ba.''
zama tayi tace '' me ya ce ?.''
Baffa yace '' yace duk wani kaɗo da ya shigo cikin wagga rugga a kashe shi, idan an mai magana da hilatanci be amsa ba , kowa ne yake jin hilatanci? shi ya saka fa kullum nake addu'a murja Allah ya sauya wa yarinyar nan miji duk da nasan abu ne me wuya tun da maɗo yake son yarinyar nan ba wanda zai iya son ta , yaron da ana zargin shi yake janyo kado suke mana ta'addanci a cikin ruggar nan uban sa kuma ya ɗaure mai gindi.''
fuskar murja ce ta sauya domin ita ba wanda take fata take buri ya auri yar'ta sama da maude kasancewar sa da a gurin sarkin ruggar da suke, tana ganin yar'ta zata samu hutu da jin dad'i dan haka tace '' hmmmm baffa ka dena saka komai a ranka yan bani na iya ne suke wannan maganar.''
wani kallo yayi mata ya ɗauke kai tabbas, ya jima da sanin halin murja kudi ne kawai a gaban ta.''
ganin yayi shiru ta gyara zama tace '' baffa nasan za kayi wani tunani amma ni bawai kudi ko dukiya ne a gabana ba idan har ka ki aurawa mardiyya maude to ka tabbata muna cikin masifa, sanin kan kane saboda ɗansa zai auri yar mu, harɗ'o bello ya sausauta maka ni duk da ina yin wani zargi anya kuwa ba shi bane ya aiko aka kade shanayen da kake kiwo? .''
murja bar wannan zance insha Allahu koma mene Ubangiji zai bayyana gaskiya ni yanzu me ya rage min a duniya shekarun fa da nayi su da bazan yi su yanzu ba , zan so ace mardiyya ta samu mutumin kirki wanda zai ga darajar ta, da tamu yaga mutuncin ta , yaga namu.''
murja tace '' to Ubangiji yayi abin da yafi zama alkairi amma ina me shawarar tarka , kar kayi wani yunkuri idan kayi harɗ'o bello zai ce ka biya shi kudin sa ina kan su kaf cikin ya'yan mu ba me arzikin da zai biya shi kudin'sa , shi kansa yaron shu'umin kansa ne...''
wannan shi ake kira da gaba wuta baya gangami haka ya raya wannan a cikin zuciyar sa , a fili kuwa sai yace '' to Allah ya shige mana gaba.''
amin ya Allah yanzu na dauko maka furarta ka ?
ta faɗa tana kallon sa wahalar rayuwa ta jemar dashi naman fuskarsa har zazzagowa yake saboda kunci da bakin ciki da yake ciki su, suka ƙara tsufar dashi gashin kansa tamkar audiga saboda fari.
jikin sa a sanyaye Yace '' eh dauko min.''
tashi tayi, ta durkusa ta shiga cikin bukkar ta , daga gadon karfe sai tabarmar kana a shimfiɗe akasan dakin babu wani tarkace kwaryar da take karkashin gado ta dauko ta fito da ita buɗe mai tayi ta ajiye mai ludayi a ciki.
baffa rufe furar yayi jin ana kwaɗa mai kira yace '' ina zuwa kamar muryar malam Ishaq.''
to ban da abin malam ishaq gidan nan baƙon'sa ne ta fadi haka tana ci gaba da tankaden da take yi.
tun da kika ga haka baya son shigowa sauri yake, ya fadi haka yana fita daga cikin ruggar, miƙawa malam Ishaq hannu suka gaisa malam Ishaq yace '' Malam haruna bafa lafiya ba ?''
da dauri yace '' me yake faruwa?.''
wasu mutane ne na haɗu dasu a bakin gaɓar kogi a cikin mota suna neman ruggar bello da sunan ka shi ne na ce su ajiye motar nan a wajen nan na basu kaya suka sauya domin gudun tashin hankali kasan halin harɗ'o bello basai na faɗa maka ba.
