Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
tana dube-dube da alama Muhammad take nema,ganin babu Muhammad babu dalilinsa sai qaninta dayaci uban wani nad'in rawani irin wanda buzaye sukeyi, da matar qaninta wadda take Sanye da laffaya ruwan toka dasuke gefenta babu kowa,hakan yasa tagane cewa ba mafarki takeba da gaske ne shima Muhammad yatafi,shikkenan yatafi yabarta,cikin d'acin zuciya da qunci tafashe dawani irin kuka,matar qaninta ta dafa kafad'arta cikin sigar lallashi tace"Yaya kiyi haquri kidena kuka,tunda Allah yakawo ki gida lafiya ai Alhamdulillah" Qanin nata ma yadubeta cikin hausarsa da bata goge sosai ba yace"kiyi shiru" Daga haka baisake cewa komai ba ya kalli matarsa JAMILA,wadda yasha fama yayi yaqi da samari bila'adadin domin ya aureta saboda yanda takeda tsananin kyau,hakanne ma yasa mahaifinta yasa mata suna Jamila,yayi ajiyar zuciya yace"JAMI, ki kula da'ita nizan fita nema..." Jamila ta kalleshi tagyad'a kanta sannan tace"to FAROUQ saika dawo" Farouq yasa hannu yad'auki butar shayinsa dawata jaka 'yar qarama arataye a wuyansa, yafice daga gidan. Tun bayan fitar Farouq Bilkisu me gwanjo take hawaye,idonta yayi jajir kawai hawaye ne masu zafi suke zarya akan kuncinta,tsabar kuka har muryarta ta dashe,jamila tayi lallashin tayi ban baki amma Bilkisu shiru,har zuwa la'asar hawaye take,haka kuma taqiyin magana,taqi cewa komai, kawai de ta zubawa waje d'aya ido tana kallo ga hawaye yana zuba,agefe guda kuma ga nonon ta dayake zubarda ruwa kasancewar anwuni ba'asha ba. Sai yamma lis,farouq yadawo,ya kalli Yaya Bilkisu sannan ya maida kallonsa ga Jamila yace"Jami,yanaga Yaya a zaune tayi shiru har yanzu kukan takene?" Jamila ta kalleshi tace"ka ganta nan tunda kafita har yanzu kuka take taqicin komai sannan kuma taqiyin magana" Farouq ya girgiza kansa ya zauna a kusada Bilkisu sannan yacewa Jamila"had'o mata shayi" Jamila tatashi da sauri tahad'owa Bilkisu shayi acikin wani d'an qanqanin kofi irin wanda buzaye suke amfani dashi,tazo ta ajiye mata shayin itama tazauna awajan. Farouq ya kalli Bilkisu yace"Yaya kid'auki shayin nan kisha hanjin cikinki ya warware" "na salwantar da d'ana" Shine kawai abinda Bilkisu tace. Jamila ta kalli Farouq tace"kamar fa bata cikin hayyacinta,Yaya da batada kowa kana jifa maganar yaro takeyi" Farouq ya jinjina kansa yace"um ina tunanin haka,inaga iftila'in data had'u dashi ahanya shine bai barta ba,bari inje wajan liman yabani rubutu na kawo mata tasha ko Allah zaisa tadawo hayyacinta" *** *** *** Lagos Nigeria Gudun kada mutane Susan abinda yake faruwa hakan yasa Alhaji Mekud'i yana sauka a Airport babu wanda yasan da dawowar sa kai tsaye yawuce gidan yayarsa qwalli d'aya aduniya wadda suke uwa d'aya uba daya kuma iya sukad'ai suka rage a duniyar wato YAYA MARIYA,ita kanta gidan datake ciki abun kallo ne,basai an fad'aba kasan cewa gidan ya amsa sunansa na gidan yayar Mekudi. Tana ganinsa da yaro tatashi tsaye ta tareshi tareda fad'in "Mekudi ina kasamo yaro haka tubarkalla masha Allah?" Zama yayi acikin luntsuma luntsuman kujerun falon sannan yayi kissing Muhammad yace"Allah ne yabani shi Yaya,kar6eshi kisa masa albarka" Cikin sauri Yaya Mariya ta kar6i yaron fuskarta fal farinciki tana fadin"ikon Allah,Aliyu wannan yaron aid'an larabawa ne,Ina kasamo shine?" Murmushi yayi, sannan yatashi