Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
shigowa kauyen suka gane cewa sun shigo wata nahiyar daban domin yanayin mutanen da yanayin shigarsu da al adonsu ya fita daban da irin na mutanen tasu nahiyar su dai mutanen wannan kauyen suna kama da mutanan birnin hindu kuma kyawawane kuma fatar jikinsu wankan tarwadace amma kuma wani irin yare sukeyi wanda su yarima suka kamu da tsananin mamaki bawa udez ya dubi yarima da gimbiya yace waishin ta yaya muka iya isowa wata nahiyar haka acikin kankanin lokaci ku dubi mutanan nan fa ku gani sai kallonmu sukeyi kamar baso kasance mutane irinsu ba dajin wannan batu sai gimbiya musaira tayi murmushi ba tac komai ba shi kuwa yarima sai ya numfasa yace shin ka manta da wanda ya bamu umarnin hanyar da za mubi acikin tafiyar tamune? Tabbar tafiyar tamu aikine na tsafi bako karinmu bane gimbiya koba haka bane? Maimakon gimbiya tace wani abu sai ta tabe fuska ta kau da kai Al amarin da yasa yarima yaji haushi kenan yace wai me wannan yarinyar take nufine? Idan takamar ta sarauta ai nima dan sarkine kuma gashima ni da ita yan uwane ko kuwa jan aji take yi mini irin nasu na mata to ai ban nuna ina sonta ba duk da cewa ban taba ganin mai kyanta ba ni kam bazan taba son macen da ba itace ta nuna mini so ba wannan shine Ra ayin Guyson nima, gama aiyana hakan keda wuya sai bawa udex ya dubi yarima yace ya shugaba na muje muci abinci sannan mu sayi dawakai kamar yadda sarkin yaki ya umarcemu don ya gargademu akan kada mu kuskura mu kwana a nan koda jin haka sai yarima ya gyada kai yace kwarai kuwa gwara daka tuna mana kuzo muje nan take yarima ya nufa wata rumfa inda ake siyar da abinci cikin hanzari bawa udex ya bishi sannan musaira tabi bayan udex tana yanga a lokacin da gaba dayan mutanan dake wajan suka kura mata idanu ba komaine yasa mutane ke kallon gimbiya ba face yadda tayi shigar mza a matsayinta na ya mace a wannan lokaci ta saki gashin kanta ya zuba har kasan kankwasonta kuma ta cire rawanin da ya rufe fuskarta kuma ta cire mayafin da ya lullube jikinta wanda ya rufe dukkan siffofin jikinta na 'ya mace da isarsu sai suka iske wata tsaleliyar budurwa tana rabawa kwastomominta abinci musaira na ganin wannan budurwa sai zuciyarta ta buga da karfi nan take taji kishi ya turnuketa saboda bata taba ganin mace mai kyan taba budurwar ta kasance doguwa abar kwatance wacce babu 'da namijin da zai ganta bai dimauceba koda budurwar taaga shigowar su yarima sai ta taho da sauri taryesu kamar wacce taga shalakinta, cikin girmamawa ta gaishe su a cikin yarensu tana mai cewa lale marhaba da mutanan birnin madinatul haswar cikin tsananin mamaki suka kyra mata idanu duk su ukun yarima ya dubeta yace ya akayi kika iya yaranmu kuma ta yaya kika san daga inda mukazo koda jin wannan tambaya sai budurwar tayi dariya sannan tace uba na bafatake ne tun ina da shekaru bakwai yake zuwa dani ga rinku fatauci akwai lokacin da muka shafe shekara biyu da rabi a birninku a lokacinne na iya yaranku amma fa kunsha tafiya domin daga birninku zuwa nan tafiyace ta kwana sitttin da uku koda jin wannan batu sai su yarima suka sake kamuwa da tsananin mamaki amma sai sukayi shiru basu ce da ita komai ba budurwar ta dubi yarima cikin tattausan murmushi wanda ka iya sabauta matashi tace ammafa kai da wannan budurwar kona kama yar uwarka ce ko? Kafin