Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 8
fadawanka da makusantar ka ko talakawanka akwai mai shirin daukar fansa a kan ka kaga kenan idan bai sami damar cutar da kai ba zai iya kokarin cutar dani ko mahaifiyata a yanzu ko nan gaba na sani cewa idan na sanar da kai cewa ina son na koyi yaki hanani zakayi saboda ganin cewa kowa na shakkarka a garinnan kai bama a garinnan ba a gaba daya kasashen dake makwabtaka damu ba masarautar da bata shakkarka. Waishin menene dalilin da yasa kai da sarki huzainu kuke girmama juna kuma sarakuna ke nuna biyayyar dole a gareka suna kawo maka gaisuwa da dukiya amma banda sarki huzainu gashi a kasarsa babu tarin dakaru da mayaka kamar namu? Hm Yarinya kenan baki san waye ubanki bane da bakiyi wannan Tambaya b nine Al amin Ahmed Guyson me zai hana mu shirya yakin sumame muje mu murkusheshi domin mu fadada kasarmu mu bunkasa arzikin tunda kasar tasa na daf da tamu ni ina tabbatar da cewa a dare daya zamu iya cinsa da yaki ko kuwa saboda ana cewa babu matsafi kamarsa a wannannahiya shi yasa kake shakkarsa yakai abbana kayi sani cewa matsafa sunfi sarakai son duniya komai daren dadewa wata rana Sai yayi ynkurin mallake tamu kasar, sa adda gimbiya musaira tazo nan a zancenta sai sarki zamaru ya tari numfashinta cikin fishi gami da daga murya yace kada ki sake shiga tsakanina da sarki hizaunu domin amininane kuma akwai babban sirri tsakanina dashi wanda ba zaki taba sanin saba bisa laifin da kika aikata na koyon yaki ba tare da sanina ba na kafa miki takunkumin fita ko ina na tsawon kwana bakwai koda gama fadin haka sai sarki zamaru ya juya ya nufi cikin gidan sarautar ya bar gimbiya musaira a tsaye cikin tsananin fishi domin a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da irin takunkumin da sarki yake yawan kafa mata na fita da yin rangadi a birnin Tun tawowar gimbiya musaira daga kuruciya kawo izuwa yanzu da ta cika shekara goma sha tara a duniya duk inda zataje tana tare da dakaru gami da kuyangi ba a barinta ta sami sakewa bata da kawa bata da aboki sai dakaru da hadimanta kadai su kansu da zarar anga ta fara sabo da dayansu sai a sauyashi sarki zamaru ya tsara hakan kuma umarnin boka hizainu ne gimbiya musaira tasha yin kuka akan hakan kuma duk da ita don tabbatar da tsaron lafiyarta ne nan dai gimbiya musaira ta tafi zuwa masarauta cikin fishi da matukar damuwa saboda a yau dinnan ta shirya zuwa kasuwa da yamma kuma gashi an kafa mata dokar fita a rayuwar gimbiya musaira tana son tayi mu amala da talakawa kuma tana son ta yawata a cikinsu ba tare da an gane ko ita wacece ba amma saboda sarki zamaru yasa idanuwa a kanta damar hakan ta gagara lokacin da gimbiya musaira ta iso cikin turakar ranta a bace harma idanuwanta sun ciko da kwalla saboda takaici da bakin ciki sai tayi arba da wani hadiminta a tsaye yana gyara shinfidar gadonta wadansu kuyangi guda biyu na gefensa hagu da dama suna gyara matasan kan gimbiya sai yai sauri ya sunkuyar da kansa kas kuma ya juyo ya nufi kofar fita daga turakar kawai sai yaji gimbiya ta kira sunansa tana mai cewa yakai udez tsaya anan ina son yin magana da kai udez ya tsaya cak jikinsa na kyarma saboda tsoro da mamaki ba komaine ya fefa udez a cikin tsoro da mamaki ba face tunda ya fara yiwa gimbiya aiki bata taba kiran sunansa ba kuma bai taba magana da ita ba tsawon dakika biyu face tace dasu ku fita ku