yaje inda wayar gidan nata take ajiye yakira layin gidansa yacewa zaliha matarsa lalle lalle duk abinda take tabari tasa driver yakawo ta gidan Yaya Mariya, kasancewar gidan babu nisa hakan yasa nan da Nan Hajiya Zaliha matar Alhaji Aliyu Mekudi tazota cikin sauri, bayan sun gaisa nan take Alhaji Mekudi yafara basu labari tiryan-tiryan yanda akai yasamu wannan jariri. *** *** *** Niger Republic Bayan Farouq yakawo mata rubutu Jamila tajuyeshi a kofi takawowa Bilkisu tace"Yaya gashi ki kar6a kisha" Bilkisu ta kalli Jamila dajan idonta tace"ina hayyacina,lafiyata kalau Jami,talauci yasa Sulaimanu yagudu yabarni da tsohon ciki,na haihu kwana tara dasuka wuce,ahanyata ta zuwa nan munhadu da 'yan fashi....." Tsaf Bilkisu ta zayyane musu abinda yasameta har kukan da yaron yake tayi ahanya har zuwa lokacin data qwace daqyar daga hannun 'yan fashi.... Tun kafin ta qarasa basu labarin Jamila take kuka,shi kansa Farouq saida ya goge qwallar tausayi daga idonsa,cikin jajircewa irinta maza ya dubeta yace"ki kwantar da hankalin ki Yaya,insha Allahu d'anki yana cikin aminci,yanzu babu wani abu dakika riqe amatsayin shaida wanda zamuyi bincike dashi ko Allah zaisa mugane inda yaron yake? " Cikin sauri Bilkisu ta goge qwallar idonta tazana masa number motar aqasa,batajin ko nanda shekara d'ari ne zata manta number wannan mota, bayan ta rubuta masa ta kalleshi tace"motar baqar kala ce da'ita,katemaka min Farouq" Farouq ya girgiza kansa yace"kiyi haquri Yaya,insha Allah gobe zanje police station inyi report,za'a ga d'anki da iznin Allah" Sai alokacin tayi wata irin ajiyar zuciya,sannan Jamila tagoge hawayen idonta tabata shayi tasha. *** *** *** Lagos Nigeria Hajiya Zaliha takama jariri ta rungume sai walwala takeyi bakinta yaqi rufuwa kamar gonar audiga,Yaya Mariya ta kalleta tace"to Zaliha,Kinga de kundad'e kuna neman haihuwa Allah bai kawo ba,yanzu gashi sama taka kin samu yaro,dan Allah Zaliha, kiriqe yaron nan amana, bashida kowa saimu,idan muka riqe shi da gaskiya muma saiki ga Allah yatemakemu ta dalilin sa" Cikin tsananin farinciki Hajiya Zaliha ta kalli mijinta Aliyu Mekud'i da yayarsa Hajiya Mariya sannan tace"Yaya insha Allahu bazan baku kunya ba,zan riqeshi irin ruqon da mahaifiyarsa zata masa" Alhaji Mekud'i yayi wata irin ajiyar zuciya,dama Sam baya jin Zaliha, yasan bazai samu matsala da'ita ba kamar yanda yasani tana bala'in qaunar Yara. Yaya Mariya ta kalleshi tace"to Alhamdulillah,Aliyu kar6eshi kayi masa hud'uba, sai kaje masallaci atara mutane suma su shaida sunansa" Cikin farinciki Alhaji Mekudi ya kar6i jaririn daga hannun Zaliha wadda takeji kamar tagama samun komai a duniya tunda gashi Allah yabata yaro. Cikin ikon Allah Alhaji Aliyu Mekudi yayiwa yaro hud'uba da suna JAWAD, yad'ago kansa ya kallesu yace"daga yau sunansa Jawad A. Mekudi" (Muhammad d'inmu yakoma Jawad 😭) Farinciki ya wanzu a fuskar Yaya Mariya da Hajiya Zaliha,Yaya Mariya tace"masha Allah, Allah yaraya mana Jawad" Alhaji Mekudi yace"Amin ya Allah yaya" Itama Hajiya Zaliha tace"Allah yarayamin Baby na" Cikin farinciki suka amsa mata gaba dayansu,daga nan yadauki yaron yafita masallaci dashi,abunka da me kudi nan da nan aka siyo goro da alawa aka rabawa mutane a masallaci,liman ya kar6i yaro yayi masa Addu'ah yasa masa albarka,sannan Alhaji Mekudi yadawo gidan yayar tasa, basu