Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 10
sauraron bayanin nata ban san yanda akayi ba sai ganinta muka yi ta fito tana rungume da dan jariri Asabe tana biye da ita cikin katon lullubi sun sa kai sun fita sun bar gidan, ganin sun bar gidan ya sa ni nufin shiga dakin namu wai in kwanta. Abinda na gani a tsakar dakin ya sani 105 kwallara ihun da na dawo da baya cikin sauri Sallau ya fito ya leka cikin dakin ya tayani ganina binda na gani, ya koma ya dauko leda ya sanya shi a ciki ya kuma. sa omo da izal da tsintsiyar zabori ya wanke dakin tas zuwa tsakar gida dama bayan gidan baki daya maimakon karni da kazantar jini ya koma tsabta da kanshin kayaiyakin da ya yi amfani da su. Na shiga dakin nayi salla na hau gado na kwanta cikin jimamin abinda ya faru, akan idona Asabe ta haihu ta haifi da babu aure ba shiri nake yi da ita da uwarta ba amma na tausaya mata tare da dan nata, ina cikin hakan na jiyo muryar baba Lantana tana cewa ba dai dani kuke yi ba ai za mu sa kafar wando daya ni da ku, munafukan banza munafukan wofi matsiyatan mutanen da basu san mutunci ba duk zaluncin ubanku. Na yi kasake ina sauraron zage-zagen nata cikin zuciyata na ce, oh oh wannan mata da jarumtaka take ko ita da su wa take yi oho. Ina jinta ta shigadakin da Sallau yake bamuji komai ba illa iyaka dai na jiumuryarshi yana ce mata to nan take kuma ya yi waje, nima na fito don in nemawa babana abin karyawa da kuma maganinshi, lokacin ne na gane daga tafiyarshi masallaci don sallar asuba bai sake dawowa gidan ba. Ina daki a kwance ina sauraron shigowar babana don ba dabi'arshi bacewucewa kasuwa daga 106 masallaci na ji muryar Salau alamar ya dawo daga aiken da ta yi mishi na ji shi a fusace yana ce mata, kin ganta ko mnama kin ganta ko baba kinga halin Asaben ko? A gabanki bakinta ta ce min Agogo ne ba? Gabana ya yi mummunan faduwa cikir raina na ce Agogo kuma? Ban kai karshen maganar zucin nawa ba naji Sallau shima yana karasa nashi bayanin to an je anzo da Agogo ya zo ya zare m ata ido yana tambayarta' shi kadai ne su sauran me yasa bata amabci sunansu ha sai shi? Mainakon taja ta tsaya a kan shi kadai ne sai kawai ta tsorata ta ce wai Alhaji Nalami ne. Kiis ya rage in rikito kasa daga kan dan gadon nawa saboda firgitar da nayi, nayi maza nasa hannu biyu na dafe kirjina saboda harbawar da ya kama yi, nayi maza na sake tambayar kaina, Ahlaji Nalami kuma? Wannan abin mamaki da ban tsorod a yawa suke, Nalami da Agogo su Asabe take tuihuma da yi mata ciki, ita kuwa wane batan basira ne ya kaita yin hakan? Tsawon lokaci ina tunanin tsakanin biyun wanne ne dama dama? Agogo dai shi ne mutumin da ya jagoranci abinda Mubarak ya sa aka yiwa Sallau wanta da suke uwa daya shi kuwa Nalami ba sai na tsaya ina wani dogon bayani a kanshi ba ko da yake dai baba Lantana tayi nufin badani gareshi ta kuma yi 107 mishi tayin Asaben don ta samu warware mas alar kudin da suka shiga tsakaninsu to amma tunda hakan bai yiwu ba wane birgewa ko sha'awa wannan mutumin ya baiwa Asabe da har ta yarda da shi har take tuhumarshi da zamowa uban danta? Na yi maza na bar wannan tunanin na shirme tunda gani nake tamkar bai shafeni ba na amsa sallamar da naji ana kwalawa a kofar gidanmu da sauri na fita don ganin masu salalmar, tunda