temaka mata kawai dan Allah amma badan halin taba ni nayi mamaki ma wallahi da ta iya fadar sunan ki , kallon mu suke fa wasi gidadawa mara aji da wayewa..''
ajiyar zuciya ta dinga saukewa a ajere ta saki suhaila ta kwanta akan gadon ta hawaye nabin kuncin'ta...''
ya Allah haba mardiyya ya za a yi damuwar wasu ta zama taki, karki bi ki damu har ki rame, asim yace an caka mai ankai ki duk da kasusuwa kin rame..
wata uwar harara ta zabga mata , ta cilla mata pillow tace '' wallahi suhaila bakya jin nauyin fadar magana Allah ya shirye ki.''
Amin ya Allah tace tana danne dariyar ta.
★★★
Wannan kenan.
Aneesah ko zama ta kasa yi banda zagaye a daki ba abin da take yi babban tashin hankalin ta da taji gobe kahu sunusi da kahu sa'eed zasu tafi kasar mali har sun siyi ticket cije lips din ta , tayi a fili tace '' aikuwa sai na kashe auren nan dan wallahi bazan koma landon ba wanne karatu ina nan a zaune..''
adyan ce ta shigo hannun ta riƙe da try tace '' gashi inji mommy tace ki ci kafin ta zo bata yarda ki kwana da yunwa ba..''
aneesah tace '' hmmm ajiye.''
adiyan ajiyawa tayi akan Centre table ta fita daga dakin da sauri ta ƙarasa gurin asim da yake shugowa tace '' congratulations gobe uncle sunusi zai je tambayo maka aure.''
gaban'sa ne ya fadi yanzu shine zai auri wata mace ba afiyar sa ba innalillahi wa'inna ilaihir raji'un dan dai yana son cika burin mahaifiyar sa da ba zai yi wannan auren ba , fuskar'sa a ɗaure yace '' aure kuma?.''
besan ma bakin sa ba ya fadi haka ba.
tuna wa yayi da irin katoɓarar da yayi be tsaya jin me zata ce ba yayi gaba.
Amina alhasan Muhammad opay 1k
8141785374
Ku turo da shedar biya ta wannan number 08141785374
*JAMI'A*
Ina hajjiyo da yan kwalisa to ku garzayo OUMYASMEEN COLLECTION domin samun kaya na kerewa Sa'a ki zama fitila wajen oga ba abin da bana siyarwa cikin fara shi me sauki
https://chat.whatsapp.com/DSd6g96hO2F41IG6k43rEl?mode=ems_copy_t
*Episode 1¹*
Da sauri asim ya ja baya yana aikawa da rafi'a wani irin kallo saboda ta sha gaban sa , ba tare da ta kalle sa ba cikin kuka tace '' a yau daure fuskar'ka ko kwarjinin ka ba zai yi tasiri ba akai na ba , wallahi ka sani ina son ka amma ka tafi can zaka auri bare yaya asim saboda da kai har yanzu naƙi yin aure me ya saka za kayi min haka ? sai ka nuna kamar baka san ina yi ba , gida bata ƙoshi ba ai ba akai wa dawa ba .''
ɗurƙusawa tayi tace '' wallahi idan baka aure ni ba , zan iya mutuwa.''
mamaki ne ya kama shi, ji yake kamar ya harba ta in banda rainin hankali shi sa'anta ne ɗogon tsaki yaja ya ci gaba da tafiya hannu ta saka zata rike kafar sa ya janye kafar'sa ba ƙaramin kai zuciyar'sa nesa yau a ba dabe kwaɗa mata mari ba.
cikin kakkausar murya yace '' ko da wasa wannan hannun naki yayi gigin taɓa min jiki na to ranar kiyi kuka da kanki.''
yana kai wannan ya fara tafiya tamkar ba abin da ya faru mommy da ta fito daga daki ta kalli asim tace '' me tayi maka , ka dake ta ?''
mazaiwa yayi yace '' mommy wace ?''
murmushin takaici tayi daman ta riga da ta sani asim wani irin baudaddan mutum ne ba'a gane ina ya dosa yana sai ne , sai ya binne mutum kuma ba yadda aka iya dashi sai dai ido tace '' asim nima abin da kake musu za kayi min? raina min hankali za kayi me rafi'a tayi maka ?.''
ba tare da ya juyo ba yace '' rafi'a kuma mommy ni…..
da sauri ta katsai shi tace '' dakata ke rafi'a me yayi miki?.''