bani wuri ba cikin sauri da biyayya kuyangin sukafice kuma suka janyo kofar turakar suka rufeta bam ya zamana cewa udez da musaira kacal a cikin turakar musaira ta tunkaro udez gadan gadan tamkar zata rungumeshi al amarin daya kara dugunzuma hankalinsa kenan ko ina a jikinsa ya ci gaba da karkarwa yaji kamar ya fasa ihu koya runtuma da gudu don gudun kada ya aika ta wani babban laifi wanda zai iya zama sanadin ajalinsa tunda yasan halin sarki zamaru ba sani ba sabo sai da muraisa tazo daf da udez yadda suna iya jin numfashin juna sannan tace nayi bincike akanka na sami tabbacin cewa kafi kowa dadewa a bauta a wannan gidan sarauta kafi kowa sanin sirrin mahaifina da kuma sirrin masarautar nan ance kana da tarihin sarakunan da suka gabata har izuwa kan mahaifina saboda yardar da mahaifina yayi maka kaine kadai da namiji daya taba shigowa nan cikin turakata har yayi mini hidima mahaifina ya boye mini wadansu al amura nasa wadanda nakkishirwar saninsu lallai daga bakin kane kadai zanji amsar tambayoyin da na dade ina yi masa su yaki bani amsar tasu tambayoyina guda biyu ne rak mafi mahimmancin .. Ta farko mutuwar dan uwansa sarki hisham wanda akace cutar kankanin lokacine ta zama sanadin ajalinsa? Tambaya ta biyu kuma itace menene dalilin da yasa sarki ya hanani tarayya da ko wa a birninnan na taso a cikin rayuwar kadaici ta rashin kawa ko aboki? Bayan wadannan tambayoyi bani da wata bukata daga gareka sai guda daya bukatar kuwa ina son duk yadda za ayi a daren yau ka fitar dani daga cikin gidan sarautar nan ka kaini inda zanyi nishadi domin na huce bakin cikin zuciyata, in kaimin haka cikin sirri ba tare da kowa ya saniba zan sa sarki ya mallaka maka gida ka huta da biyan haya a cikin aljihunka zan baka kudin da zaka iya yin noman bana a gonarka harma ka dawo da dabbobinka da suka mutu a cutarna na annoba koda gimbiya musaira tazo nan a batunta sai idanun udez suka zazzaro ya rasa abindake masa dadi a duniya domin ga bikin zuwa amma babu zanin daurawa ehm Al amin Guyson Sunana Dan Misau, tabbas bashi da burin da yafi ya mallaki gida a rayuwarsa kuma yayi noma da kiwo to ammafa idan ya biyawa muraisa bukatarta har sarki ya gano hakan tamkar ya siyar da rayuwarsa ne koda ganin hakan sai hawaye ya zubowa muraisa nan da nan kuma fuskarta ta juya izuwa tsananin fishi da rashin imani kawai sai ta zaro wata sharbebiyar wuka a jikinta ta dora kaifin ta akan makogwaron udez ta dan danna ta yankeshi jini ya zubo udez yayi dan ihu sakamakon zafi da zugin da yaji ta dubeshi tace na rantse da girman uwata idan baka biya mini daya daga cikin bukatuna ba yanzu take zan aika ka barzahu maimakon ajalinka ya rataya a hannun sarki zai rataya a nawa saboda tsananin firgici udez baisan sa adda hawayen tsoro ya zubo masa ba ya budi baki da kyar cikin hadiyar miyau yace zanyi iya biya mikiBukatarki ta karshe na fitar dake daga cikin gidannan a sirrance batare da kowa ya sani ba har ki dawo amma bazan iya sanar dake amsoshin wadancan tambayoyi ba guda biyu, muraisa tace ashe kenan har abada bazan daina bakin cikida ya addabi zuciyata ba tunda sanin amsoshin nanne kadai zai yaye min su in kuwa hakane gwara na kashe ka muryar udez na rawa yace aa zaki iya sanin amsar tambayoyinki daga bakin sarkin yaki shine ma yafi kowa saninamsar amma bansan ta yadda zaki iya shawo kansaba har ya amince ya sanar dake sa adda gimbia