Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
kamar yana tuhumar tane saboda taqi nuna masa inda zai samu ruwan hakan yasa ranta yasake 6aci,dama ga abinda aka mata a kamfani,itama a zuciye take,6acin rai takeji sosai,hakan yasa ta kalleshi tace"da kacemin in fad'ama inda zaka samu ne? ruwa kace min kanaso,koni ce ruwan?" Lumshe manyan idonsa yayi sannan yabud'e,ransa yafara 6aci,yarinyar tafara kaishi bango,hakan yasa yace mata "kinga ya'isa!, idan baki dainamin wannan shirman ba zan kakkaryaki anan"(πŸ™†) Kai tsaye Inaas tace"tome kake jira?" Jawaad ya kalleta fuskarsa ad'aure babu walwala yasaka hannunsa yafara qoqarin cire suit d'in jikinsa yace"okay kina tunanin bazan iya bane?" ba tareda shakka kojin tsoro ba Inaas tace"ikon Allah,kaji mutum,daga had'uwa? daga tambayar ruwa saika koma yimin abu har kana qoqarin cire riga saikace wani d'an dambe? to Bismillah,kallon me kake? me kake jira kadakeni mana,nima inda Yayanah yana nan baka isa kanuna min hannu ba,Ammiy na tace inda yana nan shine zai kula dani,basai kacire rigarka ka nunamin qwanji ba, tsaya na kawo ma ruwan badan halinka ba" Tana fad'in haka tayi wuf tashige cikin gidansu domin kuwa bilhaqqi ta tsorata da yanda taga yana qoqarin cire suit d'in musanman yanda ta hango murd'ad'd'an dantsan hannunsa,kawai hargagi take masa dan karya raina ta. Yana ganin shigar ta gidan yasaki ajiyar zuciya sannan yasaka hannunsa yabude gaban motar yana dube-dube,adede lokacin takawo masa ruwan d'an kadan kamar ya roqa,batare dayayi magana ba ya kar6a yafara zubawa a motar. Inaas ta kalli motar sannan tasa qafa tadaki tayar gaban motar tace"idan na mallaki irin wannan motar nikuma shikkenan zama ya qaremin,yawo zanyi tayi waje-waje,kasan me? Ammiy na tace duk wanda ya aureni yayi sa'ah saboda nid'in tadaban ce,na tabbatar mijina saiya samu motar datafi wannan had'uwa" Jawad da surutun yarinyar yafara damunsa ya rufe gaban motar yana girgiza kansa,yabata kofin data kawo masa ruwan sannan ya kalli hannunsa cikin qenqemi saboda robon daya bude mota da kansa harya manta,yadubeta yace"ruwan yaqare,inaso na wanke hannu na" Kai tsaye Inaas tayi gaba ta nufi gidansu tareda fad'in"biyoni" Babu musu Jawad yabi bayanta suka qarasa cikin gidan nasu,yana saka qafarsa agidan yaji gabansa yayi wata irin muguwar fad'uwa kansa yasara,amma bai kawo komai aransa ba ganin tunda yashigo qasar jiya yake jin irin wannan yanayin. Inaas tadaga murya tace"Ammiy!, ga baqo" Bilkisu dake zaune akan kujera tad'ago idonta ta sauke shi akan had'ad'd'an gaye,matashin d'an kasuwa,ingarman namiji,miskili,Jawad d'in Daddy da Mummy kuma Muhammad din Bilkisu. lokaci d'aya taji gabanta yayi wata irin fad'uwa har saida tasa hannunta a qirjinta,shima a nasa 6angaren zuba mata ido yayi yana kallonta tana sanye cikin baqar doguwar rigar gwanjo,kanta yana d'aure da d'an kwalin rigar,yayinda ta tsaga dogon gashinta tarabashi abiyu ta daure sauran abaya,amma daga gashin gaban goshin ta kana iya ganin yanda gashin yake arabe ta hanyar tsagar. Lokaci d'aya yaji matar tashiga ransa ta birgeshi,da alama batada hayaniya kamar wannan ficiciyar yarinyar marar kunya. Cikin sauri taqaraso wajansa cikin sanyin murya tace"sannu da zuwa" Jawad saiyaji hausarta a goge ras kamar tasa,ba kamar hausar Inaas ba. Ammiy tajuya ta kalli Inaas tace"daga ina kika samo baqo?" Inaas tace"awaje na tsinceshi,hannunsa zai wanke wai,dan 'wai' zance saboda kinga hannun nasa nan ras babu abinda ya sameshi amma ahaka zai wanke" Bilkisu tayi murmushi sanin halin 'yartata, tawuce tad'ebowa Jawad ruwa,ta kalleshi cikin kulawa tace"zona zuba ma ka wanke hannun" Cikin sauri Jawad ya matso ya tsugunna agabanta,Ammiy tazuba masa ruwa yafara wanke hannayen sa sosai,yana wanke hannun amma idonta gaba d'aya yana kansa tana kallon yanda yake komai a nutse,ko