Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
addu’a kawai." Ya faɗa ba tareda ya haɗa ido da ita ba, sai ta saki murmushi, murmushin da ba zata ce ga dalilin yin sa ba, kafin ta ja da baya tana kallonsa ta ce "Why today, in this trip, and in this particular car? Barr." ********************** Daga makaranta duk da Mami ta ce su wuce gida, Imaan ta ƙi yin hakan saboda abinda ya faru da safe. Ba wai tana tsoron su bane, a'a, ta sani ƙarshen abinda za su yi su mata taron dangi su daketa, wannan ba sabon abu bane, abinda bata so su aibata mahaifiyarsu, ba zata yi shiru ba idan kuma ta tanka ƙarshe komai akan Mamin zai ƙare, shiyasa ta zaɓi ta rabu dasu for now, dan ba wai ta haƙura gaba ɗaya bane. Suna tafiya tana gyara zaman hijabinta da wuyansa ya buɗe. A ranta kuwa, ita kaɗai tasan irin dukan mutuwar da zata yi wa Shahida duk ranar da ta samu sa'ar kamata. A zuciyarta, ta gama ƙudura cewa ba zata hawa motar gidan Arabi ba, idan bata da kuɗi gara ta taka da ƙafa, ko kuma ta haƙura da makaranta gaba ɗaya tunda dama ta daɗe tana yiwa Mami nacin ta cire su, ta mayar dasu makarantar gomnati ko zasu huta da gorin da a kullum ake yi musu amma Mamin taƙi. Suna dab da shiga tashar, kamar daga sama, Auwalu ya faɗo gabansu. "Ke, yane? Ba ki ji ana miki magana tun ɗazu bane?" Ya faɗa yana buɗa hannu cikin halin iskanci na yan tasha. Auwalu irin masu taro passenger ne su saka su a mota, tun kama aikin Mami a tashar yake takurawa rayuwarta. Ta tsane shi, ko sau ɗaya bata taɓa buɗe baki ta yi masa magana ba amma hakan bai saka ya rabu da ita ba duk idan ya samu dama sai ya uzzura mata shiyasa wasu lokutan take ji kamar ta haƙura da bin Mamin saboda shi. "Da Allah ka bani hanya na wuce" ta faɗa, ganin ya tareta kamar zai faɗo jikinta. Bai motsa ba, sai ta ja hannun Ahmad da niyyar su zagaye shi, hannunta ya ruƙo ya fizgota baya yana cewa "Tsaya mana baby, nifa ba wani abu bane, sonki nake yi. Kije ki aje ƙaninki ki dawo minti goma ya isa magana zan gaya miki...." Bata jira ya ƙarasa ba ta ɗauke shi da mari, marin da sai data aikata nadamar yin hakan ta saukar mata, musamman yanda ya zaro idanuwansa da shaye-shaye ya rinar dasu ya buɗe baki cike da maɗaukakin mamaki yana kallonta. "Ni kika mara?" Ya tambaya yana nuna kansa kamar bai yarda abin ya faru da gaske ba. "Zan maka fiye da haka, duk ranar da ka sake ɗora ƙazamin hannunka a jikina, idan kuma kana da shakku, bismillah." Ta bashi amsa a dake, tamkar ba zuciyarta ce take tsallen dakan lugude na tsoron abinda marin zai janyo mata ba. Wani abokinsa ya yi kanta yana rangaji alamar a caji yake ya ce Ke ƙaramar yanyan, har kin isa ki mari oga a cikin tashar nan? Uban wa ya tsaya miki?" Ta ja baya tana galla masa harara ganin wani ɗan union ya shiga tsakani yana yiwa su Auwalun faɗa "An ce muku kowacce yarinya a nan gurin shashasha ce da zaku latsa? Da Allah ku wuce daga nan, idan ba haka ba yanzu zan sanarwa da Ya Alhaj (yana nufin shugabansu). Kallon da Auwalun yayi mata sai da gabanta ya faɗi, ya wuce, ko da bai furta komai ba