Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 10
flat a kan gado tana dauka kiran ya katsai number ba damar bi prevent number ce. ɗogon tsaki taja ta ajiye wayar akan drawer. hawa kan gado tayi tana kwanciya a jikin sa haɗe bakij su tayi wani irin zazzafan saƙo suke aikawa junan su. a bangaren AFIYAH tun da sukai sallama da asim ta kasa komai ganin har 1:30 tashi tayi, ta cire rigar jikin ta da sauri ta juyo jij motsin Joseph cikin mamaki tace '' Joseph daman kaman kana cikin gidan nan?.'' wani mugun yawu ya haɗiya sosai girman sa ya tashi ganin afiya a haka. dakyar ya isa saita ƙansa yace '' eh wallahi tun safe ina nan.'' Ya faɗa haka yana kafe ta da muci mucin idanunsa sheɗan na kawata mai isa dan dai yasan afiya tafi karfin sa , ba zai taɓa samun taba.'' far tayi da idon ta tace '' Ohkay.'' Joseph yace '' ya nagan ki, a haka..?.'' wanka zanyi zan tafi gurin asim ta faɗa tana shiga toilet ba tare da ta tsaya taga me zai ce ba. bathroom ɗin ta tamkar ka zauna kaci abinci komai na gurin luxury ne , tiles dark bue ne da fari hakan ba karamin kawata bathroom ɗin yayi ba shiga cikin bathtub tayi kan fanfon ta murɗa a hankali ruwa ya fara cika gurin, wani daddaɗan kamshi me sanyi yana tashi. limshe ido tayi ta dade a haka ba tare da ta buɗe idon ta ba , abubuwa da yawa suna dawo mata dakyar ta iya tashi tayi wanka. bayan ta gama ta ɗauro towel ta fito tana tsane kan'ta da towel zama tayi akan gado tana kwalawa Charity kira. da sauri ta shugo tana cewa afiya lafiya me ya faru. kan'ta ta ɗaga sama tana kallon ceiling tace '' dauko min kayana.'' to tace ta ƙarasa shugowa ta buɗe wardrobe, abaya yar gidan *HAAL INC* ta dauko mata dark grey colour buɗe bangaren da taka ajiye inner wear ɗin ta tayi ta dauko mata bra da pant ta ajiye mata turare ta dauko ta feshe su da shi tace '' shikkenan nan..?.'' ɗan murmushi tayi tace '' a'a sauran ki takalmi da jaka wanda zai yi matching da wannan kayan.'' okay ta faɗa tana juyawa inda taka ajiye takalman ta ta buɗe kofar Glass ce takalma ne sunfi guda ɗari a jere sai kace shagon sai da takalma ta buɗe, ɗauko wani purple colour tayi da adon grey kamar dai yadda adon rigar tata yake ɗab gidan *Prada pointy toe heel* ajiye mata tayi sannan ta rufe kofar Glass ɗin ta tafi ɗaya ɓangaren da jakunkuna suke kamar yadda tsarin takalma yake haka ma tayi wa na jaka daukar wata jaka tayi itama purple ce da ratsin grey colour yar gidan yar gidan Hermes birki bag. ajiye mata tayi ta fita tashi afiya tayi tana jin kan'ta yana rasa mata ko dan yau bata yi chaji bane , shi ya saka damuwa take neman jefa ta a wani hali, tashi tayi ta fara tafiya buɗe lokar ta tayi ta dauko wata roba cike da magani na kwaya, zazzagowa tayi ita kanta bata san iya adadin da ta zazzago ba ta watsa a baki ruwan da yake kan bedside lamp ta ɗauka ta kora magungunan da ta sha, riga da wando ta fara sakawa sannan ta saka a baya. ta feshe jikin ta da tsadaddun turarurruka mayafin rigar ta daura akan ta , kalbar ƙarin gashin da akai mata ta zubo gadon bayan ta jakar ta ta dauka ta saka wayar ta da key din ta. ta kalmin ta ta saka me dan matsakaicin tsayi, yau fuskar ta ko kwalliya bata tsaya yi mata ba ban da lipstick da ta shafa domin ita kwalliya sai da kwanciyar hankali ake yin ta. cikin ƙasaita irin na cikakkun matan nan masu aji da ji da kansu haka take takun ta kai kace dole akai mata ba son tafiyar take ba. ko da ta fito parlour ba kowa bata tsaya yiwa Charity magana ba ta buɗe