Futowa hafsat tayi da uban kayan kmrma duk kayannatane sukayi datti domin cike da katuwar jaka
Tawatsamin kayan tana kurma uban ashar *Narantse da Allah kikayimin wankin iskanci senayi miki Rashi mutumci domin wlhy sekin sake wani wankin yar iska kawai mebin maza๐
Har zuciata naji Kalmar tadokarmin zucia hawaye yashiga sirnanomin
Iyama ta tashi takwasomin nata wankin itama tana zazzaga matsifa *To dangin mayu atashi ayimana wanki kuma yau zaki gamashi Allah yasa munafuncinki yakaiki ki fadama Mlm wlhy dana lahira yafiki jin dadi
Tadungureni haka itama hafsat tadungureni tana zabgamin ashar
Natashi nashiga yin wankina ko kayan makarantr ban cireba๐ญinayi ina kukan maraici๐ญ
Itako hafsat tashiga yin rawa cikin wakar gwanja tana gwaso uban shoki๐๐ป๐๐ป
ita kuma iya nacewa kaga yata yar albarka yar arziki wlhy yi rawarki daga dunia se Kaduna๐ kai amma da Adam a zango ze ganki daya daukeki kirinka mishi rawa wannan rawa haka ๐
( Nikaina wani yanayi nashiga ji nakeyi tamkar nima nataka rawar ๐)
Kwance yake amma wani Abu nayi mishi yawo azuciyarshi wani irin Abu yakeji yana taso mishi na kishinta da kaunarta agaskia se ynxu ya tabbatar dacewa son yarinyarne yayima zuciarshi shigr bazata
Dare yatsala amma yakasa barci komi bayayimishi dadi fadi yakeyi azuciarshi * Meye hadinsu dazaizo yatafinmin da ita kai ya Allah kasa ba sonta yakeyiba
Cikin damuwa yake fadin hkn
Gaba daya komi yakwance mishi zuciarshi na mishi tsuya na kishinta tmkr zuciarshi zata tarwatsewa
Ayau duk kwarewar barci asata yakasa satr *ANNUR* domin har ciwan kai yakeji
Se alokacin pos dinta daya tsinta tafado mishi wadda yamanceta amotarshi
Cikin daren yafito farfajiar gidan yalatsa mukullin motar yabude murfin motar me zaman banza nakasa da direba yadauko pos tin nata yana juyawa ahannunshi harya isa dakin kan gadonshi yafada yana shinshina pos din nata ahnkli yabude zip din pos din yadauko katuwar wayarta wadda dagani kirar iPhone ce dannawa yayi yaga ba passport yabudeta kai tsaye gallery yashiga hotunanta yafara arba dashi Wanda tayi fitinannan kyau tmkr dawisu tana sakin murmushi yayinda wushiryrta tafito dimples dinta suka lotsa alokaci daya setayi wani ja'irin kyau tamkar Zara acikin wata
Manna wayr yayi tareda tareda daga hannun shi sama yana rokon rabbih yamallaka mishi zuciarta
Nan da nan yabude tashi wayr yashiga aika duk wani pics nata
Seda yadade yana kallon pics dinnata kafin daga bisani yatashi yashiga bathroom yadauro alwala yashiga nafilfili dukkan rabin addu'arshi ta danganci *INTEESAR* ne domin dukkan komi nashi aynxu ya mallaka matane
Seda yayi sallar azubahi sannan ya kwanta yashiga yin barci me cike da mafarkanta sewani murmushi yakeyi dukda acikin barci yake hakan be Hanashi bayyana murmushinba dukda besan yanayi ba (Naso ace mmn abdullahi wato Kakus taga wannan murmushi๐)
Seda takai asuba tana wankin gashi Mlm be shigoba amasallaci yakwana yana karatu domin dama yakanyi hakan wani lokaci
Seda naci wankin tmkr zan mutu ko banda kowa adunia๐ญidanuwana har lumshewa sukeyi amma ko tausaya mata iya basuyiba domin shigewa sukayi suna sharara barcinsu
Seda nayi sallar subhi sannan nasamu na kwanta ina lazimina da carbi ahannuna nakwanta akan tabarma domin hafsat takwanta akan yar katifar
Harna kwanta natashi nadauko jakata domin na dauki wayata naduba time tareda duba miss calls dannasan *Ukti* zata kirani kar taji shiru
