taje tayiwa mommy godiya sosai mommy takejin yarinyar dukda ta tsani talaka amma tana dan jin yarinyar awani bangare na zuciarta
Abu dayane yake damun *Inteesar* takasa mancewa akullum setayi kukan rashin ganinshi da batayiba hnkalinta akullum yana kanshi wato mahaifinta takan kebance kanta tayita kuka in baba talatu taganta tayita rarrashinta domin itama allah yasa mata son yarinyar hakan yasa suke kwana daki daya da ita bata barinta cikidamuwa kullum cikin debe mata kewa take dukda bata san labarintaba amma tanaji ajikinta itadin ni'imace
Allah yasama *inteeaar* son baba talatu saboda bata barin zubar hawayenta takan kwantar mata da hankali aduk lokacin data ganta tana tunanin wani abu dukda tasha tambayarta meke damunta amma *Inteesar* takasa sanar da baba talatu damuwarta
acikin kwanaki biyu *Inteesar* takara fari tayi yar kiba hips dinta yakara fitowa kullum tana sanye da hijjab koda tana aikine da hijjab dinta ajikinta baba talatu tayi2 da ita amma bata cire hijjab hatta barci in zatayi da hijjab take kwana
Dukda haka allah be hana baba talatu gano irin ni'imar kyaun da allah yama surar jikin *inteesar* dinba domin hips dinta baya boyuwa ko ahijjab din suna bayyana kyansu
Sanye take cikin doguwar riga kalar yellow da ratsin baki da fari ajiki daya daga cikin rigunan da aka siyo matane tasa hijjab baki da ratsin fari ajiki ba wata kwalliya tayiba amma tayi masifar kyau
tana shirya abincin yamma baba talatu tana zaune se dayar me aikin wadda ake cewa ma'u ita kuma tanata wanke2 tana goge kwanukan sauran masu aikin suna bangarensu suna dan hutawa wasu kuma suna cikin gidan suna gyaro gidan
sanye take da riga da siket na material me ratsin green da white ajiki kayan sun matukar mata kyau hannunta rike da wayarta iPhone10 Shigowa cikin kichin din tayi ......da sauri baba talatu tamike tare dacewa ranki ya dade dakin kirani ai
Mommy tace no bakomi kujera mommy tasamu tazauna nan masu aikin suka shiga gaidata harda Inteesar cikin isa ta amsa tareda musu barka da aiki
Kana takai dubanta kan baba talatu tace *talatu gobe shalelen naki zai dawo da allah kibada mukullin bangarenshi me gyaran bangarenshi zaizo ya amsa dama shekaran jia aka canza komi na bangaren da allah kiduba komi yatafi dai2 kinsan halin kayannawa beson kazanta
Baba talatu cikin murna tace *toh ranki ya dade mutan amerika allah yakawosu lafiya
Mommy tace amin and ahada mishi abinci sosai kinsanshi baya wasa da cikin shi don allah kada abata mishi rai amishi me dadi ina wannan yarinyarnan me take da suna
Baba talatu tace *inteesar*
Yauwa dan allah tamishi abincinnan nata me dadi da drinks din datake hada mana
Baba talatu tace angama ranki ya dade
Mommy tamike tare dabude friji tadauko drinks din da inteesar ke hada musu arobar faro mommy tabude tasha kana ta daura dacewa ki duba abinda babu kiyiwa direba magana yasiyo muku (tana fadin hakanne tareda niyar barin kichin din)
Baba talatu ta amsa da toh ranki ya dade.......
LUV U ALLππ
πSA'ADATU BINTU BINTU ABDULLAHIβπ»
[12/7, 10:11 AM] mmn usman grp: ππππππππ
BOYEYYE AL'AMARI
ππππππππ
{19/7/2018} 6: 47 pm
πSA'ADATU BINTU ABDULLAHIβπ»
*comments dinku yana karamin karfin guiwa nagode rabbih yakara dankon love* *one love*π
PAGE 3β£9β£
Nan tashiga duba abinda babu taje tasanar da direba cikin mintuna ashirin aka kawo komi aka yi mishi mazauni amazauninshi nama kuwa kowanni nama da frizarshi komi na bukata seda aka tabbatr da an tanadeshi
Sannan baba talatu ta tsaya aka gyare bangaren *annur* din aka sanya turaruka
*inteesar* tagama hada abincin dare aka kwashe aka kai kan daining ta dibar musu nasu itada baba talatu tasawa sauran masu aikin nasu suka kwashe suka kai nasu bangaren aka gyare kichin din tsaf lokacin an fara kiraye kirayen sallar magrib nan kowa yawatse yanufi bangarenshi don gabatar da salla
Suna shiga bangarensu kai tsaye drowar kayanta *Inteeaar* tanufa tadauko riga da siket din atamfa me ratsin orange da blue ta dauko hijjabi blue tanufi bandakin dake manne abangon dakin
Baba talatu ta kalleta ta girgiza kai taredacewa allah ya kyauta miki yannan kedai ko kayan bakya iya cirewa agaban mutane sedai kiyi wanka abayi kisa kaya abayi kullum kina fama da uban hijjabi sekace matar liman.......
