Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
borm azuciyarshi yace *Ummih wlhy bazan iya hakurin rashintaba kinsan itace rayuwata ......๐Ÿ˜ญ Nan yashiga rairo kuka tmkr an mishi bishara da wani mummunan abu Nan ummih ta tabbatr da babban abune lallai ba karamin so yake mataba Dakyar ummih ta rarrasheshi tareda mishi alqawarin zata tayashi addu'arh kuma inhar matarshice seya aureta Sanadin kalamannata yasa yadanji sanyi aranshi adaddafe suka kara kwana biyu batareda ummih ta sanar sa mom damuwar *Annur* ba (Nidai nace kwara da baki sanar da itaba๐Ÿ˜‰ ) Suka baro kasar cike da kewar juna musamman ummih datakejin *Annur* aranta tmkr karya wuce takeji Kai tsaye pilot din gidansu yanufo dasu .......... *Wallahy dukna gaji*๐Ÿ˜ข ๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIโœ๐Ÿป ๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘ BOYEYYEN AL'AMARI ๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘ {22/6/2018} 7:14 pm ๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI โœ๐Ÿป *fans kuna rainah*๐Ÿ’‹ PAGE23โƒฃ4โƒฃ Pilot din na tsayawa atsakiyar gidan Masu aikin gidan duk suka fito cike da murnar dawowansu nan suka shiga kwashe komi dasuka dawo dasu suna shigar dashi cikin gidan seda suka gama kwashe komi tsaf Mom tafito hannunta makale da jaka masu aikin gidan nata kawo gaisuwa baba talatu cikin sauri tazo ta amshi jakar hannunta tana mata ban gajiya......... Zira kafarshi yayi kmr zai fito daga pilot din se kuma meya tuna ya maida lallausan kafafunshi nan ya umarshi direban pilot din yajuya suje gidanshi na hutawa........... ๐Ÿค” ** ** ** Ya *ahamad* fa dukya rikice yashiga wani hali tinda *khausar* tasanar dashi Akwai wani wanda yamutu akan *inteesar* tasanar dashi yadda yatsugunnah agabanta yana furta mata kalaman soyayyah aifa tinda yaji hkn hnklinshi yatashi ga wutr santa nata ruruwa acikin zuciarshi dukya shiga wani hali *ADALILIN SO*.........๐Ÿ˜ญ ** ** ** Hmmm komifa yarikicewa *inteesar* tinda malam yatafi se bakar wahala da azaba iya take bawa *inteesar* dukta rame ta lalace ga tallar goron da iya ke daura mata tinda sassafe gashi ta kashe mata zuwa makarantrta ta boko da islamiyyah gashi tana matakin ss3 ne aboko a islamiyya kuma ss2๐Ÿ˜ญ duk wanda yasanta ada ayanzu baze ganetaba gashi 2 days *ukti* tadauke mata kafa da zuwa gidansu gashi bata da kati awaya ballan tana takirata rashin katinne ya hanata takira abbanta duk hnklinta atashe......... ๐Ÿ˜ฑ Itako hafsat afanninta dunia sabuwa jinta take tmkr kadama mlm din yadawo domin tasamu freedom๐Ÿ˜ฑtaje yawon iskancinta sanda taga dama tadawo sanda taga dama itadai iya afanninta ba kwaba se ririta hafsan takeyi saboda tana kawo mata shaggun (naira) ๐Ÿ˜‰ ** ** Akayataccen gidan hutawar tashi pilot din ya yada zango Cikin gidan yashiga ko ina agyare tsaf kmr akwai mutum aciki Kai tsaye upstairs yahaye ya yada zango a bedroom dinshi zama yayi agefen faffadan gadon dai2 lokacin daya daga cikin wayoyinshi tayi ruri jawota yayi yaga sunan umminshi ta saudia ya bayyana da fara arshi yakara wayr akunnenshi cikin girmamawa yake gaidata ta amsa tareda tmbyr sun isa lafia tayi mishi bn gajia tareda sanya mishi albarka atareda suka aje wayar Shirin shiga wanka yayi tareda yima kukun gidan tex din abincin da yake bukata (koda baya gidan akwai yan aiki