Yan dube2 nashiga yi domin kuwa nan pos tace daukeni inda kika ajiyeni ๐ณ
Nan nashiga dubawa ina fadin innalillahi wa'Inna ilairraju'un domin bala'in *Ukti* nakeji dannasan nabani๐๐ฟ
Duk iya duba wata har wajan danayi wankin bangankiba........ ๐ณ
๐SA'ADATU BINTU ABDULLAHI๐ค๐ป
๐๐๐๐๐๐๐๐
BOYEYYEN AL'AMARI
๐๐๐๐๐๐๐๐
{21/4/2018} 8:34
๐SA'ADATU BINTU ABDULLAHIโ๐ป
PAGE2โฃ6โฃ
Duk nabi nabircike domin nasan *Ukti* seta kusa cinyeni yau
Hakanan nagaji da nemana nakoma na kwanta ina addu'ar Allah yasa ba bacewa tayiba
Karar wayrshiceta tasheshi daga haddadn barcin dayakeyi tare d dumbin mafarkanta cike da shaukin so d kauna
Jawo wayr yayi yana magagin barci bema lura da sunan me kiranba yakara akunne
Daga dayan bangaren cikin so da kauna da iya kissa tace hello dear
Jin muryar tatane bema gama gane wake mgnba yace cikin isa da muryr barci pls wake mgn?
Daga dayan bangaren taji zafin jin duk da voice dinta amma yanason ce mata be gane me mgnba
Amma kasancewar ba ayin fushi da Wanda ake so tace cikin kissa haba my only nicefa wadda kake kauna
Cikin Bacin rai yace domin yadago me wayr ke banason rashin hnkl bana hanaki kirana da safeba kuma ubanwa yace miki ina sonki
Nan hawaye yafara bin kuncinta tace cikin so da kauna haba my alawa pls kasoni wlhy in babukai bazan iya rayuwaba ๐ฅ
Cikin jin haushi yace ke jahilar inace wlhy kinci sa a kin kirani ina mafarkin abar kaunah yau dana nuna miki ni wanene kuma last warning wlhy karki kara kirana
wlhy inma kina mafarki ki farka kona rasa matr aure bazan aurekiba mara hnkli kawai๐ณ๐
Yana kaiwanan yakatse wayr ranshi abace yana karajin tsanar yarinyr har can kasan hat dinshi๐
Wani irin kuka tashigayi tana rantse rantse wlhy *Annur* kai nawane kai mijin *fa'iza* ne wlhy kai nawane ni kadai kmr yadda nakasance an haliccenine dan kai
Tana kaiwa nan tarushe da kuka
Kukannatane yajawo hnklin *haji samira* wadda take kan daining table tanayin brkfst aguje tarugo tafado dakinnata tatura kofar tana fadin sha lelena waye yatabaminke meya sameki fadamin inji
Nan takara rushewa dawani uban kukan tana kundumo ashar mum wai *Annur* haryana fadamin yana mafarkin wata yar iska matsiya ciyar yarinya mum ni wlhy so nake akasheta dazan ganta wlhy sena kasheta takara rushewa da kuka
Wani irin tashin hnkli *hajia samira* tashiga tazaro uban ido daman idon yasha uban zara2 gashin ido tana fadin nashiga uku ni samira kadafa kwabata tayi ruwa tafadi hkn tare da karasawa tarungumeta
Itako *Fa'iza** se uban kuka takeyi
*Hajia samira* taci gaba dacewa karki damu inde boka dan tatsitsi se kaifin aiki da bakaken aljanu wlhy inde yana raye sekin aure *Annur* kin fanjama da dukiarshi kuma ki haifa mishi yara kizama fitilar gidan dan shugaban kasa kuma babban mutum wlhy sekin aureshi kisa aranki
Murna *Fa'iza* tashigayi tanajin dadin yadda mum tayi Mata promise domin tasan wacece mahaifiyar tata itame fadi da cikawace
Nan sukayi shawar sati nasama zasuje garin sakkoto inda boka dan tatsitsi yake can cikin wani kauyen sakkoto cikin wani dajin bameyi
Kwance yake adaya Daga cikin kujerun dake katon falonshi Wanda yaji kayan alatu amma tunaninta ya addabi zuciarshi ji yakeyi tmkr zuciarshi tafito fili don sonta
Daga wayarshi yayi yakira kanwar tashi tare dace mata tazo yana karamin falonshi