muraisa taji wannan batu sai tayi shiru tana tunani kawai sai ta tafi izuwa wata turaka ta dauko auduga tazo ta likata awuyan udez don tsai da jinin dake diga sannan ta dubeshi cikin murmushi tace misalin wane lokaci zaka fitar dani daga cikin gidannan Koda jin wannan tambaya sai murmushin farin ciki ya subucewa udez saboda yasan cewa ya tsira daga hannun mutuwa don haka sai ya dubi muraisa cikin fara a yace bayan rana ta fadi gari ya soma duhu a lokacin da ake ta hada hadar cin abinci kedai kawai kiyi duk abinda zan umarceki da yi sabawar hakan zata janyo rashin nasara udez na gama fadin haka sai ya mika mata wani kullin kaya dake hannunsa yace wannan kyana aikina ne na gidannan da zarar rana ta fadi gari yayi duhu ki shiga cikin kewaye ki cire tufafin dake jikinki ki sanya wadannan ki tabbatar da cewa kinyi shigar maza kin batar da duk wata sura ta ya mace ajikinki udez na gama fadin hakan sai ya juya da sauri ya fice daga cikin turakar har yana tuntube kamar ace kyat ya saki fitsari a wando burinsa kawai yaga ya fice lafiya ba tare da ya rasa rayuwarsa ba ita kuwa gImbiya muraisa sai ta bishi da kallo tana yi masa murmushin dariya gami da farin ciki bisa ganin cewa zata sami biyan bukatarta.....KISAN GILLA Littafi Na Biyu (2) Part B. . . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... KAMAR YADDA udez ya umarceta da yi haka tayi wato rana na faduwa muraisa ta shiga kewaye ta cire tufafin dake jikinta ta sanya wadanda udez ya bata ga shin kanta kuwa saita tattareshi ta sanya wata hula sai ta zama kamar askin kwalkwal Gimbiyq tqyi Ta boye gashin ko alamarsa ba agani dama an bayar da dokar kada kowa ya sake shigowa cikin turakarta face bawa udez sai da gimbiya muraisa ta shafe sa a na wani lokaci a wannan lokaci tuni an dan jima da fara hada hadar cin abinci nan fa hankalinta ya duunzuma tafara tunanin ko bawa udez yaci amanar tane yaje ya sanar da sarki duk abinda ya faru a tsakaninsu tana cikin wannan haline kawai taji an turo kofar turakar tata nan take zuciyarta ta buga da karfi saboda ta san cewa in banda sarki babu wanda ya isa yayi mata irin wannan shigowar ta banko kofar daki ta wangame gaba daya haka kuma da karfi har tana dukan bango bisa mamaki sai gimbiya taga ashe bawa udez ne dauke da wani kwanan abinci babba kwanan a cike yake da abincin dakaru udez ya dubi gimbiya cikin alamun tsoro yace ki gafarceni ya shugabata yau zan saki dako gashi baki taba daukar abu mai nauyin kamar haka ba tayi murmushi tace waya gaya maka ban taba daukar abu mai nauyin wannan ba to ka sani cewa na dauki dutsen da yafi wannan kanon nauyi sau uku a lokacin da nake karbar horon yaki a wajan sarkin yaki udez ya maida mata da martanin murmushi yace tabbas na gamsu yanzu ina son ki bini a baya ki sunkui da kanki har mufice daga cikin gidan nnan kada ki dago da fuskarki kuma ka da kiyi magana da kowa mutum daya ne jal zai iya gane ki a wannan shiga da kika yi kuma ba kowa bane face sarki amma na tabbatar da cewa babu abinda zai fito da sarki daga cikin turakarsa a wannan lokaci zomu tafi udez na gama fadin hakan sai ya juya ya fice yana dauke da wani babban tambulan na ruwan inibi ita kuwa gimbiya muraisa sai tayi sauri ta dauki wannan kwanon abinci ta aza a kanta kuma ta sunkui da kanta kas tabi udez a baya tamkar bawa da ubangidansa komai kallon kurillan mutum bai isa ya gane cewa muraisa mace ce