Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
aka yiwa dolen yin magana. Kanta a ƙasa ta amsa mata da "Toh." Sai kuma ta kalli ɗayar ta ce "Husna, ke kuma mai za'a dafa miki....?" "Point of correction, Anty Husna, Anty Hasna, haka zaki ringa kiranmu kamar yadda duk ma’aikatan gidan nan suke yi. Ko Mama bata gaya miki ba?" Wadda ta fara maganar ta katseta cikin tsiwa, tana kallonta tana zare idanu kamar mai son bata tsoro. "Yi haƙuri Anty Hasna, manta nayi." "Better," ta ce tana jan dogon tsaki. Sai ta ɗora da cewa "Dama ki faɗawa wannan baƙar yar taki mara tarbiyya kada ta kuskura mu haɗu. Har mu zata ringa kallo tana harararmu bamu isa ta gaishemu ba, har kuma tana yi mana tsaki. To wallahi ki gaya mata, ta kiyayi kanta a cikin gidan nan." Ta finciki hannun yar uwarta suka bar Mami tsaye tana kallonsu, hawaye na malala akan kuncinta. Cikin gidan ta shige tana sharewa da bayan hannu, zuciyarta na cike da mixed emotions. A ranta, take cewa Tabbas ɗan adam abun tsoro ne. Halittar da tafi kowacce saurin mantuwa da alheri ita ce mutum. Ba kowanne mutum ne yake tuna halacci a rayuwarsa ba. Sau da yawa zaka taimaki mutum cikin tausayawa da jin ƙai ka janyo shi daga cikin wuta zuwa inuwa, amma daga ƙarshe, ya saka maka da sharri. Taga aya. Kamar yanda hausawa sukace; kayiwa mutum rana ya maka dare, hakan ce ta kasance da rayuwarta. Bata tarar da kowa cikin katafaren falon da aka cika da kayan alatu ba. Cikin hanzari ta shige kitchen tana godewa Allah da bai saka ta haɗu da kowa ba. Jikin wani ƙaramin allo da ke makale a bango ta tsaya, ta shiga karanta jerin abubuwan da ya kamata ta dafa wa kowa daga cikin gidan. A cikin few seconds, ta gama fahimtar jerin, sai ta fara haɗa lemuka, tana duba agogo lokaci zuwa lokaci. Ganin su Husna ya tuna mata da jiya taji suna zancen yau ɗin akwai dinner auren yar Hajiya Shafa, ƙawar Hajiya Alawiyyah. Hakan ya saka ta samu nutsuwa akan makarar da tayi, zatayi aikinta cikin nutsuwa harta kammala ƙila basu dawo gidan ba musamman daya kasance abubuwan da zatayi yau ɗin duka ba masu wahala bane. Da haka ta shiga aikinta cikin tsafta da kuma ƙwarewa. Lokaci-lokaci tana kallon agogo gudun kada ta shagala har su dawo bata kammala ba, da yake bunners ɗin da yawa kuma girkin duk bai wuce cin mutum ɗaya ba zuwa ƙarfe goma na dare ta gama komai har ta gyara dining table. Still, bata ji motsin su ba, alamar ba su dawo ba har sannan. Tana tsaka da gyara zaman kwanukan bayan data gama ajiye komai da zasu buƙata ta jiyo ƙarar takun takalmi. A hankali ta ɗaga kai ta kalli stairs, inda ƙarar ke fitowa. Tun kafin su haɗa ido, ƙamshin turaren data riga da saninsa ya sanar mata da ko wacece. Gabanta ya faɗi, zuciyarta ta tsinke. Ta dafe ƙirjinta, tana karanta "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un..." cikin ƙaramin sauti. Matar data sauko daga saman step ɗin ta tsaya daga sama tana kallonta da wani judgemental look wanda ke nuna zallar tsana ga wanda ake yiwa haɗi da raini da kuma ƙyama. Fuskarta cike da izza da taƙama. A first glance zaka gane jinsinta, Bororoji. Farace fat, wani irin haske gareta da kai tsaye zaka