Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 10
ki gane ba Mubarak ne mijin da ya dace da aurenki ba, mijin da baya rarrashima me za a 70 yi da shi ne? Ke kanii kika ce min bai iya ramashiba, bai iya bada lakuri ba, bai iya fadin naganganun soyaiya ba, to ai Mansur ya iya wadannan duka yana kuma sonki domin ko bayan aukuwar wadannan al'amuran ya zo gidan nan sau biyu yanzu ma don baya nan ne yasa kika ga shiru, to don me za ki damu kanki, akan mutanen da suka ki mu? Kin mu fa suka yi sun kimu ne saboda sun rainarmu in ba haka ba wane irin wulakanci ne haka su zargi lalacewa tsakaninki da dansu sannan su barki su aura mishi wata? Wannan wane irin son kai ne wannan? Wannan wane irin rashina dalci suka yi mana? Bana sonsu, bana son dansu, bana son duk wani abin da ya shafesu. Tana fadin maganar tana kuka, nima kuma ina kara jin tsanar Mubarak da iyayerishi da duk wani abinda ya shafeshi cikin raina. Assalamu alaikum, wai a gayawa yaya Dija tanna da bako a waje. Sau biyu yaron yana shigowa yana fadin irin wann an maganar a tsakar gida, tana jinshi bata tanka mishi ba. Yaya Ibrahim ne ya fito daga úakin su yana yi mata magana, anene bakon na ki da yake wajen? Mubarak ne kuma bana son ganinshi, Eai yi magana ba ya fita wajen sai kawai gasu sun shigo tare, falon yaya Dija ya shigo da shi. 71 Sannu da zuwa Mubarak, ya nuna mishi wuri ta zauna shima ya zauna suka gaisa sosai har yana tambayar shi anyi hidima lafiya? Ya amsa lafiya lau to Ubangiji ya sa alheri a ka hada ya amsa main. Jin shigowar tashi ya sa yaya Dija ta matsa kusa da bakin kofar dakin nata ta labe bayan labule suka gaisa ba tare da sungajuna ba, itarna tayi mishi murnar auren nashi sai dai ita kam bai amsa addu'ar da tayi mishi ba, a hankli cikin natsuwa ya soma yn amgana wanda yake kamar dama ya samu na gaya musu abinda ke ranshi watakila don ya wanke kanshi. Mafi yawancin lokaci mutum yana shiga cikin wani irin al'amari da bai taba zatarwa kanshi ba, al amuran da suka faru a cikin watannin nan uku zuwa hudu da suka wuce wadansu irin abubuwa ne da babu wani abin da zamu ce sai dai mu kara hakuri mu kara yarda da cewar komai yana tafiya ne bisa tsari da rubutun kaddarar da take keddara mana komai. Yaya Ibrahim ya ce, haka ne, sai ya ci gaba da magana, ni dai gaskiya a Bangarena na shiga wani irin al 'amarin a kunci da damuwa, gami da bakin ciki da tsanani irin wanda bana fatan wani wanda ban sanshi ba ma ya samu kanshi a irin wanonan yanayin, duk wata fitina ina ganin kanar tana da sauki kwarai in har ta zamo babu fushin iyaye a ciki. Da sauri yaya Ibrahim ya ce mishi, kwarai kuwa fushin iyaye ai musiba ce mai hankali kuma baya 72 yarda ya zauna a irin wannan yanayin domin kullum fata muke mu rabu da su lafiya suna sanya mana albarka. Maganar da yaya Ibrahim ya yi ta zama tamkar susa ya yi mishi inda yake yi mishi kaikayi, da sauir ya ce, yauwa na gode da ka fahimce ni ina fata kuma itama yaya Dija tayi min irin wannan fahimtar halinda na samu kaina a ciki na fushin da'mahaifina ya yi da ni shi ne dalilin da ya sanyani karbar auren da suka ba ni don in samu in fita daga cikin wannan al'amarin amma ba yana nufin wani abu zai canza " bane