ba namiji ba, haka dai suka ci gaba da tafiya a cikin harabar gidan sarautar suna wuce dakaru hadimai da barori harma da kuyangi da yake bawa udez na hannun daman sarkine duk abinda yake yi a gidan sarautar babu mai tuhumarsa sai da suka iso har kofar karshe ta fita daga gidan ba tare da sun fuskanci wata matsala ba kwatsam ba zaato ba tsammani saiga sarkin yaki amzad ya shigo cikin gidan sarautar da sauri har suka bangaji juna shida udez cikin sauri udez ya zube kasa a gaban amzad yace ka gafarceni ya shuagaban mai makon sarkin yaki amzad yayi fishi sai ya wuce gaba ko kallonsa baiyi ba koda amzad da muraisa suka gifta juna sai tsigar jikin amzad ta tashi don haka sai ya waigo da sauri ya kwalawa udez kira udez ya juyo a firgice hantar cikinsa na kadawa a lokacin da idanunsa suka zazzaro ya tako a hankali ya iso gaaban sarkin yaki amzad ya dubeshi a nutse yace yau kuma nenene dalilin da yasa zakayi irin aikin da ba naka ba na tabbatar da cewar wannan tambulan da kake dauke dashi na ruwan inibi na masu gadin kofar gidannan ne saboda me zaka wulakanta kanka haka alhalin kaine babban hadimin sarki koda jin haka sai bawa udez yayi murmushi yace haba ranka ya dade baka lura bane da kyau ai wannan tambulan din irin na sarki ne kuma ruwan inibin dake cikinsa na musamman ne gidan waziri zamu kai koda jin wannan batu sai amzad yayi murmushi ba tare da ya kara cewa uffan ba sai ya juya ya nausa izuwa cikin gidan sarautar cikin hanzari udez da gimbiya muraisa suka ci gaba da tafiya har suka sami nasarar ficewa daga cikin gidan sarautar gaaba daya ba tare da sun fuskanci wata damuwa ba Nine Al amin Ahmed Misau, Guyson sunana kenan kai tsaye suka kunna kai zuwa cikin gari basu zame ko ina ba sai wani babban gidan saida abinci mallakin wata mace da ake kira kimaratu shi dai wannan gidan abinci ya shahara a cikin birnin na madinatl haswar domin matattara ce ta manyan baki da kanana kimaratu karuwace ta manyan mutane domin daga sarakai attajirai ke zuwa wajanta don haka babu wanda yayi mamakin yadda ake yi ta mallaki wannan gidan abinci wanda a kullum ta Allah akanyi ciniki na sama da dinare dubu dari fiye da shekaru goma sha biyar baya wannan gidan abinci ya bunkasa don haka ne kimaratu ta zamo babbar attajira A dai dai lokacin da bawa udez da gimbiya suka iso wannan gidan abinci ne wasu bakin fatake suka iso bisa dawakai kimanin su dari uku shugabansu na cikin wani babban keken doki na alfarma su kuwa sauran jama ar tasa suna bisa ingarman dawakai cikin shigar yaki mai kwarjini da ban tsoro domin kai da gain kura kasan zataci mutum nan da nan wani yaron kimaratu ya kai mata labarin cewa yaufa ga wadansu manyan baki sunzo dajin haka sai kimaratu ta mike zumbur ta rugo waje da gudu ta zube kasa a gaban shugaban fataken a lokacin da ya zuro kafafunsa kasa daga cikin keken doki babu abinda zai baiwa mutum mamaki kuma ya bashi dariya face ganin yadda kimaratu ta rugo da gudu duk da Cewa nauyin jikinta yakai na buhun alkama biyu sakamakon kibar da take da ita nan fa ta zube kasa wanwar a gaban shugaban fataken ta kama kwasar gaisuwa hakika rashin sani yafi dare duhu inda kimara tasan wanene wannan shugaban fatake kuma ta san abinda ya kawo shi wannan gidan abinci nata da tayi babbar nadamar yi masa marhaban nan dai tana rawar jiki ta yiwa shugaban fataken jagora shi da jama arsa suka shiga cikin gidan gidane