Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 8
a jikinta ta dubi udez tace maza ka cire hannunka daga jikina ko na tsinke maka wuyanka ka sadu da abar da kake tsoro Dajin haka sai udez yayi sauri ya janye hannunsa daga jikin na gimbiya jikinsana karkarwafaruwar hakan keda wuya sai gimbiya ta dako tsallo sama ta dira a tsakiyar dakarun yan fashin ta hausu da sara da suka ya zamana cewa tana taimakawa jarumin sai gashi suna ta ragargazar yan fashin kafin cikar dakiku dari hudu yan fasin sun zama saura su sittin da biyar a tsaye sauran sun zama matattu da nakasassu koda ganin abin dake faruwa sai bakin ciki ya turnuke shugaban yan fashin ya kwarara uban ihu karfin ihun nasane ya sa tsirarun dakarun nasa sukaja da baya suka rugo izuwa bayansa a wannan lokacine gimbiya da jarumin suka hada baya ba tare da sun juyo sun kalli juna ba sai jarumin ya budi baki yace saboda me ka taimakeni kuma wanene kai??maimakn gimbiya ta bashi amsar wadannan tambayoyi sai tayi shiru don kada tayi magana yaji muryar mace a dai dai wannan lokaci ne shugaban yan fashin ya kurawa gimbiya muraisa idanu har izuwa tsawon yan dakiku kawai sai ya tuntsire da dariya yace haba ranki ya dade menene ya shigo dake cikin sabgar talakawa haka kada ki shiga harkarmu ta neman arziki kin sani cewa ko giya na sha ba zanyi yunkurin zuwa sata gidanku ba ki koma gefe daya kiyi kallo wannan fada ba naki bane amma idan kika ki zan iya salwantar da rayuwarki a nan na dauki abinda nazo nema na bar nahiyar gaba daya idan kika mutu a nan sai mahaifinki ya dauki dubun nan rayukan talakawa sa adda shugaban yan fashin yazo nan a zancensa sai kowa ya kamu da tsananin mamaki ita kuwa gimbiya jikinta yayi sanyi ta koma gefe daya ta tsaya hakanne yasa ko ya kura mata idanu a wajan Musamman jarumin da mahaifiyarsa kimaratu domin a sannan ne suke kokarin ganoko wanene wannan bakon jarumi da aka kirashi da matsayin ya mace shugaban yan fashin ya dubi tsirarun dakarun nasa yace kada ku shiga wannan yaki tsakanina da wannan yaron koda kuwa kunga zan hallaka in kuwa kuka shiga to dukkaninku mutuwa zakuyi yana gama fadin hakan sai ya dubi saurayin jarumin yace yanzu zamuyi fadan karshe idan ka kashe ni ka tserar da dukiyar wannan karuwar wacce ba ita ce asalin uwarka ba koda jin haka sai idanun jarumin suka zazzaro ya kurawa kimaratu idanu ita kuwa kimaratu sai tayi sauri ta sunkui da kanta kas a lokacin da hawaye ya subuto mata koda ganin haka sai jarumin yayi kururuwa ya daga takobinsa sama ya rugo izuwa kan shugaban yan fashin yana mai kururuwa burinsa kawai ya gaggauta kashe shugaban yan fashin domin ya tuhumi kimaratu gaskiyar al amarin matsayinsa a gareta koda ganin tasowar jarumin sai shima shugaban yan fashin ya rugo gareshi ai kuwa suna haduwa sai suka kacame da azababben yaki mai tsananin ban tsoro wohoho ai duk sa adda tsohon gwani masanin yaki da tuggu ya hadu da sabon jini mai jarumtaka da juriya dole ne ayi mugun gumurzu mai ban sha awa da ban tsoro saboda kowannensuyana da irin baiwar da Allah yayi masa sai da shugaban yan fashin da jarumin saurayin suka shafe sa a uku rir suna gabza yaki na tashin hankali wadda kowannansu ya galabaita ainun tamkar zasuyi ragas wani irin salon yakin suka rinka yi ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka gami da kai naushi da bugu hannu da kafa duk a lokaci