Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
daga kan tsuntsun ya dubi nasmirat yace maza ki hau wannan tsuntsun nawa zai kaiki maboyata inda zaki samu nutsuwa da kwanciyar hankali lallai idan muka gama wannan yakin zamu riskeki a can kidi duk abinda ya faru ba tare da wata gardama ba kuwa sai gimbiya nasmirat ta haye kan wannan tsuntsun ya tashi da ita sama yana mai juyawa da baya, A dai dai wannan lokacin ne gimbiya nasmirat ta juyo ta hada idanu da mahaifinta sarki zamaru taga fuskarsa a murtuke take babu ko annuri koda yaga wannan tsuntsun zai tafi da ita sai ya kwalla mata kira yace mata, kawai sai gimbiya nasmirat ta kauda kai da fuskarta ga barin kallonsa a lokacin da hawaye ya sake subuto mata a karo na biyu nan da nan tsuntsun ya luluka da ita cikin sararin gajimare ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen, faruwar hakan ke da wuya sai sarki zamaru ya zare takobinsa guda biyu yana mai saukowa kasa daga kan dokinsa ya tunkari yarima da lasmin gadan gadan boka hizainu da sarkin yaki amzad kuwa sai suka taho ga juna kowannansu fuskarsa na yin gatsine saboda tsananin fishi gami da kiyayyar juna koda ya rage sauran baifi taku shida ba su hadu sai boka hizainu ya rikide ya zama wata shirgegiyar kada mai tsawo da kaurin gaske a iya yawon duniyar amzad bai taba ganin kada mai girman taba koda ganin haka sai shima amzad ya rikide ya zama wata narkekiyar macijiya wacce kaurinta da tsawon ta ya ninka na kadar sau uku koda ganin haka sai nima Al amin da nake typing na rikide na zama zaki domin cigaba da ganin wannan gumurzu Ai kuwa sai kadan ya nufi cikin wannan korama itama sai tabi kadan suna haduwa a cikin koramar suka kacame da masifaffen fada Al amarin yarima da lasmin kuwa koda suka ga sarki zamaru ya zare takobinsa guda biyu ya durfafo su sai suma suka zare na su takubban suka tsaya cak a inda suke suna jiran karasowarsa a nan ne yarima ya dubi lasmin yace ranki ya dade kiyi amfani da duk irin salon yakin da kikaga ina yi domin ta haka ne kadai za mu iya kare kanmu daga sharrin wannan tsohon makiyin namu lasmin tace idan kuma shi yazdo da wani salon wanda yafi namu yarima yace ai duk irin salon da yazo mana dashi muma shi zamuyi kinsan na samu horo a wajen sarkin yaki kuma babu salon da ban iya ba lasmin ta danyi guntun murmushi tace masa, ashe malamin mu daya ne domin nima a wajen sarkin yaki amzad na samu horona ina dai haka ne bamu da matsala amma fa ka sani wannan mutumin ba karamin annoba bane a tare da mu kuma shirinsa ya wuce duk yadda muke zato kawai dai muyi iya yinmu wajen ganin mun gama dashi kafin yarima ya budi baki ya kara magana sai kawai suka hango sarki zamaru a sama kamar an harboshi kafin suyi wani abu ya daki kirajensu da kafafunsa guda biyu saboda karfin dukan sai da kowannansu yayi sama suka yi baya suka fado kasa tim bisa gadon bayansu sai gashi ko wannansu ya furzar da jini daga cikin bakinsa A WANNAN LOKACI TUNI SARKI zamaru ya dira a kasa bisa kafafunsa biyu yana mai kura musu idanu kawai sai sarki zamaru ya bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa yace yanzu a haka ne kuke tunanin zaku iya samun galaba a kaina? Na rantse da darajar karagata ko shi malamin naku ne ya kusance ni sai dai a dauki buzunsa domin shirina yafi nasa ni murucin kan dutse ne wanda ban fito ba sai dana shirya babu wani makiyana wanda banyi tanadin ganin bayan sa ba, Yanzu take anan zan yi muku kisan gilla irin wanda ba'a taba yiwa wani ba a