itadai *Inteesar* tana jinta harta karasa shigewa toilet din....... cikin minti goma tagama tayi alwala tafito sanye da riga da siket din atamfar ta zumbula hijjabinta har kasa sekace me shirin zuwa unguwa...... π€£ Akan dadduma tasami baba talatu tana lazimi wadda tafita tayialwala atoilet din dake waje
Shafa mai *Inteesar* tayi tadan shafa powder kadan tareda man baki ta dan fesa turare kana tadauko dayar daddumar tashimfida akusa da baba talatu tagabatr da sallar magrib tareda jero addu'ur'i aciki harda addu'ar allah yahada fuskarta data mahaifinta π’
Seda suka gabatr da sallar isha'i da shafa'i da wutiri sukayi lazimi kmr yadda suka saba sannan *Inteesar* tazubo musu hadaddiyar jalop din shinkafa da wake wadda taji kifi bushashe se kamshi take zubawa ta zubo musu farfesun naman kazan asaman shinkafari
Sunaci suna hira sama2 *Inteesar* ce tafara cire hannu tasha lemun kwakwar data hada musu
kallonta baba talatu tayi kana tace kai yarnan bade kin koshiba?
*inteesar* tayi murmushi tareda cewa nakoshi baabaa
Taba baki baba talatu tayi tareda cewa ke kam yarinyar nan kinada abun haushi kwata2 bakyason cin abince kedai gakinan ne
Itada batace komiba taje bandaki tawanke hannunta kana tadawo tazauna kusa da baba talatun tana jira takarasa takwashe kwanonin
Seda baba talatu taci takoshi tayi nak takora da sansanyan lemun kwakwar me dankaren dadi tanasha tana santi tace * Waini kam yarnan kodai kinyi makarantar girki ne? gaskia kin iya girki wlhy in takaice miki ban taba cin abinci me dadiba seda kikazo gidannan ke kam kin godewa allah ga kyau kmr yar larabawa
ga iya girki kuma
Dariya *Inteesar* tayi sosai harda rike ciki sannan tace *kai baabaa seda kika gama cin abincinki ashan drinks sannan kike santi ko insa miki waigine π€£
Itama dariya tayi sosai *wlhy kuwa yar nan da gaske nake miki ke nifa tin tini naga kinamin kama da wata adangin hajiya amma wlhy na mance wacece
Dariya inteesar tasakeyi sosai dan ita kawai tasan santi baabaa takeyi...... seda tagama tsaf sannan takwashe kwanukan takaisu kichin din dake nan bangarensu ta wankesu tsaf sannan tadawo suka cigaba da hira da baabaa talatu tana bata labarin yadda hajiya da alhaji keji da dansu tilo *Annur*
Da aka ambaci sunan seda gaban *Inteesar* yayi wani mummunan faduwa amma takasa gano meye dalilin faduwar gabannata...... haka kawai tatsinci kanta dason jin hirar guy din
Aiko kmr tana ziga baba talatu se zuba mata labarin *Annur* din take tareda rokonta tashirya mishi abinci me dadi in allah yakaimu gobe......... se wajen goma suka kwanta domin gobe tashin asuba zasuyi saboda bakaramin girke2 za ayima shalelen gidanba
aiko tin asuba suka tashi sukayi salla inteesar tayi wanka suka shiga kichin da dukkan yan aikin gidan kowa yakama nashi aikin
Nan inteesar tashiga hada abun brkfst amma tariga ta rarraba duk wani abu datake bukatr ayanka mata na fannin girkin *Annur* sauran yan uwanta masu aiki sunata tayata hatta baba talatu seda tasa hannu anata aiki bakama hannun yaro
Ruwan lipton wanda yaji kayan hadi Yanata tafarfasa se kamshi ke tashi a kichin din tajuye a plast tashiga soya dankalin turawa da wainar kwai da kunun gyada da kosai da doya da kwai kai harda abincin turawa wanda ni kaina ban sansuba
Se wajen goma aka gama komi aka hada akan daining table
Goma da minti goma mommy tafito daga bangaren dady kai tsaye kichin tanufa nan ta tadda aiki kace2 anata kiciniya masu aikin suka shiga koro mata gaisu tana amsawa cikin isa da kasaita
Baba talatu takalla tareda cewa ashirya komifa da allah yama taho yana hanya amma yacemin zai biya gun wani abokinshi dan haka zai kai 2 na rana sannan zai iso plx ayi komi atsanake
Baba talatu ta tsugunna tareda cewa toh ranki ya dade allah ya tsareshi