ta sani na ɗaukar alwashi ne. "Addah, me yasa zaki mara shi? Mami ta ce ki dena kulasu, ko sun tare mu, mu gudu kawai. Bakya tsoro ya miki irin abinda yayi wa Balaraba mai kantun nan?" Ahmad ya faɗa kamar zai yi kuka. Ita ma sai idanunta sun cika da ƙwalla, ta ce "In sha Allah hakan ba zai faru da ni ba, kuma kar ka gaya wa Mami, ranta zai ɓaci kaji?" "Kuɗin da kika bamu ne ya faɗi, shi ne nazo ki bamu wani." Imaan ta faɗa, voice ɗinta flat ba tare da ta bari sun haɗa ido ba. Mami ta kalleta, kamar za ta ce wani abu sai kuma ta fasa. Ta san da wahala su wuce gidan kai tsaye ba tareda sun biyota ba dama, ta zuge lalitar da ke ɗaure a kugunta, ta zaro dubu biyu ta miƙa mata tana cewa "Ki siya omo da sabulun wanka, naga ya kusa ƙarewa, sai ki yi cefanen miya, tuwo za ki yi da kuma na abinda Ahmad zai tafi dashi Tahfiz gobe." Imaan ta karɓi kuɗin tana juya su, hararta Mami ta yi, sai ta saki murmushi kawai. Bata son aike, ita Mami sai ta ce wai tana ɗaukar kanta ta girma, ko dan bata gaya mata yanda samari suke harassing nata ne? Shine dalilin da ya saka bata so a aiketa. Mami ta juya tana cewa su yi sauri su tafi saboda hanyar akwai masallacin Juma'a. Imaan ta marairaice mata, ta ce "To Mami, ki rakamu mu hau Napep mana." Mami ta sake kallonta, sai a lokacin ta lura da hijabinta da ya farke. Ta tsureta da ido "Shahida da Hasna ne, kuma wallahi sai na rama" Imaan ɗin ta faɗa, ƙwafa Mami ta ce "Wato duk abinda zan faɗa miki akan yaran nan ba zakiji ba ko Imaan? Shikenan." Ta wuce ta barsu. Ba ta daɗe ba ta dawo, suka wuce bakin titin. Sai da ta samar musu adaidaita suka wuce kafin ta koma gurin aikinta. Suna tsaye tana jira mai Adaidaita ya bata canji su Hasna suka wuce su a mota, da alama gidan bikin da suka je jiya za su koma. Wannan ya bata damar sakewa ta yi wankinta a laundry, bayan sun yi sallar la'asar ta tafi cikin garden ɗin gidan ta zauna tana kallon irin tsuntsayen da asali nata ne tun tana yarinya Abbinsu ya siya mata, kafin su fi ƙarfin ta a ƙwace, tsakaninta da su sai idan ta samu irin wannan damar mutanen gidan basa nan sannan ta zagaya ta gansu. A gurin ta zauna har magriba tana watsa musu abinci, wasa da tsuntsayen ya sanyata farin cikin data daɗe bata yi irinsa ba, an ƙara breeds kala-kala masu kyawun jiki da kuka mai daɗin sauraro. Nan ta shantake sai kiran sallar magriba taji, kamar kada ta tafi haka ta wuce tana waigensu, ta tasa ƙeyar Ahmad da shima ya samu sarari ya shige gurin kayan wasan Al'amin suka koma ɗaki. Page 9 Tayi mamakin rashin dawowar Mami har sannan, sai da tayi sallar magriba kafin ta ɗora musu tuwo kamar yanda Mamin ta gaya mata ta yi. Sai da gari yayi duhu Mamin ta dawo da ledoji manya. Da alamu kasuwa ta biya, abinda ya tsayar da ita kenan. Lawalli mai gadi ne ya ta ya ta shigo da kayan, bata ko zauna ba, jakarta kaɗai ta ajiye ta wuce cikin gidan tana cewa Imaan ta ware komai ta ajiye a gurin daya kamata. Bayan ta kwashe tuwon da ta tuƙa musu na semo, tayi sallar isha'i kafin ta buɗe kayan da Mami ta siyo. Tun daga kayan abinci