Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 10
hakuri da su? To kuma ba zan barki yin aiki ba don kar ki ji ina cewa za ki koma makaranta don ki samu takardarki ki yi tunanin ko har da aiki cikin lissafin nawa. Na yi murmusih na ce nima ban damu da yin aiki ba amma cikin zuciyata ina sha'awar yin sana'a, da sauri ya ce wonderful tamkar ace kin shiga zuciyatakin gani ai ni mai sha'awar taimakon mace yin sana'a ne, Maryamu ina son ganin matata ta tsaya da kafafunta tana dogaro da kanta saboda karki samu damuwa akan wannan wacce irins ana'a kike son yi? Na ce a'a ban sani ba tukunna ni dai kawai cikin zuciyata ina son yi amma ban zabi wacce zanyi bal to ai kin gani ma shi kenan sai in duba in ga abinda zaifi dacewa da ke ina ganin ma kawai dinki za ki yi domin shi ya fi bani sha'awa ko kuwa? Na ce mishi to. Tun ranar da Mubarak ya zo gidanmu ya rokeni alfarmar fita hanyar Mansur na ce mishi ba zan iya ba 88 ya dauki mataki in ya ganni bei kulani ko yana fara'a ya hangoni sai ya yi maza ya tsuke fuska, a zuciyata na ce nima gara irin haka, abu guda daya dai da na kasa fahimta ko dalilin yin shi shi ne wunin da Isiyaku yake yi kan dakalin kusa da gidanmu a zaune bana dai ko amsa gaisuwarshi balle-wani abu ya hadamu tunda kowa ya san dan gidan Mubarak don haka na kara kiyaye mu'amala da shi don Mansur ya kara samun kwanciyar hankali. Ni da Mansur muka zama bamu da wani fata ko buri sai na jiran dawowar babanshi daga tafiyar da ya yi. Mansur dak ullum yake ce min ai kawai kwana daya zan yi mishi in ya dawo da rana in barshi ya kwana ya wayi gari kafin inje mishi da maganar. Sai gashi baban Mansur ya dawo har ya kwana bakwai babu wani motsi ko yunkuri daga gidan nasu shi da kanshi ma sai nake ganin shi tamkar a sanyaye yake ban dai ce mishi komai ba tunda dama can ba ni ce mai zumudin maganar ba ni yar tawa ce. Wurin baba Lantana mai yade maganganu a tsakar gida na samu labarin wai ashe da baban nashi ya dawo ya kai mishi maganar sai ya ce mishi ba zai sake takowa ya zo wurin babana kan maganar aurena ba ya dai zuwanf arko ya kuma isheshi haka don haka in har auren yake so da gaske to ga 'yan mata nan bila adadin tun daga na dangi har bare yaje ya duba gida na mutunci ya zabi yarinya zai tsaya ya aura mishi ita 89 ko da kuwa nawa zai kashe, amma bani ba in ba rashin hankali irin nashi ba ko iyayen Mubarak da suka san da dansu na rinka lalacewa ai ba su bar shi ya aureni ba balle shi. Wannan bayanin da naji a bakin baba Lantana ba Raramin dukan zuciyata yayi ba, don kuwan a riga na Sakankance na saki jiki zuciyata ta riga ta amince da maganar aurena da Mansur sai dai duk da haka ban bari yanayin da na sanu kaina a ciki ya baiyana ba sabdoa na riga na koyi shanye bacin rai ba komai ya taba zuciyarka sai na kusa da kai ya gane ba, haka nan 6acin ran da na samu bai sa naji haushin iyayen Mansur ba to balle kuma shi Mansur din da na tabbatar shima bai ji dadin hukuncin da aka zartar mishi ba, sai dai ya yi biyaiya kamar yanda kowane da na kirki yake yiwa iyayenshi biyaiya kan umarni ko hani da sukayi mishi, bai dai ce min komai ba nima kuma bance mishi na ji ba sai dai kuma biri yayi kama da mutum gaba daya ya canza fara'arshi, kuzarinshi duk sun sauya