babba mai dauke da babban falo cike da kujeru da tebura gidan a cike yake da mutane maza da mata ana ta ciye ciye da shaye shaye ma aikatan wannan gida masu raba abinci a abin sha a kalla sunkai su dari da sha daya kuma kaso biyu cikin ukunsu mata ne sannan akwai dakaru masu tabbatar da tsaro , lokacin da kimaratu da wadannan bakin bafatake suka shiga cikin gidan abincin bawa udez da gimbiya muraisa na tsaye a gefe daya a kofar gidan abincin koda muraisa taga yadda ake ta haba haba a wannan wuri cike da jama a sai zuciyarta tayi sanyi ta kamu da matukar farin ciki nan daisuma suka shiga cikin gidan da shigarsu sai suka nufi wani teburi daban wanda babu kowa a kansa suka je suka zauna nan take suka bayar da umarni aka kawo musu ruwan inibi caraf sai gimbiya ta tari numfashin bawa udez tace A'a ni ba zansha ruwan inibi ba abinci zak sa a kawo mun cikin tsoro da mamaki udez ya zaro idanu ya dubeta cikin rudu yace haba ranki ya dade yaya ke da kika saba cin abincin irin na gidan sarauta mai lafiya da daraja yanzu kuma zaki zokici na kasuwa koda jin haka sai gimbiya tayi murmushi tace ai mahaifina yace idan kaje gari kaga kowa da bindi kaima ka nemi wani abu ka daura haka dai udez ya sake bayar da umarni aka kawowa gimbiya farfesun kifi da gurasa ta fara ci koda ta dago kai saita hango shugabawadannan bakin fatake tare da wani yaronsa suna kalle kalle a cikin gidan kuma suna yiwa junansu rada koda ganin haka sai hankalin gimbiya ya tashi ta dubi bawa udez cikin alamun tsoro tace ban yarda da wadancan mutanenn ba ba cin abinci ne ya kawo su nan ba da jin haka sai udez yayi murmushi yace saboda me kika ce haka gimbiya ta numfasa tace sarkin yaki ya gaya min cewa alamar munafiki shine yawan kallo da gulma nidai jikina ya bani cewa wadannan mutanann barayi ne kafin kowa ya ankara zare takubbansu sun ritsa dukkanin dakarun dake tsaron gidan shikuwa shugaban dakarun fataken sai yayi wuf ya cafko kimaratu ya dora wata sharbebiyar wuka a kan makoshinta yace maza kisa a kaimu inda ma ajiyar kudinki suke cikin razani da firgici gami da rawar murya kimaratu tace aini bana ajiye kudi a nan gidan shugaban yan fashin ya daka mata tsawa ta firgita ainun sannan yace idan kika raina mana hankali zaki rasa rayuwarki yanzun nan ki sani cewa kafin muzo nan saida muka san sirrinki da sirrin gidan nan a cikin dakarunnan can guda goma sha biyu akwai rijiya a cikin na tsakiyarsu a cikin rijiyar akwai wata katuwar akwatin karfe mai tsawo da fadin kamu ar ba in mukullin wannan akwatu muke bukata yanzu yanzu ko kuma ki rasa rayuwarki koda jin wannan batu sai tsoro da mamaki suka baibaye kimaratu ta tabbatar da cewar lallai wadannan bakin fatake rikakkun yan fashine kuma lallai sun sami hadin kan daya daga cikin hadimanta wanda ya sanar da su sirrin ma adanarta har kimaratu ta budu baki za tayi magana sai akaga an banko wannan kofar daki dake tsakiyar dakunan goma sha biyu wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga cikin dakin ma abocin kyawu da kwarjini kallo daya zaka yiwa wannan saurayi ka gane cewa ya cika sadauki domin kirar jikinsa itace amsa riga mai yankakken hannuce wadda ta bayyana faffadan kirjinsa gami da damatsan hannayansa saurayin na dauke da wata zabgegiyar takobi goye a gadon bayansa hannunsa na hagu na rike da wata katuwar kuba fuskarsa cike da murmushi ya dubi shugaban yan fashin yace lale