zauna ba, kai tsaye asbiti suka wuce duka su ukun,wani qwararran doctor yaduba Jawad ciki da waje ya tabbatar musu da cewa yaron yanada cikakkiyar lafiya babu abinda yake damunsa,daga nan likitan ya rubutawa Hajiya Zaliha magungunan da zatayi amfani dashi ruwan nono yazo domin taci gaba da shayar da Jawad. Sai dare suka dawo gidansu shida Zaliha,kasancewar dare ne hakan ne yasa ba kowa ne yaga Jaririn dake hannun Hajiya Zaliha ba. Saida yaraka su ciki sannan yasake futowa driver ya dauke shi suka fita da mota guda biyu,kai tsaye sayaiyar kaya yafara yiwa Jawad,hatta da d'an qaramin gadon kwantar da jarirai irinna turawa saida aka hado dashi,siyaiya aka yi masa ta hauka kamar a yarinta zai tabbata bazai girma ba,duka mota biyun dasuka fita da'ita saida suka cikota da kayan Jawad,bayan sun dawo gida yatsaya a farfajiyar gidan mutane suna sake yimasa Allah sanya Alkhairi akan sabon kamfanin dayaje qasar Nijar yabude,yayinda ma'aikata suke shigar da kayan siyaiyar tasa zuwa cikin falo. Bayan yadawo falo yana zama guard dinsa guda daya yashigo falon cikin ladabi ya rissina yace"Yalla6ai ya za'ai da mutumin da muka kusa kadewa jiya,kace a bashi masauqi idan kadawo zaka ganshi" Alhaji Mekudi yadafe goshinsa da hannunsa yace"subhanallah, na manta dashi wallahi, jeka shigo dashi" Cikin sauri guard din yajuya,yayinda Alhaji Mekudi yajuya yana bawa Hajiya Zaliha datake sanyawa Jawad pampers labarin abinda yafaru jiyan. Cikin mintuna qalilan aka gabatar masa da Malam Manu wanda kwana daya kawai harya fara sauya wa black beauty din fatarsa taji esi da naman kaji,Alhaji Mekudi yazuba wa Malam Manu ido yana kallonsa,yayinda Malam Manu ya shagala a kallon kyakykywan yaronda Hajiya Zaliha take sakawa wata hadaddiyar singlet ta jarirai,jiyake kamar ya dauwama yana kallon yaron,yaji lokaci d'aya wata matsananciyar qaunar yaron tana ratsa shi. Alhaji Mekudi yace"bawan Allah daga ina kake? Sannan tunanin mekake kana tafiya haka akan titi har mota tazo tabigeka baka sani ba?" Malam Manu yayi shiru cikin yanayin damuwa,bai dauki wannan bigeshin da mota tasoyi abakin komai ba face haqqin Bilkisu daya fara bibiyarsa,ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan yace"Ina tunanin aikin dazan nema nafara ne intara kudi sannan in koma wajan iyalina,ni mutumin jihar jigawa ne,nabar iyalina a halin babu,damuwa tamin yawa ganin tunda nazo cikin garin Lagos babu wata sana'ah dana samu domin in riqe kaina, tunani yamin yawa hakan yasa bansan motarku tazo kusana ba" Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya,Hajiya Zaliha tayi kissing goshin Jawad tasakashi a qirjinta ta rungumeshi tana shashshafa masa baya tana so yayi bacci, sai lalla6ashi take saikace d'an gwal (😚). Kallon Manu yayi bayan yagama ajiyar zuciyar yace"to zan baka aikinyi insha Allah, kaga nima asali na dan arewa ne, nema ne yakawo ni garin nan har Allah yasa nan garin yazama kamar shine tushena yanzu,zaka iyayin driving din mota?" Cikin sauri Manu yace" zan'iya Alhaji,a dacan ai na'iya tuqin mota kafin iyayena su rasu" Alhaji Mekudi yace"to zan baka driving,sannan akwai wajan zama, zaka dinga zama anan tare damu insha Allah" Cikin sauri Manu yasake rissina wa duk da yana zaune, yayi godia Iya godia, Alhaji Mekudi ya kalli guard dinsa yace"aje anuna masa masauqinsa " Guard d'in ya amsa cikin