iya kiranta da zabiya in badan baƙin gashin ido, gira dana kai da take dasu ba. Su kaɗai ne kalar baƙi a jikinta. Bata da jiki sam, a bushe take kamar tattasan da aka shanya a rana. A ƙiyasi zatayi shekaru 45 zuwa sama, haka nan tamkar waɗancan yammatan wanda da alama ita suka gada a komai bata da wata ƙira ta mata mai jan hankali idan ka cire farar fata sai tsayi kamar daren baƙin ciki. Hajiya Alawiyyah Kenan Mata a gidan Alhaji Muhammad Arabi. Cike da izza haɗi da taƙama ta cigaba da sakkowa idanunta akan Mami da tunda ta mata kallo ɗaya ta mayar da kanta ƙasa, tamkar an zare mata lakar jikinta ta kasa cigaba da abinda takeyi saboda tsananin bugun da ƙirjinta yakeyi. A ranta addu'a take kada Allah ya kawo abin da zai sa Hajiya Alawiyyar tayi mata magana, se dai addu'ata bata karɓu ba daidai sanda ta juya da nufin komawa cikin kitchen ɗin bayan data gama tattaro duka ƙarfin halinta. Wani kallo Hajiya Alawiyyah ta bita dashi na tsantsar tsana kafin da sauri, cikin ɗaga murya da gurbatacciyar hausarta ta ce "Ke... karuwa. Mene na gaya miki akan shigo mini gida ba tare da Hijabi ba? Wato kin fara raina maganata ko?" Nan da nan jikinta ya ɗauki rawa, hannunta ya shiga tsattsafo da zufa. Shaf ta manta da kashedin Hajiyar, Saboda taji daɗin yin aikin sanin babu kowa a gidan ya saka ta cire hijabin ta rataye. Allah Allah take ta ƙarasa gyara gurin ta mayar, rabon ayi haka ta tsaya sake gyara kwanuka. "Ba magana nake miki ba munafuka kin wani sunkuyar da kai ƙasa kamar ta Allah?. Naga alama kin fara gajiya da zaman gidan nan. Ko kuma na ce na sake miki da yawa, kin fara manta matsayinki a gidan nan har kina ƙoƙarin wuce gona da iri. Idan bakiyi wasa ba nan ba da daɗewa ba zaki barshi kinga se ki koma can cikin tashan ki cigaba da yawon karuwanci dake da yayan zinar naki." A duk irin kalaman da Hajiya Alawiyyah ta ke gaya mata, babu wanda ke cutar da zuciyarta kamar yadda take kiran yayanta da ‘ya’yan zina. Tana ƙoƙarin ta maida mata martani ko da kuwa gargaɗi ne kawai akan ta daina alaƙanta yayanta da kazanta, amma duk sanda suka fuskanci juna, ji ta ke yi tamkar an ɗaure mata baki, bata iya cewa uffan. Ba babu wata kalma da take iya iya furtawa a gaban Alawiyyar face "na gode", "yi haƙuri", ko karɓar umarni. Sai kawai ta juya, zuciyarta na mata wani irin suya amma harshenta ya gaza bata haɗin kai balle ta furta abinda zai rage mata nauyi da raɗaɗin zuci. Tana jin Hajiya Alawiyyah na cigaba da aibata ta ita da yaranta, sai ta shige kitchen ɗin kawai ta tsaya gaban sink ta tsaya tana haki. Ji take tamkar an ɗora mata dutse mai nauyi a zuciya. Hatta da hawaye yayi mata tawaye, a lokacin da take buƙatar saukarsu ko zasu sanyaya mata zuciya sai dai ƙamas tamkar ƙasar sahara babu abinda ta iya matsowa sai ma raɗaɗi da idanuwanta suka ɗauka. Da zuciya ɗaya ta taimake su. Ta tashi bata da wani mahaluƙi a duniyar nan da zata kalla ta kira jininta shiyasa without second thought ta taimakin mutanen da take gani gani da irin ƙaddararta. Ashe bata san kara da kiyashi ta kwaso ba, a zatonta kowanne mutum yana da kyakkyawar zuciya amma gashi yanzu ta fahimci cewa wasu