tashi rafi'a tayi tana ci gaba da kukan ta , tace '' na faɗa mai irin son da nake mai shi ne yaja tsaki wallahi mommy idan ban aure shi ba zan iya mutuwa ni na yarda ya auri wacce yake zai aura nima ya aure ni, rana ɗaya sai ayi bikin namu.''
jikin mommy yayi sanyi ta kasa cewa komai Asim tafiyar sa yayi, yabar mommy da sakakken baki cikin kwantar da hankali mommy tace '' kiyi hakuri rafi'a, idan har asim mijin ki ne wallahi zaki aure shi.''
mommy tana kaiwa wannan ta shiga daki ta zauna daukar wayar ta , tayi ta dannawa Asim kira bugu daya , ya dauka mommy tace '' banji kana maganar lefe ba, kasan bana so a saka bikin nan da nisa asim.''
gaban'sa ne ya faɗi wanne lefe ita da za tayi mai aiki shi da ace zai iya fadawa mommy gaskiya da wallahi faɗa mata zai yi yasan za tayi fushi dashi fushi me tsanani besan ya zai yi da soyayyar afiya ba sau tari yayi yunkurin juya mata baya baya iya wa ya rasa dalili shi ƙansa yasan afiyah ba lallai mommy ta amince da ita ba cikin kwantar da murya yace '' mommy wallahi naman ta , kawai abar shi idan ta zo na siya mata kaya.''
cikin mamaki mommy tace '' asim anya kuwa lafiyar ka qalau ? me zaka siya mata ? asim kar naji karna gani karka raina asalin ta ka kasƙantar musu da yarinya, idan kasan baka son ta kawai kayi haka ne domin ka gujewa auren yar uwar ka rafi'a to ka nemo wata dai-dai darana daya na same ka da wani abu na rashin gaskiya ranka zai ɓaci asim lefe kuma ka tambaye ta innerwear din ta , kace size nawa take sakawa sannan number takalmi duk ka tambaye ta.''
cikin son kawar da zancen yace '' mommy ko na tambaye ta ba faɗa min za tayi ba , shi ya saka nace miki haka amma ina ganin kamar adyan ta fita jiki, duk da a cikin hijabi nake ganin ta amma mommy komai idan zaki dauko ki dauki kasa dana adyan.''
dan shiru mommy tayi bata musa shi ba tun da bafulata na ce , kuma duk inda fulani suke an san su da kunya dan haka tace '' to shikkenan amma shekarar ta nawa naji kana cewa kasa da adyan?.''
Asim shiru yayi baya son yayi karya amma idan zai iya tunawa a takardun ta kwanaki da tazo office din sa yaga an saka 2007 yanzu idan akai la'akari da muna Shekara ta 2025 shekarar ta 17 haka ya fadi a cikin zuciyar sa dan haka a fili sai yace '' 17.''
mommy tace '' Allah sarki, Allah ya saka abokiyar zama ce Ubangiji ya zaunar da ku lafiya to fa asim sai kai hakuri kaga yarinya ce amma tana level nawa?.''
takaici ne ya kama shi a zuciyar sa yace '' ba amin ba a fili kuwa sai yace '' level 1 first semester yanzu idan sun gama jarabawar nan second za su shiga.''
Allah sarki Ubangiji ya she mana gaba amma dai ba zaka hana 'ta karatu ba?.''
mommy ta tambaya domin ita fa zancen dadi yake mata domin hasashen da tayi asim ba zai taɓa dana sanin auren mardiyya ba duk da bata ganta ba amma karan farko taji ta samu nutsuwa ta kuma kwanta mata a cikin zuciyar ta.
asim da ya lura mommy maganar dad'i take mata yace '' eh zan barta mommy ina son tafiya asibiti ina da patients da zan duba aikin kwana zan yi.''
okay ba damuwa Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya.
amin yace ya kashe wayar sa zuciyar'sa nayi masa kunci haka kurum daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaki ta dauki son duniya ta ɗorawa yarinyar daba tasan ta ba , dama ace afiyaaaah take so haka da yafi kowa murna shi anya kuwa ba zai fasa ba kar kuma ya aure ta tace ba zai sake ta ba koya sake ta , tace akan wanne dalili ko ita da kanta ta fahimci gaskiya yasan ba za su kwashe ta dadi ba amma bara ya tambayi mukhtar shawara.''
daukar wayar'sa yayi ya nemo number Mukhtar ya danna mai kira har sai ya ya kira sau uku Sannan ya daga hakan ba ɗabi'ar sa bace kira ɗaya biyu ya katsai kiran Muryar mukhtar a shake yace '' kai baka san yanzu lokacin hutawar ma'aurata bane ka kira ni ? ko da yake ba laifin ka bane baka sani ba kai gauro ne har yau baka san wannan ba sai aikin shan pills domin ya rage maka nauyin mara.''