guda, nan da nan suka hadawa juna jini da majina da kyar jarumin saurayin ya sami nasarar yiwa shugaban yan fashin rauni uku shi kuwa sau shida yana yiwa jarumin rauni alhalin ga wasu raunika ukun a jikinsa hakan ne yasa jarumin saurayin ya galabaita ainun a lokacin da jiri ke dibarsa sakamakon jinin dake ta zuba a jikinsa kuma asannan ne idanunsa suka fara gani dishi dishi kawai sai ya yanke jiki ya fadi kasa da ruf da ciki tamkar ya zama gawa koda ganin haka sai farin ciki ya lullube shugaban yan fashin ya bushe da mahaukaciyar dariya ta murna yazo kan jarumin saurayin ya tsaya yana mai raba kafafunsa a kansa sannan ya sunkuyo da nufin ya tallafo kan jarumin yayi masa yankan rago ba zato ba tsammani sai akaga jarumin saurayin ya yunkuro cikin bakin zafin nama na bazato ya gabzawa shugaban yan fashin wawan naushi a fuska saboda karfin naushin sai da yayi sama yaje ya maku da bayansa a jikin bango ya fado kasa magashiyan kafin ya samu damar motsawa tuni jarumin saurayin ya daka tsalle sama daga inda yake ya dira a gadon bayansa da kokon gwiwarsa ta dama kowa dake cikin falon gidan abincin sai da yaji karar karyewar kashin bayan shugaban yan fashin nan take ya baje a kasa matacce Al amin Guyson sunana kenana koda ganin abinda ya faru sai wadannan tsirarun dakarun nasa suka zube kasa suna masu mika wuya nan take dakarun kimaratu suka kamasu suka daddauresu shikuwa wannan saurayin jarumi sai ya sulale kasa sumammc e lokacin da jarumin saurayin ya farfado yana bude idanuwansa sai yaga kimaratu tare da bakon jarumin da ya taimakeshi da kuma bawa udez sai sarkin yaki amzad tsaye a gefe guda a cikin daga daga cikin dakunan gidan abincin yana bisa gado saurayin jarumin ya dubi raunikan jikinsa yaga duk an dinkesu kuma an sa musu magani kawai sai ya dubi kimaratu ya ce wacece uwata ta gaskiya kuma wanene wannan baokn jarumin daya taimakeni?? Maimakon kimaratu ta bashi amsa sai ta fasa kuka a sannan ne sarkin yaki amzad ya dubi saurayin jarumin yace mahaifiyarka itace matar marigayi sarki hisham na wannan birni namu babu wanda yasan inda take a yanzu kimaratu ce ta reneka tun kana jariri kuma nine na kawo ka gareta na baka horon yaki ne domin ka dauki fansar ran mahaifinka akan sarki yanzu wanda ya kasance kanin mahaifinka wannan bakon jarumin dake gabanka wanda ya taimakeka ba kowa bane face gimbiya muraisa ya ga sarkin yanzu kasani tsakaninka da ita babu gaba kada ka kuskura kayi tunanin daukar fansa a kanta...... .. A nan ne LITTAFIN KISAN GILLAH NA BIYU YAZO KARSHE MARUBUCIN YACE MU HADU A LITTAFI NA UKU wanda ni Al amin Ahmed Dan Mutan Misau Dake Bauchi Nayi hidimar rubuto muku shi . Guyson Inkiyata Kenan Dan Garin Kd... Nake cewa mu zama lafiya KISAN GILLA 3 Littafi na uku Na Abdulaziz sani madakin gini Ebook creator:- Shuraih Usman 99% Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini KISAN GILLA Littafi Na Uku (3) Part A. . