Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
tana wani ɓata rai, Husna na bayanta itama ranta babu daɗi. Laure mai aikinsu na biye dasu da ƙaton basket da Mami ta jera musu abincin da ta dafa musu. Ganin Shahida a ƙasa tana kururuwa yasa suka ƙara sauri suka iso gurin. "Ke Imaan, me tayi miki da zaki mareta?" Husna ta faɗa tana kallon Imaan, wacce ta haɗe rai tana kallon gefe, fuska a ɗaure. Basu fiya shiga shirgin juna ba ita da Husna. Miskika ce, ba kuma ta da son hayaniya ko rashin ɗa'ar da suke yiwa Mami da wahala kaji bakinta a ciki, shiyasa ko yan uwan nata bata fiya jituwa dasu sosai ba saboda su ɗin wasu irin mutane ne da ko tsohuwar radio ba zata gaya musu hayaniya ba, sak kakarsu, ita kuma Husnan uwarsu ta biyo dukda a zahirance bata da mugun hali irin na mahaifiyar tasu. Wannan ɗan mutuncin dake tsakani ya saka ta mayar mata da amsa da cewa "Ahmad ta mara ba tareda yayi mata komai ba, nikuma na rama masa." "Dan uwarki saboda ta tari wannan shegen ƙanin naki me suffar yan ruwa, shine zaki mareta? Meye afaninku dama idan ba a dake ku ba?" Hasna ta taso kamar zata kai mata duka. Sheƙeƙe Imaan ta kalleta, da ita suka saba bugawa dama kuma kar tasan kar ne tsakaninsu. Tsayinta baya bata tsoro, banda kashedin Mami da idan ta mata abu duƙawa take ta kwashe ƙafafun yar banza ta watsar da ita a ƙasa, sai dai a sakata a injin markaɗe a niƙa. Damuwa da yanda ake sauke fushin akan Maminta ya saka dole ta koyi haƙuri da ɗauke kai akan abubuwa da yawa da sukeyi mata, amma banda akan Ahmad, ta faɗa ta sake nanatawa ko za'a saka kanta gabas a yanka ba zata zuba ido ya sha wahalar da suka sha ba. Gyara tsayuwa tayi ta fuskanceta dakyau ta ce "Me suffar yan ruwa tana cikin gida, amma ga babbar yar ruwan nan, wadda ta haifi irin masifa irin tsafi." Ta mayar da idonta kan Inno data taho zani a hannu, tamkar zata kifa saboda sauri. Tsohuwa ce, yanayinta kamar wacce aka ciro daga cartoon ɗin SpongeBob. Cikin wani yare mara fasali ta hau zagin Imaan ɗin tana ambato harda Mami ba tareda ta tambayi ba'asin abinda ya faru ba. Kallon cikin ido Imaan ɗin ta yi mata kafin ta ce "Duk abinda kike faɗa, da kanki da zuriyarki kike bamu ba. Kuma idan ba tsoro ba, ki faɗa da Hausa mana. Aikin kawai, mutum ya tsufa amma maimakon ya koma ga Allah, sai ƙara dulmiya yake a mugunta. Ramin ƙarya dai gajere ne, duk nisan jifa kuma ƙasa zai dawo dan haka, ki bi a sannu." Tana gama faɗar haka ta fizgi Ahmad suka shige mota. Tana jin kakar da jikokinta suna ta haushi tamkar karnukan da suka hango mugun abu, ma'aikatan gidan sunyi cirko cirko suna kallo sai dai babu damar tsoma baki, ta jingina kanta jikin window haɗi da lumshe ido zuciyarta na bugawa da sauri. Fatanta har ayi a gama kafa Mami ta fito, balle abinda tayi ya shafeta. Bata san me ya faru ba taji hayaniyar ta ɗauke gurin yayi shiru tamkar babu sauran mai rai. Ta buɗe idonta tana neman dalilin shirun nasu ganinta ya sauka akan mutumin data ƙi jinin ta buɗe ido ta gani a duniyarta. Baƙin bafulatani, kyakkyawa. A kallo ɗaya zaka hango kamanceceniyar da ke tsakaninsa da Ahmad, Al'amin, Shahida, har