Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 8
talatin alhalin na san cewa baka kaunata ka tsaneni kamar yadda ka tsani mutuwarka saboda karagar mulki ina son ka tura su izuwa can kauyen limras su karasa sauran rayuwarsu a can a matsayin talakawan gari kawai koda ba zaka taimaka musu da komai ba na san wacece matata shamilat macece mai zuciyar maza ko babu aure zata iya rike kanta kuma tare da abinda ta haifa Guyson Sunana Koda sarki hisham yazo nan a zancensa sai hawaye ya sake zubo masa a lokacin da ya kurawa yarima zamaru idanu nan take yarima zamaru yaji ya kamu da tsananin kunyar sarki hisham gami da matukar tausayinsa har shima hawaye ya sake zubo masa kawai sai yarima zamaru ya mike tsaye ya juyawa sarki hisham baya yace nayi alkawar idan har matarka da abinda ta haifa sun shigo cikin garinan a raye lallai zan zamo mai rike su da amana kamar yadda ka rikeni har izuwa sa adda mutuwa zata rabani dasu koda gama fadin hakan sai yarima zamaru ya fice daga cikin turakar yana kuka da fitowarsa yana kuka yayi arba da sarkin yaki amzadu a tsaye shi kadai a kofar dakin nan fa sukayi wani irin kallo kallo na rashin yarda kawai sai yarima zamaru ya yiwa amzadu dan guntun murmushi yyi tafiyarsa shi kuma sai ya bude kofar turakar da sauri a dimauce ya shiga ciki da shigarsa yayi arba da sarki a kwance kamar yadda ya fita ya barshi dazu cikin hanzari sarkin yaki amzadu yaje ya sake zama daf da sarki ya dubeshi a firgice yace ya shugabana me ya faru tsakaninka da dan uwanka na ga shima ya fita yana kuka koda jin wannan tambaya sai sarki hisham yayi dan guntum murmushi cikin matukar karfin hali sannan yace Alhini ne na rabuwa da juna ya sakaga duk muna kuka domin mutuwa zata shammace mu a lokacin da bamu taba zato ba tafi na sallame ka wasiyata ta karshe a gareka ita ce ka tuna da duk irin abubuwan alherin da nayi maka a rayuwa a duk sa adda wata masifa ta taso kada ka kasance mai yin butulci a bayana sa adda sarkin yaki amzad yaji wannan batu daga bakin sarki sai ya kamu da tsananin mamaki kuma ya kasa fahimtar abinda yake nufi har ya budi baki da nufin ya sake tambayarsa sai ya kasa nan dai ya juya ya fice daga cikin turakar cikin tsananin damuwa da tashin hankali wanda bai taba tsintar kansa ba . Daga wannan rana sarki hisham ya ci gaba da ciwo wanda ba sauki kuma babu alamar za a sami saukin har saida ta kai cewa ko motsi da baki baya iya yi abinci ma da ruwa idan aka dura masa baya shiga cikinsa a ranar kwana na bakwai ne ciwon ya tsananta ainun hankalin kowa ya dugunzuma a tsawon kwanaki bakwan da sarki hisham ke kwance cikin jinya yarima zamaru bai sake zuwa ya duba shiba amma sarkin yaki Amzad kuwa dare da rana yana tare dashi a ranar kwana na bakwan da magariba rai yayi halinsa nan fa labari ya bazu a ko ina cikin kasar mutane suka kama koke koke sai a wannan lokacinne aka ga yarima zamaru ya shigo cikin fadar a lokacin da aka fara shirye shiryen binne sarki ana ganin yarima zamaru hankalin kowa ya tashi domin an san cewa dolene yanzu komai ya sauya a birnin duk irin adalcin da ake yiwa talakawa an daina kuma za a matsa musu a kan biyan haraji mai yawa za a rinka zaluntarsu babu sauran masu jin dadi da kwanciyar hankali face sarakai da attajirai wadanda zasuyi biyayya ga