kofa ta fita, motar ta da take harabar gidan ita ta buɗe ta shiga, sakin kiɗa tayi a motar a hankali tana bi ta fara tafiya horn tayi wa me gadi ya wangale mata gate din ta fita a guje sosai take sharara gudu domin bata da wata bukata da ta wuce ta gan'ta agaban asim. a gabaƙin get ɗin makarantar, ta tsaya aka soma checking ɗin ta , wata mota ce ta tsaya white colour ƙirar Bugatti la voiture noire zoge glass ɗin motar mamallakin motar yayi. baki ne amma jikin sa irin chocolate colour ne kansa babu gashi ko ɗaya sai tarin ƙasunba da gemu da ya tara. ƙurawa afiya ido yayi da take tsaye ranta duk a ɓace kamar basu saba ganin ta ba amma duk lokacin da zata wuce sai sunyi checking ɗin ta sai kace zata shigo da mugun abu cikin makarantar. jikin tane ya bata ana kallon ta ɗago idon ta tayi, four eyes sukai dashi ɗauke idon ta , tayi tana yiwa me mara checking ɗin motar ta magana tace '' ka gama zan iya tafiya?.'' be bata amsa ba sakamakon hannu da wannan mutumin ya ɗaga mai jikin sa na rawa yace '' ina zuwa shugaba yayi kira?.'' taɓe baki tayi bata ce mai komai ba ya tafi da gudu ɗurƙusawa yayi yana cewa oga gani nan ranka ya dade Allah ya ja zamanin ka , Abdulwahab yace '' wannan irin ta mu ce?.'' ƙasa ƙasa yace '' tab gurin dr ASIM nake ganin tana zuwa kuma sau tari ina ganin su tare ranka ya dade daga ganin wannan za tayi maiƙo komai gashi nan a ciki dam dam?.'' cikin mamaki yace '' daman shima yana yi amma yake kallon mutane tara tara saboda shi ne babba ba me iya tsawatar mai kana ga kwana ki wata shegiyar doka da ya kafa wao duk malamin da aka kama ya lalata yarinya sai an kore daga makaranta kuma sai ya auri yarinya.'' wani ashar jallo ya lailayo yace '' yace kyale dan kan uba shi waliyi ne da zai ga irin wannan a kusa dashi ya kasa taɓa ta karya yake ai tuggu za ku haɗa mai wallahi gwara yayi gaba nima fa ina tunanin bincike yake akai na ya fara lura ina daukar yan mata ana kai wa oga su.'' Abdulwahab yace '' hmmm jallo wannan wanne irin sharri ne bamu kulla mai ba sai ya fita ya iya takun sa wallahi yadda kasan me gani har hanji ita dai wannan kwantenar a san yadda za a yi a kawo min ita yau na huta da ita domin wallahi jallo ganin ta da nayi , ji nake ina tsiyaya dole ko dan na baƙanta mai rai na fara soyayya da yarinyar nan yasan abin da yake mun sani.'' baka da damuwa yallaɓai cewar jallo. kudi ya ciro daga aljihun sa ya miƙa mai godiya ya shiga yi yana komawa da sauri kallon afiya yayi yace '' kin yi babbar Sa'a ranki ya dade oga ya ƙyasa.'' haɗe rai tayi ji take kamar ta zabga mai mari, dauke kanta tayi ta buɗe motar ta , ta shiga da gudu ta shiga Cikin Makarantar har tana neman taka jallo. bata tsaya a ko ina ba sai a bakin office ɗin asim parking tayi. ta fito tana tafiya dakyar ji tayi taci karo da mutum a bakin kofar shiga office ɗin nasa da sauri ta ja baya tana ƙare wa mardiyya kallo yawu ta tofa mata a fuska yana matsawa gefe ya tsuna fuska tayi ganin takalmin kafarta da be wuce naira biyar ba domin irin slipper ɗin nan ne cikin tsawa da bala'i tace '' ke wacce irin dabba ce da bakya lura da hanya zaki bige ni?.'' SUHAILA da taji wulakancin da tayiwa mardiyya yayi mata zafi ta zabgawa afiya mari kafin ta ƙara wani yunkuri ta ƙara zabga mata hagu da dama tace ''ke a gidan ku ba a koya miki, sanin darajar ɗan adam ba ? gaki nan dabba a cikin jakuna kina abu na dabbobi kin tawo kina rangwada to ba wanda zaki birge sai dabba irin ki.'' ASIM da jin ana cin mutunci da