dan jim yayi domin dai shi yasan bashi da alaka da kowa na birni malam Ishaq yace '' yana ga kayi shiru gasu can fa ?.''
to ka ce su zo muji dame suke tafe ko?
to ya faɗa yana tafiya inda ya ajiye su yace '' ku tawo anci Sa'a yana gida be fita kiwo ba.''
to su kahu sunusi suka ce mai, tun da suke basu taɓa shigowa daji irin wannan ba malam Ishaq yana gaba, suna bin sa a baya suna isa gaban ruggar malam haruna yace '' to ga malam haruna nan da kuke nema.''
baffa miƙa musu hannu yayi suka gaisa.
baffa yace '' ina zuwa.''
to suka ce mai shiga gida yayi ya dauko tabarma ya shimfida sannan ya dauko kwaiyar fura da nono da ruwa ya ajiye yace bismillah ga , gurinan.''
kahu sunusi godiya sukai mai suka zauna malam Ishaq shima zama yayi kusa da baffa domin jin me yake tafe da su.''
Uncle Sa'eed yace '' nasan za kuyi mamakin ganin mu ko? to da alkairi mu ka zo mun zo nemawa ɗan mu auren yarka mardiyya da take , kasar birmu.''
da sauri baffa ya ɗago tab ina ba zai yarda ba haka kurum yaje yan , yankan kai ne wa yake dashi ? da zai mai bincike yana cikin wannan tunanin yaji uncle Sa'eed yace '' ni sunana Alhaji Sa'eed mansur turai mu ya'yane ga tsohon ministan man fetur mansur turai shi kuma yaron mu aseem dan gidan Marigayi sir EL'BASHIR.''
malam Ishaq yace '' tabbas naga kamar wallahi tun da na ganku nake kallon ku kai ba kai ne ka fito takara ba a kasar birmu lokacin da naje naga hotonan ka, a manne a bango.''
uncle Sa'eed yace '' eh hakane.''
boyayyiyar ajiyar zuciya baffa ya sauke jin Malam Ishaq ya san su yace '' to gaskiya mardiyya tana da wanda zata aura.''
da sauri kahu sunusi yace '' innalillahi wa'inna ilaihir raji'un an gama magana ne ?.''
baffa yace '' a'a sai ta gama wannan karatu sannan za a yi magana.''
Malam Ishaq yace '' a'a baffa mafita ce fa muka samu, ya faɗi haka fa yaren fulatanci
baffa kallon sa yayi Sannan yace '' to shikkenan zan yi magana da yarinyar domin bazan iya yi mata auren dole ba, sannan dole za a yi shadi duk wanda yaci nasara shi zai aure ta.''
da sauri kahu sunusi yace '' ba matsala za muyi magana da yaron.''
malam Ishaq yace '' insha Allahu za mu neme ku.''
canzan number suka yi sannan sukai sallama har wajen motar su, sukai musu rakiya.
a hanyar dawowa baffa ya kalli aminin nasa yace '' me ya saka kai saurin amsa musu bayan kasan kaf garin nan tsoro ya hana kowa karawa da Maude ? ina tsoron kar a cutar musu da yaron su kaga yaron birni ba kamar na , nan bane basu san wannan al'adar ba.''
malam Ishaq yace '' wallahi ba shaɗi ba inhar da akwai abin da yafi shaɗi zai yi in har yana son ta.''
hmmm malam Ishaq kasan halin Maude ba sai na faɗa maka ba , ni yanzu wannan zancen ma bana son mu ci gaba da yin sa dan kasan mushuriki ne za mu iya ganin sa a gaban mu.