mutane babu Allah a ransu, kuma suna iya amfani da mutum tamkar takalmi daga ƙarshe su watsar da kai a rana. Page 6 A hankali ta zube ƙasan tiles ɗin. Muryar mai gidan data jiyo wanda da alama tare suka sakko da matar tasa ya sake rura wutar da take ci a zuciyarta. Saukar kalamansa a masarrafar jinta ya kwance notin daya toshe hanyar fitar hawayenta. Ta fashe da kuka mai tafe da shassheƙa, sai dai babu sauti, sai da tayi mai isarta sannan ta wanke fuska, ta saka hijabi ta fice ta ƙofar baya ba tare da ta ci ko loma ɗaya daga cikin abincin da ta dafa ba. Dokar matar gidan kenan, ta musu lamuni su zauna a cikin gidan, amma daga ita har yayanta ba su da ikon ci daga abinci ko amfani da duk wani daya fito daga cikin gidan ba. Sai dai abinci ya ruɓe ko a zubawa karnuka. A ƙofar shiga ɓangarensu su suka ci karo da Abbo, asalin maigadinsu kuma mahaifin Hajiya Alawiyyah. Zuciyata tana yawan saƙa mata cewar shine silar komai, da ace bai kwaso su ya kawo su gidan ba ƙila da ƙaddararta bata kasance mai muni irin haka ba. Sai dai tana matuƙar ƙoƙari gurin hana zugar shaiɗan yin tasiri akanta, ita ɗin ba kowa bace face marainiyar data tashi bata da kowa. Ubangiji ya ɗagata a lokacin da ya so, ya kaita matsayin da masu uba suke ganin bata isa ba, dan haka ba zata tuhume shi a yanzu daya juya al'amarinsa ba domin ya fita sani akan hikimar dake tattare da hakan. Yanayin fuskarta ya gusar da fara'ar dake shimfiɗe akan fuskar tsohon, cikin lafazin dake nuna tausayawa ga wanda ake yiwa magana ya ce "Hajiya Aisha, ki cigaba da haƙuri da yanda rayuwa ta juyo miki. Ba zan gaji da nanata miki ki riƙe addu’a ba, kada ki taɓa yanke ƙauna. Tabbas sauyi yana tafe, ko ba daɗe ko ba jima, gaskiya zata yi nasara akan ƙarya. In shaa Allahu, ba zaki mutu ba sai kin ga sakayyar da Allah zai miki akan duk wanda ya cuceki." Ta goge hawayenta da gefen hijabi ba tareda ta ce masa komai ba. Shi ɗin ma bai saka ran zata ce ba dan haka ya miƙa mata ƙatuwar baƙar ledar dake hannunsa ya ce "Ban ji motsin dawowarku ba, yau na tashi jikina baya mini daɗi ko sallah duka a ɗaki nayi. Saƙon Alhaji ƙarami ne, tun jiya mai gida ya bayar ban samu na kawo ba shi kuma bai shiga gurina ba." Kallon ledar tayi kafin ta mayar da idonta tana nazarin gurin fuskarta kuma ta bayyanar da tsoron dake cikin zuciyarta, sai yayi murmushi ya matsa bakin ƙofa ya ajiye mata ledar yana cewa "Ki shiga ciki, ki gaida mini da yaran, Allah ya tashemu lafiya" ya matsa ita kuma ta shige tana yi masa godiya. Aliyu kaɗai ta tarar a falon yana kwance ya zubawa bango ido ya lula duniyar tunani. Motsinta ya maido dashi hayyacinsa, ya kalleta gajiya rubuce ƙarara a fuskarta sai ya tashi zaune yana mata sannu. "Yawwa Aliyu, tun yaushe ka dawo?" Ta mayar masa tana zama a ƙasa, ƙafafunta sun riƙe saboda tsayuwa shiyasa ta zauna ta miƙe su ko zata samu sauƙin tsukon da sukeyi mata. Tashi yayi ya ɗauko ruwa daga fridge ya aje mata yana cewa "Na ɗan jima da dawowa, kina fita na shigo. Gajiya da yawo kawai na dawo Mami, dukkan inda nake tunanin zuwa naje amma ba'a dace ba." Cike da tausayi ta ringa kallonsa, bata maida hankali akan maganar