kuma jin hayaniya da sauri ya fito ganin abin da yake faruwa ya harde hannuwansa a kirjin sa suhaila da sauri ta juyo gaban ta na faduwa ita kuwa MARDIYYAH ta kasa ko da motsi ganin irin kallon kaskancin da yake jifan su dashi. juyawa yayi yana cewa ku shigo. mardiyya kuka ne kawai bata saka ba idon ta har ya fara kawo kwallah daman akwai fanfo a gurin wanke fuskar ta , tayi ta bi bayan su ganin yadda office ɗin nashi yake a share a goge gudin kar yayi musu faɗa sai suka ajiye takalmin su a waje afiya kuwa tuni ta dade da shiga. bi bayan ta suka yi zama sukai nesa da ita mardiyya da gaba ki ɗaya tsoron asim ya gama cika mata zuciya. ASIM sai da ya gama shan kamshi sannan yace '' me ya haɗa ku?.'' AFIYAH tace '' no sweat karka damu basai ka dauki action akan su ba na yafe musu, na lura jahilci ke ɗawainiya dasu musamman ma wannan kidahumar ita ce babbar mara hankali bige ni tayi, nayi mata magana suka fara zagina daman ba su ke mana kidnapping ɗin yan uwan mu ba ba mamaki har da iyayen ta a ciki ko wani nata Saboda tsabar talauci yayi musu yawa da rashin sanin ciwon kai da hakkin dan adam su dinga sace yan uwan su , suna cewa a bada kuɗin fansa tur da halin ku..'' domin kallo ɗaya tayi wa tayi wa mardiyya ta lura ita bafulata ce. ASIM yace '' okay ku me kuka zo yi?.'' inda inda suhaila ta fara. tsawa ya daka mata yace '' ku fita waje idan na gama magana da ita kwa shigo idan kuma sauri kuke ku yi yafiyar ku.'' MARDIYYAH tashi tayi ta yi sauri buɗe kofa ta fita suhaila na biye mata baya hawayen da take riƙe wa suka sami nasarar gangarowa daga kurmin idon ta tace '' suhaila anya kuwa zan iya ? kallo wannan shegiyar ta ci mutuncin mu be tambaye mu yaji me ya faru ba yace mu fita.'' suhaila da take jin kamar ta rufe afiya da duka tace '' inshallah kamar yadda ta saka mu bakin ciki mardiyya sai kin saka ta ciwon zuciya wata kilama wannan ce da bayan ya sake ki ta gama gararan barta a gari ta shirya aure za su yi aure ko baki ji sunan da take kiran sa da shi ba ?.'' ciki rawar murya tace '' wallahi wannan be dame ni ba amma suhaila karfa yace ya fasa ko baki ga kallon da yake jifan mu da shi ba? ni wallahi tsoran matsala nake.'' hmmmm kyale shi akwai ranar da zaki rama, Cewar suhailah. Mardiyya tace '' suhaila idan anyi aure ana samin ciki ko?.'' SUHAILA tace '' da zai biya sadakim ki ne ya zuba miki ido kina cika mai masa da kashi ko shi waliyi ne yana kallon halak ɗin sa ya kau da ido? da ace yana da wata matar ne da sauki amma wallahi ki cire wannan aran ki.'' da sauri ta girgiza kai tace '' wallahi bazan iya ba idan kuma na koma gida da ciki gaskiya na fasa mece makomar abin da na haifa..?.'' SUHAILA da sauri tace '' ke wasa nake miki inshallahu sai kin zama kwararriyar likitan ƙashi.'' ɓangaren asim kuwa kallon afiya yayi yace '' afiyaah be kamata kina zagin yaren su ba ko ki kalle su kice mara hankali kinji ki ɗena abin da kike yi suma Mutane ne kamar mu idan kin ga mutum a cikin rana bawai hakan yana nufin Ubangiji baya son sa ba ?.''' okay na fahimta ta faɗa tana dauke kanta daga kallon sa. Asim yace '' afiyaah bakya zancen auran mu ko bakya sona ne?.'' haɗe rai tayi tace '' sweet ina son ka mana kawai kasan mu ba ma aure da huri , yanzu dai bazan tauye ka ba ka nemi wata ka aura ko dan farin cikin mommy idan lokacin aurena na yayi sai ka sake ta.'' rintsai ido yayi wannan maganar tana ɓata mai rai duk lokacin da ya tambaye ta yaushe za su yi aure sai ta faɗa mai haka amma sai