biyaiya,sannan yasaka malam Manu agaba zasu fita daga falon, saide kafin su fice saida Malan Manu yasake juyawa ya kalli Jawad dake kwance a kafad'ar Hajiya Zaliha. Washegari tun safe har azahar ruwan nonon Hajiya Zaliha baizo ba,saboda wannan dalilin Alhaji Mekudi ko office baije ba,Hajiya Zaliha kuwa hawaye tafara ganin Jawad din yafara galabaita,dole saida aka kira doctor gida yazo yasake dubashi yafada musu yunwa yakeji,gashi nono yaqi zuwa,hakan yasa likitan ya rubuta musu Kala kalar madara ta jarirai,Alhaji Mekudi yabada umarni akawo wannan madara, aikuwa nan da nan aka kawowa Jawad madara katan katan,Hajiya Zaliha tahad'a masa tafara bashi,nan take yafara sha babu musu,sai alokacin hankalinsu ya kwanta. *** *** *** Niger Republic A6angaren mutanan Niger kuwa tun safe da Farouq yafita da number motar wajan police yanaso yaji yanda za'a yi,Bilkisu taqi ci taqi sha tana jira yadawo taji Ina aka tsaya,Jamila sai kallonta take cikin tausayawa,duk da bata haihu ba taji zafin rashin wannan yaro jitake kamar d'anta ne aka tafi dashi. Farouq yana dawowa Bilkisu me gwanjo tamiqe tsaye tanufeshi tana fadin"Farouq ya ake ciki?" Cikin sanyin jiki Farouq yace"Yaya abun nanfa ba d'an qarami bane,naje nayi report sannan na basu number motar sun tabbatar min cewa ba motar qasar Nijar bace,motar daga Nigeria take,wai wani gari Lagos, kuma nima sai bayan nakai musu naga sunan garin sannan natuna ba motar qasar nan bace,tashin hankali ne ya hanani fahimta tun jiya dakika rubuta min,amma kiyi haquri sunce zasu tura wasiqa zuwa hukumar garin ko Allah zaisa adace...." Tun lokacin dayace ance motar qasar Nigeria ce, daga nan tadena fahimtar komai tasan cewa a Nigeria ma taji labari ana cewa Lagos da nisa,sai an kwana ake zuwa,tasan cewa shima Muhammad shikkenan yatafi yabarta,lokaci d'aya idonta ya rufe ruf...tadena ganin haske sai duhu.... Cikin sauri Jamila tatarota tana fadin"innalillahi Farouq riqeta karta fadi tasuma fa" Farouq yayi azamar tareta shida Jamila, suka samu suka kwantar da'ita akan tabarmar kaba wadda take shimfide a saharar tsakar gidan nasu, Jamila ta debo ruwa tashafa mata,lokaci daya taja wani irin numfashi tafarka azabure tana fadin "Muhammad!!!" sannan tafashe dawani irin kuka,Jamila ta goge hawayen idonta, cikin muryar kuka tace"Yaya kiyi haquri,inda rabo watarana zaku had'u,kisa dangana aranki Yaya ubangiji shine yasan nufinsa akan hakan" cikin tashin hankali da damuwa Bilkisu tafara magana tana fad'in"yanzu shikkenan na salwantar da d'ana dakaina? nasan cewa bazai soni ba, bazai yafemin ba" Cikin sauri dakuma juriya irinta maza Farouq yace"Yaya meyasa zakice bazai soki ba? akwai yaron da uwa zata haifa sannan yazo yaqi uwarsa?" Cikin kuka Bilkisu tace" Farouq ban shayar dashi ba tayaya zai soni? koda zai soni ba kamar yanda natsaya na shayar dashi tsawon shekara biyu ba,nasan yanzu duk inda yake bashida lafiya,baisha isasshen nono ba,ba lalle yayi basira kamar sauran yara sa'anninsa ba,ba zaiyi kuzari kamar suba,bazai tashi da qawazucin uwa ba..." Jamila ta girgiza kanta cikin muryar kuka tace" karkice haka Yaya,jariranda uwa take mutuwa tabar su kuma su tashi da basirar sufa Yaya? ubangijin daya rabaki da d'anki zai azurtashi da wad'annan abubuwan dakika lissafa koma fiyeda haka..." (karfa ace inason kashe Bilkisu saboda yanayin rayuwa