wannan nahiyar tamu koda jin wannan batu sai lasmin da yarima suka dubi junansu kawai sai suka yi wata irin tasowa sama daga tsaye kamar an saki majajjawa kafin sarki zamaru ya sake yin wani yunkuri sun dako tsalle sama zuwa kasa ai kuwa sai yarima ya daki fuskar shi da kafarsa ita kuma lasmin ta daki kirjinsa Al amin Ahmed Misau, da kafafunta guda biyu saboda karfin dukan sai da sarki zamaru yayi baya kamar an janye shi da majajjawa, bayan shi ya gwaru da jikin wata bishiya ya fado kasa a galabaice yana mai tofar da gudan jini daga bakinsa amman hakan bai saka ya yadda takubban da suke hannunsa ba kawai sai ya mike tsaye zumbur kamar babu abinda ya same shi yana mai gyara tsayuwarsa, da ganin haka sai suma suka rugo izuwa kansa aka kacame da sabon azababben yaki ya zamana cewar suna kai masa sara da suka cikin tsananin zafin nama shima yana maida martanin sai dai kaji karar haduwar takubbansu tamkar ana dukan karafa a makera, Al amin Misau wani lokacin har tartsatsin wuta ke tashi gami da hayaki sakamakon gogaiyar takubban uku babu abain da zai baiwa mutum tsoro a cikin wannan yakin face yadda jaruman uku suke yaki da matukar zafin nama kuma da dukkan karfinsu cikin burin Gaggauta ganin bayan junansu, kai da ganin yanayin gumurzun kasan cewar duk wanda yayi kuskure kadan daga cikinsu tasa ta kare kamar yadda ake yin wannan mummunan artabu a tsakanin su sarki zamaru dasu yarima, haka ake yinsa tsakanin amzad da boka hizainu a cikin wannan korama, duk sa'ar da wannan kadar ta samu sa'ar laftar jikin wannan macijiyar da bakinta idan ta gatsa da hakoranta sai taji kamar karfe ta gatsa ko alamar kwarzane babu haka itama katuwar macijiyar idan ta samu nasarar fara hadiye kadan sai taji kamar wuta take hadiya don haka ba shiri take amayar da ita, Al amin Ahmed Misau, idan kuma maciyar ta samu nasarar kanannade jikin kadan da nufin ta matse shi ta karairaya dukkanin kasusuwan jikinsa sai taji ta kasa domin ji take kamar dutsen lu'u lu'u take matsewa wohoho tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da sukace bala'i ba a sa masa rana kuma duk mai rabon shan duka sai ya shata sai da wannan kada da macijiya suka shafe sama da sa'a uku suna kokawa da birgima gami da cizon junansu a cikin wannan korama wani lokacin ma idan suka rukunkume jikin juna sai kaga sun nutse izuwa kasan koramar sun sake tasowa sama suna hargitsa ruwan koramar gaba dayansu tamkar zasu karar dashi, wuya mai saka dole kanwar naki lokacin da macijiyar da kadan sukaji sun galabaita ainun domin sun sha ruwa sun gaji kuma jiki ya jigata sai suka saki junansu ba shiri suka fado daga cikin koramar kowannansu ya koma gefe daya a sannan ne kuma kowanne ya rikida zuwa ainihin halittar sa ta bil'adama gashi dukkan su suna haki kamar ransu zai fita ko mikewa tsaye basa iya yi a haka suka tsaya suna kallon kallon juna kamar zasu cinye kansu har izuwa kimanin dakika dari da sittin sannan suka mike tsaye atare suna yin murmushin mugunta...KISAN GILLA Littafi Na Hudu (4) Part B. . . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... SANNAN SUKA MIKE TSAYE A TARE SUNA MASU YIN MURMUSHIN MUGUNTA boka hizainu ya dubi sarkin yaki Amzad yace tabbas ka samu babban shiri , gumurzun da muke yi yanzu ya tabbatar min da cewar ba zamu iya hallaka junan mu da karfin sihirin tsafi, don haka yanzu lokaci yayi da za mu jarraba juna da karfin damtse, daman kai kadai ne jarumin da ban taba yin gumurzu da shi ba gaba daya a wannan nahiyar tamu daga cikin fitattun jaruman da suka yi shuhura sa ar da boka hizinu yazo nan a jawabinsa sai sarkin yaki amzad ya kamu da mamaki kuma ya dubeshi cikin alamun rashin yadda yace yaushe ne ka fafata da gaba daya fitattun jaruman wannan nahiyar tamu ? Koda jin wannan batu sai boka hizainu ya bushe da dariyar mugunta sannan yace, ashe ka manta da jarumi mai bakar hular karfe kenan wanda ya hanaka amsar kambun gasar jarumta shekaru bakwai da suka gabata a can birnin shamshal ? Koda jin wannan tambayar sai mamaki ya kara turnuke sarkin yaki amzad yana mai nuna hizainu da dan yatsansa cikin alamun kaduwa yace daman kaine wannan jarumin mai bakar hular karfe wanda har aka gama gasar babu wanda yaga fuskarshi, boka hizainu ya gyada kai yace tabbas nine wannan jarumin kuma ka sani cewar ragas muka yi ni da kai a wannan gasar babu wanda ya tafi da wannan kambu abinda nake nufi bamuyi yaki gaba da gaba ba shine bamuyi yaki ido na kallon ido ba sai yanzu za muyi , lallai yau ne zamu fidda raini a tsakanin mu gama fadin haka keda wuya sai boka hizainu ya mike tsaye yana mai zare takobinsa kuma ya buda hannayansa yana mai kallon sarkin yaki Amzad yace maza ka mike mu fafata ba tare da wata gardama ba sai sarkin yaki amzad ya mike tsaye shima ya zare tasa takobin yana mai gyara tsayuwarsa sannan ya dubi boka hizainu yace tabbas ka burgeni daya zamana cewar baka fito ba sai daka shirya ai ba a samun duniya a banza sai dai kash ! Baka kama turba mai kyau ba domin shi zalunci baya daurewa ka tambayi masana tun daga farkon wannan duniyar kawo yanzu babu wani azzalumin sarki ko boka ko kuma jarumin da dauwama a doron kasa sai dai kawai yaci zamaninsa ya shude kamar bai taba wanzuwa ba, Al amin Ahmed Misau Guyson, amzad na gama fadin hakan sai ya afkawa boka hizainu suka kacame da sabon masifaffen yaki wohoho ! Idan tsohon hannu ya hadu da takwaransa dolene aga tuggu, wayo gamai da makircin yaki kuma dolene aga kwarewa jajurcewa da sanin dabarun salon yaki kala uku ma ana sai gashi suna kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama gami da naushi da bugu hannu da kafa da kuma yin tsalle tsalle suna yin alkafira suna shallake juna tamkar sun kasance tsuntsaye masu fuka fukai inda ace akwai yan kallo lokacin da ake yin wannan bakin gumurzun to da ihunsu da shewarsu ne zai cika dajin gaba daya domin basu taba ganin jarumta da jarumtaka irin wannan ba bugu da kari duk wanda ya tsaya yana kallon wannan fafatawa to ba zai taba samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba saboda bala in dake faruwa a wajen zai iya samunsa kuma ya sami duk wata halitta mai rai dake wajen kamar yadda ake wannan yakin a bangaren sarkin yaki amzad da boka hizainu haka abin ya kasance a bangaren sarki zamaru dasu yarima amman koda aka shafe awa guda ana gumurzu sai labari yasha banban komai ya sauya, ba komai ne ya haddasa haka ba face alamar gajiya a jikinsu amma shi sarki zamaru sai ya zamana sannan ne ma yake jin sabon karfi a jikinsa, hakan ne ya tabbatar musu da cewar ya fisu samun horo a jikinsa na jarumta da kuma juriya da dadewa ana gumurzu Al amarin daya matukar dugunzuma hankalin yarima kenan domin ya tabbatar idan har aka ci gaba da wannan gumurzun a haka har tsawon wata rabin Sa'ar to koda bai samu nasara akan su ba to zai yi musu babbar illah. Nan fa yarima ya soma tunanin dabarar da ya kamata suyi dan ceto kansu da kuma samun nasara akan makiyinsu yana cikin wannan tunanin ne sarki zamaru ya