masu mishi hidima duk month yana tura musu kudinsu ta account) kashe dukkan wayoyinshi yayi guda daya yabari wadda mom and dad dinshine kawai keda lambar sim card din dake wayar ** ** ** Juyi takeyi akan gadon tana kara rungumar filo tana kai mishi kiss๐Ÿคฃ Ahankali taturo kofar dakin nata tsayawa tayi tanata kallonta tanata kaiwa fillo kiss๐Ÿคฃseda tayi 5mnt tana kallonta ahaka sai kara kaiwa fillon raruma takeyi๐Ÿคฃajiye jakarta tayi takarasa gareta tadan bubbugata๐Ÿคฃ Aifa tayi nisa batajin kira se kara kaiwa fillo runguma takeyi (nidai nace ayi hkr kar alalata fillo๐Ÿคฃ) Kara kai mata duka tayi da karfi afirgice ta farka tana murza ido ta sauke idon akanta cikin matsifa ๐Ÿคฃsunayin ido biyu tahadiye matsifar tata tare dacewa haba masoyiya yazaki tasheni inata mafarkinshi Haฤe rai tayi tareda cewa *haba my baby kinsan inada kishi fah waye yake neman sacemin zuciarki๐Ÿ˜ฅ Murmushi fa'iza tayi tareda jawo hannunta tazaunar da ita kusa da ita tace *kai my nice kin mance my guy annur wannan dan shugaban kasan Mtwssss...........! ๐Ÿคฃ *Boyeyyen al amari fans kunji wani zunubi*๐Ÿ™„๐Ÿค *iska na wahalar dame kayan kara* ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ LUV U ALL๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜ ๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI โœ๐Ÿป ๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘ BOYEYYE AL'AMARI ๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘ {25/6/2018} 9: am ๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI โœ๐Ÿป *Rahama abdullahi kina nan acikin nan dina*๐Ÿ‘‰๐Ÿฝโค PAGE3โƒฃ5โƒฃ Diyana taja uban tsaki tareda cewa *kai my baby nifa wlhy kinsan inada kishi kosu muktar dakike hulda dasu kinsan baso nakeyiba so nake naci gaba da mallakarki ni kadai har abada runguma fa'iza takai mata tareda manna mata kiss *kinsan yadda nake jinki anan dina (tanuna mata saitin zuciarta) shima hk nake jinshi burina kawai na mallakeshi narinka juyashi tamkar waina atanda bata fuska diyana tayi tareda daga kafada tace *knga dear ni bashi bane damuwata kwanto kafadarta fa'iza tayi tareda manna mata kiss akuncinta na hagu tace *ni nasan damuwarki ๐Ÿ˜‰ nan tajawota suka afka wata duniyar........ *** diyana kawar fa'izace ta fatsikanci sun hadune a London daganan suka kulla alaqa diyana iyayenta masu kudine sosai sun tara dukia tamkar zasu tada fillo dasu su hudu iyayensu suka mallaka mata biyu maza biyu diyanace auta iyayenta sun shakwabata sosai sun daura mata son dunia tmkr zasu hadiyeta da kaunah diyana bata da wani kyau bakace wuluq amma taji bilicin tini takoma kalar amai yellow๐Ÿคฃ itadin tsiririyace bata da wani shape atsaye take kikam๐Ÿ˜ฑagirme zata girmi fa'iza dashekara biyar wannan kenan..... ** ** ** Yau kwanansu uku da dawowa daga saudia be leka koda gidanba sedai sunata waya da mom da dad dinshi kwance yake akan kujera me mazaunin mutum uku wato three seater yana danna remote control din tamfatsetsen t.v din daya mamaye bangon falon yanayi yana kora hollandia milk kallon yakeyi ammafa dukkan sassan jikinshi da zuciarshi da numfashin shi duk suna gareta.... tunani yakeyi waishi wannan wanni irin sone yake mata..... wayarshice tahau rurin neman agajin gaggawa jawota yayi yakara akunne cikin ladabi yace *ina kwana daddy daga daya bangaren ya amsa da lafia