Malam Ishaq yace '' ba abin da yace zai karfin Ubangiji Allah ne ya kawo mana mafita, wallahi duk da ban sheda fuskar yaron nan ba amma jiki na ya bani mutumin kirki ne yanzu ita sai ka kirawo ta kaji ta bakin ta , duk da kana da ikon zaɓa mata mata miji duk wanda kaga dama inhar na gari ne, lokacin ɗaya zuciya ta , ta aminta da wannan zancen insha Allahu ba baza mu taɓa dana sani ba.''
jikin baffa a sanyaye yace '' to Ubangiji ya shige mana gaba.''
amin ya Allah yace sai da ya rako baffa har gida sannan sukai sallama, baffa shigowa yayi cikin gidan yana kallon giɗaɗo da yake zaune kusa da dada, zama yayi gidado gaishe da shi yayi yana cewa kaji abin da mutumin nan yace ko baffa gaskiya ana mulkin kama karya a cikin ruggar nan.
ajiyar zuciya baffa ya sauke yace '' alhamdulillah to giɗaɗo kowa yayi na gari dan kansa ni wallahi ina cikin tsaka me wuya rana zafi inuwa ƙuna.''
giɗaɗo yace '' baffa me ya faru badai harɗ'o bane ya kirawo ka akan maganar kudin sa?.''
girgiza kai baffa yayi cikin tsananin tashin hankali yace '' malamin su mardiyya ne ya turo iyayen sa yana son ta , kasan halin da ake ciki ba sai nayi maka bayani ba , bana so ran mutum ɗaya ta sulwanta a dalilina inhar ina son zaman lafiya a cikin garin nan sai anyi shaɗi kasan hatsabibancin Maude zai iya zuba guba a jikin sandar da zai yi shaɗi da ita ya kashe dan mutane saboda haka fa kowa ya kasa tsayawa da mardiyya , abu na biyu wannan yaron dan gidan EL'BASHIR MANSUR Turai ne bana so nakai ya'ta gidan da za'a raina mu a raina ta na fiso ta auri dai-dai da ita.''
da sauri Dada tace '' a'a kar mu zo muna dana sani kwana biyu hankalin mu ya kwanta da wannan tujarar ta mutumin nan gaskiya ni daman halina, be kwanta da karatun da take ba ko wacce sa'ar ta , tana dakin mijin ta , ita , tana ce sai tayi boko.''
Giɗaɗo yace '' a'a Dada ilimi shi ne hasken rayuwar al'umma, muma duk da ace mun yi ilimin nan da rayuwar mu ba zata kasance cikin hudu ba , komai sai da ilimi ake yin sa , jahili baya jan ragamar al'umma, dan haka ki ci gaba da yi mata addu'a ga wata shawara me zai hana a daura musu aure tun da shadin nan ba addini bane al'ada ce , amma ku, kun saka shi ya zama wajibi ayi mata auren sirri tun da ba wani shegen ne ya haifa maka yar'ka ba.''
baffa murmushi yayi yace '' ta yaro kyau take bata karko ya za a yi na aurar da yarinya ta a sirrin ce ? ita ba mutuniyar banza ba kuma ba shedu idan wani abu ya faru fa ? duk da bana fatan haka , malam Ishaq yace zai yi bincike idan mutumin kirki ne sai mu yi abin da ya dace mu kuma ci gaba da rokon Ubangiji Allah ya zaɓa mata abin da yafi zama alkairi.''
amin dukkan su, suka amsa dashi.
wannan kenan
karurruka ne a gaban sa bakake hulik da su sai uban haushi suke yi wuyan sa , sakar huri ce , sai kuma wata katuwa kamar laya dantsan hannun sa kuwa, duk gurune na laya , taɓar wiwi ya zuƙa ya fesar idanuwansa sun kada sun yi jajir.
Allah ya wuci zuciyar ka ranka ya dade cewar wani makakken matashi ya fadi haka kamar zai mai sujjada.
Wallahi wallahi wallahi Modibo inhar zancen ka gaskiya ne yau lassana ba zai yi kwanan duniya ba, budurwar tawa zai ce yana so lallai tarihi zai maimaita kansa.
