Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 8
take kuyangin suka risina ga sarkin yaki amzad suka kwashi gaisuwa sannan suka bude musu kofa suka shige suna shiga fadar sai musaira ta zama cikakkiyar yar kauye ta kama kalle kalle saboda kawar dake cikin wannan fadar ya ninka na can inda suka baro sau goma me yasa sarkin yaki Amzad ya zauna yana yin bauta a gidan mu tsawon shekaru alhalin yana da irin wannan daula a gidan duniya? Al amin Ahmed Misau tambayar da musaira tayi wa kanta a cikin zuciya kenan kuma ta kasa baiwa kanta amsa kai tsaye sarkin yaki amzad yaja gimbiya musaira izuwa kan wadansu kujeru na alfarma wadan da aka yi su da farin lu'u lu'u suka zauna, zamansu ke da wuya sai taga fadar ta cika makil da hadiman aljanu sama da su dubu, dukanninsu sai suka zube kasa gaban amzad suka kwashi gaisuwa sannan ko wannen su ya samu kujera ya zauna wajen yayi tsit tamkar mutuwa ta gifta a wannan lokacin ne sarkin yaki amzad ya dubi wadan nan hadiman aljanun gaba dayansu cikin nutsuwa yace yaku dirkokin wannan gida nawa kuyi sani cewar ban taraku anan ba domin komai ba sai domin sanar daku cewar zan tafi aiwatar da wani babban aiki mai mugun hatsari domin dauko takubban sarki zamaru, ina son ku sake tsaurara tsaro a gidan nan fiye da koyaushe domin idan kuka bari wata halitta guda daya ta samu nasarar shigowa gidan bayan bana nan ko a lokacin dana dawo to a lokacin ayyukan ku koda jin haka sai gaba daya hadiman suka sunkuyar da kansu kasa shugaban su ne ya dago kai ya dubi sarkin yaki amzad cikin ladabi da nutsuwa tace ya shugabana kamar yanda muka yi tsaro wannan gida tun zamanin iyayenka da kakanninka haka zamu ci gaba da tsaron shi har izuwa zuri'arka ta karshe, dan haka ka kwantar da hankalinka ka tafi izuwa aikinka zamu tafiyar da komai bisa ka'ida alkawari da amana, koda jin wannan batun sai farin ciki ya lullube sarkin yaki amzad nan take ya daga hannunshi na dama zuwa sama yana baiwa hadiman inkiya ai kuwa sai suka bace bat daga cikin fadar kamar basu taba wanzuwa ba a wajen faruwar hakan keda wuya sai sarkin yaki amzad yayi ajiyar numfashii sannan ya dubi musaira yace ya shugabata ki gafarce ni bisa sanyaki a cikin wannan aiki na sato takubban mahaifinki dalili kuwa babu wanda zai iya taba takubban face ya kasance jinin sarautar gidanku, asalin wadan nan takubban gado ne tun daga sarkin farko na birninku kuma an sihirce su da jinin zuri arku duk wanda bai kasance zuri arku ba indai ya taba wadannan takubban ko kuma suka sareshi ko suka yanki jikinsa sai dafinsu ya zama sanadin ajalinsa, Don haka ni kaina ban isa na taba wadannan takubban ba kcece kadai zaki iya dauko su a lokacin da muka sami damar satosu, lokacin da sarkin yaki amzad ya zo nan a jawabinsa sai gimbiya musaira ta firgita ainun tace kai Sarkin yaki amzad yanzu ta yaya zamu iya sato wadannan takubban alhalin ko yaushe suna jikin mahaifina kuma kome kake takama dashi na sihiri ba zai iya tasiri akansa ba tunda yana tare da boka hizainu sa dda amzad yaji wannan batu sai ya gyada kai yace tabbas duk abinda kika fada gaskiya ne amman kinsan suma babu abinda zasu iya yi mana na cutarwa kuma ki sani shi yaki dan zanba ne, da izinin abin dogaro sai mun samu nasarar sato wadannan