Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
akan cewar kada su kuskura su bari ya tsere, idan kuwa ya gudu a bakacin ransu su duka. Gama tunani ke da wuya sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya fashe da matsanancin kuka, A karshe ya kudiri aniyar cewa komai rintsi da tsanani sai ya jure duk irin bala in dake gaban sa domin ya tsira da rayuwarsa, ya koma gidan kurkukun darul maut ya ruguje shi kuma ya kone wannan RIJIYA ta gaba dubu domin a daina azabtar da al umma,Bayan nan kuma yayi alkawarin cewar sai ya koma gidan Likiciya Zumaira domin ya dauke tsoho imzanu su gudu izuwa wata nahiyar daban inda da sannu zai cigaba da bincike domin ya gano asalin iyayensa da danginsa, haka dai Imhal yayi ta sakar zuci har dare ya raba bai sani ba sannan bacci ya kawo masa mamayar ba zato, Kashe gari kuwa da safe aka sake kawo masa abinci da abin Sha mai rai da lafiya ya kimtsa cikin sa,sai bayan ya huta sosai sannan aka zo aka bude dakin aka fito dashi a daure cikin sarkoki, aka nufi filin gasar JARUMTA dashi. koda aka iso filin gasar da jarumi Imhal a daddaure cikin sarka, da jama'a suka yi arba dashi sai filin gaba daya ya rude da shewa gami da tafi. Gimbiya lamirat da Shumaira na hango shi sai su duka suka mike tsaye, suka kura masa idanu domin a wannan rana kyawunsa da siffar jarumtakarsa sun bayyana a fili muraran,ita dai Gimbiya Shumaira nan take taji ta kamu da tsananin kaunar sa,bata ma San sanda ta kama yin murmushi ba a gareshi, ita kuwa Gimbiya lamirat sai kawai taji zuciyar ta taci gaba da bugawa da karfi, bugawar da bata San dalilin ta ba,shin kiyayya ce ko soyayya ta janyo hakan? amsar da ta kasa baiwa Kanta kenan. Koda aka kawo jarumi Imhal tsakiyar filin gasar wanda sama da dakaru dubu dari ne suka kewaye shi rike da makamai don tabbatar da tsaro harma da wadanda suka dana kibiyoyi akan baka, kawai jira suke suga wani yayi ba dai dai ba yasha ruwan kibbau, aka kwancewa jarumi Imhal dukkanin sarkokin da ke jikinsa sannan aka bashi takobi da garkuwa ya rike, nan fa Imhal ya fara waige-waige da dube-dube domin ya ga abokin gwaninsa, amma bai ga kowa ba,Alokacin ne sarki taryan ya bushe da dariyar mugunta ya dubi sarki gurzalu yace,Yanzu wannan Dan jarumin ne lake tunanin zai iya karawa da gwarzo na abin alfahari na?Sarki gurzalu yace,Ai a inda babu kasa nan ake gardamar kokawa, ina naka jarumin ya fito su kara mu gani,Koda jin haka sai sarki taryan ya daga kai ya dubi wani barde,take barden ya daga wata katuwar gudumar danko ya daki wani katon bandiri, karar bandirin ta cika birnin gaba daya da amsa kuwwa, Faruwar hakan ke da wuya aka bude wata katuwar kofa, sai ga sadauki Darwaz ya fito cikin shigar yaki rike da takobi da garkuwa, Tunda Imhal yazo duniya bai taba ganin mutum mai tsananin tsawo, kauri, da murdewar jiki ba irin ta sadauki Darwaz, nan take zuciyar Imhal ta karaya ya fara tunanin cewa, ai bazai iya ba da wannan katon domin da sadauki Darwaz ya karaso ya tsaya daf da shi sai ya zama Dan mitsitsi akansa kamar an ajiye dantsako a gaban shirwa, tun kafin a bayar da umarnin a fara gasar sai Darwaz