Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 8
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KISAN GILLA 1 Littafi na biyar Na Abdulaziz sani madakin gini Ebook creator:- Shuraih Usman 99% Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini KISAN GILLA Littafi na Daya (1) Part A. . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... MARUBUCIN YA RARA DA CEWA, A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude anyi wani babban birni mai suna madinatul haswar a cikin daular larabawa birnin madinatul haswar ya bunkasa a kan karfin arziki girman kasa, karfin mayaka da yawan al umma sarkin dake mulkin birnin madinatul haswar ya kasance adali mai tausayi da jin kan talakawa ana kiransa da suna HISHAM IBN UBAIDA . SARKI HISHAM yana da matar aure guda daya jal mai suna shamilat wadda ta kasance yar wani babban sarki mai mulkin wata kasa da ake kira da hushush ana kiran wannan sarki da SAHIBUL HILAYAT sai da sarki hisham ya auri shamilat da shekaru goma sha daya sannan Allah ya albarkace su da samun juna biyu nan fa sarki hisham da shamilat suka cika da tsananin farin ciki domin a duniya basu da wani buri wanda yafi ganin sun sami haihuwa saboda a shekarun baya babu abin da basuyi ba, domin su sami haihuwar amma abu ya gagara, lokacin da mahaifin shamilat ya samu labarin cewa 'yarsa ta sami juna biyu sai ya kamu da tsananin farin ciki fiye da ita kanta shamilat din da mijinta saboda shi kuma bashi da burin da yafi yaga jikansa kafin ajali ya riske shi kasancewar tsufa ya riske shi a ko yaushe ta Allah zata iya kasancewa Al amin Ahmed Misau, Guyson nake magana, bisa wannan dalili ne sarki sahibul hilayat ya tashi manzanni da dukiya mai yawa ya aiko su izuwa ga sarki hisham yace ga wannan ayi renon ciki kuma idan haihuwa tazo daf yana son shamilat ta je gida ta haihu, yayin da wannan sako ya isa ga sarki hisham sai hankalinsa ya dugunzuma domin baya son ya rabu da matarsa dai dai da dakika daya amma kuma yana matukar jin nauyin surukin nasa don haka sai ya amince da hakan ita kuwa shamilat sai ta kamu da matukar farin ciki saboda a rayuwarta babu abinda take so sama da ta kasance tare da mahaifinta a ko yaushe saboda ita kadaice 'yarsa a duniya sarki Hisham yana da dan uwa yarima ZAMARU wanda ya kasance azzalumi kuma mara imani mai tsananin son duniya uwa daya uba daya suke dashi da hisham, a zahiri yarima zamaru yana nuna cewa yana matukar kaunar dan uwansa sarki hisham amma a karkashin zuciyarsa babu abinda ya tsana sama da shi ba wani bane ya haddasa wannan gaba ba a tsakaninsu face kawai hassada da kyashi da kuma tsananin son KARAGAR MULKI TUN mahaifin su sarki hisham na raye ya futa cewa hisham ne zai gaje shi daga wannan lokaci ne yarima zamaru yaji ya tsani dan uwansa sarki hisham ya fara tunanin hanyar da zaibi ya kawar dashi daga doron kasa sau bakwai yarima zamaru yana bayar da kwangilar a kashe hisham amma yana kubuta kasancewarsa sadauki mai dakawa maza gumba a hannu Guyson nake magana Al amin Kenan Lokacin da yarima zamaru yaga ya kasa ganin bayan sarki Hisham sai ya zuba ido izuwa lokacin da tsufa zasu riskeshi har rai yayi halinsa saboda ya tabbatar da cewa indai babu sarki hisham dole shine zai hau karagar mulki, ana cikin wannan hali ne na jiran lokaci kwatsam sai shamilat ta sami juna biyu hm Al amarin da ya kara dugunzuma hankalin yarima zamaru kenan saboda ya san cewa idan matar hisham ta haihu to fa sarautar