qalau son i miss u tinda kuka dawo daga saudia bakazo na gankaba my son hp kana cikin koshin lafia ya amsa da lafia qalau daddy insha allahu yau zan shigo zuwa anjuma Allah yakawoka lafia my son๐Ÿ˜˜ ya amsa da amin tareda tsinke wayar kittt....... yaci gaba da aikin tunanin kyakyawar tashi(sunan daya raฤa mata kenan acikin birnin zuciarshi) ** ** ** tin anasa idanun ganin malam har yau satinshi uku ba aji duriyarshiba hankalin *inteesar* yafi na barawon asuba tashi ๐Ÿ˜ฑtazama tankar zautacciya domin tashin hnkli bata iya cin abinci bata iya barci kullum se kuka๐Ÿ˜ญgashi iya taga wayarta ta amshe ta nakaฤa mata dankaren duka ta balla simcard dinta tabawa hafsat wayar domin acewarta hafsat dince tadace da rike waya ba yar zi........ ๐Ÿ˜ณ๐Ÿค suko iya abangarensu duniya sabuwa jinsu suke tamkar sun shigo wata duniyane domin basu da aiki itada hafsat se barci ga jakarsu acewarsu *inteesar* itake komi na gidan har ruwan wanka seta kai musu bandaki abindai abun tausayi๐Ÿ˜ญ ** ** ** da yamma yashirya tsaf ya yaje gidansu kai tsaye falon dad yanufa mom ma tana falon azaune kusa da dad yakarasa ya gaidasu cikin girmamawa suka amsa dad yace *Son se ramewa kakeyi mun tambayeka kace bakomi intayi wari maji koh? hmmm dad bazaku ganeba wlhy sontane ke dawai niya da zuciata ๐Ÿ˜ณazuciyarshi yafurta hakan amma afili seyace *Daddy bakomi kawai canjin yanayine murmushi kawai dad yayi yakawar da maganar dacewa jibi inason zamuje wani taro dakai a India kashirya yadan sosa keya tareda cewa to dad insha allahu zan shirya daganan zan duba kamfanonin dake indian itadai mom tana jinsu batace komiba tana daddanna wayarta washe gari suka shirya tsaf se india........ ** ** ** hajiya jimmalace zaune akan tabarma hannunta rike da mafici tana fifita iya akusa da ita tace *ni hajiya mijifa yafi sati hudu baya garinnan duk hankalina yatashi domin kayan abincinmu yakare wlhy niba damuwata mijinba aah yan kwabben dayake bani gashi yanzu se buga2 mukeyi wlhy ba wani kawo light nifa kin sanni dason kudi hajia jimmala ta kyalkyale da dariya tareda cewa *kumafa hkne nasanki idonki idon naira hajara me idon naira๐Ÿคฃto yanzu yakikeso ayi? to ai mafitar nake nema shiyasa na kawo miki maganar yazanyine nairori surinka hada kai adakina๐Ÿ˜‰ hajia jimmala takai mata hannu suka tafa * tace to mizai hana kikaisu yaran naki aikatau? LUV U ALL๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜ ๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI โœ๐Ÿป ๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘ BOYEYYE AL'AMARI ๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘ {1/7/2018} 7 :33 am ๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI โœ๐Ÿป *Masoyana ina tabbatar muku da bazarku nake taka rawata.........*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’‹ PAGE3โƒฃ6โƒฃ *****Zaro idanuwa hajara tayi tareda cewa *Hajiya kidena musu jam'i kinsan acikinsu akwai wadda ba diyataba sedai ki kaita dama wlhy na tsani nabude idanuwana na ganta agidana Hajiya jimmala tace *Kai hajara kuma knsan allah wlhy ita wannan wadda kika tsanar tafi wannan diyar taki kyau da hankali wlhy yarinyar kamar ita tayi kanta dan kyau ga mazaunai ta ajiye sekace diyar larabaw...... Iya taja wani uban tsaki * hajiya wannan ai cin fuskane kikemin toh ni wlhy gani nakeyi