marhaban da sarkin barayi Huzaga bn Salfas ka sani cewa wannan kuba dake hannuna itace mabudin wannan akwatin kudin da aka zo nema nine maigadinta wannan mace daka ritsa da wuka mahaifiyata ce idan ka kuskura kayi mata rauni kwatankwacin girman silingashi zaka koma gida ka iske gawar matarka razina da danka Darsil wadanda ka rabu dasu a jiya sun tafi izuwa birnin darul hasin kamar yadda ka shafe kimanin watanni uku kana nazari da bincike akan dukiyar mahaifiyata haka nima na shafe watanni uku ina nazari da bincike akan ka da iyalanka don tabbatar da tsaron dukiyar mahaifiyata kasani cewa shekarata goma sha shida ina karbar horon yaki a wajan sarkin yakinmu ba don komai ba sai domin na kare wannan dukiya ta mahaifiyata ga fili ga mai doki ga makullin akwatin kudi kuma gaka ga yaranka idan zaka iya karbar makullin ku jarraba mu gani sa adda wannan saurayi yazo nan a zancensa sai shugaban yan fashin ya kamu da tsananin mamaki ya kurawa jarumin saurayin idanu kawai kuma yayi shiru har zuwa tsawon yan dakiku A wannan lokaci gaba dayan mutanan dake cikin wannan dakin abinci a firgice suke kowa ya kame kamar gunki an daina ci da shan komai wasu da yawa jikinsu kyarma yake yi babu wanda yafi bawa udez firgita da Da shiga tashin hankali domin yasan cewa idan wani abu ya sami gimbiya tasa ta kare gaba daya dakin cin abincin yayi tsit tamkar babu mai rai a cikinsa kawai sai akaga shugaban yan fashin ya ture kimaratu daga gabansa ta fadi can gefe daya cikin zafin nama ya zare takobinsa maimakon ya afkawa saurayin sai ya dubi wasu daga cikin dakarun nasa yace ku cisgo mun kan wannan yaron ai kuwa nan take kimanin su dari suka rugo da gudu izuwa kan jarumin saurayin wohoho bala i ba a sa masa rana kuma mai karfi sai Allah ya isa nan fa aka ruguntsume da masifaffen yaki da farko hankalin gimbiya a tashe yake donji take kamar ta rusa ihu amma ana fara bakin gumurzun tsakanin yan fashin da saurayin sai ta sami abin debe kewa abu na farko da ya jefata cikin tsananin mamaki shine ganin irin salon yakin da jarumin yake yi iri daya ne sak danata shin malamin da ya bata horon yaki shine ya koyar da wannan saurayi amsar da bata sani ba kenan suma sauran jama ar dake wajan sai suka kamu da tsananin mamakin jarumtar wannan saurayi saboda yaune karo na farko da aka ga irin jarumtakarsa A lokaci guda dakarun darin sukayi masa rubdugu suna kai masa sara da suka ta ko ina yayinda ya rina yin wata irin katantanwa a tsakiyarsu yana kare dukkan hare harensu ba tare da ya maida martani ba sai da aka shafe kusan dakika dari uku da sirrin ana wannan fafatawa ba tare da dayansu ya sami nasarar koda karzanar jikin jarumin ba tabbar jarumin ya nuna ba ajinta da jarumtaka a mma fa hantar cikin kowa ta kada a dakin saboda babu wani tebur ko kujerar da bata ragargaje ba a cikin dakin sakamakon wadannan artabu hankalinn kowa sai da ya dugunzuma banda na Guyson mai typing din littafin hatta ita kanta gimbiya data kasance jaruma sai gashi tana buya da labewa a karkashin abubuwa don kada tsautsayi ya sameta bisa dole wadannan dakarun dari suka janye daga kan jarumin suka koma can baya inda shugabansu yake sukayi cirko cirko suna haki saboda gajiya suna sauraron umarnin da shugabansu zai sake bayarwa ...... . Anan zan dakata Sai Allah ya kaimu Gobe zamu cigaba Sunana Al amin Ahmed Misau Guyson Inkiyata Kenan Admin Na Zauran Labarai May 5 at 7:40 AM · PublicKISAN GILLA Littafi Na Biyu (2) Part C. . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... suna sauraron umarnin da shugabansu zai sake bayarwa kawai sai shugaban ya daga hannunsa na dama ya bude dukkanin yatsunsa biyar ashe hakan na nufin gaba dayan dakarun su dari uku su afkawa jarumin ai kuwa sai suka zare takubbansu duka suka ruga izuwa kansa koda ganin hakan sai shima ya zare takobinsa dake bayansa ya tunkaresu aka sake kacamewa da masifaffen yaki amma wannan karon yakin ya sauya salo domin shima jarumin ba kare kansa kawai yakeyiba yana maida marta ni nan fa labari ya sha ban ban domin sai gani akayi yana bazar da dakarun suka rinka zubewa kasa sakamakon jinin dake tsartuwa da feshi ajikinsu duk da kasancewar hakan in dai ba kawunansu ya tsinkeba sai gashi suna mikewa suna kai masa muggan hare hare saboda nacinsu da juriyarsu tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da sukace sarkin yawa yafi sarkin karfi duk da cewa wannan jarumin saurayi yana da matukar karfi jarumtaka da zafin nama sai gashi wadannan mayaka dari uku sun fara kuntata shi domin har sun sami nasarar yi masa rauni guda biyu daya raunin akan cinyarsa na dama aka yankeshi wurin ya dare jini na zuba rauni na biyu kuwa a gadon bayansa aka sareshi wajan yayi dan rami yana zubda jini tsabar juriya da jarumta kace tasa bai sare ba bisa kwarin guiwar ganin shima ya bazar da kimanin mutane dari da sittin a cikinsu wadanda ko mikewa ba zasu iya ba wasu ma halin da suke ciki zai iya zma sanadin ajalinsu lokacin da gimbiya muraisa ta lura da halin da take ciki a wannan yaki tsakanin jarumin saurayin da wadannan yan fashi sai hankalinta ya dugunzuma taji ta kamu da tausayin saurayin komai taji tana son ya sami nasara akan yan fashin to wai shin ma saboda me naji ina tausayinsa tambayar da gimbiya ta yiwa kanta kenan kuma ta kasa gano amsarta tana cikin wannan tunani ne taji saurayin ya kurma uban ihu sakamakon sara na uku da akayi masa akan cinyarsa na dama cikin tsananin fishi da juriya ya daka tsalle sama ya sare kawunan mutum goma daga cikin yan fashin a lokaci Guda hakan ne ya razana su duka suka ja da baya shi kuwa jarumin sai ya durkushe kasa cikin yar galabaita yayi sauri ya yanki rigar fatar dake jikinsa ya daure raurin cinyar don tsaida jin koda ganin abinda ya faru sai kimaratu ta fashe da kuka don ta san cewa komai zai iya faruwa ga wannan da nata shi kuwa shugaban yan fashin sai ya bushe da dariyar mugunta ya nuna jarumin da hannunsa guda yace kai yaro karyarka tasha karya yanzun nan zamu yi maka KISAN GILLAH sannan mu karbe kubar dukiyar dake hannunka ita kuwa wannan uwar taka tsohuwar karuwar zata zamo mai shar dani ruwan giya koda jin wannan batu sai jarumin ya kamu da bakin ciki har hawaye ya zubo masa nan take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone cikin tsananin fishi ya ynkura ya mike tsaye da sauri yana mai kwarara uban ihu ai kuwa sai dakarun bayin suka sake afka masa aka ruguntsume da sabon azababben yaki koda ganin haka sai gimbiya muraisa ta yunkura domin ta kaiwa jarumin saurayin dauki amma sai bawa udez ya yi wuf dakatar da ita ya dubeta cikin tsananin tsoro yace kiyi mun rai ya shugabata idan wani abu ya same ki mutuwa zanyi dajin haka sai gimbiya ta murrtuke fuskarta tamkar an aiko mata da sakon mutuwa tayi wuf ta zaro wata karamar adda

Chapter 3 of 8