ƙofar ganin haske ta ƙasan ƙofar falon Baba saboda fitulun corridor a kashe suke kamar yanda ya barsu ɗazu, da alama kuma Mom bata sake hawowa saman ba ko kuma ba ta wannan ƙofar ta shiga gurin Baba ba shiyasa bata kunna ba.
Fasa shiga ɗakinsa yayi ya matsa ƙofar Baban ya buga a hankali. Alamar kore da wata yar danja tayi a jiki ya saka ya latsa mabuɗi kafin ya shiga da sallama.
Falon ba babba bane can, amma tsaruwarsa ba a iya kwatanta shi a rubuce.
Alhaji Ahmad Gayawa, dattijo fari mai matsakaicin jiki yana zaune a kan kujerar 1-sitter, ya miƙe ƙafarsa akan coffee table hannunsa riƙe da Littafin Hisnul Muslim yayin da idanuwansa ke sanye da gilashin ƙara ƙarfin gani.
A kallo ɗaya zaka hangi kamanninsa da Yusuf ɗin sai dai banbancin kalar fata. Alhaji Ahmad fari ne tas, dukda shekaru da suka ja kuma haskensa bai disashe ba. Yusuf wankan tarwaɗa (Chocolate king), bai yi duhun da za'a kirashi baƙi kai tsaye ba amma kuma bashi da jiɓi da fararen mutane.
Yusuf dogone sosai, ƙirar jikinsa kuma mara rama ita ta sake bayyanar da tsahon nasa ko ace ya zama ingarma. Ba kiɓa ce dashi ba, amma jikinsa a murje yake yana kuma da faɗin ƙirji sakamakon ƙarfe da yake ɗagawa haka hannayensa a murɗe suke musamman idan yana fushi har wasu jijiyoyine suke tasowa a cikinsu.
Idan ka kalli fuskarsa, ba zaka ka kirashi kyakkyawa kai tsaye ba. Amma abubuwan da ke fuskar tasa duk sun haɗu sun karɓi juna.
Girarsa cikakkiya ce, tana da perfect shape, kamar ta mata. Wannan siffa daga Hajiya Hadiza, kusan kuma ita kaɗaice wani abu da kai tsaye zaka kalla a jikinsa kace na mahaifiyarsa ne, sai dai ɗabi'u. Saurin fusata, rashin magana da rashin fara'a (dan Baba mutum ne mai faran faran da barkwanci) da kuma yalwar gashi su kaɗai ne abubuwan daya tsinto a gurinta, DNA doesn’t lie.
Abinda ya fi jan hankali a tattare dashi su ne idanuwansa.
Suna da wani sirri da kaifi, kamar suna magana.
Idan Yusuf yana cikin annuri suna sheƙi.
Amma idan zuciyarsa ta harzuƙa sai su janye, su koma ciki, kamar idon macijin da ke shirin kai hari.
Hancinsa daidai ne, not too pointed, not flat.
Amma laɓɓansa...
Yammatan da suka rasa hankali a kansa sun san me yasa...Yammata da dama sun zo sun durƙusa suna roƙonsa da kansu
"Just one kiss, Yusuf... please."
**********************
Fuska a sake, cikin nutsuwa, Baba ya ɗaga kai ya kalleshi ta cikin farin reading glasses ɗinsa.
Ya ƙarasa ya zauna a ƙasan soft carpet ɗin falon kafin ya shiga gaisar da Baba.
Baba ya saki murmushi yana cewa
"Malam Isuhu, kana gidan ashe tun asuba rabon da mu haɗu."
Sai ya taɓe baki kamar yaron da aka ce ba za'a tafi unguwa dashi ba, Baya son sunan "Isuhu" da Baba ke kiransa, kuma Baba ya san haka shi yasa ma yake ƙara tsokanar sa, even in public. Har ma wasu daga cikin business partners ɗin Baba sun fara kiran shi da sunan.
Amma da yake shi ɗin gwanine, yi yake kamar bai ji ba, Baba ne kaɗai bai isa ya ƙi amsa masa ba.
"Na yi tunanin ka fita ne tunda ban ganka a masallaci da Azahar ba shiyasa ban shigo ba". Ya bashi amsa.