kad'an takasa janye idonta daga kansa, yana gama wanke hannun tamiqe zata maida kofin kan randa,cikin sauri Jawad ya kar6i kofin har hannunsu yana haduwa waje daya,yamaida kofin kan randa. Inaas tazuba musu ido tana kallonsu sai wani abu suke kamar basa son rabuwa da juna. Jawad kotakan Inass baibi ba ya kalli Bilkisu yace"MAMA nagode,sai anjima" Gaban Bilkisu ya yanke yafad'i,MAMA? ta maimaita sunan a bakinta,lokaci d'aya tatuno da yaronta Muhammad,mama shine sunan da taso yakirata dashi idan ya girma saide kuma Allah bai nufa ba,haka tunda ya 6ata babu wanda yata6a kallonta yace da'ita Mama sai yau da wannan yaron yafad'a mata,ta tuna lokacin datake wa Muhammad dinta wanka tana fad'a masa kada shima ya gudu yabar mama,mama tana sonsa idan ya gudu bazata iya jurewa ba,tasaki ajiyar zuciya ta kalli Jawad taga harya juya zai fice daga gidan tayi sauri tace"tsaya yaro,zokasha shayi saika tafi" Cak! Jawad yaja yatsaya yaji kwata-kwata yakasa yin musu da matar. Bilkisu tayi sauri ta Shimfid'a masa tabarmar ta mai kyau tace"zoka zauna" Babu musu Jawad yadawo ya zauna yanata kallonta. Inaas datasan cewa ita Ammiy zata ce tahada masa shayin hakan yasa ta dauko butar shayin zata hada masa,cikin sauri Ammiy tace"bani nahad'a masa dakaina" Inaas ta kalleta da mamaki,duk wani baqo da zaizo gidan kullum saide tace Inaas ta had'a musu shayi,amma abun mamaki yau itace da kanta take qoqarin had'a wa wannan baqon,babu musu tabata butar shayin ita kuma takoma gefe ta zauna ranta duk ba dadi. Jawad ya kalli yanda Ammiy take had'a masa shayi cikin nutsuwa, tazuba masa a dan qaramin kofin shan shayi irinna buzaye,sannan ta qarasa tabashi,tazauna kusada Inaas tamaida nutsuwarta gaba daya kan Jawad,tunda yashigo gidan takejin wani irin nishadi wanda rabon da taji nutsuwa da nishadi irin wannan tun kafin Malam Manu ya gudu yabarta. Cikin farinciki ta kalleshi dakyau tace"yarona kaima anan qasar kake ne?" Jawad yayi murmushi ya ajiye kofin shayin hannunsa sannan tace"a a,ni d'an Nigeria ne Mama" Wannan sunan na Mama daya sake fad'a saita sake jin wani irin dad'i,tasaki ajiyar zuciya tace"masha Allahu,nasan Nigeria sosai,nima nazauna acan shekarun baya,Yaya matarka?,tana lafiya?" Jawad yasake murmushi sannan yace"Mama ai banda aure" Bilkisu tasaki 'yar qaramar dariya sannan tace"ikon Allah,ashe yaron nawa tuzuru ne,to Allah yabaka mace tagari,yanda kake da nutsuwa Allah yabaka nutsats-tsiyar mace,nasan duk yarinyar data aureka tayi sa'ah,babu wata budurwa dazata kai matarka sa'ah saboda tayi dace da miji nagari" Inaas tanajin haka tacuno bakinta gaba cikin shagwa6a tace"Ammiyyyy.....,nimafa irin wannan maganganun kike fad'a min" Bilkisu ta kalleta tayi murmushi tace"to sarkin Kishi,fad'amin waye yata6amin ke tunda kika shigo naga ranki a6ace,Yaya wajan aikin naki meyasa kika dawo dawuri yau?" Cikin tsananin damuwa Inaas tace"Ammiy ai sun koreni,wai shugaban kamfanin ne yazo koya sunansa ko Jawad? oho masa de, shine yace afad'amin yakoreni daga kamfanin sa wai in koma makaranta,wallahi Ammiy duk randa naganshi da idona,saina saka hannayena nashaqe masa wuya"(πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ) Tafad'i hakan tana dunqule hannayen ta alamar yanda zata Shaqe wuyan Jawad. Jawad dake shan shayi lokaci d'aya gabansa yafad'i,cikin sauri ya kalleta tare zaro idonsa. cikin ransa yake magana dama itace?,shiyasa tazo wucewa tagabansa dazu take sababi tana fada tana cewa kora daga kamfani aiba itace kora daga duniya zuwa lahira ba? nan take yaganeta,tabbas itace wadda akace masa tana shigar da bayanan kamfani yace afad'a mata ya sallameta. Inaas taci gaba da fad'in"wallahi Ammiy wannan Jawad d'in ko, tunda naji sunansa nasan cewa bashida mutunci,daga sunan mutum nake gane me mutunci da marar mutunci,yanzu daya koreni dan Allah Ammiy