tsakanina da Maryamu. Cikin natsuwa naji shima yaya Ibrahim ya soma yin tashi maganar bayan ya yi gyaran murya, to arna Ahmadin kayi haka ai ina ganin baka kiyayi bacin ran iyayen irin kiyayewar da ya kamata ka yi mishi ba, ci gaba da mu'amala da Maryam kaima kasan ba zai zamo karbabben abu ba a wurinsu domin rabuwa da ita yana cikin sharadin da suka sanya maka, ina ganin maimakon ka dage kan ci gaba da mu'amala da ita har hakan ya sake jawo maka wata mas'alar tsakaninka da su da rabuwa da ita kawai kayi tunda ai ka riga kayi aurenka itama ta fidda miji tayi nata, ina ganin wannan shi ne abidna zai fiye mana sauki domina I'amura sun riga sun faru marasa dadi masu bata rai da tayar da hankali, ya kamata ace mu dukan mu mu kiyaye sake aukuwarsu, don haka ina so in yi amfani 73 da wannan zaman namu in rokeka ka fita hanyar Mero ka daina bibiyarta ka barta ta samu natsuwa da kwanciyar hankalin da zata fuskanci al'amarin ta, kaima ka samu natsuwa tare da iyalinka don ka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da iyayenka. To amma yaya Ibrahim kana nufin don na kar6i auren da iyayena suka yi min sai hakan ya zama dlailind a ni kuma ba zan yiwa kaina nawa auren ba? Eh haka zaka iya yiwa kanka, bance ba zaka iya ba to amma kuma gaskiya ba Mero bace wannanm atar domin mun riga mun samu labarin komai don haka ina so in gaya maka cewar na rokeka ka fita hanyarta kawai. Ya ce to babu laifi na gode. Ya yi musu sallama ya mike ya fita. Yana fita daga gidan yaya Ibrahim yakirani din na zauna cikin ladabi ina sauraronshi, kin ji yanda muka yi da Ahmad, na ce mishi ch, ya ce to ki fitar da miji ki yi aure kinji ko baki ji ba? Na ce mishi naji, zai fitar ko ba zaki fitar ba? Na sake cewa zan fitar. Ya ji dadin yanayin da na bashi amsa r a ciki, to Ubangiji ya yi miki albarka, na ce amin. Ya tashi da nufin fita yana magana, dagan an zuwa rana itayau ina so in ji bayani wurin Dija, na ce mishi to. Da daddare rannan ina kwance kan gadon yaya Dija yayin da ita kuma take wurin mijinta bacci ne yaki daukata na rasa abinda ke yi min dadi, cikin 74 raina na sani ni da kaina na gayawa yaya Dija cewar da Mubarak din da kuma Mansur duk daya ne wanda duk aka bani zan zauna da shi, amma a yau sai na kasa jin irin kuzarinda nake tare da shi a wannan lokacin da nayi wancan maganar, gaba daya dai halin da nake ciki nayi jarumtakar daina hana kaina yarda da cewar son Mubarak ne yake haddasa min abubuwa da nake fama da su na faduwar gaba da kauracewar bacci a idona, na yarda da cewar bacin rai ne na wulakanci da tozartawar da aka taru aka yi min. Washegari da safe ina kicn ina kokarin sallamar ya'yan yaya Dija su tafi makaranta saboda bata fito ba a dalilin ta san ina gidan, ina cikin aikina sai kawai na jiwo muryar matar wan yaya lbrahim tana cewa wata da ban sheda ta ta muryar ba, lalle ne su hadu su je wajen uwar mijinsu su kai karar yaya Dija kan neman da take yi ta jawo ni ta dawo da ni nan gidan da zama bayan duk abin kunyar da na akata na jawowa iyayena da yan uwana abin magana, tana nema sai tayi dalilin da na shafa m usu na bata musu sunan gidansu, in mu bamu damu da abin kunya abin magana ba saboda bamu da yawa ba wasu