Baba ya cire gilashin idonsa tareda ajiye littafin hannunsa ya kuma sauke ƙafafuwansa daga coffee table ɗin ya ce
"Mun je gidan gona ne tun safe, an kawo shanun nan, har sun ƙara guda biyu, mace da namiji, suka ce a ba ka."
Murmushi ya yi ba tareda ya ce komai ba.
Baba ya cigaba
"Dama yanzu nake shirin kiranka a waya. Gobe, idan Allah ya kaimu, zaka rakani Kano gaisuwar iyalin Alhaji Manzo."
Yusuf ya ɗaga kai da sauri ya kalli Baba kamar wanda aka watsawa ruwa.
Kano kuma? Rakiya? Kuma gobe??
Bai san a fili ya furta ba, sai da Baba ya ce
"Eh... ko ba zaka samu damar zuwa ba ne?"
Ya shafa sumar kansa da batayi tsayi sosai ba, yana wani shagwaɓe murya ya ce
"Aa, Allah ya kaimu. Amma... ƙarfe nawa za a tafi?"
"Da wuri, Tafiyar mota ce kuma ba kwana zamu yi ba. A goben za mu dawo in Allah ya yarda".
Sai ya zabura kamar wanda aka nuna masa bindiga.
Cikin muryar shagwaɓa irin wadda yayaye ke yi a gaban iyayensu, ya ce
"Baba... Kano to Abuja, a mota? Mu je mu dawo kuma a rana ɗaya?"
Baba ya tsarashi da ido, yana ɗan dariya ya ce
"Idan yawonka ya tashi ba haka kake tafi ka dawo ba? Ina ko last week, sai da ka kaiwa budurwarka birthday cake, wannan ai baka ji wahala ba."
Yusuf ya lumshe ido, ya sauke kansa ƙasa, yana miƙe kafafunsa har yana turzasu kamar yaron
"Ni dai kai nake jiyewa, Baba. At this age, bai kamata ka ringa stressing kanka ba.
Ko tafiyar jirgi mai nisa yanzu ya kamata ka rage shi balle tafiyar mota, kuma abinda bai zama dole ba".
"Gaisuwar matar Abokina kake cewa bata zama dole ba, Isuhu?"
Baba ya ɗaga murya yana kallonsa da mamaki, lokaci ɗaya kuma dariyar yanda ya miƙe kafafu yana abinda ya kamata ace a shekarun sa ya fara ajiye yaran da su ya kamata suyi, amma ya sani idan Yusuf ɗin ya a gabansa kallon ƙaramin yaro yake yiwa kansa, sai dai ya kasa gane dalilin da a koda yaushe kuma yake ƙoƙarin nunawa mahaifiyarsa shi fa ya girma ita da take son riritashi ta na masa kallon jinjirinta har a yanzu.
"Toh, ka dirza ƙafa, idan kaga dama kuma kayi birgima amma tafiya babu fashi in Allah ya yarda" Baban ya sake faɗa kafin ya mayar da gilashinsa sannan ya janyo wani littafi da biro ya fara rubutu a ciki
Kusan minti uku Yusuf na zaune kafin ya miƙe yana kumbura baki yayi masa sallama. Sai ga Hajiya Hadiza ta shigo falon cikin sabuwar kwalliya ba wadda ya barta da ita ba ɗazun.
Yusuf ya bita da kallo, Mom dai, she never misses.
Tun yana ƙarami ya tashi ya ganta da gayu, har yanzu kuma bata bari ba kullum ma ƙarawa takeyi dan kamar yanda zamani yake juyawa haka itama a kullum take cikin canzawa, ta yuwu shine dalilin daya saka tayi ƙarko harta kawo wannan lokacin ita kaɗai cikin gidan Alhaji Ahmad.
Yar gayu ce ta gado, ko yanzun da yake ƙarfe sha ɗaya na dare she looks like she's going for brunch at Transcorp. Doguwar riga ce a jikinta yar kanti, bata nuna tsiraici ba, amma ta mata kyau matuƙa ta kuma dace da irin yanayin.
Ta wuce shi without a glance ta ajiye ƙaramin tray mai ɗauke da butar shayi da kofuna biyu a kan coffee table kusa da Baba.
Tsayawa yayi yana kallon murmushin da Baba ke yi mata.
