Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
ido, sai ya banka mata harara. Yanda yayi sai ka ɗauka wata tsohuwar gaba ce a tsakaninsu ba wai yau ɗin suka fara haɗuwa ba, to me tayi masa kuma? Page 4 Ga mamakinta suna haɗa ido, sai ya banka mata harara. Yanda yayi sai ka ɗauka wata tsohuwar gaba ce a tsakaninsu ba wai yau ɗin suka fara haɗuwa ba, to me tayi masa kuma? Bata da mai bata amsa dan haka ta mayar masa da martanin hararar data fi wacce yayi mata zafi, ai bashi kaɗai yake da idanuwan tsorata mutane ba. Yanda ya buɗe ido haɗi da ɗage gira abinda ta fassara da "For real?" Sai ta ɗauke kai da sauri, ta juyar da fuska kamar bata aikata komai ba. Ai shi ya fara dama. Tana ji Baba ya tambayeshi "Sai ka gaya mata abinda zaka ci, kaima." Yana kallon Yusuf. Yanda ya tsaya masa a kai yana muzurai sai ka ɗauka aiki aka daukeshi saboda hakan ana biyansa albashi. "Ni bana cin komai." Ya faɗa kamar ƙaramin yaro da aka hana chocolate. Sannan cikin hasala ya ƙara da cewa "Amma dai... da ka haƙura mu tafi restaurant, Baba. Wane irin tuwo ne ba za ka samu a can ba? Kalli gurin fa... dan Allah! Yanzu ko dan saboda lafiyarka ma ya kamata ka ci abu daga irin wannan guri? Bafa ba ka san waɗanne ƙazamai ne suka dafa abincin ba..." Baba ya ɗaga masa hannu yana cewa "Shikenan. Tunda ba zaka ci ba, I no get energy for long talk today, Sarkin tsafta." Sannan ya juyo ya kalli Imaan, wadda ta kafe Yusuf da ido ɓacin rai ya bayyana ƙarara akan fuskarta. Ƙazamai? Did he just insult Mami too...? Ji take kamar ta kwaɗa masa mari. Cikin lallashi Baba ya ce mata "Rabu da shi. Jeki kawo min tuwon, kinji." Imaan ta ja ƙaramin tsaki, kallaon da Yusuf yayi mata kuma ya tabbatar mata da yaji. Dama saboda shi tayi, taji daɗi da yaji. Ƙwafa ta sakeyi duk akan idonsa ta wuce, a ranta tana ayyana abinda zatayi masa ta huce haushin ƙazamai daya kira su Maminta kafin ya bar gurin. "Wallahi I’ll deal with you before you leave here, Mr." Da kanta ta zuba masa abincin. Ta saka Miyar taushe wadda taji tantaƙwashi. Ita ire-irensa suke siya, daban ake yinta ma dan yawanci masu aikowa daga waje siyan abincin ake sakawa ba regular customers ba sai kuma wanda kuɗinsa ya kai ya ci. Ta zuba miyar kuka ita ɗin ma ta musamman. A try ta jera komai VIP customer style kafin ta ɗauki ruwa, ta ƙara da robar zoɓo roba biyu dukda bata da tabbacin wancan mutumin zai barshi yasha. Mami ce take yin zoɓon ta kawo nan bisa sahalewar Anty Iyami, A sace ta galla masa harara, ƙazamai daya kirasu yayi mata zafi ainun, kafin ta ajiye kayan hannunta gaban Baba tana sakin murmushi ta ce "Baba, ga abincin. Ban tambaye ka abin sha ba amma ga zoɓo nan. Ban sani ba ko kana sha. Babu sugar a ciki." Baba ya ɗauki zoɓon da murmushi "Sannu. Nagode ƙwarai. Kamar kuwa kin sani ina matuƙar son zoɓo." Yusuf ya kalli Baba da mamaki, yana ce "Baba... fisabilillah, abincin bai isheka ba sai ka haɗa da zoɓo? Do you even know what they put inside?? Allah kaɗai yasan wace irin masifa suke ɗurawa a cikin irin waɗannan abubuwan..." Baba ya katseshi da sauri "Bazamu ga masifa ba bi’iznillahi ta’ala." Ya kai zobon bakinsa bayan ya ce " "Bismillah." Tas ya shanye robar