Mommy tace amin... kana tajuya tanufi hanyar fita se kuma tajuyo tareda cewa *Naga an aje mana brkfst afalona kisa akawo mana falon Dady
Baba talatu tace angama gimbiya........ cikin minti biyar tasa aka kwashe komi aka kai bangaren dady
Kana suka dawo suka karya amma seda baba talatu tayi da kyar sannan *inteesar* ta tsaya takarya
Seda inteesar tayi iya bakin kokarinta tahada mishi abincin gargajiya kala biyar irin na gani na fada dinnan sannan abincin turawa kala bakwai se abincin larabawa kala hudu ga drinks iri daban2 kala goma (nasan masu karatu zasuyi mamakin yadda *inteesar* ta iya girki toh karku mance tana karance2 na littafin girke2 hkn yasa ta kware agirki iri2)
Zuwa karfe daya da rabi an shirya komi a daining area abangaren mommy (seda baba talatu ta tambayeta tace ashirya komi abangarenta)
aka turare ko ina na gidan da turare hatta kichin seda aka wankeshi da sinadarin kamshi akasa turare irinna sudan me dankaren jamshi ko ina agidan seda yayi tsaf hatta mommy sedata jinjinama *inteeaar* domin taji dadi sosai
Dukkan masu aiki kowa yakoma bangaren dayake domin su gabatr da sallar azahar hk suma su *inteesar* itada baba talatu kai tsaye ban daki *inteesar* tafada domin duk tagaji wankan take bukata ita dama baba talatu tafison bayin tsakar gida shi tanufa don yin alwala
Sanye yake cikin yadi ash colour wanda yaji aiki awuya da hannu kayan sun matukar fito da kirar jikinshi da tsantsagwaron kyawunshi yayi kiba se sheki yakeyi babu hula akanshi gashin kanshi har sajen fuskarshi ya kwanta yayi luf wayyo allah nah naso ku ganshi fansπ
Ahankali yake saukowa daga matakalar jirgin yana wani barin murmushi sosai yake kallon gidan tamkar yashekara dari baya gidan
Masu take mishi baya sunata kwasar kayanshi suna kaiwa bangarenshi
Kai tsaye bangaren mommynshi yanudfa domin yana kwadayin ganinta
Taji alamar saukar pilot dinshi dan haka tana shirin saukowa kenan daga matakala yakaraso da gudu ya rungumeta yanajinshi tamkar jariri
Momy taji dadin ganinshi tankar ta maidashi ciki takeji gashi taga yayi kiba ta manna mishi kiss agoshi tareda mishi ban gajiya takama hannunshi suka nufi bangaren dad dinshi shiko babu abinda yake kallo se yadda tsarin gidan ya canza ga wani sihirtaccen kamshi me rasa zuciya yana tashi shakar kamshin yake yana lumshe ido zuciyarci na mishi wani irin bugu ahaka har suka isa bangaren dad dinshi
πSA'ADATU BINTU ABDULLAHIβπ»
ππππππππ
BOYEYYE AL'AMARI
ππππππππ
{26/7/2018} 4:37 pm
πSA'ADATU BINTU ABDULLAHI βπ»
*Plx auntynah zuwairat ummu maryam kiyi hakuri ki kara hakuri ta hannun damana ni nasan kedin kainuwace dashen allah........*ππ
PAGE 4β£0β£
Daddy yana zaune yana kallon news atashar aljazera suka shigo falon da sallamarsu
Da gudu *Annur* yakarasa yarungume dad dinshi cikin murna
Daddy cikin murna ya rungumeshi...... sosai suka shiga murnar ganin juna itadai mommy tana zaune tana kallonsu tana murmushi azuciarta tana addu'ar allah yanuna mata ranar dazataga jikokinta..... Sun dau kusan minti ashirin suna hira shida daddy akan compan dinsh na kasar dayaje nan *Annur* yashiga bashi labarin cigaban daya samu...... seda mommy tayi mishi magana yaje yayi wanka yasauko abincinshi najiranshi
Mikewa yayimi yanufi bangarenshi.... cikin 30 mnt yayi wanka yashirya cikin kananan kaya yagabatar da sallah kana yanufi bangaren mommynshi
Yana isa kai tsaye daining area yanufa nan kamshin abincin tin kafin yabude kulolin sun fara kai ziyara ahancinshi sosai yakosa yafara cin abincin domin ya tabbatar abincin zaiyi dadi...... daya daga cikin kujerun yaja yazauna tareda danna lambobin mommynshi yasanar da ita yakammala komi yana falonta
Cikin minti biyar ta iso falon wurin dayake tanufa taja kujerar kusa dashi tazauna tana kallonshi cikin so da kauna
Shagwabe fuska *Annur* yayi tareda cewa * mommy wazaiyi saven dina?