Cewar Maude da yake busa hayaki yana ta cije baki kamar wanda zai tsinke labɓan'sa.
Modibo yace '' adai jamai kunne gaba idan ya kara sai ka aika shi lahira.''
kwafa yayi ya fara tafiya a guje karurrukan'sa suka soma take mai baya modibo bin bayan sa yayi yana wata irin tafiya irin ta yan iskan nan wa'yanda suka addabi al'ummar gari.
hadari ne ya hado iska ta soma rangaji tana Kada, bishiyun da suke cikin dajin amma ko a jikin su, nan danan ruwa ya kece kamar da bakin kwarya.
a bangaren su kahu sunusi masaukin su, suka koma uncle Sa'eed yace '' anya kuwa ba hakura za muyi ba yaushe aseem zai iya yin shadi daman wai har yanzu ana irin wannan al'adar? .''
Sa'eed ina zan sani amma muji ta bakin sa idan har yaga zai iya gashi ga hanya nan
cewar kahu sunusi.
wayar uncle Sa'eed ce tayi ringing ganin sunan Alhaji sani yaja guntun tsaki ya ajiye wayar yana cewa wallahi hat abada sani ba zai canza halin sa ba , tun ɗazu yake kirana yanzu nasan yana nan yana ta ɓala'i , ya rasa inda zai saka ƙansa.
Kahu sunusi yace '' kulu baya ba mamakii ma suna tare.''
hmmm baka ji abin da ya faru ba ai sun yi faɗa kuma kasan idan sun yi faɗa suna jimawa basu shirya ba.''
Kahu sunusi yace '' haka ne wallahi.''
Ya faɗa yana tashi rufe tagar dakin da suke ciki yayi domin ruwa har ya soma shigi musu ruwan da ake ba ƙarami bane.''
gajiya yayi ya daga wayar tare da karawa a kunnen sa ne yi magana ba cikin faɗa kahu sani yace '' wato kun ware ni ko? bani da matsayi kun tafi nemo wa dan dan uwana aure ba tare da Ni ba ko da yake sai kadangare yaga bango Ya tsage yake samun samar shigowa kai naga ba dakin mu ɗaya ba kana dan kishiyar babar mu amma kafi kowa iya shishshigi ko wanne waje kai ne sahun gaba wallahi yaya sunusi kanan kunya kai ake kira da dankasa a sarar dangin.''
karɓar wayar kahu sunusi yayi yace '' haba sani me ya saka kullum kana girma ka a ƙara shiga dawa?.''
ai daman haka za kace ya faɗa yana kashe wayar 'sa
dan murmushi kahu sunusi yayi domin idan da samu sun saba da tijarar sani.
Wannan kenan.
K'asar birmu
washe gari.
Asibiti.
zuwa yanzu cikin ta ya saki period din ta , ta zo har ta ƙarin ruwa an cire mata idon ta a rufe bawai bacci take ba tunanin rayuwa take.
gaban ta ne ya fadi jin sallamar aseem SUHAILA amsawa tayi tana gaishe dashi ciki ciki ya amsa tare da tambayar ta yame jiki.
kallon fuskar mardiyya tayi da tayi fayau, kallo ɗaya za kayi mata kasan bata da lafiya tace '' da sauki amma ɗazu ma ce min tayi cikin'ta yana yi mata ciwo.''
karasawa gaban gadon ta yayi be ce wa SUHAILA komai ba , allurar da take hannun sa , ya saita yace '' gyara zan miki allura.''
da sauri ta buɗe idon ta , tana ta matsar kwalla bakin ta na rawa tace '' na samu sauki wallahi yanzu ba abin da yake min ciwo kafar ma na samu lafiya.''
sarke hannuwansa a kirji yayi ya zuba mata ido sai kace wanda yace zai mata wani abu duk tabi ta rude.
