Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 10
in je in shedawa yaya Dija labarin aurcn Mubarak da naji, garin ya ki wayewa nisand aren ya kai matukar nisa duhun daren ma ya kai iyakacin duhu, gani nake tamkar in naje na gayawa yaya Dija tana da wani taimako da za ta yi min ko wani amfani da zata yi min, ko wani amfani da gaya mata zai amfanar da ni, waiyo waiyo waiyo abinda kawai nake iya ji yana fitowa daga cikin bakina kenan, saboda tsananin zafin da zuciyata ke yi, da kyar na samu garin ya waye. 53 Muna hada ido da baba Lantana a tsakark gida ta saki wani irin lallausan murmushi wanda rabon da in ganta tana fara'a tun ranar da Nalami ya karbi takardar filinta ya tafi, muna hada idon sai ta yi dariya ta ce, anya ashe kema kin ji labarin, ta sake sakin wani lafiyayyan murmushin kafin ta ce, uhun in dai da namiji ne ai kuka ba ki ma fara shi ba tukun balle ke da kika wulakanta jama'a a kanki ai kadan kika soma gani. Ban tanka mata ba na sa kai na fita gidan yaya Dija nake nufin zuwa. Ina fitowa daga gida na kara rudewa na kidime jikina ya dauki rawa karkar kar, cikin hanzari na juya da baya don in koma gida, amma saboda tsananin firgitar da nayi maimakon in shga gidanmu sai na smau kaina a zauren gidan su baba Sumaye, tsugunawa nayi a zauren cikin wani irin rudani, cincirindon mutanen da na hango a kofar gidan nasu Mubarak ne ya yi matukar razanani tafiya daurin auren nashi za a yi ko kuwa har sunje sund awo ne? Ban kara sanin irin rudewar da nayi ba sai da na ganni durkushe gaban baba Sumaye ina kuka alhalin ba abinda nayi nufin yi kenan ba. Za ki yi kuka mana Mero za ki yi kuka kai me sonki ma ai zai tayaki zubar da hawaye, wadannan abubuwan da suka faru dole ai ba kananan abubuwa bane ko ni din nan nayi kuka nayi addu'ar ubangiji ya jikan Ramatu da rahamarsa sanda akayi bikin Dija da 54 yake tana raye ai ba a yi haka ba shiru akayi komai aka gama cikin rufin asiri da mutunci su na murn amuna murna, kema maraicinta ne ya ja miki shi ya sa bana jin zafinki sosai bacin raina daya ne da kikaje kika bashi kanki to ga abinda gari ya waya, yanzu waye a kasa? Waye kuma a wulakance? Babu amfani in tsaya ina yiwa baba Sumaye bayani kan cewar banyi abinda ake zargina da aikatawa ba, tunda nasan ba yarda zata yi ba don haka sai kawai naja bakina nayi shiru ina sauraron abinda ake gaya min. Ahmad Mubarak zai yi aure don yana son daidaitawada m ahaifinshi, yin aure da kuma alkawari na zai fita daga lamarinki gaba daya su ne ka' idojin da ya yarda da su kafin shi Alhaji Muhammadu ya yarda ya yafe mishi laifuffulkan da ya yi mishi, kema kuma don baki da mai taimakon kuruciyarki ya doraki a kan hanyar da tad ace ne ya sa aka barki kina wannan kai kawon ana yi miki wadannan wakokin na shakiyanci da iya shege, ni dai banga laifinsu kan abinda sukayi ba sun mutunta dansu ne shi da ai daraja ne gareshi sannans hi Alhaji Muhammadu shi kadai ke gareshi in dai a kan da namiji ne sannan ya' yanshi duk mata ne abinda ya 6atamin rai kawai shine da basu tausayawa maraicinki ba in ba haka ba komai kikayi ai kuruciya in ya hadu da maraici lamarin ba karami bane sai gyaran Ubangiji, to saukia Sunce bai zama dole a ce da dansu kadai kika lalace 55 ba don