Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 10
kullum a cikin tashin hankali da miji ake kishiya kuma ta kamata tayi amta dukan tsiya ta kaima baba Lantana da kanta tayi damara taje har gidan Nalami wai zata ramawa Asabe dukan da matarshi ke yi mata ban san yanda akay ba sai naga tadawo kaca-kaca da kamar akwal rayuIwar addini a gidan nasu to da komai ma da sauki to babu. Daga tsakar gida na soma jiwo wata magana da ta katsemin maganar zucin da nake yi saboda an fara daga murya ana yinta sama-sama alamar rayuka sun fara hassala. To bakya cewa ya sakeki, ke wacce irin sakarya ce yaya za a ce miji ne zai auna maka hatsi abincin da ba zai isheka ba babu kudin cefane babu koami sai abinda kishiya ta baka, sannan in abincin bai isa ba sai ace. kai ne ka rasa, wannan wane inn zalinci ne, 141 Sannan in dare yayi ya zo ya fada miki da yunwar da komai ba dama ki ki yarda da shi, ke ko irin 'yar tirjiya da yangar nan da mata ke yi a rarashesu a yi musu abinda suke so baki iya ba. Ai rufeni da duka yake yi yana ganin alamar zan yi mishi tawaye sai kawai ya tashi ya zauna ya yi ta jigbata da duka wai ladan hatsinshi da na wuni ina ci, baba Lantana tayi shiru kamar yanda Asaben' ma ta tayata yin shiru, imawa cna na ji ta ja wani mummunan tsaki da bai da dadin ji kafin daga baya ta bishi da fadin, kai Nalanni dai tsnanne ne. Shi ne nace to ko zance ya sake nin ne kawai? Da saun ta ce ys sakeki mana tun yaushe nake gaya miki hakan? Ta dan rage nurya kadan ta ce, to amma fa ba Zai yarda in abr mishi wannan yaron a can ba ya ce wai zaunana ya ke yi na barin gidan shima zai bari wannan dai ya yarda nashi ne tunda yana kama da ya'yanshi amma si wannan ai bai ga ta inda ya daukoshi ba shi ne nace ko zan kawo miki shi ne kawai in bar mishi wannan din: wahalar da nake sha tayi min yawa kajin mafa day ake bani figarsu yana bani sisi-sisi ina samun na sabulu yanzu ta hanashi bani ko kwabo wai... Ni da nake kashc da kunne in ji abinda baba Lantana zata fadi kan kawo mata dan da Asabe ta ce Za ta yi sai naji ta hassala ta daka mata tsawa, ke barni haka da wannan mugun albari naki sakarya kawa 142 shashasha sauna mara zuciya ace mutum bai da wani aici sai na bayar da mugun labari? Ki dauko yaro ki kawo min ya zama duk tattakar da ya yi miki a banza kenan ko me? Wannan yaro ai dole ne ya girmaa gidanshi ladan sukurkutaki da ya yi ya maida ke wata yamutsattsiyar tsohuwa, tsinannan mutum kawai. Na ce oh oh ta kacame tsakanin siriki da sirika, ina zaune kan kekena ina dinkin kayan dana gama yankawa zuciyata tana tunaina al'amarina irin kokarin da baba Lantana tayi na ganin ta sa babana ya baiwa Alhaji Nalami aurena duk da tafi kowa saninshi da duk wani al'amarinshi tunda tun a loakcin ta sha gaya min cewar in dai matar Nalami tana nan a yanda ta santa ai zata yi mata magani na to gashi abin baiyo kaina ba sai ya fada a kan yarta nan take na tuna da karin amganar hausawa da ke cewa wai, mugunta fitsarin fako, in kayi sai ya dawo maka kanka. Kwalliya mai kyau nayi a ranar da na yi nufin kaiwa masu kayan kayansu, doguwar riga na sanya har Rasa ta farar atamfa da aka yiwa ratsi da kananan filawowi koraye da