dangi ne da mu ba ai su nan gidan dole su ji tsoron abin kunya ko don yawansu. Ko kadan ban ji dadin maganganun da na ji ba to amma kuma sai na kudurawa raina kame bakina in yi shiru ba tare da na gayawa yaya Dija abinda naji ba, 75 iyaka dai kawai in hanzarta barin gidan in koma namu tun ban haddasam ata wata fitina ba, don nasan in taji ba zata yarda ba aurenta kuma aure ne da bashi da wani tarihi na wata fitina mai karfi sai danabin da ba za a rasa ba, kawai wanda zo mu zauna zo mu saba ke haddasawa musamman ma kuma da yake kusan a hade suke da iyaye da 'yan uwa a wuri daya, ginin da yayi baisa ya yi nesa da su ba don haka ina gama aiyukan da zanyi mata sai kawai na yi shirina na jira ta fito nace mata za ni gida, tayi ta tambayata menene ban ce mata zan kwana biyu ba? Nace mata eh amma ai na fasa saboda zan bar baba shi kadai a gida. Ta gallamin harara, baba shi kadai m atarshi fa? An ce miki zaki yi ta zaman gida ne saboda baba? Kema zaki yi aurenki. Nayi dariya kawai na kama hanya na tafi. A gida ina zaune ne kawai bana komai bana kuma zuwa ko ina, ba makarantarboko babu ta allo, bana kuma fita ko ina ko daidai al'amura sun dan lafa na wakoki da rashe-rashen mutuncin da akayi tayi min a baya, na dan samu sauki na dan samu saukin ciwon da zuciyata take yi min a kan Mubarak saboda na daina yarda ina zama in bata lokaci wajan tunanin al'amufanshi, ina kuma kiyaye duk wani abin da zai hadani da shi ko da kuwa hango ni daga nesa tunda asan har yanzu ban samo maganin faduwar gaban da 76 nake fama da shi ba a duk lokacin da' na hangoshi ko na ji maganarshi. A cikin gida dai ni da su baba Lantana muna cikin wani hali ga babu ga kuma rashin dadin zama komai a tsaye yake cak, bani da komai nå abin amfani ba ni kuma da ko kwandala, rabon da in yi rashin irin wannan har na manta. Watakila tun ban isa komai ba tunda in ma ban samu an yi min a gida ba to dai bana rasawa zan samu wurin Mubarak ko Umamnshi, to yanzu babu su baban nawa kuma ba shi da shi, ta lafiyar shi ma ake yi bata maganar runfa ba don ma anyi sa'a Sallau yana matukar taimakawa a kan bude rumfar babana yana cikin wani hali na rasa karfi mai yawa a tare da shi, a hakan kumna wai baba Lantana bata tausaya mishi a bata dai a bata kawai ta sani ko da kuwa babu abinda take so a baka din kusan kullum zaka sameshi ne cikin jiri ko ciwon kai, amma hakan baya hanata zama tayi ta gaya mishi bakaken maganganu ni kam ma sai nake ganin tamkar karbem ata fili da Alhaji Nalami yayi ba kairamin kara mata son kudi da neman tashin hankali yayi ba. Rannan ina jinta ita da Sallau da ya dawo daga runfa in da ya danyi aiki, bani kudin nan duka nace maka ka bani su, a'a baba in na baki su dukan gobe fa? A ci yau a ci gobe ai shine cin rana daya, kumburin ciki ne. Nace maka ka bani su, ina ce dai rumfar bata gidanku ba ce? Cikin natsuwa ya ce mata, 77 eh baba bata gidanmu bace amma shi mai rumfar ai bai nuna min hakan ba don haka zan tattala mishi abinda yake ciki ko na samu nima in koyi sana'ar tunda dai ke baki kaini makaranta ba baki kai ni wajen koyon sana'a ba. Ina daga kwance ina jinsu ko motsawa banyi ba, cikin zuciyata na co kunfi kusa in kuka ga dama kuc inye