sabon sarki Yarima zamaru nine dai Al amin Ahmed misau Guyson nake Bayan an gama jana izar sarki hisham an binne shi a cikin dakin da aka binne sarakuna arba in da uku na kasar sai yarima zamaru ya tara gaba dayan yan majalisar kasa a dakin taro ya tabbatarmusu da cewa gobene za ayi bikin nadin sarautarsa sannan kuma ya umarci sarkin yaki da ya tabbatar da tsaro a ko ina a cikin birni da kewaye kuma ya sanar da dakarun dake tsaron kofofin gari cewa ba shiga kuma ba fita daga yanzu har izuwa gobe sa adda za a kammala bikin nadin sarautar tasa koda jin wannan umarni sai kowa ya cika da tsananin mamaki amma sai gaba daya yan majalisar sukayi shiru suna masu sunkuyar da kansu kasa saboda tsoron yarima zamaru aka rasa wanda zaice kala sai sarkin yaki amzadu ne ya dubeshi yace yakai sarkin gobe kayi sani cewa wannan hukunci da ka yanke baiyi dai dai ba domin tsarin mulki bai yarda da hakan ba saboda bai dace ba ka hana mutane zuwa cikin gari nan ba koda ka hanasu fita a wannan lokaci da ake ciki na babban rashin da akayi na dan uwanka ka sani cewa mutane da yawa zasu zo ne domin su ziyarci kabarin sarki su nemi tabarrakinsa kuma suyi masa addu a wasu kuma zasu kawo ziyara ne izuwa kallon bikin nadin sarautarka, sarakuna da yawa daga makwabtan kasashe ma zasu zo wannan gagarumin biki kafin sarkin yaki amzad ya gama rufe bakinsa tuni yarima zamaru ya tari numfashinsa yana mai daaka masa tsawa yace wanene kai harda zaka gaya mini abinda zanyi ka sani cewa in banda kana da matukar muhimmanci da amfani da yanzu take zan sauke ka daga kan mukaminka na sallameku kowa ya kama gabansa nan take kowa ya kama gabansa jikinsa a sanyaye ya fice daga cikin dakin taron aka bar yarima zamaru a zaune shi kadai Al amin Guyson, lokacin da sarkin yaki amzad ya isa kofar gidansa sai ya hango kofar gidan wayam babu dakarun da suke yi masa gadi kuma kofar gidan a bude take wanwar al amarin da yayi matukar razana shi kenan yayi wuf ya sauko daga kan dokinsa yana mai zare takobinsa kawai sai ya ruga da gudu izuwa cikin gidan yana mai kiran sunan matarsa da danta himar wanda ya kasance yaro dan shekara hudu amma shiru baiji sun amsa ba kuma baiji duriyarsu ba ,,, Al amin Guyson Kenan Anan Zan dakata amma Kafinnan Nidinne dai AL AMIN AHMED MISAU guyson inkiya Admin Na zauran Labarai KISAN GILLA Littafi Na Daya (1) Part C. . . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... Yana isa falo yayi turus saboda tsananin kaduwa da mamaki bisa abinda yayi arba dashi ba wani abu ya gani ba face yarima zamaru zaune akan kujera cikin shigar yaki ya harde kafafu daya kan daya yana kallonsa cikin murmushi abuna farko da ya daure masa kai shine yaya akayi zamaru ya riga shi zuwa nan alhalin a can gidan sarauta ya barshi kuma yaushe ma ya canja kayansa har yazo nan din kawai sai amzad ya baiwa kansa amsa yace tabbas wannan al amari ne na tsafi cikin alamun fushi sarkin yaki ya dubi yarima zamaru yace ina iyalina tuni jikina ya bani cewar wani abu makamancin wannan sai ya faru kuma yanzune na tabbatar da cewar kana da hannu a kan ciwon da sarki ya samu wanda ya zama sanadiyar ajalinsa lokacin da yarima zamaru yaji wannan batu sai ya bushe da mahaukaciyar dariya lokaci guda kuma ya turbune fuska yace ina son mutum mai kaifin