bulu, saman rigar na yi shi a matse yayin da na yiwa tsakiyar yankan umbrella ya sauka har Kasa, dankwalin yadin' atamfar ne a kaina na yi dauri mai kyau sosai na sanya yan kunne kanana na yafa farin gyale madaidaici a-kafadata yayin da na kawata hannayena da adon awarwarai, agogo da zobuna biyu na zinari daya kuwa na azurta 143 da aka yava kira mai kyau na shuri takalmana silifas 1masu igiya a baya yan Italy da suka kara kawatamin kwaliyar tawa, nasa garkamemen kwado na kulle kofar dakina a dalilin gajiyar da na yi da biyan mutane atamfofinsu da suke bata don haka nama canza kofar dakin gaba dayanta. Na baro gida rike da ledar kayan dinki da kuma pos a hannuna bayan na gayawa babana inda zani, yar tafiyar da nayi ba wata mai yawa bace na ja na tsaya don tarar mashin din da zan hau. Wat ke me yasa bakya įin magana ne? Sau nawa nake gaya miki in zaki fita ki daina amfani da turare ki kuma daina hawa mashin bana so. Ban kalteshi ba balle in bashi amsa iyaka dai nasan nayi mamakin ji ko ganinshi a wannan lokacin tunda nasan ya taf Legos bar kima san da dawowar tashi ba. Amma shi baba tsareki da ya yi a gida kike ta wannan zaman a gabanshi yana ganin kamar ya yi mishi daidai? Shi bai san kin kai kowane irin munzali bane, bai san kinas ha'awa ba? Ke ba za ki gaya mishi kina da mas'ala ba? A muku mukuns anyin nan kin fito za ki je ki kai akyan da kika dinkawa wasu in kina gidan aurenki mijinki zai yarda da haka? Gaskiya na gaji da ganinki a haka yanzu fa Rumasa'u ya' yanta biyu ne. 144 Maganar ta dak zuciyata a hankali na tunawa kaina da kullum muka gamu da shi bama rabúwa sai ya san yanda yayi ya sokamin abkar maganar da ta tsaya mina raina. To wai ni ina abinda ya dameka da ni ne? Kaga ni na damu da kai e? Kaga ina. daga ido ina kallcka ne balel in san abinda kake ciki? Ina dalilin da kake nema ka maida mahaifina abokin wasanka, kullum ka ganni sai ka san abinda ka fada a kanshi. Ban maidashi abokin wasa ba Mero amma gaskiya zan gaya miki yana 6ata min rai don me zai hanani ke? Don... Na yi maza na katseshi, in ya hanaka ni sai ka rinka gaya mishi magana a kan ido na wane hurumi ke gareka na yin hakan? Nace bana sonka nace ka fi ta harkata nace ina kwai wani mutumin da zance na tsana a yau to kai ne don me ba za ka yi zuciya ka fi ta hanyata ba? Ranshi ya yi amtukar 6aci da kalarman da nayi mishin, wani irin kallo ya yi min irin wanda shi kadai ya san abinda yake nufi da kallon, kina ganin kamar ba za a iya fita harkar taki bane? Kina ganin kamar in an fita harkar taki wani abu zai faru ne da kike wannan cika bakin? To ni don na fita harkar ki ma menene Maryamu? Ai ni ina da mace a gida har da ya'ya kece kike zaune ke kadai kece kike rayuwa cikin kewa da kadaici, duk sanyin da ya taso ya kare a 145 kanki kina zaune kan kujerar dinki, ni ai da aurena sannan karya kikeyi kice bakya sona in bakya sona me ya hanaki yin aure? Fitar da wani ki aura mana ki zauna kema a dakinki ki dandani dadi da zumar dake cikin auren sakarya kawai sokuwa shashsha wacce babu halin a batawa mutum rai ya gaya mata ta tausaya mishi, sai ta ce zata bishi da bakar magana sau dubu nawa yake so in turo mishi mutane kafin