su duka a yanzu. Ganewar da nayi Sallau da iyakacin gaskiyarshi yake mu' amala da baba na yasa nima ko kadan bana sa mishi ido kan cinikin da yake yi komai yace min kuma sai ince mishi to, bana dai sake mishi sosai don haka sai muka koma m u'amala ta matunci kawai da ganin girmanjuna, a wannan lokacin babu abinda yafi tsayamin a ai irin in kwanta da daddare in tuna gobe da safe bani da kudin da zan sayawa babana abin karyawa gashi a yanzu baba Lantana sai tayi kwana da kwanaki bata yi girki ba, wai abinda ake batan baya isa a yi girki, na kuma san har da daina yarda da ayi girki aci ni a hanani da na yi ya kara sata daina yin girkin. Kan hakı yasa naje na samu Sallau a rumfar baba na ce' mishi Sallau. Yayi m aza ya taso, anti Mero ai da kin jirani a gida ma zan zo. Nace e babu damuwa so nake mu yi magana. Ya ce to, nayi mishi bayanin da ya kawo kullum in kayi ciniki ka rinka cire kudin da zaka rinka saro kayan gobe abinda ya saura ka 78 kasashi biyar kai daya baba daya baba Lantana daya ni daya, dayan kuwa a rinka sakashi cikin bankin karfe dake cikin rumfar nan, saboda bacin rana, ya ce min to. Yana dawowa kuwa da daddare ya zo ya yi min bayanin abin da aka yi da yanda ya yi kasafinsu. Yaya Dija tana iyakacin kokarinta a kan mu sai dai kuma ita din mata ce da bata iya sana'ar komai ba duk wani abinda kaga tana yi in dai na kudi ne to daga aljihun mijinta ya fito ko kuma daga abinda ta iya tattalawa na canjin cefanenta don haka sai na kudurawa kaina ba zan taba zama bani da abin yi ba, ba zan zauna bana sana'a ba, ba zan iya zama sai an bani ba, zan nemi kudi ko don in yi hidimata da ta babana ba tare dan a tsaya jiran an bani ba sai dai a sana'ar ban san wacce zan yi ba. An wayi gari yau tun asuba zuciyata take ta kai kawo kan al'amarin Asabe wacce na lura tayi matukar canzawa duk wani abin da za ta yi ta kan yi shi ne ba a yanayin da ta saba ba, hatta zamanta da tashinta amma wai har yanzu baba Lantana tana kallonta bata gane abinda take ciki ba ko kuma ta ganę tayi shiru ne kawai oho. Tsawon lokaci ina wannan tunanin kafin na yi maza na kawar da wannan tunanin na koma kan nawa al'amarins aboda ganewar da nayi cewar in na tsaya kan nawa mas'alolin ma kawai sun isheni ba sai naje 79 ina shiga harkar da ba tawa ba ce, don haka na koma lissafin tawa damuwar gaba daya kayan sakawar baba sun kare sunyi datti bani da ko sabulun da zanyi mishi wanki, nmaganin da yake sha yana gab da karewa babu kudin sayen wani ga zuwa asibitin shima ya zo da dai ace so shine samu to da na samu wani abinda na rinkayi ina samuz ko da kwaho kwabo ne don in rinka aiwatar.mana da abubuwanmu ba komai ya taso sai naje na gayawa yaya Dija ba. Gari ya waye da safe nayi abubuwan da na saba yi mana ni da babana na yau da gobe na kai mishi ruwan wanka na dawo kenan sai ga yaro dan makwabta ya shigo, anti Mero wai inji Mansur wai ki zo. Na daga ido na kalli yaron yanda ya ambaci sunan Mansur din gatsu bai yi min dadi ba kamar in yi mishi magana sai na fasa na kame bakina nayi shiru cikin zuciyata dai na tabbatarwa kaina da cewar gimamai na gaba yana da dadi. Gyalena na dauka na yafe jikina na kama hanyar fita zuciya'a sai faman harbawa