ato nasan haliπŸ˜‚) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El YaqoubβœπŸ»πŸ’ *ME 'DEBE KEWA*πŸ’ ('yar me gwanjo) Writing By Amnah El Yaqoub Dedicated to Bilkisu's name https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu 7&8 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. ___ Shima Farouq yayi ajiyar zuciya ya kalleta yace"abinda Jami tafad'a miki hakane Yaya,kiyi haquri ki kwantar da hankalin ki,ki daure ki kar6i wannan qaddarar a yanda tazo miki,Yaya kefa musulma ce,nasan ki da haquri ko a baya,yanzu ma ki daure kici gaba da haqurin" Bayan yayi shiru itama Jamila tad'ora daga inda yatsaya,haka suka zauna su biyun sukai amfani da kalamai masu dad'i da hikima suna yi mata nasiha suna qara lallashinta. Aranar babu inda Farouq yasake fita,yazauna agida yana taredasu,sai yamma yafita kai tsaye yaje wajan limamin unguwarsu yayi masa bayanin halin datake ciki,yanemi yabashi taimakon wasu addu'o'in wanda zai dinga yimata ko Allah zaisa ta kwantar da hankalin ta,babu musu kuwa liman yazauna ya rubuta masa addu'o'i kala-kala,sannan yayi masa rubutun dangana yace akai mata tasha, sannan kullum ya dinga zuwa yana kar6a mata rubutun. hakan ce ta kasance kuwa,kullum Farouq zaije wajan liman ya kar6o mata rubutu,agabansa zata shanye sannan ne hankalinsa zai kwanta,cikin ikon Allah da taimakon Farouq Bilkisu tafara dawowa cikin nutsuwarta,tadena suma tadena kuka. **** Haka kwanaki suka dinga tafiya suka koma satittuka har zuwa watanni,acan Nigeria kuwa har Jawad yafara rarrafe,abincin sa idan za'a bashi ma'aikata kusan guda uku ne suke kula da abincin,idan yafara 6arna babu wanda yake masa magana,ko anyi magana tofa Hajiya Zaliha zatace a barshi yayi wasansa qwaqwalwar sace take bud'ewa a wannan lokacin,ma'aikatan gidan mata suna so su dinga d'aukar sa saboda yanda yake basu sha'awa amma basu Isa su doshi inda yaron yakeba Hajiya Zaliha zata hana,komai sai ita,haka idan anayi masa wani abu kamar wanka kokuma idan yana wasa yad'an bige hannunsa yafara kuka,ma'aikaciyar datake kula dashi alokacin batayi saurin daukar mataki akan kukan Jawad ba, to kai tsaye Hajiya Zaliha zata koreta daga aiki,kwata-kwata batason ganinsa yana kuka,da Jawad yayi kuka gara taita korar ma'aikatanta.(πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ) Lokacin da aka sakashi a makaranta yana playgroup motoci guda biyar ne suke kaishi,haka guda biyar ne suke zuwa d'aukoshi gaba d'ayansu security ne acikin motocin suna bashi kariya,har gaban motar Hajiya Zaliha zata kaishi tasa shi a motar har motarsu tafita daga get d'in gidan bata daina yimasa bye bye. Lokacin daya fara koyon magana da sunan MAMA yafara a bakinsa,amma Hajiya Zaliha saita hanashi cemata Mama saide Mummy. **** Niger Republic Acan Nijar kuwa Bilkisu takasa sukuni, koda yaushe zaka sameta shiru babu um bare um-um,yauma photon Jawad ne a hannunta tana kallon photon da'aka yi masa tun yana jariri kafin subar jihar jigawa,photon ma ko kala babu irin farin photon nan ne nada fari marar kala. Jamila datake zaune agefenta tana tufke dogon gashinta wanda yazo mata har gadon bayanta,ta kalli Bilkisu sannan tayi wani irin murmushi na damuwa,cikin lallashi tace"Yaya Photon nanfa ba yaron ne zai futo daga ciki ba" Hawaye yazubo daga idonta,tasaka hannunta ta share hawayen " yatafimin da d'ana..." Abinda