ya danne yace '' zan saka mukhtar, ya nemo min.'' wani murmushin mugunta tayi da , ta tuno da wani abu da sauri tace '' no wannan yarinyar ba me abayar nan ba wacce nace wa iyayen ta yan kidnapping ka aure ta mana kaga yarinya ce ƙarama bata san yancin kan'ta ba , ɓalle idan ka sake ta, tace zata kai ka ƙara ko ta fadawa iyayen ka gaskiya da ita za muyi amfani wajen cikar burin mu , iyayen ta basu da wata waye wa da zasu ce ta cuci yar su idan zaka sallame ta sai ka dan bata na ɓatarwa domin ta dan samu abin kashewa kafin ta samu miji tayi wani auran.'' ta kara sa zancen ta , tana jin ta asararin samaniya saboda jin dad'i tasan halin asim baya son kazamar mace ko yarinya ya fison babba wayayyiya yar gayu wannan idan ya aure ta ko kallon inda take , ba zai ba balle ya haɗa shinfiɗa da ita kuma zata samu damar kaskantar da rayuwar ta , domin wallahi sai ta nuna mata iya kacin ta sai taga uban wa ya tsaya mata , tun da har ta nemi shiga gonar ta sai ta zamar da ita abar tausayi kawar ta , ta jaja mata bala'i. balle babu wani kayan arziki a tattare da ita domin idan tana da ƙira da diri ba zata ding saka hijabi ba, bisa dukkan alamu yarinya ce ƙarama domin ba lallai takai 18 year ba dan haka bata da hankalin sanin me ya dace da ita. Asim kallon ta yayi yace '' anya kuwa afiya kina so na ?, ko kishina bakya yi?'' kwantar da muryar tayi tace '' haba asim nafi kowa son ka nafi kowa son na aure ka nayi rayuwa da kai ta har bada mu haifi ya'ya wallahi a yanzu iyaye na baza su yarda ba ita kuwa wannan kowa yasan fulani suna yiwa ya'yan su aure da wuri itama wannan da kaga tazo makaranta rasa mijin aure tayi domin wallahi kamar ta karka raba ta da ya'yan uku wasu fa tun suna shekara goma sha biyu ake musu aure balle wannan da ba lallai takai 18 year ba , ƙasan kowa da irin al'adar su.'' asim yace '' Hakane nan da shekara uku ko?'' eh tace mai tana tashi jin wayar ta na ringing tace '' sai mun yi waya zan tafi.'' okay Allah ya kai mu ya faɗa yana kallon ta. AFIYAH tace '' na kirawo maka su?.'' barsu zama su shugo idan sun ga kin fito wani murmushin mugunta tayi tana jin farin ciki a cikin zuciyar ta , tace '' to .'' tana fita daga cikin office ɗin nasa. da sauri suhaila ta tashi afiyaah wani kallo tayi musu tana dariya musamman da ta tuna irin lalata rayuwar mardiyya da za tayi, domin ba mamaki wannan bakin cikin ya hanata sakat abin takaici ne da hawan jini ace da yarinyar ka kayi aure shekara uku zuwa biyu ace aure ya mutu. ko kallon inda take ba su yi ba suka shiga bakin su dauke da sallama zama suka yi be ɗago ya kalle su ba hankalin sa yana kan laptop ɗin sa. SUHAILA ce tayi karfin halin cewa daman mun zo ne akan maganar nan idan zaka biya mata kudin makaranta dana jarabawar nan da ta rasa ta amince ita yar scholarship ce to gwamnatin hajar su da ta dauki nauyin su tace , kowa ya biya na gaba daman na farko zata biya musu. duk wannan bayanin da take be ɗago ba sai da ta kai ƙarshen zancen ta yace '' oh ba damuwa amma ita tayi bayani da kan'ta bata da baki ne?.'' da sauri ta kalle sa da sauri ta kawar da idon ta kirjinta na dukan uku uku, bata fiye son yin magana ba, ba zata iya wannan bayanin ba ba lallai ya gane hausar taba, domin dole wannan bayanin ta haɗa mai da fulatanci bata iya hausa sosai ba su a cikin fulanin ma a zaune suke a daji, basu da wata wayewar rayuwa wannan karatun ma sai da aka kai ruwa rana sannan baffa ya yarda cewa yayi ita ce ƙarama ba zata rusa mai tsarin gidan