takubban na mahaifinki don ceto rayuwar gimbiya lasmin da yarima, in kuma shawartarki da kiyi taka tsantsan da alakar ki da lasmin kuma ki iya sanin lafazin da zaki yi mata magana saboda akwai alamar kishi zai iya hadaku akan yarima koda jin haka sai dariya ta kwace wa gimbiya musaira tace haba sarkin yaki shin ka mantane cewa yarima dan uwa nane na jini akan wane dalilin zan yi kishi da lasmin? Amzad yayi murmushi yace tabbas yarima dan uwanki ne na jini ammah nasabar taku ba zata hana faruwar soyayya ta kullu a tsakaninku ba tunda iyayanku ne yan uwa juna, ko kuma kema kin manta da hakan ? Musaira tana jin haka sai ta sauya hirar tasu tace yanzu dai kayi min bayanin ta yadda zan iya zuwa inda sarki zamaru yake har na sato wadannan takubban yayin da sarkin yaki yaji wadan nan tambayoyin sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi musaira cikin nutsuwa yace Al amin Ahmed Misau, A halin yanzu sarki da boka hizainu suna nan a cikin dajin da muka baro su suna ta binciken akan yadda zasu gano inda muke bisa binciken da nayi sai sunyi kwana bakwai suna bincike sannan zasu gano inda wannan gidan na sihiri da muke ciki yake wanda na gaje shi tun iyaye da kakanni, a halin yanzu naga wani ayari na makiyaya suna kan hanyar zuwa dajin dasu sarki zamaru suke dan haka ya zamar mana dole mu batar da kamanni muje mu riski wadanannan fataken mu shiga cikinsu don mu isa inda su sarki suke dole za a samu wata mu amala da zata hada tsakanin sarki da wadan nan fataken, damar da zamu yi amfani kenan da ita mu sace wadan nan takubban lokacin da sarkin yaki Amzad yazo nan a cikin byaninsa sai musaira ta jinjina kai cikin matukar tsananin damuwa . TO ANAN NE KUMA LITTAFIN KISAN GILLA NA HUDU YAZO KARSHE MARUBUCIN YACE MU HADU A CIKIN LITTAFI NA BIYAR 5 DOMIN JIN CI GABAN WANNAN KAYATACCEN KASAITACCEN LABARI DAGA MAI DEBE MUKU KEWA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI KARKASHIN JAGORANCIN TYPING DIN AL AMIN AHMED MISAU INKIYA GUYSON KO A SQUARE DAN GARIN KADUNA NAKE CEWA MU ZAMA LAFIYA ALLAH YA KAIMU GOBE DOMIN JIN CIGABAN WANNAN LABARI its Real Al amin Ahmed Misau KISAN GILLA 5 Littafi na biyar Na Abdulaziz sani madakin gini Ebook creator:- Shuraih Usman 99% Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini KISAN GILLA Littafi Na Biyar (5) Part A. . . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... BAYAN MUSAIRA TA DANYI GUNTUN TUNANI SAI TA DUBI SARKIN YAKI AMZAD TACE, shi kenan kawai ka tashi muje mu riski wadan nan makiya da wuri domin kwanaki bakwai kacal kadanne akan wannan gagarumin aiki dake gabanmu mai matukar hatsari koda jin haka sai Amzad ya yi murmushi yace, tabbas kinyi zance mai kyau ya shugabata, yanzu kema ki shiga wancan dakin zaki ga tufafi irin na birnin hindu ki dauka ki sanya su ki dubi kanki a cikin madubi sannan ki fito ki sanar dani yadda kika ga kyawunki a cikin madubin, cikin zumudi da walwalar fuska musaira ta mike da sauri ta nufi cikin dakin da sarkin yaki amzad yayi mata nuni dakine na barci mai dauke da gadon barci guda daya rak sai wata doguwar kabet ta karfe gami da dogon madubi like a jikin bango tun daga kasa har sama, da shigowar musaira cikin wannan dakin sai ta nufi inda wannan doguwar kabet din take ta