farko, Imaan tayi mamaki, not just for the fact that Baba drank it… Amma yanda ya shanye kai tsaye babu wata damuwa ga kuma annuri da kuma gamsuwar da fuskarsa ta nuna tabbas yayi masa daɗi, Data kalli Yusuf ɗin sai taji kamar ta kwashe da dariya. Yanda yake kallon Baban idanuwa a zare, cike da tsoro sai ka ɗauka yaga Baban ya shanye robar sniper ne. Hakan kuma ya mata daɗi matuƙa, sai ya haɗiyi zuciya ya mutu Babansa yaci abinda ya fito daga hannun ƙazamai. "Zuba min ruwa, na wanke hannuna," Baba ya ce, yana kallon Yusuf wanda ya haɗe fuska kamar hadari yana muzurai. Ganin da tayi bashida alamar yin abinda Baban ya buƙata yasa ta zuba masa ruwa. Bayan ya gama, ya kalleta ya ce "Allah ya yi miki albarka, yata." A bazata furucin yazo mata, kamar saukar ruwan sama. Bata iya tuna tsayin lokaci rabon da ta ji makamancin wannan kalmar daga bakin namiji, babba bayan Abbo da Maminta sai yau a bakin Dattijon nan. Sai taji furucin tamkar daga bakin Dadynta, wani irin daɗi da annuri suka ratsata. Barin gurin tayi tana waiwayen Baba daya saka hannu ya fara cin tuwon hankali kwance har yana lumshe ido, alamar daɗi da garɗin miyar taushen da yake ci yana ratsashi. Sai da yaci malmala biyu, ya yi hamdala, ya kalli Yusuf dake tsaye kamar an dasa shi ya ce "Wallahi, idan baka ci abincin nan ba, ka bar daɗi Isuhu. Kiramun yarinyar nan tayi packaging wani nayi guzuri. Gaskiyar Alhaji Sammani kenan, ya ce tunda ya fara cin tuwon gurin nan babu wata miya da take masa daɗi bayan tasu. Kira min yarinyar mu bata kuɗin mu wuce, lokaci yana tafiya " Yusuf dai kallon Baban yake cikin wani yanayi, maganar Baban ta saka fuskarsa ta canza daga mamaki zuwa tsoro. Ashe gaskiyar Mom ne da tace masu abincin siyarwa suna amfani da sihiri su kama mutane, ta yanda idan ka fara cin abinci a wajensu ba zaka iya dainawa ba? Tun yana yaro take yawan maimaita masa haka. Ya tashi ya tarar duk wani abu da zasu ci Mom ce take girkawa da kanta duk kuwa tarin ma'aikatan da suke gidan wanda wani lokacin har mamakin dalilin ajiye su yakeyi in har zata ringa yin ayyukanta da kanta. Idan Baba yana gari ko zai raba dare a office zata aika masa da abinci can, duk wani abu da mutum zai gani a waje yayi kwaɗayi Mom tana yi musu har kawo yanzu bata fasa ba. Shiyasa ya sha wahala sosai tafiyarsa boarding School saboda rashin sabo da abincin da bana gida ba, dalilin kuma daya saka ya koyi girki bayan daya tafi UK kenan dan baya taɓa sakewa yaci abinci da kyau duk kuwa tsaruwa ko kyawun gurin abinci sai dai yaci saboda lalura kawai ba dan hakan ya masa ba. "Matsamun daga kai, ana magana ka kafe mutane da idanuwa kamar na kuliya, sai kace sabon shigar kurmanta." Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke yana ja baya kaɗan, hangen ta inda zai ganota ya shigayi amma babu alamarta. Ya juya da niyyar cewa Baba a kira wata mana tunda ga ma'aikatan nan da yawa ba lallai sai ita ba amma yaga babu Baba a gurin. Zuciyarsa tayi tsalle, kafin ta kai ga direwa ƙasa ta tarwatse ya hango Baban a can gefe kusada wani Famfo tareda Yarinyar data kawo abincin da kuma wani ƙaramin yaro tana wanke masa fuska. Ƙirjinsa ya shafa, kamar mai lallashin kansa