yasa hannu daya ya make Imhal, saboda karfin dukan sai da Imhal ya yi tsalle sama yaje ya gwaru da karfen da aka kewaye filin gasar ya fado kasa Tim!yana aman jini,Koda Faruwar hakan sai filin gasar ya rude da shewar jama'a, Attajiran da suka shiga cacar kudi da sadauki Darwaz suka kama murna suna ihu da tsalle domin suna ganin cewar lallai jarumin sune zai lashe gasar su kwashi tsabar kudi, shima sarki taryan sai ya kama kyalkyala dariyar mugunta, ita kuwa Gimbiya Shumaira sai hankalin ta ya dugunzuma ta rude ainun ta kamu da tsananin tausayin Imhal, har kwalla ta cika mata idanu. Ba zato ba tsammani sai aka ga jarumi Imhal ya mike tsaye zumbur! ya ruga da gudu izuwa kan sadauki Darwaz sun ruguntsume da azababben yaki suna masu kaiwa junan su SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama da juriya da bajinta ta ban al'ajabi. WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GASA TSAKANIN JARUMI IMHAL DA SADAUKI DARWAZ? SHIN SARKI GURZALU ZAI SAMU NASARAR KASHE JARUMI IMHAL YA LASHE GASAR KAMBUN JARUMTA? SHIN IMHAL ZAI CIKA BURINSA NA RUGUJE KURKUKUN DARUL MAUT DA KONE RIJIYA GABA DUBU?YAUSHE NE IMHAL ZAI KOMA BIRNIN MISRA YA SAKE SADUWA DA TSOHO IMZANU KUMA YA SAN 'YAR UWAR MAHAIFIYARSA LIKICIYA MUZAIRA? Mu hadu a littafin RIJIYA GABA DUBU 3 don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. to jama'a zan Dan huta kafin Ku jini a cikin na uku . RIJIYA GABA DUBU Littafi na uku 3 Na Abdulaziz sani m gini Ebook creator:- Shuraih Usman 99% Ebook publish by http://hausaebooks.cf Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 3A . Lokacin da jarumi Imhal da sadauki Darwaz suka ruguntsume da azababben yaki a tsakiyar filin fadar birnin misra wanda yan kallo sama da mutane miliyan dari suka kewaye, sai filin ya cika da ihu da shewar jama'a, nan fa kowa ya cika da mamakin yadda Imhal ke iya kare hare-haren sadauki Darwaz har yake mai da martani, sai da aka day lokaci mai tsawo ana wannan artabu, daya daga cikin jaruman biyu bai samu nasarar Koda kwarzanar jikin daya ba,Al'amarin da yasa jikin sarki taryan yayi Dan sanyi kenan, kuma ransa ya baci, bai San sanda ya mike tsaye ba daga kan karagar sa ta mulki ya fara yiwa jarumin sa kirari, abinda sarki taryan bai taba yiba kenan a tarihin gasa da ake yi tsawon shekaru, Koda sadauki Darwaz ya ga sarkin sa ya mike tsaye Daga kan karagar sa yana Koda shi,sai ya fusata ainun ya kara zage damtse iya karfin sa ya dinga kaiwa Imhal Sara da suka da dukkan karfin sa,cikin wata irin sabuwar jarumtaka mai tsananin zafin nama ta BAZATO, Nan fa shima Imhal ya dinga yin iya kokarin sa don kare kansa,amma sai ya zamana cewa dakyar yake iya kare hare-haren, kuma baya iya mai da martani, Koda ganin haka sai murna ta kama sarki taryan ya dinga shewa, Ai kuwa sai jama'ar gari suma suka dinga taya shi,ya zamana cewa babu mai yiwa jarumi Imhal jinjina a filin, Duk abinda yake faruwa sarki gurzalu yayi shiru yana guntun murmushi kawai don yasan wanene Imhal, A gaba dayan filin gasar babu wanda hankalin sa ya dugunzuma ainun bisa ganin halin da jarumi Imhal ya shiga sama da Gimbiya