ƙaramin buhun shinkafa, taliya, macaroni, da sauran essentials, sai kayan ƙwalama, biscuits, drinks, cosmetics, turaruka, har da undies da ta ɗaga ta gane nata ne da pad. Harda wasu bubu gown na material kala uku ta siya mata. Babu abinda ya burgeta daga cikin kayan, knowing exactly daga inda kuɗin suka fito. Da safe Aliyu ya gaya mata kayan da aka kawowa Ahmad da kuɗin da suke ciki, ita ta sake zugashi akan kada ya karɓa, gara ya haƙura da dai yayi amfani da kuɗin Arabi. Ta matsar da kayan abincin inda aka saba ajiye su, sauran kuma ta maida cikin ledoji ta aje su a gefe. Da Ahmad zai ɗauki lemo ma, hanashi ta yi, ta zaro ɗari biyu daga cikin canjin ɗazu ta ce ya tafi kiosk ɗin Bashir, a ƙofar gidan da yake jikin nasu ya siya. Da wuri Mami ta gama girkinta ta dawo, abincin maigida kawai tayi yau. Imaan na wanka sanda ta shigo, Ahmad kuma yana homework. Mami ta zauna, ta duba kayan da Imaan ta bari. Sake fitar dasu tayi ta ware nata ta shige ɗaki dasu. "Ni fa ina da komai Mami, wancan basu ƙare ba" Imaan ta faɗa sanda Mamin ta ce ta kwashe kayan, cikin ko in kula Mami ta ce "Sai ki zuba su a bola." Ta cigaba da sabar gabanta. Yanda ta tsume ya saka Imaan tattare kayan tana ƙunƙuni, Mami tana da sauƙin hali, amma idan ta murɗe musu bata sakkowa da sauƙi, shiyasa data kalleta ta ce ta faɗa mata abinda take faɗa cikin ƙunƙunin sai kawai ta shige ɗaki, kafin ta karɓi bulala da carbi. Sai da Mamin ta shiga kwanciya Imaan da batayi bacci ba ta ɗakko takardar suspension ɗin da aka basu ta miƙa mata, bata ko bata damar kare kai ba ta rufeta da faɗa tamkar zata doketa, kacokam ta ɗora mata laifin abinda ya faru, wannan ya ƙara bata mata rai ta fashe da kuka har sai da kanta ya fara ciwo kafin ta yi shiru lokacin Mamin ma ta daɗe da yin bacci abinta. Kullum, wani abu yana haɗa su da su Shahida, ita take bawa laifi ko da kuwa ta san ita ce da gaskiya, ko a gabanta abin ya faru sai ta ce wai suyi haƙuri. Shikenan su haka zasu ƙare rayuwarsu cikin wulaƙanci da rashin yanci a gidan ubansu ba wai zaman agolanci ko cin arziƙi ba?? ------------------------------------- Pass twelve Napep ya sauke Aliyu a ƙofar gida. A ƙasa da awa biyu suka kammala duk wani abu da zasuyi a makarantar, akwai sauran kusan sati biyu kafin a fara karatu, ba wani suke dashi a garin ba, idan ma sun zauna zaman banza ne kawai dan haka Aliyu ya cewa Ibrahim su juyo Kano kawai. Motarsu ce ta lalace a hanya ba dan haka ba magriba zata iya musu a Kano. Ibrahim ya ringa mita ga abinsa gaggawar Aliyun ta janyo musu, da sun kwana washe gari su taho a nutse amma ya sakasu hawowa motar da dama shi tunda ya ganta sam hankalinsa bai kwanta da ita ba. Sun iso Kano lafiya dai gurin sha ɗaya da rabi, da zai bi Ibrahim ɗin ma da yayi tunanin ba lallai a buɗe masa gida ba, sai kuma ya canza shawara, yana ganin lokaci yayi daya kamata su ƙwaci yancinsu da hannunsu, zai ga ubanda zai hanashi shiga gidan tunda mata ma suna fita su kai sama da haka babu kuma mai rufe musu ƙofa. A gajiye ya shiga buga get. Lawwali ya leƙo, ganin shi