kafin ya fara takawa a hankali ya doshi gurin. "Nawa ne kuɗin abincin?" ya tsinci muryar Baba yana tambayarta. Sai yaji kamar ya kwaɗa mata mari yanda ta tsaya tana wani lissafi da yatsun hannunta kafin ta ce "Gaba ɗaya 2500 ne Baba." Cikin sigar zolaya Baba ya ce "Wai yanzu har naci 2500 a ɗan zaman nan nawa?" Imaan ta ɗan yi shiru. Yanayinsa ya saka bata tsaya tambayar na nawa za'a zaka masa ba kawai tayi gaban kanta ta zuba. Tuwo da miya ko na nawa mutum yake so akwai a gurin, har tuwon masara, wata miyar ma kamar an wanke kai, iya kuɗinka iya shagalinka. Ganinsa babban mutum ya saka ta kawo masa na musamman irin wanda akeyi saboda sarakai da attajirai da suke aikowa a siya musu. "Toh Baba, ka bada dubu biyu, zoɓon na Mamina ne. Sai nace mata na baka kyauta." Baba ya saki dariya "Na gode ƙwarai, yata. Amma baki gaya mun sunanki ba." Ya zaro kuɗi daga aljihunsa Yusuf ya rigashi miƙa mata kuɗin da shi kansa bai san nawa bane, zaro su kawai yayi. “Baba, muje. Kasan tafiya ce a gabanku ga abu muhimmanci yana jiranka kuma muna bata lokaci a nan." Kallo ɗaya ta yiwa hannunsa ta ɗauke kai ba tareda ta karɓi kuɗin da yake miƙa mata ba. Baba ne ya cire dubu biyar ya bata yana cewa "Gashi nan. Ki ƙara saka min tuwon kamar wanda naci a pack, harda zoɓo. Ta karɓa da hannu biyu, ta juya ciki. Babu jimawa ta fito da ledar kayan abinci, da chanjin ɗari biyar a hannunta. A gurin da ya ci abincin ta tarar dashi tareda Ahmad yana cin sauran malmalar tuwon da Baban bai cinye ba. Ta balla masa harara, ba shiri ya tsame hannunsa daga abincin. Baba ne ya jashi ya kuma ce masa ya ci dukda Ahmad ɗin ya ce ya ƙoshi kuma Mami ma zatayi masa faɗa idan taji wani mutum ya bashi abinci yaci "Addah Imaan dukana ma zatayi in dai naci, kuma ni na ƙoshi ma, mun ci abinci da muka dawo daga school" Ahmad ɗin ya faɗa masa. Sai Baban ya ce "Mami ba zatayi faɗa ba idan kace mata Baba ne ya ce ka ci, Addah Imaan ma ba zata doke ka, ita ta kawo min abincin". Haka ya ringa jansa har ya yarda ya fara cin to tuwon. Yusuf kuwa dama mota ya wuce ganin Baban ya sake neman guri ya zauna. A ransa ya ringa ji, ko dai ya kira Mom ya gaya mata abinda yake faruwa ne? Amma kuma ya san halinta, yanzu zata tashi hankalinta, zama ta iya cewa zata kamo hanya ta taho. Wannan tunanin ya saka ya fasa kiran Mom ɗin, yayi bakam a cikin mota yana hango Baban da suke ta surutu da yaron tamkar sun daɗe da sanin juna. "Ya zaki harare shi haka? So kike ki firgita min aboki?" Baba ya faɗa fuska a sake yana miƙewa tsaye. Tana riƙe da ledar abincin ta ce "Ga abincin Baba" "Muje ki rakani mota toh." Ya faɗa yana kama hannun Ahmad. Jin bata biyo bayansu ba ya saka ya waiga yana sake ce mata "Kinji?" Bin bayansu zuciyarta na bugawa. Baba bai yi kama da mugu ba ko kaɗan. Dukda har cikin ranta ta yarda da shi sai dai ta san, ko da tunaninta ya banbanta da zahirinsa, gurin da suke tsaro da yawan jama’a ba zai bar su cikin haɗari ba. Wannan tunanin ne ya ba ta ƙwarin gwiwar rakashi har can gaban mota. Motar tayi mata kyau, ita ɗin tana son ƙyale-ƙyale da abubuwa masu kyau. A fusace Yusuf ya sakko ya buɗe ƙofar bayan motar, kafin ya amshe abincin daga hannunta ya saka