Murmushi tayi tareda cewa * Waya saba saven dinka inba baba talatu ba bari akira maka ita. tadauki wayarta tayi dailing lambar baba talatun ringin daya ana biyu *Inteesar* tadauki wayar takara akunne
Mommy tace *Ina baba talatun?
*Inteesar* tace yanzu ta tada sallah
Kai tsaye mommy tace toh *Annur* ne zatazo tayi saven dinshi gashi yanajin yunwa inta idar ki sanar da ita
Cikin girmamawa *Inteesar* tace toh ranki ya dade...... kit mommy takatse wayar
Kallonta *Annur* yake tayi tin farkon fara wayar tata tana katsewa yayi charab yace *Wai mommy bata nan ne?
Mommy tace *No son tana sallah ne bari ni nayi saven dinka koh? tafadi hakan tareda mikewa tadauki plate
Sosai yaji dadin hakan domin tin tasowarshi mommy bata taba saven dinshiba se yau *No mommy ki barshi zan jirata ta idar barima naje bangarenta dama idanuwana na mararin ganinta nayi missn dinta
Komawa mommy tayi tazauna tareda cewa Toh son adawo lafiya
Mikewa yayi tareda daukar wayarshi yanufi bangaren baba talatun amma yarasa dalilin dayasa kirjinshi ke mummunan harbawa...... da sallamarshi yatura kofar dakin aiko seya jita abude kai tsaye yashiga
Tana zaune akan dadduma ta idar da sallar kenan ita kuma *Inteesar* tana tolet
da sauri yakaraso kusa da baba talatu cikin mrnarshi
tashafa addu'arta ta waigo gareshi cikin farin ciki tace *Barka da zuwa ranka ya dade
Murmushi yayi tareda zaunawa akan gefen gado wanda yasha gyara agun *Inteesar* yana fuskantar baba talatu yace *Baabaa kinki zuwa kiyi saven dina inatajin yunwa
cikin hanzari baba talatu tamike taredacewa ranka ya dade tashi muje ina zanso kaji yunwa
Murmushi yayi tareda mikewa yanabin dakin da kallo amma yana jiyo karar ruwa atoilet yakasa dauke idanuwanshi akan kofar toilet din
baba talatu tayi gaba yabita abaya har suka isa bangaren mommy tana zaune a inda yabarta tana latsa wayarta
Baba talatu tagaidata cikin ladabi ta isa taja mishi kujera yazauna tashiga bude mishi kulolin abincin tareda tambayarshi abinda zata zuba mishi
hmmm aifa gogan dukya rikice domin kamshin abincin yagama dashi duk yakosa yafara cin abincin
Mommy kanta seda kamshin abincin yasa ta aje wayarta agefe tana hadiyar miyau
Shiko gogan da kyar ya iya zabar chainis rice baba talatu tazuba mishi hadi da farfesun naman kasa ta aje mishi agaban shi
Mommyma tace azubo mata dukda ba yunwa take jiba amma kamshin abinci kawai yasa tafarajin yunwaπ nan tashiga aunawa cikinta ba kama gannun yaro
Aifa shima gogan nan yafara kai lomar abincin yanajin wani ni'imataccen dadi na shigarshi yanaci yana sambatun dadi baba talatu nata mishi dariya domin itama mommy bakunne se baka