na jiwo muryoyi da yawa alamar ba mutum daya bane. Ina fita naga an ciccibo babana rabe-rabe wai faduwa yayi a kasuwar timatirin su nan take na kama salati, ina yin kuka, wani daga cikin mutanen dake rike da baban nawa ya dakamin tsawa, kaice ki ba mutanc wuri munafuka kawai duk ba ku kuka jawo mishi ba, ita ce fa wacce kwanaki aka yi tsiyar nan a kanta ran daren da zan daura mata aure da wani aka kamota a dakin wani kato wanda shi babu yanda ba a yi da shi ba ya auretan ya ki amma don hauka da rashin zuciya taje ta kai mishi kanta shi kuwa warda zai auretan da ya ji labari ya cco ti ya fasa. Wani daga bayan yace, a'a to zai fasa mana da ka auri bduurwa fanko ai gara ma ka auri bazawara da ma kasan abinda ka aura, ni da aka bada labarni haihuwar yar tashi ai na dauka ita wannan din ce ta haih:, ashe wata ce kuma daban? Wato shi 'ya' yan nashi duk haka suke? Su matan lalacewa ta bin maza 108 shi kuma namiin kana ganinshi ba sai an yi maka bayani ba, baki a rube ko ina kuma a fuska tabon adda, to amma dai dan gara shi tunda ba zai dauko mishi irin wannan maganar ba, lalacewar 'ya mace ai babbar musiba ce ko ba komai kuma gashi ya fara dawowa kan hanya tunda yana binshi kasuwa yana kuma taimakonshi ba kadan ba. Kukan da nake yi bai hana zuoiyata tunamin maganganun nasu ba wannan wane irin rashin adalci ake yiwa babana wato su Asabe su Sallau din ma duk ya' yanshi ne? Ban kai karshe ba na ji wani ma ya kama bayanin 'ya mace, nifa shi yasa ma ban cika son haihuwarta ba na kuma yi sa'a 'ya'yana bakwai gaba dayansu maza ne babu mace ko daya. Wani kuma daga can gefe ya ce kai ba fa duka matan ne haka ba in akayi sa'ar su aka dace da na kirkin dadin al'atmari ne da su saboda su din masu tausayi ne, shi malam Habu har da laifinshi cikin lamarin iyalinshi don kana da hakuri ba dalili bane da zaka zuba ido ka barwa matarka da' ya'yanka sai yanda tayi da su ai cewa akayi ku kare kawunanku da iyalanku daga shiga wuta to shi ya zuba ido a kan komai ya bar mata tafi karfinshi, yaushe ake yin haka? Haka ne haka ne suka amsa. Suna barin gidanmu nima na fita don nemana motar da zata daukar min babana zuwa asibit, a kan idona ina ji ina gani nake jin mutnac suna bayani an 109 haifi shege yau a gidan malam Habu wanda ake yiwa bayanin sai ya tambaya wane malam Habun? Sai a tsaya bayani malam Habu mai tmnatiri, nan na wajen kan kwana baban wannan Maryam din da kwanakin can watannin da suka wuce aka kamota a dakin saurayin da take kwanan gida har kan haka mutumin da zai auretan ya fasa? Sai ace haka haka na tuna, dattawan unguwa kuwa fadi suke yi kai malam Habu bai yi sa'ar iyali ba. Raina ya baci zuciyata tayi zafi hankalina ya tashi, na rasa inda zan tsoma rayuwata in ji dadi, da dai ace nasan abin da zafi àru kenan to da na ja Asabe na fitar da itn daga gidanmu in ya so ko a kan titi ne ta haihu, gaba daya sai masu magana suka mance dabana ba shi ne uban Asabe da Sallau na asali ba suka kuna mance da cewar bayanin da nice 'yarshi ta asali yana da ya' ya Dina in ni ban zamo mutuniyar kirki ba ita ta kirki ce don kuwa in dai biyaiyar aure shi ne kirkin mace to yaya Dija ta kirki ce. Ina kuka nas higo gida lare da direban motar da na samo don ya tayani daukan babana, yaya Dija na gani a gidan ta zo