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... Lokacin da jarumin saurayin yaji wannan jawabi daga bakin sarkin yaki amzad sai hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe a rayuwarsa ya kurawa kimaratu idanu a lokacin da kowa a dakin ke zubar da hawaye ita kuwa gimiya Musaira kuka take yi sosai tamkar ranta zai fita saboda bakin ciki da kuma takaici bisa jin cewa wannan bakon jarumi dan uwanta ne na jini amma aka rabata dashi tsawon shekaru sannan kuma gashi mahaifinta ne ya kashe mahaifinsa ya salwantar da rayuwar sa da ta mahaifiyar sa bayan shafewar yan dakiku kowannan su na zub da hawaye sai saurayin ya dago kai ya dubi kimaratu yace yake ummina kiyi sani cewa ban san kowa ba a wannan doron kasa sama dake nononki nasha na rayu har na kawo iyanzu tabbas uwa uwace amma ke ce uwata ta zahiri ina neman alfarma guda daya a wajanki ina sonki yi mini izini na tafi neman uwata ta jini saboda nafi son na dauki fansar ran mahaifina a gaban idanunta tun ina yaro karami naji kina kirana da sunan yarima ashe kuwa ni yarima ne na gaskiya ban sani ba koda jin wannan batu sai kimaratu ta rungumi yarima suna masu fashewa da kuka a tare cikin kankame juna sannan ta numfasa tace yakai dannan kayi sani cewa ni kaina bansan cewa kai yarima ne ba sai bayan ka girma a ranar da sarkin yaki yazo zai tafi dakai domin ya fara koya maka yaki A wannan ranane ya sanar dani ko kai waye sannan ya umarceni da kada na kuskura na sanar dakai wannan sirri ka gafarceni yakai dana bisa renon dana baka a cikin yanayin rayuwata wanda ya kasance mukaddari ka sani cewa ban taba haihuwa ba a rayuwata kuma bani da wani dan uwa ko masoyi wanda ya fika a doron kasa, na sani cewa lallai akwai rana irin wannan da zata zo wato ranar rabuwarmu don haka nayi maka izini ka tafi neman mahaifiyarka, koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube yarima ya sake kankame kimaratu a kirjinsa yana mai yi mata godiya, daga can kuwa sai ya janye jikin sa daga cikin nata ya tako kafafunsa yazo daf da sarkin yaki Amzad ya dubeshi yace nagode maka bisa tserar da rayuwata data mahaifiyata da kayi, kamar yadda kabani labarin cewar kai kanka yanzu baka san a inda mahaifiyata take ba kuma babu tabbacin tana raye, to kasani ni ina ji a jikina cewar mahaifiyata tana raye don haka ina neman Taimako guda daya a wajanka, ta yaya zan iya shaida mahaifiyata alhalin bantaba ganinta ba itama baata taba ganina ba sa a dda sarkin yaki Amzad yaji wannan batu sai ya shiga tunani daga can sai ya dago da kansa ya dubi wata sarka dake wuyansa yace mahaifiyarkace ta sanyata a wuyanka kana jariri kuma itama tana da irinta sak duk macen da ka gani da irin wannan sarka itace mahaifiyarka koda jin wannan batu sai yarima ya kama sarkar dake wuyansa ya kura mata idanu sannan ya sumbace ta yana mai lumshe idanu, sa adda hawaye ya subuto masa sannan ya dubi kimaratu yace nifa a daren yau zan bar garinnan idan kin amaince, bani da ikon hanaka yin wannan tafiya a duk sa adda kaso fatana kawai ka dawo lafiya. Gama fadin hakan keda wuya sai kuwa Udex ya dubi Gimbiya Musaira cikin alamun firgici yace ya shugabata kizo muyi sauri mu koma gidan sarauta tun kafin mahaifinki ya gano fitarki idan hakan ta faru kashina ya bushe musaira ta dubi udez a fusace tace ya zan ga dan uwana na jini a yanzu kace zaka yi gaggawar rabani dashi caraf sai sarkin yaki Amzad yace ai babu mai rabaki dashi sai dai mutuwa to amma ya zakiyi idan kikaga ya kashe mahaifinki saboda zaluncin sa da rashin tausayinsa akan talakawan kasarnan. A yanzu da naji cewar ya kashe dan uwansa saboda karagar mulki kuma ya tarwatsa iyalinsa sai naji na tsaneshi fiye da komai inba don darajar uwataba da har abada ba zan sake komawa wannan gidan sarautar ba nayi sallama dashi kenan har abada Dajin wannan batu