ASIM naushin iska yayi yace '' mukhtar wallahi ka kiyaye ni an fada maka kowa irin ka ne.''
da sauri mukhtar ya tashi zaune daman tsokana ya shirya mai yana office yace '' haba asim wallahi ko makaho ya shafa yasan gaskiya kafi kowa sani ko kafin nayi aure bana yin azumi kai kuwa azumi ya zame maka jinin jikin ka saboda gujewa saɓon Allah ni wallahi Allah tauyasawa yarinyar nan nake domin wallahi Allah ba zaka iya barin ta ta huta ba , kai da yanzu allura ma ta dena daukar ka , kayi wa kanka kiyamul laili ka ce kar a saka auren nan da nisa kai ma ka rage lalurar'ka.''
cije lips din sa ya shiga yace '' lefe na ne dana bari kasan waye ne, ka riƙe tausayin ka , saboda bata isa macen da zan iya hada jiki da ita ba , ka bari idan takai sai kayi min wannan maganar kai nifa duk wace mace idan ba afiyaah ba , bata kai mace ba.''
dariya mukhtar yayi yace '' Allah ya kai mu da rai da lafiya, lafiya kake jera min wannan uban kiran ?.''
Mukhtar ina cikin wani hali mommy bata ga yarinyar nan ba , amma ta fara son ta , har fa da yimin maganar lefe to idan nayi mata lefe sake sabon list za a yi domin sai ta yi min aikin miliyoyin dana kashe mata a kayan lefe duk da nasan mommy ce zata kashe amma ai ya dalilina ta kashe kudin anya kuwa bazan fasa ba kaga yadda yake zabga addu'a mukhtar gobe zasu je tambayo auren ta yadda kasan akan su nake , wannan wacce irin rayuwa ce kowa bakai aure ba , ni ina hakuri da yadda Ubangiji ya yi ni afiyaah nake jira idan lokacin auren'ta yayi sai muyi.''
dariya mukhtar ya danne gaskiya ba haka afiyaah tabar asim ba zai samu lokaci ya bada ayi mai saukar Alqur'ani Allah ya yi mai maganin ta , wannan wacce bakar kaddara ce baya ji baya gani yana tare da wannan lalura amma kace sai ka jira wata shegiya ta gama iskancin ta , sannan kuyi aure aikuwa zai yi maganin ta , duk yadda asim yake kaunar mahaifiyar sa amma ya kasa yi mata biyayya duk yadda akai na , banza wannan me dogon bakin ta bar'sa ba gashi dai ta musulta amma har yanzu ba hasken Musulunci a tare da ita.''
cikin hikima da son nuna mai illar abin da zai aikata yace '' a'a asim kar kayi haka ka daure saboda mommy wallahi idan taji ka fasa wannan aure zata shiga damuwa wacce tafi ta baya tun da babban burin'ta shi ne taga kayi aure taga ya'yan'ka haba asim ka dinga tausayin yarinyar nan wanne aiki za tayi maka har kaci riba kayi hakuri ku zauna lafiya har lokacin da wa'adin'ta zai cika tunda kaga kai kaju ka gani ko dai shadin ne ba zaka iya bane zaka fake da mommy?.''
ya kara jefo mai wannan tambayar.
tsaki asim yayi yace '' ni wallahi mantawa nake ma da wata maganar shadu inshallah zan yi kuma zanyi nasara amma wallahi itama sai taji a jikin ta , ba zan kawo ta nan ba ta miƙe kafafuwa ta zo hutu sai ta gwammace kida da karatu ni gani nake ma setup ne wannan kwailar wa zai wani ce yana son ta idan tana da me son ta a yadda Fulani suke da aure da wuri da tuni tana gidan mijinta shi ya saka ma na amsa zan yi sai naga abin da ya turewa buzu naɗi.''
mukhtar yace '' uhmm uhmmm Asim abin da baka so shi wane yake so yarinya kyakkyawa wallahi idan aka haɗa ta da afiyaaaah ba wanda zai dauki afiyah ko ta ko ina tafi afiyaah kyau ga kyauhun hali yarinya ba ruwanta shiru shiru da ita komai nata cikin nutsuwa take yin sa.''
dogon tsaki asim ya saki yace '' mukhtar dan sa ido ka koma ban sani ba ? kaga kar ka ɓatan rai wallahi ko maganar ta bana so ayi min shegiya da fuskarka yawa butter itafa a fararen ma farin ta bame kyau bane nifa yellown abu baya birge ni.''
mukhtar yace '' asim kafi karfina wallahi.''