SUHAILA tashi tayi tace '' dan Allah mardiyya ki tsaya a yi miki allurar nan , ita ce samun saukin ki kalli kafar'ki duk ta kumbura.''
wata uwar harara ta zabga mata , aseem mamaki ne ya kama shi ashe abin nata iskanci ne cikin daure fuska yace '' za kiyi abin da nace ko sai ranki ya ɓaci?.''
hawaye ta share tace '' dan Allah kayi min a hannu na.''
suhaila dariya ce ta kusan subbuce mata dan haka ta fita ban da abin mardiyya, kwana nawa ne zasu mallaki junan su abin da , take boyewa dole ya gani.
aseem kuwa ran'sa ne ya ɓaci yace '' ke me kika mai dani ? bansan aiki na ba ko kuma dan iska mene abin da zai birge ni a jikin ki ? kallon ki nake matsayin ku ɗaya dana , namiji.''
da sauri mardiyya ta tashi tsaya chak da kukan ta , ta ɗago da dara daran idanuwan'ta wanda sun fara canza launi daga fari zuwa jaaa.''
jikin ta a sanyaye ta juya bayan ta , ya mutsa fuska yayi yana cewa ke wacce irin ƙazama ce ki kwana ki tashi da kaya ga jini ya fara ɓata miki jiki amma baki san ki, gyara jikin ki ba to bazan iya taɓa ki ba sai kin gyara jikin ki,
sosai halayen sa, suke bata mamaki ga kunyar da ta kama ta , tashi tayi zaune ta sauko daga kan gadon tace '' kayana suna makaranta..''
banza yayi mata ya fita be jima ba ya shigo ledar da ya miko mata ce ta amsa kan'ta yana ƙasa.''
Cikin deep voice din sa kamar ko da yaushe yace '' maza kije ki gyara jikin ki , kiyi sauri ina jiran ki.''
to tace mai shiga toilet tayi ta buɗe ledar doguwar riga ce sai sabon wado sai pad a ciki wanka tayi ta saka kayan ta a cikin ledar.da ya sako mata kayan da ya , yawo mata, fitowa tayi tamkar wacce tayiwa Sarki karya.
ransa ne ya ɓaci lokacin da ya kalle ta , ko hijabin nan na uban mene sai wani takurewa take a cikin'sa , ko mene abin boyewa a jikin ta owo.
ɗaga rigar'ta yayi ya zame wandon ta kasa da sauri ta yi rufa da ciki domin bata taɓa zaton haka zai mata ba , ta zata irin yadda yayi mata jiya haka zai mata..''
asim kau da ƙansa yayi ya saita allurar daidai ida yake so ya shiga sannan ya tsira mata ,
ban da gumi babu abin da take yi dan ma ta lura dashi kamar hankalin sa baya kan, ta shi ne babban samun sauƙin ta.
gamawa yayi ya saka mata audiga sannan yace '' kisha maganin ki.''
bata ce mai komai ba ta gyada kan'ta aseem da sauri ya fita daga cikin dakin, jikin ta a sanyaye ta , tashi zaune ta mai da wandon ta , ta zuga uban tagumi suhail shigowa tayi tana cewa ya dai ko dai an sha love ne? shima naga kamar baya cikin nutsuwar'sa.
MARDIYYAH tace '' me kike nufi?.''
zama SUHAILA tayi tace ''. Kin fi kowa sani.''
Hmmm kawai tace , ta koma ta kwanta.
SUHAILA tace '' mrs aseem dan Allah me ya faru ne ? kin ga a yadda ya fita kowa tab gaskiya fa kina da aiki wallahi.''
takaici ne ya kama mardiyya tace '' ko kuma uban aiki, dan Allah suhaila ki dena saka auren da zanyi a cikin jerun aure, ni wallahi yadda kika san na ce na fasa.,....