take yi don rabon a kirani inje har na mance da lissafin. Yana tsaye ne cikin zauren gidanmu kanshin shi ya gauraye ko ina. Kunyarshi ta yi matukar kamani na kasa sakewa a gabanshi saboda sanin da nayi ya ji komai yana da labarin duk kan abubuwan da aka yi tayi har wakokin da nayi ta fama da su duk nsan ya jisu, amma hakan 80 bai hanashi zuwa wurin yaya Dija ba gashi kuma yau a gabana, me yake nufi? Yana nufin har yanzu yana kan bakanshi bai fasa aurena ba kamar yanda yaya Dija ta gaya min kome? Kan in kai karshen tunanin nawa sai naj1 ya ce min, ran yan mata ya dade ina kwana? A kidime kwarai na nemi wuri na tsuguna, yan mata yake k irana bayan tun ba yanzu ba na saba jin mutnae masu zargi suna fadin ai ni din tun ba yau ba na salwantar da budurcin nawa, yana ganin an tsuguna shima ya nemi wuri ya tayani tsugunawa. A tsarge kwarai na soma amsa mishi gaisuwar tashi tun bayan faruwar al'amuran da suka farun yau ne ranar farko da ni da Mansur uka hadu a wuri daya. Ya ya Dai Maryam? Yaya jikin baba? Na amsa mishi da sauki, 'yan maanganu kadan mukayi hirar tamu ba ta yi wani nisa ba watakila don bamu saki jiki ba tamkar dai ace muna jin kunyar juna. Takardar naira ashrin guda biyu ya. miko min wato naira arba' in ko ince fam ashirin, hannu biyu na saka na karba tare da yi mishi godiya, bai tsaya jin wata magana ba ya ce min, zan tafi sai na dan huta na fito za ki ganni, na ce mishi to. Yana tafiya na dauki takardar naira ashirin guda daya na nufi shago don yi mana sayaiya, babu wani abin da ban saya ba na kayaiyakin amfani har man shafawa da na dade bani da shi na saya, sai dai 81 maimakon 10-0-6 da Mubarak ya koya min shafawa sai na koma man shafawa na kamfanin shield don dai in samu in kara fitar da duk wani tunanin shi daga cikin zuciyata. Na shigo gida na kama wankin babana cikin kuzari na gama nayi nawa nayi mana guga na adana mana kayanmu na gama ba tare da gajiyar aikin ta dameni ba can cikin zuciyata nace kai babu tana cikin mas'alolin da ke addabar rayuwar dan adam matukar dai shi din mai lafiya ne. Kudin da na samu wurin Mansir sai suka wattsakar da ni na samu kuzari mai yawa a tare da ni, nayi duk wani abinda ya dace, ranar asibitin babana ya zo mukaje muka daow na saya mishi magungunan da aka rubuta ba tare da na jira ko gayawa yaya Dija ba, sai da na gama komai ne sannan naje na gaya mata yanda aka yi. Tun daga wannan lokacin da Mansur ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Ghana sai gidanmu ya zamo nan ne wurinshi sai dai in baya nan, tun ina jin kunya ina nonnokewa saboda al'amuran da na san ya sani ya ji game da ni har na wattsake muka shiga harkar soyaiyar na samu natsuwa da kwanciyar hankalin da na dadeb an samu ba, na murje na yi kyau saboda nayi sa'a shima man shafawar shield din ya karbi fata ta. 82 Yaran unguwa sun yi matukar fita harkar yi min wake-wake sun yi sun gaji sun hakura, dama hausawa Sunce wai watan wataran din guda daya ne in naka ya mutu sai kuma na wani ya kama. Mu'amala ta da Mansur ta yi amntukar sama min natsuwa da kwanciyar hankali a tare da ni, har na samu karfin da na ji zuciyata ta daina faduwa don na hango Mubarak ko na ji wata magana game da shi, a wannan