yarima ya budi baki ya bata amsa sai gimbiya ta tari numfashinta tace kinga ba hirace ta kawo mu ba abinci zaki bamu muci a kan hanya muke dajin haka sai budurwar ta bata rai tace kwantar da hankalinki ba son dan uwanki nake ba sanin darajar kwastomoni ce tasa kikaga Ina magana dashi anan garin nafi zinare daraja maza da yawa sun mutu saboda ni ki bincika kiji koda jin haka sai gimbiya ta bushe da dariya tace ai banyi mamaki ba tunda nan kauyene budurwar tace kwarai kuwa ai a birnima babu kamata idain kuma akwai kaini na gani sama da sarakuna dari sunzo daga birane neman aurena basu samuba cikin mamaki yarima ya dubi budurwar yace meye sunanki? Budurwar tace bazaka jishi ba daga bakina ba ka tambayi kowa koda yara kuwa domin ni fitacciya ce a wannan nahiya gaba daya duk fadin kauyan nan babu mai arziki na kaso tamanin na kasuwarnan tawace yarana ke gudanar da ita dajin haka sai gimbiya tayi dariya tace amma kika boye da siyar da abinci budurwar tayi murmushi tace kamar yadda mahaifinki ya buge da nunawa dan uwansa kauna har yaci amanar sa ya kashe shi don ya hau karagar mulki haka nima na buge da wannan sana'a don cika wani babban burina na duniya ni marainiyace ba uwa ba uba sai dukiya dolene na cika burin da iyayena suka mutu a kansa. Koda jin wannan batu sai jikin su yarima yayi sanyi matuka musamman gimbiya musaira domin sun kuyar da kanta tayi kas tayi shiru bata kara cewa uffan ba saboda tsananin mamaki har budurwar ta kawo musu abinci suka gama kimtsawa dayansu bai kara cewa ko mai ba.KISAN GILLA Littafi Na Uku (3) Part C. . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... sun kare cin abincin ne yarima ya yafito kyakkyawar budurwar da hannunsa ta taho gareshi fuskarta cike da annuri da murmushi nan take a karon farko yaji kibiyar soyayya ta sokeshi domin kyawunta ne ya riba ceshi baisan sa adda ya mike tsaye ba kuma ya risina a gareta yace ranki ya dade nawa ne kudin abincin mu? Koda jin wannan tambaya sai budurwar tayi murmushi tace bana bukatar ko sisi daga gareku nasani cewa zaku sayi dawakai guda uku don ci gaba da tafiyarku zan baku kosassun dawakai kyauta ya kai yarima ka bar kudinka hatta guzuri ni zan baku duk abinda kuke bukata har yarima ya budi baki zaice wani abu sai budurwar ta tari numfashinsa tace kar kace komai saimun isa gidana ku biyoni muje cikin fushi gimbiya musaira ta dubi yarima tace wai akan wani dalili zaka dauki amincinka ka bata alhalin yau ka fara ganinta shin kasan irin nufin da take dashi akanmu dajin yadda tasan komai akanmu matsafiyace baka tunanin cewa zata iya cutar damu? Har yarima ya budi baki zaice wani abu sai budurwar ta tari numfashinsa tace ni bana tsafi amma kusani wanda ya umarceku da zuwa nan kauyan shine ya sanar dani komai naku kuma zan taimakekune bisa wani alkawari dake tsakanina dashi bisa wani taimako da zaiyi min akan cika burina koda jin wannan batu sai jikin gimbiya yayi sanyi tayi shiru bata kara cewa komai ba nan take kyakkyawar budurwar ta kirawo wadansu yaranta mata su uku ta basu umarnin yadda za a tafiyar da komai ba tare da bata lokaciba matan suka risina suna masu amsa umarni daya daga cikin su ta dubeta tace ranki ya dade gimbiya yaya batun bakon ki dake can bayan gari koda jin wannan tambaya sai budurwar tayi murmushi tace duk abinda ya bukata ayi masa koda bana gari gama fadin hakan