ne ya buɗe masa yana masa sannu da zuwa. A gefen entrance na main house, ya hangi Hasna da Husna cikin ƙwalliya, suna ɗaukar hotuna tamkar after-party glam shot, ko tsoro basa ji. Suna haɗa ido da Husna, ya ƙara tamke fuska ya ɗauke kai. Har ya gota su, sai yaji ƙarar takalmi a bayansa obviously, biyo shi ta yi. Gabansa ta zagaya, tana kallonsa tamkar karen da yaga ɗanyen nama, cikin yauƙi da iyayi ta ce "Sannu da zuwa Yah Aliyu." Tana wani narke fuska, ta kai hannunta kan kafadarsa da niyyar zare jakar daya rataya tana sake cewa "Handsome, daga ina kake da daren nan?" Da ƙarfi ya make hannunta daga jikinsa yana jifanta da kallo tsana haɗi da ƙyama ya ce "Is your brain setting corrupted? Sau nawa zan gaya miki ni muharraminki ne. Google it, ko ki tambayi wannan raƙumar uwar taki idan ta san ma'anarsa ta gaya miki tunda naga alamar baki taɓa shiga ajin islamiyya ba." Bata daddara ba, ta sake kai hannu da niyyar riƙe nasa tana cewa "Duk saboda nace ina sonka ne kake min haka Aliy..." Mari ya ɗauketa dashi, sai da ta durƙusa, ta fashe da kuka dan ya shigeta sosai. Ya ɗaga yatsansa yana nuna kansa ya ce "Let this sink in your premature brain, wannan ya zama last warning da zan miki. Billah, idan kika sake yi min wannan haukar ko ki turo mini nonsense texts ɗin ki, sai na canza miki facial structure live and direct. Na fahimci generation ɗinku gaba ɗaya dabbobi ne in designer skins. And trust me, I know better ways to deal with your type." Ya ja tsaki mai ƙarfi, ya tureta daga gabansa inda take durƙushe tana kuka ya wuce da sauri kamar zai tashi sama. "I hate them, i hate seeing them in my life. If I had the power, i would pass the harshest judgment on them, one that matches the gravity of the crimes they have committed....." Aliyu. Husna ce tayi abin kunyar, amma Hasna ce taji mata takaici da baƙin ciki, yadda kasan ƙasa ta tsage ta shige ciki haka taji. Takaici yazo mata wuya ganin Husnan ta miƙe kamar zata bishi, sai ta fincikota baya tana cewa "Hankalinki ya kwanta ko? Dama idan baki yi abinda zaki zubar mana da mutunci ba, ke bakya jin daɗi. Ki kalla yanda mutane suka taru suna kallonki." Ta ƙarasa tana harar securities ɗin da suka zobo musu na mujiya da alama kuma duk abinda ya faru ya isa cikin kunnuwansu. Tsaki Husna tayi tana karaɗe jikinta, she was contemplating, ta bishi ɓangaren su ko ta tsaya nan ɗin ko zai sake fitowa? Ta jarabtu akansa, tun daga sanda Allah ya haɗa idonta da shi, tun ma bata fahimci abinda take ji tattare dashi ba take dakon wani nauyi a ƙirjinta da sai a yanzu ta fahimci menene. Ta ƙara kusan minti goma kafin ta wuce jiki a sanyeye dan tuni Hasna ta wuce ta barta a gurin. "Like, wanene Aliyu a cikin maza har kike wannan abin saboda shi, har yanzu kin kasa gane there can't be anything like love relationship between you two ba?" Hasna ta faɗa bayan data shiga ɗakinsu. Cike da borin kunya da haushin yanda Aliyu ya yi mata, ta juyo kanta tana cewa "Abeg leave me alone. Ai Mama tace ba yayan Dadynmu bane, shegu ne Aisha ta yi cikinsu a waje, that