Daga daya bangaren tace to ya *Ahmad* dama tashirya tsaf shirin zuwa gyaran kafa domin yau weekend ne tana sanye da Riga da siket dinkin yayi matukar yimata kyau seta fito tmkr ba itaba tayane kanta da mayafi Marun kasancewar dama akwai ratsin Marun ajikin atmpr haka takalmintama marun ne
Ta iso bangarennashi kai tsaye karamin falonshi tanufa cikin sallamarta
Yatashi zaune tare da amsa mata sallamar yayi mata izinin shigowa
Tashigo tatsugunna tagaidashi cikin ladabi ya amsa mata tazauna adaya daga cikin kujerun domin ganin yadda yanayin dan uwannata yacanza
Cikin wani yanayi tace Ya *Ahamad* duk ka rame wlhy jia muke mgn da mum da dad suke cewa kwana biyu dukka canza kmr bakaiba dukka rame mum tace ta tmbyeka kace mata bakomi wlhy Ya *Ahamad* duksun Shiga damuwar ganinka awani yanayi nadaban and nima kasani adamuwa wlhy ๐ญ
Taja dogon numfashi kana takara raunana fuska taci gaba da fadin pls Ya *Ahamad* dan girman allah kafadamin damuwarka pls
Yace cikin wani yanayi wlhy swt sis ina cikin damuwa kuma kece kusan maganin damuwata
Zaro idanu *Khausar* tayi tace ni๐ณ Ya *Ahamad*
Yazamo daga kan kujerar yayi zaman dirshan akan kafet idanuwanshi sukayi rau2 yaci gaba da fadin pls swt sis taimakamin zakiyi pls wlhy ina cikin wani hali..........
*Kubini asannu dan jin yazata kaya*๐
LUV U ALL๐๐
๐SA'ADATU BINTU ABDULLAHIโ๐ป
๐๐๐๐๐๐๐๐
BOYEYYEN AL'AMARI
๐๐๐๐๐๐๐๐
{23/4/2018} 7:55
๐SA'ADATU BINTU ABDULLAHIโ๐ป
*Allah yataimakeki mmn shaheed nima kina rainah*๐น๐
PAGE2โฃ7โฃ
Ya matso daf da ita yakamo hannayenta yaci gaba da fadin *Sis nasan kinason farin cikina nasan kinason naci gaba d rayuwa nasan kinason walwalata pls my sis kisamaminsu
Khausar takara bude kunnuwanta danjin me yayannata yakeso agareta tace *Ina bukatr ganin walwalarka da nishadinka da farin cikinka saboda kaima kanason farin cikina pls Ya Ahamad ka gaggauta fadamin ta yadda zanyi nasamo maka duk wadannan abubuwan daka fadi wlhy zan sama makasu
Yadaura dacewa *Ukti*dinki itace farin cikina dan girman Allah kisan yanda zakiyi namallaki zuciarta wlhy inasonta sonta ta jinin jikina yake
*Khausar* tadago takalleshi cikin mamakin yadda duk yayannata ya susuce akan *Ukti* cikin farin ciki tace *Wow Ya ahamad naji dadih domin wlhy Ukti matar aurece wlhy Ya Ahamad ka aureta kahuta domin batada matsala gason addini am happy Ya ahamad๐
Cikin farin ciki *Ahamad* yace *yauwa my lovely sis wlhy uwa uba gata da kyau kmr balarabia
Murmushi *khausar* tayi domin yau tana cikin farin cikin *Ukti* zata zama matr yayanta
*Ahamad* yadaura dacewa kinga lovely sis kiyi yadda zakiyi nasamu shiga azuciarta knji
Tace *insha allahu big brother ai kamasa aranka kasamu Inteesar
Wani irin lallausan murmushi yasaki me dauke da wani ni'imataccen farin ciki yace *Wow dole nayi miki tukuicin wannan alqawari naki
Yamike tare dacewa kijirani ina zuwa
Murmushi tabishi dashi tareda hango rnr aurennasu
Kai tsaye bedroom dinshi yanufa yajawo durowar gadonshi cike take da kudi bandir2 harda kudin kasashen waje yadauko bandir biyu
Tana zaune afalon yafito yamika mata kudin dubu Dari biyu
Yadaura dacewa kiyi manage kiyi saloon
Ta amsa cikin murna tare dacewa big brother jiafa kayimin trnfr a accnt dina ngd Allah yabaka *Inteesar*
Cikin jin dadin addu'arta yace amn my sis
Tamike tareda dura kudin ajakarta
Yace ina zuwane haka?