Shumaira, domin duk sanda taga an kai masa wani mugun gari sai kaga ta kai da kai kamar ita ake kaiwa, wani lokacin ma har mikewa take yi tsaye zumbur! kamar zata kwalla ihu,ita kuwa Gimbiya lamirat kawai tana kallon fadan ne,ba ta ma San jarumin da take so ba acikin ranta, amma kuma sanda ta tuno da bayanin da mahaifin ta sarki gurzalu ya gaya mata cewar idan Imhal ya samu nasarar lashe wannan gasar JARUMTA sai ya ga bayansu sai ta ji ta tsani Imhal fiye da komai a duniya, domin babu abinda take so sama da sarki gurzalu da mahaifiyarta, ana cikin haka ne sadauki Darwaz ya kara kuntata Imhal har ya matse shi a waje daya ya hana shi matsawa, kuma ya cigaba da kai masa Sara da suka na hauka ba sassauci, ai kuwa sai ya samu nasarar dankara masa Sara a saman kirjin sa,take Imhal ya kwalla ihu ya fadi kasa a lokacin da jini yayi tsartuwa daga kirjin nasa, Koda Darwaz yaga Imhal ya fadi kasa sai ya kai masa suka da takobi a ciki, Cikin zafin nama Imhal ya goce ya doki marainansa da kafa, kawai sai ji akayi Darwaz ya kurma uban ihu ya fadi can gefe daya, a sannan ne Imhal ya mike tsaye dakyar jini na zuba kirjin sa yana yin layi,Cikin sauri ya cire wani yanki dake daure a goshin sa ya daure raunin don ya rage zubar jinin, a sannan ne Darwaz ya mike tsaye zumbur! ya kwarara uban ihu bisa ganin ya samu nasarar yiwa Imhal rauni, A sannan ne fa sarki taryan ya cigaba dakyakyata dariyar mugunta, Koda suka had a idanu da sarki gurzalu sai gurzalu yayi masa murmushin mugunta ba tare da nuna karayar zuciya ba,Al'amarin da yasa jikin sarki taryan yayi Dan sanyi, kuma ya daina kyalkyala wannan dariyar muguntar,A wannan lokacin Imhal ba karamin kokari yayi ba ya tsaya bisa kafafunsa, don jiri ne yake dibarsa sakamakon jinin da ke zuba daga kirjin sa kuma idanunsa suna lumshewa yana gani dishi-dishi,Koda Darwaz ya lura da irin halin da Imhal ke ciki sai ya bushe da dariyar mugunta don yasan cewa yanzu ne zai gama da Imhal farat daya. Kawai sai Darwaz ya gyara tsayuwarsa, sannan sannan ya sake zaro wata sharbebiyar adda a bayansa wato ya hada makamai guda biyu a hannun sa yana mai gyara tsayuwarsa gami da fuskantar Imhal, A sannan ne fa filin gasar ya rude da shewar jama'a, Attajiran da suke yin caca akan gasar suka dinga yiwa junansu kirari, Kaso bakwai cikin kaso goma na 'yana cacar duk sadauki Darwaz suka zaba a matsayin jarumin su,kaso uku ne kacal suka yi kundunbala suka zabi Imhal, tun da ake yin caca a wannan gasar ba a taba zuba kudade masu yawa ba irin na bana,Da yawa Daga cikin attajiran da suka shiga wannan caca idan ba jarumin su ne yaci gasar ba karayar arziki tazo musu kenan. Lokacin da jaruman biyu suka fuskanci juna, sai filin gasar yayi tsit! aka zuba Ido don ya ga wanda zai yi nasara, saboda ansan cewa wannan gamon da za ayi na karshe ne, Koda Darwaz ya ga shima Imhal cike yake da burin neman sa'a, sai ya budi baki ya karanta wadansu Dalasumai na tsafi guda biyu, kawai sai Imhal yaga wata irin gagarumar iska ta kanannadeshi tasa ya kasa Koda daga hannun sa,ko matsawa daga inda yake, kuma sai Darwaz ya rugo izuwa kansa yana mai daga makamansa