya Lamirat yace, amma fa kin bani mamaki, wai shin duk ina zafin zuciyar taki ya tafi ne alhalin ga babban makiyin namu a gabanki amma ko dukan sa ba kiyi ba bare kiyi masa azaba ko wulakancin da kike furucin za kiyi masa, koda jin wannan batu sai lamirat tayi dan guntun murmushi tace,ya kai Abbana kasani cewa bana cin zalin ramamme ko nakasasshe, na fison na zalunci lafiyayyen mutum Wanda ko yaya na taba shi zai ji mugun ciwo amma ba ragowar mutuwa ba,Koda jin haka sai sarki gurzalu ya bushe da dariyar farin ciki yace Dakyau 'yata hakika barewa bata gudu danta yayi rarrafe, lallai yanzu na gamsu cewar kin gaje ni kuma ko a bayan raina nasan zaki iya tafiyar da mulki kamar yadda nake tafiyar da shi. . . RIJIYA GABA DUBU Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 2F . Koda gama fadin hakan sai sarki ya kama hannun Gimbiya lamirat ya na ta suka tafi izuwa can kofar gidan sarautar inda aka ajiye keken dokin da za su hau don tafiya birnin Misra kuma ga dakaru masu yawan gaske sun kewaye keken dokin gaba da baya, kuibi-kuibi, wadanda zasu yi musu rakiya, kamar yadda sarki gurzalu ya bayar da umarni haka akayi, wato sai da aka yiwa Imhal wanka aka sa masa magani a jikin raunikansa sannan aka kawo abinci mai rai da lafiya aka bashi yaci yasha ya koshi,daga nan kuma aka sanya masa kayan yaki a jikinsa, amma maimakon a dama masa makami sai aka sake zuba masa sarkoki aka daure shi aka kawo shi cikin tawagar sarki da zata tafi birnin misra, nan take aka sanya Imhal acikin wani akurki Wanda dawakai ke Jansa aka kulleshi a ciki, sannan aka dunguma gaba daya aka fice daga cikin birnin gaba daya. Tsakanin birnin kisra da misra tafiya ce ta sa'a bakwai don haka fun safe aka fara wannan tafiya ba a iso birnin kisra ba sai da rana ta take, kai tsaye tawagar sarki gurzalu ta nufi gidan sarautar sarki Taiyara don haka sai ya shirya ya fito ya tare su cikin tsananin murna, nan take aka shigar da Gimbiya lamirat da mahaifiyarta izuwa inda iyalan sarki Taiyara suke, shi kuwa jarumi Imhal sai aka kai shi cikin wani daki mai kama da kurkuku aka kulleshi, Sarki gurzalu da sarki Taiyara kuwa sai suka shige izuwa turakar sarki Taiyara inda suka zauna aka kawo musu abinci da abin Sha har da giya suka ci suka Sha suka yi tatul suna ta kyalkyala dariya, daga can sai sarki Taiyara ya numfasa ya dubi sarki gurzalu yace, Ya kai tsohon abokina jarumin jarumai na wannan nahiyar, wai shin bana da wanne guzuri kazo mana da shi ne?ka sani cewa duk shekara Kaine kake lashe gasar nan don haka babu sabon wani al'amari Wanda zai sa mu samu kudade masu yawa tunda kowa ya San cewa kaine zakaran gasar, yayin da sarki taryan yazo nan a zancen sa sai sarki gurzalu ya bushe da dariya sannan yace, Kwantar da hankalin ka ya kai abokina kayi sani cewar nazo mana da wani gwarzon jarumi wanda zai burge yan kallo kuma nine kadai zan iya gamawa da shi, kafin na kara dashi zan bashi dama yayi wasa kamar sau shida, ina mai tabbatar maka da cewar a ranar da yayi wasan farko labarinsa zai bazu a ko ina, kuma kashegarin da zai sake wasa sai filin gasar ya cika ya batse da yan kallo don haka kafin ranar da zamu kafsa ni da shi ba kananan kudin shiga zamu samu ba. Wannan karon har dukkanin sarakunan da ke nahiyar nan sai sun zo sun kalli wasan karshe, domin suga yadda zata kaya, Yau baza ayi wasa ko guda daya