ta kara yi masa nisa, a ranar da zamaru ya sami labarin cewa shamilat ta samu juna biyu sai ya kasa zaune ya kasa tsaye har dare ya raba bai rintsa ba Babban abinda ya kara jefa shi cikin bakin ciki shine shima matarsa ba ta taba haihuwa ba don haka duk ranar da ya mutu shi kenan bashi da magajin mulki, cikin tsakar dare yarima zamaru na kai kawo a cikin turakarsa ya kasa barci sai matarsa sarima ta farka daga barci koda taganshi a tsaye yana kai kawo saita dube shi cikin tsananin damuwa ta mike da sauri tasha gabansa tana mai rike kafadunsa, tace yakai mijina menene ya tayar maka da hankali a yau har ka kasa bacci? Koda jin wannan tambaya sai yarima zamaru ya yi ajiyar zuciya sannan yace baki da labarin cewa matar sarki ta samu juna biyu ne? Sarina tayi ajiyar zuciya tace haba maigida yanzu a kan haka ne ka tayar da hankalinka har ka kasa bacci koda jin haka sai zamaru ya rufe sarina da fada yana cewa bata da hankali bata da kishin rayuwarta, sarina ta bushe da dariya sannan ta ce ka kwantar da hankalinka mijina ina so ka sani cewa ni na san abinda ba ka sani ba idan har kana so ka san abinda na sani yanzu ka tashi mu tafi izuwa can bayan gari wajan wani bakon boka da yazo cikin alamun karayar zuciya yarima zamaru ya dubi sarina yace ke nifa na gaji da maganganun bokayan nan tunda an dade ana ruwa kasa na tsotsewa kuma na gaji da gafara sa har yanzu banga kaho ba Guyson nake magana, sarina tayi murmushi tace aiko bokaye suna suka tara wannan bokan ya wuce yadda duk kake tsammani duk wani bayani da zan yi maka ba zaka gamsu ba don haka gani ya kori ji kawai kazo muje wajansa yanzu a cikin wannan daren cikin sirri koda jin wannan batu sai yarima zamaru ya cika da farin ciki kawai sai ya mike zumbur ya kama shiri yayi badda kama itama sarina yasa ta ta batar da kamanninta sannan sukayi hawa suka fice daga cikin birnin madinatul haswar a sirrance ba tare da kowa ya shaida su ba sai da suka yi tafiyar kusan rabin Sa a sannan suka iso gaban wani katon dutse wanda a kansa akwai wata yar karamar bukka abinda ya daurewa yarima zamaru kai shine ganin matattakalar bene a kan dutsen tamkar sassake dutsen akayi aka samar da ita shi dai zamaru ya san wannan dutse sama da shekaru talatin baya amma bai taba ganin wannan matattakala a jikinsa ba tabbas wannan matattakala aikin aljanu ne bana mutum ba abinda zamaru ya ayyana kenan a cikin zuciyarsa bayan zamaru da sarina sun tsaida dokunansu a gaban dutsen sun sauka sai suka daure dawakan nasu a jikin wata bishiya sannan suka taka wannan matattakala suka hau kan dutsen suna isa gaban wannan bukka sai sukaga bokan tsulum ya bayyana a gabansu yana kyakyata dariya al amarin da ya dan razana yarima zamaru kenan ya dan ja da baya kadan , shi dai wannan boka ya kasance dogon mutum garjeje mai kirar mutanan farko jikinsa gaba daya a murde yake alamar karfi ta bayyana karara a tare da shi yana da yar faffadar fuska kyakkyawa cike da kasumba da gajeran gemu babu riga a jikinsa face wata fatar damisa wacce ya yafata bisa kirjinsa ta zagayo izuwa bayansa daga cikinsa zuwa gwiwoyinsa a rufe suke da bante irin na fatar damisar da ya yafa kuma takalmin dake kafarsa ma anyi shine da wannan fatar damisa gaba dayan damatsansa na hagu dana dama a cike suke da gurayen tsafi , tabbas wannan boka yana da kwarjini da cika ido kai da ganinsa kasan cewa murucin kan dutse ne wato bai fito ba sai da ya shirya bokan ya dubi yarima