Dariya asim yayi yace '' dole ka fadi haka Saboda na faɗi gaskiya sai anjima.''
okay mu jima da yawa ya faɗa yana kashe wayar'sa.
cikin sauri ya tashi ya shiga toilet wanka yayi ya fito ya shirya cikin ɗayanr shadda light blue , sosai tayi mai kyau ta dauki fatar'sa bakin glass ya saka ya shefe jikin sa da turarurruka sannan ya daura a gogo Rolex takalmi ya saka, ya dauki brief case din sa.
ya fara tafiya fitowa parlour yayi ya kashe duk wata wuta da take cikin bangaren nasa sannan ya kulle ya fito, sallama ya shiga yayi wa mommy albarka ta dinga saka mai sannan ya fito.
samun driver sa yayi yana jiran sa , yana fitowa ya buɗe mai mota ya shiga mazaunin me zaman banza ya dauki jarida ya soma karantawa a hankali suka fara tafiya yayiwa mai gadi horn.
ya buɗe musu sannan suka fara sharara gudu wani uban birki yaja da sauri asim ya ɗago yace '' dan ladi lafiya?.''
dan ladi cire bleat ɗin'sa yayi yace '' oga bara na duba ina ganin kamar na buge wani abu.''
kafin ya ƙarasa asim ya buɗe ya fito chak ya tsaya ganin mardiyya tana kuka haka ma suhaila wani tsaki ya ja ko uban me ya fito dasu ana gab da sallar magariba, ga wannan uban hadarin abin da yake fadawa mukhtar kenan ya kasa fahimta.
sosai hankalin mardiyya ya tashi ta ɗago dajin wannan uban tsakin daman zuciyar ta wani irin bugu take mata jin kamshin turaren asim da ya zame mata wani dafi a cikin zuciyar ta , a duk lokacin da taji shi, tsoro da farga ba suka taru sukai mata yawa jikin ta yayi wani irin sanyi 4eyes sukai dashi da sauri ta sunkuyar da kan'ta kasa ga ciwon marar'ta da ya ƙara daɗuwa fargabar da take cikin ce ta haddasa mata jin ciwon ya karu fiye dana da suhaila ce riƙe da kati a hannun ta , ta share hawayen tace '' sister baki ji ciwo ba ko?''
mardiyya girgiza kai tayi domin kafar'ta da mararta wani irin ciwo suke mata daga rigar ta za tayi asim ya daka mata tsawa ban da rashin sanin darajar kai zata buɗe jikin ta kallon suhaila yayi yace '' ki kamata , mu tafi asibiti.''
to tace cikin kuka domin sosai hankalinta yake a tashe ganin yadda mardiyya take kuka tana juyi dakata tayi dan dali ya buɗe musu kofa yana cewa ko nan gaba ku dinga kula Yanzu Allah ya rufa asiri abin be yi MUNI ba.
ya fadi haka yana satar kallon asim domin yadda yaga ran asim ya ɓaci yasan dole zai mai faɗa me ya saka baya lura idan yana tuki.
shiga suka yi asim ya koma mazaunin gaba dan ladi ya zauna gurin tuki ya ci gaba da tafiya basu tsaya a ko ina ba sai a asibitin asim da sauri suhaila ta kalli mardiyya, ba damar yin magana ya ji su ina suka ga kudin biyan wannan asibiti tamkar a kasar waje suke ita tun da take a birmu bata , taba zuwa ba , tadai ji ana fadar sa rabi da kwatan likiticin turawa ne da Indiyawa, ya saka yake da tsada amma aikin kamar a kasar waje.
parking dan ladi yayi da sauri ya fito ya bude musu kofa.
cikin kuka mardiyya tace '' SUHAILA bazan iya tashi ba , wallahi marata tamkar zata fashe.''