bawani kyaun data fita ga kyakyawata hafsat hajiya jimmala takwashe da dariya tareda cewa *haba hajara wannan me muni kmr asata arami arufe dan muni ai wlhy kima fadi gaskia ๐Ÿคฃ Iyakar shaka *iya* tagama shaka ji takeyi kmr ta kashe hajiya jimmala da mari ๐Ÿ˜ก itako hajiya dataga haka tace allah yabaki hakuri๐Ÿ˜œ sannan tadan sace daga bacin ranta tace *Hajiya ya maganar tamu wlhy nifa ko wani irin aikine akaita bawai ina kaunarta bane Hajiya jimmala tace *Aike nasanki da rashin imani toh amma hajara yakike gani in mahaifinta yadawo yazaki kare dashi in yaji abinda kikayi? Taba fuska tayi tareda cewa *toh ni ina ruwana iyakadai fadane kumafa abokan tafiyarshi sun dawo tin tini sunma bamu labarin cewar su bemajeba ke yanzu dai anata addu'arh allah ya bayyanashi Hajiya jimmala tace *toh amin dai Nan suka rabu akan zata samarwa *inteesar* din aikin zuwa jibi insha allahu ** ** ** Shiko Gogan akasar India sun halarci meeting din satin dady daya yadawo gida nigeria shiko *Annur* seda yayi sati uku agarin yagama aikace aikacenshi kana daga bisani ya cilla America domin yadubo companinshi na motoci dake kasar American adaddafe yake gudanar da aikinnashi amma zuciarshi cike take da kaunarta da begenta gashi yayi ragon azanci be amshi lambartaba ๐Ÿ˜ฅako wanni dare yakan kasa barci ga yawan mafarkinta yanayi tana miko mishi hannu akan ya taimaketa ๐Ÿ˜ญ duk ranar dayayi mafarkin yakan wuni jiki ba kwari gashi yadauri aniyar yin 3 weeks a America domin yanason ya kammala komi nashi...... ** ** kwance take afaffadan gadonta daga ita se pant da brezia ๐Ÿคฃtana danna wayarta cikin zullumi Amma ji takeyi yau gaskia bazata iya jurewaba ta kwammace ta kira lambar tashi taji ko aikin bokansu yayi kuwa Sadakarwa tayi ta danna kira yana kwance afaffadan gadonshi awani kayataccen gidanshi dake American daya daga cikin wayoyinshi dake kusa dashi tayi ruri dayake ba barci yakeyiba kawai aikin tunaninta yakeyi jawo wayar yayi yakara akunnen nashi kwantar da murya tayi cikin kissa tace *Ranka ya dade taurarona ya.... tana fara magana yadagota yagane itace cikin bacin rai yace *Ke dallah wacece nifa kinsan banson rashin hnkli Ranta yadan tsotsu amma tadaure tace *Sarauniyarkace me fatan haifa maka yara......๐Ÿคฃ Wani uban tsaki yayi tareda cewa *a gidan uban waye zaki haifamin yara to wlhy in kina mafarki ki farka domin nafi karfinki kuma wannan bashi bane karo na farko danake miki warning akan kidena kiran lambata toh wlhy wannan ne na karshe inba kinason na ballakiba toh ki kiyayeni kar kisake kiran lambata domin na tsani jin koda me kama da voice dinkine yana gama fadin hkn ya katse wayar........ Kuka ya kwace mata acikin zuciarta tace *Duk randa kashigo hannu wlhy sena rama...... Tana gama fadin hakan tamike tana sharar kwalla tanufi dakin mommy Bako sallama ta afka dakin tana kuka mommyn na zaune abakin mirrow tana kwalliya da sauri tamike tareda tarbota tana tambayar waya taba mata ita cikin kuka tace mommy aikinnan beyiba mukoma asake wani yanxu na kirashi ya wulakantani mommy ki agazamin....... ๐Ÿ˜ญ Mommy tace kiyi hakuri insha allahu zamu shirya mu koma dear kirinka hakuri ze shigo hannu sekin rama abinda yamiki Nan tashiga rarrashinta da kyar tasamu tahakura tareda alqawarin next week zasu koma gun bokan (Nidai nace allah yasa mufi karfin