sama yana ihu, Abin al'ajabi shine, babu wanda yaga wannan guguwa wacce ta kanannade jarumi Imhal face sarki gurzalu, domin shine kadai yake da karfin ganin sihirin tsafin Darwaz,Imhal yayi iya kokarin sa akan ya kaucewa guguwar ya kasa,Al'amarin da ya dugunzuma hankalin sa ke nan yana ganin mutuwa muraran, Koda sarki gurzalu yaga abin da ke shirin faruwa sai yayi nuni da hannun sa izuwa kan guguwar da ta kanannade Imhal don ya kawar da ita ,amma sai nasa sihirin tsafin ya ki yin tasiri, Take ya tuna cewar ai Yau ya manta bai dauro gurunsa na tsafi ba ya barshi a can cikin wata akwati a dakin da aka sauke shi,nan take bakin ciki ya rufe shi ya sunkuyar da kansa kas yana mai rufe fuskarsa don baya son Darwaz ya samu nasarar kashe Imhal, A dai-dai wannan lokaci ne hankalin Shumaira ya dugunzuma ainun bisa ganin za a hallaka jarumin da taji ta kamu da tsananin sonsa a Yau dinnan kuma farat daya,kawai sai ji tayi hawayen bakin ciki ya zubo mata.Gaba daya attajiran da suka zabi Imhal a matsayin jarumin su suka zuba kudin su na caca akansa sai jikinsu yayi sanyi, suka ayyana cewar asara tazo musu tunda gashi suna gani an durfafoshi da gudu za a sare shi,amma ko motsi ya kasa yi,Koda ya rage bai fi taki uku ba kacal Darwaz ya iso kan Imhal ba sai ya daka tsalle sama da nufin ya sare kan Imhal da makaman dake hannun sa,wato takobi da adda, Kwatsam!ba zato ba tsammani sai Imhal yaji guguwar da ta kanannadeshi ta sake shi ta bace bat!t take ya samu damar sunkuyawa ya kaucewa harin da Darwaz ya kawo masa ,makaman Darwaz din suka sari iska, kafin Darwaz ya juyo da baya tuni Imhal ya soka masa takobi a gadon baya, takobi ta burma gadon baya ta fito ta cikin sa ,Darwaz ya kwarara ihu saboda tsananin zugin sukan da akayi masa ,sannan ya fado kasa yana shure-shuren mutuwa, Ai kuwa sai attajiran da suka zabi Imhal a matsayin jarumin cacar su suka kaure da ihu gami da shewar farin ciki, Gimbiya Shumaira kuwa bata San sanda ta daka tsalle ba sama don murna ta kama kyalkyala dariya, amma tana hada ido da sarki taryan sai taga ya kame, saboda tsananin mamaki da takaici, fuskarsa ta murtuke babu alamar annuri ko kadan, Sarki gurzalu da 'yarsa Gimbiya LAMIRAT kuwa, suma sai farin ciki ya lullube su suka kama yiwa Imhal tafi. Sauran 'yan kallo kuwa kamewa suka yi kamar gumaka saboda tsananin mamaki bisa ganin yadda aka gama dajarumi Darwaz farat!daya, duk da cewar babu kamar sa a karfin damtse da karfin sihirin tsafi a garin,shi kuwa jarumi Imhal yayi matukar mamaki yadda akayi ya tsira daga sharrin wannan guguwar tsafin, Haka ma sarki gurzalu yayi wannan mamaki, kuma hankalin sa ya Tashi, ya fara tunanin cewa lallai akwai wani ma'abocin tsafi da ya taimaki Imhal daga cikin'yankallo,don haka ya zama wajibi yayi bincike don ya gano ko wanene, nan take ya ayyana a ransa cewar yana komawa turakar da aka sauke su zai daura gurun tsafin sa don yayi binciken.Ana cikin wannan halin ne aka ga jarumi Imhal ya yanke jiki ya fadi kasa,Koda ganin haka sai Gimbiya Shumaira ta yunkura za ta ruga izuwa cikin filin inda Imhal yake, amma sai sarki taryan ya ruko hannun ta