asim fitowa yayi, ya dauki jakar sa ya kara wayar sa a kunne ko barin gurin be ba sai ga nurse nurse da gado ɗorawa mardiyya suka yi akai rintsai idon ta , tayi tsoro ya ƙara kama ta , yadda suke tafiya da ita , da gudu tsoro take kar ta fadi ga kafar'ta da take mata wani irin ciwo.''
kai tsaye emergency room suka huce da ita suhaila ta , tsaya a waje tana baza ido tun da suka rabu da asim a harabar Asibitin bata gansa ba , ko da suka shigo reception bata gansa ba ko yana ina ? oho bata da me bata wannan amsar.
cikin daki kuwa MARDIYYAH ban da kuka ba abin da take yi, ta kasa tsayawa ayi mata allura, ga ciwo nacin'ta.
Dr aleema tsaki taja tace '' bara na kirawo doctor ko idan yayi mata magana zata tsaya, yawa ba mace ba ta kasa tsayawa a yi mata allura ta samu relief.''
ta ƙarashe maganar ta , tana kara sakin tsaki tun ɗazu taka lallaɓa ta , amma ta kasa tsayawa gudun kar taje tayi a inda be kamata ba dole ta daka ta.
wata nurse tace '' gaskiya gwara ki , kira shi, shi yayi mata dakan sa tun da mu ta raina mu.''
ba tare da tayi magana ba ta dauki wayar ta , tana dannawa ta kara a kunne tace '' Dr ta ki tsayawa sai kuka take yi, kuma wallahi allurar ita , zata rage mata zafin ciwon kafar ta ta kumbura ga ciwon period da take yi jikin ta zazzaɓi ne amma taki tsayawa ban san ya zan mata ba.''
Okya kawai yace ya kashe wayar sa a aljihu ya saka ya fito ya rufe kofar office din nasa ta wata hanya ya bi sai gashi a emergency world room din da aka shigar da ita ya shiga.
toshe kunnen sa yayi ransa ya kara baci ban da iskanci ta mai da mai asibiti sansanin zaman makoki batare da yayi magana ba ya miƙa, mata allurar da ta haɗa ta bashi mardiyya jin kamshin turaren asim da sauri ta buɗe idon'ta, zare ido tayi ganin sa yana saita allura
yarfa hannu ta fara tana matsar kwallah
safa ya saka, fuskar sa a hade yace '' juyo bayan ki.''
zaro ido tayi, ta share hawaye aleema tace '' barana na temaka mata jikin ta ba dad'i kalli gumin da take amma taki yarda a cire mata hijabi.''
batare da asim ya kalle ta ba yace '' barshi basai kin cire mata hijabi ba ta , daga shi nayi mata allura.''
mardiyya tace '' ba zaka iya yimin a hannu ba ?.''
domin gaskiya ba zata iya buɗe jikin ta ba ya gani kuma duwawun ta.
asim narkakkun idanuwansa ya zuba mata , bece komai ba da sauri ta janye idon ta , ta runtsai ido dakyar ta iya juyawa saboda ciwon kafar'ta, a hankali ta daga hijabin ta , bata daga rigar ta ba.
Asim yace '' aleema riƙe ta.''
gam ta ruke ta ɗaga rigar ta yayi ya danyi ƙasa da pant din'ta ya tsira mata allura ne tsaya kallon jikin ta ba sai ma kau da kai da yayi yan , ya tsuna fuska tamkar yaga kashi.''
mardiyya, bata ji komai ba Bama tasan a gama ba cirewa yayi ta , ya miƙa wa dr aleema audiga.,
amsa tayi ta saka hannun ta a inda, Dr yayiwa mardiyya allura.
tana mulmula mata.
fita yayi ya bar dakin da sauri suhaila ta , tashi zaune tana cewa ya jikin nata..?
asim yace '' da sauki.''
ya faɗi haka a takaice, da sauri tace "zan iya shiga na ganta...?"
banza yayi mata domin wata nurse ta tsayar da shi tana nuna mai wata folder.
Amina alhasan Muhammad opay 1k
8141785374
Ku turi da shedar biya ta wannan number 08141785374
Yan Niger my nita.
1000fcfah
Ku turo d shedar biya ta wannan number 08141785374
*JAMI'A*
Ina hajjiyo da yan kwalisa to ku garzayo OUMYASMEEN COLLECTION domin samun kaya na kerewa Sa'a ki zama fitila wajen oga ba abin da bana siyarwa cikin fara shi me sauki
https://chat.whatsapp.com/DSd6g96hO2F41IG6k43rEl?mode=ems_copy_t
*Episode 12*
DA sauri SUHAILA ta bi bayan'sa tana cewa Dr zan iya shiga.?