means I can totally marry him if I want." Sai Hasna ta rasa abinda zata ce mata, ta buɗe baki sau biyu tana rufewa kafin ta ce "Dagaske, dabbar ce ke… kamar yanda ya faɗa." Ta shige toilet zuciyarta na tafasa. "Yanzu duk waɗannan big boys ɗin da suke so ki, manyan yara, rich kids, sons of billionaires ki rasa wanda zaki ce kina so sai Aliyu? You're not even thinking straight, Husna. That guy is literally our step-brother, ubanmu ɗaya…" Hasna ta faɗa cikin maɗaukakin mamaki lokacin da Husnan ta ce mata she is having feeling for Aliyu Arabi. Cikin ko in kula Husnan ta mayar mata "Look, there are many reasons… Wai ma, what’s your own? Those so-called big boys you like, I just play with them to catch cruise because I already have dahir in the house. Shi ya min, and shi nake so, kawai na faɗa miki ne saboda no secrets between us, ka da ki gani a sama ki ce na munafunceki." Sai Hasna ta ringa kallonta kamar tana duban mai rashin lafiya ta ce "To Allah ya taimaka. Amma yanzu kinyi hauka ne da zaki ce kina son Aliyu, kina expecting Mama da Inno su yarda? Ke even his mom? You think zata bari ya aure ki, even if it’s possible legally?" Sai tayi tsaki ta ɓalle murfin motar da suke ciki, a lokacin sun dawo daga salon ne suke maganar "Wai what's your business sef? Did I say I'm looking for anybody's approval? As long as he agrees, fine. Kar uban kowa ma ya yarda. This is my life, stop monitoring me like I monitor you. Kuma wallahi, idan maganar nan ta fita wani ya ji, i swear you won’t like what i will do to you." * Aliyu kuwa, sanda ya shiga part ɗin su, ya tarar su Mami sun kwanta. Waya ya haɗa ya buɗe ƙofar, ya san dai zai sha faɗa a gurin Mami da safe, ta hanashi buɗe mata ƙofa in dai ba da key ba, amma ya za'ayi yanzu ya fara buga ƙofa ya tashe su? Wankan da bai samu yi da safe ba ya yi shi hankali kwance da ruwa mai zafi, ya ɗauki lokaci sosai yana gasa jikinsa. Ya fasa sababbin kayan tea ɗin daya gani yayi haɗin kauri ya sha kafin ya kwanta cike da mafarkin yanda rayuwarsu zata sauya da zarar burinsa na tuƙa jirgi ya cika. Se da asuba Mami ta ganshi. Ta yi masa faɗa me yasa ya yi tafiyar dare, ba ta yi zancen ƙofa ba, ta kuma yi masa addu'a da fatan fara karatun cikin nasara. Shi ya kama aikace aikace bayan su Imaan sun wuce tahfiz, ita kuma ta wuce cikin gidan dukda weekend ne basa tashi da wuri. Asabar da Lahadi bata zuwa gurin siyar da abinci, lamunin kwana biyar matar gidan ta bata ta fita ta nemawa kanta da yayanta abinda zasu ci tunda ta haramta musu su ci daga taskar wanda ubangiji ya ɗorawa alhakin kulawa da su. Tayi mamakin tarar da Hajiya Alawiyyah da mahaifiyarta Inno a kitchen ɗin, suna haɗa ido jikinta ya ɗauki rawa, zuciyarta ta shiga bugu cike da tsoro irin yanda ta saba a duk sanda suka gamu. Wani baƙin shayi suke dafawa, kasancewar a butar shayi wacce akayi da glass ne dan haka ana ganin abinda yake ciki. Gefe ta samu ta tsaya bayan data gaishe su, sanda shayin ya fara tafasa, warin abinda bata san ko menene ba ya bigi hancinta take zuciyarta ta harzuƙo, amai