yana mai daka mata harara, take ta shiga taitayinta ta sunkui da Kanta kasa cikin alamun kunya.RIJIYA GABA DUBU Littafi na uku 3 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 3B . A wannan lokaci ne sarki taryan ya umarci likitansa yaje ya ceci rayuwar Imhal, a guje likita ya isa filin gasar ya kama aikin sa na ceton rayuwar Imhal tare da dinke masa saran da Darwaz yayi masa,nan take aka dauke gawar sadauki Darwaz Daga filin gasar sai sarki taryan ya ba 'yarsa Gimbiya Shumaira izuwa cikin gidan sarautar, Al'amarin da yasa filin gasar ya watse kenan, kowa ya kama gaban sa,shi kuwa sarki gurzalu da Gimbiya LAMIRAT sai suka wuce izuwa masaukin sarki gurzalu, shi kuwa jarumi Imhal bayan likita ya gama dinke raunin da ke kirjin sa yasa masa magani sai aka dauke shi aka kai Shi izuwa cikin wannan daki mai kama da kurkuku aka kulle shi. Lokacin da sarki gurzalu suka isa cikin masaukinsu suka zauna, sai wata kuyanga ta kawo musu ruwan inibi suka Sha,a lokacin da fuskar sarki ta cika da annuri yana ta farin ciki amma sai yaga gimbiya lamirat tayi shiru tana mai sunkui da Kanta kasa cikin alamun damuwa, Gurzalu ya dubi LAMIRAT yace, Yake 'yata,ina dalilin wannan damuwa taki? Koda jin wannan sai lamirat ta kawo gwauron numfashi ta ajiye sannan ta dube shi cikin alamun tsananin damuwa ta ce,Ya kai Abbana akan wane dalili kake farin ciki alhalin babban makiyin mune ya samu nasara a wannan gasa? sabo dame kake son lallai kayi wannan gasa da jarumi Imhal alhalin na gani da idanunka cewar shi mutum ne mai tsananin sa'a? shin baka tunanin cewa kana neman kayi ganganci ne da rayuwarka akan jarumi Imhal? maimakon kai ceci rayuwar sa kamata yayi kasa a kashe shi,ko a sirrance ne kai bani dama a daren Yau nayi baddakama naje har dakin da aka kulleshi na kashe shi.Kafin lamirat ta gama rufe bakin ta tuni sarki gurzalu ya daka mata tsawa har ta firgita taji hantar cikinta ta kada,ta Dan na da baya kadan Daga kusa dashi, Koda yaga ta firgita sai ya bushe da dariya, sannan ya dubeta cikin nutsuwa da murmushi yace,Haba yake 'yata, shin kin manta da ko ni waye ne? NINE FA MURUCIN KAN DUTSE,WANDA BAN FITO BA SAI DA NA SHIRYA! NINE SA GUDU, MAGANIN KI GUDU! KUMA NINE BAKIN TAKOBI MAI RABA MASOYA! Ina mai tabbatar miki da cewar na gama yin bincike a cikin halwar tsafi na gano cewa idan har ba ta hanyar wannan gasar jarumtaka ba,bazan samu damar hallaka shi ba,duk da cewar na gwada jarumtaka ta da tashi,naga karfin mu yazo daya, ai yanzu zanyi amfani ne da karfin sihiri na,na hallaka shi a yayin da muke yin wannan gasa,ni yanzu Abu daya ne ya shige min duhu, kuma ba komai bane na fuskanci cewar akwai wanda ya taimaki Imhal da sihirin tsafi a Yau lokacin da ake wannan gasa,kuma bansan ko waye ba, amma yanzun nan zan bincike na gane ko waye.Koda gama fadin hakan sai sarki gurzalu ya mike tsaye ya shige cikin kuryar dakin da ya kwana inda akwatinsa ta ke,da Isarsa gaban akwatin wacce ta kasance katuwar gaske mai nauyi, kuma wacce ke datse da katon kwado,sai ya kurma uban ihu, Cikin firgita lamirat da dakarun sa dake can kofar turakar suka rugo izuwa cikin dakin, A