Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
tsohuwar karya yanda ta saba. Ta ci sa'a ta samu ƙofa a buɗe dan haka ta tura ta shiga tana yamutsa fuska dalilin warin hayaƙi mara daɗi da a ko da yaushe gurin yake yi. Tun daga corridorn farko take jiyo muryar Inno kamar speaker coci, cikin yare, da alama waya take tana ta sababi. Sai taja ta tsaya tana saurarenta. Ita ta rainesu, a gidan ta tashi taga tsohuwar, ba ita ba hatta Aliyu ya ce a gidan yayi wayo ya gansu, tun kuma tashinta har yau harshen Innon yana nan a yanda ta san shi, bata taɓa iya yin cikakkiyar jimla da hausa, zama da ita a shekarun ƙuruciya ya saka ta naƙalci harshen tamkar yaren mahaifiyarta. Amma bata san dalilin da ya saka take ɓoyewa ba, ba su ba, hatta Mami bata san tana jin yaren mutanen gidan ba, bata cika magana ba, hausar ma ba wani yin ta takeyi ba balle wata rana ta yi suɓul da baka har su fahimta, ko dan yaren ya kasance makamin sharrin da ake ƙulla boma-boman da suke dab da tayar da duniya? Ko dan taƙi jinin masu yaren sama da komai a duniyarta? Koma menene dai, ba zata taɓa yara shi akan harshenta ba, zata cigaba da saurara, tana kuma wargaza duk wani shiri da hannunta ya samu damar kaiwa kai. Tana jiyo ta tana cewa "Ni dai babu ruwana. Ki kirata da kanki ki gaya mata, gani takeyi ta samu duniya, matsalolinta sun kau. Giji ya gaya mata, muddin Aicha tana raye, ba zata taɓa bacci da ido biyu a kulle ba. Ki duba, Mussafa baya iya ɗaga ido ya dubeta, balle yayi mata musu, amma yau har yana iƙirarin ko za'a kori yayanta daga makaranta babu abinda ya shafe shi. Babu ruwana, idan abu ya lalace zan haure ne na barta a nan." Tayi shiru alamar tana sauraren wacce suke magana, kafin taja numfashi ta ce "Wannan baƙar yarinyar ce, saboda ita ne, sun yi faɗa da Gambo da Hassana, sai da na ce mata ayi.... " Maganar ta katse dalilin hannun Imaan daya goce ta ture mopper dake ajiye a corridor ɗin, ƙarar ta saka Inno zabura, ta kashe wayar kafin ta taho da sauri tana tambayar wanene a gurin. "Wane ɗan abu taka kazan uba ne yake mini laɓe?" Inno ta sake faɗa tana nufo Imaan. Imaan, wacce a farko ta yi stiff, ta ɗaga ƙafa a hankali da niyyar fita kafin ta isketa, sai kuma ta tsaya, wata zuciya ta raya mata "And so what? Me zata mini? Let's see." Sai ta gyara tsayuwarta, ta tamke fuska tana kallon Innon da ta fito daga falon tana zare ido kamar za ta cinye ta. "Dama raina ya raya mini kece. Wato laɓe kike mini ko, Mairam? Wane shege ya baki izinin shigo mini ɗaki eye?" Ta yi maganar cikin hargagi, kamar za ta kai mata duka. Imaan ta taɓe baki, tana sake gyara tsayuwarta ta ce "Masu ɗaki manya. Ke da kike zaman cin arziƙin kin ce ɗakinki, balle ni a gidan ubana ya za'ayi ki tuhumeni dan na shiga wani guri? This is my dad's house you crazy old woman, ina da damar shiga duk inda naga dama." Kallonta Inno ta ringayi kamar wacce taga wani abin mamaki, zuciyarta na tafasa. Ta san wannan baƙar yarinyar hatsabibiyace, tamkar mai makarai akanta. Duk wani shirin da za su yi akanta baya tasiri, yar ƙarama da ita amma nema takeyi ta zame musu ciwon ido. Ganin da Imaan ta yi Innon ta kasa ce mata komai, sai ta saki murmushi, saboda neman magana raɓeta tayi ta shige cikin falon ta samu kujera ta zauna tana ƙarewa falon daya sha kayan alatu kallo, kamar falon wata uwar gomna, sai dai tarkacen ƙyale-ƙyalen har sunyi yawa kwatankwacin can cikin gidan. A fili ta furta "Rich but no taste." "Idan kika sake mini engilishi, sai