ma da ita kanta. Aliyu da Mami yake kama, su Hasna kuma da Hajiya Alawiyyah. Sanye yake da farar shadda mai ƙyalli, ƙamshin turarensa ya mamaye gurin. Siririn glass ɗin dake sanye a idonsa ya ƙara masa kwarjini. Akan Imaan ya sauke ganinsa, wani abu ya daki ƙirjinsa sai yayi saurin ɗauke idonsa ya kalli gefe dalilin zuciyarsa data hau bugun wuce ƙa'ida, idanuwansa suka ɗauki raɗaɗi tamkar an fesa masa ruwan barkono. Husna ya tambaya abinda ya faru, Hasna tayi caraf ya shiga zana masa ƙarya da gaskiya. Ya sake kallon inda Imaan ɗin ke zaune ta juya musu ƙeya, bai ji abinda yake ji idan suka haɗa ido ba, dan haka ya kira sunanta cikin kaushin murya. Bata ko motsa ba, tamkar ma bada ita yake ba, fushin da bai san daga inda ya taso masa ba ya mamaye zuciyarsa, ya buga mata tsawar da ba ita ba, hatta sauran da suke tsai-tsaye sai da suka shiga taitayinsu kafin ta sakko daga motar fuskarta na ƙoƙarin ɓoye razanar da tayi. "Ki bata haƙuri," ya nuna Inno, bayan daya janye ganinsa daga kanta. Inno ta gyara tsayuwa, ta zaro idanuwa yanda kasan kwarton da aka kama in action. Ba tareda Imaan ta kalle shi ba, tana ƙoƙarin danne kukan da yake neman kufce mata ta ce "Ni ban yi mata komai ba" "Shut up my friend, ni kike gayawa ba ki yi mata komai ba, ban isa na saka ki yi abu ba kenan?" Ya sake faɗa cikin fushi har yana ɗaga hannu kamar zai doketa. Ahmad ya ƙanƙameta ya fashe da kuka, haka Al'amin jikinsa tsuma yake ya riƙe hannun Shahida. Cikin kukan data kasa dannewa ta kalli Inno ta ce "Allah ya baki haƙuri, amma ka da ki sake shiga sabgata, kuma su ma ki gaya musu, duk wacce ta sake taɓa Ahmad wallahi sai na rama masa, duk abinda zai faru ya faru."Ta fizgi hannun Ahmad suka nufi get, kamar iska. Da ido Alhaji Arabi ya bisu har suka ɓacewa ganinsa. Ji yayi kamar ya taka da gudu ya ruƙo su, amma bashida wannan ƙwarin guiwar. Ya sauke numfashi mai nauyi kafin ya mayar da ganinsa kan sauran da duk suma shi suke kallo, musamman Inno, idanuwan nan kamar zasu faɗo ƙasa. "You all get into the car, kuma ka da ku kuskura a kawo mini rahoton kun yi rigima a school," ya faɗa strictly. Ba tare da gardama ba, suka shige motar. Su suka fara fita kafin motar Alhaji Arabi ta motsa. Inno, ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kamar wacce ta farka daga mummunan mafarki bayan data tabbatar sun fice daga gidan, sai ta juya kan ma'aikatan ta hau musu jaraba wai me suke kallo? Sai da kowa ya watse kafin ta wuce cikin gida tana waigen get kamar mai tsoron su dawo. A daidai junction inda Imaan da Ahmad ke tsaye suna jiran abin hawa tun fitarsu, suna tsaye motar su Hasna ta wuce, har Driver yayi slow down alamar zai tsaya sai kuma ya wuce da sauri da alama hana shi akayi. Baki ta taɓe ta rakasu da harara, dama ko sun tsaya ba hawa za ta yi ba, ba yau ba, bata zaton zata sake hawa wannan motar tasu har ƙarshen rayuwarta. Kai gidan gaba ɗaya ma ta daɗe tana burin su barshi dan dai Mami taƙi ne kawai amma ba yanda Aliyu bai yi, har inda zasu koma ya samo amma Mamin taƙi, ƙarshe tace ko bayan ranta bata yarda su bar cikin gidan mahaifinsu ba. Ta