zamaru yayi murmushi yace kada kaji tsoro ya shugabana ni mai taimako ne a gareka ko ince zamu yiwa juna taimako ku biyoni izuwa cikin bukkata mu zauna domin mu tattauna sosai koda gama fadin haka sai bokan ya juya ya shiga cikin bukkar nan take yarima zamaru da sarina suka bishi a baya ba tare da fargabar komai ba da shigarsu cikin bukkar sai yarima zamaru ya sake cika da tsananin mamaki domin kansa ne ma ya kusan juyewa saboda ya tsinci kansa ne a cikin wata makekiyar fada wacce ta kawatu ainun ninkin fadar sarki hisham sau uku wadansu kuyangin aljanu sunata hidima da kai kawo bokan yaci gaba da tafiya a tsakiyar fadar ya nufi inda karagar mulki take su zamaru na biye dashi amma basu isa inda karagar mulkin take ba sai da suka yi taku dari da arba in, da zuwa sai bokan ya zauna akan karagar mulki yarima zamaru da sarina kuwa sai kuyangin aljanun suka kama hannayansu suka kaisu izuwa kan wadansu kujeru dake daf da karagar mulkin suka zaunar dasu nan da nan aka kawowa yarima zamaru da sarina ruwan inibi a cikin tambulan na zinare da kofuna suka fara jika makoshinsu a sannan ne bokan ya dubi yarima zamaru a karo na biyu yace lale maraba da yarima zamaru dan uwan hisham sarkin gobe Al amin Ahmed Misau Guyson Sunana Kenan koda jin wannan batu zamaru ya natsu sosai bokan ya ci gaba da bayani yana mai cewa ka kwantar da hankalinka ya kai wannan dan sarki kayi sani cewa matarka tazo nan kafin kai kuma mune mukace ta kawo ka mun san duk abin dake damunka da kuma burin dake zuciyarka tabbas mune zamu magance maka dukkan matsalarka muddin muma zaka bi umarnin mu shin ka amince da wannan sharadi? Koda jin wannan batu sai yarima zamaru ya dubi bokan cikin alamun rashin fahimta sannan yace menene sharadin da kake so ka gindaya mun bokan yayi murmushi yace ina so ka dauki alkawari cewar idan bukata ta biya zaka raba birninka biyu ka bani kaso guda na mallakeshi haka kuma zaka bani rabin dukkan dukiyarka lokacin da yarima zamaru yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa abin dake masa dadi yayi shiru yana tunani bokan ya tuntsure da dariya alamun da ya janyo katsewar tunanin yarima zamaru kenan ya dago kai a firgice ya dubeshi yace ni ne Hizainu ibin Markasi masanin sirrin gobe, yakai wannan dan sarki ina so ka sani cewa babu wani abu da mutum ke samu a saukake kuma a banza face ya rasa wani abu ina mai shawartarka daka dauki sharadina ni kuma na taimaka maka na sanar dakai duk abinda zaka yi ka samu biyan bukatarka kuma yanzu ne kadai damarka idan ka bari wannan dama ta wuce ka har abada ba zaka samu wata ba sa adda yarima zamaru jai wannan batu sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye gami da ajiyar zuciya ya sake yin dan guntun tunani sannan ya dubi boka hizainu yace na yarda idan ka taimakeni burina ya cika zan raba mulkina da dukiyata gida biyu na baka rabi amma bisa shardi guda sharadin kuwa shine sai dai kayi rantsuwa da girman tsafi da kuma darajar iyayenka cewar a gaba ba zaka yi yunkurin rabani da mulkina ba domin ka mallaki kasar gaba daya kuma ba zaka taba cutar dani ba ko wani nawa koda jin wannan batu sai idanun boka hizainu suka zazzaro ya kamu da tsananin mamaki saboda bai taba zaton cewa yarima zamaru zai daureshi ba da jijiyarsa haka, al amarin da ya jefa shi cikin shakku da wasu wasi kenan ya kama muzurai yana kallon kuyanginsa dake kai kawo a cikin fadar suna hidama sai da yayi dan tunani da nazari sannan ya