kin ci uwarki" Inno data biyo bayanta ta faɗa, sai ta kwashe da dariya tana kallonta. Zama itama tayi ta janyo wayarta ta sake kiran matar da suke magana ɗazu, Imaan tayi bakam tana sauraronta harta kammala kafin ta juyo kanta ta lailayo ashar cikin yare ta watsa mata. "Idan ba tsoro ba, mutum ya yi magana da yaren da duk gidan nan za su fahimta," Imaan ta ce, tana kallonta kai tsaye. "Na ce uwarki Aicha na cinye da kika zuba mini ido kina kallona ko kuwa?" Innon ta faɗa, Imaan ta watsa hannu biyu alamar 'oho' ta ce "Kurwar Mamina tafi ƙarfinki, ko kin ci sai kinyi amanta." Daga haka ta miƙe dan dama ba niyyar zama ta zo yi ba, tana murɗa ƙofa aka turo daga waje da ƙarfi, suka kusa yin karo da Shahida, sai tayi saurin ja baya tana kallonta. Tsaki Shahidan tayi haɗi da tofawa Imaan yawu a fuska tana cewa "Disgusting". Ba ta yi niyyar kulata ba, ba wai ta yafe abinda suka mata bane amma ta bari ba yanzu ba, sai dai abinda tayi mata yanzu ya matuƙar tunzura zuciyarta ta yanda ta kasa controlling fushinta. Fizgo Shaidan tayi ta maido ta baya, kafin ta gama dai-daita akan ƙafafunta ta watsa mata mari sannan ta haɗe kanta da ƙofar tana cewa "Ni sa'arki ce? Kin cire mini hijab a school sannan yanzu ki yi mini tsaki har ki tofa mini yawu? Zaki san baki da kunya, sai na koya miki tarbiyya da ba'a samu lokacin baki ba." Ta rufeta da duka tamkar uwa da yarta. Da ace iya tsakin ta mata zata iya sharewa, amma yawu fa ta tofa mata, har ta kirata abin ƙyama, ai ko su Hasna bata zaton zata yafe idan suka tofa mata yawu balle Shahida. Kware baki Shahidan tayi ta shiga kururuwar neman taimako, Inno na tsaye mamaki ya daskarar da ita a guri gida, bata zaci tsaurin idon yar Aisha har ya kai ta kama Shahida a gabanta ta jibga ba. Daga tsakar gida, Hajiya Alawiyyah wacce ta rako baƙuwar da ta yi ta ringa jiyo kamar ihu daga ɓangaren Inno. Sallamar matar tayi ta nufi gurin da sauri, kafin ta isa ƙofar ta fahimci ihun ne dagaske kuma na Shahida. Cikin azama cike kuma da tsoron daya mamaye zuciyarta ta tura ƙofar da ƙarfi ta shiga. A sukwane ta sauke ajiyar zuciya, ba abinda ta tsammata bane, sai mamaki ya maye gurbin tsoro da firgicin data shiga dashi, ta buɗe ido tana kallon Imaan dake zaune kan ruwan cikin Shahida tana jibgarta tamkar mai casar gero. Baƙin ciki mai tsanani ya mamaye zuciyarta, a cikin yayan Aisha, idan akwai wanda ta tsana yabi bayan wannan baƙar yarinyar. Da hannu ɗaya ta fizgo Imaan, ta riƙeta, kafin ta watsa mata mari da ɗaya hannun. Yanda take ƙashi da rai haka hannunta yake tamkar rodi, Imaan ji tayi kamar da kaca ta mareta, kafin ta saketa ta fara dukanta ta hannu da ƙafa. Tamkar abin banza haka ta ringa gare-gare da Imaan ɗin, tun daga falon Inno har tsakiyar compound ɗin gidan. Tuni hijabin jikin Imaan ya fara canza kala, daga ruwan madara mai haske zuwa ruwan kasa da sirkin maroon dalilin jinin da yake zuba daga hancinta. Duka ta yi mata bana wasa ba, bata ko damu da yanda ta daɗe da daina motsi ba, umarnin zuciyarta kawai take bi, so take ta rage wani kaso na haushin yarinyar da take ji, Hasna da Inno na gefe suna ƙara zugata, ma'aikata mata da maza duka sun fito sai dai an rasa wanda zai yi ƙarfin hali shiga tsakani ya ceci Imaan ɗin, kaɗan ne daga ciki suke bata haƙuri daga gefe, suma muryoyi a ƙasa tamkar masu tsoron ta san su ne su ka yi magana. Mami na tsaye a gefe, zuciyarta na dokawa tareda duk bugun da Hajiya Alawiyyah take yiwa Imaan ɗin. Tana tsaka da aiki Lawisa