saki tsaki a karo na babu adadi, dama hanyar ba kasafai ake samun abun hawa ba, yawanci sai idan an ka taki sa'a wani ya kawo passenger ya fito, yanzu kuwa safiya ce, duk wanda suke fitowa a cike suke irin masu ɗauko yan makaranta ne babu guri. Ganin mota ta tsaya a gabansu ya saka ta ƙara haɗe fuska tana matsawa baya, Malam Habu ya sauke glass daga ɓangaren da suke tsaye, yana kallon Ahmad ya ce "Ƙaramin Alhaji, ku shigo mu ƙarasa kun makara." Da sauri Ahmad ya fisge hannunsa daga nata dan dama ya gaji da tsayuwa. Tun da suka fito yake mata mita akan cewa da sun tsaya, da yaga motar ta wuce ma kuka ya kusa yi yana cewa shi daya sani bai biyota ba. Gaban motar ya shige abinsa, ta zabura da niyyar janyoshi Alhajin ya buga mata tsawa. Hawaye ya ɓalle mata, haka ta buɗe gidan baya kusa dashi ta zauna haɗi da takure kanta tsakanin cinyoyinta ta fashe da kuka kamar wacce suka sace. Wata tsawar ya sake buga mata yana cewa ta yi masa shiru ko ya kwaɗa mata mari, shi kaɗai ya san mai yake ji a dalilin kusancinsu, tamkar yana tsaye gaban tukubar tsire haka ya ke jin wani tururi yana bugunsa, ga kuma kukanta dake barazanar tarwatsa masa kai shiyasa yayi mata tsawar, yanda ta zabura kuma cike da tsoro haka Ahmad sai ya sake motsa wani abu a cikin zuciyarsa. Shiru Imaan tayi ta dafe kanta da hannu biyu jikinta na karkarwa, memories ɗin baya suka shiga gilmawa a cikin kanta. Hotunan lokacin da Abbinsu yake kai su makaranta da kansa, ita da Yaya Aliyu. Lokacin da kullum safe sai ta yi kuka, wani lokacin har ta yi birgima a ƙasa kafin ya ɗauke ta ya saka a mota, yana lallashinta haka zai kaita har cikin ajinsu. Bata ɗaga kai ba sai da taji Malam Habu yana cewa sun iso makaranta. Ta share hawayen fuskarta da hijabin jikinta, kafin ta buɗe motar ta fita. Yau bata jira Ahmad ta rakashi primary section ba ta wuce gurinsu kawai. Sun makara sosai, ta san ganin wanda ya sauke su ne ma ya saka aka buɗe musu ƙofar kai tsaye. A ƙaramin get ɗin shiga secondary section, Imaan ta ci karo da Shahida. Jiran Imaan ɗin take yi dan ta ƙudure a ranta ba zata haƙura da marin da ta yi mata ba, Hasna ce ta zugata akan ta daina ragawa Imaan ɗin, yanda bata tsoronsu dukda sun girmeta haka itama kada ta raga mata tunda a girman jiki ma da me Imaan ɗin ta fita? Tunda Shahidan nada tsayin ƙafa irin yayyenta ba zakace shekararta goma ba. Hakan ya sa ta tsaya a gurin tana jiranta, Imaan bata lura da ita ba sai ji tayi an fincike guntun baby hijab ɗin da suke sakawa, ta shaƙe mata wuya, sannan ta hankaɗa ta ƙasa. Taji zafin faɗuwar da tayi, gurin ƙananan duwatsu ne a zube, da fuska ta tafi zata kife Allah ya taimakata ta dafe hannayenta, yanda abin yazo mata a bazata ya saka hannayen kasa riƙeta ta zube gaba ɗaya a gurin. Tana jin Shahidan da ƙawayenta da suka rakota suka fashe da dariya, baƙin cikin ya zame mata biyu sanda Hasna ta iso kanta ta ƙarasa fizge hijabin haɗi da ribbon ɗin data ɗaure tulin gashinta da sai da Mami tayi mata faɗa akan ta taje shi, kusan sati ɗaya kenan data kwance kitso take yawo da kan a haka, ashe rabon tasha kunya ya saka taƙi jin maganar