zukatanmu ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ‘๐Ÿผ) ** ** ** Tsaye take tanata faman kwankwasa tantsamemen get din takai minti biyar tana kwankwasawa Wani sojane yaleko Yana ganinta yaganeta domin tasaba zuwa gidan cikin girmamawa suka gaisa yabude mata get din tashigo nan suka rinka gaisawa da sauran sojojin da masu aikin gidan Wayarta tazaro takira lambarta tareda tambayarta ta wacce hanya zata shigo Daga daya bangaren tace *kishigo ta kofar kichin domin Hajiya tana falon kasa Tace *toh ai shiyasa na tambaya Ganinan zuwa Kofar kichin din tanufa masu aiki duk sunata hidima baba talatu tana zaune akan wata kayatacciyar kujera tana bada umarnin abinda za ayi Da sallamarta tashigo duk masu aikin sunata koro mata gaisuwa Baba talatu tace sannu da zuwa hajiya jimmala Gefenta hajiyar tazauna suka gaisa nan aka gabatr mata da kayan sha dana tanฤe2 Gaisawa sukayi sosai nan suka shiga hira kasancewar sudin kawayene tin suna yara Hajiya jimmala takai glass cup din bakinta tazuki sansanyar Hollandia kana tadaura dacewa *Nikam hajiya talatu da hajiyarku nason karin me aiki dana kawo muku Baba talatu tace *Kinsan hajiyata da wuyar sha'ani batason kazanta ko daya kinsan larabawa da kyankyami kingama dazu tagama fada akan lantana me gyaran falonta akan kazantarta tace yau ta hada kayanta ta bar gidannan wlhy ai ta tsani kazanta hakama yaronta bayason kazanta Hajiya jimmala tace *Wlhy hajiya talatu sekinga yarinyar akwaita da tsafta Baba talatu tace *Toh allah yasa ta yarda kin san hajiya da wuyar sha'ani Tace toh dan allah ki lallabota dai itama seta dangwali arziki Dariya tayi tace toh tareda mikewa tanufi hanyar dazata isar da ita zuwa falonnata kwance take akan kujera me zaman mutum uku hannunta rike da remote tana sanye da doguwar riga ta atampa me ratsin red da yello anyi mata aiki agaban rigar kayan ba karamin amsar jikinta sukayiba tayi matukar kyau dukda ba wani makeup me hayaniya tayiba Da sallamarta tashigo cikin falon Dan dagowa tayi tareda amsa sallmar zubewa tayi akan karfet din tace *Ranki ya dade barka da hutawa Yauwa ya aikin hope basamin kazanta pls kirinka matsa musu suna wanka sau uku arana Toh ranki ya dade angama shiru yadan ziyarci gun kafin daga bisani hajiya tace Wani abunne ko da wata matsalarne? tace ranki ya dade dama nace tinda lantana ta tafi shine nace koh kina bukatr wata jimmala tasamo mana wata kin sanni da kyama kuma kinsan *Annur* da rashin son kazanta inde tanada tsafta ba matsala akawota ๐Ÿ˜Œ Da fara'arta tace toh ranki yadade allah yakara girma Mikomin jakarnan tanuna mata jakar dake gefenta da yatsa cikin hanzari ta miko mata jakar Zugewa tayi tadauko dubu hamsin tamika mata tareda cewa kibawa ita watake dasuna? Jimmala take ranki ya dade Tace to kibata cikin giemamawa ta amsa tanata zabga godiya sekace ita aka bawa.......... ๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI โœ๐Ÿป ๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘ BOYEYYE AL'AMARI ๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘ {9/7/2018} 7: 35 am ๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIโœ๐Ÿป *Gaisuwar ban girma tareda alawa ga masoyanah๐Ÿ˜œina tabbatar muku da koh a ina masoyi yake yafi makiyi.........