haka a matsayinsu na iyaye ya zama musu dole su tsaya su ga yayi aure mai tsabta don neman Zuriya mai albarka. A zuciyata na ce wato ni in an aureni ba zaa samu zuriya mai albarka ba saboda tunanin da sukeyi na na riga na lalace? To in ni a lalacen nake ba da dansu aka ce na lalacen ba? Wato in ma da dana baiwa Mubarak kyautar budurcin nawa ya karba irin hukuncin da za su zartar a kaina kenan? Tambayoyin da suka rinka kai kawo a cikin zuciyata kenan kafin lokacin da na katse maganar zuci na koma sauraron abinda baba Sumaye ke gaya min. Ai ita uwar goyon nashi, nayi maza na daga ido na kalleta saboda ban gane maganar da take son yi ba, uwar goyon wa? Cikin natsuwa ta ce min shi Mubarak mana, na sake kallonta sai ta shiga yi min bayanin saboda ta gane abn san komai ba kan maganar da take nufin yi min din. Ita Hajiya Ummulkairi ai ba ita ce mahaifiyarshi ba, na azro ido ina kallon baba Sumaye cikin tsananin mamaki, ban taba kawo irin wannan tunanin ba cikin raina, saboda ban taba tunanin akwai wata kyakkyawar mu'amala tsakanin matar uba da dan miji ba balle har aje ana samun dama ko shagwaba irin wacce na saba gain Mubarak yana yiwa Ummanshi ita kuma ta bar komai da takeyi tayi ta tarairayarshi. 56 Mahaifiyar Mubarak ai Hindatu ce budurwa ya aureta tazo ta haifeshi shi kadai zaman yaki dadita tsallakeshi ta yi tafiyasta tunda ta tafi kuwa ban sake jin ko da labarin ance ta zo ganinshi ba, ina ganin kuma sanda ta barehi baifi.shekara guda ba a duniya don sansdin mutuwar, aren ne. ya zama sanadin yayeshi saboda shi uhen ya ce ba zaa tafi mishi da shi ba, sai ya baiwa ita Ummulkairin shi da yake mata ce mai hikima sai ta sa hannu biyu ta rike irin rikon da ko ya'yanta bata yiwa haka ba, bata bari mummunan zaman da sukayi da uwarshi ya shafeshi ba. Na sake kallon baba Sumaye saboda tsananta mamakina yayin da ita ukma ta ci gaba da bani labarin da ban sani ba. Shi Alhaji Muhammadu ai ya auri mata da yawa a sanina nama akan idona ina ganin sun kai biyar, iyaka dai mafi yawancinsu basu haihu da shi ba daga ita Ummulkhairin ce sai A'indatu su ne masu 'ya'yan, ita Ummulkhairi ya'ya mata uku su ne su Kaltume ita kuwa dama ba budurwa ya aureta ba bazawara ce ta ma haifi 'ya'ya biyu a can wani gidan, a cikin jikokin ta na can gidan nema yanzu aka baiwa Mubarak din guda daya, ai Rumasa'u ce yarinyar da zai auran. Ban san yanda akayi ba sai kawai na tsinci kaina da tsanar Mubarak da Ummanshi da babanshi da ma i ta Rumasa' un tunda na santa na saba ganin tana zuwa gidan sai dai ban taba sanin alakar dake tsakaninsu 57 ba da ya wuce na 'yar babbar yarsu ce na fassarasu a matsayin wadansu irin mutane mayaudara marasa adalci wadanda basu san kowa ko komai ba in banda kansu. Shi da ai darajanta shi ake yi a adanashi a yi tattalin darajar shi da mutuncinshi baka barin shi ya wulakanta a gaban jama'a balel ya je yana lalacewa masoya da makiya suna kallo wasu na bakin cik wasu na madalla, shi Alhaji Muhammadu ya yi nufin adana danshi ne don ba zai yiwu ya zuba mishi ido yana nema ya shiga wani al'amari ba, ita kuwa Ummullkoiri sai tayi amfani da damar da tas am wajen oshi jikarta ya aura, kunga ai ya kara zama nata a. hakan kuma sai ta kara samunshi a hannunta kamar