ya taso mata. Da dabara ta fice daga kitchen ɗin ta tsaya gurin wanke-wanke tana sauke numfashi bayan data gama amayar da ɗumamen tuwon data sakawa cikinta. Mamaki ta ringa yi da cikin su biyun babu wanda yayi ko gezau har ta juye a ɗaya daga tea flask ɗin maigidan, ta haɗa da ƙaramin cup da spoon akan tray Hajiya Alawiyyah ta shige dasu ciki ita kuma Innon ta fito ta ƙofar bayan. Wani murmushi ta sakarwa Aishan da sai da hantar cikinta ta kaɗa, a duniyarta bata taɓa gani ko jin labarin azzalumai marasa tsoron Allah kamar waɗannan mutane biyun ba. Ita kaɗai ta san abinda ta sani game da su, ba kuma zata iya furtawa wani ba ko da tayi niyyar yin hakan, bama zata iya ba. A kullum fatanta Allah ya tsare mata yaranta daga sharrinsu, shiyasa taƙi jinin duk wani abu da janyo rigima ko sa'insa tsakanin Imaan da yaran gidan, sam kuma Imaan ɗin ta kasa tsare hakan, ita kuma ba zata iya buɗe baki ta faɗa mata sharrinsu ba domin bata fatan yaranta su rayu cikin tsoro da fargaba kwatankwacin rayuwar da take ciki. Tana aikin girkin zuciyarta na tsinkewa, haka ta ringa janyo duk addu'ar da tazo bakinta tana yi harta samu ta kammala musu abin karin, Lawisa ce ta fita dashi ta jera dan taji sakkowar maigidan, ko karen hauka ya cijeta kuma bata isa ta shiga su haɗu ba, tamar ta kaiwa masifa goron gayyata ne da hannunta. Guri ta samu ta zauna a kitchen ɗin tana jiran sha biyu ta ƙarasa ta ɗora abincin rana kawai ta huta gaba ɗaya, tana jiyo tashin muryar maigidan yana dariya, da alama yana cikin raha, ta ɗauke ƙwallar data zubo mata da gefen hijabinta. Daga sanda ya aureta, ya canza mata muhalli daga gidan marayun data sani a matsayin komai nata, tarin alƙawarurrukan da yayi mata na kula da ita har ƙarshen rayuwarsa, rayuwar auren da suka gudanar mai cike da aminci. Ta sani, he was never a saint, tun kafin suyi nisa cikin zamansu ta fara fuskantar ƙalubale musamman akan halayyarsa ta tsalle-tsalle. A tsayin lokacin da suka kasance tare, kullum tana cikin yi masa addu'a da neman shiriya daga ubangiji akan wannan dabi'a. Ba abu bane mai sauƙi, amma haka ta jure ta zauna dashi kullum cikin yaƙinin zai bari kamar yanda a kullum yake mata alƙawari. Bata manta lokacin da ta haifi Imaan, lokacin da ya ɗauki yarinyar ya ke ce mata, "Ko dan saboda ita zan daina Aisha, ki cigaba da yi mini addu'a." Sai dai bata sani ba tun kafin nan ya rigada ya dasa irin da ya yi tsiro ya tarwatsa rayuwarsa da tata baki ɗaya, kwaɗayinsa ya kaishi ga faɗawa rami, gashi fitowa daga cikinsa ya yi masa wahala. Tana da yaƙini, da ace za'a bashi zaɓi, ya fanshi kansa daga wannan rayuwar da bashida maraba da yaron goye, sai inda aka kaɗa hankalinsa, tabbas zai zaɓi ya rasa komai daya mallaka domin ya fanshi yancinsa. A hankali raha da dariyar da take jiyowa ta koma fushi, ko tace rigima. Tana yawan faɗa masa a lokutan baya ta ce "Ka daina faɗa, in'ina da harɗewar bakinka basa tashi sai kana fushi da faɗa" dalilin daya saka ta fahimci abinda yake faruwa kenan saboda jiyoshi yana ta jan kalma guda ɗaya ya kasa