mainakon zuwa kullum ya koma yin fashi in yau ya zo gobe ba zai zo ba watarana ya yi kwanaki na yi kamar in ya zo in rinka kin fita sai kuma na ga to a na me? Rannan dai ya gaji shi da kanshi ya zaunar da ni ya yi min bayanin komai, hakuri mai yawa ya bani ya kuma rokeni kan kar gaya min gaskiyar da ya yi ya kawo karshen mutuncni dake tsakaninma, na ce 90 mishi a'a ko kadan ba za a yi haka ba sai dai ma a kara nima nayi mishi godiya kan alherinshi a gareni. Ko ban tsaya yin bayani nayi bacin rai ko ban yi ba an san nayi saboda na riga na so aure na kuma soo Mansur don haka fadama batawa ne kawai. Tunda Mubarak ya taso ya zo gidanmu ya rokeni in fita hanyar Mansur na ce mishi ba zan iya ba na Tura al'amura sun sauya a tsakanina da shi amma ban kara sanin irin tsananta da lamarin yayi ba sai a ranar da nayi shiri da niyyar zuwa gidan Yakumbo Halima saboda dadewar da nayi banje ba har na samu labarin korafinta wajen yaya Dija. 'Yar madaidaiciyar kwalliya nayi a dalilin tsala kwalliyar ta daina burgeni ta daina sanyani nishadin da ta saba sanyani a baya sai dai kuma bai hana kwalliyar tawa zamowa mai ban sha' awa ba. Ina tafiya cikin natsuwa ba tare da na damu da kallo ko sanin su wa nake wucewa bisa hanya ba har na kai ga shiga lungund a fi ta daga cikinshi zan bulla kan layin da gidan su Yakumbo Halima yake. Kasancewar lungun a matse yake gashi kuma da .yawan kwata 'yar hanyar da ake bi din ba wata mai fadi bane ya sani hi hanyar waiwayawa in ga wanda ke biye da ni yana taku cikin sauri dan in kauce mishi in bashi hanya ya wuce in har naga alamar akwai bukatar hakan, abin mamaki Mubarak na gani gabana ya yi mummunan faduwa bisa dalilin guda biyu dalili 91 na farko shi ne faduwargaban da na saba samu a duk lokacin da na ganshi ko na ji nmuryarshi wanda kwanakin baya nakem urnar na rabu da shi to ya sake dawowa, daliil na biyu kuma shi ne mummunan kallon da ya tsiri yi min a tsakanin nan ko yana walwala ya hangoni sai ya yi maza ya daure fuskaw ani irin daurewa kuma mai tsanani. Na maida kaina kan hanyada nufin ci gaba da tafiyata, yayin da wani 6angare na zuciyata yake bani shawarar in karta kawai da gudu don in samu in yi nesa da shi tunda ga dukkan alamu zai kamoni saboda dogon taku: da yake amfani a tafiyar ta shi. Tsaya mana mu yi magana, na yi kamar ban ji abinda ya ce ba na ci gaba da tafiyata sai kawai na ji caraf ya kamo gyalena ya rike, ina yi miki magana kina ji nakina tafiya. Raina a bace saboda fusatar da nayi na rike min gyalena na juya da nufin yi mishi tuni kan hana shi yi min hakan da na taba yi in da hali ma in yi mishi tuni cikin tsiwa den kar gobe ya yi tunanin sakewa. Muna hada ido da shi gabana ya sake faduwa na yi maza na sunkuyar da kaina kasa saboda wani irin kallo da yake yi min wanda ban saba da shi ba. Kina nufin ko saurarona ba ki da lokacin yi da pake kiranki kina ji na? So nake in tambayeki yaya naji maganar aurenki da.masoyin naki tayi sanyi kamar ma babu ita? Sakarya kawai sokuwa mara 92 wayo wacce rashin mafadi ya hanata sanin abinda ya kamace ta in taso in zo in rokeki ki fita hanyar shi ki ce min wai ba za ki yi ba? Ai nayi hakan ne don ina zaton ina da matsayi a wurinki saboda kin yaudareni kin yi min abinda na yi