ba sai gobe saboda ina son jarumin nawa ya huta sosai ya samu karfin jikinsa, Koda sarki gurzalu yazo nan a zancen sa sai sarki taryan ya bushe da dariya sannan yace, Ya kai abokina nifa duk wannan labarin da na bani naji sane kamar tatsuniya, duk da cewar banga wannan jarumi ba da kazo dashi nasan nawa jarumina sadauki Darwaz ya fishi komai da komai, don haka a goben da safe ina son Darwaz da jarumin naka su kara.Koda jin wannan batu sai sarki gurzalu ya sake bushewa da dariya yace Ai shikenan, dama masu salon magana sun ce sai an gwada akan San na kwarai. Sarki Taryan yana da 'ya' guda daya wata kyakkyawar budurwa ta kwatance mai suna Shumaira, Shumaira da Lamirat sun kasance kawayen juna tun suna yara kanana saboda abotar dake tsananin iyayensu, don haka suma sun shaku ainun, Wani abin mamaki shine, ko kadan ra'ayinsu baizo daya ba,domin ita Gimbiya Shumaira tana da tsananin tausayi, sabanin lamirat wadda ta kasance Mara imani ga zalunci, hakan bata sa sun kasa shakuwa da kaunar juna ba,amma suna yawan samun sabani domin ako yaushe Shumaira tana matsawa lamirat akan ta daina zaluntar talakawa da masu rauni, wani lokacin ma idan suka samu sabani, sai su kwana uku basa magana da juna,kuma su daina kwana a waje daya da con abinci tare. Gimbiya Shumaira na zaune a cikin turakar ta sai ga Gimbiya lamirat ta shigo, Koda ta dago kai suka yi arba da juna sai Shumaira ta Mike zumbur! ta ruga gareta cikin tsananin farin ciki suka rungume juna,Shumaira ta janye jikinta daga cikin nata suka fuskanci juna sannan tace,Ai tun jiya nake zuba ido naga kun iso amma sai naji shiru tunda dai shekara ta zagayo, Lamirat tayi murmushi tace Ai mun kara kwana daya ne akan lokacin da muka saba tasowa, saboda wannan karon mun taho da wani gagarumin jarumi, wanda za a samu kudade da yawa a dalilin sa,Koda jin wannan batu sai mamaki ya Kama Gimbiya Shumaira tace, Haba ya ke kawata yanzu Ashe har za a iya samun wani jarumi wanda zai burge mutane a wannan nahiyar tamu sama da mahaifina ki?Lamirat tayi murmushi tace,Ai bana nufin yafi mahaifina JARUMTA, amma dai zai taka muhimmiyar rawa a wannan gasa da za ayi ta bana,kuma ina tabbatar miki da cewar inba mahaifin nawa ba babu wanda zai iya kaishi kasa a wannan gasa, Shumaira ta girgiza kai tace Yake kawata kin sani cewa ban taba zuwa kallon wannan gasa ba saboda ko kadan bana son naga jini yana zuba, bana son naga ana kashe mutane a aikin banza, amma wannan karon naji zuciyata tana son taga wannan bakon jarumi wanda kika zo mini da labarin sa don haka indai zai yi wasa gobe zan fita filin gasar na kalle shi don kawai naga iyakar jarumtakar tasa da kike kodawa, Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Gimbiya lamirat saboda ta dade tana son ta dinga Jan Shumaira suna fita kallon wannan gasa tare amma taki tsawon shekara da shekaru, Tabbas lamirat tayi mamaki da taji Yau dare daya Shumaira ta amince zata fita kallon wannan gasa. . . RIJIYA GABA DUBU Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 2G . A daren wannan rana kuwa aka yi ta shela birni da kauye cewar sarki gurzalu yazo da wani sabon gwarzon jarumi kuma ansa cacar kudi akan sa cewar duk jarumin da ya kai shi kasa za a bashi dinare miliyan daya,kuma sannan zai yi wasan farko a gobe da safe tare da sadauki Darwaz na birnin misra, Koda wannan labari ya bazu sai gari