furtata, alamar ransa yayi ƙololuwar ɓaci kenan. Sai ta ajiye shinkafar da take tacewa ta matsa jikin ƙofar kitchen ɗin zuciyarta ta shiga bugawa jin Hajiya Alawiyyah dake nata faɗan cikin yare tana ambaton sunan Imaan. Abinda take gudu kenan, shiyasa kullum take jan kunnenta akan ta kiyaye su. Ta karɓi ƙaddarata, bata san wane hali zata shiga ba idan wani abu ya samu wani daga cikin yaranta. Data kasa kunne sai ta fahimvi faɗan akan suspension ɗin da aka basu ne, tana ji yana rantsuwar ba zai je makarantar ba, sai dai su koresu tunda dama asarar kuɗi kawai yake yi ba karatun suke ba. Sunan Imaan da Alawiyyah take nanatawa shi yafi komai ɗaga mata hankali, haka ta cigaba da aikin sukuku a ranta tana addu'ar Allah ya kare mata yarinyarta daga duk mugun nufin su. Bata samu sukunin komawa ɓangarensu ba bayan ta kammala abincin rana, wani girkin Alawiyyar ta ce ta ɗora, za ta yi baƙi. Shirun da ta yi bata ce mata komai akan faɗan su Imaan ɗin ba ya saka ta sake shan jinin jikinta, akwai abinda ta ƙudure a ranta kenan, koma menene tana fatan ubangiji ya yi musu tsari dashi. Sai bayan la'asar ta samu ta kammala, tamkar ta cire ƙafafunta ta yar tsabar yanda suke yi mata ciwo amma bata samu zarafin hutawa, wanka kawai tayi ta sake komawa cikin gidan. Cake da cin-cin ta ce zata kuma yi mata da zata kaiwa ƙawarta, za'a kawo lefen yarta a washe gari lahadi. Ba yanda Imaan ba ta yi akan suje ta tayata ba ta ce a'a, gargaɗi ta mata akan kada ta kuskura ko ƙofa ta fita, sai dai jan kunnen Mamin bai je ko ina ba dan da tayi sallar isha'i taji ɗakin ya mata shiru, Ahmad yana gama cin abinci ya yi bacci bayan da ya gama kuka akan ta hanashi yaje gurin Al'amin, ta zauna shiru tana dakon dawowar Mami amma har ƙarfe tara sai ta zura hijabi akan kayan baccin data saka ta fito. Page 10 Ba yanda Imaan batayi akan suje ta tayata ba ta ce a'a, gargaɗi ta mata akan kada ta kuskura ko ƙofa ta fita, sai dai jan kunnen Mamin bai je ko ina ba dan da tayi sallar isha'i taji ɗakin ya mata shiru, Ahmad yana gama cin abinci ya yi bacci bayan da ya gama kuka akan ta hanashi yaje gurin Al'amin, ta zauna shiru tana dakon dawowar Mami amma har ƙarfe tara sai ta zura hijabi akan kayan baccin data saka ta fito. A irin ranakun yau Mamin bata ko kaiwa la'asar a cikin gidan tunda yawanci a waje su ke yin dinner, ta zata kuma cake da ta ce za ta yi musu ba zai ɗauki lokaci ba amma gashi ta shafe awanni. Chalet ta fara tsayawa suka gaisa da Abbo, ya mata ƙorafin kwana biyu ba ya ganinsu, shi kuma baya jin daɗi sosai shiyasa yafi zama a ɗaki. Ganin zai jata da hira ya sa ta ce masa zata je ta karɓi littafi gurin Lawwali, ta sani idan ta gaya masa cikin gidan zata shiga, hanata zai yi. Har ta wuce part ɗin farko, asalin tsohon ginin gidansu, kafin a shigo da gidajen kusa da su aka tayar da katafaren bangaren da yake matsayin main house ɗin a yanzu da sauran sassan da akayi har da ɗan akurkin da aka saka su a ciki. Haka kawai zuciya ta kaɗa ta ta koma baya, so take ta tsokano tsohuwar tayi ta haushi kamar

Chapter 6 of 7