saboda labarin da ya je mata sai dai kuma wai cacar baki na samu suna yi da baba Lantana, Asabe ai mai imani ce shi yasa ta haifi nata dan mai rai ke sau nawa kanwarki tana cikin shege kina cire mata? Ko ance miki ban sani ba ne. 110 Wuceta nayi ko kallonta banyi ba na shiga dakin da babana ke kwance na cewa direban shigo daga nan kan ya shigo ta biyoni ina kuka nace mata babanmu yana kwance kina fada da ita? Kan tayi min magana baba Lantana ta cafe tana zaton zan kyale ta ne take wani zuwa wai kar 'ya' yana su sake shigowa nan gidan to wannan gidan har wani gida ne da za a yiwa mutane doka a kanshi? Ban amsa ba itama yaya Dija ta yi shiru, ai a shirye nake don ni din warki ce dai dai da kugun kowa wanda duk ya shiga lamarina zan shiga nashi in ka gayamin cuta kuma zan gaya makam utuwa, munafukan banza munafukan wofi duk sai kun ci gidanku a hannuna. Muna jinta tana tayi muka fitar da babanam uka tafi asibiti gado aka bamu ni ce kuma na zauna tare da shi a wannan karon ko tayani kwanan da Sallau ke yi ban yarda ya yi ba. Ina zaune kan kujera gaban gadon babana yake kwance ina kallon babana da halin da yake ciki, tunani kawai nake yi na al'amuran dake ta faruwa da mu daga wannan mu koma wannan, sai ina ganin kamar al'amura sun soma wucewa an fara samun sauki sai kawai wani abin ya sake tasowa a sake fadawa cikin wata mas'alar da zan rinka ganin tamkar tafi wacce aka baro baya tsanani. 111 Ana cikin haka naji motsi a kusa da ni, nayi maza na daga kai don ganin ko waye? Mubarak na gani a tsaye daga gefe kadan kuma babanshi ne Muhammadu, cikin tsananin kaduwa da firgita nayi maza na sauka daga kan kujerar da nake zaunen na tsuguna a kasa karo na farko da na ga baban Mubarak bayan faruwaral'amuran da na daina shiga gidanshi. Tashi maryam tashi ki hau kan kujerar ki ki zauna. Ban iya motsawa ba ban iya tashi na hau kan kujerar ba ban kuma iya buda bakinan a gaisheshi ba, kuka kawai nake yi. Ubangiji ya bashi lafiya, Ubangiji ya sa kaffara ce, Mubarak ne ya amsa addu'ar da baban nashi ya yi da amin. Maganar da na ji Mubarak din ya fara yi min ta tabbatar min da cewar bayan yayi addu'ar bai tsaya ba tafiya yayi don haka na mike na zauna a kan kujerar da na bari. Kina ganin kamar akwai wani dauwamammen abu ne a rayuwa? Duk wadannan abubuwan da kike gani wata rana za su wuce don hakaki rinka yin hakuri. Ya ciro kudi masu yawa ya ajiye a gefen gadon, ki rike wannan a wurinki ni zan tafi baba yana jirana: Na yi maza na ce mishi bana so dauki kudinka ka tafi da su, bana bukatar komai daga gareka. Ya yi 112 kamar bai ji ba ya juya da nufin tafiya, nayi maza na ce mishi, da ka yardar kca daukárdon kar su zamo maka sanadin bacin rai saboda zan iyabadasu a kaiwa ma... Ban san yanda aka yi ba naji ba zan iya karasa abinda na yi niyyar gaya mishin ba, wucewa yayi ya yi tafiyarshi baftare da amsa min ba, nima na zubwa kudin ido ina kallonsu: lokaci mai tsawo kafin nasa hannu a kansu na daukesu na adanasu. Kwananmu uku kafin a ka sallamomu muka dawo gida. Mutane suka sake tasa babana da gidan mu da ni ma a gaba kai kace nice na haifi dan shegen. Ina dakina ina zaune cikin damuwa da tunani iri- iri na ji Sallau yana cewa, baba Lantana ai Asabe ta kamanta ruwa ido 6atan 6akatantan zata yi tayi dalilin da