ya rude da kace nace ana mamaki, attajirai kuwa suka yi ta shirya cacar kudi a tsakanin su kowa na zabar gwaninsa a tsananin jarumi Imhal da sadauki Darwaz, Jama'ar gari kuwa mata da maza yara da manya kowa ya dinga dokin gari ya waye yaje ya biya kudin shiga filin gasa domin ya ga irin gumurzun da za ayi tsakanin wadannan manyan jarumai. Kai! tun kafin ma gari ya waye filin gasar ya cika makil ya zamana cewar har akan katanga mutane ne a zaune, duk inda mutum ya duba baya ganin komai sai kawunan bil'adama, babu wani guri da yayi saura sai na sarakuna da manyan attajirai, sune kadai basu iso ba,sai kuma jaruman da za suyi gasar, wato jarumi Imhal da sadauki Darwaz. Sadauki Darwaz wani narkeken katon mutum ne mai girman gaske wato mai kirar mutanen farko, Darwaz ya kasance shahararren gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin daga,A ranar da suka fara yin gasar kambun JARUMTA shi da sarki gurzalu, dakyar shi sarki gurzalu ya samu nasarar kaishi kasa,don har sai da ya yanki sarki gurzalu sau biyu bayan sun shafe sa a daya da rabi suna bakin yamutsi, daga wannan lokaci basu sake haduwa ba kawo I yanzu, kuma har gobe ta ciki na ciki, domin kowannensu yayi matukar bakin ciki bisa yadda gumurzun nasu ya kasance saboda sun Sha bakar wuya sun zubar da jini, wannan karon da sadauki Darwaz yaji cewar jarumin da zai kafsa dashi, sarki gurzalu ne yazo dashi sai yaci mugun burin daukar fansa a kansa ya kudurce a ransa cewar a gaban sarki gurzalu zai yiwa jarumin kisan gillah. Sai da gari yayi haske sosai sannan jama'a suka ji anfara buga tambura ana busa algaita da sarewa alamar cewa sarakuna zasu fito daga cikin gidan sarautar, nan take gaba daya jama'ar dake filin gasar suka mimmike tsaye don girmamawa, Fadawan sarki taryan da manyan attajiran kasar suka fara shigowa cikin filin gasar, sannan sai ga sarki taryan, sarki gurzalu, Gimbiya lamirat da gimbiya Shumaira sun shigo,dakaru da kuyangi na take musu baya har suka iso wajen da aka tanadar musu mai dauke da kujeru na alfarma,Koda jama'ar gari suka ga Gimbiya Shumaira ta fito kallon wannan gasa sai suka cika da matukar mamaki, nan dai su sarki taryan da su Shumaira suka isa mazauninsu suka zazzauna. Al'amarin jarumi Imhal kuwa, tun a jiya bayan anyi masa wanka, ansa masa magani ajikin raunikan jikinsa, kuma an bashi abinci na alfarma ya cika cikin sa sai ya nutsu sosai ya dawo cikin hayyacinsa inda ya fada cikin kogin tunanin abubuwan da suka faru a baya. Babu abinda ya fara fado masa a rai face irin tsananin azabar da aka gana masa a dakin RIJIYA GABA DUBU ta tsawon kwana goma Sha hudu, A tsawon kwanakin azabar gobe tafi ta jiya, haka akai ta azabtar dashi babu sassauci, azabar farko itace wadda kunamun nan suka fito suka yi ta cizon sa,kashegari kuwa macizai ne suka fito suka yi ta saran sa,haka abin ya cigaba da wakana, wata ran ya ga dodanni suyi ta dukansa suna tamola dashi. Koda jarumi Imhal ya gama tuno wannan masifaffiyar wahala da ya Sha acikin RIJIYA GABA DUBU wacce ke cikin kurkukun darul maut, sai ya takarkare ya kwarara uban ihu,Ihun nasa ya cika gidan sarautar gaba daya, har sai da dakaru masu yawa suka rugo izuwa kofar dakin da yake,Koda suka leka suka gan shi a kwance a kasa kuma a daure ga kofar dakin a kulle sai hankalin su ya kwanta, sabo da dama can an gargade su matuka

Chapter 4 of 7