lokacin sai naji a shirye nake in har Mansur ya yi maganar aurena in amince don kuwa na yarda na sakankance da cewar shi din miji ne da zai kula da 1yalinshi ya samar musu farin ciki da natsuwa da suke bukatar samu. Ina zaune a dakina hutawa nakeyi saboda dawowa ta kenan daga asibiti don yau ma na raka babana ganin likita saboda gaya min da ya yi cewar ya yi kwanaki uku cur bai samu yin bacci ba da daddare, hutawar da nake yi tare da kara tuna kalmomin da likita ya yi game da jikin nashi sai naji yaro yana magana a tsakar gida wai anak iran Mero a waje. A zuciyata na ce Mansur kenan shi da yace in shiga gida in huta sai an jima zai zo me kunma ya tuna ya sashi fasa hakan? Na mike na fito na wuce baba Lantana tana fadni, o'o shi wacan ya ja jiki wannan Kuma ya maye gurbi ya samu an bashi wuri ya zama shi kadai. 83 Ban kalleta ba na yi wucewata na fita, ban ganshi a zaure ba kamar yanda ya saba shigowa ciki don haka na leka kofar gidayasan na zo ina lekawa sai kawai mukayi ido hudu da Mubarak, ya sha kwalliya cikin kananan kaya ya yi kyau sai dai ban ji faduwar gaba a tare da ni ba, dadi ya kamani na kara gamsuwa da kaina. Yana ganin naja baya ya biyoni cikin zauren, sunkuyar da kaina nayi don in kaucewa idanuwan da ya tsareni da su, zuwa nayi in rokeki ki yi min wata alfarma Maryam. Na dan yi kokari na daga ido kadan na kalleshi saboda maganar tashi da yanayin da yayi maganara ciki, alfarmar me ni kuma zanyi maka? Na rokeki na kuma sake rokonki ki yi min wannan alfarmar ki fita hanyar Mansur bana so ina ganinki tare da shi. Cikin natsuwa hankalina kuma a kwance na buda bakina na ce mishi, gaskiya ba zan iya ba. Maganar tawa tayi matukar bashi mamaki saboda abinda na gani a tare da shi, cikin wani irin yanayi ya tambayeni, ba za ki iya ba? Shiu nayi ban bashi amnsa ba, ban kuma sake daga idona na kalleshi ba, saboda har yanzu ina jin nauyinshi a zuciyata. Me na yi miki Mero? Me nayi miki haka da kike nemaki sani bakin ciki? Ai ban cuceki ba, ban zalunceki ba, ban yi miki wani laifi ba, in kumakina gani nayi to gaya min shi in abki hakuri Mero, ai in 84 rai ya baci hankali baya bata a kowane hali muke ciki ko muka samu kanmu, bai kamata ki rufe ido ki kasa ganin gaskiya tsakanina da ke ba. Juyawa nayi da nufin shiga gida in barshi a zauren, ban san yanda akayi ba sai kawai na yi kicibis da baba Lantana a kusa da bakin zauren watakit da shigowa zatayi taga abinda muke yi, tana ganin Mubarak ta shiga salati tana tafa hannu tare da fadin, yau ga abin da mamaki yau ga abin al'ajabi, yau ga wata musiba da ta addabeta ta addabi sauran jama'a, ashe ba iyayenka sun yi maka aure na rufin asiri don ka fita hanyar wannan yarinyar ku daina lalacewar da kuke yi ba, haba wannan wane irin al'amari ne shi? Aure baifi wata shida ba masifar ka ta sa kullum yarinya tana kan hanyar yin yaji ta tafi a dawo da ita, ta tafi a dawo da ita, to kar ka ji da wai zan wanke kafata inje har gidan iyayenka in kara yin kashedi tunda na san su ma ba son mu'amalarka da ita suke yi ba tunda ina da labarin komai sai da ka yarda da sharadir da šuka sanya maka na fita hanyarta sannan ne suka bar ka ka dawo suka kuma yi maka aure na rufin asiri wanda a yanzu kake wulakantawa ko da yake ba haka kawai suka barka ba 'yarta ai babu abinda ba zata iya ba. Wuceta nayi na shiga dakina na yi kwanciyata a kan gadona sai na ganta itama ta dawo na tabbatar tafiya yayi ya barta. 