keda wuya sai ta juya ta nufi har cikin garin kauyan cikin hanzari yarima da bawa udez suka bi budurwar ita kuwa gimbiya musaira sai ta dan noke ta dubi daya daga cikin yaran nata tace me yasa naji kin kirata da suna gimbiya matar tayi murmushi tace ai sarkin garinmu kanin uwartane musaira ta gyada kai tace to menene sunan ta na asali budurwar tace sunanta Gimbiya Lasmin. Musaira ta tabe baki cikin alamun kishi ta kara gaba yar doguwar tafiya kadan sukayi suka iso gidan gimbiya lasmin a gaba daya kauyan babu wani gida mai girma da kawatuwa kamarsa, babban abinda ya daurewa su yarima kai shine duk inda suka ratsa a kauyan sai suga ana zubewa Gimbiya ana kwasar gaisuwa duk inda suka iske tsofaffi ko almajirai sai suga lasmin na ta fiddo kudi a jikinta tana rabamusu suna tay mata godiya kamar za suyi mata sujjada da isowarsu gidan nata sai ta wuce da su kai tsaye zuwa inda bargar dawakar take da shigarsu cikin bargar suka iske wadansu kosassun fararen dawakai guda hudu lasmin ta dubi udez da gimbiya musaira tace kowannan ku ya zabi doki guda daga cikin guda hudunnan ba tare da gardamar komai ba kowa sai dukkaninsu suka zaba nan da nan aka daurawa dawakan siddi har da guda dayan da ya rage kuma aka kawo jakunkunan guzuri guda hudu ko da ganin haka sai yarima ya dubi gimbiya lasmin cikin alamun rashin fahimta yace waishin kina nufin tare dake zamuyi wannan tafiya dajin wannan tambaya sai lasmin tayi murmushi tace ai dolene ma ayi wannan tafiyar tare dani saboda nice kadai nasan inda zamuga mahaifiyarka tabbas nasan garin da take amma bansan a inda zamu ganta ba duk da cewar sarkin yaki ya kwatan ta mini kamanninta abune mawuyaci na shaidata abu daya ne zai taimaka mana mu sameta muga irin sarkar wuyanka a wuyanta ka sani cewa dole sai na biku sannan zan iya cika nawa burin bamu da wani isashshen lokaci yanzu domin nan da cikar sa a biyu dakarun sarki zamaru masu farautarku zasu iya isowa garin idan kuma suka riskeku anan komai ya rushe koda jin wannan batu sai yarima gimbiya da bawa udex sukayi sauri suka kama dawakansu suka haye suka rataya jakunkunan guzirinsu a gadon bayansu itama lasmin sai tayi hakan ta wuce kan gaba suka bita a baya suna masu zaburar dawakansu da gudu kamar yadda gimbiya lasmin ta fada haka al amarin ya kasance. Wato suna barin kauyen da ta zarar sa a biyu da rabi sai ga rundunar dakarun sarki zamaru sun iso dauke da zanen fuskokin su yarima nan fa sukayi ta yawo a cikin kauyan kwararo kwararo lungu da sako suna nemansu amma saboda an ga su yarima tare da lasmin babu wanda ya amsa cewar ya gansu haka dai suka gaji da yawon nema suka hakura sai da su yarima suka shafe kwanaki biyar suna ratsa dazuzzuka kuma basa ya da zango face idan dare yayi da yammaci kwana suke iske wani babban birni da ake kira Darul Kushuf birnine babba wanda yafi birnin madinatul hashwar girma da kawatuwa suna shiga farkon garin suka gane cewa mulkin zalunci akeyi domin bayi suka gani maza da mata suna ta aikin bauta na gina wani dogon gida dakaru na tsaye a kansu duk wanda ya sare sai kaga an zabga masa wata murtukekiyar bulala mai kaurin gaske sai dai kaga bayan bawa ya kwaile jini na zuba yana ihu nan take su yarima suka kamu da tausayi da takaici cikin hanzari lasmin ta juya ta dubesu tace A cikin rada duk abinda ya faru kuji ku gani amma babu ruwanku da kowa