ya yarda ya bani ke? Me nayi mishi a rayuwa i banda adalci. Sauri nayi na tari mashin babur na dale kai muka tafi don kar bakin ciki da dacin da nake ji a zuciyata ya sa in fara yin kuka a gabanshi. Zagin da ba a taba yi min ba yi min, yayi min gorin aure da 'ya'ya da... na kasa karasa bayanin nawa na shiga yin kuka sosai da sosai, tana ta bani hakuri, jimawa can kuma sai ta nisa ta ce, nima dai abin yana damuna ina mamakin yanda baba ya ja ya tsaya ya ki baiwa Mubarak aurenki bayan nima nayi iyakacin tunanina ban gano laifin da ya yi mishi ba to inma ya yi a yafe mishi mana, Umma ma fa kwanaki tazo gidan nan maganar kuma ce ta kawo ta na kuma san ba dadi ne ya sa ta yin hakan ba, to ya bashi ke din mana kawai a huta, zan sake zuwa wajen baba in sake rokonshi inji.. Kan ta karasa na yi mata wata irin rantsuwa mai karfi kafin na ce mata, ba zan taba aurenshi ba har 146 abada ba zan taba aurenshi ba bana sonshi bana son shi ko da sunanshi ne a kusa da ni da in aureshi gara ma in yi ta za... Ta dakamin tsawa na kame bakina na bar maganar na koma yin kuka, tun ina yi ni kadai har itama ta shiga tayani muka yi tayi sai da muka gaji muka yi shiru. Mubarak ya saba zagina ko tsareni ya gaya min bakaken maganganu iya son ranshi a duk lokacin da ya turo maganar aurena wajen babana ya ce ba zai bashi ni din ba, to ni yake tsarewa ya gaya min duk wani abinda yake son fada, in yi bacin ran in hakura amma bai taba gayamin maganar da ta daki zuciyata ta sani bakin cki na yi kuka mai tsanani irin wannan karon ba. Na gaji, na gaji, na gaji da iin wulakanci da cin zarafin da yake yi min a kan aurena don kawai ya ga bani da auren da ina karkashin inuwar aure ai shima da bai isa ya yi min irin wadannan abubuwan da yake yi min ba don haka ya zame min dole in tsaya in yi duk wani abin da zanyi don ganin na yi auren saboda in huta da wannan wulakancin da kuma cin mutuncin kan haka yasa washegari da sassafe na yi shiri na tafi gidan Yakumbo Halima wacce ta dade tana kirana inzo muje wurin malaminta da take ta faman bani albari. 147 Ina shiga gidan ta fara murmushi, 'yar halal kin ko ambato yanzun nan nake maganarki a zuciyata. Na tayata murmushin kafin na tsuguna na sOma gashcta tana amsawa tana kallona cikin wani irin yanayi dake baiyanar da jin dadinta. Kai wannan yarinya da iya kwalliya kike wannan kuma wane irin dinki ne? Mu ganshi. Na numa mata ta gansi sosai, to me sunanshi? Na gyara na koma na zauna cikin natsuwa, kwalliya ta fa ke kadai take burgewa. Ta yi maza ta ce wane mutum ai duk wanda ya kalleki ya san ke din gwanar kwalliya ce Mero ai rashi aurenki ba yana nufin ke din kina da wani aibu a tare da ke ba ne a'a lalura ce dake wani aljani ke gareki wanda yake biye da ke bana baki albarin abinda wannan maiamin ya gaya min a kanki ba, ai nace miki ki zo muje wurinshi don ya ce min akwai abinda zai yi ya rabaki da shi kika fi zuwa. Na ce to ai gani na zo yau Yakumbo zuwa nayi don ki kaini inda duk za ki kaini na gaji, na gaji da wulakancin da Mubarak yake yi min, na kwashe bayani duka na yi mata. Maimakon yauma ta nanata maganarta da kullum take fadi cewar shi ne ya yi min sihirin da na kasa yin