*๐Ÿ˜… PAGE 3โƒฃ7โƒฃ Mikewa tayi tanufo kichin din ta zayyanawa *Hajiya jimmala* yadda sukayi da hajiyar ta mika mata dubban kudaden da hajiyar tabada abata Jikina bari hajiya jimmala tanufi falon hajiyar ta sunkuya tafara zayyano dubban godiya ji takeyi tamkar tabiya mata hajji hajiyar yatsina fuska tayi tace bakomi kawai ta tashi tawuce (nidai nace me hali baya barin halinshi๐Ÿค”) Jikina bari hajiya jimmala tafice afalon tasanar da baba talatu insha allahu gobe gobennan zata kawota seda tayi sallar la'asar abangarensu baba talatu taci tasha tayi hani'an sannan tawuce harda guzurin wani tayi....... ๐Ÿ˜… ** ** Kwance yake afaffadan gadonshi yanata juyi abun duniya dukya isheshi ๐Ÿ™„ayau ji yakeyi feeling din nashi yafi na kullum ๐Ÿ™ˆ joystick dinshi ta tashi sosai babu abinda ke mishi gizo se surar jikinta dukda matan turawar dake kawo mishi hari amma sam bayajin feeling akan ko wacce mace se ita......... ji yakeyi kmr adire mishi ita amatsayin matarshi ayau akan gadonshi......... hmmmm wlhy dataji jiki.......๐Ÿ™ˆ Dan madaidaicin agogon dakin yabuga alamar karfe biyun dare.......... mikewa yayi yajawo durowa yaballi maganinshi yasha...... seda yadan kwanta kimanin 5 mnt sannan komi yafara lafawa agareshi....... kai tsaye mikewa yayi yanufi bandaki yadauro alwala yafito yashimfida dadduma yafara jero nafilfili..... addu'arh yakeyi allah ya mallaka mishi ita allah ya tsareshi daga zina........ seda yayi sallar asuba sannan ya kwanta wani barawon barcine yasureshi....... ** ** Bakina da hannuna bazasu iya misalta muku irin tashin hnklin da *Inteesar* tashigaba kwata2 tafita hayyacinta tazama tmkar zautacciya zuciyarta na mararin mahaifinta idanuwanta na bukatar ganinshi ๐Ÿ˜ญakullum bata iya barci ga gori da wulakanci da iya da hafsat suke mata..... ga aminiyarta *Khausar* tagujeta bata nemanta gashi iya bata barinta fita ballan tana taje taganta tagaya mata damuwarta taji dan dadi (itako khausar fushi takeyi da ita saboda bata kirataba kuma batazo gidansuba shiyasa tayi alqawarin bazataje gidansuba harse itace tanemeta saboda ita aganinta itace tadamu da *Inteesar* ita bata damu da itaba shi kanshi yaya ahamad yayi2 da ita taje takiya gashi yakai sau uku yana zuwa kofar gidansu anace masa batanan...... duk kaidinsu iyane da yarta hafsat) Yau made kmr kullum tagama aikin gidan takunce kanta adaki tanata zabta kuka kmr ranta zai fita.......... Sallama hajiya jimmala tayi nan iya tafito daga dakinta tana gyara zani tace maraba lale da hajaju....... suka shige daki iya tashimfida mata tabarma tazauna takawo mata ruwa me sanyi....... agefenta iyan tazauna aifa nan hajiya ta laburta mata ansamu aikin insha allahu da kudi me tsoka Rangaฤediyar guฤa iya tayi tareda mikewa ta taka rawa sannan tamikowa hajiya hannu suka tafa ji kake rasss.......... hajiya tace ahado mata kayanta su tafi takaita nan iya tamike cikin murna tashiga dakin nasu Tana kwance ta kudindine kanta idanuwanta sunci kuka kantane keta sarawa iya tashigo dakin wani uban duka tayi mata abaya afirgice tadago kanta hnklinta atashe takalleta idanuwanta sun zama tamkar gauta don ja Cikin tsawa tace *ke mike dan ubanki ki haฤo tsummanki agana masgo dinki ki fito ku tafi da hajiya jimmala Tsintar bakinta tayi tana cewa cikin sanyin murya *ina zamuje? Kai tsaye iya tabata amsa *gidan ubanki zakuje mara kunya kawai fitsararra...... nan tashiga