ba ta tambaye shi ko su Imaan sun ci abinci kafin su kwanta. Da ka ya amsa mata, sai ta miƙe tana cije baki ta wuce cikin ɗakin tana ce masa bari tayi wanka. Ta rigada tayi sallar isha'i, ta yi wanka kafin ta shiruayta dawo falon ya haɗa mata baƙin shayi kamar yanda ta buƙata dan bata jin wani abu mai nauyi zai iya ratsa maƙoshinta ya wuce duk kuwa da tana jin yunwa. Ledar da Abbo ya bata ta buɗe bayan data ajiye tea ɗin data kasa sha. Ta zazzage kayan ciki a ƙasa, Shaddoji ne kala biyu da yadi shima biyu duka a ɗinke, sai takalma ƙafa uku da huluna suma uku sai jaka da takalmin makaranta, duka kayan size ɗin Ahmad. Cike da mamaki take kallon kayan haka ma Aliyu daya taso daga in da yake kwance ya tsaya akanta, ya ɗaure fuska yana muzurai dalilin fahimtar daga inda kayan suka fito. A sanyaye ta ɗauki brown envelope da ta gani, ta buɗe kuɗaɗe suka zobo, notes na 100$ guda ashirin ta irgasu sai farar takarda. A gefe ta ajiye kuɗin kafin ta warware takardar ta shiga karanta content ɗin ciki "Na Aliyu ne, ya yi hidimar makaranta. Idan basu isa ba ki sanar da Abbo." Iya abinda aka rubuta kenan. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke kafin ta turawa Aliyu dake tsaye kuɗin da kuma takardar. Takardar ya ɗauka ya karanta, a fusace ya tsagata biyu ya watsar yana cewa "Sai dai na haƙura da karatun da dai nayi amfani da kuɗinsa, ashe dama ya san ya haifi wasu yayan? Ya san muna raye kuma muna da haƙƙi akansa?" "Bana son sakarci Aliyu" ta katse shi. "Baka isa ka canza gaskiyar cewa Muhammad ne ya haife ku ba. Jarabawar da yake ciki daga Allah ce, Aliyu, fushinka babu abinda zai canza addu'a kaɗai yake buƙata a yanzu. Ban sare ba kuma ina so ku jajirce mu cigaba da kaiwa Allah kukanmu, ina da cikakken yaƙinin wata rana komai sauƙi zai samu, ko menene aka yi domin a raba mu dashi, ubangiji zai yi mana magani." "Kullum haka kike cewa Mami, babu wani asiri yana sane. Idan bai san mai yakeyi ba yanzu mai yasa zai aiko da kuɗin yace nayi hidimar makaranta? Yana sane kawai so yakeyi kullum ya ganmu cikin baƙin ciki da wahala amma babu wani..." "Aliyuu" ta kira sunansa da yanayin daya saka shi haɗiye sauran maganganunsa. Ta kama hannunsa ya zauna a gefenta haɗi da ɗora kansa a kafaɗarta, tana shafa kansa kamar ƙaramin yaro cikin taushin murya ta ce "Kana so kace mun ka manta irin tarin so da kulawar da Abbi ya nuna maka tun daga tasowarka? Har ka manta lokacin da yake cewa in sauke Imaan daga cinyata tana jaririya na ɗoraka saboda kada kayi kishi kace na samu wata na daina damuwa dakai? Aliyu ka manta lokacin da yake ɗaraka a bayansa yayi ta zagayawa da kai dukda ciwon bayan da yake fama dashi saboda kada ranka ya sosu an goya ƙanwarka? Ka manta lokutan da yake baro gurin aikinsa ya ɗakko ku daga makaranta saboda kayi ƙorafin duka abokananka Abbinsu ne suke ɗauko su daga makaranta ba driver ba? Wane irin gata da kulawa ne wanda uba yake bawa yayansa da bai nuna muku ba? Shine yanzu saboda jarabawa ta same shi har kake iƙirarin so yake yi ya ganmu cikin ƙunci da baƙin ciki? Ko da ace kowa zai juya masa baya ban ɗauka kaima zaka kasa yi masa uzuri ba, ko