dimauce LAMIRAT ta dubeshi tace,Me ya faru ya kai Abbana kai kurma uban ihu haka? maimakon ya bata amsar tambayarta sai ya juyo a fusace ya fuskanci wadannan dakaru nasa masu tsaron dakin yace, Bayan mun tafi filin gasar JARUMTA waye ya shigo cikin dakin nan? Shugaban Dakarun ya risina yace, Ya shugabana babu wanda ya shigo, in baka manta ba kai da kanka na kulle dakin da mukulli da zaka fita ,kuma yanzu ma da kai dawo kai ka bude shi da hannun ka... Kafin badakaren ya rufe bakinsa tuni Sarki gurzalu ya sare takobinsa cikin bakin zafin nama ya fille masa kai, sai ga jini yana tsiri izuwa saman dakin ta cikin jijiyoyin wuyan badakaren, sannan kuma sai gangar jikin ta fadi kasa rub da ciki,Faruwar hakan ke da wuya sai ragowar dakarun suka firgita ainun suka dauke gawar dan'uwansu da sauri suka fice da ita,A sannan ne sarki gurzalu ya dubi lamirat a lokacin da idanunsa suka kada suka yi jawur yace,Wani yazo ya sace min gurun tsafina, maza ki tafi neman wannan barawo a cikin garin nan,shine wanda ya taimaki Imhal a filin gasa. Da jin haka sai LAMIRAT ta juya da sauri ta tafi izuwa can bangaren da turakar sarki taryan take domin ta sanar dashi abinda ya faru kuma ta nemi izininsa akan tafiya cikin gari don farautar barawon mahaifinta. Lokacin da sarki taryan ya tafi da Gimbiya Shumaira izuwa cikin turakarsa, bayan Angama wannan gasar JARUMTA, sai ya tunkude ta ta fada kan wata doguwar kujera, ya dubeta cikin fushi har muryarsa na rawa yace,akan me Zaki so jarumin da yake fada da nawa jarumin?sabo dame Zaki nuna soyayyar ki a fili gaban jama'a ki zubar da kimarki da mutuncin gidan nan?Shin kinsan irin makudan kudaden da nayi asara a wannan gasa bisa kudin da na zuba a cacar da mukayi ni da sarki gurzalu? Lokacin da sarki taryan yazo nan a jawabinsa sai gimbiya Shumaira ta sunkui da Kanta kasa cikin biyayya tace,ka gafarceni ya kai Abbana, ka sani cewa a rayuwata ban taba son wani da namiji ba a rayuwata ba face wannan bakon jarumi, kai da kanka kayi mini tayin 'ya'yan sarakai guda ashirin da uku a wannan nahiya amma nace akai kasuwa, idan baka manta ba na gaya maka cewar, bazan yi aure ba face na samu jarumi mai tsananin sa'a da JARUMTA, kaga kuwa lallai babu wanda ya dace dani face wannan bakon jarumi tunda gashi sa'arsa ta bayyana a fili, tunda gashi ya kashe jarumin da babu kamarsa, alhalin a zahiri bai isa ya iya da shi ba.Yayin da sarki taryan ya ji wannan batu sai jikinsa yayi sanyi, kuma hankalin sa ya dugunzuma yayi shiru ya kasa cewa komai, kwatsam! sai ga wani babban hadimansa ya shigo cikin turakar sa,hadimin ya risina ga sarki taryan yace,ya shugabana Gimbiya LAMIRAT 'yar sarki gurzalu tazo yanzu, tace tana son ganinka cikin gaggawa, Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama sarki taryan tare da Gimbiya Shumaira suka dubi juna sannan ya dubi hadimin yace, he ka kace ta shigo,nan take hadimin ya fita sai ga gimbiya LAMIRAT ta shigo fuskar ta a murtuke babu annuri, kai da gani kasan cewa tana cikin tashin hankali, LAMIRAT ta risina ga sarki taryan tace,Ranka ya dade barawo ne ya shiga cikin masaukin Abbana ya sace masa wani Abu mai darajar gaske.