yanda hikimarta tasa ta samu mijinta, to shima malam Habu da. samun wani yayi ya daura miki aure da shi ya kaki dakin mijinki da ya fi ye mishi barinki da da ya yi ana yi miki wannan wulakancin da tozartarwar, to bai yi ba bai kuma da mafadi abokiyar shawararshi daya ce matarshi ita kuma bata taba shawarta mishi wani abin ariziki ba sai na sharni za kuma ta ga yanda abin zai juya mata. Sallama nayi da baba Suimaye na fita na koma cikin gidanmu na fasa zuwa gidan yaya Dija. Ina shiga gidan naga baba Lantana tare da Asabe a zuciyata na tabbatar labarin auren Mubarak da ta ji ne ya dawo da ita. 58 Baba Lantana sai farin ciki take yi tana kyalkyalewa da dariya irin wacce ta dade bata yi ba, ita mace kowacce ai tana da kufu'in aurenta in kana da hankali kaima ba sai an gaya maka ba ni dama can nasan wannan yaron mubarak ba zai aureta ba yaro dan gata irin wannan ya rasa matar da zai aura sai ita, ai kema kin san ba zai yiwu ba, a yanda yake da irin arzikin ubanshi da îrin gatan da yake da shi habawa? Timatiri ne fa sana'ar ubanta kowa ya sani to ko basu lalace tare ba yaushe zai aureta? Ita ba kyau ba ita ba gata ba, ita ba dangi ba, ita ba asali ba haka kawai? Ai idonsu ya rufe ne kawai.a kan sun duniya ba don haka ba da tuntuni suka gane gaskiya da akayi abin nan da sai malam ya bi bayan Alhaji Muhammadu Nalami ya bashi hakuri a daura' aure to baiyi ba saboda shi agwagwane bin ya'yan shi yakeyi yanda suke so haka ake yi don haka nunawa ido ne. dama kuma ina addu'a na kuma san alhakina ne ya fara kamasu, nayi nufin yi musu abin arziki in rufa mata asiri duk da cikin da na san tana da shi na hadata da wanda nasan zai aurcta duk da cikinta don asiri ya rufü itæ da 'yar uwarta da taimakon ubansu suka watsa min kasa a ido, to ai mu na nan da su. Ta yi kwafa ta mike ta nufi dakinta. Asabe dai ba ta ce mata ba to balle kuma ni can cikin zuciyata dai mamaki ne ya kamani na yanda ita da bakinta ta zauna tana bayanin gata irin na Mubarak 59 a yau alhalin kullum abinda ta saba fadi shi ne karyar banza karyar wofi mu za a kawowa barazana, daga karyar ziki kawai haka masu kudin suke. A wannan lokacin sai baba Lantana ta zama bata da wata hira sai na Mubarak da iyayenshi tayi ta bada labarin arziki da irin alherin Alhaji Muhammadu a wurinta a kuma bakinta naji wai ashe sabon gini aka yiwa Mubarak din a can cikin gidansu banda haka kuma aka saya mishi sabuwar mota, don ya yi angwanci a ciki, ai kwarya tabi kwarya in tabi akushi sai ta fashe, karin maganar da baba Lantana ke wuni tan ayi kenan a yanzu. Asabe dai bata shiga harkata ba nima ban shiga tata ba ta dai dawo gidanmu gaba daya har da kayanta da na watsar sai dai kuma a yanzu ba abinda yake gabana kenan ba ina ji da kaina, ina cikin wani irin tashin hankali da rudanin da ban san yanda zanyi in fita daga cikinshi ba. Gaskiya ne duk wani abinda baba Lantana ta fada akan Mubarak da irin gatan da iyayenshi suka shirya mishi tunda aka fara bikin ummanshi ke bin gidajen makwabta da abinci dana sha ko kaje gidan bikin ko kar kaje za a kawo maka nau'o'in abincin da aka girka kala kala, ina ganin tamkar a unguwar nan gaba daya gidanmu ne kawai bata yiwa irin wannan aiken ba. A ranar da aka kammala bikin kuwa