Imaan duk fushin da takeyi bata taɓa cewa baya sonku ba domin ta fika fahimtar abinda yake faruwa. Fushinta na rashin sanin ta hanyar da zata taimake shi ne ba wai dan ta tsane shi ba. A yanzu Muhammad tamkar rakumi ne da akala, bashi da tunanin kansa, sai inda aka ja shi aka kai. Addu'a kaɗai yake buƙata. Bana son yanda kake ɗaukar al’amura da zafi, hakan babu kyau, Aliyu." Jin ta kawai ya ringayi, ya gyaɗa mata kai bayan da tace kada ta sake jin wata magana mara daɗi daga bakinsa akan mahaifinsu, ya kuma ɗauki kuɗin sannan idan sun haɗu gobe yayi masa godiya. Ya amsa tane kawai amma baya jin zai iya yin hakan, to akan me zai gode masa? Sauke haƙƙin da Allah ne ya ɗora masa ya banzatar ko me? Sai da ta tattare kayan ta mayar dasu cikin leda kafin ta wuce cikin ɗakin ta barshi. Ya kashe fitila bayan ya tattare kuɗin ya watsasu ƙasan kujera ya kwanta a kai. A ganinsa, idan ma jarabta ce daga Allah, halinsa ne ya janyo masa hakan. Bai manta komai ba, abubuwan da suka faru suna nan daki-daki a ƙwaƙwalwarsa. Gaskiyar Mami ya sani mahaifinsu ya so su a baya. Yana tuna komai, yanda yake kiransa da "Aliyuna, ko ya ce my pride," yana shafa kansa da murmushi. Yanda suka saba fita tare a ranakun Asabar ya kaishi gidan gonarsa ko ya tafi dashi site ɗin ayyukan kwangila da yake yi. Shekararsa bakwai sanda aka haifi Imaan, haka nan zai kwanta yayi ta birgima yana kuka wai Mami ta daina sonsa yanzu babynta kawai take so kuma Abbin ya biye masa saboda kada ransa ya ɓaci ko ɗaukar Imaan ɗin bayayi sosai wani lokacin kuma ya tayar da rigima sai an bashi ita kuma Abbin ya ce a bashi haka Mami zatayi ta binsa cike da farfabar kada ya kayar mata da yarinya. Sai dai duk wannan farin ciki ya tsaya cak, kamar an datse waya tsakanin su. Lokaci guda mahaifinsu ya zama baƙon mutum a rayuwarsu. Abbin da idan ya shigo gida su zai fara nema ya tabbatar da lafiyarsu kafin ya amsa ko sannu da zuwan Mami sai gashi rana tsaka yace su tattara su bar masa gida nan duniya babu fuskokin daya tsani gani sama dasu. Baya son tuna dalilin faruwar komai domin wani ciwo ne a zuciyarsa da baya fatan buɗewarsa. Kuskure ɗaya ne ya jefa rayuwarsu cikin garari, kuskuren da tun bai san kansa ba ya fahimci ba abu bane mai kyau Abbin yake aikatawa, daga sanda ya san ma'anar abin kuma kullum zuciyarsa cike take da tsoron kada Mami ta sani. A tunaninsa ɓoye mata shine zai zama katangar da zata karesu daga afkawa damuwa sai dai bai sani ba hakan shine babban kuskuren daya canza zanen ƙaddararsu gaba ɗaya. Babban abinda yake ci masa zuciya ta yanda shi yake aikata laifi amma su suke karɓar humuncin kuskurensa. Baya ga haka, bai taɓa taɓuka komai domin nuna cewa yana sane da cewa har yanzu su ɗin 'ya'yansa ne kamar sauran ba, sai dai a bayan ido ya nuna yasan da zamansu. Wannan ne dalilin da yasa kalmar "haƙuri" tayi masa nauyi, kalmar "uzuri" kuma ta zama kamar zunubi idan ya jiɓanta ta dashi, to akan me zai yi masa uzuri? Laifin daya aikata yana sane ko ma ya ce yake aikatawa? Rayuwar daya zaɓawa kansa?? * Washe gari, kamar kowacce rana, tun kiran sallar farko suka tashi suka hau shiri. Seda sukayi wanka