Tace zanje saloon ne awankemin kafa
Yace ke kadai zakije?
Tace zan bia ta gidansu *Ukti* muje tare inata kiran wayrta dama tin jia bata dauka bansan meya faruba
Yace okay Allah yasa tana lpy
Tace amn
Yace sis inason itama ayi mata saloon din awanke mata kafa zanyi miki trnfr din 1 milyon ynxu zakije alert inbe isaba kiyimin mgn nakara miki pls agyarata sosai
Tace angama big brother insha Allah za a gyarata sosai
Yace yauwa adawo lpy
Tace tanks dan uwa
Taje tayima mum sallama tayi mata fatan dawowa lpy
tafito harabar gidan tashiga farar mota me azabar kyau
Me gadi yawangale mata get tafita tanajin nishadi azuciarta
*** *** ***
Wanka yayi yashirya tsaf cikin kananan kaya kasancewar yau ana zafi
Farar T-shert ce tareda bakin jeans wanda sukayi mishi matukar kyau agogon danyar azurfa yasa atsintsiyar hannunshi yayi matukar fito datsantsar kyaun hannun nashi
Nanfa yafito tmkr wani gwold domin ko makiyi ze tabbatr da guy din me tsadane
Gashin kanshi yayi baki wuluk sajen dayayima fuskarshi kawanya yakwanta yayi luf hnklinshi akwanshe
Fuskarshi na fitr da Annuri yafito se zuba kamshin tsadaddan turarenshi yakeyi
Futowa yayi hannunshi dauke da mukullin motarshi
Kai tsaye bangaren mum dinshi yanufa sallama yayi ababban falonta
Kwance take akan kujera me zaman mutum uku wato 3siter sanye take da doguwar riga marun tayane kanta da black din gyale kasancewar akwai ratsinn black ajikin rigar fuskarta dauke da glass fari tayi matukr haduwa tmkr dawisu
Tana kallon film din larabawa daka ganta zaka tabbatr film din yana nishadantar da ita domin har fara'a takeyi tana nishadi
Sallamar tashice tasata dawo da hnklinta kan kofar shigowa tareda amsa mishi sallamar tana fadada fara'arta
Shigowa yayi yatsugunna yagaidata
Ta amsa cikin jin dadih tare da mishi izini yazauna
Zama yayi tare dace mata (cikin harshen larabci)
Mum Yakika tashi?
Tace lpy qalau son wai kunyi waya da dad dinka kuwa jia yayi tafia jahar legos zasuyi meeting
Yace no mum nibansanma yayi tafiaba
Tace ai kasan abazata tafiar tazo mishi
Yace okay Allah yadawo dashi lpy
Ta amsa da amin
Tacigaba dacewa wai ya mgnr shugowar motocin dakayi oder ne daga America?