zaton ni din daban ne a wurinki sabdoa kin yaudareni kin yi min alheri wanda na yi zaton bani da abokin gami a wurinki, ashe ba haka bane to amma kuma na gode shi da akayi mishi hani a kanki ya hanu. Gabana sai harbawa cikin sauri yake yi, bakaken maganganunshi sun yi tsanani da nauyi cikin zuciyata kokari mai yawa nayi kafin na danne hawayen da ke shirin zubowa a idanuna na hanasu zuba don kar in yi kuka a gabanshi don haka najuya da nufin ci gaba da tafiya, sai naji ya ce, ni babu inda za ki sai kin bani amsar tambayar da na yi miki. Cikin natsuwa na bude baki wanda bai ma san zan bashi amsa ba dan ya san ban cika yin hakan da shi ba na ce mishi, kayi hakuri ba yaudara ya sani yi maka hakan ba kuskure ne. Ya yi maza ya gyara tsayuwa tare da kara tsareni da idanuwanshi cikin saurarona binda zai kara fitowaa daga bakin nawa, ni kuwa ban fasa ba na ci gaba da yi mishi bayani, kuskure na yi nayi maka abinda na yi makan wanda ya sanyaka yin tunanin kana da matsayi na daban a wurina da har zaka ganni a masoyina ka roki alfarmar in fita hanyarshi, ko Mansur ya rabu da 93 ni ba zan zamo wani sabon al'amari a wurina ba don sunnar magabata ya bi zan kumaci gaba da girmamashi tare da soyaiyar da muka yi wa juna saboda mun yi ta mun gama ta ba tare da ta yi min wani sanadi na wulakanci ko tozarta ba a wurin jama'a, na kuma gode maka da baka yi amfani da kuskurena da wautata da sakarcina da sokoncin da na rayu a ciki a dalilin bani da mafadi ya sani nayi a kanka ba da ka yi amfani da damar da wadancan abubuwan suka sanyani na baka a kaina da ka yi dalilin da na kara zama shashasha sokowa sakarya waçce ta aikata kuskure a rayuwarta, kuskure kuma har abada, don haka duk abinda ya faru tsakanina da kai tun daga farkonsa har zuwa karshensa kus... Ban kai karsen maganar da zanyi ba sai kawai na ii kafafuwana sun zurma cikin kwatar dake bayana, nayi maza na kalleshi cikin tsananin bacin rai nan take kuma na sake dago idanuwan nawa suka hadu da na Mubarak dake yi min wani irin kallo, yanayin da na gani a tare da shi ya tabatar min da cewar ba ji nayi kama ba shine ya hankadani cikin kwatar da na zurma. Kar ki sake yin kuskuren kallon idona ki ce za ki yi min rashin kunya irin wanda kika yi min yau in kuwa ba ki ji kashedinda na yi miki to za ki gane baki da wayo, sakarya kawai sokuwa shashasha mara wayo 94 wacce rashinmafadi ya hanata sanin abinda ya dace da ita. Yana gama fadin hakan ya ja wani mummunan tsaki ya wuce yayi tafiyarshi ya barni cikin kwatar ko a jikinshi. Da kyar na iya zare kafafuwana daga cikin kwatar takalmana kuwa asararsu nayi don kafafuwan nawa kadai na iya zarewa, a hakana rinka diddingisawa na doshi gidan Yakumbo Halima cikin zuciyata dai ni kadai nasan abinda nake ji game da Mubarak, na tsaneshi na kishi na rinka jin wani irin ciwo a zuciyata game da shi, babu abinda ke kai kawo a zuciyata in banda na tunanin yanda zanyi in dau fansa a kanshi kan irin wulakancin da ya yi min, da dai ace so shi ne samu to da na tashi daga wannan unguwar na koma wata don in yi nesa da shi in dains ganinshi dan ya daena shiga harkokina. A haka na shiga gidan Yakumbo Halima, tana ganina ta kama yin salati, wane irin rashin dabara ne wannan Mero? In zaki fada kwata