da isowar su bakin kofar birnin sai dakaru suka tare su cikin hanzari gimbiya lasmin ta zuba hannu cikin aljihunta ta fiddo zinare dubu ta mikawa masu gadin kawai sai aka bude musu kofa suka kunna kai ciki ba tare da an caje suba don tabbatar da tsaro kai tsaye suka nufi cikin birnin lasmin nayi musu jagora kai da ganin yadda lasmin ke kutsawa dasu ta cikin lunguna kasan cewa ita yar gari ce haka kuma Al amin Guyson ma Dan garine wajan son kawo muku labarai na litattafan yaki, sai da sukayi tafiya ta a kallah rabin sa a sannan suka iso wani bakatafaren gida zaune a kofar gidan wani attajirine bisa wata kujera ta alfarma hadimai sun kewayeshi koda attajirin ya hango su gimbiya lasmin sun durfafeshi sai ya mike tsaye zumbur da sauri cikin matukar farin ciki ya nufosu da gudu har yana tuntube cikin girmamawa attajirin ya kamawa lasmin dokin ta ta sauka tana mai yi masa marhaba nan take aka kaisu masauki suka zauna suka huta kuma suka ci suka sha bayan sun huta attajirin ya shigo babban falon dasu gimbiya lasmin ke zaune ya zuba a gabanta wanwar yana mai tankwashe kafafunsa yace ranki ya dade yau kuma wace bukata kikazo da ita kin sani cewa a shirye nake na biya miki ita koda kuwa zan rasa rayuwata a dalilin haka sa adda lasmin taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace na zone neman wata bakuwar mace a garinnan wacce a halin yanzu ta shekara ashirin da biyar anan tana rayuwa kuma ta zone daga birnin madinatul hashwar sunanta shamslat ta kasance matar marigayi sarki hisham kuma gudun hijira tayi daga can birnin don tserar da rayuwarta koda jin wannan batu sai attajirin yayi shiru yana jinjina kai gami da tunani har izuwa tsawon yan dakiku sannan ya dago kai yace ranki ya dade gano wannan matar sarki acikin wannan babban birni namu abune mai wuyar gaske tunda ma babu tabbacin tana nan a raye inda ace akwai wata shaida da za a iya shaidata to da bamu da matsala caraf sai yarima yace akwai shaida tana da wata irin sarka irin wannan dake wuyana nan take yarima ya zaro sarkar daga cikin wuyansa sarkace wacce aka yita da zallan karfen lu u lu u kyan hatimine na gidan sarautar birnin madinatul hashwar a jikinta koda ganin wannan sarkar sai attajirin ya kurawa sarkar idanu ya fada kogin tunani daga can sai ya dago kai yace na taba ganin wata baiwa da irin wannan sarka a can gonar sarki dake bayan gari kimanin shekaru takwas baya tana aikin bauta a wannan lokaci wani badakare ya cafi sarkar a wuyanta ya fisgeta saboda tsananin fusatar da tayi sai ta gabza masa wawan naushi ya zube kasa sumamme nan fa dakaru suka rufeta da duka suna neman sumar da ita nine na ceceta na basu kudi suka kyaleta koda na tambayeta matsayin sarkar a wajanta sai tace dani gwara a raba ta da ranta akan a rabata da wannan sarka Al amin Ahmed Nake Guyson Kenan A square koda jin wannan labari sai yarima ya rugo ga attajirin yace yanzu a ina kake ganin zamu iya ganin wannan mata attajiri yace ai duk bawan da aka kaishi bauta wannan gidan gona ta sarki sai dai gawarsa ta fito abu daya ne zai iya sawa a fito da ita ba komai bane face kudi a garin nan kudi yafi komai daraja shi kansa sarkinmu ana siyan sa da kudi koda jin haka sai farin ciki ya kama su yarima gimbiya lasmin tace gobe da safe zaka kaimu wannan gidan gona ta sarkinku bana son mu baiyana bukatarmu kai tsaye kawai mu siye