ina kwance a kan gadona ina jin dirin motocin abokan Mubarak 60 da suka rakoshi wurin babanshr ya şa mishi albarka kafin su rakashi dakina maryarshi don ance wai tunda aka yi abin yau ne ranar farko da baban nashi ya yarda zai ganshi. A wannan daren bana iya kwatanta komai game da halin da zuciyata ke ciki, iyaka dai kawai na san kasancewar Asabe a dakin nan ba ya hanani yin kuka ba tare ikuma da na damu da ta ni ko bata ji yi kawai nake yi don in samu in samu saukin ciwon da kirjina ke yi. Ban san abinda take ciki ba sai jinta nayi ta ce, uhun dama kin hakura kim yi shiru tunda taki mas'alar ma ai mnai sauki ce. Ban kulata ba itama bata sake ce min komai ba. A wannan lokacin sai na zama babu abinda nake sha'awa irin in ga mutane masu yan uwa da dangi a wasu garuruwan na nesa sai in rinka jn tamkar inama dai nice da tuni na tattara kayana na koma can inda suke dan in samu in samu seukin 6acin ran da nake ciki, wani lokacin kuma nice inama dai dai babana yayi min irin abidna baba Sumaye ayi sha'awar ace ya yi min na aurar da ni ga duk wanda ya ga damada yanzu nima ina can gidan mijina ko ina son shi ko bana sonshi kuma ai zan zauna darajar shi baban nawa ne ya bani shi sannan ko bana son nashi kuma ina ganin ba zan gamu da bacin ran da ya kai wanda nake fama da shi ba a yanzu. 61 Ana gama bikin Mubarak kuma sai na sake zama abin nunawa wurin 'yan mata da samarin da dama na rike musu wuya sai da ya gama da ita sannan yaje ya auro gal a leda, abinda suke ta fadi kenan ko naji suna fada suna dariya bana kulasu ko kuma su yista rera wakokin da makada da mawaka sukayi ta rerawa Muberak din da iyayenshia wurin bikin, sai da ta kai ma na sake daina fita waje saboda tsananin dana shiga cikin zuciyata na rika tambayar kaina sai mace? Kullun in za a yi maganar ta nashi bangaren da ya gama da ni din akan furta a yansyin da bai yi kama da aikata wani iaifi ba sai dai ma kaga tamkar ya yi wani alin gwaninta ne ko bajinta, a nawa bangaren ne za a yi ta a yanayi na wulakanta ko tozarta ko kurna muna ailkata wani abin kunya da wuiakantar, kai da na lura da kyau da yanayin da ake bayar da labarurrukan sai na gane shi Mubarak ma sha'awa yake baiwa mutane ga kuna gatan da iyayenshi suka yi nishi wanda mutanen unguw8r basu gsiiya da bayar da iabarin, bisa wanan lurar da nayi da abinda ya sameni sai nima da kaina na yardanwar kang da cewar ita mace ita ce mai yin abin kunya in har abin kunyar ta zo, ita ce kuma mai tozarta in abin tozartar ya zo, ita ce mai shiga ta wulakanta saboda ita ce mai rauni komai ya faru a kanta yake karewa, ita ce a kasa, ita ce take bukatar mutunci da kunya don su 62 zamo sutora a gareta, shi namiji karfi kawai yake nema. Dana kara tsunduma cikin tunani sai na tuna da wasu kalmomi da na taba gani a cikin wani littafi a hannun Mubarak, ga abin da suka ce: MAN IS BORN FACE AND EVERY WHERE HE IS IN SHAKKLE" Da na natsu na dawo cikin haiyacina sai na samu kaina a yanayi na godiyar Ubangiji da ya taimakeni ya rufamin asiri ya bana Mubarak karbar kyautar da na yi mishi, in tuna kaina in tabbatarwa kaina ni din budurwa ce gal a leda, shi ne abin da yafi komai sanyaya min zcuiyata a wannan lokacin. Bikin Mubarak da kwana goma na hangoshi