dan nata zai rasa madogara kamar.... Da sauri baba Lantana ta wulwulo ashar ta antaka mishi, ya ce to shi kenan baba nayi shiru na kuma ji ni mahaukaci ne to na rokeki ki taimakeni ki daina tunani wajen maganar Asabe da samarinta da dantaki samu masu hankali su rinka zuwa miki. A wannan lokacin wata irinr ayuwa na tsunduma yi da ba ma zai yiwu ince zan tsaya ina bada labarinta ba, abinda dai na sani kawai shi ne ina wuni ban kai wani abu bakina ba saboda kwata-kwata yunwa ta rabu da cikina mafi yawancin lokaci ruwan kawai 113 nake sha saboda bushewar makogaro dake yawan damuna. Rannan an wayi gari da safe wankin kayan babana nake yi saboda ya dan fara samun sauki ya yi amfani da tsabtataccen kayaya dan ji dadi, ina cikin yin wankin ne naji anyi sallama a kofar gidanmu, Sallau baya nan don haka na yi maza na leka tun da nasan babana bai mallaki karfin yin hakan ab. A hankali nayi leken don ganin mai sallamar a dalilin ban cika son hada ido da yaran unguwar ba, malamina na makarantar islamiyya na hanga malamn Yahuza da sauri na karasa fita wajen naje na tsuguna kasa cikin wani irin yanayi na kunya da kuma girmamawa, sannu da zuwa malam. Haba Maryamu shirun naki ai yayi yawa shiru- shiru shiru da ba zai yi auren ba ai sai ki dawo karatunki, ai ba haka rayuwa talke ba komai kika gani yana da lokacinshi shi aure lokaci ne in har lokacin shi bai zo ba babu yanda za a yi a yi shi, watakila mijin naki bai zo ba, ita kuma mace bata aure sai mijinta don hakaki dawo karatu kin gane ko? Nace mishi to malam. Kar fa kice min to'ki zo baki dawo makarantar ba don sau biyu ina turo yara abokan karatunki su zo su kiramin ke ba ki zo ba. Kamar ince mishi babu wanda ya zo ya kirani sai naga bari in yi mishi shiru kawai. Ai ba a girman da 114 ake wuce yin karatuna addini, shi dan adam yana rayuwa ne a kan neman ilimin sanin nahalicci don haka ki dawo makaranta kin gane? Na sake ce mishi e malam. Muka yi sallama ya tafi nima na shiga gida, a zuciyata na'rinka tunanin ko su waye malam ya turo su kirai oho, ina cikia tunanin hakan sai kuma na watsar na bari saboda na gane sanin ko.su waye din ba zai amfanar da ni da komaib a. Zuwan da malam Yahuza ya yi ya sanya ni na ji wani canji cikin zuciyata saboda irin nasihun da ya yi min, kwadayin karatu ya sake dawowa cikin raina, sai dai kuma yaya zanyi in sake fuskantar yan makarantar bayan duk irin kwaramniyar da na yi ta fama da ita? Da wane idon zan sake kallonsu? Wannan shi ne abinda ya fi komai tsaya min a rai. Kwana biyu bayan zuwan malam har lokacin ban fara zuwa makarnatar ba sai dai kumna bana jin dadin hakan da nayi, in na yi tunanin menene ya dame ni wanda ya sa zuciyata take yi min nauyi? Sai int una malarn Yahuza ya tako har gidanmu ya nemi in koma makaranta in yi ka ratu abin yi hakan ba, abinda ni da kaina na sani ba sai an gaya min ba yin hakan rashin girmamnawa ne ga na gaba musamman malaminka. Rannan dai na daure na tafi gabana kuwa sai faman bugawa yake yi, kirjina yana ta faman harbawa da sauri-sauri, a tsarge kawai nake zaune a ajn motsi 115 mai dan karfi in akayi sai inji na kara takura in yi kamar ni ake nunawa ko ake bada labari na. Malam Wahuza ya yi matukar farin ciki da ganina ya yi mana karatu ma1 gamsarwa ya yi mana kuma nasiha