Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels RIJIYA GABA DUBU Littafi na daya 1 Na Abdulaziz sani m gini Ebook publish by - http://hausaebooks.cf Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 1A . Saurayin gudu yake iya karfinsa acikin dajin domin ya ceci rayuwarsa, . yana gudu yana waigen bayansa cikin tsananin tsoro,amma baya ganin komai kuma baya jin sautin komai face na masifaffun karnukan dake biye dashi. . Su dai wadan nan karnuka sun kai guda saba in da doriya kuma sun kasance jibga jibga tamkar ba karnuka bane kai kace kurayene sabo da girmansu da kwarjininsu gami da ban tsoro,musamman aka kiwata wadan nan karnukan kuma aka basu horo na musamman domin suyi gadin babban kurkuku na birnin Kisra. . A tarihin birnin na kisra tunda aka gina kurkukun tsawon shekaru arba in ba ataba samun fursuna da ya taba guduwa daga cikin sa ba sabo da karfin tsaron da ke cikinsa sai wannan saurayi wanda ake kira IMHAL IBN IMZANU, . sabo da tsananin karfin gudun Imhal ne ya baiwa karnukan tazara ta kimanin taku sittin amma sabo da nacin karnukan da mugun horon da suka samu sai gashi sun fara hango shi,nan fa suka kara kaimi,nan fa Imhal ya kara kaimin gudunsa alokacin da ya waigo ya hango su yaci gaba da falfala azababben gudu ta cikin kwazazzabai da sarkakiya, sabo da karfin gudun ma har tashi sama yake yana tsallake duwatsu da karyayyun bishiyoyin da suka fadi kasa . Shi dai Imhal gudun kawai yake yi acikin dajin amma baisan inda yake dosa ba,sabo da baisan ma a inda yake ba bare ma yasan hanyar da ya kamata yabi, a duk sanda ya tuno da bakar wahalar da ya sha kafin ya sami nasarar guduwa daga kurkukun sai ya kara kaimin gudun nasa yana mai ayyanawa a ransa da dai a kamasa a raye a mai dashi cikin kurkukun gwara a sami gawarsa sabo da azabar da take cikin kurkukun ta wuce tunanin mai tunani. . Asalin Imhal bin Imzanu mutumin birnin misira ne kuma shi ba dan kowa bane kuma bai aikata laifin komai ba,mahaifinsa wani makiyayi ne mai kiwon dabbobi a daji,don haka rayuwar Imhal gaba daya a cikin daji take,sai dai a karshen kowane sati ranar Lahadi sukan shiga cikin gari suyi dan siye-siyen su sannan su koma daji inda suka gina bukkarsu. . Imhal ya taso da Jarumtaka juriya da iya farauta,sanan komai yawan dabbobi idan ya tafi kiwo dasu yana iya sarrafa su . Lokacin da Imhal ya fara girma ya cika shekaru goma sha shida ne ya tambayi mahaifinsa tsoho Imzanu yace ya kai Abbana me yasa baka taba bani labarin mahaifiyata ba?ban santa ba kuma bansan yanda akayi ta mutu ba kullum sai kace dani kawai mutuwa tayi,kayi sani cewa yanzu ni ba yaro bane karami na mallaki hankalin kaina yakamata ka sanar dani gaskiyar al amari, koda tsoho Imzanu yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun yayi shiru yana mai sunkui da kansa kasa,kawai sai idanunsa suka ciko da kwalla hawaye ya fara zubowa kas, a sannan ne ya dago kai ya dubi Imhal yace yakai dana kasani yau ka tambayeni wani sirri wanda dama nayi alkawarin bazan sanar dakai ba sai bayan ka mallaki hankalinka,don kada hankalinka ya dugunzuma kwakwalwarka ta kasa daukar al amarin, koda imzanu yazo nan a zancensa sai ya sake yin shiru kamar bazai iya cewa komai ba,da kyar ya sake dago kai ya dubi Imhal muryarsa na rawa yace ka gafarceni yakai dana bisa abinda