bude sutura irin na kasar hindu sama da kala dari a jibge a ciki, nan take ta dauko wata shudiyar doguwar riga da wando gami da dankwali da mayafi duka shudaye nan take musaira ta cire kayan jikinta ta sanya wadannan data dauko sannan ta je gaban madubi ta tsaya taga yadda kayan suka yi mata kyau Al amin Ahmed Misau, da farko hankalinta yana kan kayan, amman ganin yadda kayan suka yi tsananin mata kyau sai tayi murmushi da farin ciki amma koda ta kalli fuskarta a cikin madubin sai nan take zuciyarta ta buga da karfin gaske, tsoro ya kamata saura kiris ta kurma uban ihu sai ga sarkin yaki amzad ya shigo cikin dakin ganinsa yasa ta kasa yin ihu, ba komai ne ya firgitata ba face ganin kamannin fuskarta sun sauya izuwa wata fuskar daban wacce bata sani ba, fuskace irin ta matan hindu mai matukar kyawun gaske cikin hanzari sarkin yaki amzad yazo daf da ita sannan yace mata, kwantar da hankalinki ya shugabata fuskar ki zata dawo yadda take bayan mun kammala wannan aiki na sato takubban mahaifinki, yana gama fadar haka sai ya dafa madubin dake gabansu faruwar hakan keda wuya sai kamanninsa da kayan jikinsa suka sauya ya zamana cewar shima ya zama ba indiye a cikin gagarumar shiga irin ta manyan attajiransu, kawai sai ya sake daafa kafadar musaira suka bace bat daga cikin dakin basu sake bayyana ba sai a cikin wani jeji kuma a cikin keken doki na alfarma ga dakaru masu tsaronsu kumanin mutum dari har da hadimai hudu nan take aka sa keken dokin nasu a tsakiya aka ci gaba da tafiya aka durfafi dajin dasu sarki Zamaru suke +++ ++++ ***** AL AMARIN SU BOKA HIZAINU KUWA, tun daga wannan lokaci da sarkin yaki amzad ya dauke su yarima suka bace daga cikin daji a lokacin da ake fafata wannan mugun yakin sai takaici ya turnuke sarki zamaru da boka hizainu bayan sunyi iya yinsu basu gano inda su amzad suke ba sai suka zauna a kasa dirshan suka yi tagumi, zuwa wani lokaci daya bai ce uffan ba, daga can sai sarki zamaru yace da boka hizainu cikin alamun fushi da damuwa yace Yanzu daman amzad yafika karfin tsafi? Idan nasan haka ne da tun wuri bamzo wajenka neman wani taimako ba sa adda boka hizainu ya ji wannan magana sai ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta, lokaci guda kuma sai ya turbune fuska ya kalli sarki zamaru yace idan da yafini karfin sihiri ai da ba zai gudu ba ka sani shi tsafi kogo ne dai dai da rana daya idan mutum ya barshi to shi kuma zai barshi da shekara kada ka damu abokina nan da kwana bakwai zan gano maboyar amzad da makiyanka kuma zamuje har can muyi musu kisan gilla koda jin haka sai hankalin sarki zamaru ya dugunzuma ainun kuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, Al amin Ahmed Misau, AA Misau Ke magana, sai ya kalli boka hizainu a fusace yace masa ai sai ka tashi na koma kasata na ci gaba da mulkina idan yaso idan ka gano su sai mu kai musu harin ba zato, dajin haka sai boka hizainu ya bushe da dariya al amarin daya baiwa sarki zamaru mamaki kenan yace masa Menene kuma ma anar wannan dariyar ? Boka hizainu yace ai jarumi na kwarai idan ya fito filin daga baya gudu kuma baya ja da baya lallai ba zamu koma kasashenmu ba face mun kammala da makiyan mu mun aika da su barzahu hm Idan kuwa ba haka ba zasu shammace mu su