kwakwalw da hasashe irinka tabbas duk abinda ka fada haka yake gaskiya ne nine na kashe sarki domin na sami wannan karagar mulki wacce ta gagareni tsawon shekaru ban zo nan domin muyi doguwar magana nazo ne domin na sanar dakai cewar iyalinka suna hannunmu kuma mun boye su a inda babu wanda ya isa ya gansu ko ya dauko su face mu da kanmu ina son yanzu take ka debi dakaru dubu dari shida a cikin shigar badda kamanni ku nufi jeji na bayan gari ku tari gimbia shaliat tare da dakarun mahaifinta wadanda sukayi mata rakiya izuwa nan birnin ina son duk yadda za ayi ka kashe su gaba dayansu ban son mutum daya ya tsira da jaririn da ta haifa ku tabbatar da cewa kun kashe shi idan kuka yi wannan aiki dai dai zan dawo maka da iyalinka gobe da safe idan kuma ka ki bin umarnina gawar iyalanka zamu kawo maka idan kunne yaji gamgar jiki ya tsira kuma shawara ta rage ga mai shiga rijiya Koda gama fadin hakan sai yarima zamaru yayi girgiza ya bace bata daga cikin dakin yana mai kyalkyala dariya tamkar bai taba wanzuwa ba a ajan Al amin Guyson nake nan fa sarkin yaki amzad ya dimauce kuma ya fusata ainun bai san sa adda ya kurma uban ihu ba kuma ya fashe da matsanancin kuka saboda tsananin bakin ciki da takaici daga can sai ya juyada sauri a guje ya koma kofar gida ya kama dokinsa ya hau ya zabureshi da gudun tsiya A can daji kuwa Gimbia shamilat na zaune a cikin keken doki rungume da jaririnta dakaru sun kewayeta gaba da baya dama da hagu ana tafiya saboda kwarjinin wadannan dakaru da irin kayan yakin da suke dauke dasu babu abinda zai gansu bai yi shakkarsu ba , da yake duhu yayi gaba dayan dakarun sun kunna fitilun itace don haka hanya sai tayi haske sai sauri ake tayi saboda an san cewa saura baifi tafiyar rabin sa a ba a iso cikin birnin madinatul hashwar a wannan lokacinne shamilat na cikin tsananin farin ciki sai yawan kallon jaririnta take yi tana murmushi saboda tunanin cewa a yau ne sarki hisham zai ga dan cikinsa da idonsa abinda ya shafe shekara da shekaru yana burin gani bai gani ba saboda zakuwar da tayi taga an isa cikin garin har umarni take bayarwa a kan a karawa dawakai kaimi nan fa aka ci gaba da gudu kai kace hari za a kai kaico rashin sani yafi dare duhu ashe wadannan zuga ba su san cewa mahallaka suke kai kansu ba lokacin da tawagar gimbiya shamilat suka iso dai dai wani fili mai fadi wanda tsakaninsa da karshen dajin bai wuce zira i arba in ba sai kawai sukaji ana yi musu ruwan kibiyoyi ta gabas da yamma kudu da arewa wayyo Ajali idan yayi kira sai an amsa babu makawa Nan fa dakarun da dawakai suka rinka ihu da haniniya suna zubewa kasa matattu kafin su ankara an kashe kaso daya a cikin kaso uku ita kanta gimbiya shamilat taga matukar tashin hankali domin ta gefen idanunta da kunnuwanta kibiyoyi suka rinka giftawa da kyar aka sami wasu zakwakuran mayaka suka rinka kade kibiyoyin da ake harbo mata da takubbansu A sannan ne kuma dakarun suka yi wata dabara wadanda keda garkuwoyi sai suka yi kawanya a tsakiya suka kare sama da kasansu aka sanya gimbiya shamilat da sauran dakarun a tsakiyar da irar duk da haka sai aka ci gaba da harbo kibiyoyin har zuwa tsawon lokaci a wannan lokaci jaririn shamilat na ta faman kuka itama gimbiya tana kukan sai da aka saina harbo kibiyoyin sannan