zaka ji daga bakina yanzu domin zakayi matukar mamaki kuma zai iya girgiza ka,maganar gaskiya ita ce ni ba mahaifinka bane na jini,koda jin wannan batu sai zuciyar Imhal ta buga da karfi,nan take idanunsa suka kada sukayi jawur,bai san sanda hawaye ya zubo masa ba yace yanzu idan ba kaine mahifina ba to wanene? Bansan kowa ba a rayuwata sai dai kai kadai, kaine kasan cina da shana tundaga kuruciyata har izuwa yanzu,me yasa uban nawa ya gujeni ya barni a wajanka cikin daji inda babu jin dadi da tsaro? . lallai kuwa ashe babu soyayya tsakani na da uban nawa tunda bai damu da rayuwata ba. Koda Imhal yazo nan a zancensa sai tsoho imzanu ya zubar da hawaye sannan yace Ni kaina bansan waye mahaifinka ba,ka saurara dakyau kaji labarin da zan baka yanzu, wata kila idan kaji labarin zuciyarka tayi sanyi ka rungumi kaddara a bisa halin da ka tsinci kanka a ciki ....... ..¤¤¤¤¤¤¤ Wata rana da safe na fito kiwo acikin dajin nan ina kada dabbobi na sai kawai na hango wasu mutane bisa keken doki sanye da bakaken tufafi kuma sun rufe fuskokinsu su biyu sun nufi bakin wani katon rami mai zurfi da fadin gaske,cikin hanzari na kada dabbobina izuwa cikin duhuwar bishiyoyi nima na sami wuri na buya, dama wadannan mutane basu ganni ba,ina nan labe cikin duhuwa sai naga wadannan mutane sun fiddo gawar wata mace daga cikin keken dokin sun cillata cikin wannan ramin, kawai sai suka shiga cikin keken dokinsu da sauri suka fice daga cikin dajin gaba daya,sai da na tabbatar da cewa sunyi nisa da tafiya kuma babu alamar cewa zasu dawo sannan na ruga izuwa bakin wannan ramin na leka cikinsa kawai sai naga ashe wata kyakkyawar mace ce aka yanka ta har a sannan jini na bulbulowa daga cikin makogwaronta kuma tana dauke da tsohon juna biyu,nan take naji na kamu da tsananin tausayinta, . don haka sai na yanke shawarar na shiga cikin ramin na dauko gawar wannan mata domin na suturta ta sosai na haka kabari mai kyau na binne ta,idan ma na barta acikin ramin zata rube ne warinta ya dameni tunda ramin yana kusa da inda bukkata take,nan fa na fara tunanin dabarar da zanyi na iya shiga cikin wannan rami har na iya dauko gawar,sai da nayi tunani na tsawon 'yan dakiku sannan dabara ta fado mini,kawai sai na ruga da gudu izuwa cikin bukkata,na dauko igiya mai tsawo sannan na dawo bakin ramin,na daura igiyar a jikin wata bishiya na wurgata cikin ramin sannan na kama igiyar ina binta ina shiga ramin,sannu a hankali na isa kasan ramin,koda naje kan gawar na duba ta sai naga ashe da ranta bata mutu ba domin numfashinta na fita kadan-kadan,cikin gaggawa na sunkuci wannan mace na goya ta a bayana na daureta tamau,na sake kama igiyar nayi iya kokarina na fito daga cikin ramin goye da matar a baya na,hankalina a dugunzume,sauri nake kawai na jarraba ceto rayuwarta,ina fita daga cikin ramin na ruga da ita izuwa cikin bukkata,na shimfide ta a kasa sannan nayi sauri na dauko allura da zarin dinke fata na dinke raunin wuyanta sannan na shafa magani akan raunin,A sannan ne na kara hancina a dai dai hancin matar don naji ko tana yin numfashi,amma sai naji shiru alamar babu rai a jikinta,nan fa bakin ciki ya lullube ni naji kamar na fashe da kuka sabo da takaici,gashi nasaa wahalar dauko ta daga cikin wannan ramin mai zurfi har ma tafin hannuwana sun dade