sai kuma ki fada da kafa duka biyu kamar wata yarinya 'yar karama? Ban iya ce mata komai ba kuka kawai na kama yi don daman daurewa kawai nayi na hana kaina soma kukan tun daga waje. Cikin hanzari ta tsame hanunta daga cikin kullin danwaken da take jefawa da sauri ta iso inda nake tsaye ina ta faman kuka. 95 Haba Mero haba Maryamu da so don kin shiga kwata kuma sai ki tsayakina kuka? Ai tsautsayi ne shi kuwa kin ji ance bai wuce ranar shi ba, bari in kwara miki ruwa a kafar in wanke miki dagwalon sai ki shige bandaki ki yi wanka ki canza kayan jinki da wasu. Har nayi wanka na fito na gama abinda zanyi duka na zo wurin Yakumbo Halima na zauna ina tayata jifan danwakenta idanuwana basu daina zubar da hawaye ba, na kasa gane dalilin bakaken maganganunshi musamnman gorin da yayi min kan fasa aurena da Mansur ya yi sunyi min ciwo da yawa. Rarrashi, banbaki da wayon da Yakumbo Halima tayi tayi min ya sani kwashe bayani duka na yi mata. Dama ashe zancen da nake ji a gari na bar yanzu baku rabu da juna ba gaskiya ne? Tsuru na yi ina kallon Yakumbo ashe kuskure nayi da na yi mata wannan bayanin, ashe da ma kadan take jira da ni, to kuwa ba zai barki ki yi aure ba kin ji na gaya miki ke ya hanaki aure ya tsareki a waje a cikin gida kuma yana tare da matarshi duk tsiyar da yake yi mata wanda ke sanyata zirga-zirgar yaji tun da dai yana kusantarta ya biya bukatarshi a tare da ita ai aikin banza ne karyar iya shege kuma yake yi wanda bai Son mata ai baya kusantarta indai har da gaske yakeyi yanzu da ta tafi kwanan nan iyayenta suka aiko a gayawaAlhaji Muhammadu cewar tana da ciki wata 96 biyu yayi musun cikin? Ba cewa sukayi sun janye sakin da yayi mata ba sukaje suka dawo da ita dakinshi kuma suna nan tare su na zamansu ana tarairayarta ana murna zata haifar m usu da ko ya, shi ne ke ba za ki yi zuciya ki kama mutuyncin kanki ki fita harkarshi ba sai ki je kina biye mishi kuna lalacewa tare... ta kama kuka irin wanda bai kwatantuwa. Jikina ya kama 6ari hankalina ya yi mummunan tashi ganin irin kukan daYakumbon keyi, na rantse aiki Yakumbo... kan in fadi abinda nake nufin gaya matan tuni ta rufeni da duka da hannaycnta duka biyu, rantsuwar karya zaki yi min saboda kin maidani shashashar uwa to ai ni da yaya Ramatu duk daya muke uwa daya uba daya muka tasha nono ta bani da kike nema ki maidani mara mutunci. Tana kuka take wannan bayanin. Tuni nima na shiga nawa kukan, ba don dukan da tayi min din ba sai don bakin cikin al'amarina da bakni cikin yanda na zamo gaba daya iyayena da jama'ar gari suka yarda da cewar lalacewa mukeyi ni da Mubarak, yaya Dija ce kawai na tabbatar ta yarda da maganar da nayi m ata na babu komai a tsakanina da shi don ta babans kuwa ba zan iya cewa koami ba tundaban taba jin ya bude bakinshi ya fadi wata magana ba balle in san a wane hali ya dauki lamarin. 