gama damu yanzu zamu ci gaba da tafiya a cikin wannan dajin ni kuma ina ci gaba da bincikena domin gano wajen da suke mu kai musu mamayar ba zato komawar mu gida tamkar hutun jaki da kaya ne ko nace maka rufe kofa da barawo kasan ance ka kashe makiyinka kafin makiyin naka ya samu damar kasheka ka sani kamar yadda muke shiri akan makiyan nan namu haka suma suke yi akan mu koda boka hizainu yazo nan a jawabinsa sai jikin sarki zamaru yayi sanyi ya aminta da wannan shawarar ta boka hizaimu ba tare da bata wani lokaci ba suka ci gaba da tafiya suna masu kutsawa cikin daji A CAN WANNAN GIDAN SARKIN YAKI AMZAD KUWA, BAYAN TAFIYAR SU Amzad da Musaira sai gimbiya Lasmin ta samu kwarin jikinta tamkar babu sauran wani dafi a jikinta kawai sai ta fito daga cikin dakin da take kwance ta nufin dakin dasu yarima suke kai tsaye saboda dama tasan ko'ina a cikin wannan Gidan sakamakon amincin su da sarkin yaki Amzad da shigarta cikin dakin sai ta iske har yanzu yarima yana kwance akan gado yana bacci, mahaifiyarsa shamilat na zaune daf dashi a gefen gadon ta kura masa idanu a lokacin data fada kogon tunani, ba komai take tunawa ba face al amuran da suka faru a baya tsakaninta da mahaifinsa marigayi tun daga lokacin data sami juna biyu kawo izuwa rabuwarsu, A wannan lokacin bawa Udex na zaune a can gefe guda shima yayi tagumi yana ta tunani bisa yadda za ayi su kubuta daga sharrin sarki zamaru Kuyi Hakuri Babu Page daya daga cikin littafin saboda haka zakuga kamar anyi tsallake ina ji a jikina zamuyi nasara akan wannan azzalumin sarki kuma zamu kubuta daga sharrinsa, ni yanzu abinda nake so dake da bawa udex ku soma tunanin hanyar da zamu bi domin debo tsumin tsafi na sarki zamaru tunda dai kune kuka fi kowa sanin inda yake da kuma yadda za a iya debo shi sa adda lasmin ta zo nan a zancentsa sai shamilat da bawa udex suka dubi junansu suka yi shiru kawai sai shamilat ta dubi bawa udex tace zomuyi tattaki zuwa kofar gidan nan ba tare da wata gardama ba bawa udex ya mike ya nufi kofar fita daga cikin dakin har shamilat ta bisu sun fita daga cikin dakin sai ta waigo ta kalli lasmin tace kada ki fice kibar dana shi kadai saboda a koda yaushe zai iya farkawa ya bukaci wani abun , dajin haka sai lasmin tayi dan guntun murmushi tace, zan kula dashi kamar yadda zan kula da kaina bisa amana shamilat ta mayarwa Da lasmin murmushi kamar yadda tayi mata fitarta keda wuya sai lasmin ta zauna a wajen da shamilat ta zauna kuma ta kurawa yarima idanu kawai tana murmushi Al amin Ahmed Misau, AA Misau Ke magana, kamar wanda yayi mafarki na ban tsoro haka yarima ya farka daga barci a firgice yana mai mikewa zaune koda yayi arba da lasmin zaune a gabansa ya dubi gabas da yamma kudu da arewa dakin yaga su biyu ne rakm ya kalleta cikin mamaki yace wai shin menene ya faru gare mu ina sauran abokan tafiyarmu lasmin ta kalli yarima cikin alamun damuwa tace kada ka damu duka zan baka amsar wadannan tambayoyin amma yanzu ya ya kake jin jikinka kuma me kake da bukatar kaci ko kasha? Yarima ya saukar da ajiyar zuciya yace mata ina jin kishir ruwa dajin haka sai lasmin ta tafi zuwa ga wani teburi dake gefe daya jikin bango ta daga wani tambulan na zinare ta tsiyaya ruwan ciki a cikin kofi ta dawo sai ta