tsaye a Rfoar gidansu a dalilin fitowar da nayi za ni shago don sayawa babana ruwan swan din da nake amfani da shi wajen bashi magani, ban san yanda akayi ba ina tsaye as hagon nan cikin 6ari saboda kaduwar da nayi a dalilin hangoshi da na yi wanda shi ne ganina da shi na farko tun bayan faruwar abubuwan da suka faru a tsakaninmu. Motsi na ji a bayana tare da shakar wani irin sanyayyan kanshin da ya yi sanadin da na yi matukar tsarguwa da zuciyata ta yi, da sauri na juya don fidda rai daga zato saboda in samu natsuwa a tare da ni, sai kawai idanuwanmu suka hadu an yi maza najuya don karbar abinda nace a bani, jikina sai rawa yake yi har 63 kárkarwa tamkar sanyin hunturu ne yake kadani, cikin wata irin kwalliya yake ga kamshi gashi in ba kuskure nayi ba sai naga kamar kiba ya yi, nan tkae na ji Zuciyata tana gayamin shi bai da damuwa shi dadi yake ji, shi hankalinshi a kwance baida wata matsala a tare da shi, da sauri na mika hannu na kar6i ledar siyayyar tawa da ya yi nufin karba, ban 6ata lokaci wajeu tsayawa karbar canjin ba nayi maza na bar wurin. To tsaya mana Mero jirani mana ai wurinki na zo. Bai ji kunyar fadin hakan ba a gaban mutanen da suka cika a shagon, ina jin maganganun na shi na yi amza na kara maimakon sauri na yanka da gudu nayi amza na shige cikin gidanmu ba tare da na saurareshi ba. Kwana biyu bayan nan na fita gida da sassafe don sayawa babana kunu da kosan da na saba siya mishi, ina zaune wurin mai kosan ina jiran ta zubamin saboda na samu wasu a gabana da yawa sai kawai na ganshi ya iso wurin, kallo daya nayi mishi nayi maza na sunkuyar da kaina na.dora hannu akan guiwata yayin da na zagaye guiwar tawa da hannayena duka biyu, doguwar farar jallabiya ce a jikinshi duk da ban tsaya kare mishi kallo ba nasan ta karbeshi. Ina kwana baba? Ya soma gaida baba mai kosan tana amsawa, lafiya lau Amadu ya ya su Hajiya da iyalin naka? Lafiya lau. Ya amsa mata, sakun kosan 64 bai so kan Mero baba nc? Da sauri ta ce mishi ko baizo ba ai sai a zuba mata Amadu. Nan da nan ta zuba da yawa fiye kudin da na bata ta kunsa ta mikomin nasa hannu biyu na karba na dora a kan murfin kwanon kunun na dauka na kama hanyar zuwa gida, Mubarak yana biye da ni babu halin in ruga da gudu in tafi in barshi saboda tsoron kar kunun nawa ya zube. Ki tsaya mu yi magana mana Mero. Ban kula shi ba tafiyata kawai nake yi, ban fa yi miki laifin komai ba ballekice na za ki yi fushi da ni, ni da ke mun shiga wani irin al'amari ne a dalilins harrin da matar babanki ta kulla mana na kuma san ba zai yiwu ta shanye ta gama lafiya taga yanda take so a rayuwarta ba tunda ita sharri tasa a gaba, in ma kina da wani tunani ko kulli game da ni a zuciyakri to ki yi hakuriki sake kawai duk abinda kika gani kuma ya zama dole ne kawai ya sa kika ganshi a yanda kika ganshin, a shirye nake kuma in yi miki bayanin da zai gamsar da ke. Ban kalleshi ba balle in tanka mishi har muka zo kofar gidanmu muna isowa kuwa nayi maza na wuce cikin zauren gidanmu na barshi a can waje. Tun daga nan na zama bana fita daga gida kai tsaye sai na dan tsaya na yi waiwaye waiwaye in tabbatar ban hangoshi a kusa ba. 65 Rannan ina zaune a dakina ni kadai sai ga Isiyaku ya shigo yana sallama, na amsa