97 Ban san abinda ta gani ba ko abinda ya faru ba naga maimakon dukan da take ta kai min da hannayenta duka biyu ta jawoni jikinta ta kankame da karfinta kuka mai yawa ta yi kafin daga bisani ta sakeni, ki yi aure Maryamu ki yi aure abinda kawai zan gaya miki kenan. Magaiar da ta fara yi kenan bayan ta gama kukan nata. Cikin sauri na ce mata to Yakumbo ba tare da na san wanda zan auran ba sai dai kawai don in kwantar mata da hankali. Alkawarin da nayi wa Yakumbo Halima na cewar zanyr aure ya sans himmatuwa wajen ganin na fidda mijin aure ko da kuwa wane iri ne babu maganar tsayawaduba cancanta balle a yi maganar zabe, aure kawai nake so in yi ko zan samu in fita daga zargin da ake yi min na akwai wani abinda ke faruwa tsakanina da Mubarak na lalacewa sannan yin auren nawa zai zamo dailin da zan bar unguwarmu in yi nesada ita in daina ganin Mubarak wanda a yanzu na tabbatarwa kaina da cewar in har akwai wani mutumin da na tsana a rayuwata a halin da nake ciki to shi ne na tsani Mubarak, na tsani duk wani abinda ya shafeshi, na tsani duk wani labari da ya danganceshi, musamman ma labarin matarshi da cikin dake gareta wanda kuma ya zamo shi ne labarin baba Lantana da take wuni tana bayarwa ta rinka fadin karyar banza karyar wofa, yana kinta yake kwabewa 98 a gabanta? Sai kuma ta ja wani mummunan tsaki ta ce, ku dai da ya mayar sakarkaru ke da ubanli sai ku yi tayi ya rinka samunki yana rage gajiyarshi ta rana a kanki tunda haka kuka zaba. Rabon da in tankawa baba Lantana ko wani nata wata magana har na manta saboda abinda nake ji yafi karfin duk wasu maganganun na ta ciwo a raina. Rannan ina tsaye tare da wani sabon saurayi da nayi wanda inda ya biye min da ko kwana goma bai yi da fara zuwa wurina ba ya turo iyayenshi aka daura mana auren saboda irin karbar da na yi mishi da kuma za a tsareni a tambayeni dalili na na yin irin wannan bare-baren a kanshi abu guda da zan iya fadi kawai shine ba dan unguwarmu ba ne ina son aurenshi ne kawai don in samu in yi nesa da unguwar in banda haka babu wani dalili. Ina tarę da shi muna hira a kofar gidanmu sai kawai ga Mubarak tamkar daga sama aka jehoshi, gabana ya yanke ya fadi saboda ganin inda muek zaune ya tunkaro gauan-gadan nayi maza na kawar da kaina daga gareshi saboda irin kallon da na lura yana yiwa wanda muke tare da shi din wanda shima na gane ya tsargu da Mubarak din. Yana isowa sai na ji ya ce mishi, malaml afiya na ganka anan wurin? Da sauri mutumin ya daga ido ya kalleshi latiya? Ban gane tambayar taka ba, ya zuba mishi ido cikin natsuwa yana kallonshi, wannanai 99 iyalina ce baka ji abidna ke tsakanina da ita ba ne? Ya shiga waige-waige hankalinshi a tashe jin da ya yi Mubarak ya ce mishi ti din iyalinshi ce. Ai ban san matar aure ce ba ni asanina... Kan ya karasa bayanin ya yi maza ya ce mishi, bar nan kawai tun kafin abin ya kai ga ranka ya baci. Yanzu kuwa in ji mutumin, ko raina b a zai baci ba ma ai da sanina b za ni wurin iyalin wani ba, ita ta ha'ince ni ta boye min gaskiya, ya kama hanya ya yi tafiyarshi, nima na mike na shiga gida na barshi a wurin ban tsaya jin wata magana tashi ba. Ina gida akan gadona a kwance ina tunanin al'amarin cikin zuciyata dai nasan babu mutumin da yake shiga harkokina yake takuramin yake bata min rai yake sanyani bakin ciki a rayuwata irin Mubarak sai daiban san yanda zanyi da shi ba tunari mai tsanani na shiga ciki har daga karshe na yankewa kaina hukuncin komawa gaban Yakumbo Halima in gaya mata abinda ke faruwa don kar ta dauka ban ji maganar da tayi min na inf ito da miji ba. Na gyara na yi kwanciyata da tunanin na kaiwa Yakumbo Halima bayanin abinda Mubarak kc yi min. Ina kokarin tilasta kaina yin bacci kenan sai na ji Asabe tana kwalawa sunana kira, cikin irin muryar tsoro ne ya kanani saboda sanin da nayi cewar ni da Asabe bama ko ga maciji. 