A kullum, iyayensa suna sakashi yarda da soyayya bata tsufa. They loved each other, deeply.
Suna tattali da gudun ɓacin ran juna, yanda ta zuba shayin ta miƙawa Baba shi kuma ya haɗa kofin da hannunta yayi kissing kafin ya saki ya saka shi sakin murmushin da bai yi niyya ba.
Amma da sauri abinda ya faru ɗazu ya dawo masa, take farin cikin da ya samu ya ɓace, tamkar kawowar hasken wutar lantarki ɓacin rai ya sake mamaye zuciyarsa. Haka ya fita ya barsu ya wuce ɗakinsa.
Kwana yayi da fushin tafiyar Kano, ya ringa addu’a Allah ya kawo hujja da zata sa Baba canza shawara. Ko dai su tafi a jirgi, ko tafiyar ma a soke.
Sai dai addu’arsa bata karɓu ba dan bayan sallar Asuba Baba ya ce masa ya shirya yanzu dan zasu tsaya a Kaduna yayi wani uzuri duk a yau ɗin.
Karfe shida bata gama cika ba ya fito cikin shiri, kallo ɗaya zakawa fuskarsa ka fahimci ba yanda ya iya kawai tursasashi akayi tafiyar.
Haladu ne ya ba shi key ɗin mota da aka shirya zasu yi tafiyar da ita.
Ya karɓa, yana jujjuya shi a hannu zuciyarsa na kaiwa da komowa.
Something didn’t feel right. At all.
Ya nufi motar data sha wanki, tana kyalli da ɗaukar ido amma sam bai jin zai iya tafiya da ita.
Sai ya juya, ya koma cikin gida da sauri, a falo suka ci karo da Baba da Mom na shirin fita ya wuce su yana cewa
"Mantuwa nayi".
Bai jima ba ya dawo rike da key ɗin motarsa, da kuma hula domin ya san Baba sai yayi mita akan mai yasa ya saka manyan kaya idan ba zai saka hula ba?
A jikin motar ya tarar dasu Baba na gaisawa da ma'aikata Mom na gefe sai Barr Salahuddeen da bai san lokacin daya zo gidan ba. Ya ƙarasa ya gaishe shi. Motarsa ya nufa ganin Baban ya sallame su, duka suka bishi da kallo
Mom ta kira da sauri
"Ina kuma zaka je? Ba tafiya zaku yi ba?"
Sai da ya zauna cikin mota, ya sauke glass, ya ce
"Eh, tafiya zamu yi. Bismillah, Baba".
Ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan ne ya buɗewa Baba ƙofar mazaunin mai zaman banza inda yake zama idan zasu fita da Yusuf ɗin.
Cikin fushi Momy ta katse Baba dake shirin shiga motar tana kallon Yusuf ta ce
"What do you mean by tafiya zaku yi?
Dama a wannan motar akayi arrangement din tafiyar ku? Or you just decided that yourself?"
Bai ce komai ba sai Baba ne yayi magana cikin natsuwa da ƙoƙarin kwantar mata da hankali ganin yanda ta hasala akan abinda bai kai ya kawo ba
"Duk mota ai mota ce, Khadija. Kuma tunda shine mai tuƙi, ya kamata ya ɗauki motar da yake fi jin daɗin tafiya da ita, ai."
"Haka ne Sir," cewar Barr. Salahuddeen yana shiga maganar.
"Amma da tun jiya ya kamata ya faɗa cewa da ita za a tafi, so that a yi checking, a tabbatar babu wata matsala" Barr ya sake faɗa.
Idanun Yusuf suka sauka kan Barr, harara mai kyau suka aika masa da ita amma ba da niyya ba dan shima bai san yayi hakan ba,
Baba yayi murmushi
"Bai san da tafiyar ba sai bayan ka tafi tukunna na sanar masa, Mota kuma, ai lafiyarta ƙalau. Kafi kowa sanin ɗanka is very conscious. Ba zai hau karfen da yake da matsala ba."
Hajiya Hadiza ta kwaɓe fuska, cikin kakkausar murya tace
"Ni dai, koma yaya ne, ba zaku tafi da wannan motar ba. Irin gudun da yake yi da ita a gari, who knows ko duk tayoyin sun kwance?
Rami kaɗan za a shiga su iya cirewa".