shugaban dakarun ya dubi gimbiya shamilat yace ranki ya dade yanzu me ye abinyi ba muga wadanda suka kawo mna wannan hari ba har yanzu domin sun boye ne a cikin duhuwar bishiyoyi shin zamu ci gaba da tunkarar birnin madinatul hashwar ne wanda tazararmu da shi a yanzu bata wuce zira i arba in ba ko zamuyi kokarin komawa da baya ne domin mu tserar da rayuwarki data wannan yaron naki sa adda shugaban dakarun yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa gimbiya a lokacin da zuciyarta ta buga da karfi kuma tsoro ya shigeta kawai sai ta dubi shugaban dakarun ta ce sarki Hisham ya fadi '' cikin kaduwa shugaban dakarun ya cubeta yace ranki ya dade ya akayi kika sani? Shamilat ta fara zubar da hawaye ta ce inda mijina yana raye babu yadda za ayi a taremu a kan iyakarsa domin a hallakamu abu ne mai hadarin gaske muci gaba da tunkarar cikin birninnan yanzu kawai muyi Kokarin komawa da baya in munyi sa a mu tsira da ranmu kafin gimbiya ta gama rufe bakinta sai kawai sukaji sukuwar dawakai an durfafosu kafinsuyi wani yunkuri dakarun masu yawan gaske ninkinsu uku sunyi musu kawanay gimbiya shamilat ta fito daaga cikin keken dokinta a fusace rike da jaririnta domin taga ko suwaye ne wadannan dakaru da suka kawo musu hari kawai sai taga ashe dakarun sunyi shiga ne irin ta bakaken kaya ba shigar kayan yakin dakarun birnin madinatul hashwar ba kuma duk sun rufe fuskokinsu da bakin kyalle idanunsu kadai ake gani a dai dai wannan lokaci ne shugabam dakarun gimbiya ya rugo gareta ya dubeta cikin alamun tsananin tsoro da damuwa yace haba ya shugabata yaya zaki fito fili haka gaban wadannan makiya alhalin muna kare rayuwarki da ta jaririnki shamilat tayi ajiyar zuciya tace ai zancen kare ni da jaririna ya kare ka dubi wadannan dakaru ka gani ai sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma ba zamu iya guje musu ba duk mutuwa zamuyi ni kawai yanzu ina son na san wanda ya turo a kasheni kafin na mutu Al amin Guyson Sunana don bana son na mutu cikin wasu wasi koda gama fadin hakan sai gimbiya shamilta ta dubi wadannan dakaru masu bakaken tufafi ta daka musu tsawa tace ku su waye kuma waye ya turoku ku kasheni mtar sarkin birnin madinatul hashwas dajin wannan tambaya sai bakaken dakarun suka dare shugabansu ya ratso ta tsakiyarsu ya matso kusa da ita ya tsaya duk da cewar fuskarsa a rufe take idanunsa kadai ake gani saida gimbiya shamilat ta shaida ko wanene shi nan take hawaye ya zubo daga cikin idanunta ta dubeshi tace yakai Amzad yanzu dakai za a hada baki aci amanar mijina Yanzu ashe dama zaka iya yiwa sarki butulci aashe zaka iya mancewa da duk irin halaccin da yayi maka a rayuwa sa adda shamilat tazo nan a zancenta sai sarkin yaki Amzad ya kwaye fuskarsa sai ga hawaye na zuba masa a lokacin da suka kurawa juna idanu shi da ita tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba sannan Amzad yace ki gafarceni ni ya shugabata idan ban bi umarni ba nima zan rasa matata da dana Koda jin haka sai shamilat ta fashe da kuka tace haka ne rai baifi raiba amma kafin ku kashe mu ina son ku fada mun iyakar gaskiyar menene ya faru ga mijina dajin wannan tambaya sai hawaye ya sake zubowa sarkin yaki amzad ya ce mijinki ya mutu koda jin haka sai jiri ya debi shamilat ta yanke jiki zata