kan yan uwantaka irin na musulunci tare da bayani kan wanene musulmi? Lokaci mai tsawo ya dauka yana bayani akan siffofin musulmi na kwarai da Manzon rahama (S.A.W) a kai daga cikinsu akwai kubutar musulmi dan uwanka daga sharrin harshenka ya gama, ya y mana addu'a muka shafa nad awo gida. Na soma zuwa makaranta a kunya ce a darare sai dai ba a dauki lokaci mai tsawo. ba sai na wartsake har ma karatun nawa ya zamo daga cikin abubuwan da suke ragemin damuwata su nutsar min da zuciyata musamman ma da yake yayi dalilin da na koma yin karatun Alkur'ani mai girma sosai da sosai wanda da na daina yi saboda damuwa da rudewa in ba haka ba ai na dade ina jin malamai suna fadin cewar shi Alkur'ani waraka ne ga duk wata cuta ciki kuwa har da na zuciya. Daga komawata makarantar Islamiyya sai mu'amala mai karfi ta kullu tsakanina da malam Yahuza, saboda kullum idonshi yana kaina na zo makaranta ko ban zo ba. Ki koma makarantar oko don ki samu damar mallakar takardarki ta karatun college, na ce a'a 116 malam ai ni bokon nan ba wani damuna yayi ba. Ya vi murushi to at ko bai dameki ba kin rigakin yi shi takardar da za ki mallaka ta zame miki shedar wahalar kiken emaki yi wasa da ita, alhalin ilimin yanzu ya ta'allaka ne a kan abidna aka gani a rubuce don hakaki koma ki yi karatunki karki yi wasa da lokacinki, shi lokaci da kike gani ba a wasa da shi tsada ke gareshi, baki ji abin da wani bature mai hikima ya fada ba? Ya ce "A man who dares to waste an hour of time was not discovered the value of life. Mamaki ne ya kamani jin da nayi malam Yahuza yana rangada lafiyaiyen turanci da bakinshi bayan na dauka arabiya ko larabci kawai ya iya. Shirund a nayi ya sashi tambayata ko kinfi gane dai ki jira mijin aurenki ya zo ki yi.aurenki kawai? Shiru nayi ban amsa ba iyaka dai kaina a sunkuye ban kalleshi ba, amma nasna murmushi yayi kafin ya ce min, iaina zamna jiran miji Maryam saka al'amura masu yawa a gabanki sai ki ga ma yafi saurin zuwa gareki tunda shima ya san bashi kadai kike jira ba kin gane? Na ce mishi to. Kalamai da nasihohin da malam Yahuza ya yi ta yi min su ne suka karfafa min zuciyata da ta riga ta karaya da al'amuran rayuwa har na rinka ji da ganin tamkar bani da wata mas'ala ko damuwa a tare dan i in dai ba ta rashin lafiyar babana ba ne. 117 Makarantar koyar da sana'o'in mata ta Markas wacce Mansur ya taba bani labari na shiga da taimakon malamina malam Yahuza shi ya karbomin form din na cike ya mayar ya kuma biya kudin form din gashi kuma anyi sa'a kyau ta ce form din kadai ake saya, ajin dinki na shiga shi en.a raina tun sanda Mansur ya ce min ya fi sha'awata da yin dinkin. Na fara zuwa Markas mas'alolin da na fuskanta ba su wuce na wahalar tafiyar kafar da nake yi da kuma dawowa gida da nake yi ban samu abincin da zanci ba sai na nemawa kaina hakan kuma na jira. Na wayi gari rannan ina gida banje wurin koyon sana' ata wato Markas a dalilin renar da Jumaa ce ranar Juma'a kuma ranar hutu ce a garemu, ina kwance kan gado na na hutawa bayan na kammala wanke mana kayanmu ni da babana sai kawai naji Sallau yana cewa uwarshi, kai an auná arziki yau dai an daura auren Asabe magana ta kare. Sauri nayi na kara maida hankalina wajen jin maganar tasu tare da tunanin Asabe tayi sa'a itama ta samu