a ciki ba tare da ya ce komai ba ya rufe. Ita dai ta bishi da kallo a ranta tana ayyana "Ikon Allah, shi kuma da alama cutar fushi gare shi". Matsawa tayi gaba, inda Baba ya zauna ta miƙa masa canjin kuɗi. "Allah ya tsare hanya." Ta faɗa "Amin, Addahn Ahmad. Ungo nan ki kai wa Mami, ta ƙara jarin zoɓo." Baba ya amsa. Ya miƙa mata bundle ɗin 1k notes sababbi. Ta girgiza kai da sauri "Aa Baba, kabarshi... ga chanji ma baka karɓa ba." Ta sake miƙa masa ɗari biyar ɗin hannunta. "In dai har na kai matsayin Baban da kike kirana dashi...To, ki karɓa." Yanda yayi maganar babu wasa, ya kuma toshe hanyar da zata cigaba da yi masa gardama. Sai ta sauke numfashi, a hankali kamar zatayi kuka ta ce "Mami zata yi faɗa..." "Addah ki karɓa fa, kinga sai mu ringa hawa mota idan Addah Hasna ta hana mu..." Ahmad yayi tsagal ya shiga maganar, sai dai bata bashi damar kaiwa ƙarshe ba ta katse shi ta hanyar doke masa baki. Da ƙarfi ta make masa bakin, yaji zafi take kuma gurin ya tsage shi kuma ya fashe da kuka. Niyyar sake balbale shi da masifa tayi, sai dai saukar marin da bata san daga in da ya taho ba ya katse mata hanzari. Tayi wuri-wuri da ido, azabar raɗaɗi har ƙwaƙwalwarta, haka idanta na ɓangare da aka mara tamkar tayi kwalli da barkono. Suna yin ido huɗu da Yusuf dake tsaye gabanta yana huci kamar shi aka mara ta fahimci shi yayi mata wannan aika-aikar. Ta zuba masa ido, shock ne kawai ya hana ta yin ihu. Da farko so tayi ta kware baki ta kurma ihu ko hakan zai sassauta mata abinda take ji, sai dai ganinsa ya saka ta daure, amma ta kasa. Raɗaɗi is unbearable, kamar da ƙarfe ya mareta ba wai fatar hannu ba, sai ta fashe da kuka. Muryar Baba ce ta katse shirun da sukayi "Wannan wane irin rashin hankaline, Yusuf? Me tayi maka? Sau nawa zan maka magana akan saurin hannu?" Har ga Allah ba iya marin ya saka ta kuka ba. Wulaƙanci, a gaban mutane. Ya mareta babu laifin tsaye babu na zaune. Gashi har mutane sun fara taruwa suna kallonsu. Ta rufe fuska da hannu biyu, ta kasa tare hawayen da suke tuttuɗowa daga idonta. Juyawa tayi ta bar gurin da sauri ba tareda ta saurari kiran da Baba yake mata ba. Cikin faɗan da ba kowa ya san Baba dashi ba ya kalle shi ya ce "Ka kyauta, Yusuf. Ni da na kawoka, ni ya kamata ka mara ba ita ba. "Baba, baka gani ba? akan me zata doki yaro? Because the boy said the truth? Idan na munafunci ba mai ya kawo mace kamarta aiki a nan idan basa buƙatar taimako? Shikenan saboda yaro ya faɗi gaskiya ta dokesa? Ta fasa masa baki?" Yanda yake magana zaka fahimci tsantsar jin haushi da zafi akan abinda Imaan ɗin tayi. Ya ɗago fuskar Ahmad da tunda aka mari Imaan ya daina nasan kukan duk ya diririce. "Kalli bakinsa har ya kumbura" ya sake faɗa yana nunawa Baba leɓe Ahmad daya tashi. A fusace Baba ya fizge Ahmad ɗin daga hannunsa yana cewa "Ina ruwanka? Ba ta fika kusanci dashi ba?" Ya koma gurin abincin ya bar Yusuf a tsaye kamar zaiyi bindiga saboda fushi. Bayanta ma Baba zai goya kenan? A hanya suka ci karo da Mami data fito hankali tashe saboda kiran da aka mata wai tazo ana faɗa da Imaan, tsabar gulma irinta mai kai mata rahoton. Kallo ɗaya Baba ya mata ya gane itace mahaifiyarsu saboda