sallamar tare da bashi izinin shigowa, ya nemi wuri ya zauna muka shiga gaisawa har da yin hira tun da dama can abokin hirana ne, na yi ta tunanin abin da zan dan kawo mishi ya dan taba saboda nuna girmamawa ga bakonka ban tuna ba don bani da komai a dakin don haka na hakura muka ci gaba da hirar a haka jimawa can sai ya ce min, Mero ni zan tafi. Nayi maza na ce mishi ai na gode maka Isiyaku sai dai ka shigo yau dakin nawa babu komai a cikisnhi. Ya yi murmushi tare da fadin, babu komai. Ya dan karkace kadan sai naga ya zaro wata takarda daga cikin aljihunshi ya miko min tare da takardun kudin naira ashirin ashirin cunkus a hannunshi wai gashi in kawo miki. Nayi maza na zuba musu ido tare da tambayarshi menene wannan? Cikin natsuwa ya yi min bayani, wasika ce tare da kudi ya ce in kawo miki. A hankali na sake tambayarshi, in ji wa? Ya dan yi murmushi kadan kafin ya ce min, inji yaya Mubarak mana wa zai yi mikıi irin wannan aiken in ba shi ba? Ya baka kudi ba kawo min? Ina yi mishi tambayar na soma kuka tun katin ya kai ga amsa min nan da nan ya hidime ya shiga bani hakuri yana yi min magana, to menene in ya baki kudi an shi Mero? Yanda duk kika dauki abin fa ba haka yake ba shi 66 yaya Mubarak. Na yi maza na katseshi, dakata na fadi hakan taré da share hawaycna da bannayena duka biyu, maida mishi kudinshi tare da wasikar na rokeka ka gaya mishi yayi hakuri ya fita harkata bana son kulanin da yake yi bana so bana so, ka gaya mishi na ce bana so. Zai yi min magana na yi maZa na salke ce mishi, acte bana so ko kuwa dole ne? Ya mike ya fita, ya tafi ni kuma na kwanta a nan wurin naci gaba da kuka cikin tsananin bacin rai da takaici, wautar kudin ce ta fi komai kona min rai wato ni kudi ne bukatata, duk abinda akayi min na wulakarici da tozartawa aiken kudi ya kanmata a yi min? Na tuna kalmomin da na ji baba Lantana tana furtawa na rainin arziki ne yasa iyayenshi suka hanshi aurena saboda sun ga babana ba kowa bane face mai saida timatiri, zuciyata ta sake rayamin wasu abubuwan, ya yi aurcnshi ban kulashi ba ban shiga harkarshi ba yana nema ya rinka shiga nawa bayan an tabbatar min da cewär har da fita hanyita cikin sharadin da babanshi ya'sanyå*mishi, ya amsa sanna ne ya cce ya yafe msihi ya dawo gida; to menene kuma ya saurä tsakanina da shi? Ban san dalilk bå sai na samu kaina da bacin rai mai yawa da na-kasa daurewa zaman gidan ma ya gagareni na nemi izini wurin babana na shirya na tafi gidan yaya Dija. Tana ganina da yar jakarta dana zbe yan zannuwana na canji a ciki ta saki mirhushi, 'haba to 67 ko ke fa? Ai tun ba yau ba nake fama dake ki baro unguwar nan ki zo nan mu dan kwana biyu tare ki dan huta, ni hun ban cika son barin baba bane a gidan nan shi kadai yanzun ma na dan fito ne kawai. Na kwashe bayanin komai nayi mata ban 6oye mata komiba. Cikin natsuwa ta kallehi, kin san abin da yafi bani tausayi a cikin al'amarinki? Na yi maza na ce mata a'a, sai kawai na ji ta ce min, wai son Mubarak da kikeyi. Nayi maza na cem ata ni? Ta ce eh ke. Nace la yaya Dija ni ai ba son shi nake yi ba. Tayi maza ta ce, ke. matsa can ki bani wuri karki nemi maidani yarınya karama mana in bakya sonshi meke sawa ki na yin bacni rai a kanshi, meke saki kuka? Ai