100 Waiyo-waiyo dama dai kawai in mutum in huta da wannan wahalar. Zumbur nayi na tashi na zauna saboda jin maganar ta ta, me ya satieki haka Asabe? A tsorace na yi mata tambayar. Bata tanka min ba, waiyo-waiyo, abinda kawai take te faman fadi kenan. Na sauko gareta ina kokarin riketa don in tsaida murkususun da take yi a kasa cikin yanayi na tausayawa ina isowa garéta na gane lamarin ba karami bane, ya kuma wuce duk yanda ake zato don haka nace mata bari in kira miki baba Lantana don tazo ta ga halin da kike ciki in yaaso a kaiki asibiti. Tayi maza ta ce min u'u barta kawai kar ki kira min ita ke dai kawai ki taikameni ki kaini cikin kankon bola ki barni a wurin in ma mutuwar zanyi in mutu a can. Tausayin Asabe ya yi matukar kamani, haba Asabe daina fadin irin wadannan kalaman kankon bola a cikin tsohon daren nan ko mahaukaci ai ba zai dunfari wurin ba, na shiga share mata gumi da majina da hawayen dake ta dalala. Ki yafemin abubuwan da na yi tayi miki Mero satar kayanki da ua rinka yi ina sayarwa da kudinki da sharrin da na... Kai haba Asabe bar irin wadannan maganganu ai zanman tare ne. Ana cikin haka naga Asabe tayi rigingine ta bankade komai babu sauran kunya a tare da ita, tsoro ya sake kamani jikina ya dauki rawa cikin muryar kuka nace mata Asabe, don naga alamar bata cikin 101 haiyacinta, kan in kai kkarshen bayani na hango wani abu yana shirinf itowa da gudu na nufi kofa na 6alleta cikin rawar jiki da karkarwa na buga kofar da take ta baba Lantana da babana, tana jin bugun kofar da nayi sai na ji ta soma cewa, yauwa ai ga ranar da nake jiran zuwan nata nan ta zo ranar da asiri zai tonu, ranar da zaka gane shirunda kake kame bakinka kana yi a kan komai ba dabara bace, ai tun dazu nake gaya makaa wannan zirga-zirgar da akeyi ana ziryar bayan gida da kyar ne in ba nakuda ake yi ba, ni na dade ina fatan ganin an haifar maka shege a gidan nan, ba dai kwadayin abin duniya ya sa ka zuba mata ido tana yin abinda taga dama ba? Yaro ya ki aurenta ya kai gida amma a waje ya maida ita matarshi? To muje ka karbi haihuwar da hannunka don kar ka ce sharri aka yi mata ba a jikinta ya fito ba don haka nuje a yi kornai a kan idonka, kaga ta inda yalke fita muje mu je. Ina jin hakan nasan fitowar zasu yi tare don haka na tsaya a inda ana bude kofar babana zai ganni. Abin kunya ina jin gadonshi kukeyi malam tunda ba haka ai nayi ta gudun makashi baka yarda da shawarat bane yasa baka koreshi ba sai da ya sameka saboda bai damcka ba, muje nace muje kana ji ana ta gurnanin nakuda ka ki kayi kuzari sai wani jan kafa kake yi kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki. A na bude kofar mukayi ido hudu da babana, muje m ana kayi wani kerere ka tsaya min a hanya 102 kaki ka bani wuri in fita, abinda haba Lantana ke fadi kenan daga bayanshi saboda kasa motsin da ya yi a dalilin ganin da ya yi min a bisa da na tabbatar kuma shi ne da ni ya gani a cikin wani hali na abidna take gaya mishi watakila da ya yi faduwar da bai sake tashi ba don a haka ma