bushe da dariya nan take yayi rantsuwa da girman tsafi gami da darajar iyayansa bisa kan cewa ba zai taba neman wani abuba daban a wajan yarima Zamaru a nan gaba kuma ba zai cutar dashi ba koda jin haka sai farin ciki ya lullube yarima zamaru yace shima ya amince da bukatar boka hizaunu boka hizainu ya kyalkyala da dariyar murna yace gobe da safe idan kaje fada zaka iske dan uwanka sarki hisha, a kwance cikin cutar ajali kuma ba zai wuce kwana bakwai ba a kwance rai zaiyi halinsa abu na biyu da nake so dakai shine a yanzu haka matar sarki hisham ta haifi da namiji kuma har ta gama wankan jego ta baro can birnin darul hushush ta taho izuwa nan birnin madinatul haswar tare da jaririnta da kuma dakaru dubu biyar masu tsaron lafiyarta wadanda suka kasance zakwakuran mayaka fasa taro lallai ka shirya wadansu zakwakuran dakarun da suka fisu jarumtaka wadanda zasu je su yake su su kashe matar sarki ya zamana cewa baka da wata barazana a mulkinka ina mai tabbatar maka da cewa a daren da dan uwanka sarki hisham zai mutu ne shamilat da jaririnta zasu iso cikin garin nan don haka duk yadda zakuyi kusa a tare su a can cikin daji kafin su iso kusa da wuri, kuma kada ka kuskura ka shiga cikin mayakan da zasu je yin wannan aiki kuma ka tabbatar da cewar anyi wannan aiki a cikin sirri ba tare da wani ya sani ba lokacin da yarima zamaru yaji wannan batu sai hankalinsa ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe ma ya dubi boka hizainu cikin alamun tsananin tsoro da damuwa yace yakai wannan boka mai daraja yanzu a ina zan samo dakarun da zasu iya kashe dakarun da sarki sahibul hilayat masu yiwa shamilat da jaririnta rakiya izuwa nan birninmu? Ka sani cewa dakarun birnin darul hushush mayaka ne na asali kada su ba wasa bane boka hizainu ya sake bushewa da dariya lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa yace babu wanda zai iya yi maka wannan aiki face sarkin yakinka amzadu ibn karlyas koda jin haka sai yarima zamaru ya cika da tsananin mamaki gami da tsoro yace to yaya amzadu zai amince yayi min wannan aiki alhalin kasan cewa ya kasance babban aminin sarki hisham wanda a shirye yake ya sallama rayuwarsa domin kare ta sarki da iyalansa koda jin haka sai boka hizainu ya sake bushewa da dariya sannan yace da zarar sarki hisham ya mutu kaine sarki komai ya dawo karkashin ikonka da mulkinka a wannan lokaci kana da ikon sarrafa komai da kowa da karfin karagarka a daren da sarki hisham ya mutu ka tura akamo sarkin yaki amzadu da iyalansa a matsayin kana zarginsa da laifin sawa sarki wannan ciwon ajali tunda kowa ya san cewa dare da rana yana tare da sarkin bayan an tsare su a kurkuku shida iyalan nasa sai kasa a fito dashi shi kadai azo dashi har cikin turakarka ka kadaita dashi a sannan ne zaka gaya masa bukatarka ta son ya debi zakwakuran yaransa suyi bada da kama suje su kashe matar sarki shamilat da jaririnta da duk dakarun da sukayi musu rakiya izuwa nan birnin madinatul hashwar idan kuma yaki koyayi wani abu ba dai dai ba sabanin umarnin da ka bashi zakasa a kashe iyalansa idan kuma yayi aikin daidai bisa nasara zaka bashi babban matsayi a fadarka fiye da wanda yake da shi a yanzu... . Nan zan dan dakata Dafatan Littafin ya kayatar daku comment da like saimu cigaba kafin nan Nidinne Al amin Ahmed Misau Guyson sunana Kenan Daga Zauran Labarai NakeKISAN GILLA Littafi Na Daya (1) Part B. . . Marubucin Littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Typing AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa... Fiye da wanda yake dashi a yanzu. lokacin da boka hizaunu yazo nan a zancensa sai yarima zamaru ya kamu da tsananin farin ciki nan take ya kama kyalkyala dariya saboda murna sannan ya dubi boka huzainu yace yakai wannan boka mai daraja hakika ka cika makiru uban masharranta na duniya Hm babu makawa wannan dabara taka saita yi nasara shin yanzu ka tabbatar mini da cewa idan na koma gari zan iske sarki ya kwanta cutar ajali koda jin wannan tambaya sai boka huzainu yayi murmushi yace yau fa shekara bakwai kenan ina shiri da jiran zuwan wannan rana saboda me ma zaka rinka shakku bisa furucina ku koma gida kuje ku sha barcinku a cikin wannan dare lallai gobe da safe za a yi kiranka izuwa fada kaga zahiri nan take yarima zamaru da sarina matarsa suka yi wa boka hizaunu sallama suka fito daga cikin gidan nasa suka hau dawakansu suka koma cikin birnin madinatul hashwar ba tare da wani ya shaida suba akan hanya .hakika masu iya magana sunyi dai dai da sukace tsafi gaskiyar mai shi kuma maso abinka yafika dabara Kashe gari kuwa da sassafe aka tashi manzo daga gidan sarki ya ruga izuwa gidan yarima zamaru ya sanar dashi cewar ya rugo izuwa gidan sarauta ana nemansa yanzu yanzu a majalisa koda jin wannan batu sai yarima zamaru ya dubi manzon cikin alamun tsananin mamaki da tsoro yace lafiya ake namana a fada da sassafen nan haka Manzon ya risina yace ai sarki ne ya kamu da wani irin ciwo farat daya ko mikewa zaune ma ya kasa, koda jin haka sai yarima zamaru ya dimauce ya ruga da gudu izuwa cikin turakar matarsa sarina da shigarsa ya iske sarina a kwance tana shirin tashi kenan nan take ya labarta mata labarin da manzo yazo dashi dajin haka sai sarina ta mike zumbur daga kan gado ta daka tsalle ta rungume zamaru tana mai kyalkyala dariyar murna tana cewa shi kenan bukatar mu ta biya nan dai zamaru yayi sauri ya kintsa sannan ya bi manzo suka wuce izuwa gidan sarauta da isar su ya wuce kai tsaye izuwa cikin turakar sarki inda ya iske sarki hisham a kwance bisa gado fuskarsa ta cika da wadansu irin kuraje babu kyan gani ga likitoci da manyan bokayan garin nan sun taru a tsaitsaye a gefen gadon a daya bangaren kuwa gaba dayan yan majalisar sarkine a zazzaune suma sunyi jigun jigun cikin alamun tashin hankali koda shigowar yarima zamaru sai sarki hisham ya dubi yan majalisarsa da dukkan likitocin sa da bokayan nasa har dama duk hadimansa dake cikin turakar yace kowa ya fita ya barsu yana son ya gana da dan uwansa zamaru a wannan lokaci sarkin yaki amzadu na zaune daf da sarki ya rike hannayan sarki yana ta zubar da hawaye kuma ya kurawa sarki hisham idanu kodajin umarnin da sarki ya bayar sai kowa ya fice daga cikin fadar amma shi sarkin yaki amzadu saiya kasa mikewa ya fita har saida sarki ya dubeshi ya budi baki yace yakai babban masoyina ka sani cewa a rayuwata ban taba boye maka wani al amarina ba saboda kauna da yardar dake tsakaninmu amma yau kuma bana son ka san wani babban sirri dake tsakaninmu da dan uwana zamaru saboda uwa daya uba daya ya wuce wasa don haka ina son ka fita ka bamu wuri koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke sarkin yaki amzadu domin irin haka bata taba faruwa ba tsakaninsa da sarki cikin sanyin jiki ya mike tsaye yana waigen sarki yana zubda hawaye ya fice daga cikin turakar kuma ya janyo musu kofa ya rufe ta faruwar hakan keda wuya sai