aure sai naga ta yi murmushi kafin ta ee, ja'ira shagwaba da gata ne suka sashi yin abubuwan da yake yi su ma iyayen na shi ai sun yi nadamar hanashi 148 aurenki da sukayi yanzu tunda kwanaki ai ance korar matar tashi ya yi ya ce a barshi kawai ya yi zamashi shi kadai tunda dai suna kallo an hanashi ke sun kumna yi ko oho da hakand a akayi saboda su basu damu ba ai shi ne dalilin da ya sa ita Hajiya Ummulkhairin ta kama hanya taje gidan Dijan to shi kuma babanki shima ya kafe akan ba zai basu ke ba. Na ce wannan ruwansu ne Yakumbo. Ta yi maza ta ce ruwan su ma mai ma ya kare musu bari in yi maza in shirya mu tafi tun rana bata yi zafi ba don akwai 'yar tafiyar kafa da za a taba. Nace mata to Yakumbo ai ma ni tafiyar kafa ba mas' alata ba ce na riga na saba da ita, tayi amza ta ce, aifa na tuna kin yi ta ba kadan sanda kike zuwa wajen koyon sana' ar nan gashi ya zama tarihi sai amfanin shi ake ci ko ince muke ci tunda yaushe rabon da raina ya 6aci a kan dinkuna? Ace jaruntaka babu dadi? Bari ki gani ins hirya yanzu mu tafi ba ma sai na tsaya wanka ba tsaka tsami kawai zanyi in mun dawo in ban ji kuiya ba na yi wankan. Nan da nan Yakumbo ta shirya muka kama hanyr fita, gani bata tambaya ba ya sani tambayarta, dama kin gayawa kawu ne? Ta dan yi murmushi, mu yan tsofaffini nan da auren mu ya riga ya tsufa yaushe za ace komai za mu yi sai mun tsaya wani tambaya ai shima yasan sabgogin iyali yawa ne da su. 149 Shiru nayi na ja bakina na tsuke tunda nasan babu halin in tsaya ina tambayarta Yakunbo shi aurenn yana tsufa pe a dalilin masu yinshi sun tsufa? Bayan mun sauka a mota tafiyar kafa fosai mukayi a ciki jeji muka wuce wasu rugage muka mika cikin wani irin surkukin daji Yakumbu damun san wurin nan haka yake ai da hayar babura muka dauko a dan kauyen nan da muka wuto. Hararata tayi, kufa yaran yanzu bakuda wata jaruntaka wai ke kina so ne ki nuna min kin gaji da tafiyar kafar da ake yi ko? Na yi murmushi kawai na yi shiru muka ci gabada tafiya da kyar muka iso wata mararraba da ta ce min wannan da muke kai yanzu ita ce mai kaimu gidan nashi nace mata to. Mun samu yan daidaikun mutane da ke jiran a sallamesu amma ana sanar da shi isowar Yakunbo yace a shiga da mu. Na yi mamakin ganin mutumin da ta ce min shi ne malamin na zaci ganinshi dattijo amma sai na ganshi matashi ma'abocin tsabta da natsuwa ga sutura tamkar dai ba a cikin dajin nan yake zaune ba. Hajiya barka da zuwa, ya yi maganar cikin murya mai cike da kamala suka gaisa nima na gaisheshi. Maryamu ko? Ta yi murmushi ta ce haka aka yi kuwa malam, idonshi a kaina ya ce, ai mun gani shi mutum ai kowa da sunanshi yake yawo, gabana ya fadi jin da nayi ya ce ya gani kar dai irinsu ne kullum 150 malamanmu suke yi mana wa'azi a kansu? Cikin Zuciyata na ke wannan tunanin. Ya jawo wani littafi ya bude yana karantawa na dan samu saukin damuwa a tare da ni ganin littafi yake karantawa su kuma malamanmu kulum suna yi mana wa'azin ne akan masu buda kasa suna masu duba ko bokaye to tunda wannan ba kasa bace littafi ne kenan ba duba bane yinshi kuma bai zamo laifi ba. Mas'alar aure ko? Ya yi tambayar ba tare da ya kalli kowa ba idonshi a kan littafin