Mamin. "Kan bala’i, lallai lokacin sake askin ki yayi yarinya dan baki isa mu da muke jinin buzaye ace kin fimu gashi ba" Hasnan ta faɗa tana ja mata gashi cike da mugunta, Imaan ba tayi wata wata ba ta wawuri ƙafarta sai gata itama warwas a ƙasa. Suka kacame da dambe, sai dai taron dangi ƙawayen Hasna da na Shahida suka yi mata ya saka suka kaita ƙasa. Sai da daƙyar wasu samari ‘yan ajinsu Hasna (SS3) suka shiga tsakani, suka raba su. Head boy ya tasa su kai tsaye zuwa admin block, inda suka samu malamai suna meeting. Daga ƙarshe, duka su ukun aka buga musu suspension letter. Imaan sati ɗaya, su kuma Hasna da Shahida indefinite suspension. Wannan ya faru ne saboda dama suna da disciplinary cases, musamman Hasna da aka sha samun ta da laifin bullying. Kamar yanda principal ta ce, alfarmar mahaifinsu ce ke sawa ake rufe case ɗin amma wannan karon dole sai an kira shi, tunda abin ya koma har a tsakaninsu. Bayan an musu dogon gargaɗi, suka watse zuwa classes ɗinsu. Shahida tana JSS1, Imaan SS2, su Hasna da Husna kuma SS3. Sa'anninsu a girma da shekaru suna Jami'a, saboda rashin fara makaranta da wuri da basu yi ba ga kuma ƙwaƙwalen nasu kamar anyi musu ciko da dusa ya saka duk yanda Hajiya Alawiyyah ta so da ayi musu tsallake abin yaƙi yuwuwa. Yanda principal ta ce idan dan ta grades ɗin su repeating zasu yi ta musu har sai an gaji an cire su daga makarantar gaba ɗaya. Ranar kuwa tasha zagi a gurin Inno, a cewarta duk uban turancin da yaran suka iya amma duk akayi jarabawa sai malaman sun zugo uban yazo yayi ta jaraba yana cewa suna sakashi asarar kuɗi, bayan ga manyan asarraru nan da suka rasa ta in da zasuyi su tunɓuke su daga makarantar. ----------------------------------- A can gida kuwa, bayan fitar su Imaan cikin sauri, Mami ta shiga ƙarasa ayyukan gida. Har ta dafa musu shinkafa, tayi wanka, ta haɗa duk abinda zata tafi dashi gurin aikinta Aliyu na zaune. Daga yanayinsa, ta fahimci yana cikin damuwa, amma ta share, ta hakan ne take saka ran zai rage nuna jin zafin mahaifinsu tunda ta sani duka su ukun basa son ɓacin ranta. Seda ta gama komai, ta shirya, kafin ta ce masa "Zan fita. Idan ka gama abinda kake yi, ka kulle ƙofar, ka ajiye key a ƙasan robar can waje." "Bana son aikin nan naki Mami" ya faɗa fuskarsa na bayyanar da abinda yake cikin zuciyarsa, sai tayi murmushi kawai, itama ba so takeyi ba, amma yaya zasuyi? Suna buƙatar abinda zai samar musu da abinci da abin buƙatun lalurorin tau da kullum, domin ba jin daɗi ko walwala take nema ba, rufin asiri kawai, ko yau ta samu wani aikin daya fi wannan nutsuwa zata bari domin babu abinda taƙi jini irin zaryar da yarinyarta takeyi a cikin tasha tsakanin maza. Harta kusa get ta tuna cewa ta yi mantuwa sai ta koma. A bakin ƙofa ta tsinci muryar Aliyun yana waya. Daga yadda yake magana, ta tabbatar Ibrahim ne, abokinsa guda ɗaya. "Nifa na haƙura, Ibrahim. Ka tafi kawai. Idan Allah ya kaimu wata shekarar, idan ina da rabo, zan sake nema." Ya faɗa. Shiru ya biyo baya, kafin ya sake cewa "Bana so nayi ta ɗorawa Mami damuwa, kawai idan an kwana biyu zan ce mata an rufe registration