fuskar Ahmad ɗin daya gani a tata. Baba ya shiga bata haƙuri tun kafin ta yi magana. Dukda bata fahimci abinda ya faru ba amma ta samu nutsuwa. Imaan ba zatayi faɗa da wannan mutumin ba, koma menene kuma ya faru ba laifinta bane tunda gashi yana cewa ayi haƙuri. ******* Tunda suka hau hanya, Baba bai yi shiru ba, faɗa yake surfawa Yusuf ta inda ya shiga bata nan yake fita ba. Kamar kurma kuma haka yayi masa shiru. Tuƙinsa ne kawai ke nuna cewa ransa a ɓace yake. Gudu yake tamkar zasu tashi sama, baya ko duba cewa a cikin gari suke har sannan, kuma inda suke dosa akwai yawaitar motoci da mutane domin tasha ce a gurin. Cikin tsautsayi a dai-dai kwanar Dawaki, A ƙoƙarin kaucewa wasu mata da zasu tsallaka titi, daga can nesa suka hango motar sai dai kafin sukai tsakiyar titin har ya cimmasu hakan ya rikita su suka koma shi kuma a ƙoƙarin riƙe motar kada ya taɓa su burki ya ƙwace masa. Motar taƙi ruƙuwa, haka ya faɗa kan wata tirela dake aje gefen titi. Gaban motar ya lotse, ƙarar fashewar wani abu ta yi dai-dai da ƙarar karyewar ƙasusuwansa da hatta Baba zai iya cewa yaji, ya fasa ƙara mai gigita haɗi da salati, kafin duhu ya mamaye shi daga nan kuma bai ƙara sanin inda yake ba, a raye ko a mace. Page 5 Ƙarfe bakwai saura lokacin da Imaan da mahaifiyarsu suka bar tasha. Six o'clock ne lokacin da Mamin take tashi daga bakin aiki, akwai waɗanda suke wuce haka harda ma masu kwana a gurin. Yau kuwa ranar biyan albashi ce, duk da a lissafi akwai sauran kwanaki huɗu kafin wata ya ƙare sai dai basu san dalilin daya saka Anty Iyami biyansu a wannan ranar ba. Matar tasha banban da sauran takwarorinta a ɓangaren kulawa da ma'aikatanta, lamarin da ya jawo musu tsaiko kenan kafin a sallameta har lokacin sallar magariba yayi. Fuskar Imaan a ɗinke da fushi, ga shatin yatsar Yusuf da suka samu guri suka kwanta raɗau a fuskarta tamkar an buga stamp. A clear evidence cewa ta maru sosai. Da ƙyar Mami ta samu ta lallasheta har ta dakata da kuka, zuciyarta cike da tambayoyi Wanene ya marar mata yarinya? Me kuma Imaan ɗin tayi masa da yayi zafi da har ya ɗauki wannan matakin? Imaan nada fushi, ko kuma tace abubuwan da suka faru sun canza mata yarinya daga mai walwala da yawan fara'a zuwa shiru-shiru mai saurin hasala da fushi. Dukda haka Imaan ba ma'abociyar faɗa bace haka kawai da mutane, balle maza, kuma bata da tsokana balle ace ta takali wani da zai iya ɗaga hannu ya mareta. Aikin da take tsaka dayi yasa koda taga lafiyarta ta tabbatar kuma da wani mugun abu bane ya faru da ita, bayan ta lallasheta ta barta ta koma bakin aikinta, ta bari idan sun koma gida, zata binciketa taji cikakken bayanin abinda ya faru. Daga can nesa mai Adaidaita Sahun da ya ɗauko su ya tsaya kamar yanda Mamin ta umarceshi. Bayan ta sallame shi cikin fargabar data zame mata jiki suka doshi gate ɗin gidan. Kamar mai tsoron wani ya gansu ta tura ƙofar da aka bari a buɗe suka shiga yaran na biye da ita a baya. Wani matashin buzu dake zaune kan benchi ya taso da sauri bayan daya kalli cikin katafaren compound ɗin gidan ya tabbatar da babu wanda yake kallonsa kafin ya nufesu yana musu sannu da zuwa cikin ladabi ya ce "Sannu da zuwa Hajiya" yana