bashi ruwan da hannunta ya shanye kuma ya bukaci kari ta sake bashi da hannunta sannan ya gamsu, lasmin ta koma ta zauna suka sake fuskantar juna tsawon yan dakiku dayansu baice komaiba kuma ita ta kura masa idanu ko kiftawa bata yi shi kuma sai yaji kunyarta ta kama shi don haka sai ya rinka sunkuyar da kansa yana kauda kai ga barin kallonta daga can sai ya bude baki ba tare da ya dago kai ya dubeta ba yace me yasa kika sallama rayuwarki don ceto tawa ? Koda jin wannan tambayar sai farin ciki ya turnuketa tace masa, idan kana son jin amsar wannan tambayar sai dai ka dago kanka ka kura min idanu cikin mamaki yarima ya dago kansa yabi umarninta tace masa So shine sanadin sallama rayuwata domin ceto taka a rayuwata ban taba tunanin haka zata faru ba a kaina ba domin kaine da na miji na farko wanda naji na kamu da tsananin sonsa a gani na farko babu wata shaida da zata tabbatar da tsananin kaunata a gareka sama da sallama rayuwata domin taka, tabbas idan na boye maka soyayyata lafiyata da rayuwata zasu iya salwanta saka makon tsananin begenka da nake fama dashi dare da rana, babban dalilin daya saka na bayyana maka soyayya ta a fili haka karara ba tare da shakkar komai ba shine naga yar uwaraka gimbiya musaira ta kamu da sonka matuka dolene na rigata furtawa domin na rigata mallakarka komai kankantarsa ka fada min iyakacin gaskiyarka shin kaji kaunata a cikin zuciyarka ko kuma babu wani abu mai kama da haka ? Lokacin da lasmin tazo nan a cikin zancenta sai yarima ya gyada kai cikin murmushi daga can kuma sai ya turbune fuska kamar zai fashe da kuka yace tun a ranar farko da nayi arba dake naji zuciyata ta buga da karfin gaske, hakane ya tabbatar mini da cewar na kamu da soyayya amman sai na danne zuciyata saboda ban yarda naso abinda zai wahalar da niba ko kuma naso abinda bani da tabbacin samunsa, tun da farko na fahimci ke mai arziki ce kuma yar sarauta mai ji da kanta don haka sai na yanke shawarar na tsare mutuncina don tserewa wulakanci tabbas yanzu da kike baiyanamin sirrin zuciyarki sai naji nafi kowa farin ciki a cikin wannan duniyar koda yarima yazo nan a zancensa sai hawaye ya subutowa lasmin don haka bata san sadda ta fada kan kirjin yarima suka rungume juna ba, hm A A Misau, a can kofar wannan babban gida kuwa koda fitowar bawa udex tare da shamilat sai wannan katon goggon birin yasha gabansu ya hana su fita waje al amarin da ya dan razanar dasu kenan suka dan ja baya suka tsaya ana kallon kallo tsakaninsu da birin, bawa udex yayi dan tunani sannan ya dubi shamilat yace...KISAN GILLA Littafi Na Biyar (5) Part B. . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... BAWA UDEX YA YI DAN TUNANI SANNAN YA DUBI SHAMILAT YACE, Ranki ya dade ai mantawa nayi daga cikin dokokin da amzad ya bar mana yace babu fita daga cikin gidan, yanzu abinda zaifi mana mu koma da baya mu samu wani waje can mu zauna mu tattauna, koda jin haka sai shamilat tayi murmushi tace hakika kayi gaskiya haka za ayi nan suka juya suka koma wani bangare na gidan suka zauna, AL AMARIN SARKIN YAKI AMZAD KUWA, tare da musaira saida suka shafe sa a shida cur suna tafiya a cikin daji tare da dakarunsu da kuma hadimansu sannan suka riski wadannan makiyayan wadanda adadinsu sunkai dubu