kan kace chass gogan yacinye chainis rice dinnan da farfesunnan nan aka kara zuba mishi abincin larabawa nanma sambatu yayi tayi seda yaci yakoshi yama mance dashan ruwa sannan ya kalli baba talatu yace *Toh baba abani exotic
Nan baba tace ranka ya dade aiga drinks nan an hada maka...... tazuba mishi kunun aya wanda yaji kayan hadi ta miko mishi
Yana kallon kunun ayan yanaso amma ba hali domin yasan zai shiga yanayi dan haka yakalli baba talatu yace *Baabaa kisamin wani in akwai se asamin kunun ayan afirij zansha anjuma
Aiko mommy tayi charab ta amshe tashanyeπ
Baabaa tazuba mishi lemun kwakwa tabashi aiko nan yashiga sha seda yashanye tass sannan ya aje kofin aka kara mishi yanata santi hmmmmm awannan fannin yakasa jurewa sedai kawai ya tsinci bakinshi yana cewa *Wai baabaa waye yayi girkinnan gaskia yayi dadi sosai ga drinks dinma irin wannan in kana samunshi ai bazaka sha na kwaliba gaskia yayi sosai
Mommy tayi tariya tareda cewa baabaa dauko waigi kisama Babana karya fadi wannan santi hakaπ€£
Aiko baba talatu tadauko karamin fillo tasa mishi tana dariya
Shima dariyar yayi tareda kara maimaita tambatar tashi
Mommyce tabashi amsa *Bakanan ai ankawo mana sabuwar me aiki itace taketa shagwabamu da girkinta me dadinnan
Wow gaskiya mommy ta iya girki dole nabada tukuici..... yasa gannu a aljihu yadauko bandir din dubu daya daya bandir biyu yamikama baba talatu yace daya nata daya na dayar me aikin
Sosai baba tashiga kwararo godiya
Mikewa yayi ya nufi gun mom yayi mata kiss tareda cewa *Mommy zan dan fita in dawo bazanyi nisaba
Abbanah ina zakaje haka kaida yakamata ka kwanta ka huta
Mukullin mota yadauka seda yakai bakin kofa sannan yace yanzu zan dawo bazan dadeba
Mommy tace allah ya tsare tareda mikewa ta haye sama itako baba talatu seda ta tsaftace gun takara sa turare sannan tanufi bangarensu tabawa *Inteesar* kudin nata da *Annur* yabata
Kallon mamaki *Inteesar* tayima baba talatu cikin wani yanayi tace *Ni nabar miki baba mezanyi da wannan uban kudin
Harara baba talatu tayima *Inteesar* tareda cewa *aiko baki isaba dole ki amfana da kudinki zan dauki dubu ishirin asiyo miki abubuwan dakike bukata zuwa gobe in aiki yayi mana sauki se in rakaki amiki saloon kinga seki fito sharr sauran se in adana miki ko atura kauye ase miki akuyoyi
itadai *inteesar* godiya tayima baba talatu sosai domin ta tabbatr da baba nasonta da wannan shawarar suka shiga kichin don gabatar da girkin dare........