Amina alhasan Muhammad opay 1k
8141785374
Yan Niger
1000fcfah ku turo da shedar biya ta wannan number
08141785374.
sauran kadan free page ya kare karki bari ayi wannan tafiyar babu ke.
*JAMI'A*
EPISODE 13
SUHAILA zaro ido tayi tace '' ki fasa me ?, gaskiya mardiyya ki dena wannan hali ke yanzu idan kin fasa wa ne zai biya miki registration? ,ni wallahi yau aseem ya burge ni kinga fa kaya, ya baki da audiga saboda yana so ya kare miki dajarar ki da mutuncin ki.''
Hmmm kawai tace domin maganar da yayi mata , tayi mata ciwo a cikin zuciyar ta wai bata da maraba da namiji a gurin sa.
suhaila kayan ta , ta dauka ta shiga toilet ta wanke ta shanya sannan ta fito lokacin tayi bacci.
kallon agogon wayar'ta tayi karfe goma sha biyu, jarabawar yamma ce da su ya kamata ace sun bar asibitin nan.
tana cikin wannan tunani , taji kar'ar buɗe kofa tare da sallama.
da sauri ta ɗago kan'ta tace '' wa'alaikassalam barka da rana.''
dr Haris amsawa yayi yana kallon mardiyya da take bacci yace '' ya mai jiki?.''
dr Haris ya tambaye ta cikin murmushi.
suhaila tace '' da sauki alhamdulillah muna so mu tafi saboda muna da jarabawa.''
jan kujera yayi ya zauna yace '' okay ɗazu na gama duba folder din ku da dr aleema ta turo min ta , computer naga kumburin kafar ma ya yi ƙasa sai kadan Allah ya bata lafiya.''
amin ya Allah SUHAILA tace.
mardiyya a hankali ta a buɗe idon ta , da sauri ta , tashi ta zauna tace '' SUHAILA karfe nawa ??.''
dr Haris sosai ya kurawa mardiyya ido, tafarar ɗaya yaji son yarinyar a cikin zuciyar sa , tun da ya shigo zuciyar sa ta ƙasa nutsuwa.
dan murmushi yayi mata yace '' masha Allah, kyakkyawa ya jikin naki?.''
da sauri ta kalle sa ido hudu suka da aseem da yake sanye cikin shadda gezna dark brown sosai ta haskaka farar fatar'sa, aikin jikin shaddar milk colour monogram, hular da ya saka ma milk ce hannun sa riƙe, da briefcase da alama yanzu ya shigo cikin asibitin, farin glass ne a fuskar'sa.
dr Haris juyowa yayi yana cewa oga barka da zuwa.
ba tare daya kalle sa ba , yace '' brk dai..''
dr Haris yace '' dr ina fa kamu dan Allah a temaka min ashe daman rabo ne ya shigo dani dr aleema ce min tayi dakin nan yana karkashin ikon ka amma ga folder din na duba kafin ka shigo kai masha Allah wallahi ina kamu.''
cije lips din sa yayi, ya kalli suhaila yace '' I have dismissed us; come back every week to wash the feet ta ci gaba da shan magani.''
Godiya suka yi mai gaba ki dayan su fita yayi yana ji kamar ya shake haris ban da rashin kamun kai shi zai saka a cikin wannan zancen nasu to wai ma ina ruwan sa , aure n za suyi na contract idan maza dari zata tara wannan damuwar ta ce ,
ha ya fara tafiya ya juyo kiran haris ya shiga yi haris fitowa yayi yana cewa oga wallahi cewa nake ta bani number wayar ta amma taki wai bata da waya nasan faɗa tayi kawai bani ne ba za tayi ba idan suka tafi ban san inda zan same su ba.
ya faɗi haka cikin damuwa.
ASIM ji yayi kamar ya kifa mai mari yace '' kaje lab kace a baka result din test din dana turo ɗazu.''
to yace mai badan ya so ba da sauri ya juyo su mardiyya har sun fito ganin yadda asim ya zare gida, dole ya tafi lab badan ya so ba su kuma suka fita daga asibitin
sai da ya tabbatar yayi nisa sannan ya huce office ɗin'sa.''