shi, ta yi maza ta ce mishi eh malam aure ne damuwar kullum sai manema sun fito mata gasu gasu kamar za a yi auren sai kuma a nemesu a rasa sun gudu, tun ina ganin laifinta ina ganin kamar ita ke korarsu har na daina jin zafinta na koma tausayi saboda na gane babu hannunta cikin lamarin. Ya girgiza kai cikin natsuwa tare da fadin, ai ba zai bari a aureta ba, wa kenan malam? Ta yi tambayar tana mai kallonshi. Ya ce mai ita mana ai wani maketacin aljani ne yake tare da ita shi ya sa babu halin tayi aure don ba zai bari ba shi yake korar mata samarin da siddabaru iri-iri suna tare da ita su rinka ganin ta caccanza musu tanayin launi lauru su ganta fara su ganta baka su ganta ja su ganta bulu ko kumna su rinka ganin fuskarta tana rabuwa biyu sai ta koma ta hade ta sake rabewa ta sake hadewa, to kinga kuwa ai babu lafiya. 151 Yakumbo tayi maza ta ce, ko kadan cikin sanyin murya ni da kaina da ba sosai nake yarda da irin wadannan abubuwan ba jikina bari yake yi jin bayanin malamin. To yanzu yaya za a yi kenan malam? Ya ce eh to da yanda za a yis ai dai kumaaiki ne babba sai an rabata da shi gaba daya in ba a tsaya an yi hakan ba ko anyi auren kashe mijin zai yi don haka sai an yi juriya da jarumtaka. In dai za a rabata da shi ai duk wani abin da za a yi ba zai gagara ba malam a gaya mana kawai abin da za a yi. Ya ce to babu laifi akwai aiki da za a yi wanda za a bukaci sadaka mai karfi ko dai shekararrun zakaru guda bakwai ko kuma rago sannan zata rinka zuwa nan muna yi mata wani aiki har kwana bakwai in har komai ya tafi daidai to kafin cikar kwanaki bakwan din nan mijin da zata aura zai baiyana ana gamawa sai a daura auren mu kuma in ayzo to shi ne zai biya ladan aikinmu baku ba. Nan da nan Yakumbo ta shiga yi mishi godiya tare da tambayar to wanne ya yi tsakanin rago da kajin? Ya ce a'a ao na za a hada ba rago yafi sai dai in babu hali sai a yi da kajin duk daya ne. Ta ce to bari mu bada kudin ragon nawa ne zai yi? Ya ce daga fan goma zuwa sha biyar ko ashirinn duk wanda kika bayar zai yi. 152 Na yi kasake ina tunanin ta inda kudin da ya ambata zasu fito sai kawai naga Yakumbo ta jawo lalitarta ta ciro kudi ta kirga fam goma sha biyar cif ta mika mshi, ya ce zuba nan cikin wannan kwaryar, ta bi umarnin nashi ta zuba muka yi mishi sallama muka fito. Babu abinda yafi komai yi min dadi irin cewar da ya yi kafin a kammala aikin mijina zai baiyana ana gamawa kuma sai a daura auren shi nne ma wai zai biyashi kenan nima zan yi aure babu sauran a tareni a zageni babu sauran a yi min gori, babu sauran a rinka nunani a unguwa ana fadin babu sauran sa'ata a' yan matan da ke yavwo a unguwar. Washegari da safe naje na samu babana a rumfarshi bayan na kammala shirina na dan zauna kamar zanyi mishi hira sai da na bari Sallau ya dauki kwanduna ya nufi kasuwa sai na kalli babana na ce mishi baba yaya Dija ta aiko ni wurinka wai ince maka akwa wata yarinyar bazawara mai hankali kusa da su ko za a yi magana da ita. Gabana yana faduwa na yi mshi bayanin, sai na ji ya ce to ina da kudi ne da za a yi min amgana da bazawara? Sannan da girmana da komai ita mace ace miki tana son tsoho ne a shekarun. kuruciyarta. A