Asim yace '' A'A.''
yana gama fadar haka , ya fara tafiya yana duba a gogon hannun sa.
tsaki SUHAILA ta saki tace '' sai shegen girman kai zaka shigo hannun mune wallahi sai ka yi dana sani.''
juyawa tayi ta koma kofar dakin da aka shigar da mardiyya.''
jingina tayi da bango sai rarraba ido take saboda ganin fararen fata, suna shige suna fice tamkar a ƙasar waje take ba a kasar birmu ba.
da sauri ta juyo jin an buɗe kofa ganin an turo mardiyya a kan gado da sauri tace '' likita lafiya naga idanuwanta a rufe?.''
dafata dr aleema tayi tace '' allura aka yi mata , so bacci ya dauke ta allurar da dr yayi mata tana saka bacci idan ta , tashi zaki ga ta samu sauki cikin ikon Allah.''
da kallo take bin dr aleema tana mamaki yadda take yin hausa gata dai yar kasar Japan.
kai kurum ta gyada mata , tabi bayan su wani daki suka shiga da ita , itama da sauri ta shiga bayan sun saka ta a gado dr ta daura mata ruwa ta juyo ta kalli suhaila tace '' Please ki kula sosai idan ya kusan karewa ki danna bell wani a cikin nurse zai zo ya cire mata.''
SUHAILA tace '' to mun gode.''
dan murmushi tayi tace '' aiki na ne ba godiya a tsakanin mu ai yar gidan doctor ce.''
Suhaila tace '' haka ne wallahi.''
yauwa ta faɗa tana fita daga cikin dakin tare da ja mata kofa.
suhaila ta gumi tayi tana bin kafar mardiyya da aka nannaɗe da bandeji.
ƘASAR MÃLÏ
TIMBUKTU DAJIN GOURMA RUGAR HARƊ'O BELLO
WASHE GARI
fulani ne cike a gurin yayin da suke sanye da kayan saki gaba ki ɗayan su farare tas da su a tsakiya wani farin dattijo ne sanye da kayan saki farare da mayafi green ya lulluɓe jikin'sa , kansa hula ce irin ta kaba yana riƙe da sanda ya harde kafafuwansa guri daya yana girgiza wa , sun dade a haka sai da ya gama alhinin'sa sannan yace '' za mu fara ɗaukan mataki akan duk me shigo mana yana kashe mana dabbobi ana kashe mana rayuwan yan uwan mu, sannan doka ce ba mu yarda duk wani bahilatani da yake cikin wagga rugga ya auri kaɗo ya kawo mana shi cikin wagga rugga a irin haka ne ake fitar mana da sirri bamu da wata ƙasa da ta huce wannan dajin idan har ba mu dauki mataki ba tofa wannan sansani da muka kafa tsahon shekara goma sha takwas zai rushe za mu ƙara tashi mu bar gurin'nan wanda hakan babban bakin ciki ne a gare mu, kowa yasan fulanin daji fulanin tashi ne amma haka mukai kokari tun da yan uwan mu suke ɓata muka sami wanga daji muka zauna ina me magana da babbar murya a matsayina na shugaba a cikin wannan daji duk wani kaɗo da kuka gani ba tare da rigar irin ta mu ba kuyi mai yaren mu idan ya'ki baku amsa ku kashe shi dole mu dauki fansar shanayen da aka kashe mana jiya sannan a na bin ya'yan mu mata ana yi mu su fyaɗe .''
jikin wasu daga cikin fulanin n yayi sanyi ganin wannan rashin adalci saboda kaɗo su, suke zuwa siyan nono ko manshanu ku kuma shanayen su daga garuruwa hakan babbar barazana ce ga , kasuwancin su.
wasu kuma suna ganin hakan shi ne dai-dai saboda ana keta haddin ya'yan'su.
harɗ'o bello tashi yayi, mutane mara mai baya yayi jikin baffa a sanyaye ya yo hanyar ruggar sa bakin sa dauke da sallama ya shigo.
Inna da take tangaden garin gero ta ajiye ta tashi cikin harshen fulanci tace '' sannu da zuwa na kawo maka abincin ka?.''
zama yayi yana cewa '' murja barshi ba sai kin kawo min ba wannan taro da naje abin be yi da dadi ba hamma be kyau ta ba ya dauki hukuncin da be dace