dukkanin dakarun dake aiki a gidan gonar mu samu izinin ganin gaba dayan bayin dake gidan da zarar mun sami damar hakan kai yarima zaka fito da sarkar wuyanka fili yadda matar zata iya gani Attajirin yayi murmushi yace tabbas wannan itace kadai hikimar da zamuyi mukai ga nasara kashe gari kuwa tun kafin alfijir ya keto su gimbiya lasmin suka yi shiri attajiri yayi musu jagora suka durfafi gonar sarki da isarsu aka kirawo shugaban dakarun dake gidan gonar tare da duk kan yaransa tashin farko sai lasmin ta kebe da shugaban ta bashi kyautar dinare dubu goma sannan ta bashi wadansu dinaren dubu uku tace ya rabawa yaransa saboda murna da mamaki sai jikin shugaban ya kama karkarwa ya zube kasa yana godiya lasmin na fada masa bukatarsu ya amince nan take aka bude musu gidan gonar suka shiga sannan aka tara gaba dayan bayin a gabansu nan take yarima ya fiddo da sarkarsa waje tana reto akan kirjinsa ya shiga duba bayin a lokacin da suka jeru a kan sahu amma sai ya nufi bangaren da aka tara mata zallah ya kama kewayasu sai da ya rage saura sau uku kacal ya gama kewayasu sai ya tsaya cak a lokacin da ya gifta wata babbar mace wadda yaga ta kura masa idanu ko kiftawa batayi nan da nan idanuwa suka ciko da kwallah jikinta ya kama tsuma amma kuma bakinta na karkarwa ta kasa magana yarima ya dawo da baya ya tsaya cak a gabanta matar daf da daf yadda suna iya jin numfashin juna suka ci gaba da kallon juna kawai daga can sai matar tayi wuf ta bude rigarta saiga sarka irin ta yarima a kirjinta kawai sai ta rungume yarima ta fashe da kukan farin ciki tana mai cewa tabbas na sani cewa indai ina raye sai na sadu da Kai ya dana yau shekara ashirin da biyar kenan ina begenka a zuciyata kuma kullum ina mafarkinka a barcina ko yanzu na mutu burina ya cika bani da sauran takaici koda jin wannan batu sai yarima ya fashe da matsanancin kuka yana mai rungume ta a kirjinsa yace nima haka na kasance a cikin begenki da son ganinki tun da naji labarinki ban san dadin uwa ta jini ba amma yanzu da na sameki zan sanshi nan take kowa dake wannan wuri ya kamu da tausayin yarima da mahaifiyar sa sakamakon jin irin kalaman da suke furtawa duk tsananin rashin imani na dakaru dake tsaron wannan gona sai gashi wasunsu na zubar da hawaye wasunsu idanuwansu sun ciko da kwallah nan take shugaban dakaru ya dubi yarima yace yakai wannan saurayi ma abocin sadaukantaka kayi sani cewa bawa baya fita daga gidannan idan ya shigo idan bawa daya ya bace indai ba gawa ya zamo ba ne da dakarun zamu iya rasa rayuwarmu amma domin mu hada wannan da da mahaifiyarsa wadanda suka rasa juna tsawon shekaru ashirin da biyar da sadaukar da rayukanmu koda jin wannan batu sai gidan gonar ya rude da shewa shugaban dakarun ya daga hannu akayi tsir sannan yace kai a yau mun sallami gaba dayan bayin gidannan mun basu yancinsu munma duk tarwatsewa zamuyi yana gama fadin haka sai aka bude gidan gonar bayi suka fice suna ihu da murnar samun yanci wasu bayinma saboda farin ciki sai suka zube kasa suna suna kuka ba tare da wani bata lokaci ba sai yarima ya dora mahaifiyarsa akan dokinsa lasmin munaira da bawa udez suka rufa masa baya suka juyo da baya izuwa hanyar da zata kaisu wani birnin daban don kada sarkin wannan gari ya sami wannan labari ya turo a kamasu cikin tsananin farin ciki sukayi ta tafiya ba sassauci har rana ta fadi a