★★★★
Wannan kenan
Mommy mommy da sauri mommy ta fito jin kamar saukar aradu cikin mamaki tace '' ahlam bakya ji sai da kika dawo.''
cire Glasses din ta , tayi tace '' wallahi mommy hankali na bazan kwanta ba , dakyar ya barni na dawo wai sati uku zan yi.''
mommy tace '' Allah y kyau ta ,
aneesah da sauri ta rungume ta , tana cewa aunty ahlam sannu da dawowa.
yauwa dan Allah ga key din mota'ta ki bawa wani a cikin ma'aikatan gidan nan ya shigo min da trolley ɗi'ta.
amsa tayi ba tare da tace komai ba ta fita.
Adyan saukowa tayi tana cewa aunty ahlam su uncle sun tafi tambayo wa yaya aure.
what da huri haka ta , fadi haka tana kallon mommy.
mommy tace '' to me za'a jira gwara ayi abin da za ayi wata kila ma yau su dawo.''
Hmmm kawai ahlam tace tana zama akan kujera babban abin takaicin ta kawayen ta , kowa cewa yake idan bikin aseem ya tashi ta fada su , yanzu ina zata saka kan'ta, da wannan abin kunyar da yaya ya janyo musu.''
zama mommy tayi tace '' me za kice a dafa miki ?.''
ahlam da abin duniya ta ishe ta , tace ''ni wallahi bana jin yunwa,mommy wai dole ne sai ya auri wannan yarinyar wallahi shi da ita akwai banbanci.''
mommy tace '' ahlam wallahi inhar kina so mu daidai ta dake ba ruwan ki da maganar auren nan wai ke ce zaki zauna da ita duk kin bi kin ɗaga hankalin ki?.''
aunty ahlam wallahi har da mommy suka hada sukai wa asiri ba iya yaya aseem sukai wa ba mommy ta kasa fahimtar wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa kamar FAMILY din mu ace yaya ya auro mana bararoji , kuma ba wayayyiya ba yar gidan matsiyata.''
Aneesah ta fadi haka hawaye yana bin kuncin ta , bata san ya za tayi ba da soyayyar asim jiya yadda taga rana haka taga dare.
mommy shiru tayi musu domin ta lura dukkan wani bayani da za tayi musu ba za su fahimta ba sunyi nisa basa jin kira, dan haka shirun ta yafi alkairi, addu'ar da za tayi musu Allah ya ganar dasu gaskiya.''
Ahlam tace '' hmmm ashe kema kin gane haka wallahi wannan zubewar mutunci zai jawo mana.''
aneesa zama tayi ta zuba ta gumi ranta na mata ƙuna, tace '' hmmmm Allah ya dawo da shi cikin hayyacin sa.''
amin ya Allah ahlam tace.
Rafi'a da ta fito tace '' aunty ahlam saukar yaushe ?.''
ahlam kallon ta , tayi tace '' yanzun nan na sauka hankalina yaki kwanciya kamar yaya shi zai auri bararoji yar zaman daji ke daga jin wannan maganar ai kinsan aikin asiri ne wallahi.''
Rafi'a tace '' hmmm Allah ya kawo karshen abin su kahu sunusi har sun tafi tambayo mai aure yadda kika san dasu aka haɗa anya kuwa ba har dasu tayiwa asirin ba?.''
tsaki aneesah taja tace '' kema da kinsan inda ake yin asirin da tuni kin tafi ni wallahi bana son mace mara class, ban da rashin sanin ciwon kai mace ta durkusawa namiji tana Allah annabi ya so ta mswww.''
ta ƙara jan tsaki.
rafi'a tace '' kan uba lallai yarinyar nan yau sai na fasa miki baki ni sa'ar