shammacesu yayi wata irin katantanwa a tsakiyarsu tamkar an murza mazari, ai kuwa sai yayi nasarar yankan lasmin a cinyarta kuma ya yanki yarima a kafadarsa ta hadu duka su biyun sai suka kwala ihu sakamakon zafi da zogin da suka ji a lokacin da jini yayi feshi daga cikin jikinsu koda sarki zamaru yaga ya samu wannan nasarar sai ya kara yunkurawa cikin zafin nama da shammace ya kawowa yarima suka da takobi a ciki, ita kuma lasmin ya kai mata sukar a gadon bayanta, koda lasmin taga takobin zata soke yarima sai ta yunkura da dukkan karfinta tasha gaban yarima ai kuwa sai tsinin takobin ya soketa a saman kafadarta ta baya daya takobin kuma ta soketa a gadon bayanta ya zamana kenan ta kubutar da rayuwar yarima, kawai sai ta durkusa kasa cikin mugun yanayi mai kama da suma, ganin yanayin data shiga ne ya saka yarima ya kurma uban ihu mai firgitarwa ya daka tsalle sama ya doki kirjin sarki zamaru da kafafunsa biyu saboda karfin dukan sai da sarki zamaru yayi tsalle sama da baya tamkar an janye shi da kugiya ya fadi can gefe daya, Al amin Ahmed Misau sunana kenan, nake typing, kafin ya mike tsaye sai yaga wata guguwa ta lullube yarima da lasmin tayi sama dasu sun luluka, kafin kiftawar ido sun bace bat, koda sarki zamaru ya juya ya duba wajen da ake gumurzu tsakanin boka hizainu da Amzad sai yaga babu sarkin yaki sai boka hizainu yana ta tsafe tsafensa don yaga inda Amzad yake amma abu ya gagara, koda ganin haka sai sarki zamaru ya takarkare ya kurma uban ihu cikin tsananin bakin ciki. Wannan shine abinda ya faru tsakanin su sarkin yaki Amzad da kuma sarki zamaru a lokacin da suka kawo musu farmaki na farko a cikin farautar da suke yi musu ++ ++ ++ ++ +++ AL AMARIN GIMBIYA Musaira kuwa lokacin da ta hau wannan tsuntsun na sarkin yaki Amzad ya tashi da ita sama ya luluka a cikin gajimare sai yayi ta tsala gudu da ita, suka yi ta keta gajimare ba sassauci har tsawon kimanin rabin sa'a kawai sai gani tayi sun iso wani babban daji mai tarin ni'ima , akwai bishiyoyi kala kala gami da tarin 'ya 'yan itatuwa naci iri iri koramai kuwa da koguna ga sunan birjik gami da manyan duwatsu da tsaunuka Kwatsam sai Musaira ta hango wani babban gida ginin dutse da dutse a tsakiyar dajin shi dai wannan gidan anyi masa gini na kawa wanda komai isar mai mulki ko attajiri sai an burgeshi, kai tsaye tsuntsun ya tunkari kofar wannan gidan ya dirgo kasa ya sauka bisa turba da farko sai musaira ta firgita bisa ganin wannan katon gwaggwan biri kikam a kofar gidan, tunda tazo duniya bata taba ganin gwaggwan biri mai girman wannan ba domin tsawon shi yakai kamu talatin da uku kuma fadin kirjinsa yakai kamu shida, can sai ta tuna ai sarkin yaki Amzad ne ya saka aka kawota wannan gidan dan haka sai taji hankalinta ya kwanta ta cire dukkan tsoro daga cikin zuciyarta, ba tare da wata fargaba ba sai musaira ta yunkura domin ta sauko kasa daga kan tsuntsun da take zaune amman sai ta kasa saboda nisan kasa daga kan tsuntsun idan tace zata dirko zata iya karyewa ko kuma ta samu targade, bisa ga mamaki sai taga wannan katon gwaggwan birin ya tunkarota, da zuwan shi gaban wannan tsuntsu sai ya mika hannunshi biyu ya kamo kafadun musaira ya daukota cak ya sauketa kasa a hankali sannan ya wuce gaba izuwa cikin wannan gidan tana biye dashi. Gidan yana da zurfi sosai kuma Al amin Ahmed Misau saida suka keta ta cikin fadoji biyar sannan suka iso wani babban falo wanda ya kawatu ainun duk irin kawar da ake shirya a gidan sarautar sarki