saboda kama igiya,cikin sanyin jiki na mike na sunkuya da nufin daukar gawar na fita da ita waje inda zan binne ta,kawai sai naji tayi tari,numfashinta ya dawo,nan take murna ta kamani na ruga na dauko wani ruwan magani na dura mata a baki dakyar tasha mukurwa uku,jin kadan sai idanunta suka bude dakyar,koda tayi arba dani sai naga ta firgita ta yunkura zata tashi amma sai na danne kafadunta na hana ta tashi,matar ta budi baki da nufin tayi magana sai ta kasa,kawai sai naga tana dariya,wani lokacin kuma sai ta hade fuska ta kama kuka tana fisgefisge,nan fa na gane lallai wannan mata ta samu tabin hankali,al'amarin da yayi matukar bakanta raina kenan domin naso ace ta iya yin magana acikin hankalinta,domin na tambayeta ko ita wacece da kuma wadannan mutane da suka kawo ta dajin acikin keken doki a matsayin gawa,abinda zuciyata ta aiyana min shine in ma basu bane to sun san wanda ya kasheta,kuma akwai wani boyayyen al'amari akan kisan nata,daga wannan rana naci gaba da jinyar wannan mata har tsawon kwana ashirin da daya,A tsawon wadannan kwanaki kullum a kwance take kuma koda tayi yunkurin mikewa zaune sai ta kasa sabo da raunin da yake makogwaronta,haka kuma bata taba yin magana ba sai fisge-fisge da dariya irinta mahaukata,abinci kuwa sai dai na dura mata abaki tana ci tana kuka sabo da ciwo,da yake naga tana dauke da juna biyu sai na dinga yawan bata madarar shanu gami da abincin da yake gina jiki domin abinda ke cikinta ya samu cikakkiyar lafiya,a kwana a tashi har wannan mata ta shafe wata uku cur a wajena,a sannan ne raunin makogwaronta ya warke sumul har ya zamana cewa tana iya magana sosai,amma a koda yaushe babu magana ta hankali da nutsuwa a tare da ita sai maganganu irin na mahaukata,nayi iya kokarina akan ta gayamin ko ita wacece,daga inda take da kuma yadda akayi ta shiga wannan hali sai tayi ta kyalkyala mini dariya,ganin hakane yasa tausayinta ya karu a zuciyata,sau bakwai ina nemo masana ilimin maganin mahaukata,wato likitocin mahaukata suna zuwa su dubata kuma su bata magani,amma duk a banza lafiya taki samuwa,sau tari matar takan sulale ta nausa cikin daji bansani ba,sai nasha wahalar nemota,bisa wannan dalilin ne ma duk sanda zan fita kiwo ko farauta sai na tafi tare da ita,wato na daina barinta a gida. Lokacin da cikinta ya tsufa sai tafiya da ita kiwo ko farauta ya gagara,don haka nima sai na hakura da zuwa ko ina,na tanadi abincina da na dabbobi na mai yawa wanda zai kai tsawon kwana arba in,Ai kuwa adaren kwana na talatin da bakwai nakuda ta kama wannan mata acikin tsakiyar dare.Al'amarin da yai matukar dugunzuma hankalina kenan tunda babu halin in ruga cikin gari in nemo ungozoma,Da yake na taba shiga irin wannan hali da nake tare da matata wacce ta rasu a wajen haihuwa abinda ta haifa ma yazo a mace,sai na shiga taimakon wannan mata,nine na yankewa jaririn cibiya,na wanke shi sannan na kimtsa mahaifiyar tasa,matar taci gaba da rainon jaririnta tana shayar dashi ni kuma ina cigaba da fita farauta da kiwona ina barinsu a gida,har tsawon shekara daya da wata bakwai muna tare sannan yaron ya fara tafiya da kafafunsa. Kwatsam wata rana naje kiwo na dawo sai na nemi wannan mata sama da kasa na rasa,kuma ga dannan ta bar shi acikin bukka a zaune shi kadai yana ta tsala kuka,cikin dimaucewa na