fadi kasa cikin zafin nama amzad ya daka tsalle ya dira a gabanta ya tallafeta tare da jaririnta yana mai baiwa dakarunsa umarnin su hallaka dakarun gimbia kaico Ajali ba a sa ma rana nan da nan dakarun amzad suka kama ragargazar dakarun shamilat wuri ya hargitse banda ihun mazaje babu abinda mutum ke ji duk da cewar sarkin yawa yafi sarkin karfi sai da aka jima ana gumurzu a karshe dai ragas aka yi aka karar da gaba dayan daakarun kowanne bangare ya zamana cewa babu daya da ya rage a raye face sarkin yaki Amzad a dai dai wannan lokaci ne gimbia ta farfado daga dogon suman da tayi idanunta suka bude tana mai gani dishi dishi idanunta na washewa tayi arba da sarkin yaki amzad a zaune daf da ita rungume da jaririnta gaba dayan dakarun dake wajan na kwance a kasa sun zama gawa shamilat ta mike tsaye zumbur ta rugo iduwa wajan amzad ta miko hannayanta da nufin ta karbe jaririnta amma sai ya tokare da kotar takobinsa a kirjinta yace ya shugabata kiyi sani cewa yarima zamaru ya umarceni da na kashe ku keda jaririnki in ba haka ba kuwa sai ya kashe matata da dana ba zan iya kashe ku ba domin idan nayi haka naci amana Koda yazo nan a zancensa sai ya durkusa bisa gwiyoyinsa agaban shamilat a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla yace ina rokonki daki bar garin nan kuma karki koma birnin darul hashbush ki sanar da mahaifinki abinda ya faru domin kina gaya masa zaice zai yaki sarki zamaru kuma kin sani cewa mayakan mu sun ninka nasa sau goma a yawa da karfin makamai cikin tsananin bakin ciki shamilat ta fashe da kuka kamar ba zata daina ba daga can saita dago kai idanunta sunyi sharkaf da hawaye tace shi kenan ka bani dana nayi alkawarin zan tafi izuwa wata nahiyar daban na reni dana a can har abada ba zan dawo nan ba kuma ba zan taba gayawa dana matsayinsa ba koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa sarkin yaki amzad ya dubeta yace ba zan iya baki yarima ki tafi dashi ba cikin razana shamilat tace yanzu kana nufin zaka rabani da dana kenan wanda shi kadai ne abinda ya rage mini a duniya amzad yace kawar kuwa domin barinsa awajanki ba karamin hadari bane nayi miki akkawari zan reni wannan yaro a cikin birnin madinatul hashwar kusa da karagar mulkinsa ba tare da ya san ko shi wanene ba kuma komai dare dadewa in dai kina raye yana raye nima ina raye saina sadaku zan tsare lafiyarsa da ransa kamar yadda na tsare na mahaifinsa wannan shine kadai gatan da zamu iya yiwa kanmu da wannan jariri naki idan har muna son mu tsira da rayukanmu sa adda sarkin yaki amzad yazo nan a zancensa sai shamilat ta sake fashewa da kuka daga can sai ta matso daf da amzad ta shafa kan jaririn ta sumbaci goshinsa sannan kuma ta ciro wata laya dake wuyanta ta Daurata a wuyan jaririn ta dubi amzad tace ina da laya irin wannan sak don haka ka gayawa dana cewar duk ranar da yaga mai irin wannan laya ba wata ba ce face mahaifiyarsa koda gama fadin hakan sai ta karbi jaririnta ta rungumeshi a kirjinta ta sake fashewa da kuka al amarin da ya karyar da zuciyar sarkin yaki kenan ya ji ya kamu da tausayinta fiye da ko yaushe sai da ta jima a kankame da jaririn sannan sarkin yaki ya karbeshi ta tafi izuwa inda keken dokinta yake tana waigen jaririn nata tana zubar da hawaye Wow nIma Al amin Guyson