ɗin tuntuni bamu sani ba muke ta wahalar banza" sai ta tura ƙofar ta shiga, ganin ta ya saka ya kashe wayar da sauri yana miƙewa tsaye. Ɗaki ta wuce ta ɗakko haɗin kayan ƙamshin data manta, ba tareda ta kalle shi ba ta nufi ƙofa, sai ya bita yana shafa kai ya ce "Ibrahim ne Mami, kira yayi yaji ko na samu cikon kuɗin, yau ya kamata mu tafi saura kwana biyu a rufe registration ɗin." "Toh mai kake so kuma na ce Aliyu? Ka girma fa, ka isa yankewa kanka hukunci dama ni ai yar bada shawara ce, tunda kuma kaga baka buƙata, shikenan" ta faɗa kamar gaske tana haɗe fuska. Sai ya rikice ya riƙe hannunta tana cewa "Haba Mami, dan Allah ki dena wannan maganar" "Dagaske nakeyi Aliyu, ka manta wahalar da kuka sha kafin kuka samu damar nan sannan yanzu saboda wani dalilinka mara tushe zaka watsar da burinka na shekaru" ta sake faɗa. Ya runtse ido, tamkar lokacin abin yake faruwa yaji muryar Alhaji Arabi a ƙwaƙwalwarsa. "Idan ina raye lokacin ina kuma da dama nayi maka alƙawarin buɗe Airline company saboda kai, Arabi Airline" Abbin ya faɗa cikin raha a lokacin da yake ce masa shi pilot yake son zama idan ya girma. Ranar daya kammala secondary school kuma haka ya sake kallonsa ya gaya masa maganar data ɓarar da duk wani sauran uzuri da yake yi masa. Ya kasa manta yanda mutumin ya kalleshi ya ce masa ya sallame shi. Bai fahimci ma'anar maganar ba sai da matarsa tayi masa fashin baƙi da cewa "Iya kar abinda ze muku kenan, ya biya maka ka yi primary da secondary, ganin damarka ka nema ka cigaba, ko ka cigaba da shaye-shaye da iskancin da kakeyi, ba zai yi asarar kuɗinsa akan abinda ba zai amfane shi ba." Ya ringa kallon mahaifin nasu ko zai tsawatar mata, ko ya faɗi wata magana akasin wacce ita ta faɗa sai dai bai ko kalle shi ba ya ce ya tashi ya bashi guri. Tun daga wannan rana ya saka a ransa shi marayane, tun sannan yake fafutuka, baya fatan lokacin da zai sallami Imaan da Ahmad yayi ba tareda ya samu abinda zai cigaba da ɗaukar ɗawainiyar karatunsu ba. Page 8 Tun daga wannan rana ya saka a ransa shi marayane, tun kuma sannan ya ke fafutuka, baya fatan lokacin da zai sallami Imaan da Ahmad yayi ba tareda ya samu abinda zai cigaba da ɗaukar ɗawainiyar karatunsu ba. Da fari ya ce zai haƙura da karatu ne ya nemi sana'a amma taƙi, ta ce ya haɗa duka, ya haƙura da burinsa tunda bashi da mai tsaya masa ya yi karatun. Bisa shawarar Ibrahim suka shiga polytechnic har kuma sun kammala HND yanzu, kamar wasa kuma wannan shekarar Baban Ibrahim ɗin ta hanyar wani tsohon abokinsa ya nema musu collage of aviation ɗin da suke buri, suka samu half scholarship, sai dai rashin samun cikon tuition fee ɗin yana neman ya sanya damar ta sake kufce masa. Karatu ne mai tsada, a lokacin daya ɗarsa burin bai taɓa hasaso wata rana irin haka zata zo da Abbin zai kasa tsaya masa ba. Ƙasar waje ya ce zai kai shi yayi karatunsa acan, sai gashi komai ya canza, ikon Allah ne kaɗai ya saka ya cigaba da biya masa kuɗin makaranta har ya kammala yake kuma biyan na su Imaan har yanzu. Kallon sa Mami ta yi. Ko da ya yi shiru, tasan abinda yake tunawa. Duk sanda maganar karatunsa