dauki yaron na gaya shi a bayana sannan na bazama neman wannan mata wacce ko sunanta ban saniba bare na dinga kwalla mata kira,Abu kamar wasa sai da na shekara daya da wata tara ina nemanta amma ko alamunta ban gani ba acikin wannan daji.A tsawon wannan lokacin ni nake kula da wannan yaro da ta haifa dare da rana,ya zama cewa na shaku dashi ainun shima haka .Kwatsam wata rana da yammaci ina wasa da yaron a kofar bukkata kawai sai na hango wannan mata daga can nesa ta durfafo bukkata,cikin alamun tsananin mamaki na mike tsaye na zuba mata idanu,matar ta rame matuka,kuma duk rigar jikinta ta yayyage,sannan tayi baki sabo da wahala da kazanta,koda ta iso daf dani ta dubeni sai ta fashe da kuka ta durkusa kasa bisa gwiwoyinta tana mai neman gafarata tamkar mai cikakken hankali,nan take naji na kamu da tsananin tausayinta don haka sai na kama kafadunta na tasheta tsaye kuma na rungumeta a kirjina a karon farko tun haduwa ta da ita,ita kuma sai ta kankame ni ta da da fashewa da kuka,kawai sai na janye jikina daga nata na dubeta nace me yasa kika gudu kika barmu?shin kin manta ne cewa kin bar danki a hannu na?koda jin haka sai matar ta dubi dan nata ta girgiza kai tace ai ni kananin yaro na bar maka bai kai wanan girma ba,da jin haka sai nayi dariya nace to ai kullum mutum dada girma yake har yanzu baki gaya min inda kika tafi ba kika barmu,Matar ta bushe da dariya sannan ta hade fuska tace shan iska na tafi na sake dawowa.Cikin tsananin damuwa nace yau shekara hudu kenan muna tare baki taba gaya min sunanki ba kuma baki gaya min sunan garinku ba bare nasan asalinki da danginki shin bakya tausayin wannan yaron da kika haifa ne?Koda jin wannan tambaya sai matar ta sake bushewa da dariya tace bansan kaina ba kuma bansan kowa ba sai kai,tana gama fadin haka ta juya ta shige cikin bukka taje ta kwanta ta kama bacci,tun daga wannan rana muka ci gaba da zama tare,amma ko kadan wannan da nata bai dameta ba,kuma bata yi masa komai sai dai ni nayi masa,wani lokaci sai naga kamar hankalinta ya dawo tana magana a nutse,amma da zarar na fara tambayarta asalinta da garinsu sai ta birkice ta koma hauka. Wata biyu da kwana uku mukayi tare ranar kwana na ukun ne matar ta wayi gari da tsananin rashin lafiya wadda bansan sanadinta ba,cikin rudewa na shiga hada mata magunguna iri-iri ina bata tana sha amma duk a banza tamkar kara mata ciwon akeyi,kawai sai naga idanunta sun fara lumshewa kuma numfashinta na sarkewa,Al amarin da ya dugunzuma hankalina kenan na fara zubar da hawaye,na shiga yi mata tambayoyi akan ta sanar dani asalinta,matar na kokarin bude baki tayi magana amma sai ta kasa,nan take jikinta ya sandare,idanunta suka kafe ta daina motsi.koda naga haka sai na rungumeta na fara kuka,ganin ina kuka ne dannata wannan yaro dan shekara kusan hudu ya rugo izuwa kaina shima ya fashe da kuka.Hakika wanan rana nayi kuka mai yawa sabo da shakuwar da nayi da matar nan sai da nayi kwana ashirin da daya bana iya cin abinci sosai,amma koda yaushe hankalina yana kan wannan yaron ina kula da lafiyarsa sosai. Koda tsoho Imzanu yazo nan a zancensa sai Imhal ya tari numfashinsa suka dubi juna a lokacin da kowannensu yake zubar da hawaye yace yakai Abbana na gane cewa wannan yaro da mahaukaciya ta haifa ba wani bane face ni dinnan,tabbas