sai sarkin yaki ya dubi gimbiya Musaira cikin alamun damuwa yace ya shugabata ai yanzuma ba zai yiyu ki koma gidan ba domin tuni labari ya riski sarki bisa duk abinda ya faru a nan tsakaninku da wadannan yanfashi kai Udez rayuwarka na cikin hadari haka kuma gimbiya, idan sarki bai cutar dake ba bisa sanin sirrinsa da kikayi yanzu to zai kafa miki takunkumin fita mai tsaurin gaske fiye da duk irin wanda ya sa miki a baya shawara da zan baki itace kibi dan uwanki ma ana ki rakashi neman uwarsa ni kuma zanyi kokarin kare duk wata baraka da zata faso a gano inda kuke bare har a cin maku kuma Udez dolene ka bisu in kuna son ku tsira domin tuni yanzu sarki ya gane cewa kaine ka fitar da gimbiya na iso nan don haka ku tashi mu tafi na saku a kan hanyar sirri wacce babu mai ganinku yayin fita daga garin The Al Amin Ahmed Guyson, A Square nake magana koda jin haka sai kimaratu ta sake rungume yarima suka fashe da kuka na bakin cikin rabuwa nan dai sukayi sallama kimaratu ta kawo musu kudi masu yawa ta bashi sukayi bankwana cikin hanzari sarkin yaki Amzad, Udez Gimbiya Da yarima suka fice daga cikin gidan abincin suka nausa daji da gudu suna masu bin wata barauniyar hanya mai sarkakiya, sai da suka shafe kusan rabin sa a suna gudu sannan Kwatsam suka tsinci kansu a bayan gari nanfa Udez, yarima da gimbiya suka kamu da tsananin mamaki domin duk su ukun babu wanda ya taba sanin wannan barauniyar hanya wacce ta fullo dasu bayan gari. Da isowarsu wannan wuri sai amzad ya tsaya cak suma sai suka tsaya zuba masa idanu Amzad ya dubi yarima cikin nutsuwa yace' to ni daganan zan koma ku nufi yamma kuyi ta tafiya ba tsayawa zaku riski wani karamin kauye a dai dai lokacin da rana ta fadi zaku iya tsayawa a kauyan kuci abinci ku huta amma kada ku kwana saiku sayi dawakai ku nemi guzuri ku kara gaba kada ka fara neman mahaifiyarka sai kun fice daga cikin wannan nahiya tamu gaba daya shawarar da zan baka guda kada ka tsananta gaba da kowa kuma ka zamo mai hakuri hakanne kadai zai taimakeka ka sami nasara bisa duk abinda zaka sa a gabanka da wannan furuci nake yi muku bankwana sai mun sake saduwa a ranar da zaku dawo wannan birni namu mai albarka na Madinatul haswar sakona ga mahaifiyarka shine ka gaya mata cewa ni Amzad na cika alkawarina na tserar da rayuwarka da kuma damuwarku koda sarkin yaki amzad yazo nan a zancensa sai yarima ya rungumeshi yana mai godiya yace tabbas ka ruke amanar mahaifina, baka kasance butulu ba kamar sarkin yanzu bani da abinda zan iya saka maka dashi bisa rike amanar mahaifina dakayi Amzad ya numfasa yace ina da alfarma guda daya da nakeso kayi mini ina son ka ruke yar uwarka gimbiya amana lallai kasota kamar yadda kake son kanka kuma ka tsare lafiyarta da mutuncinta kamar yadda na tsare taka sa adda yarima yaji wannan batu sai ya jinjina kai yace lallai na dauki alkawari zan tsare rayuwar yar uwata da mutuncinta kamar yadda ka bukata yarima na gama fadar haka sai ya juya ya falfala da gudu izuwa yammacin dajin ai kuwa sai gimbiya da bawa udex suka rufa masa baya ba tare da bata wani lokaci ba shima sarkin yaki amzad ya ruga yabi wata hanyar daban kamar yadda sarkin yaki ya fada haka al amarin ya kasance wato rabin sa a na cika sai ga sarki zamaru tare da dakaru kimanin dari shida bisa dawakai acikin shigar yaki sun iso kofar gidan abincin kimaratu duk wanda ya ga