sa ba kaf yan uwan ta basu kai kamar ta ba an musu aure tunowa tayi da Maude gaban ta ne ya faɗi domin akwai alkawarin aure a tsakanin su dole asim yayu shaɗi indan har ya amince da auren ta cikin rawar murya tace '' zaka iya shaɗi?.'' bakin ta ne ya subbuce bata san lokacin da , ta fadi haka ba domin ba ƙaramin shiga cikin tashin hankali tayi ba , domin ba lallai maude ya yarda ba dole yace ayi shadi tun da mane ma biyu sun haɗu me juriya ya samu nasarar aurar ta. Amina alhasan Muhammad opay 1k 8141785374 ku turo da shedar biya ta wannan number 8141785374. *JAMI'A* Inaa hajjiyo da yan kwaliya to ku garzayo OUMYASMEEN COLLECTION domin samun kaya na kerewa Sa'a ki zama fitila wajen oga ba abin da bana siyarwa cikin fara shi me sauki https://chat.whatsapp.com/DSd6g96hO2F41IG6k43rEl?mode=ems_copy_t *Episode 6* MARDIYYAH da take jin faduwar gaba, saboda bata san me zai fito a bakin sa ba , tana jin tsoran amsar da zai faɗa mata bakin ta har rawa yake ganin yayi mata shiru ya tsare ta da idanuwansa, alamar yana neman ƙarin bayani. MARDIYYAH tace '' akwai wanda yake neman aure na ko fii moƴƴi ɗum school am maa waɗiima iyayena suka dakatar dashi sai na gama, idan mutum biyu suna neman auren mace ɗaya dole sai anyi shaɗi, so wonaa, no ndiyam.'' mardiyya ta ƙarashe maganar ta , kan'ta yana ƙasa tana wasa da yan yatsun ta. ASIM yace '' okay Ina ne garin ku..?.'' MARDIYYAH tace '' Timbuktu a dajin GOURMA rugar harɗ'o Bello.'' da sauri ya kalle yace '' Mali..sahel tun daga nan kike zuwa birmu ?.'' A' sanyaye tace '' eh daga nan nake zuwa.'' kai ya jinjina yace '' za ki iya rubuta min sunan rigar ku da number wani wanda iyayena zasu nema?.'' mardiyya tace '' eh zan iya .'' biro ya bata rubutawa ta fara, wayar sa ya ɗauka ya kirawo mukhtar yace '' kana ina?.'' daga can ɓangaren mukhtar yace '' ina bakin kofar office ɗin ka.'' tsaki yayi ya kashe wayar ban da iskanci, me makon ya shigo sai ya tsaya ya ɗaga mai waya tun da yaga kiran sa ai yasan nemansa yake yi. mukhtar dariya yayi ya shigo da sauri suka ɗago suka haɗa baki gurin gaishe shi amsawa yayi yana zama tare da tambayar su ya jarabawa alhamdulillah suka ce mai. kallon asim yayi yace '' kai yanzun nan wannan matar ta huce ta office ɗina wai uban me ya ke kawo ta makarantar'nan?.'' Asim da ya lura neman magana mukhtar yake sai yayi mai banza ya nuna be ma san me yake faɗa ba gama printing paper yayi har guda biyu yace '' ungo idar har kun yarda da sharuddan da yake cikin takardar nan na'amin ce zaku saka hannu na saka mukhtar ya saka hannu ku riƙe copy ɗaya na riƙe ɗaya sannan zata karanta a fili kowa yaji.'' jikin ta a sanyaye mardiyya ta , tashi ta amsa ta ajiye mai paper da ya bata. zama tayi kusa da suhaila tana ƙurawa rubutun ido, ganin rubutun bibbiyu take takasa fahimtar komai dakyar ta iya saita kan'ta, cikin sanyin murya tamkar ana busa sarewa saboda daɗin Muryar tata, tace '' contract marriage rubutu ne ɓaro ɓaro a sama manya sai kasa ta fara da cewa. ni ASIM EL'BASHIR MANSUR TURAI zan biya wa MARDIYYAH HARUNA JAURO kuɗin makaranta har na tsawon shekaru uku za muyi contract marriage na shekara uku idan shekara uku tayi zan sake ta , taje ta auri wanda taga ya dace da rayuwar ta , zata kula da mahaifiyata duk wani aiki da masu aikin gidan mu suke yi za tayi wannan shine aikin ta bayan shi babu wani abu da zata ƙara yi min , idan Shekara ukun bata cika ba ta ce baza ta iya ba na sake ta zata biya ni kudin dana kashe mata .'' wani