tayi aure dukd a cikins hegen da tayi ta haihu ni ce dai... kan in karasa tunanin zuciyar tawa sai naji baba Lantana ta ja wani mummunan tsaki tare da fadin, to wani kokari kayi a hakan? Ina ce takardar filina da ya karba kawai nace ka karbo min a matsayin sadakin auren nata ka kasa ka karbomin nera goma. 118 Ya ce, uhun baba kenan ba ki ma san yanda akayi ya bada nera goman bane abinda ja yayi ya tsaya a kan nera bakwai zai bayar sai da malamin da zai daura auren ya ce mishi bai kai rubu'u dinar din da shari'a ta yarda a karba a matsayin sadaki ba shi ne ya bada goamn, ni dai tunda Asabe ta samu mijin aure zata isa gidan mijinta yau danta kuma ya samu uba ba zai yi ta watangaririya a hanya bai san ubanshi ko danginsu ba ai shi kenan magana ta kare a wurina. Duk da ganewar da nayi Alhaji Nalami Asabe ta aure kalaman da Sallau ya yi sun sani girmamashi tare da auren da Asaben tayis aboda na gane aure daraja ke gareshi Sallau kuma na gane natsattsen yaro mai kuma hankali tsayaiyar tarbiya ce kawai bai samu ba. Na fara zuwa wajen koyon sana'a ta a Markas babu dadewa'sai kuma malam Yahuza ya sake yi min magana kan wata babbar makaranta ta ilimin addini mai zurfi da aka bude duk da irin kudaden da ya yi min bayanin za a kashe kafi in so ma karatun na shige ta saboda yaya Dija ta amince da shigar tawa ta kuma bayar da duk wani abinda aka nema shi kuma malam Yahuza sai ya taimaka min da manyan litattafai masu tsada a matsayin aro kafin ta samu ta saya min nawa in mayar mishi da nashi tunda shima ba daina karatun ayyi ba tunda shi littafi abin ajiyewar dalibi ne. A wannan lokacin sai na zama kusan kullum ina da abin yi mafi yawancin lokacin ma nakan fita da 119 safe ne in dawo da yamma saboda zan tashi daga nan in nufi can don ma dai kawai babana yana raina kowane lokaci. A wannan lokacin baba Lantanaa wuni take yi tana yiwa babana gorin auren da Asabe tayi da na hada 'yarka da shi kuka ki ai gashi ni na bashi tawa tana kuma zaunen abin ta tsaf cikin rufin asiri da kwanciyar hankali ga mutunci shi aure ai darajarshi yawa ne da ita ba kowane yake samun darajar yin shi ba. Na jinsu bana cewa koami, iyaka dai na sani na kuma yarda da kalaman nata duka iyaka dai can cikin zuciyata a yanzu bani da damuwa mai yawa kan maganar yin auren nawa na yarda na kuma gamsu da cewar dak ullum malam Yahuza yake yi na komai lokaci ne kowa kuma yana da nashi lokacin, Nalami kuwa in dai shi zan aura to ina ganin kamar gara in yi rayuwata kawai a haka ya fiyemin don haka ko kadan bana jin zafin kalaman nata. Ina zaune a dakina bayan na idar da sallar magariba takardun da zan tafi da su wajen malam Yahuza nake hadawa saboda muraja'ar da yake yi min kan wasu darussan masu dan nauyi da nake bukatar fahimta mai kyau a kansu, har zan yafa hijabina in fita sai kawai naji yaro ya shigo yana cewa wai ana sallama da Maryam a waje. 120 Na daga ido na kalli agogo cikin zuciyata na ce kar dai Halliru ne ya z0 a wannan lokacin. Halliru shi ne sabon saurayina da Yakumbo ialima ta turo min a dalilin ya ce mata ta duba mishi budurwa mai hankali da iya kwalliya kasancgwar shi dan mijinta da ta rike ya sa ta ce bai dace da kowaccc budurvwa ba sai ni, ni kuwa a wannan lokacin bani da wani zabi na daina Pzaba ince ga irin saurayin