Baba ya girgiza kai
Page 3
Baba ya girgiza kai
"Allah ya kiyaye, babu abinda zai faru sai alkhairi."
Sai ta kwaɓe fuska cikin yanayin nuna damuwa ta ce
"Ni dama tafiyar motar bata kwanta min a rai ba. In dai ba motar da aka yi arrangement da ita ba, then forget it.
Ku haƙura da tafiyar ko kuma ku tafi a flight kawai".
Murnar da Yusuf ya fara yi ce ta koma ciki ganin Baba yabsauka daga motar yana ce masa
"Sauko mu tafi da waccen ɗin tunda ita Nana Khadija take so".
Momy tayi wani fari da ido cikin jin daɗi like a queen whose wish just became law, ta rungume Baba nan take, ba tare da jin kunyar mutanen da suke a gurin ba..Baban ya janye ta da murmushi.
Haka ba dan Yusuf ya so ba, ya hau motar da hankalinsa sam yaƙi kwanciya da ita. He just couldn’t place what was off, but he felt it.
*******************************
Duk su biyun kallo ɗaya zakayi musu ka hango gajiyar dake tattare dasu. Imaan. Matashiyar budurwa da ba zata haura shekaru 15 zuwa 16 tareda ƙaninta Ahmad ɗan shekara 8.
Yanda yaron yake ɗaga ƙafa tamkar zai hantsila abin tausayi, gajiya yayi da yanda take jan hannunsa ya coge a guri ɗaya, ta waiwaya ta kalleshi muryarta har bata fita dakyau tace
"Ahmad ka ɗaga ƙafarka muyi sauri mana nasan yanzu Mami ta rigada ta fito".
Sai da ya yamutsa kyakykyawar fuskarsa da kana kallonsa kasan yunwa ta jigata shi ya ce "Addah Imaan na gaji, kuma yunwa nakeji.
Yau Al'amin bezo school ba kuma kinga dama shi yake bani abincin sa naci idan ban je dashi ba".
Yanda yayi maganar dole ya bawa duk mai sauraro tausayi, musamman yar uwarsa da tafi kowa fahimtar abinda yake nufi.
Cike da tausayawa ta kalleshi bayan data rage tsayinta a gabansa, kallon titin tayi da ɗaiɗaikun mutane ke wucewa saboda yanda rana ta ƙwalle yawanci kuma yan makaranta ne irinsu da basu da kuɗin hawa mota sai kuma ɗai-ɗaikun jama'ar gari da kuma motoci.
Hannu ta saka ta share ƙwallar data taru a gefen idonta kafin tayi masa alama daya hau bayanta. Kallonta ya tsaya yana yi, hakan ya saka tace masa
"Kayi haƙuri kaji ƙanina hau na goyaka mu ƙarasa nasan In sha Allah Mami ta ajiye maka abinci harda nama".
"Addah kema fa kin gaji" ya faɗa yana kallonta da tausayi.
"Ka hau nace bana son dogon surutu" ta faɗa tana ɗaure fuska.
Jakarta ya karɓa ya goya kafin ya hau bayan nata suka ci gaba da tafiya, dagasken itama ta gaji amma ya zatayi?
Ire-iren lokutan nan da wata ya doshi ƙarewa sukan shiga matsin daya zarce na ko yaushe.
Yau ɗin 300 Mamin ta tashi da ita a hannunta, a ciki ta cire 150 da zatayi kuɗin motar zuwa gurin aikinta su ma ta basu 150.
Bata kuma ta san ya akayi ta rasa naira 100 ba, sai naira 50 ta gani a jakarta bayan da aka tashi. Duk kuma masu Adaidaitan data tare ta roƙesu akan su kaisu Unguwa uku a naira 50 daga Farm center sun ƙi, daƙyar ta samu wani ya ɗauke su, suna zuwa Gadar Lado kuma yace ya fasa zuwa su sauka cikin gari zai koma.
Da kansa ya tare musu wani mashin ɗin dan haka ba tareda fargabar sake biyan wani kuɗi ba suka hau sai dai suna fara tafiya yace mata har yanzu ba'a zo inda zasu sauka bane tace masa tasha zasu sauka nan yace shi ai ba haka wancan ya ce masa ba, cewa yayi ɗan gaba kaɗan zasu sauka kuma dan yaga daga makaranta suke ma shiyasa ya ɗauke su akan abinda ya bashi dan haka su sauka su nemi wani kawai.
