Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *WASU MATAN* *Labari/Rubutawa Maryam Farouk (Ummu-mahir)* *Women of worrds writers association (WOW)* *Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01* *Wattpad @MaryamahMrsAm* *TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels* *Ban yarda wani ko wata ya juya mini labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba* *Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mini da littafi* *WASU MATAN littafin kuɗi ne, a biya naira 1k, biya a asusun* *7061838488* *Opay* *OR* *1840175439* *Access bank* *Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama* *Ina yiwa ɗaukacin mabiyana waɗanda sukayi rashi na yan uwa da abokanan arziƙi ta'aziyya, ubangiji ya jiƙan magabatanmu ya sa suna Aljanna maɗaukakiya, idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani.* *Waɗanda suka samu ƙaruwa Allah ya raya mana zuri'a, ya yi musu albarka.* *Masu aure Allah ya ƙaro farin ciki da wadata a cikin zamantakewarmu, marasa aure ubangiji ya yi muku zafi na mafificin alkhairi.* *Marasa lafiyarmu na gida da asibiti Allah ya ƙara lafiya ya sa jinya ta zame muku kaffara, mu da mu kuma Allah ya ƙare mu da lafiya mai amfani.* *SADAUKARWA* *Na sadaukar da wannan littafin kacokam ga masoyana, masoyan rubutuna. Alkhairin Allah ya tarar daku har gidajen baccinku. Nagode da lokutanku da kuma kuɗaɗenku da kuke iya zarewa domin ku tallafi kasuwanci na. Ubangiji ya fi ni yabawa* *JINJINA* *Jinjina ta musamman ga marubuta musamman n ƙungiyata (WOW). Idan karamci na da siffa, tabbas kune. Allah ya ida nufi cikin shirye-shiryen alkhairi da cigaba muke ƙoƙarin cimma. Long live WOW* *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM* FREE PAGE 1 * Shehu Shagari Crescent, Maitama, Abuja*. Sassanyar iskar dake busawa, irin wacce take faruwa a lokutan da hadari ya haɗo, sai ya wuce ba tareda ya zubar da ruwa ba, ita ta ƙarawa yanayin garin wani daɗi da armashi na musamman. Kasancewar rana tana dabda faɗuwa ne amma kuma garin tarwai yake da wani irin haske na yayewar hadarin yammaci, yanda dogayen bishiyun da suka ƙawata layin suke rangaji, zuwa duk inda ƙarfin iskar ya tafi dasu sai ya zama wani yanayi mai daɗin kallo da ban sha'awa. Gidajene jere hagu da dama cikin layin da yake close (baya ɓullewa) sai titi shimfiɗe tsakani. Gidajene manya kuma na alfarma wanda duk tarin ƙawazucin ɗan Adam da kuma buri tabbas zai saurara har idan akace ya mallaki ɗaya daga cikinsu, domin kuwa ko daga kallon tsari da zubin ginin daga waje zaka hakaito tarin kayan more rayuwa da suke danƙare a ciki sun ishi mutum komai son duniyarsa kuwa. Layin shiru baka jin motsin komai sai na iskar dake kaɗa ganyan bishiyu, sai kuma haushin karnuka daga wasu daga cikin gidajen. Gidan ALHAJI AHMAD GAYAWA shine gida na ƙarshe a cikin layin, kuma gidan daya fi kowanne girma da kyawu na taswira da kuma zubi. Makeken Get ɗin gidan mai kama da ƙofar gari ya buɗe kansa dalilin kusantowar wata baƙar mota ƙirar Lexus LX 600, mutum biyu suka fito daga cikin gidan da sauri dukanninsu sanye da uniform, baƙin wando da riga mai ruwan ƙwanduwar ƙwai, da ƙaramin tag mai ɗauke da sunans da matsayin kowanne saƙale jikin aljihun rigunansa.a Cikin nuna girmamawa ga wanda yake cikin motar suka ƙame a gefe, sai dai, bai ko nuna alamar ya gansu ba, cikin tuƙin dake