hada kanta da bango tana zabga mata ashariya....... nan da jini ya fara zarya agoshinta.......seda hajiya taleko ta kwaceta dakyar....... aiko tace ko kaya bazata daukaba seda na jikinta kawai....... haka ta wanke fuskarta suka fito da hajiya jimmala itako iya se zaginta takeyi tana fadin saura inkinje ki nuna musu bakin halinki har suka fito suka tari keke napep *Inteesar* nayima gidansu kallon karshe gidan data fito gidan da farin cikinta ke ciki amma tarasashi nan da nan hawaye suka fara kai komo a kuncinta ๐Ÿ˜ญ Hajiya jimmala ce talura da hawayen datakeyi ta tsaida me napep din tareda cewa ki rufamin asiri kiyi shiru dan allah haka zamu shiga gidan dake kina kuka gaskia kiyi shiru Da kyar tasamu ta tsayar da hawayenta takoma kukan zuci...... ๐Ÿ˜ญwanda yafi na hawaye zafi Awani katafaren gida me keke napep din ya tsaya suka fito hajiya tabiyashi sannan suka shiga gidan Yanayin yadda inteesar taga gidan har get uku gashi ko ina inka gifta sekaga sojoji nan zuciyarta ta tsinke ta tabbatr da gidan yankankai aka kawota nanfa zuciyarta tashiga dukan tara2 tana kakalo kuka hawayen yaki zubowa sunayen allah kawai take jerowa azuciyarta....... hmmm bata ankaraba se kawai tagansu awani kayataccen kolido se gasu awani hadadden kichin kutsa kai sukashi cikin kichin din hannunta cikin na hajiya jimmala Yauma kmr kullum masu aiki nata hidima a kichin din suka shigo kichin din nan masu aiki suka fara gaidata suka sanar da ita baba talatu tana bangarenta Bangarennata suka nufa shima me kyau dashi yamafi gidan wani me kudin keruwa Da sallamarsu suka shiga falonta tana zaune akan kujera tana amsa wayar uwar gijiyarta suka shigo da sallamarsu suka zube akan karfet din falon Seda tagama wayar sannan tajuyo garesu suka gaisa da hajiya jimmala amma idanuwanta nakan *Inteeaar* kallonta takeyi sosai azuciarta tace ikon allah toko kamace dai......๐Ÿค” hajiya jimmalace tadawo da ita daga duniyar tunanin data afka *Talatu game aikin nakawo muku kinganta nan batajin jikinta akwaita da aiki Gaban *inteesar* yayi wani mummunan bugawa dataji ance game aikin wato aikatau aka kawota..... ๐Ÿค” Wata kaunartace tashiga baba talatu ta tabbata yadda taga yarinyarnan akwai wani *BOYEYYE AL'AMARI* atare da ita......... *Eh hajiya naganta kyakyawa da ita yasunanki? tafadi hakan tareda maida kallonta gun inteesar Cikin sarkewar murya tace * inteesar Masha allahu suna me dadi Hajiya jimmala tace *Yaza ayi kinsan gari na ruwa talatu ni ynxu saurima nakeyi Toh amma sedai hajiya tana gun oga kinsan in yana gari bata da time din kowa amma bari nakirata na sanar da ita......... tadauki wayarta ta danna lambobinta takara akunnenta bugu biyu ta dauka nan tasanar da ita Tsintar bakinta tayi tanacewa bakomi kuzu ku sameni abangarena afalon sama Da mamakin baba talatu tasanar dasu suka mike sukanufi falonnata da sallamarsu suka shiga Tana waya da shalelennata cikin nishadi da kewar juna Zubewa sukayi akasan karfet din tinda suka shigo idanuwan hajiya nakan *Inteeaar* kallon sani take mata kuma tanajin wani abu nabin dukkan ilahirin jikinta...... basu gama wayarba ta tsinke wayar tajuyo da kallonta sosai kan *Inteesar*...... gaisuwa suka shiga jero mata ajere........... amma ina duk ilahirin tunaninta yana kan *inteesar* waddda tuni ta sunkuyar da kanta itama tanajin wani abu nabin jinin jikinta......... ๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHI โœ๐Ÿป [12/7, 10:07 AM] mmn usman grp: ๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘ BOYEYYE AL'AMARI ๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘๐ŸŒ‘ {18/7/2018} 7: 59 am ๐Ÿ“šSA'ADATU BINTU ABDULLAHIโœ๐Ÿป *Kuyi hkrn rashin jina na 2 days abubuwane sukamin yawa............