da nake so ko ga irin mijin da zan aura, aurcn kawai nake so wanda duk yazo kuma a shirye nake zan aure shi, in dai huta babana ma ya huta mu duka mu huta damunmu da ake yi ana bada bayanin mu a kan idona sai ka ji dattawan unguwar suna cewa ai nan kusa kusa duk ai babu sauran sa'arta kai kannenta na kusa ma babu duk sun garna yin aure sai ita kadai. Na debi littafin nawa na rungume na jawo kofata na rufe na yiwa babana sallama na fito da nufin in mun gama maganar da za mu yi sai kawai in wuce na kuma san ganina tare da litattafan a hannuna zai kara sashi tafiya da wuri tunda yasan ina da abin yi. Ina fita waje maimakon in ga Halliru, Mubarak na gani a tsaye, wani irin lalataccen kallo ya yi min da ya sanya gabana faduwa cikin zuciyata na yi maza na ce, ban yafe maka ba zuwa kofar gidanmu da kayi ka fadar min da gaba. Shima malamin naki yana nema ya rikide ne ya Zama saurayinki? Da sauri na daga ido na kalleshi 121 cikin tsananin mamaki abinda ban taba zaton wani zai yi tunanin hakan ba don babu wata alama da take nuni da hakan. Idan kika kuskura na gane da wani abu a tsakaninki zaki bar karatun naki gaba daya ki koma Zaman gida in kumakina ganin kamar wasa nake yi to bari in gane halkan ki gani kina nufin don yana koyar da ke karatu a da sai kuma a yanzuki rinka kwasar litattafaikina zuwa wurinshi kuna zama ku biyu? A kidune nace mishi, ba fa mu biyu bane? Ya yi maza ya katseni ko ku dubu ne ban yarda ba kar in sake gani ko jin kin fita daga gida bayan sallar magariba, na gaya miki. Kuka na soma yi mishi saboda bakin cikin abinda yake yi min, takuraw ar ta kai duk inda ta kai, komai nake yi ya sani ko baya nan nayi in ya dawo zai ji labari. Cikin karfin hali na daure zuciya ta na ce mishi, to wai ni ina ruwanka da ni ne? Ina abinda ya shafeka da abinda nake yi, kullum sai ka shiga harkata, kullum sai ka takurawa rayuwa ta. Ban san dalili ba rannan sai na kasa zuwa wurin mraja'ar da Malam Yahuza ke yi min, maimakon washegartnma inje ban i cb a sai kawai na hakura da muraja' ar na koma maida hankalina sosai a aji wajen fahimtar dukkan darussan da ake yi mana. 122 Kullum dai burina bai wuce in samu lokaci in tatawa Mubarak rashin mutuncin da zai sa ya fita harkata kwata-kwata ba amma in na ganshi sai in kasa saboda kwarjininshi da yake yi min nauyi a idona. Gabatowar watan azutin ra:nadan mai girma ya sa aka shirya mana jarrabawar da a bayanshi muka samu hutun makaranta har sai bayan salla mu koma, farin ciki sosai nayi a wannan. Jlokacin a dalilin jarrabawa ta tayi kyau banda haka zan dan samu hutun wahalar da nake yi ta zuwa makaranta da kafa in dawo da kafa, Sannan zan dan fuskanci wani abinda nake kuma dokin yi shi ne dinki don na dan fara iyawa har yaya Dija ta gamsu da labarina bayan dinkin 'ya'yanta dana dade ina yi musu ta hada min har da nata nayi a dalilin hakan kuma ta ma karbar min na kawayenta da abokan zamanta. Ki natsu sosai ki yi musu mai kyau don sai ya zamo tamkar tallan iyawarki kikayi, nace mata to. A wannan lokacin hutun makaranta da dokin dinkin azumi da nake yi ne ya ragemin damuwa ko bacin ran da na samu kaina a ciki ra turowar da Halliru ya yi a ka karbe mishi kayanshi, shi ko kayan na gani ina so kamar yanda wasu suke fada da da ya kawo

Chapter 7 of 10