mugun yawu ta haɗiye , aiki kuma wanne irin aiki ne ta zata kawai aure ne za suyi shi zata zauna a matsayin matar sa kawai kenan a matsayin yar aiki ya ɗauke ta , tayi mai aiki ya biya mata kudin makaranta, kallon suhaila tayi, SUHAILA da jikin ta yayi sanyi amma bakomai addu'a ba abin da ta bari tace '' saka hannu na saka.'' tamkar wata ɗoluwa ko sokuwa haka ta saka hannu zuciyar na yi mata wani irin bugu hannun ta na rawa , miƙa wa SUHAILA tayi, itama ta saka hannu mukhtar ya saka shima ya saka sannan yace '' kuje na sallame ku , ku riƙe wannan copy ɗin zan riƙe wannan a hannu na.'' to tace , tana ninke takardar fita suka yi jikin su a sanyaye da sauri mukhtar ya kulle kofar ya dawo ya zauna yace '' asim wannan wanne irin cin mutunci ne yar aiki ka ɗauke ta kenan ma?.''' ASIM cikin halin ko in kula yace '' to bayan wannan wanne amfani za tayi min aikin ma dana bata share share ne da goge goge karta sake ƙafafuwan ta su shiga hanyar kitchen din mu.'' Hmmmm wallahi akwai ranar da zan maimaita maka wannan maganar asim ba'a raina mace ko wacce da irin baiwar da Allah ya bata karka zo kana neman hanyar da zata amince dakai nace maka nima ban san hanyar ba. Cewar mukhtar. ASIM yace '' wa Ni...? Allah ya kiyaye gaskiya mukhtar ka cuce ni me zanyi da wannan kwailar wallahi har ka saka zuciya'ta tana tashi ni na haɗa gado da wannan nace na haɗa gado da wa ?.'' mukhtar yace '' kayi nisa baka jin kira wallahi, amma lokaci yana nan zuwa inshallahu da za kayi amai ka lashe zancen ka , bana fatan ku rabu da mardiyya fata nake naga har jikokin ku.'' ASIM dogon tsaki yaja ya ci gaba da aikin da yake gaban sa. wannan kenan aginɗin wata bishiya ta zauna domin tafiya ma , ta ƙasa yin ta , zama tayi tana sauke numfashi tace '' SUHAILA gaskiya bazan iya ba , cimin mutunci zai ɗinga yi yana hulakanta ni, bani da wani gata yan uwana ba anan suke ba shekara uku fa ba kwana uku bace ba..?.'' dan Allah mardiyya ki tashi ki dena wannan zance wallahi ba ayi namijin da zai hulakan ki ba inhar ina raina, ki kyale sa ba sai kin shiga sabgar sa ba , sannan zai hulakan'ta ki ba Cewar suhailah. tashi tayi tana dafa ta da sauri mardiyya ta rufe idon ta sakamakon motar afiyaah da ta , tawo a guje ta fallatsa musu ruwan , da ya kwanta a gurin da suke a hankali ta buɗe idon ta kayan ta duk ya ɓaci haka kayan suhaila afiyaah ganin basu gane wace tayi musu wannan aikin ba dawowa tayi ta tsaya tare da zuge bakin glass ɗin motar ta , tace '' talakawan banza ku da kusan a kafa kuke yawo, kuka fara faɗa dani..?'' nonsense.'' Mardiyya da zuciyar ta , ta kawo har wuya bata san lokacin da ta dauki dutsai ba ta buga a glass din motar afiyaah wucewa yayi ya sauka akan goshin ta anan danan jini ya balle glsss din gaban motar ta ya gashe domin dutsai da ta dauko ba ƙarami bane. Ihuuuuuuuuuu afiyaah ta saki tare da rufe bakin ta domin tuni bakin ta ya kumbura , har ta leɓen ta sai da ya fashe. da sauri mardiyya ta fita a guje haka ma suhaila sai dai kafin suyi wani yunkuri security sun riƙe su, Abdulwahab da yake kusa da gurin da sauri ya ƙara so yana cewa maza ku kai su gurin police. da yake akwai police station a cikin makarantar. mardiyya da ranta ya ɓaci ta ture hannun mutumin da ya riƙe ta , tace '' cika ni da kaina zan kai kana?.'' cikin tsawa abdulrazak yace '' wato ke ce mara kunyar ko to za kici ubanki yau za mu nuna miki shegen birni yafi na ƙauye.'' AFIYAH fitowa tayi dakyar da sauri Abdulwahab ya

Chapter 4 of 10