kafin Mami ta shiga cikin gidan don haɗawa su Hasna abinda zasu ci da kuma wanda zasu tafi dashi makaranta. Kwanukan da aka yi amfani da su daren jiya duk suna kan dining table abincin maigidan kaɗai aka taɓa. Seda ta kwashe komai wanda zai ajiyu ta saka musu a fridge, tunda tasan zuwa anjima musamman yaran suna iya mata tijara har idan suka nema ba su samu ba. A cikin kitchen ɗin tayi sallar asuba, sannan kafin shida da rabi ta gama komai har da abin karyawar maigidan, wanda Lawisa ɗaya daga cikin masu aiki ta bata sallahun cewa Hajiya ta ce ta haɗa masa domin da wuri zai fita. Sanda ta koma ɓangaren su, har su Imaan sun karya da ragowar abincin jiya da suka ɗumama, ta zuba wa Mami nata a ƙaramar kula da zata tafi da shi. Duk su ukun suka gaisheta, ta amsa wa Imaan da Ahmad cikin kulawa, amma ta basar da gaisuwar Aliyu. Tana kallo sanda ya ɗaga cushion ɗin kujera ya zuba kuɗin jiya hakan yana nufin duk nasihar da tayi masa ta kunnen dama ta shiga ta fice ta hagu. "Ku je Addah Imaan, kar suyi jiranku, dan naga har Sayyadi ya fito da mota sanda nake shigowa. Idan an tashi ku taho gida kai tsaye, ba sai kun jirani ba. Kinga, se ki samu kiyi muku wankin uniform. Kafin na fita zan tafasa muku farar shinkafa, se ku ci da sauran miyar can. Ga wannan, ko zaku siyi wani abu." Ta ƙarasa tana zaro 1k daga cikin albashin da aka basu jiya. Ahmad ne ya janyo ledar saƙon da Abbo ya bata jiya. Cike da zumuɗi, ya buɗe yana cewa "Mami, kayana ne ko?" Imaan ta kalle shi fuska a haɗe bata dai ce komai ba, sai Mamin ta ce "Yawwa, Ahmad, roƙon Abbo kayi ya siya maka kaya?" Ta tambaye shi da siga da zai fi buɗe baki ya faɗa mata komai ba tareda yaji tsoro ba dukda ta san daga in da kayan suka fito, sai dai bata san dalilin bayarwa ba. Sai ya marairaice fuska ya ce "Mami, ba roƙon sa nayi ba. Ranar nan ne fa zamu tafi school, kin tuna na saka slippers, lokacin takalmina ya ɓare kafin ki siya mun wannan?" Ya faɗa yana ɗaga kafarsa kafin ya cigaba da cewa "Mami, ba roƙon sa nayi ba. Ranar nan ne fa zamu tafi school, kin tuna na saka slippers, lokacin takalmina ya ɓare kafin ki siya mun wannan?" Ya faɗa yana ɗaga kafarsa kafin ya cigaba da cewa "Shine fa Abbon ya ganni ya tambaye ni ina takalmin makaranta, na ce masa ya lalace. To, shine yace zai siya mini, har da school bag. Kuma ya tambayeni sai me nake so bayan takalmin? Ni kuma nace ina son irin kayan da Al'amin yake sakawa ranar Juma'a idan zasu tafi sallah da Abbansu. Dama Yah Aliyu ne yake mana ɗinki tare, yanzu kuma yana tara kuɗi zai biya makarantarsa." Ya ƙarasa yana satar kallon Imaan da Aliyu da suka zuba masa ido kamar zasu cinye shi ɗanye. "Shi da waye a gurin lokacin da kukayi maganar?" Ta sake tambayarsa. Sai yayi shiru kamar yana tunani kafin yace "Lawwali ne… au, Baba Lawwali, se Abban su Al'amin, da Baba Habu, drivern sa. Zasu fita, ya tsaya harma ya bani wata chocolate mai daɗi. Bana gaya miki bama Addah?" Yayi maganar yana kallon Imaan da siga tamkar tambaya. Numfashi ta sauke kafin tace "Shikenan, ku tafi, kar ku makarar dasu. Allah ya tsare. Ayi karatu sosai. Allah yayi muku albarka." Seda Ahmad ya canza