sittin da doriya, a lokacin wannan makiyayan sun yada zango a gefen wata korama sun kafa tantuna dabbobinsu suna shan ruwa koda suka hango dawakan dakarun amzad daga can nesa sai suka kama shirin ta kwana saboda a irin wannan lokaci ne yan fashi suke kawo musu harin bazata nan take shugaban makiyayan ya tashi manzo daga cikin jama arsa ya hau doki ya tunkari tawagar su amzad koda karasawar manzo ya karewa dakarun kallo yayi arba da keken dokin wanda su amzad suke ciki sai ya risina yace mace ya shugabana ni manzo ne daga ayarin makiyaya dake can gaba an aiko ni ne domin naga ku din su waye? Koda jin haka sai amzad ya bushe da dariya yace masa ka koma ka fadawa shugaban ku cewar nine sarki Dilwal na birnin Hadsham kuma hanyace ta ratso dani ta cikin wannan dajin amma bani da wata manufa ta cutar da wani koda jin haka sai murna ta kama manzon ya yi godiya kuma yayi sauri ya kama dokinsa ya haye ya juya da sauri ya koma wajen jama ar tasu ya isar da sakon, hankalin makiyaya ya kwanta suka karbisu amzad cikin farin ciki har suka kawo musu madarar shanu suka sa aka ya da zango a wajan ana hira, ana cikin hirar sai amzad ya lura da wata cuta wacce ta haddasa mutuwar kimanin shanu biyar da rakuma uku nan take cikin alamun damuwa sarkin yaki amzad ya kalli shugaban makiyayan yace A A Misau Sunana yaushe dabbobinku suka soma wannan cutar yace mac, kimanin sati guda kenan tunda muka shigo farkon wannan dajin suka kamu da wannan annobar kuma munyi iya bakin kokarinmu dan maganin wannan cutar abin ya gagara koda jin haka sai amzad ya mike yaje ya dudduba dabbobin da suka kamu da wannan cutar yayi nazarin cutar sosai kawai sai yayi guntun murmushi yace kunyi sa a da zuwana nan nasan irin wannan cutar kuma nasan makarinta, amman badan haka ba to gaba daya dabbobinku sai sun halaka saboda cutar ci gaba take da kara yaduwa kuma kwana uku kacal take yi a jikin dabba ta halakashi, nan take amzad ya fadi wasu itatuwa uku da wasu saiwowi guda hudu yace a shiga daji aje a samosu ai kuwa sai makiyaya suka tashi wasu masana abin su uku suka nausa daji kafin sa a guda sun dawo dauke da abinda aka tura su amzad ya saka aka hada wuta karkashin murhun duwatsu aka dora tukunya sannan aka wanke wannan itatuwan da saiwoyi aka zuba a cikin tukunyar gami da ruwa Al amin Ahmed Misau ke Magana Bayan Magani ya dahu kuma ya huce sai aka zo aka zubawa dabbobin maganin, ko dakika talatin ba a yi ba sai gashi dabbobin dake kwance magashiya sun mike sun warke sumu, ba wai makiyayan ba hatta gimbiya musaira sai data kamu da tsananin mamaki nan take shugaban makiyayan da jama a suka yi ta zubewa kasa gaban amzad suka yi godiya cikin matukar farinciki kamar ba zasu dainaba wannan ce tasa nan take zumunci mai karfi ya kullu tsakanin su amzad da ayarin makiyayan tamkar daman can sun dade a tare a wannan wuri dai ayari biyu suka kwana sai washe gari aka dunguma gaba daya aka ci gaba da tafiya, da yake amzad yasan su sarki zamaru suna gabansu sai ya saka dakarunsa suka kara kaimi wajen tafiya ai kuwa suka zaburi dawakansu da gudu kai kace so ake a cemma wata dabbar da aka fito farauta, koda ganin haka sai suma ayarin makiyaya suka sakarwa dawakan su linzami suka mayar da abin tamkar gudun tsere ake yi, nan