nuna fushi ko gaggawa ya kutsa kai cikin shimfiɗeɗiyar harabar gidan dake nan tamkar a fadar shugaban ƙasa. Wasu mutum biyun dake sanye da uniform irin na waɗancan ne suka sake nufar gurin da aka tanada domin ajiye motoci, wanda ke tsaye ta ɓangaren da matuƙin yake ya saka hannu da niyyar buɗe masa bayan daya gama dai-daita parking sai dai mutumin cikin motar ya katse masa hanzari ta hanyar buɗewa ta ciki haɗi da hankaɗo murfin ta yanda ya buge shi cikin sani ko akasin haka babu wanda zai faɗa. Kallo ɗaya yayi masa ta cikin baƙin glass ɗin dake manne akan fuskarsa kafin ya ɗaga masa hannu alamar ban haƙuri, cikin takun sauri wanda ya haɗa harda sassarfa ya doshi ƙofar shiga ainihin gidan ma'aikatan dake barbaje cikin farfajiyar gidan kowanne ya ajiye abinda yakeyi suka shiga yi masa sannu da zuwa amma bai tsaya ba sai hannu kawai ya ɗaga musu. Seconds uku da ƙofar ta ɗauka kafin ta gama scanning zanen yatsansa da yayi amfani dashi gurin buɗeta sai ya jishi tamkar awanni uku ya ɗauka a tsaye a gurin. Da gudu tamkar yaro ya haye matakalar benen da aka zuba a tsakiyar falon cikin wani irin tsari mai ƙawa da burgewa, tabbas, ko wanene architecture ɗin daya zana taswirar ginin gidan ya cancanci babbar lambar yabo domin kuwa sai an sha dogon musu kafin a gamsar da wanda yaga tsaruwar gidan a hoto kawai cewar a nan ƙasa Nigeria gidan yake ba wai turai ba. Jin sa ya ringayi tamkar wanda aka busawa sabon rai, ya ringa sakin iska daga bakinsa yana share zufar data tsattsafo masa da tafin hannunsa a ransa yana ayyana anya a duniya kaf akwai abinda ya kai daɗi da samun nutsuwar yin bayan gida? Wani irin yanayi yake shiga wanda ba zai iya fasaltawa ba a duk sanda buƙatuwar zagayawa ta kamashi. Baya iya matsewa duk sanda cikinsa ya juya toh fa sai yayi juye zai samu nutsuwa sai kuma aka samu akasi shi ɗin ya kasance baya iya yin wannan buƙatar a ko ina idan ba'a gida, ba sai dai idan ta kamshi a inda bashida halin komawa gida idan ba haka ba kuwa duk inda yake a cikin gari ya matsoshi sai ya nemi gida kamar dai yanzu daya matsoshi suma tsaka da hirar yaushe gamo a taron tsofaffin abokanansu da sukayi secondary school tare. Ƙasan shower ya tsaya ya sakarwa kansa ruwa yana cigaba da sakin ajiyar zuciya. Momy tace tun yana yaro haka yake. Duk inda yake yaji bayan gida toh fa da gudu zai dawo gida ko unguwa sukaje haka zai matsa mata su taho idan kuma taƙi ya kasa riƙewa ya sakeshi a wando. Yana iya tuna wasu lokuta a sanda yake primary school ya sha yi a wandon idan yace a mayar dashi gida suka ƙi haka zai samu guri ya shirga musu aiki sai dai a wanke masa a canza masa uniform. Har ya shiga JSS 1 yana wannan iyashegen, tsokanar da abokai suka fara masa shi kuma ba mutum bane mai jure raini dole ya koyi matse abinsa har sai ya koma gida amma fa haka zai ƙare lokacin a tsaye ko yayi ta zagaya makaranta ba zai saurari darasin ranar ba har sai an tashi tukunna. Ko yanzun kallo ɗaya Hammad yayi masa ya fahimci dawar garin, dukda bai so zuwa taron ba Hammad ɗin ne ya tilasta shi amma kuma daya je yaga old friends wasu ma ya manta tsayin lokacin da bai sanyasu a idanuwansa ba sai kuma ya ware ana tsaka da sabga kuma ciki yace bai san zance ba dole ya bada uzurin ana jiranshi yayi musu sallama domin ba zai iya komawa ba tunda magriba ta kawo kai ga kuma hadari daya taso a can area