tace kenan. Jamila ta matsa kusa da'ita tace"Yaya kiyi haquri,kwana biyun nan kinsake saka damuwa aranki kamar baya,tun safe kin riqe photon nan kinkasa saka komai acikin ki ina tsoro kada ulser ta kamaki yaya" Cikin sauri tasaka bayan hannunta ta share hawayen,sannan tamaida photon ma'adanar sa ta6oyeshi,ta dauki butar shayinsu ta zuba tafara sha. **** Lagos Nigeria Lokacin da Jawad yayi shekara uku,a lokacin yana yawo ko'ina yana gudu,haka kawai Alhaji Mekudi da Hajiya Zaliha zasu sa ad'aukeshi a kaishi wajan wasan yara,awajan wasan ma duk inda yatafi da gudu guard din dasuka rakashi suke binsa su kamo shi,ko da yaushe idonsu yana kansa saboda kada wani abu yasame shi,sosai suke masa gata kamar d'an shugaban qasa. A shekarar 1996 Jawad yayi shekara goma,har zuwa wannan lokacin Malam Manu yana taredasu,yanzu yazama shine yakejan Alhaji Mekudi zuwa duk inda zasu. Har zuwa wannan shekarun Malam Manu bai koma gida ba,bai nemi Bilkisu ba. daga wannan lokacin ne kuma abun mamaki Alhaji Mekudi yake daukar Jawad da kansa ya kaishi kasuwa,ya had'ashi da wasu 'yan kasuwa su dinga d'ora masa tallar pure water,gashi tun yana yaro kasancewar kafin ya nemi abu anyi masa hakan yasa yazama baqin miskili,duk lokacin da Alhaji Mekudi ya kaishi yayi tallar pure water baya fad'awa Mummy,haka kullum yake sashi agaba ba tareda wasu security ba ya kaishi a wuni ana dora masa tallar pure water yana yawo dashi cikin kasuwa waje-waje yana siyarwa,saida yagama gogewa a fannin saida ruwa sannan yafara daukar sa yana kaishi wajan dako,kullum zai kaishi wajan 'yan dako yashiga cikinsu shima yayi dako yasamu kudinsa. Da Hajiya Zaliha taga fitar tasu tafara yawa kai tsaye ta tambayi Alhaji Mekudi cewa Ina yake kai Jawad ne? Shima Alhaji Mekudi kai tsaye yafuto fili yafad'a mata wajan dako da tallar ruwa yake kaishi, Hajiya Zaliha tanajin haka tafashe da kuka harda shashsheka. Alhaji Mekudi yakama hannayen ta yariqe ya sassauta murya yace"Zaliha, ki saurareni dakyau,sonake nakafa Jawad dakyau yanda zai zama cikakken mutum yasaba da gwagwarmayar rayuwa,abinda nake kaishi yakeyi yanzu nima dashi nafara har Allah yakawoni wannan matsayin a yanzu,inaso Jawad ya goge a fannin kasuwanci karki manta yaron nan shine goben mu,idan muka ce ahaka za'a ci gaba tayaya zaisan rayuwa har ya'iya kula damu idan muka tsufa?,duk abinda kikaga inayi kiyi haquri nasan kinajin ciwo to kiyi haquri ki kawar dakai" Hajiya Zaliha bata sake magana ba, amma qunci iya qunci tana jinsa,a wannan lokacin ne kuma kasuwancin Alhaji Mekudi yasake ha6aka,yana harka da manyan mutane yasake bude wasu kamfanunnika a jihohi daban daban na Nigeria harma da qasashan qetare,yazama babban mutum ganinsa sai ansha wahala saboda yanda yamaida kansa busy saboda aikin,ya mallaki abubuwan duniya dayawa kama daga jiragen ruwa,dana sama,helicopter,babu wanda Alhaji Mekudi bashi dashi,ganin capital d'in Nigeria yakoma Abuja yabar Lagos kuma yana harkoki dayawa a Abujan hakan yasa suka tattara suka bar Lagos da zama suka koma Abuja. Shekarar dasuka koma Abuja a shekarar Hajiya Zaliha tasamu ciki ta haifi d'anta namiji aka sanya masa suna FU'AD. 2003 Alhaji Mekudi yatura Jawad karatu qasar Italy. **** Tsawon wannan shekarun Bilkisu ta d'auki dangana tasawa ranta haquri akan 6atan yaronta,Farouq yabata Jari taci gaba da saida