so ne Mero, ya yi miki aike ba yau ko jiýa ya fare ba ya dade yanayi ba wulakanci bane in yanzu kin daina karba shi kenan babu 6acin rai a ciki da har za a je ana ta kuka shawarar da zan baki ita ce ki fidda shi a cikin ranki fito da miji kawai ki yi aurennki ga Mansur. Na yi maza na katseta ta hanyar fadin kai Mansur? A'a ni yanzu bana son kowa. Ta sake zuba min ido saboda Mubarak da iyayenshi sun ki mu shi ne shima Mansur laifin zai shafeni, ai in ban manta ba a nan ne mukayi maganar nan da ke cewar da Mansur din da kuma Mbarak rdukansu daya ne wanda duk maganar aurent a kama za a yi da shi, to ba za ki samu mas'ala ba za ki zauna lafiya da shi za kuma ki yi 68 mishi biyaiya domin su dukansu biyun masu alheri ne babu kuma wanda zai iyakacin lokacinki a kanshi. Nan take nas oma yi mata kuka saboda jin irin kalaman da ta tsareni da su na baro gide na zo wajenta don in huta ita kuma ta zo tana yi min wasu maganganu da suke karawa zuciyata nauyi. Assalarmu alaikum, wai ana sallama da Mero a waje. Sau biyu yayi maganar kafin na takarkare na daka mishi tsawa wanda watakila tsayar da nayi misHi'ne ya yi dalilin fusatar yaya Dija tayi maza ta zabura ta mike tsaye ta ce min, maza tashi ki je kiga waye mai kiran naki ai don Mubarak ya yi aure ba zai zamo danin karewar maza a duoiya ba, da ke wata mai zuciya ce ma da tsayawa kikayi kika fidda mijinki nan da kwata talatin a yi bikinki ki tafi gidan mijinki kije ki yi zaman aurcnki kowa ya huta. Na tashi na fito don ba zan iya yin jayaiya da ita ba. Mubarak na gani tsaye a kofar gidan tsaye jikin motar tashi da ga shi har ita sai wani sheki suke yi suna daukar ido, ga dukkan alamu dai shi Mugbarak dadinshi kawai yake ji bai da wata mas'ala a tarc da shi, wanna shi ne abin da yafi komai bata miu rai wato ni ce mai damuwa, ni ce a cikin bakin ciki, ni ce rashin zuciya ya hanani samawa kaina zaman lafiya da kwanciyar hankali, ina ma dai ace nima halina irin na yaya Dija ne?... saurayi na yi na katse tunanin 69 nawa saboda ganin ya nufoni zai zo in da nake tsaye, nayi maza najuya zan shiga gida, caraf naji ya kama gyalen da nake rataye da shi ya rike, abinda ya yi dalilin tsayawata. Kina ganin kamar kin tsayawar da za ki yi ki saurareni yana da wani abin da zai amfanar da ke ne? Ni da ke ai muna bukatar fuskantar juna ne don musan abinda muke ciki. Kaina a sunkuye saboda nauyin shi da nake ji, muryata tana rawa alamar idanuwana suna shirin zubar da hawaye na ce mishi, sake min gyalena bana so kar kuma ka sake yi min haka bana so. Da sauri ya sake min gyalen nawa, ban tsaya sake sauraron komai ba na yi maza nas hige cikin gida na barshi nan wurin a tsaye, maimakon in tsaya wurin yaya Dija tunda har lokacin tana zaune a inda na barta wucewa nayi naje can cikin dakinta na hau gadonta na kwanta ina kuka, na kaska gane dalili, na kasa gane al'amarina, na kasa fahimtar yanda za a yi in zama jarumar kaina in fita hanyar Mubarak in daina ganinshi ina jin wani abu ganie da shi, na zafi ko ciwo ko faduwar gaba a cikin raina. Ina kwance ina yin kukan yaya Dija ta shigo ta sameni, nayi zaton wani fadan zata sake yi min sai na ji ta ce min, ki yi hakuri Maryamu wani loakci zaozi da ke da kanki za

Chapter 4 of 10