sarki hisham ya dubi yarima zamaru ya yafito shi da hannu ya sake budar baki da kyar yace matso nan kusa dani ya kai dan uwana rabin jikina cikin nuna alamun tsananin damuwa har idanun na zubar da hawaye zamaru ya je ya zauna agefen gadon sarki daf dashi suka kurawa juna idanu har izuwa tsawon yan dakiku sannan sarki ya dubeshi yace yakai dan uwana kayi sani cewa a daren jiya na kamu da wannan cuta farat daya kuma likitocina da bokayena sunyi iya bakin kokarinsu akan su gano abinda ya haddasa wannan cuta da maganinta sun kasa, tabbas jikina ya bani cewa mutuwa zanyia cikin yan kwanaki kalilan ka sani cewa bani da wani makusanci wanda yafika sai kuma matata shamilat da abinda ta haifa tuni mahaifin shamilat sarki sahibul hilayat na birnin darul hushash ya aiko da manzo cewar shamilat da jaririnta data haifa sun taho nan birnin bisa rakiyar dakarunsa kuma zasu iso a daren kwanaki bakwai masu zuwa koda sarki hisham yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa yaci gaba da cewa a duniya bani da wani buri wanda yafi naga dana na cikina wanda ban same shi ba sai bayan na shafe shekaru goma sha daya dayin aure amma gashi burina ba zai cika ba domin ina ji a jikina cewar kafin shamilat ta iso garinnan ajali ya riskeni Al amin Ahmed Misau, guyson nake magana koda jin haka sai yarima zamaru ya rungume sarki hisham yana mai fashewa da kuka yace yakai dan uwana kayi sani cewa dukka mai rai baya fidda tsammani rabo kuma babu wata cuta wadda bata da magani a doron kasa don haka ni yanzu ina so ka bani dama na garzaya izuwa makotan kasashenmu na nemo maka magani koda jin wannnan batu sai sarki hisham ya busheda dariya cikin Matukar karfin hali da juriya, al amarin da yayi matukar baiwa yarima zamaru mamaki da tsoro kenan yaji a ransa kamar sarki ya gane cewa yana da masaniya a kan wannan ciwo da ya same shi, lokaci guda kuma sai yaga sarki hisham ya fashe da matsanancin kuka na bakin ciki da kyar zamaru ya rarrasheshi yayi shiriu sannan ya dube shi yace yakai dan uwana tunda na hau kan karagar mulki ban taba kamuwa da ciwon da ya kaini ga kwanciya ba sai jiya fruwar hakan ce ta tabbatar mini da cewar nesa ta matso kusa ina so ka sani cewa ba wani abu bane ya sa na sallami kowa daga cikin dakin nan ba sai domin muyi wani sirri guda daya wannan sirri ba komai bane face ina son na roke ka wata alfarma guda daya ka sani cewa rayuwa ban taba tauye wani hakki naka ba a matsayinka na kanina kuma baka taba neman wani abu a wajena ba wanda banyi maka shi ba tun daga kuruciyarmu kawo izuwa girmanmu a lokacin da mahaifinmu ya ke raye da kuma ya mutu koba haka bane? Yarima zamaru ya gyada kai a lokacin da hawaye na gaskiya ya zubo masa domin take yaji tausayin sarki hisham ya ratsa jikinsa saboda sanin cewar gaskiyar ya fada sai yace hakika ka fadi iyakar gaskiya yakai dan uwana sarki hisham yayi dan guntun murmushi sannan yace ni kuwa ban taba neman wani abu ba a wajanka kuma ka taba saka mini da kwara zarra ba koda karfin jikinka bisa duk irin abubuwan alherin da nayi maka a rayyuwa zamaru ya gyada kai yana mai nuna alamar haka ne sarki hisham yaja dogon numfashi sannan yace alfarmar da nake nama a wajanka itace idan har matata ta iso birnin nan a raye ita da jaririnta kada ka sa a kashesu ko a boyesu a wani wuri bisa tsoron nan gaba zasu iya rabaka da mulkinka idan har ba zaka iya zama tare dasu ba kamar yadda na zauna tare dakai tsawon shekaru

Chapter 1 of 8