ya sani ba zasu ƙara lokaci mai tsayi ba suma kafin kowa ya kama gabansa. Fitowa yayi daga bathroom ɗinsa, ƙugunsa ɗaure da white towel sai wani ƙaramin towel ɗin a hannunsa yana tsane sumar kansa daya wanke. Ya kalli agogon dake kan bedside drawer, only few minutes left before Magrib. Sai ya wuce gaban dressing mirror ɗinsa dake shaƙe da kayayyaki tamkar na mace kama daga kan body creams, lotions, perfumes da sprays tamkar wani mini shelf ɗin cosmetics store. Cikin zafin naman da yake ɗabi'arsa ya shiga shiryawa, sumar kansa ya fara gyarawa bayan daya jona hand drayer ya busar da ita sama-sama ya shafa hair cream kafin ya ɗan gyara shape ɗinta da comb, daga nan ya fara shafa mai a jikinsa. Ya sakin towel ɗin dake ɗaure a ƙugunsa kafin ya nufi walk-in closet ɗinsa domin ya saka kaya, wayarsa daya jefar da ita a inda bai sani ba sanda ya cire kaya ta shiga ringing, hakan ya saka ya dakata, turned sharply yana jiyo ƙasar daga ɓangaren gado. Tsalle ɗaya ya doka cikin wani irin zafin nama tamkar Zakin daya faki barewa, dukda zafin daya ratsashi sakamon bige kansa da yayi da ƙofar closet ɗin da take ta jan katako bai kula ba ya ƙarasa shigewa ciki yana nanata "Hasbunallahu wani'imal wakeel" cikin sautin dake nuna mix of fushi haɗi da firgici a tareda shi. "Wane irin sakarci ne haka? Salon ka jiwa kanka ciwo" Hajiya Hadiza data tashi tsaye da sauri cikin razani da damuwar ganin irin tsallen da ɗan nata ya buga ta faɗa tana nufar closet ɗin. Hannu biyu ya saka ya dafe ƙofar ta ciki ganin tana ƙoƙarin buɗewa, cikin ɗaga muryar yace "Meye haka kikeyi Mom? get out of my room". Tsayawa tayi, cikin ɗaga murya ta ce masa "Ni kake yiwa tsawa Yusuf? You must be mad, kayi hauka ne zaka yi mun ihu kace na fita daga ɗakinka?" Bai amsa mata ba, yayi locking ƙofar ta ciki dan rikicewar da yayi ta saka sam ya manta da tana rufuwa, cikin fushi ya shiga zaro jallabiyya, a jikin hanger suke jere neatly amma yanda ya fizgota sai da ɓangare ɗaya na ƙarfe da ake rataye hangers ɗin a jiki ya cire daga jikin katakon da yake, hangers ɗin jiki suka shiga rige-rigen zarewa. Baibi takansu ba ya ɗauki guɗa ɗaya ya zura a jikinsa ba tareda ya saka singlet ba sannan ya matsa inda dogayen wandunansa suke nan ma ya ciro ɗaya ya saka. Yanda ya buɗe ƙofar ya saka Hajiya Hadiza dake tsaye har sannan tana jiransa matsawa da baya da sauri, kafin tayi magana ya rigata da cewa "Why Mom? Sau nawa, saboda Allah sau nawa zance miki ki daina shigo mini ɗaki anyhow? Don't you respect boundaries? Dama saboda ki ringa faɗo mini ɗaki duk sanda kikaga dama cikin yanayin daya dace ko wanda bai dace ba ya saka kika tilasta sai na baro part ɗina na dawo nan?" Yaja numfashi, idanuwansa suka kaɗa a kallo ɗaya kuma zaka fahimci fushi da wani abu mai nauyi a tattare dasu, "Akan me? Dan Allah, Don't you have shame?" Ya sake faɗa yana kafeta da idanuwansa dake fallatsin bacin rai. Magana yake cikin ɗaga murya tamkar zai kai mata hannu, muryarsa da fuskarsa sun bayyana duk abinda yake kwance cikin zuciyarsa. Ya sake tareta ganin tana shirin yin magana, ya san mai zatace, same recycled line "Ni uwarkace, tun baka san kanka ba na rigaka ganin abinda yanzun ka girma kake ɓoye mini". Seriously? Saboda Allah a ina akace uwa ta ringa irin wannan kutsen cikin rayuwar ɗanta baligi? Har yaushe Mom zata fahimci cewa he’s not Baby