ta kirata, tana kallo duka wanda suke tayata aiki suka fita tun farkon hayaniyar, ta yi zaton Inno ce da wani daga cikin ma'aikatan gidan tunda kusan kullum bata gajiya sai ta samu wanda zata liƙawa laifi an ci masa mutunci. Sai da Lawisar ta ce mata Imaan ce, da farko kasa tashi ta yi daga inda take, tunaninta me zai fito da Imaan yanzu? Meye ma zai haɗa ta da Hajiya Alawiyyah? Data tuna zancen rigimar da ta yi da yaran gidan ne yasa ta tashi da sauri ta tafi, dama tasan za'ayi haka, amma bata yi tunanin Alawiyyar zata ɗauki mataki ne ta hanyar cutar da Imaan a zahiri ba. Da karsashin zuwa ta ƙwaci yarta ta fita, amma, tana zuwa gurin duk wani ƙwarin guiwar data fita dashi ya gushe, tsoro da shakka suka maye gurbinsu. Tana tsaye tana kallon yanda take dukanta dukda tana kwance guri ɗaya alamar ƙarfin da take ƙoƙarin kare kanta daga dukan ya ƙare, akan idonta ta bugata da flower vase, take kuma jini ya fara naso a jikin hijabinta har zuwa kan fuskarta alamar kanta ya fashe, sai ta rintse ido, ta toshe bakinta da hannu biyu kafin ta bar gurin cikin sassarfa tana jin yanda numfashinta yake barazanar barin jikinta. Hajiya Alawiyyah kuwa, sai da ta gaji da dukan Imaan ɗin dan kanta kafin ta dakata tana haki haɗi da zagin Imaan ɗin da sam ta daɗe da yin balaguro daga duniyar da suke ciki, horn ɗin da aka danna da ƙarfi kamar za'a tashi gidan ya saka hankalinsu ya kona can. Lawwali ya tafi ya buɗe da sauri fuska shaɓe-shaɓe da hawaye kamar ƙaramin yaro. Tun da aka fara rigimar ya tafi ya kira Abbo, shi kaɗai ne zai iya dakatar da Alawiyyar sai dai ya tarar da yayi bacci, ya sani kuma maganinsa na hawan jini ya sha tunda gasu nan a gefensa, da wahala ya tashi dan haka ya koma ya shiga sahun yan kallo da ban baki daga gefe yana share hawaye. Hamdala ya yi lokacin daya ji horn ɗin maigidan dan haka ya tafi da gudu ya buɗe masa. ALH. ARABI Tun da motarsa ta danno kai cikin compound ɗin, idanuwansa suka sauka akan dandazon mutane kamar masu kallon wani show. Yana jin muryar Alawiyyah tana maimaita sunan Imaan cikin kalmomin daya fahimta da zagi ne a cikin yarensu. Sai da ya cire glasses ɗin idonsa bayan daya fito daga cikin motar kafin ganinsa ya kai kan Imaan dake kwance cikin jini, dokawar da zuciyarsa ta yi ne ya alamta masa ita ce tunda bai ga fuska ba, yana jin Alawiyyah na cigaba da sababi tana faɗin Aisha ta zo ta ɗauke yarinyarta, kafin ta hallakata. Cike da fushin da bai taɓa jin makamancinsa ba, ya fizgota ganin ta sake nufar inda yarinyar take kwance, ya hankaɗa ta baya, a bazata komai ya faru dan haka sai tsintar kanta ta yi yashe a ƙasa tana zare idanu. Duk irin wutar tsanar yarinyar da yake ji a zuciyarsa, haka ya sunkuya ya ɗora yatsunsa biyu a saitin hancinta da yake ta zubar da jini har sannan, shiru babu ko ɗumin numfashi, zuciyarsa ta buga da ƙarfi, tamkar za ta faso ƙirjinsa ta fito. Da sauri ya ɗago ta jikinsa, yana jijjigata, yana maimaita sunanta da muryar da ta karye, "Imaan… Imaan please, wake up!" Amma shiru. Duk yanda yake jin zafi mara misali yana ratsa tsokar jikinsa, haka ya rintse idonsa, ya ɗauketa, zuciyarsa na rawa kamar mazari. Dama Habu bai kashe mota ba, ciki ya shiga da ita, ya rungumeta tsam a jikinsa yana cewa "Drive Habu, let's go" Habu ya taka mota da gudu suka fice daga gidan. Tamkar an danna pause button haka wajen ya ɗauki shiru. Sai bayan sun fita kowa ya rakasu da kallo har sai da motar ta ɓace kafin aka fara watsewa, kowa ya koma bakin