Yace ai mum inajinma senaje inason bude wani company ne na hada motoci dadai company dayawa nakeson budewa na hada abubuwa
Tace Kai my son duk company dinka na America basuyi maka yawaba gaskia yakamata abarsu haka
Yace toh mum addu'arki nakeso
Tace Allah yataimaka
Yace amin
And mum inason insha Allah zan karasa saudia in duba Mum dina tacan
Tayi murmushin jin dadih tace wow gaskia daka gyauta son Allah yataimaka
Yace amin mum nizan fita
Tace Allah yatsare
Yace amin tareda mikewa
Haryakai bakin kofa mum tace son inka dawo inason mgn dakai
Yace tohnm mum
Yafito yashiga bakar motarshi haryayi mata key seya tuna yabar pos din tata adakinshi kuma itace tushen fitr tashi
Komawa yayi yadauko pos din tare dasa wayar tata aciki
Yafito yafada motar tini me gadi ya wangale mishi get din yana shararo mishi addu'ar Allah yakaishi lpy
Kudi bandir ukku yan dubu2 yamikama me gadin tare dacewa kuraba dukkanku masu aikin gidannan
Jikinshi narawa ya amsa tareda kwararo mishi godia
Jan motar tashi yayi kai tsaye layinnasu yanufa
Adaidai kofar gidansu yafaka motar fitowa yayi yaharde hannayenshi akirjinshi
Seda yakai minti biyu atsaye
Can wani almajiri yafito
Kiranshi yayi da hannunshi AL'AMARI yazo
isowa yayi gurinshi tareda tsugunnawa yagaidashi
amsa mishi yayi tare dacewa *dan Allah yarinyar gidannan zaka kiramin
Almajiri yace toh yallabai wacce aciki๐ค
*Annur* yadanyi tunani can yace *Inteesar*
Almajirin ya wangale baki tareda cewa toh yanufi cikin gidan
Iya na zaune tana saka danwake hafsat na zaune da gajeran wando ajikinta da yar riga iya mono tana latsa wayrta nikuma ina zaune ina wanke kwanonin da aka siya danwaken ina kikkifewa
Sallama almajirin yayi tareda cewa wani me mota yana sallama da *Inteesar*
Atare dukanmu muka dago hadda iya itama hafsat duk suka zaro idanuwa๐ณ
Iya taja wani uban tsaki tare dacewa...........
*Takunce me bukatr shawarwarinku*
*ina jiran shawarwarinku akan lambata 09036421950*
*Nagode da kaunah*
*Masu nunamin so karku damu ina kara tabbatr muku kuna rainah*๐
LUV U ALL๐๐
๐SA'ADATU BINTU ABDULLAHIโ๐ป
๐๐๐๐๐๐๐๐
BOYEYYEN AL'AMARI
๐๐๐๐๐๐๐๐
{27/4/2018} 1:23 pm
๐SA'ADATU BINTU ABDULLAHIโ๐ป
*Masoyana da wadanda nasani d wadanda bansaniba ina tabbatr muku kuna rainah*๐
PAGE2โฃ8โฃ
Ke dan ubanki yan iskan naki har gida suke biyoki dan tsabar iskanci๐ก
Hafsat ta amsa dacewa hmmm Iya ai dande ina rufa mata asirine amma wlhy nataba ganin wani dan iska yadauketa amota sunje Hotel๐ณ
Dagowa nayi arazane ina kallon Hafsat
Hafsat tamatso kusa dani ta dunguremin kai tare da fadin ke dan ubanki karya nayi kika saukemin na mujiya๐
Iya tahau tafa hannu innalillahi ke Hafsat Ashe iskancinnata haryakai haka amma ba laifinta bane laifin malam ne domn shine yadaure mata gindi gashi wataran zata kwaso mana abin kunya ๐
Almajiridai be wuceba yana tsaye girgiza kai yayi domin yasan halinsu yan Sharrin da kuma yadda suke takura mata
Iya ta kalli inda almajirin yake tace dan ubanka kaima kaje kace bazata zoba
Almajiri yajuya sululup2 yawuce abinshi domin yasan bala'in hajara bakowa tabariba kuma agaskiya baze iya tunkarar babban mutum hakaba yace ance bazatazoba dan haka yawuce abinshi
Shidai yana tsaye harya gaji da tsayuwar azuciarce yana tunanin ko batananne
Dai2 lokacin yaga wata farar mota tafaka akofar gidannasu fitowa tayi idanuwanta suka sauka akanshi azuciarta tace wow guy dinnan ya hadu kmr aturai๐
Hanyar gidan tanufa tana tafe tana waiwayenshi
Da sallamarta tashiga gidan
Ina tsugunne ina jin bakin cikin wannan bakin Fentin da iya sukeson shafamin sallamartace tasani dago kaina nasauke mata dara2 idanuwana
Nan iya tashiga wangale baki (domin iya akwai son kudi)
Tana fading lale2 sannu da zuwa hajia khausar
Cikin sauri tamike jikinta narawa tabata kujera