Yusuf anymore? She’s still seeing him as some soft little boy, amma yanzu he’s a grown man. Wannan abun da take yi is totally wrong in every way. A addinance, a al'adance, hatta a basic human boundaries, it's a sin. Bai san irin tunanin da Mom ke masa ba... Har ya shekara goma sha biyu a duniya ita ke masa wanka, saboda wai idan yayi da kansa,a cewarta baya fita, that's why he turned dark, in her words. Tunda daga ita har Baba fararene tas shine kalarsa ta fita daban da su, wai ita a fari ta haifeshi. Dukda yanda yake nuna baya so, sai ta nuna ɓacin ranta sannan zai yarda a hakan yana kakkare jikinsa daga baya ma sai ya saka boxers haka zata tasashi da faɗa tace masa "What are you hiding from me?" Seriously? Hide? Sai da Alhaji Ahmad da kansa yayi mata magana kafin ya samu ta rabu dashi da zancen wanka amma dukda haka yana takura da abubuwa da yawa da takeyi masa, Har yanzu tana ƙoƙarin rungumesa, tana sumbatar sa 'anyhow,' ko ace 'just a peck,' a fahimtarta, tana cewa: "Ni na haife ka, ai zan iya rungumeka yadda nake so." Amma shi kam abin yana masa nauyi, even shame. Tun yana shekara sha huɗu, jikinsa ya fara sauyawa. Idan ka ganshi, sai ka rantse he was 18, even 20. Har gemu ya fara, muryarsa ta fashe hara girmansa har kunya yakeji ya saka kayan da zasu bayyanar da gurin, amma koda yaushe a idanun Mom, he’s just her boy, her possession. Sosai yake jin kunya a lokacin, deep shame, wanda shine dalilin da yasa ya roƙi a tura shi boarding school. Ba dan yana son independence kawai ba, amma domin ya guje wa takurar Mom ɗin da ta ɗora duk soyayyar duniyarta akansa, kasancewarsa ɗa tilo da suka haifa a duniya. Bayan ya gama secondary school, ya tafi UK inda ya ci gaba da karatunsa. Bai dawo Najeriya da zama gaba ɗaya ba sai shekaru huɗu da suka wuce, bayan ya kammala har da Master's degree a fannin Business Management. Amma koda ya dawo, babu abinda ya canza. If anything, things got worse, komai ya sake lalacewa ne kawai. Mom har yanzu tana masa kallon kamar yana cikin pampers. Ta mayar da part ɗinsa wanda aka gina masa a gefe inda swimming pool ɗin gidan yake kamar nata ne gaba ɗaya. An gina masa private duplex mai ɗakuna uku a sama, harda gym. A ƙasa kuwa akwai falo, ɗaki ɗaya, kitchen, da ƙaramin ɗaki da ya mayar da shi study room. Amma Mom ba ta da takamaiman lokaci. Any time, any mood, any situation tana iya faɗo masa. Yayi roƙo. Yayi lallami. He even tried to reason with her like an adult amma duk a banza har sai da ta kaishi wuya har baya sanin sanda yake balbale ta da a duk sanda tayi masa abinda baya so. A ƙarshe ma sai ta tilasta masa barin part ɗinsa, ta mayar da shi ɗaya daga cikin ɗakunan main house. Da farko, ta ce ya zauna a ɗakin kusa da nata, amma Baba ne ya ce "bai kamata ba, Ta yaya zai ringa karakaina tsakanin mata?" ganin yadda mata da ma’aikata ke kai-kawo a cikin part ɗin nata. Hakan yasa yace ya koma ɗaki a second floor, kusa da part ɗin Baban wanda shi kadai ke da nutsuwa a gidan da zai iya sakashi numfashi kadan. Babban abin da ke tayar masa da hankali ba wai yawan tunani bane amma irin hotunan da ƙwaƙwalwarsa ke haska masa lokaci-lokaci. Hotuna da duk lokacin da suka bayyana, sai ya ƙaryata kansa. "No. This can’t be real... It’s just my mind playing tricks". Ba zai taɓa yarda cewa akwai wani abu da idanuwansa ke gani tattare da Mom