ta taso wannan baƙin cikin yakan tsaya mata a zuciya itama, shi ya sa kullum addu’a da fatanta ubangiji ya shirya mata yaranta, ya kuma ƙarfafa ta wajen ɗaukar nauyinsu har su kai matakin da ba a zata ba. Idan ta duba ni’imar da Allah ya yi mata, ya killace mata yaranta duk abinda yake faruwa babu mummunan tasiri da abin yayi akansu, sai ta ji cewa rasa jin daɗin aurenta da mijinta ba komai bane idan aka gwada da wannan ni'ima. "Shikenan ai, Allah ya kaimu baɗin, idan da rabo lokacin, sai ka tafi. Amma ka sani ubangiji yana bawa mutum dama da lokaci, idan bai yi amfani dasu dakyau ba, babu lallai ya sake samun kamarsu. Sai ka kwashe kuɗin idan kun haɗu ka mayar masa ka gaya masa baka buƙata." Ƙarara ɓacin rai ya bayyana cikin muryarta har ma da kan fuskarta, ta wuce, sai ya yi saurin sake ruƙo hannunta yana cewa "Cewa fa ya yi ya sallameni Mami, mai yasa yanzu zanyi amfani da kuɗinsa? Idan ya dawo ya yi mini gori akan hakan fa? Ranar da wata buƙatar irin haka ta taso ban samu ba ya zanyi? Hakurin dai zanyi Mami, gara na saba tun yanzu". "Bana son maimaita magana Aliyu, kayi duk yanda kaga ya maka. Tunda ban isa in faɗa maka magana kaji ba, da wanne kake so naji? Halin dana tsinci kaina ko kuma taurin kanka?" ta faɗa tana fizgewa daga ruƙo da ya yi mata, muryarta tana karyewa. Sai ya saketa da sauri ya ɗaga cushion ɗin ya ɗebo kuɗin yana cewa "Dan Allah kada ki zubar da hawayenki Mami, zanyi amfani dasu amma bashi. In sha Allahu da zarar na samu dama zan mayar masa da kuɗinsa." Dariya ya bata ta murmusa tana buɗe jakarta, kuɗin da mutumin jiya ya bawa su Ahmad ta zaro ta miƙa masa tana cewa "Ga wasu ma ka ƙara, kayi maza ka shirya ku tafi, Allah ya bada sa'a ya tsare ku a duk in da zaku shiga." Bai karɓi kuɗin ba ya ce "A kansu aka marar mun ƙanwa ko? Ko wanene ina fatan Allah ya gwada mini shi sai na nuna masa kuskuren daya tafka. Waɗannan ma sun isa Mami, idan na canza su, zasu isheni nayi komai har in samu rara, ba zama zanyi ba idan naje Zari'a Mami, i will look for business opportunities, zan nemi abinda zan cigaba da riƙe karatuna kema na hutar dake daga wannan wahalar da kikeyi, kafin daɗi yazo. Idan na fara tuƙa jirgi Mami zakiji daɗi in sha Allah" ya faɗa yana rungumeta. Ta san Ahmad ne ya bashi labarin abinda ya faru a tashar jiya, wani abu mai nauyi ya danne mata zuciya, amma bata bari yayi tasiri ba ta yi murmushi bayan data janye Aliyun tana ce masa ya makarar da ita, yayi maza shima ya shirya ta fice yana mata a dawo lafiya.. Abuja, Nigeria. Hajiya Hadiza tana kishingiɗe akan katafaren gadonta da yasha shimfiɗa ta alfarma tamkar gadon sarauniya. Tun tafiyar su Yusuf ta hau saman, bata sauka ba, duk da sau biyu Talatu, amintacciya kuma mafi daɗewa cikin masu aikin gidan, ta hau saman ta ce mata akwai baƙi. Babu wanda ta gani a ciki, ce mata ta yi "Please, ki ce musu I’m not available, duk ma wanda ya zo yau, kawai bana nan." Bata gane exactly me ke damunta ba, amma zuciyarta ta yi nauyi, jikinta kuma kamar zazzaɓi zai rufeta. Sanyi take ji, irin sanyi mai tasowa daga cikin jiki, ta sa aka kashe AC, aka sauke mata