Khausar tagaidata tare dacewa no iya basena zaunaba ina saurine
Takalleni tare dayimin murmushi
Iya taje tadebowa khausar ruwa akofin malam๐tace hajia ga ruwa
Khausar tace ngd iya nasha ruwa banjin kishi๐ pls alfarma zakiyimin
Iya tawangale jajayen hakoranta tare dacewa haba hajia aiki fadi ko menene anyi miki mu asuwa za a nemi alfarma garemu
Murmushi *Khausar* tayi tareda fadin *Ukti* nakeso tarakani zanje saloon๐
Jiki na rawa iya tace haba wlhy bkm hajia adawo lpy
Takalleni tare dacewa ke mike kutafi maza adawo lpy (Shegiya naira)๐
Namike nawanke kafada domin daman ban jima da fitowa daga wankaba nafada aikin wanke2 ๐
Nashiga daki nacanza kayana nasa atampa doguwar Riga me ratsin red and blue nasa hijjab blue da takalmi blue
Banyi wata kwallia ba powder kawai nashafa nasa man baki nafesa turare
Nafito se zuba kamshi nakeyi
*Khausar* takalleni tasakarmin murmushi
Ita kuwa *Hafsat* wata uwar harara tawatsamin ๐cike da bakin cikin kyaun da Allah yayimin
*Khausar* tazuge Jakarta taciru dubu hudu tamikama iya
Nanfa iya ta fisge kmr dambe๐tashiga kwararo uwar godia harda hawayen muna funci wai takai shekara hudu bata rike dubu biyu tata takantaba๐
Itadai Khausar kallonta kawai takeyi takara Ciro dubu biyu tamikama *Hafsat*
Iya tazaci ita ake bawa har tana tuntube garin amsa๐
Se itama *Hafsat* tayi wuf kmr zata ture uwar ta amshe bako godia๐ฌ
Tana fadin kai iya nifa banson haka haba anfa baki naki kina neman kwace nawa ta gatsine hanci๐
Itadai *Khausar* daria abun yabata domin dabadan *Ukti* ba datayi musu daria
Kamo hannuna tayi muka fito
tacemin waike *Ukti* ina wayarkine inata kiranki
Nace ammm....... Eh ..... Tana ......
Dai2 lokacin muka fito kofar gidan idanuwana suka sauna akan fuskarshi
Shine dalilin dayasa nakasa bama *Ukti* amsa koda dama bansan mezance mataba
Yana tsaye ya harde hannyenshi akirjinshi domin yau yadau aniar in be gantaba koze kai dare seya zauna zaman jiranta
Kallonta yashigayi har yana neman rasa hnklinshi domin shi ma'abocin son hips ne ajikin mace segashi ita dukda zumbulelen hijjab din datasa be hana aga hips dinta ba domin ko ahijjab bayyana kamshi yakeyi
Azuciarshi yakara godia ga uban gijin dayayi wannan halittar me tsananin kyau
Nan dunkulelen sonta ya mulmula akahon zuciarci
Acikin yan dakiku yagina mata katon gida me dauke da kayan shakatawa tareda falo 10 acikin babbar birnin zuciarshi๐
Kokarin dauke kaita nayi domin kallon nashi danayi yasa naji wani irin yanayi me wahalar misaltuwa
Kara tsugunnar da kaina kasa nayi muna kokarin wucewa Khausar narike da hannunta
Cikin sanyin murya yayi mana sallama
Muka amsa amma nakasa dagowa nakalleshi
Suka gaisa shida *Khausar* yace pls dan Allah inbazaki damuba ki aramin 2 mnt mana inason mgn da ita. Yafadi hkn tare da nunani da yatsa
Kwarjininshi duk yafi yacika gurin da baki dayan Layin๐
*Khausar* tace cikin fara'arta dukda batasanshiba ai bkm gatanan. Tamatsa tabamu guri tashige motarta
Yakalleni tareda sakarmin fara'arshi yace toh ina wuni ni nagaidaki
Nadan karayin kasa da kaina Nace ai karami shike gaida babba kaga ni zan gaidaka
dadinta mgnr nata tadaki dodon kunnenshi domin har zuciarshi yaji mgnr
Yace ai naga kina nuna kmrma baki taba ganinaba and kinamn rowar face dinki
Azuciata Nace kaji mutum to nasankane inbanda Daka bugeni ๐ค
Amma afili nayi murmushi kawai
Ya gano banason yawan mgn dukda shima miskiline amma yatsinci kamshi dason yimin mgn (shaukin love)๐
Yace okay ammm...... Damade ajiyarki Nazo kawo miki
Nadanyi Jim nadago nakalleshi da lumsassun idanuna nace ni ๐ณwlhy ban baka ajiaba
Yace hmmm kwantar da hnklinki irin wannan zaro idanu haka toh maidasu pls kar ayimin asararsu
Nadanyi murmushi azuciarta na maimaita kar ayimin asararsu kuma๐ค meyake nufi da hakan?