Hmm ai yana fita kai tsaye yanufi ma ajiyar motocin gidan yashiga daya daga cikin manyan motocin gidan yamata key nan da nan yabar harabar gidan
kai tsaye unguwar tasu yanufa zuciyarsa cike da mararin son ganin gimbiyar tashi wadda sonta yahanashi kwanciyar hankali
Tafiyar 20mnt ya isar dashi kofar gidannasu yafaka motarshi yafito ya karasa zuwa zauren gidannasu..... shi kanshi azuciyarshi yayi mamakin ganin zauren gidan bakowa kmr anshareshi ba kamar adaba kullum cike yake da almajirai
Da wannan tunanin yadawo zuwa jikin motarshi yajingina nan da nan bakon yanayi yaziyarceshi addu'ar yakeyi azuciarshi allah yasa yaganta ko kadanne domin yasamu natsuwa......... seda ya dauki kusan 10mnt yana tsaye akofar gidan aiko se yaga giftawar wani yaro yakira yaron yaron yakaraso ya gaidashi Ko amsawa *Annur* yakasayi burinshi kawai ya aiki yaron yakira mishi ita aiko be bata lokaciba ya aika yaron zuwa gidan shiko yaro da gudunshi yanufi gidan
Suna zaune a tsagar gida akan tabarma iya tayi male2 Hafsat tana gefenta wadda tayi wata irin mahaukaciyar kiba sekace zata fashe {ko kibar meye ohoπ€·π½ββ} sun tasa gasasshen naman kaza agefe sunata yaga musammanma iya data dade bata sa naman kazar abakintabaπ€£
Da sallmarshi yaron yashigo gidan...... cikin sauri iya taboye naman kazar abayanta ππ€£ita duk azatonta bako sukayi seda duk suka dago sukaga yaron sannan iya ko amsa sallamar batayiba ta tambayi yaron cikin zaro idanuwa *Kai lafiya zaka shigomin gida kmr tsohon barawo
shidai yaro be tanka mataba saboda duk wanda ke layin babu wanda besan halin matarba da ruwan matsifa
Hafsat takara zare mishi jajayen idanuwanta sekace gauta *Kai bakai ake tambayaba? kagamin dan bura uban yaro
Turo baki yaron yayi tarexa cewa wai wanine me mota yake sallama da wata yarinya agidannan yace wai fara
Hafsat taji ance me mota aiko nan tayi zumbur tamike cikin sauri tareda cewa au ashe mani ake nema kai kayi hakuri kaji πtafadi hakan tareda mincino naman kazar tamikawa yaron
Girgiza kai yaron yayi alamar bazai amsaba sannan yafice dagudu daga gidan
Cikin matsifa *Hafsat tace aikin banza tsiyata da yayan matsiyata kenan toh ohon maka dai...... tafadi hakan tareda nufar dakinnasu
Itadai iya cewq takeyi ke kiyi sauri ki fito kilama alhaji usman sabo ne kiyi sauri yannan karki mana bukulun samun kudiπ€£
Cikin minti biyar Hafsat tayi tsaka tsami rabonta da wanka tafi sati dayaπ€ͺaiko nan ta zabga uwar kwalliya tasa dogon wando matsastse se riga iya cibiya kai yaji uban gashin doki sekace diyar arnaπ€£aiko tana fitowa iya tashiga koda diyar tata harta fice
Tin bayan dawowar yaron daya sanar dashi tana zuwa yadauki dubu daya yamikama yaron nanko yaron yashiga murna yana godiya harya bar gun
Ya kudirci aniyar koda zai kwana agun zai jirata harta fito shidai burinshi yasata a idonshi
Hmm karasowa gun tayi be ankaraba yaji anata taba mishi hannu aikocikin hanzari yadago idanuwanshi sukayi tozali da ita dominshi bemaji tafiyartaba
Kallon sama da kasa yayi mata ga wani karni dake dukan hancinshi cikin bacin rai yace *ke lafiya zaki tabani?
Fari tashiga mishi da idanuwa kana tace *Haba Malam kaifa ka aiko akirani toh nazone naga kanata tunani bakasan nazoba shine na tabaka
Kara kallonta yayi kana yace *da allah malama kiyi hakuri bake nake nemaba dayar yarinyar gidanku nake nema plx help me ki kiramin ita
wani irin uban kallo ta watsa mishi domin tafara tunanin rainin hankali zaiyi mata tace *Ni nikadaice budurwa agidan ai dan allah malam inni kazo nema gani kwana kakeso kayi dani ko wuni ko sati duk zan yarda kaini har wata inhar zaka biyan...........
πSA'ADATU BINTU ABDULLAHIβπ»
ππππππππ
BOYEYYE AL'AMARI
ππππππππ
{12/8/2018} 8:6 am
πSA'ADATU BINTU ABDULLAHIβπ»
*Kai ina zansa kaina ni ade ππ»πnaga so naga kauna naga kula naga tattali duk ina godiya rabbih yabarni da ku har a aljannah amin*ππΌπ
PAGE4β£1β£
Cikin tsawa *Annur* yakatseta * Ke ni ba irin yan iskan dakika saba hulda dasu bane hasalima ni bake nake nemaba kinajina koh niba fasiki bane kema allah ya shiryaki****** Yana gama fadin hakan yashige motarshi yayi mata key yafigeta yabar harabar gun
Bakaramin kololon bakin ciki bane yaziyarci zuciyar *Hafsa* taso ace koda wuni daya suyi da wannan guy din domin daga ganinshi zeyi dadin harka zuciarta cike da kwadayinsa tashige cikin gida
** ** **
Tin daga ranar da khausar tazo neman *Inteesar* agidansu bata gantaba hankalinta yatashi sosai ta iso gida arude take shaidawa Yaya ahamad shima nan nashi hankalin yatashi sosai har seda yakwanta a asibiti nanma jikin yaki dadi suka canza wani asibitin satinsu uku a asibitin amma nanma sauki sedai na musulunci gaba daya yafita hayyacinsa tunanintane kawai keta kai komo azuciarshi hakanne ya haddasa masa mummunan ciwo har yakaiga jininshi yahau fiye da tunanin me karatu.