takalminsa da sabon kafin suka fita, yana ta mitar ƙin barinsa da Mami tayi ya juye littattafansa a sabuwar jakar. Aliyu, tun sanda Mami ta yi banza da gaisuwarsa, jikinsa yayi sanyi, suna fita ya matsa gabanta murya a ƙasa ya ce "Kiyi haƙuri, Mami…" "Da ka yi mini me, Aliyu?" ta faɗa kamar babu komai, ba tare da kallonshi ba ta shiga tattare takalman da Ahmad ya cire. Shiru ya yi yana muzurai, tayi ƙaramin tsaki ta wuce cikin ɗaki a ranta tana roƙa masa shiriya daga gurin ubangiji. Yana da kafiya musamman akan abinda yake ganin shine akan gaskiya, ita kuma ba zatayi masa lako-lakon da zai cigaba da ƙullatar mahaifinsa a zuciyarsa alhalin ba laifinsa bane, jarabawa ce ta same shi. Sai da Imaan da Ahmad suka shafe kusan minti goma sha biyar suna jiran sauran yaran gidan kafin Al'amin ya fito shi kaɗai. Da gudu ya nufe su, ya fara rungume Imaan. Tayi ƙaramin tsaki tana tureshi, haushin yanda yaron yake shishshige musu takeyi sai kace akwai wata alaƙa ta musamman tsakaninsu. Ta tsani hakan. Sakinta yaron yayi suka rungume juna da Ahmad cikin murna, Ahmad na tambayarsa "Ya jikinka? Jiya Baba Sayyadi yace mun baka da lafiya shiyasa baka je school ba." "Ciki na ne yayi ciwo amma na warke," Al'amin ɗin ya faɗa kafin ya daki Ahmad ɗin yana ɓata fuska ya ce "Ashe ma ka sani, kuma shine baka zo ka duba ni ba." "Da zan zo, Mami tace na bari da safe se nayi maka sannu, tunda Inno tace kada na sake shigar muku gida…" ya ƙarasa a hankali saboda harar da Imaan ta banka masa. A kunne Al'amin ɗin ya raɗa masa "Gara da baka zo ba. Wannan witch ɗin tace seta zuba maka hot water idan ka sake zuwa room ɗina, ko idan ni na zo naku. Na gayawa Dady, yace na bari tunda basa so na je… amma ai baza su hana mu haɗuwa a school ba, ko?" Kafin Ahmad bashi amsa, suka ga Shahida tsaye kansu tana huci "Se kaci uwarka, shege jaki, Inno ɗin ce mayyah? To wallahi sena gaya mata. An rabaka da waɗannan shegun amma baka ji ba, kana sake shige musu," ta hayayyaƙo masa, tana fincikarsa daga kusa da Ahmad. Page 7 Al’amin ya dage ya gantsara mata cizo a hannu sannan ya fizge ya na cewa "Ke ce jaka, bani ba. Kuma baki isa ki hana ni kula Ahmad ba, because he is my only brother" yayi maganar cike da fitsara, yaja gefe ya riƙe ƙugu irin yanda yaga tana yi wa su Husna rashin kunya, harda kaɗa jiki tamkar mai jiran su daku. A maimakon ta hukunta shi, shi da ya mata laifi, a zafafe ta juya ta kwaɗawa Ahmad mari. Imaan, wacce dama ta tsammaci faruwar hakan, cikin sauri ta mayar wa Shahida nata marin, hagu da dama. Shahida ta kurma ihu kamar wadda aka soka wa wuƙa, ta zube a ƙasa ta hau birgima tana kururuwa "Na shiga uku na lalace, ku taimaka mini ta fasa mini ido" take faɗa. Gefe Imaan taja ta tsaya tana kallonta, ƙarshen abin kenan dama, yanzu yayunta da kakarsu zasu fito kamar mayunwatan karnuka su fara haushi. Ta iya tsokana da mugunta, ba damar su haɗa hanya da Ahmad sai ta ci zalinsa abinda Imaan bata taɓa iya ɗauke kai kenan. Idan zasu kwana suna mata abu a karankanta ba lallai ta ɗaga kai ta kallesu amma ba dai a taɓa mata ƙani ba. Ihunta ya fito da sauran. Hasna ce akan gaba

Chapter 4 of 7