ɗinsa wanda ba daidai ba ne. Domin soyayyarta gare shi ba ɓoyayya bace. She was all over him. Too much, even. Amma dalilin da yasa ƙwaƙwalwarsa ke so lallai ta ɗarsa masa wani abu dabam wannan shi ne yake rikita shi. Yana ganin wani yanayi cikin idanuwanta, not the eyes of a mother, but the type of gaze he had seen from girls.. Yammata masu yi masa kallo mai tattare da wasu ma'anoni ba wanda uwa take yiwa ɗanta ba, kamar dai abinda yake gani a yanzu, tana yi masa irin kallo ta juya ta fice daga ɗakin. He tried to interpret the look as anger, as disappointment...Amma zuciyarsa ta ƙi karɓar haka. Sai dai ya rasa da wane yare zai yi mata bayanin da zata fahimce shi, yana so ta gane duka waɗannan abubuwan ba dai-dai bane amma ya kasa. And worse... he couldn't tell anyone. Not even Baba. Ta yaya zai faɗa masa cewa Mom tana binsa banɗaki wai saboda tana son magana dashi? Kuma tana tsayawa tana kallonsa naked, ba tare da ko damuwa ba? Har ta rungume shi, kamar yadda mace ke rungumar mijinta. Shi da kansa ya rasa mai yake faruwa. There was even a morning… ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yana ɗaukar wayarsa daga kan gado, baya son tunawa ya kuma rasa yanda zai yi ya goge tunanin daga ƙwaƙwalwarsa. Ya fito cikin sauri zai tafi office. Zip ɗin wandonsa bai gama rufewa ba. Shi kansa bai sani ba. Maimakon ta yi masa magana da baki tace ya gyara... She reached for it. With her hands. Calmly, Slowly tana cewa "Tsaya na gyara maka..." Da kallon da baki ba zai iya misalta shi ba. Wani irin kallo ne na macen da ta manta cewa wannan mutumin ɗanta ne. Her face was calm. She meant it. Sai kuma ta juyo ta yi kamar ba komai ya faru ba... Taci gaba da haɗawa Baba abin karin sa akan dining. "This is not normal. This is not right. Maybe I'm overthinking. Maybe I'm just tired. If someone told me this kind of story... wallahi I’d say they were sick in the head. But me? Why is it playing in my head? What if... what if I'm not wrong?" Page 2 Har ya kai bakin ƙofar fita daga falon, idonsa ya sauka kan reflection ɗinsa a cikin glass panel ɗin bangon ƙofa. Ash ɗin jallabiyya ya saka da jan wandon track suit. Bedroom slippers ne a ƙafarsa kana kallonsa kaga mara nutsuwa. Dogon tsaki ya ja, ya juya da sauri ya koma ciki, ya cire kayan gaba ɗaya, ya saka black jeans da black plain T-shirt. Sai bayan ya kalli kansa a mirror ne ya fahimci kayan daya saka. He loves black, it’s his favorite color, Amma Baba hates it. Ya san idan Baba ya ganshi yanzu, zai fara mita akan kayan "Black on black kamar zaka je jana'1izar kiristoci?" Amma gaskiya... he just didn't care anymore. Su suka dace da yanayin da yake ciki a yanzu. Ya lalubo black P-cap, ya saka. Ya ɗauki dark sunglasses da ya shigo da su ɗazu, sai kuma wallet da key ɗin motarsa. Maybe getting out of the house would help him breathe, he is suffocating right now. A kan dining table ya hango Mom tana gyara kayan abinci da aka ajiye. Da sauri ya ɗauke kai, he didn't want her eyes to meet his, ya kuma ƙara saurin tafiyarsa dan baya so ta tsayar dashi, amma kafin ya kai ƙofa ta kira shi "Yusuf..." Cak ya tsaya. Ya motse fuska kamar ƙaramin yaro da aka kama yana shan sugar. A hankali ya juya yana ƙoƙarin dai-daita yanayinsa, dark glasses dake fuskarsa ya taimaka masa gurin ɓoye abinda idanunsa ba zasu iya shanyewa ba. "Ina zakaje?" Ta