hankali na ce mishi, baba ai ita yaya Dija ina ganin kamar sun fahimci juna ita da matar tace min ne in yi maka magana in ka yarda ta turo maka ita don ka ganta, a hankali ya ce a'a ni kam ai ba sai na ganta ba in 153 dai ku tayi muku ai shi kenan fitina ce dai kawai ni bana so. Nace mishi too nayi mishi sallama na tashi na tafi, can cikin zcuiyata kuwa mamajki nake yi ban taba zaton haka amsar babana zata zamo ba, na kama hanyar tafiya wurin malam don karbo alkawarin da akayi duk da wata zuciyar tana nunamin in fara ganin yaya Dija tukunna sai kuma naga to bari dai kawai inje can din in yaso in na dawo sai in biyo ta wurinta in yi mata bayanin yanda muka yi da babana daga nan kuma taga abin da na karbo wurin malam. Wajen karfe goma sha dayan safe na isa kauyen nan inda daga shine muka soma yin tafiyar kara, nayi tafiyar kafar har na raina kaina sai da na soma kaiwa matuka wajen gajiya ne ma na tuna ko sunan malamin da zani wurin nashi ban ji ba balle kuma na kauyen da zanin, abin ace na bata hanya ban san yanda za a yi inyi tambayar da zata zamo mai amfani a gareni ba, sa'a kawai nayi da na ci gaba da tafiya sai kawai na ganni a mararrabar nan wacce daga ita ne muka dauki hanyar da ta nufi gidan malam. Tsayawa nayi cak. na zubawa hanyoin nan ido ina kallonsu tare da tunanin wacce muka hau ne a ranar? Na gaji da dubawa na yankewa kaina bari kawai in hau kan guda daya tunda bajuyawa baya zanyi ba don haka na kama ta tsakiyar nayi ta tafiya a kanta banga komai ba banga wata alama da na gani wacce ta karfafaa min guiwa ba don haka na juyo da baya zuwa inda 154 nararrabar nan take na sake zabar wata hanyar na hau an nma nayi iyakacin iyawata nayi tafiya sai da na fara debe tsammani ina cikin tunanin komawa da baya kawai in koma gida inje in gayawa Yakurmbo Halima cewar ban gane hanyar ba tazo kawai ta karbar min maganin da kanta ko ta tasoni a gata mu zo tare kamar yanda tayi min rannan tunda ni na kasa gane wurin da kaina sai kawai naga mutum tsaye cif a gabana tamkar daga sama aka jehoshi, tsoro ya.yi matukar kamani ba tare da ya ce min komai ba sai naji ya ce min, wuce mu tafi malam ne ya turoni in kai mishi ke saboda an gaya mishi cewar kin kauce hanya don haka ya kwatantamin inda zan sameki shi yasa na yanko ta cikin bishiyoyin can, nabi hannun nashi da kallo don inga can din da yake magana akai, wani irin surkukui ne da sunkurun duhun bishiyoyi da ban taba tunanin dan adam zai iya shigarsu ba ban iya buda baki na ce mishi komai ba haka nan duk da tsananin tsoron da nake cikin ba zai yiwu in yi musu binshi ba tunda ban san inda zan dosa ba. Tasani kawai yayi a gaba muka kama hanya 'yar tafiya "yar kankanuwa sai kawai gamu mun isa gidan. Shiga nan, yana bani umarni nayi maza na shiga sai ga malam zaune daram a kan buzunshi cikin manyan kaya ga hularshi a kanshi yayi kwalliya irin wacce ta dace da shi. Maryamn da so ya kira sunan nawa yana ma kallona, ina babar taki? Na isar da gaisuwarta gareshi bayan na gama gaisheshi ya ce, alheri ya gaieta, ai ga 155 kwaryar da na hangki a ciki can, nayi maza na waiwaya na kalli kwaryar da ya ce min daga cikin nata ya hangeni babu komai a