Yace Inadan zuwa
Yabude murfin motarshi nakusa da direba
Juyowa naga yayi nan nakara kasa da kaina domin banason mu hada ido inajin wani yanayi
Kusa da ita yamatso tareda mika mata pos din yace amsa ajiarki
Nadago da idanuwana mezan gani senaga pos dina ๐
Nasa hannu na karba tareda tunanin toh ina yasamu
Kmr yasan abinda nake tunani
yayimin bayanin yadda akayi yasamu pos din
Naji dadih nayi mishi godia
Yace no bkm amma ina bukatr alfarma agareki
Cikina yaduri ruwa nazaro idanu
Wace alfarmar ? Kuma kaga *Ukti* tana jirana
Yace yeah nasani amma pls kibata hkr kibani only 1mnt sena fada miki
Nagyara tsayuwata nadaga mishi kai
Yace bantaba tunanin haka kikeba banyi tsammanin haka halinki yakeba
Nazaro idanuwana๐ณ bakina na rawa nace.........
*Masuyimin fatan alkhairi ngd masu nunamin hassada irinsu ta annabi (Khadijat) toh kumade ngd*๐
LUV U ALL๐๐
๐SA'ADATU BINTU ABDULLAHIโ๐ป
๐๐๐๐๐๐๐๐
BOYEYYEN AL'AMARI
๐๐๐๐๐๐๐๐
{9/5/2018}1:49pm
๐SA'ADATU BINTU ABDULLAHIโ๐ป
*Dumbin so da kauna nadauka namika muku kyauta soyayyarku a blood dina take YAN GRP DIN BOYEYYEN AL'AMARI FANDS ngd da kaunah rabbih yakara mana dankon LOVE*๐๐
PAGE3โฃ0โฃ
Yana shirin Yatarwatsa zuciar jarumin
tareda addu'ar Allah ya mallaka mishi zuciarta
Toh muma zamu saka a addu'ar tareda fatan Allah yabaka *INTEESAR* amin
Acikin yan kwanaki biyu *Annur* ya susuce yafita ahayyacinshi domin hatta cin abinci yagagareshi tunanintane abincinshi kallon pic dintane mahadin gishirin numfashin shi gaba daya yazama bashida abokin hira se kallon hotonta
tin mom tana tasashi gaba tana tmbyrshi abinda yake damunshi amma kullum shiru ba amsa kullum amsar dayace bakomi
Gashi wannan karon alhaji yadade akasar waje be dawoba
Gaba daya ita kanta mom dukta rude tafita ahayyacinta har wata rama tayi tilon shalelenta ba lafia domin itadai gani takeyi tmkr bashi da lafiane ๐ญ
*** ***
SAUDIA
*** ***
Sanye take da milk din doguwar riga tasa baby hijjab baki tayi matukar kyau amma fuskarta cike take dam da damuwa
Ahnkli take taka matattakalar kmr me ciwon kafa
Tana takowa ahnkli tasa kafarta ana hudu nanfa tazame tafadi sedai karar faduwarta akaji
Karar faduwar tata tajawo hnklin masu aikin gidan Da gudu suka rugu ganinta akasa yatada hnklinsu
Dasauri wata yar dattijuwa takaraso cikin hanzari ta tallafota tana ihu
Jin ihun nasu yatasheshi daga barcin dayakeyi domin yau weekend ne yana gida
Fitowa yayi cikin hanzari akwance yaganta male2 rai ahannun Allah dasauri yakarasa gareta yana kiran sunanta Habibaty pls kitashi karki barni๐ญ
Sungumarta yayi yasa akafadarshi
yafita harabar gidan cikin hanzari sojojin dake tsaronsu daya daga cikinsu yazo yabude musu daya daga cikin motocin gidan nanda nan yasata amazaunin baya yadaura kanta acinyarshi yanajinta ko numfashi batayi cikin hanzari sojan yashiga yaja motar
Awani katafaren hospital suka faka motar tsayawa lissafa kyan hospital din bata lokacine domindai agaskia seda nasaki baki domin asibitin yakeru