yanzu na tabbatar da cewa ni marayane wanda bashi da uwa bashi da uba kuma wanda baisan asalinsa ba,koda Imhal yazo nan zancensa sai tsoho Imzanu ya rungumesa suka fashe da kuka tare,can sai Imhal ya janye jikinsa suka fuskanci juna ya dubi Imzanu yace Bazan taba yarda bani d uba ba amma ni kai na sani a matsayin ubana,ina son nayi maka wata tambaya guda daya menene dalilin da yasa kake kirana da suna IMHAL? . WASA FARIN GIRKI .RIJIYA GABA DUBU Littafi na daya 1 Na Abdulaziz sani m gini Typing:- Ibrahim S combatant Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Part 1B. Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa tsoho Imzanu yace Abinda yasa nasa maka suna Imhal shine a iya zama na da mahaifiyarka har ta mutu ban taba jin ta ambaci sunan wani mahaluki ba face IMHAL,A kullum duk sanda za taci abinci sai naji tana kiran sunansa tana cewa yazo suci abincin tare,abinda na fahimta shine,koma wanene wannan Imhal din lallai ya kasance babban masoyi a gareta,zai iya kasancewa mijinta ne ko dan uwanta ne ko mahaifinta,Abu na biyu da nake zargi shine,duk yadda akayi mahaifiyarka ta fito daga babban gida domin a ranar da na tsince ta acikin wannan katon ramin mai zurfi sutturar dake jikinta mai matukar tsada ce,babu mai sanya irinta face sarakai da manyan attajirai,babban bakin cikina shine babu wata shaida a tare da mahaifiyarka wadda zata iya sawa a gano asalinta,koda tsoho Imzanu yazo nan a zancensa sai suka sake rungume juna,daga can sai Imhal ya dubi tsoho Imzanu yace,Lallai zan rike sunana a zuciyata da bakina,lallai wata rana wannan suna zai taimakeni na gano asalina. Tun daga wannan rana Imhal da tsoho Imzanu suka cigaba da rayuwarsu acikin daji kamar yadda suka saba,amma sai ya zamana cewa kullum sai Imhal ya shiga cikin garin Kisra kuma duk inda yaje si ya tambayi mai suna Imhal,idan aka tambayeshi wane Imhal yake nema sai ya kasa bayani domin baisan wata inkiya ba ta Imhal din da yake nema,hakane yasa suka dinga yiwa Imhal dariya suna cewa dashi Bagidaje mutumin daji,saboda ganin yanayin shigarsa ta makiyaya. Wata rana Imhal yazo giftawa ta kofar gidan sarkin kisra akayi sa a kuwa a lokacin sarki ya fito daga cikin gidan sarautar zai fita rangadi kwatsam sai yayi arba da sarki,Abinka da wanda baisan yadda ka idar sarauta take ba sai kawai ya kurawa sarki idanu,maimakon ya zube kasa gabansa ya kwashi gaisuwa,ai kuwa sai dakarun sarki suka afkawa Imhal da duka har suka kai shi kasa,cikin fushi ya yunkura ya watsar dasu duka duk da cewar sunkai su ashirin,nan take shima ya rufesu da duka,duk wanda yayi wa naushi daya sai ya baje a kasa sumamme,koda ganin haka sai ragowar dakarun sarki suka zare takubbansu sukayi caa akan Imhal zasu sassara shi,amma sai sarki ya daka musu tsawa suka saurara,nan take sarkin kisra ya sauko daga kan dokinsa yazo daf da Imhal yadda har suna iya jin numfashin juna,sannan ya dubeshi cikin murmushi yace,A duniya babu abinda yake birgeni sama da jarumtaka,tabbas na yarda kai jarumi ne amma ina son na gwada jarumtaka ta akan taka,nasan baka san koni waye ba to nine Sarkin garin nan,koda jin haka sai Imhal ya zube kasa bisa gwiwoyinsa yana mai sunkui da kansa kasa yace ka gafarceni ya shugabana,kasan cewa ni rayuwata gaba daya cikin daji nayi ta,sau daya a sati muke