na tayata haka dai taje ta zauna a kan keken dokin ta sakarwa dawakan linzami suka zabura da gudu suka nausa da ita cikin daji suka nufi wani bangare daban wanda bai shafi nahiyar ba gaba daya a sannan ne shima sarkin yaki Amzad ya tafi da jaririn izuwa inda dokinsa yake ya kama ya hau ya nufi hanyar da zata kai shi cikin madinatul hashwar a lokacin da yake bacewa a cikin duhun daren tun kafin sarkin yaki ya iso kofar shiga gari ya boye jaririn a bayansa tamkar baya dauke da komai kawai ya wuce gaba masu gadin kofar garin ba tare da jaririn yayi kuka ba ai kuwa yana isowa bakin kofar sai masu gadin suka tare shi saboda basu gane shiba sakamakon yana sanye ne da bakaken kaya kuma basu ga sa adda ya fice daga cikin garin ba tare da dubun nan daakarunsa saboda ta wata barauniyar hanya suka fice masu gadin na tare shi sai yayi sauri ya bude fuskarsa don kada su bata masa lokaci koda suka dallare fuskarsa da madubi sukaga shine sai suka yi sauri suka bude masa kofa ya shigo suna masu binsa da kallo cikin alamun tsananin mamaki domin su dai basu ga lokacin da ya fita daga cikin garin ba kuma tunda suka ganshi a cikin shiga ta bakaken kaya lallai sun san cewa wani aiki ne na sirri yaje ya gabatar amzad na shiga cikin gari bai zame ko ina ba sai gindin wata karuwa wacce ake kira kimaratu a wannan lokaci dare ya fara nisawa kuma sawu ya dauke ba a jin sautin komai face haushin karnuka amzad ya kama buga kofar gidan da karfi a fusace kimaratu tazo ta bude kofar tace wanene nan yake neman fasa mini kofar gida ka kama gabanka ina da abokin kwana a ciki koda jin haka sai amzad ya daka mata tsawa yace bude kofar na shigo nine sarkin Yaki Amzad jikin kimaratu na karkarwa tayi sauri ta bude kofar nan take amzad ya mika mata jaririn sannan ya danka mata jakar kudi cike da dinare yace wannan kudine dinare dubu dari uku ki rike su ki reni wannan jariri har izuwa lokacin da na bukaceshi idan wani abu ya tafa lafiyarsa a bakacin ranki . SHIN SARKI ZAMARU ZAI CIKA ALKAWARIN DAKE TSAKANINSA DA BOKA HIZAINU.?? . YAUSHENE SHAMILAT ZATA SAKE GANIN DANTA??? . ME ZAI FARU IDAN DAN SHAMILAT YA GIRMA ??? . MU HADU A LITTAFI NA BIYU DON JIN CI GABAN WANNAN LABARI DAGA MARUBUCIN LITTAFIN ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI KANO WANDA NI AL AMIN AHMED MISAU INKIYA GUYSON NAYI TYPINGDINSHI NAKE CEWA SAI MUN HADU A NA BIYUN KISAN GILLA 2 Littafi na biyu Na Abdulaziz sani madakin gini Ebook creator:- Shuraih Usman 99% Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini KISAN GILLA Littafi Na Biyu (2) Part A. . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... Filine mai fadi wanda aka kewayeshi daragar karfe musamman sarki zamaru yasa aka shirya wannan wuri domin baiwa kansa horon yaki tsawon shekaru ashirin da daya kullum sai sarki zamaru ya jarraba jarumtakarsa akan dakarunsa acikin wannan fili kuma yana yin yakine da mutum arba in shi kadai yake ragargazarsu a cikin kankanin lokaci saboda jarumtakarsa da iya yakinsa, mutum daya daga cikin arba in din baya tsira da lafiyarsa wani lokacin ma idan tsautsayi ya ratsa wasunsu na rasa rayuwarsu banda sarkin yaki Amzad babu wani sadaukin daga cikin mayakan kasar wanda sarki zamaru bai kaishi kasa ba shima din don basu taba kafsa wa bane