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke sarki taryan da Gimbiya Shumaira, sarki taryan ya dubi lamirat yace, Tun da aka gina gidan sarautar nan tsawon shekaru dari da goma Sha daya ba a taba yin sata ba a cikin sa sai Yau,lallai ko wane ne yayi wannan sata ya cika hatsabibin gaske, domin nasan irin tsaron da yake gidan nan yafi gaban misali, ko sarkin barayin aljanu yana shakkar yazo yayi sata a nan, wai shin mene ne abinda aka satar muku? lallai zan sa a tsananta bincike har a kamo wannan barawo, kuma ki gayawa mahaifin ki cewar komai kimar abinda aka sace masa zan biya shi.lokacin da gimbiya lamirat taji wannan batu sai ta gyada kai cikin alamun takaici tace,Inda zaka cika gidan sarautar nan taka da darhami, baza ka iya siyan abinda aka sacewa ubana ba,ni yanzu abinda ya kawo ni gareka shine, ka bani izinin shiga cikin gari don farautar wannan barawo, kuma ka bani dakarun ka wadanda za suyi mini rakiya, wadanda suka San sirrin birnin ka sosai, in yaso kayi naka binciken daga baya, Koda jin wannan batu sai sarki taryan ya sake kamuwa da tsananin mamaki, kuma hankalin sa ya dugunzuma ainun, nan take ya tura aka kirawo masa wani badakare mai suna DARHUS, ya dubeta shi yace, maza ka debi jama'arka mutum dubu uku Ku tafi tare da Gimbiya lamirat izuwa cikin gari, lallai ina son Ku bincika gida-gida,lungu-lungu da duk wani sako da ke cikin garin nan domin Ku gano barawon da yayi wa mahaifin ta sata har cikin masaukin da na bashi, kada Ku dawo gareni face kun kamo wannan barawo, idan bakwa son Ku fuskanci fushi na.nan take DARHUS ya risina yace, Angama, kawai sai ya juya da sauri ya fice daga cikin turakar, Gimbiya lamirat ta bishi da sauri. A wannan rana dai sai da hankalin gaba daya mutanen birnin misra ya tashi, domin sama da dakaru dubu arba'in DARHUS ya diba bisa jagorancin gimbiya LAMIRAT suka dinga shiga gida-gida,unguw anni da kasuwanni suna dukan mutane suna caje kayayyakin su ana neman abinda aka sacewa sarki gurzalu.RIJIYA GABA DUBU Littafi na uku 3 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 3C . Duk gidan da aka shiga sai an tarwatsa kayan ciki anyi filla-filla da su kin a duk Inda aka riski bako tasa ta same shi domin anfi tsananta bincike a kansa saboda sai anfara yi masa dukan tsiya anyi laga-laga da shi sannan ma za a fara tuhumarsa, Tun safe aka fara wannan bincike amma har dare ya raba ba a ga abinda ake nema ba,kuma ba a ga wanda ya dauke abin ba,Bisa dole su Gimbiya lamirat suka hakura suka koma gidan sarautar suka sanar da sarki gurzalu da sarki taryan abinda ake ciki, nan fa hankalin sarakunan ya kuma dugunzuma fiye da ko yaushe, musamman ma sarki gurzalu wanda ya tabbatar da cewar duk burinsa na duniya ya rushe idan har ba a ga wannan Abu da aka sace masa ba,nan fa sarki taryan ya sake dimaucewa bisa ganin yadda hankalin sarki gurzalu ya Tashi ainun, don haka sai ya sake baza dakaru izuwa cikin birni da kauye kai har izuwa cikin dazuzzuka ma yace duk inda aka ga wadansu baki a kamo su azo dasu Koda kuwa sun kasance fatake ne masu wucewa,haka kuwa al'amarin