tsinkewar da yayi ta kai duk inda ta kai. Kurdawa tayi ta bayanshi ta fito saboda ta kasa hakurin ya matsa ya bata wuri, tana ganina a tsaye tayi maza ta ja ta tsaya ta yi turus cikin tsananin kaduwa nan take tsoro ya baiyana a idonta, a'a to wake zirga-zirgar da gurnanin nakudar da ke fitowa. Ban ce mata kala ba balle kuma babana da ya zama tamkar mutum mutumi, to wane irin abu ne kuma haka mai nakuda tana tsaye kememe, da gani dai nasan kece kike wannan zirga-zirgar da gurnanin nakudar inma... Kan ta karasa maganganun nata masu kama da sanbatu sai kawai mika jiyo kukan jariri daga cikin dakin namu. Ina kallon yanda jiri ya debi baba Lantana ya yi wuji-wuji da ita kafin ya fyadata da kasa, tayi faduwar yan bori vato da mazaunanta, tsoro ya kamani saboda ganin irin faduwar da tayin, sai kawai na ga ta zabura da iyakacin karfinta ta yanka da gudu ta nufi cikin dakin namu. 103 Wato da ma shari ne abin? Watp ni za a kawowa iya shege? Dama da hadin baki ne tsakáninki da m atsiyacin likitan da yace min kaba ce da ke? Ni za ki kawowa tsiya? Ni za ki jawa magana? To ai kuwa yanzu za ki gane wautar ki don kuwa kasheki zanyi murus har lahira. Tana fadin hakan mulka jiwo-ibun Asabe da sauri Sallau ya fito ya fada cikin dakin; ba zaiki kasheta anan ba baba ba zaki yi mana kisan kai a gida ki jawo mana wata fitina ba, tunda dai har kin kaita gun likita ya ce miki kaba ce ai kin san da komai, lokacin baya ta kawo miki gasassun kaji kina ci kowa ai yana girban sakamakon abinda yake aikatawa ne. Da karfi Sallau ya jawo baba Lantana ya fito da ita waje, tana-kicin kwancewa daga gareshi tana kurma ihu da iyakacin karfinta, ka sakeni kawai in hadata ita da shegen dan natain murkushesu kowa ya huta. Wannan dai duk kina kokarin jawowa kanki wani abin magana ne kawai in har kika bari makwabta suka jiyoki suka gane abinda kike ciki da ma ki yi maza kin san abinda kike ciki da ita da dan nata kafin gari ya waye magana ta watsu. Daga cikin gidan baba Baidu muka jiwo muryar baba Sumaye tana cewa, kar makwabta su ji na nawa tunda ni naji? Ai ko ladan cikins hegen da tayi ta rokarwa ya'yan jama'a sai na baza wannan labarin, 104 barde a gonar wani sunkuru ya rufe naka, ddonki kam ya' yan jama'a ammakin kasa sawa naki balle ki gano abinda suke ciki, wai likita ya ce miki kaba ke gareta? Ta kwashe da dariya kafin ta ce, saboda ya gane ke din mahaukaciyar uwa ce shi ya sa ya yi miki hakan, kar kumaki ji da wai ba nan unguwar ba ko a wani wuri na ji 1abarin an tsinci mataccen jinjiri zan kai rahotonki don nasan halinki kin kuma furta zaki kashe uwa da da kat su jawo miki abin kunya, sai kace in da ana kashewa da ke kin kawo yanzu, ai yanda kika sa su Jkuka da bakin oiki lokacin da kikayi naki haka kema za á sa ki ki yi abinda,kukayi ne ai za a yi muku, shi kuma malam Habu Ubangiji ya yaye mishi abinda ya sameshi, yauwa duk inda naji an tsinci mataccen jinjiri nasan kece zan fada na kangon bola ma da aka gani kwanaki wa ya sani ko ke kika kaishi? Fitinannun mutane masu jawa mutane annoba iri-iri. Baba Sumaye tana rufe baki baba Lantana ta yi zumbur ta maike da sauri ta sake shigewa cikin dakin namu inda Asabe da dan jaririnta suke tamkar dai ace dama kasake tayi tana

Chapter 6 of 10