fa karar sawun dawakai ta cika dajin gaba daya hakanne ya firgita tsuntsaye da sauran kananan dabbobi suka kama guje guje da sauya sheka sarki zamaru tare da boka hizainu suna cikin tafiya sai suka hangi tsuntsaye nata sowa daga inda suke sannu a hankali kuma sai suka soma jiyo sautin sawayen dawakai kawai sai boka hizainu yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak cike da damuwa da kuma mamaki sai sarki zamaru yace masa wai shin menene amfanin tsayuwarmu anan alhalin kasan akwai gagarumin aiki a gabanmu na gano inda makiyanmu suke boka hizainu ya sauko ya debi kasar wajen ya shinshina yace masa yana da kyau mu tsaya musan rundunar dake zuwa don kada mubar baya da kura babu mamaki wani tuggu ne makiyanmu suka shirya mana bamu saniba sarki zamaru yaja tsaki sannan ya sauko daga dokinsa yace amma ai kace makiyan mu suna gabanmu taya kuma zasu bullo ta bayanmu ? Boka hizainu ya gyada kai yace ai kofofin sharrin makiya yawa garesu babu ta inda ba zai iya bullo maka ba dan haka yana da kyau muyi taka tsantsan bisa ga duk wani bakon al amari da zai bijiro mana kada ka manta gumurzun Da mukayi da makiyan mu mune muke da nasara tunda har ka samu nasarar yankar jikin yarima da lasmin, babu yadda za ayi su tsira daga dafin jikin takobinka dole su zama gawa nan da cikar kwanaki bakwai koda jin haka sai ya bushe da dariyar farin ciki yace masa, hakane nan dai boka hizainu da sarki zamaru suka tsaya rike da dawakan su suna jiran zuwan abinda yake bayansu , dakika dari bata cika ba kuwa sai ga ayarin makiyaya da na su sarkin yaki amzad sun iso, tun daga nesa da boka hizainu ya hango su sai yayi sauri ya dauko madubin tsafinsa sai yaga madubin tsafin yayi duhu yaki ya nuna masa komai, koda yaga haka sai ya kalli sarki zamaru cikin alamun damuwa yace masa ban yadda da wadan nan mutanen ba saboda suna da karfin sihirin tsafi, kodai sun kasance gawurtattun yan fashi masu badda kama, ko kuma sun kasance hadiman makiyanmu, ya zama dole muyi taka tsantsan dasu babu maganar mu saki jikinmu dasu, idan kuma sunzo mana da wargi kawai mu yake su mu sharesu daga doron kasa' kafin sarki zamaru ya buda baki yayi magana sai suka hango ayarin biyu sun tsaya cak a can baya kadan kuma sai suka tazo manzo ya taho gasu sarki zamaru yace musu Al amin Ahmed Misau Sunana yaku wadannan matafiya ma abota daraja da daukaka kuyi sani cewar waccan tawagar da kuke gani guda biyu dana fito daga cikinsu ayari ne na makiyaya dana sarki Dilwal na birnin Hadsham dake can kasar hindu, kuma hanya ce ta ratso dasu ta cikin dajin nan muna fatan ba zaku zama masu cutarwa a garesu ba koda jin wannan batu sai boka hizainu da sarki zamaru suka kalli juna suka kyalkyale da dariya a lokaci guda ya dubi manzon yace masa ka koma ka fadawa sarkin ka cewar nine sarki zamaru na birnin madinatul haswar tare da boka hizainu , mun fito ran gadi ne dan haka muna yi masa barka da zuwa cikin yankin kasarmu dajin haka sai manzon ya juya yaje ya isar da sako cikin farin ciki su Amzad suka iso wajen su sarki zamaru ai kuwa ana haduwa sai boka hizainu yaji zuciyarsa ta buga da karfi a lokacin daya hada ido da amzad wanda a halin yanzu kamaninsa irin na mutanen hindu ne, boka hizainu bai nuna wata

Chapter 7 of 8