fuskar sarki a wannan lokaci dolene ya firgita saboda kokadan babu annuri a tare dashi saboda tsabar bakin ciki har yatsine fuskarsa keyi kai tsaye sarki Zamaru da dakarunsa suka sauko daga kan dawakansu suka shiga cikin gidan da sauri a wannan lokaci kimaratu da yaranta na ta kokarin gyara barnar da akayi a falon wato suna kwashe karyayyun kujeru da tebura wasu na goge jinin da ya malala a kasa dama tuni an fice da gawarwakin yan fashi da kuma nakasassunsu koda ganin shigowar sarki da dawakansa sai kimaratu ta rugo da gudu izuwa ga sarki tana kuka ta zube kasa gabansa har kimaratu ta budi baki zata ce wani abu sai sarki ya zabga mata wawan mari sabida karfin marin saida ta zube kasa, kimaratu ta dafe kuncinta da hannayanta biyu a lokacin da wani zafi da zugi ya addabi mukamukinta taji kamar ya goce batasan sa adda hawayan wuya ya zubo mataba sarki zamaru ya dakawa kimaratu tsawa yace kada ki yaudareni da irin halinku na tsofaffin bariki lallai jikina ya bani cewa akwai wani munafunci da ake kullawa tare dake na sami labarin cewa danki ya kashe shahararran danfashin nan Bazazga yaushe danki ya koyi yaki har ya zama gawurtaccen jarumi acikin birnina bansani ba? Na nemi yata gimbiya da kuma amintaccen bawana Udez na rasa kuma ance anga udex anan dazu sa adda akayi gumurzu da yan fashin lallai kuwa udez yna tare da gimbiya yanzu gashi babu dan naki anan kuma babu udez da gimbiya ki sanar dani gaskiyar lamari ko kuma ki gwammace mutuwa da rayuwarki the Al amin Ahmed Guyson A Square nake magana duk abinda kika mallaka zan kwace shi kuma zan sa ayi ta gana miki a zaba kullum har ta zamo sanadin ajalinki lokacin da sarki zamaru yazo nan a zancensa sai kimaratu ta tkarkare ta bushe da dariyar Mugunta al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan a wajan lokaci guda kuma sai ta tarbone fuskarta ta dubeshi cikin gadara ba tare da jin wani tsoroba ta ce yakai wannan sarki kayi sani cewa labarin da kakeso kaji yanzu daga bakina dai dai yake da allura ta tono garma zaifi kyau mukadaita dani dakai kasani cewa ni yanzu bani da wani sauran buri a duniya domin idan ka kwace abinda na ke dashi ma wannan gari naka ina da ninkin uku nashi a can wani garin daban inda baka saniba, bani da da na cikina bani da wani dangi a duk fadin duniyar nan babu abinda bangani ba a rayuwata nasha wuya kuma nasha dadi aiko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba ko ka kasheni ka ka barni a raye bani da asara kuma babu wanda zaiyi asafa face wanda ya ke son jin labarin da kake so kaji daga bakina shine kadai zai iya taimakonka ka tunkari makiyanka kuma dole sai dani zaka iya riskar makiyan naka wannan babban kasuwancine a tsakanina dakai Lokacin da kimaratu tazo nan a zancenta sai hankalin sarki zamaru ya dugunzuma ainun ya rasa abinda zaiyi yau ya shiga tunani daga can sai ya kama kafadun kimaratu da hannayansa biyu yana murmushi ya tasheta tsaye ya kaita kan kujera ya zaunar da ita sannan shima ya Zauna daf da ita kawai sai yasa hannu cikin aljihunsa ya dauko hankicinsa mai daraja ya goge jinin dake kan leben kimaratu da kansa ya dubeta yace ki gafarceni yake kimaratu hakika nayi kuskure da nayi saurin kai hannuna fuskarki amma rashin sanine ya janyo hakan yanzu zan tafi kuma zan aiko miki da dinare dubu dari uku domin ki gyara abubuwan da suka lalace a gidan nan zan dawo da kaina cikin dare domin mu tattauna sai nazo ''......KISAN GILLAH Littafi Na Uku (3) Part B. . . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... Mun tsaya ne a inda sarki yace.. Ki zan aiko miki da kudi ki gyara abubuwan da suka lalace a gidan nan zan dawo da kaina cikin dare domin mu tattauna sai nazoo. Zamu cigaba. Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya fice daga cikin gidan da sauri dakarunsa na take masa baya tafiyarsa keda wuya sai kimaratu ta kama kyalkyale dariya kamar bazata dainaba daga can kuma saita fashe da matsanancin kuka har gaba dayan yaranta suka kamu da matukar tausayinta suka shiga rarashinta da kyar suka shawo kanta ta daina kukan sannan aka tasheta tsaye ta tafi izuwa inda turakar take Al amarin sarki kuwa lokacin da ya koma gida sai ya kasa zaune ko tsaye yayi takai kawo cikin tsananin tashin hankali bayan ya dan jima yana tunani da nazari sai yasa aka shirya wani hawan na musamman ya debi dakarunsa na musamman masu tsaron rayuwarsa wadanda ya yarda dasu domin zakwakuraine kuma jajirtattu su dari suka tafi izuwa birnin boka Hizainu tafiyar sa a dayace da rabi tsakanin birnin sarki zamaru da birnin boka hizainu koda su sarki zamaru suka shafa rabi wannan tafiya sai kwatsam suka ga an harbo wata kibiya dauke da wasika tazo ta cake a jikin wata bishiya dake gabansu kadan nanfa suka kama waige waige ko zasu ga wanda ya harbo kibiyar amma ba a ga alamun mutumba a gabas da yamma kudu da arewa nan take sarki zamaru ya yiwa daya daga cikin dakarunsa inkiya yaje ya cire kibiyar daga jikin bishiyar ya kawo masa wasikar har sarki zamaru yayi nufi ya ajiye wasikar sai yaje can gidan boka hizainu sai kuma ya sauya shawara ya warware wasikar da hannunsa ya fara karantata a cikin ransa kamar haka..... Takarda daga hannun sarkin Yakin ka Amzad yakai wannan tsohon azzalumin sarki kayi sani cewa duk abinda mutum ya shuka shi zai girba shekaru ashirin da biyar da suka gabata kaci amanar dan uwanka sarki Hisham domin ka kashe shi ka hau kan karagar mulki ka umarceni dana kashe matarsa da dansa amma sai naci amanarka maimakon naci amar sarki hIsham gawar dana kawo maka ta matar marigayi da jaririnta basu bane, gawar wadansu fatakene da yan fashi suka kashe kuma tsafi akayi aka mayar da kawunansu irin na matar marigayi da jaririnta shi wannan jaririn dan marigayi shine dan da kimaratu ta raina ya girma har ya zama jarumi a boye kuma ba kowa bane ya bashi horon yaki face ni, mahaifiyarsa kuwa tuni tun a wancan lokaci ta bar wannan nahiya don haka wannan yaro yarima ne kuma ya tafi neman mahaifiyar tasa duk ranar da yaga mahaifiyarsa zai dawo nan birnin madinatul haswar ya tsinke maka kai ya hau karagarsa ta mulki a yanzu haka ni da iyalina da kimaratu tuni munyi nisa ga birnin kasar ka har abada ba zaka sake ganinmu ba, kai bayan ka fadi zamu dawo kasani karshen azzalumi maci amana shine kaskanci da mutuwa. Koda sarki zamaru ya gama karanta wannan wasika sai ya takarkare ya kwarara uban ihu ihun da ya firgita gaba dayan dabbobi da tsuntsaye dake cikin dajin saboda tsananin bakin ciki da takaici sai da sarki zamaru ya fado kasa daga kan dokinsa ya kama zubar da kwallah jim kadan sai ya mike tsaye ya dubi daya daga cikin manyan dakarun sa ya ce dashi maza ka koma gida kasa a taro dakaru dubu dari biyu a basu guzuri mai yawa su rabu gida hudu su