shigowa cikin garinnan,yau ne ranar farko da na fara ganinka a rayuwata,ya shugabana kayi min afuwa domin bazan iya fada da kai ba,Koda jin wannan batun sai sarki ya bushe da dariya ,lokaci guda kuma ya hade rai ya dubi Imhal cikin nutsuwa yace,ya kai wannan saurayi ma abocin jarumtaka kayi sani cewa nahiyar nan gaba daya babu wani jarumi ko mayaki mai karfi da iya yaki kamata,yau shekara talatin kenan ina gwagwarmaya da gumurzu kuma sau arba in da uku ina lashe GASAR JARUMTAKA a kasashe arba in da uku dake cikin wannan nahiya tamu ko sau daya ba a taba samun jarumin da ya lakuci jikina ba bare ya kaini kasa,naga jarumtakar jarumai da yawa a rayuwata,amma ban taba ganin jarumi mai zafin nama da karfin naushi kamarka ba,ina da tabbacin cewa idan muka fafata sai na sami nasara akan ka duk da cewar na yaba da karfinka,ka sani cewa kana da zabi guda biyu kodai ka yakeni ko kuma yanzun nan nasa tagobi na sare maka kai,koda jin wannan batu sai hankalin Imhal ya dugunzuma ya mike tsaye cikin sanyin jiki,abu na farko da ya fado masa a rai shine,Ai bai kamata ya mutu yanzu ba har sai ya gano asalinsa,koda gama aiyana hakan acikin zuciyarsa sai ya mikawa wani badakare hannu yace bani tagobinka,ba tare da gardama ba kuwa ya mikawa Imhal tagobinsa ya karba,koda ganin haka sai murna ta kama sarki,shima ya zare tagobinsa,a lokacinne dakaru suka buda suka yi musu da ira aka sa su a tsakiya,nan fa sarki da Imhal suka fara zagaya juna suna kallo-kallo. Lokaci guda kowannensu ya daga tagobinsa sama suka ruga izuwa kan juna,suka ruguntsume da azababben yaki ya zamana suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta ta ban al'ajabi,sai da suka shafe sa a guda suna wannan bakin artabun amma dayansu bai samu nasarar koda kwarzanar mutum daya ba,Al'amarin da ya fusata sarki kenan kuma ya cika da tsananin mamakin yadda akayi wannan mutumin dajin ya samu gagarumin horon yaki haka,nan take sarki ya canza salon yaki,ya dinga tsalle-tsalle da kwance-kwance,kawai sai yaga Imhal ya iya duk irin abinda yake yi tamkar tare aka koya musu yaki babu wani banbanci,koda ganin haka sai sarki ya ja da baya taku biyar,shima Imhal sai yayi hakan amma shi taku uku yayi,duk su biyun suka kurawa juna idanu na tsawon yan dakiku kadan,kawai sai sarki ya rugo da gudu izuwa kansa,shima sai ya ruga gareshi,kafin su hadu sai kowannensu ya daka wawan tsalle sama ya kai hari cikin mugun nufi,Acikin tsananin zafin nama kowannensu ya kaucewa harin takubbansu suka sari iska,amma kafin su duro kasa sun gwarawa juna fuska,ai kuwa sai hancin kowannensu ya fashe,a saman sai suka sake kaiwa juna hari,sai sarki ya sami nasarar yankar Imhal a saman cibiyarsa,Shi kuma ya sami nasarar yankar sarki a gefen wuyansa,kowannensu jini yayi tsartuwa daga jikinsa suka rikito kasa a matukar galabaice,A guje Dakaru suka ruga aka baiwa Sarki rawani ya daure wuyansa da jini,take likitan Sarki yayi masa magani,Kawai sai Dakaru suka ruga izuwa kan Imhal wanda yake kwance a kasa ya dafe raunin don tsaida jini zasu halaka shi,Sarki ya daka musu tsawa suka fasa,kawai sai sarki ya dubi likitansa yace Idan ka gama dani kaje kayiwa wannan saurayin magani,Cikin gaggawa kuwa likita ya gama yiwa sarki magani sannan yaje yayiwa Imhal,Sa ar da Sarki da Imhal sukayi raunikan basuyi zurfi