ƙoƙarin karɓar ledar da ke hannun Imaan, amma ta ƙi sakar masa, sai ya juya, ya ɗauki Ahmad da jakarsa, ya wuce dashi ciki yana tafiya da sauri. Sai da sukayi yar tafiya, suka wuce ɓangarori biyu da aka gina su cikin tsari mai kyau da burgewa. Daga gefen chalet, inda ɗakunan ma'aikatan gidan suke suka shiga wani guri da aka zagaye da langa-langa, Mami ta zaro key daga cikin jaka ta buɗe. Nan ne buzun da ke ɗauke da Ahmad ya tsaya, ya rusuna cikin ladabi, yana sake yi musu sannu da zuwa tare da sallama, sai ya juya da hanzari ya koma bakin aikinsa. Falo ne mai ɗauke da ɗakin bacci guda ɗaya sai bandaki da yake a cikin falon. Babu wasu tarkace, kujera 3-sitter ce guda ɗaya, sai carpet dake malale tsakiyar falon sai ƙaramin fridge, da ganin kayan tarkace ne irin wanda aka daina amfani da su. Cikin ɗakin ma Katifa ce irin gado huta ɗin nan, sai wardrobe ta jikin bango, sai kuma wani ɗan Table da Mami ta saka kafinta ya buga mata suke ajiye tarkacen kayan shafa akai da kuma mudubi data manna a jikin bango. Kai tsaye Imaan ta shige uwar ɗaki, Ahmad kuwa nan tsakiyar falon ya aje jakar makarantarsa ya shiga tsalle tareda kiran fitsari. Wanka Mamin ta haɗa tayi masa a gurguje bayan da yayi fitsarin, Imaan is visibly upse. Idan ta ce tayi masa wanka ta sani a kansa zata huce rabin fushinta musamman tunda yana da alaƙa da silar ɓacin ran nata. Alwala tayi ta tada sallar magriba, cikin hanzari, tana gyara hijabin jikinta taji Ahmad yace "Mami, bari na biki na duba Al-Amin. Bashida lafiya yau bai zo makaranta ba." Yana maganar yana zura takalmi. Sai ta tare shi da sauri ta ce "Aa Babana. Ka bari idan yaji sauƙi sai ku haɗu a school. Ka manta Inno ta hana ku shiga gidansu? So kake ta yi maka faɗa ko ta saka Hasna su doke ka?" Ahmad ya girgiza kai, idanunsa suka cika da hawaye kamar zai fashe da kuka. Ya buɗe school bag dinsa ya fito da bundle na sababbin 1k, ya miƙa mata. Mami ta zuba masa ido cike da tsoro bayan data kalli kuɗin da yake miƙa mata, kafin tayi magana ya rigata "Wannan Baban ne ya bamu. Addah Imaan taƙi karɓa. Na ce ta karɓa saboda idan an tashi daga school zamu ringa hawa mota idan su Hasna sun hanamu shine ta dokeni har ta fasa min baki. Shi kuma Uncle ɗin nan ya mareta, Baba kuma ya bani kuɗin yace a siyo min magani." Shiru tayi, tana kallonsa kamar mai ƙoƙarin fassara maganar sa zuwa yaren da zata fi fahimta. Saboda ta kwaɓi Ahmad ya saka mutumin ya mareta kenan? To waye ma mutumin? Kuma akan me kawai daga haɗuwa haka nan zai ɗauki maƙudan kuɗi kamar haka ya basu? Ji tayi zuciyarta ta fara tsinkewa da tsoro. An shata ta warke akan halayyar mutane. Ba tare da cewa komai ba ta karɓi kuɗin, tana cewa "Maza kaje ku zauna da Addar ka. Koda wasa kar na ji ka fito. Ga abincin da muka taho da shi nan ku ci, ku kwanta kafin na dawo" ta ajiye kuɗin akan kujera ta fita da sauri. A dai-dai lokacin Imaan ta fito daga ɗaki. Fuskarta har sannan babu walwala, yanda idonta yayi luhu-luhu da alamun sabon kuka tayi. Tunda ta fito tayi alwala ta sake komawa ɗakin sai yanzu. "Ko nazo na tayaki? Naga lokaci ya ja da yawa" ta faɗa tana bin bayan Mamin, sai ta dakata ta kalleta da murmushin ƙarfin hali ta