aikinsa, kowannensu cike da tunanin da ba za su iya furtawa ba. --------------------------------- Kasa komawa kitchen ɗin Mami ta yi. A karo na farko tun da abubuwa suka canza a gidan, tayi gaban kanta bata jira umarnin Hajiya Alawiyya ba ta wuce ɗaki. A kan kujera ta zauna, ta fashe da kuka. Ta yaya za'ayi ace tana kallo yarta na neman halaka amma ta kasa taɓuka komai ta taimaketa? Wane irin abu Alawiyyah ta aikata mata haka da take shakkar ta sama da komai a duniyarta? Wannan wace irin jarabawa ce? "Allah, ka sassautamun wannan jarabawa… Allah, ka yantani daga wannan ƙangin bautar." Ta faɗa a fili cikin hawaye. Zargin kanta ta fara yi, mai ya sa lokacin da suka bata zaɓi ta bar wa Alawiyya mijinta ta tafi, ta yi rayuwarta bata karɓa ba? A lokacin gani take idan ta fita, ina zata je? Wa take dashi a duniyar nan sama da Arabi? Wace irin rayuwa yaranta zasu fuskanta? A ƙarshe, ta zabi ta zauna, ta sadaukar da rayuwarta saboda yaranta. Amma yau, a karon farko taji nadamar hakan. Kasa zama ta yi, sai ta fita, a lokacin ne kuma maigidan ya dawo. A kan idonta ya ɗauki Imaan ɗin ya saka a mota, sai ta rasa me ya kamata taji, farin ciki za ta yi ko kuwa baƙin ciki? Idan ta yi murna, Mustafa ya nuna kulawarsa akan Imaan, abinda ta jima bata gani ba ko a cikin ƙwayar idonsa, tsoron abinda hakan zai haifar sai ya disashe murnar har ta ji kamar ta bishi da gudu ya bata yarta. Ba cetonta ya yi ba, sake jefa rayuwarta ya yi cikin garari domin ba zasu zubo ido, shirinsu na shekaru ya rushe arana ɗaya a kan idonsu ba. Wannan tsoron ya saka ta nufi ɗakin Abbo da sauri, ta ringa bugawa har sai da ya farka, cikin magagin baccin da yake kansa ya buɗe mata ƙofar. Ganinta a birkice ya sa shi tambayar mai ya faru, dukda ya sani, tatsuniyar gizo, bata wuce ta ƙoƙi. Daƙyar ta tsaida kukanta ta labarta masa komai a taƙaice, Mamaki ya kamashi. Abbansu? Shi da kansa ya tafi kai Imaan asibiti? Sai ya girgiza kai, ya ce a fili "Subhanallah… Allah kenan, mai tsara komai a lokacin da yaso. Alhamdulillahi. Bari na ɗauko wayata mu kira shi, ki daina kuka." Ya koma ciki. Ya dawo da wayarsa, ya miƙa mata. Hannunta na rawa sosai ta amsa, ta kira lambar har sau uku, amma ba a ɗauka ba. Sai ta dubeshi cikin hawaye, ta ce "Bai ɗauka ba. Ina tsoron wani abu ya samu yarinyata Abbo." "Ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu babu komai. Bari in je wajen Lawwali, ta yuwu ya san asibitin da suka je. Idan da hali, sai mu bi bayansu." Ya wuce yana takawa daƙyar zuwa bakin get. Bai jima ba ya dawo, har sannan tana zaune tana kuka a gurin. Cikin tausayawa ya kalleta ya ce "Kiyi haƙuri Aishatu. Lawwali ya gaya mini komai daya faru. Don Allah kiyi haƙuri, ki cigaba da addu’a, wannan jarabawar da kika jure, in sha Allahu, Allah ba zai bar ki haka ba." Hawaye ta cigaba da sharewa, ya ce "Lawalli ya kira Habu, ya ce suna asibiti kuma an bata taimakon gaggawa. Babu wata damuwa, ki kwatar da hankalinki, zuwa da safe sai kije ki ganta kinji." Haka ya ringa rarrashinta harta haƙura dan da tace a lokacin zata bi bayansu. "Idan kika fita shi kuma ƙaramin Alhaji da wa zaki barshi? Ki yi haƙuri da yanzu da safiyar duka ɗaya ne a gurin Allah, fatanmu Allah ya bata lafiya." Ya faɗa bayan daya rakata ƙofar ɗaki. END OF FREE PAGES WASU MATAN is 1k on Telegram pay in to 7061838488 opay Maryam Farouk Ko ku karanta a Arewabooks @Maryamfarouk01 Contact me on 07061838488 Nagode An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7