ya kasance aka yi ta kamo baki ana kai su kurkuku ana kullewa, har sai da babban kurkukun birnin ya cika fal sannan aka dinga kaiwa sauran kananan gidajen maza da ke wurare da bam.A wannan dare dai sarki gurzalu bai yi bacci ba har gari ya waye bisa tsananin tashin hankalin da yake ciki. Ba wani abu aka sacewa sarki gurzalu ba face gurunsa na tsafi wanda shine kadai abinda ya dogara da shi akan cewar yana bashi sa'a a gasar jarumtakar da akeyi a birnin misra tsawon shekaru, abinda ya fi razana shi shine, yanzu yaya zai yi da batun shiga wannan gasa,ya sani cewa saura wasa biyar ga jarumi Imhal su hadu a filin gasa su fafata, Koda yake dai yanzu Imhal bashi da lafiya, dole ne yayi jinya ta tsawon Koda kwana bakwai ne,kuma ya San cewa ko babu wannan gurun tsafi a tare dashi ba ya shakkar karo da Imhal domin Idan har bai samu nasarar kashe shi ba sai dai ayi RAGAS indai da zallan karfin damtse da kwarewar yaki za suyi fadan, babban abin tashin hankali shine, barawon da ya sace gurun tsafin sa ba karamin sihirin tsafi ne da shi ba tunda har ya iya shiga har cikin masaukinsa ya sace gurun ba tare da asirin sa ya tonu ba kuma tabbas zai cigaba da taimakon Imhal a cikin wannan gasar jarumtaka da ake yi har ya kai ga nasara. Abinda ya fadowa sarki gurzalu a rai shine, yana da zabi guda biyu rak! Ko dai ya koma can birnin Kisra ya shiga halwar tsafin sa yayi bincike don ya gano ko waye wannan barawo da kuma inda yake kafin a cigaba da gasar JARUMTA, ko kuma duk yadda za ayi ya gano barawon kafin gasar tazo kansa,nan fa sarki gurzalu ya rasa hukuncin da ya kamata ya yanke, Babu yadda sarki taryan bai yi ba don ya San abinda aka sacewa sarki gurzalu amma abun ya gagara, domin yaki ya gaya masa,Dama ya dameshi da tambaya sai yace dashi, Abinda aka sace mini yafi komai da kowa daraja a idanu naka wannan duniya, tunda sarki taryan yaji wannan batu sai yayi shiru bai kara yi masa magana ba.kashe gari kuwa tun kafin hasken rana ya fito su Gimbiya lamirat suka sake bazama izuwa cikin gari neman barawon sarki gurzalu. Al'amarin Gimbiya Shumaira kuwa,a wannan rana sai ts rasa sukuni, domin ta kasa zaune ko tsaye, kuma ta kasa yin bacci, ba komai ne ya janyo hakan ba face duk sanda ta runtse idanunta bata ganin komai face jarumi Imhal, nan take taji tunani da begensa sun addabe ta kuma taji bata da sauran kwanciyar hankali idan bata je ta gan shi ba,domin gani take kamar mutuwa zai yi sakamakon wannan Sara da jarumi Darwaz yayi masa a kirji, nan fa Shumaira ts fara tunanin hanyar da zata ni taje ta ga jarumi Imhal a can inda aka tsareshi, Samun wannan dama kuwa ba karamin aiki bane saboda babu wanda yake da ikon zuwa wannan wuri face sarakunan biyu wato sarki taryan da sarki gurzalu domin dokar da aka kafa kenan tun jiya da aka kai Imhal aka tsare, Koda Shumaira taga tunanin yayi mata yawa ta kasa komai sai ta fito daga cikin turakar ta,A wannan lokaci da ko wanka ba tayi ba,kuma tana sanye ne da rigar bacci wacce ke nuna dukkan siffofin jikinta, kawai sai ta kama kai kawo a cikin harabar turakar ta ta inda kuyanginta ke ta kai kawo suna

Chapter 5 of 7