85 Wunin ranar nan bakin baba Lantana bai huta ba fadi suke haka kawai basu shirya yarinya ba sun kunsota sun kawo sun ajiye mishi ba dole su da ita su yi ta ganin abinda basa so ba, tunda ya riga ya saba da tsome-tsome ai zama da shi kuma sai an shirya, Maganar tayi matukar watsuwa ta yanda har Mansur ma yazo ya sameni hankalinshi a tashe, ranshi a bace, me ya saura ne tsakaninki da shi kuma? Na rasa yanda zan yi na rasa abinda zan gaya mishi saboda bacin ran da na gani a tare da shi, don haka na kama yi mishi kuka, kuka kuwa mai yawa irin wanda na kwana biyu ban yi ba. To menene kuma na kukan hakan? Ya soma yin maganar a yanayi na sanyin jiki alamar bacin ran da ya zo da shi din ya kau, to ni me nace miki da kike wannan kukan? Kinga share hawayen nan ki ji abinda zan gaya miki, to ai kuma na gane so kawai kikeyi raina ya baci shi yas akike ta kukan, in ba haka ko ma menene nace ki yi hakuri ki yi hakuri ina ce shi kenan zance ya kare. Kinga tunda abin nan ya zama haka ana nema a rinka kai kawon maganganu a tsakani to ina ganin gara kawai a kawo karshen al'amarin gaba daya in kina dakina da wani wanda ya isa ya zo yana Rananan maganganu ne a tsakani? Don hakan ni in kin yarda kawai a shirye nakwe in je in samu babana ya dawo 86 ya sake yin amgana da baban nan gidan a daidaita a sanya lokacin auren mu kome kika gani. Lokaci mai tsawo na dauka ban ce mishi komai ba har ta kaima ya sake tambayata, ba ki ce komai ba Mero ko kuna da wani tunani ne? Na sunkuyar da kaina kasa kafin nace mishi, kai ne dai nake ganin kamar ya kamata ka kara tunani akan maganar tunda ka sani sarai an fadi maganganu da yawa a kaina har yanzu ma ba a daina ba tunda ga ma wanda aka je har gidanku aka fada kwanan nan in... Ban karasa zancen nawa ba ya yi maza ya katseni, yanzu ina amfanin wannan maganar da kikeyi in dai ba so kike sai döle kin sa raina ya baci ba? Shiru nayi bance mishi komai ba, kar ki sake kawo min irin wannan maganar bana so. A hankali cikin natsuwa na ce mishi, to kayi hakuri. Dadi ya kamashi saboda hakurin da na bashi, ya dan gyara tsayuwa kafin ya ci gaba da magana, shi baba yana dawowa zanje in same shi da maganar. Na ce Ubangiji ya dawo da shi lafīya, yayi maza ya ce amin Maryam. Kafin babansu Mansur ya dawo wata irin lafiyaiyar soyaiya mu ka shiga, ka'ida ne kullum sai ya zo ko da rana ko da daddare, wataran ya zo ya sake dawowa, in na ce mishi baka riga ka zo ka dazu ya ce ai wata magana ya tuna da ya manta dazu da ya zo din bai gaya mini ta ba. 87 Rannan muna hira ni da shi tattaunawa muke yi irin ta fahimtarjuna, ra'ayinshi yake fada kan irin tsarin da yake ganin zan gudanar a gidanshi wanda hakan yake matukar taimakawa ma'aurata bayan an yi aure. Kin fa san 'yan uwane da ni masu yawa ina fata zaki yi hakurin zamada su. Na yi murmushi na ce, insha Allahu. Can cikin zuciyata kuwa tunani nake yi ni da nake rayuwa cikin kewar 'yan uwan miji zasu isheni har in kasa yin

Chapter 5 of 10