ba a jikin su,Tunda Likitan ya fara yiwa sarki magani sai zuciyar Sarki ta fara tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin bakin ciki da takaici bisa ganin yadda a yau wannan bakon saurayi ya karya alkadarinsa na jarumin dake rike da KAMBUN JARUMTAKA na nahiyar gaba daya,Bayan angama yiwa Imhal magani ya mike tsaye sai yazo gaban Sarki ya risina yayi godiya,Sarki ya dube shi cikin yake yace Tabbas ka cika jarumi abin kwatance amma ka saurari ranar da zamu sake haduwa a filin gasar JARUMTAKA wacce za ayi a birnin MISIRA nan da cikar wata uku,ko kana so ko baka so sai ka shiga wannan gasa kuma ina tabbatar maka da cewar sai na sami nasara akan ka na kasheka murus har Lahira,yin hakane kadai zai sa na huce bisa takaici da bakin cikin da ka jefani a ciki,Koda ya gama fadin hakan sai Sarkin Kisra ya dubi wani babban Badakare nasa yayi masa rada a kunne sannan ya juya ya kama dokinsa ya hau ya kada linzaminsa yayi gaba,sauran dakarun gaba daya suka rufa masa baya.Shi kuwa jarumi Imhal sai ya tsaya cak yabi sarkin kisra da kallo cikin tsananin mamaki,Imhal ya tambayi kansa cikin zuciyarsa yace WAI SHIN MENENE YAYI ZAFI HAKA,HAR DA SARKI YACE ZAI KASHENI MURUS HAR LAHIRA ALHALIN MA BASU TABA GANIN JUNA BA SAI YAU?AKAN WANE DALILI ZAI TSANANTA GABA A TSAKANINMU HAKA?koda Imhal ya kasa baiwa kansa amsa sai ya juya ya falfala da gudu ya nufi hanyar da zata kaishi daji. Imhal ya ci gaba da gudu har sai da ya iso dajin da bukkarsu take,yana cikin gudu ne ya hango tsoho Imzanu ya goyo jakarsa ta tafiya yana dogara sanda ya baro bukkar acan baya,cikin kaduwa da matukar mamaki Imhal ya karasa wajen Imzanu da gudu ya tareshi yana mai rike kafadunsa ya dube shi yace Ya kai abbana lafiya kuwa?ina zaka je naga ka dauko jakarka ka nufi hanyar cikin gari?Koda tsoho Imzanu yaga Imhal a tsaye gabansa sai fuskarsa ta fadada da murmushin farin ciki,har ya budi baki zai ce wani abu sai idanunsa suka kai kan raunin dake kan kasan cibiyar Imhal,cikin firgici Imzanu ya dube shi yace yaya akayi ka samu wannan raunin?koda jin wannan tambayar sai Imhal ya kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninsa da sarki Kisra ya zayyana masa ba tare da boye masa komai ba,koda jin wannan labarin sai hankalin tsoho Imzanu ya dugunzuma ainun har idanunsa ya ciko da kwallah ya dubi Imhal yace ya kai dana ina so ka sani cewa kamar yadda ka kasance maraya a garin nan haka nima nake,iyayena da kakannina duk sun mutu,matata ta mutu tare da dan da ta haifa kamar yadda na baka labari,A halin yanzu bani da kowa face kai wane irin hali kake tsammanin zan shiga idan na rasaka?ina mai tabbatar maka da cewa idan har ka halacci gasar jarumtakar da za ayi nan da cikar wata uku a birnin Misira sai ka rasa rayuwarka domin tabbas sai sarkin garinnan ya kashe ka,domin zai je yayi gagarumin shiri ne yayi amfani da karfin sihirin tsafi wanda dole sai ya samu nasara akan ka,A halin yanzu bamu da wani zabi wanda ya wuce mu sulale mu bar Nahiyar nan gaba daya,indai muka isa wata nahiyar daban shikenan mun tsira daga sharrin sarkin kisra,duk inda muka tsinci kanmu sai mu fara sabuwar rayuwa,duk da cewa ni tsufa ya kamani ina da sauran buri guda daya a duniya,wannan burin ba na komai bane face nason ganin aurenka,koda tsoho Imzanu

Chapter 1 of 7