bazama neman sarkin yaki Amzad da iyalansa tare da kimaratu da danta gabas da yamma kudu da arewa har zuwa karshen iyakokin mu da zarar an gansu a kashesu a zo mini da kowannansu duk rundunar da tasamu nasarar aiwatar da wannan aiki zan mai shesu attajiran da babu kamarsu a kasata kuma zan daukakasu acikin majalisata koda jin wannan umarni sai badakaren ya risina da sauri jikinsa na bari yace an gama ya shugabana cikin hanzari badakaren ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya ya nufi hanyar da zata mayar dashi birnin madinatul hashwar tamkar zai tashi sama saboda karfin gudu bacewarsa ke da wuya sai sarki zamaru ya sake jagorantar dakarun suka ta samma birnin boka hizainu da yake wannan karon sarki zamaru a fusace yake kuma gudu yake bisa dokinsa a lokacin da zuciyarsa ke tafarfasa kamar zata kone nan da nan suka isa birnin da isowarsu kofar gidan sarautar sai suka iske boka hizainu tsaye fadawansa sun kewayeshi fuskarsa a murtuke al amarin da yasa zuciyar sarki zamaru ta buga da karfi kenan tsoro ya darsu da mamaki suka baibayeshi sarki zamaru da dakarunsa na gama shigowa cikin harabar gidan sarautar sai dakarun hizainu sama da dubu biyu suka kewayesu sukayi musu kawanya cikin rudewa da rashin fahimta sarki zamaru ya dubi boka hizainu yace, me zan gani haka? Akan wane dalili zakasa dakarunka su ritsamu maimakon ka tarbemu hannu biyu? Sa adda boka hizainnu yaju wadannan tambayoyi sai ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya lokaci guda kuma sai ya turbone tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi sarki zamaru a fusace yace akan wane dalili zaka debo zakwakuran dakarunka ka kawo mini ziyarar ba zato? Rabona da kai yau shekara ashirin da biyar kenan tunda ka raba kasarka da dukiyarka ka bani rabi ka manta dani ko sakon gaisuwa baka taba aiko mini ba bare ziyara babu mamaki yanzu ka zone da shirin ka yakeni ka karbe abinda ka bani, sa adda boka hizainu yazo nan a zancensa sai sarki zamaru yayi murmushi sannan yace ai kai boka ne kasan abinda bansani ba me yasa bakayi bincike ba ka gano dalilin zuwana gareka, tsawon shekaru ashirin da biyar baya ina zaune lafiya cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali kaima haka tabbas ruwa baya tsami banza kaima kasan cewa akwai abinda ya kawo ni gareka babu wanda yasan sirrina sama da mutum biyu a cikin fadin wannan duniya daga kai sai sarkin yakina Amzad to ka sani yanzu sarkin yakina yaci amanata domin duk abinda ya faru a baya yaudarata yayi bani ya taimaka ba abokan gabaata ya taimaka wannan yaro wato yarima dan marigayiii...... Kafin sarki zamaru ya gama fadin abinda ke bakinsa sai boka hizainu ya dakatar dashi yana mai daga masa hannu kawai sai ya kyalkyale da dariya sannan yace nasan komai hatta tare ka da nayi yanzu dan kurum na gwada ka nayi don naga karfin zuciyarka kazo ka iyayin abinda nakeso kayi ina son ka kwantar da hankalinka tamkar tsumma a randa zo muje ka huta sannan saimu tattauna bisa abinda zai fishshemu koda gama fadin haka sai farin ciki ya lullube sarki zamaru ya sauko daga kan dokinsa da sauri ya rungume boka hizainu suna masu kyalkyalewa da dariya a tare. The Guyson naci gaba da cewa Al amarin su yarima da gimbiya kuwa tunda suka nausa cikin daji suna masu bin yamma basu yada zango ba ko inaba har sai da suka iso wannan kauye. Da

Chapter 4 of 8