Hankalin mommynsu khausar yatashi da ganin yarannata ba lafiya an rasa gane kanshi nan ta tasashi agaba yazayyana mata damuwarshi soyayyar *Inteesar* ce ke dawainiya dashi nan mommy tayita mishi nasiha tasanar da mahaifinsu shima yayita mishi nasiha
Dady yasa malaminshi yayitama *Ahamad* din addu'a
Cikin yardar mahaliccinmu dominshi allah maji rokon bawane Ahamad yadan samu sauki ammafa karku mance masu karatu son *Inteesar* yakasa barin zuciyar yaya *Ahamad* dukya rame Ganin saukinne yasa yanemi sallama aka sallameshi yadawo gida amma jikinshi ba kwari
dakyar yaya ahamad ya iya sati biyu yanemi izinin mahaifinshi akan zai koma kasar indiya yadaura da karatunshi domin nigeria bata masa dadi
Dady ya yarda ya amince tareda mishi addu'a da fatan allah ya tsare
Haka itama mommy tabishi da addu'ar domin lallabashi takeyi tamkar kwai saboda ciwanshi
Bayan tafiyarshi da sati uku itama *Khausar* tanufi kasar india domin tayi karatunta na likitanci ta tafi da kewar inteesar da mararinta akullum takanyi addu'ar allah ya hada fuskokinsu π
Hmmm duk suka tafi sukabar iyayensu da kewarsu tareda dumbin kaunarsu a zuciarsu.
** ** **
Toh fa ina masoya annur gogan nakufa yarikice hankalinshi yafita ajikinshi yashiga wani yanayi wanda harshena bazai iya lissafa muku shibaπ
Yaje gidansu inteesar yafi sau goma amma baya samun ganinta tin hafsat nafitowa yanzu tadena fitowa sedai yakaraci zamanshi be gantaba haka yake dawowa gida zuciarshi taf kunci
Abangaren *Inteesar* ayan kwanakinnan batajin dadi ga yawan mafarkin *Annur* tanayi takan ganshi yana tsugunne yayi tagumi hadi da kwalla taf idanuwanshi tarasa gane dalilin mafarkin
Baba talatu tafuskanci tana cikin wani hali dan haka tazaunar da ita take tambayarta meke damunta tadaice mata bakomi kawai dan zazzabine yake damunta badan tayardaba takyaleta ta kaita chamis din muntari yadubata yabata magunguna
Yaumade kmr kullum bayan sun gama aikin gidan tana zaune tana karatun askar bayan idar da sallar la'asar baba talatu tazo tasameta tace tinda yau da sauki aikin se suje gun salon amata kyaran gashi domin baba talatu tafuskanci gashin nata yana bukatar gyara
Mikewa tayi tare da nannade daddumar ta ajiyeta amazauninta shima askar din ta ajeshi akan durowar gado kusa da alkur'ani kana tajuyo fuskarta dauke da murmushi tace *Baba bari inyi wanka koh?
Baba talatu tasaki baki tareda tafa hannu tace *Ke ni wannan yarinya kodai kinada aljanun wankane yanzufa kika fito daga wanka gaskiya bazan jirakiba in zakije kizo mutafi
Dariya inteesar tayi har seda wushiryarta ta bayyana tanufi durowarta tabude tareda cire hijjab dinta doguwar rigace maron colour me stons asaman rigar tayi matukar yimata kyau hips dinta yafito sosai haka suma dukiyar fulaninta wadanda suke atsaye sun samu mazauni acikin rigar. dogon hijjab ruwan madara tadauko tasaka tasa takalmi shima ruwan madara
Itama baba talatu tayafo kyalenta asaman atamfa riga da zanin dake jikinta ta dauko bakar jakarta
Suka fito suna tafe suna hira baba talatu tana tsokanarta dacewa *Koda mun hadu da samari nasan ni zasu fara zaba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 19