yauma kamar kullum sarki zamaru ya tunkaro wannan filin jarumta a cikin gagarumar shigar yaki yana rike da wata zabgegiyar takobi gami da wata garkuwa irin ta gidan sarauta mai tambarin karagar mulkin birnin madinatul hashwar bisa mamaki sai sarki zamaru ya hango filin yakin wayam babu ko badakaren guda cikin tsananin mamaki da fishi sarki zamaru ya buda baki ya kwallawa wani hadimin kira mai suna zabbaru nan da nan saiga zabbaru ya rugo har yana sassarfa don biyayya da isowarsa gaban sarki zamaru sai ya zube kasa bisa gwiwoyinsa cikin biyayya sarki ya dubesu da kakkauran murya yace menene dalilin da yasa yau sarkin yaki bai turo da dakaru arba in wadanda zan yi yaki dasu ba? Zabbaru ya risina cikin biyayya kansa na sunkuye a kasa yace ya shugabana ai amzad ya zo da dakaru arba in kamar kullum amma sai gimbiya ta sallameshi tace itace zata fuskance ka cikin tsananin kaduwa da mamaki sarki zamaru yace wannan wace irin maganar banzace kake mini haka ? Tayaya gimbiya zatace zata tareni da yaki alhalin bata taba rike takobiba a rayuwarta kafin sarki zamaru ya gama rufe bakinsa sai ya jiyo sukuwar doki a bayansa koda ya waiga sai yayi arba da yarsa gimbiya Musaira bisa wani farin ingarman doki tayo shigar yaki na bakin sulke bata rufe fuskarta ba da hular karfe kuma ta tattare gashin kanta ta daure ya zubo har kasan kwankwasonta duk inda ake neman mace mai kyau da sura gimbiya musaira ta kai ta wuce misali sai abinda ido suka gani kafin sarki zamaru ya ankara tuni musaira ta dako tsalle a sama tana mai barin kan dokin kawai sai ta zare takobinta ta kawo masa wawan sara a wuya saboda karfin saran sai da sarki zamaru ya durkushe kasa a lokacin da yayi wuf ya kare harin da takobinsa musaira na dira a kasa bisa kafafunta sai taci gaba da kaiwa sarki zamaru sara da suka cikin zafin nama juriya da bajinta nan fa suka kacame da azababben yaki tamkar tsofaffin abokan gaba, sai da suka shafe kusan dakika dari da arba in suna bakin gumurzu dayansu bai samu nasarar kowa lakutar jikin daya ba Al amarin da ya matukar fusata sarki zamaru kenan kawai saiya shammaci gimbiya musaira ya sauya salon yaki ya fyalli kafarta tayi katantanwa a sama sannan ya doki kirjinta da kafarsa guda ta fado kasa a matukar galabaice ta mike zaune da kyar ta tofar da yawun jini kawai sai sarki zamaru ya kyalkyale da dariya sannan ya mikawa gimbia musaira hannunsa ta kama ya tashe ta tsaye ya dubeta yace yaushe ne sarkin yaki amzad ya baki horon yaki haka bansani ba a tunanina ko rike takobi baki iya ba menene dalilin da yasa kika bata lokacinki kika koyi yaki haka kuma me yasa kika boye mini koyon yakin naki sa adda gimbiya musaira taji wadannan tambayoyi sai tayi murmushi a lokacin da tasa tafin hannunta ta share dan jinin dake kan lebanta tace yakai abbana na sani cewa zaka iya kare rayuwata da lafiyata a ko da yaushe to amma ranar da babu kaifa waye zai kareni a matsayina na yarka guda daya jal a wannan duniya mai shirin gadon karagar mulkinka wata rana ya kamata ace na zama jaruma kamarka tun ina karama na gane cewa nasha jarumtaka a nonon uwata kuma na gajeta a cikin jininka, don me bazan koyi yaki ba in zama cikakkiyar jaruma ka sani cewa wannan duniya cike take da masoya da makiya ba mamakima a cikin

Chapter 2 of 8