sannan ne suka yada zango a bakin wata korama domin su kwana a wurin in yaso kashe gari ya soma duhu amma idanu na shaida komai bayan sun daure dawakansu sai suka gangaro gaban wannan korama domin su sha ruwa kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaji sukuwar dawakai gua biyu daga cikin duhuwar daji an durfafosu kafin suyi wani yunkuri sai ga mahayan biyu sun riskesu sunyi turjiya a gaban su nan fa aka tsaya ana kallon kallo ba wadansu bane wadannan mahaya face sarki zamaru da boka hizainu nan take hankalin mahaifiyar yarima ya dugunzuma ta fashe da matsanancin kuka shi kuwa sarki zamaru sai ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya yace ke tsohuwar banza ai yanzu kika fara kuka kuma ba zaki daina ba har izuwa karshen kwanakinki na duni . A nan Littafin Kisan Gillah 3 yazo karshe Marubucin Littafin Yace Mu hadu a Littafi Na hudu Domin jin cigaban wannan labari amma kafin nan ku meye ra ayinku dangane da wannan haduwar da akayi shin suwaye zasu sami Galaba nidai nacee,...... Sai naji daga gareku , nidinne dai Al amin Ahmed Misau Guyson ko AA Misau nake cewa mu zama lafiy KISAN GILLA 4 Littafi na hudu Na Abdulaziz sani madakin gini Ebook creator:- Shuraih Usman 99% Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini KISAN GILLA Littafi Na Hudu (4) mPart A. . . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... Kafin sarki zamaru yagama rufebakinsa saiyaji wata murya daga bayansu tadaka masa tsawa cikin hanzari shida boka hizainu suka waiga baya dansuga kowaye bawanibane sukayi arba dashiba face sarkin yaki amzad bisa wani gabjejen tsuntsu asama cikin iska yayi shigar yaki amzad na sanye dabaki sulke yarataya wata shimfidediyar takobi agadon bayansa akuibins cinyoyinsa biyu wadansu gajerun adduna ne guda biyu rike ahannunsa nahagu wata farar sandace sandce siririya anyiwa marikanta siffar kwarangwal nakan bil,adama komai dayake jikinsa bakine hatta takalmansa da garkuwarsa kuwa shikansa sarki zamaru saidaya dan firgita daganin sarkin yaki amzad acikin wannan gagarumar shirin yaki don baitaba ganin yayi irintaba duk irin yake yaken dayake fita nanfa aka fara kanlan kallo shamilat da sarki zamaru suka kurawa juna ido tanamaida dakamada harara cikin tsananin kiyayya saboda sanin cewar shine yakashe mata miji yarabata da danta kuma ya jefa rayuwarta cikin kunci dawuya tsawon shekaru ashirin dabiyar shima sai yarinka yiwa sarki zamaru irin wannan kallon har jikinsa yasoma tsuma yarinka kamar yazare takobi ya afkamasa shidai sarki zamaru babu wanda yake jin haushi kamar sarkin yaki amzad domin tunda ya kura masa ido ko giftawa baya yi kuma saboda tsananin kiyayya a zuci sai da fuskar sarki zamaru ta rika yin gatsine bayan anyi wannan kallon kallon na tsawon yan dakiku sai sarki zamaru da boka hizairu suka dubi junansu suka bushe da dariyar mugunta sannan boka hizainu ya dubi sarkin yaki amzad yace kai karamin kwaro kayi wani cewa ai tunda ka kasa hanamu ganin bayan mai gidanka marigayi sarki hisham to kaima ba zaka gagaremu ba ina mai tabbatar maka da cewar anan wajen zamu gama da kai sannan mu gama da wadannan yan tsakin na rantse da darajar tsafi a halin yanzu babu wani mahaluki a doron kasa walau mutum ko aljan wanda ya isa ya hanamu kammala cika babban burin mu a rayuwa, koda boka hizainu yazo nan a zancensa sai sarkin yaki Ya