Haka ya sauke su babu ko tausayi ya gwammace yaja mashin ɗin ya tafi babu kowa a ciki.
Saboda saurin da tayi cikin mintuna da basu wuce goma ba suka ƙarasa, dauriya kawai takeyi dan zata iya cewa tafi Ahmad ɗin galabaita tunda shi ya karya kafin suka fita da safe ita kuwa banda ruwa babu abinda ya shiga cikinta a yau duka.
Tasha ce da Motoci keyin jigila zuwa gari-gari suka shiga. Tana jin yanda yan iska daga cikin mazauna cikin tashar suke mata ɗan kira abunda har ta rigada ta saba dashi seta ƙara ɗaure fuskarta tare da ƙarawa tafiyarta sauri dukda yanda ƙirjinta yake amsawa saboda yunwa ga kuma goyon da tayi.
Daidai Wata Babbar Rumfa da aka jere kujeru farare da Tebura suka ci burki, ta sauke Ahmad da har ya fara baccin wahala ta dafe bayanta da take jin tamkar ba'a jikinta ba tana cewa "Wash Allah na".
"Aa Addan Ahmad se yanzu? ya akayi yau kuka daɗe ga rana ta ƙwalle kuma?" Wata Farar Mata me zanen kalangu a fuska ta faɗa tanayi musu murmushi.
Da murmushi Imaan ɗin ta amsa mata kawai. Ɗabi'arta ce, bata da yawan magana. Ba kowacce magana ce take da amsa a gurinta ba, sai dai tayi murmushi a inda buƙatar hakan ta taso ko kuma tayi shiru kawai.
Ahmad dake tsugunne saboda yanda ƙafarsa take rawa ne ya bata amsa da cewa
"Anty yau Hasna ce ta hana a kawo mu wai sai dai mu taho a ƙasa, gashi kuma yunwa mukeji..." Kallon da Imaan tayi masa ya saka yayi shiru tareda rufe fuskarsa da tafin hannunsa.
Anty Iyami ta kallesu cike da tausayawa kafin ta girgiza kanta a ranta tana Hasaso halayya irin ta WASU MATAN da kansu kawai suka sani a rayuwa.
Ta kama hannun Ahmad tana cewa "Muje Imaan kuci abincin Mamin taku tana kitchen in kuka huta se kuje gurinta".
Haka suka bita a baya suka shiga wani ɗaki dake bayan rumfunan, anan ma'aikata mata suke chanza kaya da sauran ajiye ajiyensu.
Abinci Isashshe Anty Iyami ta saka musu ba ɓata lokaci suka shiga ci, sai da suka cinye tas tareda kora ruwa mai sanyi harda zoɓo suka godewa Allah kafin Imaan ta miƙe tana kallon Ahmad daya kwanta saboda yanda jikinsa yayi laushi tace
"Tashi muyi sallah zaka wani kwanta kayi bacci" ya tura mata baki kafin ya miƙe suka nufi inda akeyin alwala. Bayan sun idar da sallah ta daɗe akan sallayar tana addu'a kafin ta buɗe inda Mamin take ajiye musu kayansu ta ɗauki wanda zata chanza. Sai da ta yiwa Ahmad takara akan kada ya kuskura ya fita ko ina sannan ta nufi kitchen gurin Mami.
Fara kyakkyawar Mace me cikar jiki wacce wahala bata boye waɗannan suffofin nata ba, da fara'a take kallon Imaan dake gaida sauran ma'aikatan gurin suna amsa mata sannan ta ƙarasa gurin da take tana cewa "Mami sannu da Aiki" ta faɗa tana ƙoƙarin karɓar magin da take ɓarewa se Mamin ta janye kwanon tana cewa
"Aa barshi ku da kuka kwaso gajiya, na kusa gamawama ai ya akayi yau kukayi Rana sosai?"
Shiru tayi tareda yamutsa fuska kawai alamar dai bazatace komai ba kafin ta matsa zuwa inda wasu keta aikin juye abinci a kuloli.