ciki in banda ruwa, na sake juyawa gareshi na kalleshi don jin bayanin da yake yi, yayin da zuciyata ke ta faman harbawa 6al 6al 6al, daga nan din ne na kira wanda ya daukokin don kar ki je ki yi wa mutanen hanayr da kike ta kakkaucewar wani ta'adi unda su di mafi yawancinsu ba hakuri ne da su ba. Wani mutum ya ashigo rike da zangarniyar dawa a hannunshi ya tsuguna ya mikawa malam, bai kalleshi ba ya ce mishi, kwaya bakwai nake bukata, ya mika mishi kwaya bakwai din ya fita da zaugarmiyar a hannunshi. Malam ya jawo wani tsohon kasko fasasshe ya debo kasa tafin hannunshi uku ya zuba a ciki ya dauki tulun dake gefenshi ya jika kasar da ruwa ta jiku sannan ya shuka kwayoyin dawan nan guda bakwai a ciki kan kace meye wannan sai kawai naga dawar nan da ya shuka a kan idona ta kamna tsirowa a cikin kaskon, nan na zuba ido ina kallon abin mamaki wanda ben atôa ganin kwatankwacin makamancinshi ba, na yi matukar kokarina wajen 6oye halin da nake ciki na tsoro saboda ganewar da nayi ina cikin wani babban al'amari,don haka nayi maza na soma karanto addu'o'i na neman tsari. Kina da wani wanda ya dameki ne a yi miki maganinshi? Na'am na amsa ina kallonshi don ban fahimci abinda maganar tashi take nufi ba, eh abinda nake nufi kenan in kina da wani wanda ya dameki 156 kawo sunanshi mu gwada miki aikinmu a kanshi ta hanayar kashe miki shi nan take. Kalululu, sautin da cikina ya bayar kenan a lokacin da na ji maganar tashi, da kyar na iya girgiza kaina don nuna mishi alamar babu, cikin zuiyata kuma tarnbayar kaina nake yi me yasa malam yake yi min irin wadannan abubuwan tunda ni ai ba abin da ya kawoni wurinshi kenan ba, sannan me yasa bai yi ba ranna na gaban Yakunbo sai yau da ya ganni na zo ni kadai Kina saurarona? Na yi maza nace mishi eh, ita babar taki ta yi miki bayani a kan ka'idojin aikinmu ko? Na girgiza kai nuna alamar a'a, to muna da ka'idojn da karyasu yake da hatsari kwarai shi yasa muke bayani a kansu don kar mutum ya jawa kanshi wata fitina da zata zo ta dameshi ta damu duk wani wanda yake tare da shi, ba a yin musu da umarnin da ake bayarwa anan ko mai tsananinshi, sannan ba a yin gardama ko jayaiya domin nan din Wuri ne da ake mu'amala da nau'o in halittu guda uku wato jinsi mutane da na aljanu sai kuma rauhanai don haka ba wurin wargi kika zo ba, yin daya daga cikin ukun can dana ambata miki ina nufin musu gardma ko jayaiya sakamckonshi yin hauka ne hauka kuma irin wacce bata warkewa. Cikina ya sake bada wani sautin na kulutuiu har ma ya fi na farkon karfi saboda tsananin tsoro da na samu kaina a ciki din. Kin taba ganin aljani ko rauhani? Na yi maza na ce mishi a'a, to ai za ki ganshi yau din nan. Na ji kamar in 157 zabura in mike in karta da gudu in shige cikin dajin nan in huta. Ya gyara zama ya soma yi min bayani, kin san akwai jinsih mutum da na aljan da raunahni kafin mala'iku ko? Angi maza na ce eh ba tare da na fahimci koami ba da yake nufi ba. To mu nan fadar rauhani kika zo ki gane? Na sake yin karfin halin cewa eb. Ya zuba min ido yana kallona ban sani ba ko shima ya gane halin da nake ciki na tsoro ne. Yanzu kafin rauhanin da zai yi miki aikin ya iso tunda

Chapter 9 of 10