tayaya ne zan tara wani kud'in in sauya miki kayan daki?, nayi alqawari duk ranar danayi kudi,saina gina kamfanin Oil guda dari ta yanda zan fuskanci Jawad inyi gogayya dashi" Bilkisu tayi murmushi kamar bataji haushin korar da'aka yiwa Inaas dinba,domin ta kwantar mata da hankali hakan yasa tace"to ayi haquri mana,saida nace miki kitashi dawuri ki tafi karki yi latti, kika tsaya zaman wanke kai,ina me tafiya wajan aiki yaga lokacin tsayawa wanke kai? ai shikkenan saiki yi Addu'ah Allah yakawo miki wani aikin,matso na turara miki gashinki karna sakejin kinsa damuwar hakan aranki kinji ko?" Inaas tayi qwafa,sannan tace"shikkenan Ammiy" Bilkisu tatashi taqara zubawa Jawad wani shayin wanda baimasan ya shanye nacikin kofin ba saboda yanda yaji d'and'anon shayin yayi masa dad'i sosai. Bayan tazuba masa shayin ta d'auko turaren wutan datake turara dogon gashin Inaas dashi kasancewar basuda halin zuwa wajan saloon, zama tayi sannan ta janye laffayar daga kan Inaas,dogon gashinta ya bayyana a fili,tasaka hannunta ta warware mata gashin nata,sannan tasake taje mata gashin, tafara turara mata shi. Jawad dake zaune yasaci kallon su lokaci d'aya idonsa yayi arba da dogon gashin Inaas,ahankali yazaro idonsa gabansa yana fad'uwa, aransa yana fad'in yanzu duk wannan gashin natane?,yasake qarewa gashin nata kallo yaga de tabbas natane. Inaas tad'an juyo ta kalleshi cikin sauri ya janye idonsa,cikin zuciyarsa kuwa fal mamakin yawan gashin yarinyar yake. Inaas kuwa qare masa kallo take talura kamar yana cikin damuwa,bayan damuwar ma da alama bashida lafiya,yana tattare dawata irin cuta,wato miskilanci,wannan ma babbar rashin lafiya ce. 'Dauke kanta tayi daga kallonsa. yayinda shikuma Jawad zuciyarsa tasake tunzurashi akan yasake kallon abun dayake mutuqar so tun kafin yabar gidan,wato dogon gashi. (πŸ€«πŸ™ˆ) Ahankali yad'an juya yasaci kallonta kamar yana tsoron karta kamashi yana ganinta, idonsa ya sauka akan d'an qaramin bakinta,yadade yana kallon bakin tsiwar tata, ahankali yamaida kallonsa zuwa dogon gashinta,adede lokacin Inaas ta juyo ta kalleshi,karaf idonsu yafad'a cikin na juna,Koda wasa Jawad yakasa dauke idonsa daga kanta,nan take wata irin fad'uwar gaba ta ziyarcesu lokaci d'aya. Ammiy kina zaune yaranki suna satar kallon juna 😍😫 Jama'ah nace ba?πŸ€” Wai yaushe wannan baqon namu na zaune daya koremu daga aiki kuma yazo yake shanye mana shayi zai tashi yatafi ne? πŸ€” Mezai faru idan Inaas tagano cewa Jawad din data gama ciwa mutunci shine a zaune a gefenta yagama Jin komai? πŸ€” Yaya batun hadin auren Jawad da Amal?πŸ€” Tayaya Bilkisu zata gane cewa Jawad shine Muhammad dinta?πŸ€” Yaya haduwar Bilkisu da malam Manu? πŸ€” Duk kubiyoni πŸ’ƒπŸΌ, Basai na fada ma,duk me bibiyar littafi na yasan cewa akwai soyaiya, wannan Karon ma akwai zazzafar soyaiya agaba,makirci,dakuma tirka tirka. Yanzu ne labarin zai fara,yanzu ne zamu nutsa cikin zallar soyaiya dakuma qalubale,munji labarin tasowar taurarinmu munji haduwar su to yanzu ne wasan zai fara,littafin nan yanada yawa,tundaga kan free page zaku gane haka,ban taba rubuta free page me yawa kamar na wannan littafin ba. Wanda suke siyan littafi na ba gajiya wa nagode banda kamar ku akoda yaushe.πŸ™ Alhamdulillah, πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌanan na kawo qarshan free page,duk wanda yakeso ayi tafiyar dashi yazo yayi payment. ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yau free page yaqare. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. idan kinsan zaki sai littafi nane danki fitar min dashi to nagode na haqura da Dari ukun ki,wanda suka siya ma Allah ya musu albarka. Wanda zamu rabu dasu daga nan wato iya free page, saimun hadu a sabon novel dina mesuna MATAR ABBANA,nagode πŸ™ Amnah El Yaqoub✍🏻 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7