labulaye, ta kwanta, ta lulluɓe da bargo, amma dukda haka ta bata gane kanta ba. Tun fitarsu take a hakan, breakfast ma sai da Talatu ta matsa mata sannan ta tsakuri abincin bayan tayi sallar azahar, tun da ta gama kuma ta sake kishingiɗa, idonta na kaiwa ga agogo lokaci-lokaci kamar mai jiran wani specific moment. Bugawar agogo dake alamta ƙarfe biyu tayi dai-dai da bugu mai ƙarfi da zuciyarta ta yi, har sai da ta tashi zaune, ta dafe ƙirjinta tana fitar da numfashi da sauri. Ta lalubi wayarta, sai dai hannayenta su ka yi nauyi kamar akwai wani invisible force da ya hana ta danna kiran da tayi niyya. Bayan kusan awa guda cikin wannan restless state, wayarta ta yi ƙara. Ganin number ɗin da ta bayyana, jikinta ya ɗauki rawa, zuciyarta ta sake bugawa fiye da na farko. Bata amsa kiran ba sai daya katse wani ya sake shigowa. Muryarsa ta ratsa kunnenta. Bata amsa gaisuwar da yake mata ba, ta ce "I'm listening" Tana magana, ta miƙe tsaye, ta nufi window, ta yaye labule. Wani irin sanyi ya ratsa ta daga ƙafa har zuwa kai, hannunta da ke riƙe da wayar ya ɗauki rawa. Bayan kusan minti biyu tana kokawa da numfashinta kafin murya a ƙasa ta ce "Yusuf…Yusuf ɗina fa?" "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Shikenan" ta sake faɗa tana sauke wayar daga kunnenta. Abinda mai kira ya faɗa mata, Jini yana zuba sosai a jikinsa, akwai manyan raunuka, there is low chance of survival, idan kuma ya rayu, da wahala ya sake moruwa. Sai ta sulale a gurin ta zauna tana nanata Hasbunallahu wani'imal wakeel. Sai dai a ƙasan wannan firgicewar, wani tunani mai nauyi ya ɗarsu a ranta, kuma nan take ƙwaƙwalwarta ta ɗauke ta zuwa safiyar yau ɗin. Lokacin da za su tafi, sanda Barr Salahuddeen ya shiga cikin maganar da suke yi tamkar wanda ya ke da wani shiri a zuciya "Amma da tun jiya ya kamata ya faɗa cewa da ita za a tafi, so that a yi checking, a tabbatar babu wata matsala" Ta tuna kuma yadda Yusuf ya kalle shi da irin wannan look ɗin nasa da wasu suke fassarawa da na raini, but she knows him. Ta ɗauka na ɓacin rai ne, ya tsoma masa baki cikin magana, ɗaya daga ɗabi'un da yake yawan complain akan Barr. Yana cewa ya fiya shiga hurumin da babu ruwansa, musamman da ya kasance yafi tsoma baki ne a lamuran da suka ci karo da ra'ayin Yusuf ɗin, yaƙi jinin haka matuƙa. Ta girgiza kai da sauri, tana ƙoƙarin korar mugun tunani, "Ba dai Barr Salahu ba… if there’s any conspiracy, it can’t be him." Ta bawa kanta tabbaci. Sai ta miƙe, sanda Talatu ta turo ƙofar ɗakin ta shiga ba tareda knocking ba, fuskarta cike da firgici. "Barr ne, yana ƙasa, wai ya ce..." sai kuma ta kasa ƙarasawa. Hajiya Hadiza ta katse ta "Bayan ke, sai waye ya san wannan maganar?" Talatu ta ce "A nan ciki ni kaɗai ya sanar, ban san ko ya yi magana da wani a waje ba." Da hannu ta yi mata alamar ta tafi, sannan ta ɗan jira kusan minti goma kafin ta fita daga ɗakin tana komawa da fuskarta kamar babu abin da ya faru. A ƙasa, Barr Salahuddeen yana ganinta ya miƙe, ba yabo ba fallasa ta isa in da yake tsaye "Alhaji ya kira ni. He’s fine, nothing happened to him. Amma Yusuf…sai

Chapter 5 of 7