tambaya tana ƙare masa kallo. Ya haɗiye yawu, zafin maganar ya tsaya masa a wuya. Seriously? Shi kam yaron goyo ne har yanzu? At thirty? Mom na tambayar shi ina zai je kamar dai wani da yake da tarihin laifi. Daƙyar ya ce "Gurin Hammad, Mom." "Wai fushi kake yi dani, Yusuf?" Ta faɗa tana ƙoƙarin ruƙo hannunsa. Yaja baya da sauri, ya ce "I told you, Mom. Countless times. Bana so ki ringa shigo min ɗaki yanda kika ga dama. Amma kinƙi. Why, Mom? Wai bakya jin kunya ne?" Wani murmushi tayi wanda ba zai iya fassara ma'anarsa ba kafin cikin sanyi ta ce "Don’t stay out too late. Ka san Alhaji yana gari." Ta matsa kusa da shi ta yi masa peck a kumatu amma har rabin laɓɓanta saida suka taɓa nasa. A razane ya janye jikinsa zuciyarsa na bugawa. This wasn’t just annoying anymore. This is scary. Ya rayu a Turai, ya zauna da mutanen da dama kala-kala, Amma ko a labari, bai taɓa jin uwa tana nuna irin waɗannan bahagwayen halayen da Mom take nuna masa ba. Ba a Turai ba, ba a Africa ba, balle a Nigeria kuma cikin gidan Musulmai. Sai da ya yi sallar Magriba a masallacin cikin gidan, kafin ya hau mota ya fita ba tare da sanin takamaiman in da zaije ba. Tun da yamma suka yi magana da Hammad, wanda yace daga wajen taron zai wuce Suleja, gurin Surayya, yarinyar da yake nema da aure. Sai da ya roƙe shi su tafi tare, amma yaƙi, da ya san irin abinda zai tarar a gida kenan, da ko leda ce ya nema yayi uzurinsa a maimakon ya koma gida. Haka yayi ta gararamba tsakanin tituna sai ƙarfe goma ya kama hanyar gida. Da ya shigo harabar gida, motocin da ya gani suka tabbatar masa Baba na da baƙi. Sai ya zauna a mota, he didn’t want to pass through the main parlour. Ya san Momy ba zata kwanta ba har sai ya dawo, kuma baya so ya haɗu da kowa daga cikin baƙin Baba, musamman da ya hango motar Barr. Salahuddeen, Dadyn Hammad. Idan ya shiga ya sani cewa zaiyi ya zauna ayi meeting ɗin dashi. Bai jima sosai ba baƙin suka fara fitowa, ɗaya bayan ɗaya, Barrister ne ƙarshe. Harabar gidan na da haske sosai dan ko allura ce ta faɗi zaka iya ganinta ka ɗauka dan haka yana hangen duk masu shige da fice daga inda yake. Momy ce ta biyo bayan Barrister. Yana kishingiɗe cikin kujera yana zare idanu kamar wanda ya shawu. Ubangiji yayi masa baiwa da yawa, yana da ƙarfi ji, gani da kuma baiwar karantar motsin laɓɓa. Ko da bai ji sauti ba idan ya kalli bakin mutum zai fahimci abinda yake faɗa ba tareda wata matsala. Daga inda yake yake kallon fuskarta da laɓɓanta, ya naɗe maganar da ta furta kamar yana jiyo sautin da kunnensa. "Ka tabbata bai yi kuskure ba a wannan karon," ta faɗa a hankali, kafin ta miƙa masa wani abu sannan ta juya ta koma cikin gida shi kuma Barr ya wuce zuwa motarsa. Buɗe murfin motar yayi zuciyarsa na buguwa da karfi, amma ya dakata ganin Haladu, ɗaya daga cikin direbobin gidan, yana nufar Barrister. Suka gaisa. Barrister ya matsa kusa dashi suka bashi baya dan haka bai fahimci mai suka tattauna ba haka nan kuma yaji bai nutsu da abinda ya faru ba dukda bai san ko menene ba. Saida yaga motar Barr ta fita, kafin ya shige ciki yana tafiya a hankali dalilin kansa da yake sara masa. Main parlour shiru, yana jin yunwa amma cushewar da zuciyarsa tayi baya zaton zata samar da hanyar da abinci zai ratsa ya isa cikinsa. Bai tsaya ba ya nufi ɗakinsa, amma kafin ya shiga, sai ya tsaya a

Chapter 1 of 7