ce "Aa, ku zauna. Ki kula da Ahmad kawai." Daga haka ta ja musu ƙofar falon ta wuce cikin gidan. A ƙasa Imaan ta zauna, ta soka kanta tsakanin cinyoyinta ta fashe da kuka sosai. Ita kaɗai tasan kalar baƙin cikin dake cunkushe mata zuciya a duk sanda ta kalli mahaifiyarta taga irin rayuwar da take yi a ciki da wajen gidansu. It hurts when you know your mother deserves better... but you can’t give her anything. Da ace tana da hali data daɗe da canza komai. A kullum ta Allah addu'arta da fatanta bai wuce ubangiji ya rayata ya kaita lokacin ta zata hucewa Maminta takaicin rayuwar data tsinci kanta a ciki. Tun daga lokacin da hankali ya fara shigarta, ta fara gane banbancin fari da baƙi ta kuma fuskanci matsayin da suke dashi a cikin gidan da yake mazaunin na mahaifinsu daga sannan tayi hannun riga da farin ciki a rayuwarta. Irin tasu ƙaddarar kenan, a cikin gidan ubansu amma karen gidan ya fisu yanci tabbas *WASU MATAN* sam babu Allah a ransu, tamkar kuma suna mantawa akwai wata rayuwa a gaba bayan wacce a ciki yanzu. Share hawayen da suka riga suka zame mata jiki tayi, ta miƙe jin ana buga ƙofa. Aliyu ne ya dawo gida. Kallo ɗaya ya yi mata, sai ya ce: "Ina Mami?" "Tana can gidan," ta amsa a taƙaice. Sai ya shige falon, fuskarsa cike da gajiya kamar mai shirin faɗuwa ya zauna yana dafe kansa. Tausayin kansu ya sake kama Imaan. Tun safe ya fita neman cikon kuɗin makarantar sa. Kuɗin da basu wuce mutumin da ake kira da sunan mahaifinsu yayiwa mutum dubu kyautarsu ba tareda yaji komai akan hakan ba, amma Aliyun ya shafe kusan wata biyu kenan banging every possible door amma har yanzu daya rage kwanaki kaɗan a rufe registration ɗin bai haɗa su ba. Abinci ta zuba masa cikin wanda suka taho da shi. Kafin ya gama ci, ta kunna masa water heater a banɗaki dan dole zai buƙaci yin wanka da ruwa mai zafi ko dan ya samu warware gajiyar daya kwaso, sai suka shige ɗaki ita da Ahmad, suka bar masa falon don ya samu damar shiryawa a tsanake tunda a nan kayansa suke. ********** Mami kuwa, bayan fitarta, cikin nutsuwa ta ringa takawa dukda bugun da zuciyarta takeyi tamkar zata huda ƙirjinta ta fito. A zahiri, babu wani firgice a tattareda ita. Cikin ranta kawai take maimaita "Hasbunallahu wa ni’imal wakeel..." Harta isa ɓangaren matar gidan. A bakin babbar ƙofar shiga ta yi karo da wasu 'yan mata guda biyu masu tsantsar kama da juna. Zasu iya yin shekara 20, koma su haura kuma suna da tsayin gaɓɓai. Sun sha kwalliya cikin wani baƙin lace da kyawunsa ya bayyanar da tsadarasa ya kuma haska farar fatarsu. Yanayin ɗinkin dake jikinsu ya bayyana rangwamen tarbiyya da suke dashi, dukda cewar ainihin surarsu a shafe take, basu da wani tudun azo a gani. Amma telan yayi amfani da abubuwan coge ya samar musu da dirin da ba yanda za'ayiyi mutum yayi musu kallo ɗaya ya ɗauke kai. Daƙyar suke takawa suna riƙe da juna saboda takalman dake ƙafafuwansu masu azabar tsini sai kace dole. "Yawwa Aisha, potato salad zaki mini. Amma don’t even think of adding too much cream yanda kika saba. Also, make sure my banana milkshake is properly iced before we get back." Ɗaya daga cikin yammatan ta faɗa tana yatsina kamar wadda

Chapter 3 of 7