numfasa yace kai tsohon azzamuli maci amana kuma butulu kayi sani cewar ramin karya kurarre ne kuma komai nisan jifa kasa zai fado ina mai tabbatar maka da cewar kafin nabar wannan duniya sai na tabbatar da cewar wannan yaron ya dauki fansar ran mahaifinsa a kanku kuma sai ya tarwatsa wannan burin naku na banza wanda dai dai yake da mafarki gama fadin haka ke da wuya sai boka amzad ya zunguri cikin tsuntsun da yake zaune akai take tsuntsun yazo gaban su yarima ya sauka wato ya fuskanci su sarki zamaru sannan ya dubi bawa udez da shamilat yace musu ku koma can jikin dotsen dake bayan bishiyar can ku zama yan kallo kada ku kuskura ku motsa daga wajen da kuke duk bala 'in da za a yi kada ku firgita kuyi yunkurin guduwa domin kuwa yunkurin yin hakan zaku fada hannun wadan nan makiyan namu da jin wannan batu sai bawa udex da shamilat suka bi umarnin suka ruga can wajen da sarkin yaki amzad ya umarcesu jikinsu yana rawa suka waiga cikin alamun matukar tsoro bayan sun isa jikin bishiyar sai sarkin yaki amzad ya dubi lasmin yace Ranki ya dade ga wanda kika shafe shekaru goma kina farautarsa wato makashin mahaifinki gashinan a gabanki wato sarki zamaru kamar yadda na baki labari a baya cewar wanda ya kashe mahaifinki na jikinsa ne kuma amininsa wanda ya yarda dashi fiye da kowa a harkokin kasuwancinsa ki sani cewar domin ya danne dukiyarsa ne kimanin dinare miliyan dubu casa'in da biyar ya kashe shi har izuwa yanzu babu wanda yasan komai akan lamarin face ni kadai kuma ina da cikakkiyar shaida har guda biyu akan kisan gillan da yayi wa mahaifinki da kuma shaidar kudin da ya bashi har da lokacin daya bashi da wurin da suka hadu domin Al amin Ahmed Misau, gabatar da wani babban kasuwanci a birnin sin ranki ya dade kinga kenan yanzu abu biyu ki ke nema a wajen sarki zamaru na farko kina neman kudinki da kika gada a wajan mahaifinki sannan kuma kina neman fansar ran mahaifinki don haka babu abun bukatar mu fara kashe sarki zamaru a yanzu har sai kin fara karbar wannan dukiyar taki abinda yanzu nake da bukata mu kamashi a raye mu tsare shi a wajen mu muyi ta gana masa azaba har sai ya fadi inda wannan dukiyar take daga nan sai mu farwa karagarsa shi kuma wannan tsohon azzalumin boka hizainu dake tare da shi yanzu take zamu maida labarinsa tarihi koda sarkin yaki amzad yazo nan a jawabinsa sai sarki zamaru tare da bokan hizainu suka bushe da dariyar mugunta a lokaci guda tsawon yan dakiku suna dariyar sannan sarki zamaru ya turbune fuskarsa yace Ai inda ba kasa a nan ake gardamar kokawa kawai ku zo muyita a kare a nan domin banga amfanin hutun jaki da kaya ba koda jin wannan batu sai sarkin yaki amzad ya dubi yarima da nashmirat yace ni ku barni da boka hizainu ku kuma ku tari sarki zamaru ke kuma gimbiya sai dai ki zama yar kallo kuma kada ki kuskura kice zaki saka hannunki a cikin wannan gumurzu da za ayi komai rintsi da tsanani kada ki ce zaki yaki mahaifinki saboda na Tabbatar da cewar shima ba zai taba cutar dake ba ko rayuwarki koda sarkin yaki amzad yazo nan a zancensa sai idanun gimbiya nasmirat suka ciko da kwalla har hawaye ya subuto mata kawai sai ta dubi amzad tace bazan iya kallon abinda zai faru ba a nan zanso na bar wajennan in da hali sarkin yaki ya numfasa yace ai wannan ba matsala bane nan take tsuntsun amzad ya sauko bisa turba ya sauko

Chapter 5 of 8