zamaru sai gashi ta zama yar kauye a cikin wannan gidan domin kawar ta nunka ta gidansu sai uku nan take musaira tayi arba da abinda yayi tsananin kadata ba kowa ta gani ba face Kimaratu tana tsaye a wajen wani faffadan teburi wanda ke cike da kwanukan abinci kala kala kamshin abincin ya cika falon gaba daya da isowar gwagwan birin tare da gimbiya musaira sai birin ya risina ga kimaratu sannan ya juya ya tafi ya barsu su biyu kacal a tsaye, kimaratu ta risina ga musaira cikin biyayya ta kwashi gaisuwa sannan tace barka da zuwa ya shugabata ga kujera ki zauna ki fara cin abinci kafin su sarkin yaki su dawo sa ar da taji wannan batun sai ta dubi kimaratu cikin tsananin mamaki tace mata, ya akayi kika tabbatar da cewar zasu dawo nan a raye ? Ni kaina ban dauka zan zo nan wajen a raye ba, kuma yanzu babu wanda yasan halin da suke ciki tund asarki zamaru da boka hizainu sun tare su koda jin wannan batun sai kimaratu ta bushe da dariya al amarin daya kara baiwa musaira mamaki kenan, maimakon ta kara bata amsa sai ta kama hannun gimbiya musaira ta jata izuwa kan kujera ta zaunar da ita ta zuba mata abinci tace mata, ya shugabata ki soma cin abinci domin ki samu nutsuwa sannan sai muyi hira cikin kwanciyar hankali ba tare da wata gardama ba sai gimbiya musaira ta fara cin abinci itama kimaratu sai ta zauna ta zubawa kanta abinci ta fara ci tsawon yan dakiku suna cin abincin dayansu baice uffan ba daga can sai gimbiya musaira ta ajiye cokalin ta daina cin abinci koda kimaratu taga haka sai ta ajiye nata cokalin ta dubeta tace mata, shugabata tunanin me kike yi ne ? Musaira ta girgiza kai tace. Nayi babban kuskure dana baro su yarima a wancan dajin kamata ya yi na tsaya ayi komai a kan idanuna koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke kimaratu tace kekuwa menene dalilin daya sa kika ce kinyi kuskure da kika baro su yarima a can dajin musaira tace Akwai abinda nake zargi nake son na tabbatar dashi, kiyi hakuri ba zan iya sanar dake wannan al amarin ba, amman idan lokacin daya dace ki sani ya yi zaki sani koda jin wannan batu sai kimaratu ta kasa gane abinda musaira ke nufi don haka sai ta sake bude baki da nufin tayi mata wata tambayar amman sai musaira ta tari numfashinta da cewar wai shin idan banda biri babu kowa a cikin wannan katon gidan ? Kimaratu tace A'a akwai hadimai, amman ba a ganinsu sai idan lokacin yin aikinsu yayi da zarar sun gama za a neme su a rasa, shi kuma wannan birin duk da rana da dare yana nan baya gusawa ko ina saboda shine mai gadi, musaira tayi Ajiyar zuciya tace,,,, Nidai hankalina bai kwanta da zaman mu Anan ba saboda na fahimci shirin mahaifina dana boka hizainu ya wuce tunanin sarkin yaki Amzad domin kuwa zasu iya kawo mana hari har nan din a ko yaushe, ke ni yanzu ma zuciyata bugawa take yi da karfi saboda tsoron abinda ka iya faruwa ga su yarima , kafin musaira ta gama rufe bakinta sai sukaji an turo kofar falon cikin kaduwa da firgici suka waiga domin suga ko su waye suka turo wannan kofar..KISAN GILLA Littafi Na Hudu (4) Part C. . . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... CIKIN KADUWA DA FIRGICI SUKA WAIGA SAI SUKA GA ASHE SARKIN YAKI AMZAD NE SUKE SHIGOWA, cikin matukar farin ciki musaira da kimaratu suka mike zumbur suka ruga zuwa garesu, suka tarye su amman koda suka hango yarima a can baya goye da gimbiya lasmin ga rauni a kafadarta kuma tana cikin wani irin mugun hali mai kama da suma sai hankalinsu ya dugunzuma cikin hanzari amzad ya kai yarima cikin wani dakin barci aka kwantar da lasmin bisa wani shamfidadden gado na Alfarma. Take Amzad ya tafa hannun sa sai ga wata budurwa Aljana yace Dunaila maza ki ceto rayuwar gimbiya ki sani cewar sarki zamaru ne ya soketa da takobinsa a kafada da gadon bayanta koda jin haka sai Dunaila ta dubi raunikan da sauri sannan ta girgiza kai cikin alamun damuwa tace hakika rayuwar lasmin na cikin mugun hatsari, zan iya yi mata magani ta samu sauki na tsawon kwanaki bakwai kacal amman ciwon zai kuma dawowa ya zama ajalinta farat daya koda jin wannan batun sai hankalin kowa ya dugunzuma har dani kaina Al amin Misau Amzad ya kama kafadun Dunaila ya girgiza kuma ya dubeta cikin daga murya yace duk yadda za ayi ki ceto rayuwarta in banda haka ina amfanin ki na uwar likitocin aljanu, ki tuna fa ke yar gado ce, kakan kakanki ma har ya bar duniya ba a sami kamarsa ba cikin likitocin aljanu, Dunaila ta gyada kai gami da ajiyar numfashi sannan tace duk abinda ka fada gaskiya ne hanya daya za a bi idan ana son ceto rauuwar lasmin dole a tsoma wadan nan takubban guda biyu wadan da sarki zamaru ya soketa da su a cikin ruwan tsumin tsafinsa a debo tsumin a baiwa lasmin tasha, wannan shine kadai makarin wannan dafin dake jikin takobin, wanda a halin yanzu dafin ya shiga cikin jinin jikinta koda Aljana Dunaila ta zo nan a jawabinta sai hankalin kowa ya sake dugunzuma musamman hankalin bawa udez domin komawa yayi gefe daya ya zauna ya fara kuka nan fa aka yi jugun jugun ana tunani da nazarin al amarin har izuwa tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba, zuwa can dunaila ta dubi yarima tace masa, ya aka yi sarki zamaru ya soki lasmin da takubba biyu a lokaci guda alhalin kana tayata yakarsa ? Yarima yace ai a lokacin ni yake so ya kashe shine tasha gabana don ceton rayuwata, koda jin haka sai musaira tace akan wane dalili lasmin zata sallama rayuwarta don ceton taka rayuwar alhalin bata kasance yar uwarka ba, hasali ma yau kwanaki kadan da haduwarku da juna? Koda jin wannan batun sai kowa ya kurawa musaira idanu nan take taji kunya ta kamata, don haka sai ta sunkuyar da kanta kasa bata kara cewa komai ba, nan take Dunaila ta hada wasu Al amin Ahmed Misau, magunguna aka durawa lasmin a baki tasha kuma aka shafa mata shi akan raunikan biyu gama haka ke da wuya sai ta dawo cikin hayyacinta har ta iya buda idanunta, koda ta hada ido da yarima sai ta kama murmushin farin ciki, ita kuwa gimbiya musaira sai taji kishi ya turnuke ta amma sai ta dake bata nuna kishin nata ba, dunaila ta dubi sarkin yaki Amzad tace to ni zan tafi amma ku tabbatar da cewar kunje kun sato wadan nan takubban biyu dake hannun sarki zamaru kunje kun tsomasu a cikin wannan ruwan na tsumin tsafinsa kun debe shi kun baiwa lasmin tasha kafin cikar kwanaki bakwai masu zuwa don kashe dafin dake cikin jikinta, nasan kuna tunanin yadda zaku iya samun wannan nasara, zan baku shawara guda biyu ku nemi mutum biyu wadan da suka san sirrin gidan sarautar tsawon shekaru, daya daga cikinsu ya kasance jinin gidan ne, dayan kuma ya kasance babban hadimi ne na gidan da wannan furucin nake muku sallama sai an kawo wannan tsumin za a sake nemana ya shugabana Aljana Dunaila tana gama fadin haka ta bace bat Tamkar bata taba wanzuwa a wajen ba, Amzad yayi shiru yana kallon kowa a wajen daya bayan daya koda yazo kan bawa udez sai yaga jikinsa na tsuma kuma idanunsa sun zazzaro, alamun tsananin tsoro sun bayyana karara a tare dashi