* *amma ina tabbatar muku kuna rainah.............*one love*๐Ÿ’– PAGE 3โƒฃ8โƒฃ Tunani takeyi tamkar ta taba ganin fuskarta amma takasa tunano inda tasanta........ Baba Talatuce takatse mata tunaninta cikin girmamawa tace *Ranki ya dade game aikin ankawo......... firgigit mommy tayi cikin sanyin murya tace *Okay Yasunanta? Baba talatu tace *Inteesar sunanta ranki ya dade Mommy takasa barin idanuwanta akan inteesar cikin sanyin murya tace *Ba damuwa talatu ki fada mata tsare tsaren aikinmu zan biyata dubu talatin awata Godiya suka shiga kwararo mata sannan suka mike tadauko dubu ishirin tamikawa hajiya jimmala nan da nan ta amshe tashiga kwararo godiya ....... har suka bar falon bata dena kwararo gafiyaba haka itama mommy bata dena kallon *inteesar* ba wani irin abu takeji game da ita amma kash takasa gane menene........ ** ** ** Zaune yake agaban *khausar* yanata kuka sekace karamin yaro dukya rame yayi baki......... Cikin kuka yace plx sister ki taimakamin kije gidansu plx sister jia ma naje ancemin bata nan wlhy zan iya mutuwa inna rasata plxx help me๐Ÿ˜ญ Mamakin yadda yaketa kukanne dukya kashe mata jiki nan da nan itama hawaye suka fara ambaliya a idanuwanta *plx Brother kayi hakuri zanje insha allahu Godiya yashiga kwararo mata cikin jin dadi mikewa tayi tanufi bangarenta tadauko mukullin motarta taja tabar harabar gidan Kai tsaye akofar gidansu tayi parking tafito tashiga gidan Tin daga zauren gidan data gani hakan yasa taji wani bakon yanayi yaziyarceta domin bata taba ganin gidan ba almajiri ko dayaba se yau...... da sallamarta tashiga cikin gidan Iya na zaune atsagar gida tanacin naman kaza ๐Ÿ˜‚ita kuma hafsat batama kwana agidanba kwatsam taji sallamarta amsawa tayi cikin wani yanayi๐Ÿ™ˆ Karasowa tayi ta gaida iyar cikin girmamawa Amsawa iyar tayi tareda tambayarta yagida? Ta amsa da lafiya qalau Aiko se iya tayi charab tace *Hmmm ke yar nan aiko kawar taki bata gida taje yawonta na karuwanci Cikin sauri tadago tare dacewa *wani irin karuwanci Nanfa iya tashiga share hawayen munafurci *hmm kibari yar nan ai cikima tayi shiyasa tagudu tabar gidannan taje gun wanda yayi mata cikin gashi sanadin hakan ubanta yagudu yabarmu agidannan...... Jinta kawai *Khausar* takeyi domin tasan duk karyane toh amma ina taje ita *Ukti* dinnata๐Ÿค” gaba daya khausar tashiga wani yanayi nan tashiga rokon iya harda kukanta akan tagaya mata gaskiar lamarin......... amma kash iya tadage akan ciki inteesar din tayi......... ahaka khausar tabaro gidan badan ta yardaba kai tsaye makwabtan su iya tanufa wani gida me kallon nasu da sallamarta tashiga gidan Wata tsohuwa na tsugunne tana alwala ta amsa sallamar tareda binta da idanu gaidata khausar tayi tsohuwar ta amsa tareda bama khausar kujerar zama khausar tazauna tafuskanci tsohuwar tace mama nasan baki sanniba amma dan allah mama ko kinsan wata yarinya anace mata inteesar Tsohuwa tace toh toh

Chapter 8 of 19