Da kallo Mami ta bita, tasan halinta sarai shirun nata na nufin wani abu ya faru amma ko menene ba zata faɗa mata ba. Tana kallonta ta kamawa matan dake juye abinci a kuloli har suka gama kafin ta fita can inda ake karɓar order tana kaiwa masu shi kamar yanda aikinta yake a kullum idan suka zo gurin wato karba da kuma delievering order abincin, duk yanda Mamin bata son hakan amma ta kance ba zata iya zama tana kallon Mamin na wahala ita kaɗai ba alhalin tana da halin taimaka mata.
A ranakun Alhamis da Juma'a babu Islamiyya dan haka daga makaranta kai tsaye tashar suke wucewa, haka Asabar da lahadi zata bita da safe sai azahar ta wuce Islamiyya daga can tunda shi Ahmad tun safe yake tafiya Tahfeez sai yamma suke tasowa tare.
Kamar kullum yau ma gurin ya cika maƙil da maza da mata masu siyan abinci matafiya da kuma mazauna cikin tashar. Ranta fes ganin yanda aketa siyan abincin da Maminta ta girka, tun bayan kama aikin Mamin a gurin wanda da farko aikin wanke wanke wata mata tayi mata hanya, sedai bata daɗe da farawa ba ta samu cigaba zuwa ɗaya daga cikin masu girki bayan da Anty Iyami mamallakiyar gurin ta tabbatar da ta iya girki ga kuma uwa uba kuma tsafta.
Yanda kasuwa ta sake buɗe mata dalilin canjin hannun girki da aka samu yasa take matuƙar ji da Mamin duk kuma yanda waɗanda ta tarar a gurin suke mata hassada se ya zama kamar wani sila na sake samun karɓuwarta. Watanni uku kenan da kama aikinta a gurin, kuma Alhamdulillah aikin ya kawo musu canji sosai a cikin rayuwarsu domin bayan kuɗin da ake biyanta ga abinci da zata ci har ta taho gida dashi domin Anty Iyamin macece mai kirki wacce kuma ta san darajar ɗan Adam tana matuƙar ƙoƙari akan ma'aikatan nata sosai.
Cike da nishaɗi Imaan ta ringa kaiwa da komowar rabon abincin fuskarta ɗauke da gajeran murmushin da Anty Iyami ta tursasa mata yi, a cewarta haba haba da customers ze ƙara jawo musu ciniki musamman da ta lura akwai waɗanda ma saboda Imaan ɗin suke zuwa gurin siyan abinci.
**********************
A hanya har sai da Baba ya gaji da yi masa magana,
"Ka rage gudun nan dan Allah Isuhu, Ba fa jirgi muka hau ba" a banza dan daya rage kamar wanda ake tsikara zai sake ware malejin motar.
Basu tsaya a Kaduna ba kamar yanda Baba ya faɗa masa tunda suka tashi, niyyar sa su fara tsayawa nan har su karya dan basu tsaya cin komai ba suka fito.
Gara Baban ma yasha kunu saboda zai sha magani amma haka Yusuf ya shamiƙe sai kawai Baba ganinsu yayi a Jaji dan ta bypass suka bi hankalinsa kuma yana kan wayarsa da yake duba wani abu sam bai zata Yusuf ɗin zai masa iya shege haka ba.
Sai a Zaria suka tsaya Baba yaci abinci shi dai Yusuf lemon power horse kawai ya karɓa kamar ma ƙyamar gurin abincin yakeyi dukda restaurant ne mai kyau shiyasa ma har y tsaya a nan kuma saboda Baba zai sha magani duk inda sha biyu tayi shiyasa ba yanda ya iya ya tsaya amma so yayi sai sun isa Kano tukunna suje guri mai kyau wanda ya yarda da tsaftarsu.
Sun isa Kano da wuri, ɗaya saura suka isa gidan Alhaji Manzo wanda yayi matuƙar jin daɗin zuwan Alhaji Ahmad ɗin. Basu jima ba saboda Baba ya ce a yau ɗin fa zasu koma kuma sai sun tsaya a Kaduna dan yana so ya duba wani tsohon yaronsa ne da yake kwance a Asibitin sojoji bashida lafiya.
Ko abinci da aka kawo musu basu ci ba, sallah kawai sukayi duk kuma azalzalar ta Yusuf ce, haka Baba ya biye masa suka sake kama hanya lokacin biyu ta wuce.