koda ganin haka sai sarkin yaki yazo gaban shi ya durkusa kuma ya dube shi a cikin nutsuwa yace duk yadda zanyi na tserar da lafiyarka da rayuwarka sai nayi, yanzu dai ku biyu ne rak zaku iya taimakawa lasmin a ceto rayuwarta, da kai da mahaifiyar yarima ne kadai kuka san sirrin gidan sarautar sarki zamaru fiye da kowa kunsan a inda sarki zamaru yake ajiye tsumin tsafinsa kuma kunsan masu kula da tsumin da kuma lokacin da za a iya fakar numfashin shi a debo tsumin ni kuma zan yi kokarin sato takubban guda biyu kunga kenan nawa aikin shine farko sannan naku, sa armu daya babu yadda za ayi boka hizainu da sarki zamaru su taba gano nan inda muke yanzu bare har su kawo mana hari Al amin Misau amman akwai dokokin da zaku kiyaye idan har kuna son mu kare kanmu, yanzu aikin dake gabana dole ne na kera takubba da suke iri daya sak dana sarki zamaru lokacin da sarkin yaki Amzad ya zo nan a maganarsa sai gimbiya musaira ta turbune fuskarta tace to waishin duk dan mu ceto rayuwar lasmin zamu jefa rayuwarmu cikin hatsari, kai zaka tafi sato takubban sarki zamaru wanda a dalilin haka su sarki zamaru zasu iya tarbarka su cutar dakai mahaifiyar yarima Da bawa udez kuma zasu sayar da rayuwarsu su tafi izuwa can gidan sarautar sarki zamaru don debo wannan tsumin tsafi alhalin sarki zamari yana neman su ya kashe su, ai wannan ma ganganci ne domin za a salwantar da rayuwar uku kenan saboda guda daya. Koda jin haka sai ran yarima ya baci bai san sa adda ya dakawa gimbiya musaira tsawa ba yace 'shin ke baki ga yadda lasmin ta saida rayuwarta bane domin ceto rayuwata ? Ko godiya baki yi mata ba a matsayinki na yar uwata kafin yarima ya gama rufe bakinsa sai idanunsa suka kama lumshewa a lokacin da jiri ya debeshi, sai gani suka yi ya yanke jiki ya fadi kasa gaba dayan su suka ruga izuwa kansa a dimauce, cikin sauri sarkin yaki amzad ya duba jikinsa sannan yayi masa magani aka dauke shi aka shigar dashi cikin wani daki mai kyau aka kwantar dashi a sannan ne sarkin yaki ya tura aka dauko shamilat mahaifiyar yarima daga can wani bangare na daban da aka kwantar da yarima koda shamilat taga danta a kwance cikin mawuyacin hali sai hankalinta ya dugunzuma ta fara kuka, koda ganin haka sai sarkin yaki amzad ya dubeta cikin murmushi yace kwantar da hankalin ki ya shugabata danki zai warke sumul irin halin da lasmin ta shiga shine ya same shi, ma ana dafin takobin sarki zamaru ne a jikinsa saboda ya yankeshi da takobin gama fadin haka ke da wuya sai sarkin yaki amzad ya dauko wannan maganin da aljana Dunaila ta hadawa lasmin ya baiwa yarima yasha kuma ya shafa masa akan ciwukan da aka yi masa sannan ya dube shi yace masa yanzu kaima zaka tsira daga sharrin wannan dafin iya tsawon kwana bakwai don haka kai da mahaifiyarka sai ku tayamu da addu ar Allah ya bamu sa ar samo wadan nan takubban na sarki zamaru gama fadin haka ke da wuya sai sarkin yaki Amzad ya dubi gimbiya musaira yace zo muje mu tattauna domin ni dake ne zamuyi wannan aiki na sato takubban sarki zamaru in babu ke ba zamu samu nasara banan take sarkin yaki amzad ya juya ya fice daga cikin dakin ita kuwa musaira sai ta bishi da sauri tana waigen yarima dake kwance tana mamakin yadda za ace wai in babu ita ba za a iya sato takubban sarki zamaru ba sai da suka yi yar doguwar tafiya a cikin gidan suka iso wata katuwar fada ta musamman suna isowa daf da kofar shiga fadar sai musaira taga wadansu kyawawan kuyangi na aljanu guda biyu a tsaye nan

Chapter 6 of 8