Dasauri yaballe murfin motar yafito yauko jiran abude mishi beyiba yasun gumota cikin hanzari yashiga cikin asibitin da ita
Dai2 lokacin Dr khaleed yafito daga tiyata nan sukayi ido hudu cikin hanzari aka amsheta akayi emergency room da ita suka shiga suka fara bata taimakon gaggawa
Hankalinshi atashe yake shi kadai yake sharce hawaye wani nabin wani domin bayason yarasata kmr yadda suka rasa farin cikinsu wato HUM@IR@H yanada tabbacin damuwar rashin HUM@R@H itace silar faduwar matar tashi yarasa yaushe masoyiyar tashi zata cire dmwr wadda takomaga mahaliccinta ๐ญ
Kuka yakeyi tmkr karamin yaro azuciarshi yana addu'arh Allah yasa kada masoyiyarshi tabarshi domin bazai iya rayuwa babu itaba
Duk iya kwarewar Dr khaleed aiya aikin likitanci awannan fannin abin yaci tura domin duk iya yinshi yakasa dawo da numfashinta ๐ญkwata2 tadena motsi
Cikin hanzari Dr khaleed yafito yana sharce zufa
Da hanzari Alhaji Muhammad yanufoshi yana tmbyrshi ya jikinnata nasan ta tashi ko Dr pls kacemin ta tashi? tmbyrshi yakeyi tmkr zautacce
Cikin kwantr da ahnkli Dr khaleed yace karka damu ercalency pls kakwantar d hnklinka zata tashi yanxu zan kira wani Dr ibnu ma'azzam ne yataimakamin adawo da numfashinta (cikin harshen larabci suke magana)
Girgiza kai kawai yayi yana zubarda hawaye
Dasauri yadanna lambobin Dr ibnu mu'azzam yakirashi tareda rokonshi yazo cikin hanzari
Cikin yan mintoci ya iso asibitin fuskarshi sanyeda glass Dan dattijone domin akalla zaikai 40 years farineshi Sol balaraben usul
Yana isowa suka dukufa awurin kokawar dawoda numfashinta amma kash abunya gagara
Akarshedai suka gane tariga tarigamu gidan gaskiya.....
Kuka sosai Dr khaleed yakeyi Dr mu'azzam nabashi hkr shi kanshi Dr khaleed besan yazaiyi wurin tarbar Alhaji Muhammad dawannan zancenba
Dr ibnu mu'azazam ne yayanke shawarar tunkararshi
Da sallamarshi ya iso Inda yake yanata safa da marwa
Daga ganin yadda fuskarshi take cikeda damuwa hkn ya tabbatrwa da alhaji Muhammad ba lafiya Dan haka yayi saurin tmbyrshi tamutu koh?๐ญ
Nasiha Dr ibnu mu'azzam yashiga yimishi
Girgiza kai alhaji Muhammad yakeyi cikin wani yanayi numfashinshi na neman daukewa yace inta mutu kawai kafadamin karka damu
Daurewa Dr yayi yace muyi hkr Allah ya amshi kayansh....
Begama jin abinda yake fadiba duhu yaziyarci idanunshi yafadi akasa sumamme........
LUV ALL๐๐
๐SA'ADATU BINTU ABDULLAHIโ๐ป
๐๐๐๐๐๐๐๐
BOYEYYEN AL'AMARI
๐๐๐๐๐๐๐๐
{5/5/2018} 7:52 am
๐SA'ADATU BINTU ABDULLAHIโ๐ป
PAGE2โฃ9โฃ
Nashiga uku๐๐ฟโโhalina name? Menayi maka?
Yayi wani murmushi tare dacewa eh kinsacen zuciata๐
Ajiyar zucia tasaki sare da rufe fuskarta
Nan yashiga mata kalaman soyayyah
Itadai azuciarta tunanin yadda zasuyi soyayyah takeyi shinko beyi la'akari da ita talaka bace
Cikin karfin guiwa yace pls kice kema kina sona?
Tazaro idanu๐ณtare dacewa kasan soyayyah tsakaninmu bazata yuba kagadai yadda nake banida komi niyar marasa........
Daka mata tsawa yayi tareda cewa karki kuma fadin hakan dominni ke nakeso baruwana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 19