A tashar Unguwa Uku, Baba yace
"Dakatar. Mu shiga ciki."
Yusuf ya kalle shi, the look said it all. Mamaki yake toh mai zasuyi a tasha kuma ana zaune lafiya? Amma yanda shima Baban ya tsare gida ya saka dole yayi abinda ya buƙata suka shiga tashar.
Tiryan tiryan Baba ya kwatanta masa hanya har suka isa inda kallo ɗaya ya yiwa gurin ya fahimci gurin siyar da abinci ne
Ya ƙare masa kallo
"Are you for real?" Ya faɗa yana kallon Baba cikin mamaki da shakkun dalilin zuwansu gurin.
"Zuwan da nayi ɗaurin auren yar gidan Alhaji Zailani, ai na baka labarin tuwan da sukayi na ɗaurin aure. Naji daɗin miyar..... Shi ya kwatanta min a nan gurin suka kawo aikin abincin.
Ina ta so na sake cin irin ɗanɗanon sai yanzu Allah yasa na tuna dana ga tashar" Baba ya faɗa kafin kuma Yusuf ya iya cewa wani abu har ya ɓalle murfin motar ya fice.
Dole ya bishi.
Yana tafiya a hankali, cikin takatsantsan kamar wanda yake ƙoƙarin guje wa wani mugun abu da zai dame shi a gaba.
Like one wrong step could ruin everything...tasha fa.
Tashar ma irin wadda bata da wani banbanci da bola.
Kuma a nan ne Baba yace za su ci abinci?
He couldn’t believe it.
Binsa kawai yakeyi a baya yana raba ido tsakanin mutanen dake zirga-zirga da motocin dake ajiye a gurin. Everything felt... wrong. Tabbas akwai wani abu da yasa sam yaji tafiyar bata kwanta masa ba.
************************
"Addahn Ahmad, jeki can ki tambaye su mai suke buƙata"
Lami, ɗaya daga cikin ma’aikatan gurin, ta ce faɗa tana nuna wani dattijo da ke zaune a ɗaya daga cikin jerin kujerun zama.
Imaan ta tsaya daga gefe bayan data isa gurin ganin yana magana da wani saurayi, wanda sai da ta karasa kusa dasu kafin ta lura da tsaiwarsa akan mutumin.
Baba ya juyo ya kalleta bayan daya amsa sallamar da ta sake maimaitawa cikin siririyar muryarta,
Cike da ladabi ta gaida shi idonta a ƙasa, ba tareda ta kalli wanda suke taren ba shima ta gaida shi.
Baban ne kaɗai ya amsa yana ƙare mata kallo, duk inda ta fito ta samu tarbiyya, can ƙasan zuciyarsa kuma yana jin wani abu dangane da gurin daya ganta.
Ya cigaba da kallonta cike da yabawa yana nazarin da bai san dalilin yinsa akanta ba. Muryarta ta katse shi,
"Baba, me za a kawo maka?"
Ta tambaya da murmushi akan fuska.
Baba ya maido da martani cikin annuri ya ce
"Wani aminina ne ya kwatanta min wannan gurin.
Kwanaki, naci wani tuwo a gidansa ya matuƙar yi mun daɗi.
Ya tabbatar min daga nan ne aka kawo.
Tun lokacin nake son sake ci.
Yanzu har zamu wuce, amma na tuna sai nace ai sai na tsaya naci."
Ya ƙare da murmushi mai kyau.
Imaan ta dan saki ƙaramar dariya, not loud, but genuine.
Taji daɗi yanda babban mutum kamarsa ya zo takanas saboda tuwon data san Maminta ce ta girka shi, da alama ma ba a jahar nan yake ba kamar yanda taji yace wucewa zasuyi.
Muryarta ta sake, ba kamar da ba ta ce
"Toh Baba, guda nawa za a kawo? Kuma da wace miyar?"
"A sako daidai wanda zan iya cinyewa, kinsan cikin tsofaffi ba wani ɗauka da yawa yakeyi ba."
Sai ta ɗaga kai a hankali, first time ta kallin saurayin da ke gefen Baba tun tsayuwarta a gurin.
Ga mamakinta suna haɗa