kayan Gwanjo. A da mutane suna cewa tanada nasibi akan saida kayan gwanjo bata tabbatar da haka ba sai yanzu,gida gida take shiga takai tallar kayanta kuma nan da nan kayan zasu qare tasake saro wasu,zamansu lafiya kalau itada Jamila,tana al'amuran rayuwarta cikin kwanciyar hankali saide fuskarta babu walwala,babu fara'ah,haka babu yawan magana,abinda tasa agaba kawai shine saida kayan gwanjo,nan da nan kuwa sunanta na BILKISU ME GWANJO yadawo. Acikin shekarar 2005 Allah yabawa Jamila ciki,Farouq da Bilkisu me gwanjo sunyi farinciki,gaba d'aya su ukun kowa yana qoqarin ganin sun taru sun kula da cikin Jamila kasancewar sun dad'e shekara da shekaru babu haihuwar,cikin ikon Allah 2006 Jamila ta haihu,tahaifi 'yarta mace mai tsananin kyau kamar Jamila,babu abinda yarinyar ta d'auko na ubanta,komai da komai na Jamila ne,uwa uba gashin kan yarinyar yayi yawa,idan 'yan barka sukazo ba koda yaushe suke nuna yarinyar ba saboda bakin mutane. Ranar suna aka sanyawa yarinya suna INAAS ma'ana (ME 'DEBE KEWA). Tunda aka haifi Inaas Bilkisu tafara walwala saboda gani take kamar Muhammad d'inta ne lokacin dayake yaro,tana tsananin qaunar yarinyar, Jamila bata mata komai,kullum Bilkisu ce takewa Inaas wanka,wanki da duk wani abu daya shafeta. 2007 Jawad yagama Degree dinsa,adede lokacin shekarar Inaas d'aya a duniya,a wannan yanayin ne kuma tashin hankali ya sauka a gidansu Bilkisu,inda suka wayi gari sukaga Jamila tarasu sakamakon zazza6in kwana d'aya (😭) Sun shiga tashin hankali sosai,daga nan ne ruqon Inaas yadawo hannun Bilkisu,Farouq yace yabata ita halak malak. 2010 Jawad yagama masters dinsa,alokacin shekarar Inaas hud'u,tayi bala'in wayo ga surutu kamar aku,gashi de gidan nasu babu mutane daga Bilkisu sai Farouq amma idan tazaro wata maganar tafad'a sai Bilkisu tayi mamaki. Tun tana shekara hud'un gashinta ya sauko har d'uwawunta,haka Bilkisu zata sa abu ta rage mata shi saboda yayi yawa,rana guda take warewa tazauna kawai wannan ranar ta gyaran gashin Inaas ce,sau tari idan tana gyarawa yarinyar gashinta ba kowa ne yake zuwa ranta ba sai Jamila mahaifiyar Inaas,itama haka take fama da gashi kamar 'yar India. Inaas tashiga ran Bilkisu,tanaji da'ita kamar Muhammad d'inta,ta shagwa6a yarinyar kamar goyon kaka,tun Inaas tana qarama Bilkisu ta lura yarinyar tanada masifar kyau mai fizgar mutum,wanda kallo d'aya zaka mata kaji tatafi da imanin ka,haka kawai sai tasa yarinyar agaba tana kallonta tana tunani inama ace Muhammad d'inta yana nan ta had'ashi aure da Inaas? Farouq daya dawo daga makarantar kud'i (private school) inda yake koyarwa ya dinga yiwa Bilkisu magana amma Inaaaaaa!,Bilkisu tatafi tunani tana kallon Inaas datake wasa tana tunanin inama ace d'anta yana nan, Farouq yadafa ta,tayi firgigit tadawo hayyacinta,yayi zaton tunanin d'anta takeyi,hakan yasa ya sassauta murya cikin lallashi yace"kiyi haquri insha Allah watarana zakiga d'anki" A shekarar 2014 Jawad yagama p.h.d dinsa a fannin kasuwanci,saiya kasance tundaga Degree har master's zuwa p.h.d gaba d'ayansu a fannin kasuwanci yayi bisa umarnin Alhaji Mekudi Alokacin Inaas tana primary,surutu sai abinda ya qaru,duk lokacin da za'a rubuta sunan 'yan surutu a aji to kana dubawa zakaga sunan tane nafarko (πŸ˜‚) ______ 2024 (yanzu kenan,nagama baku labari, mun bar shekarun baya mundawo zamanin mu,zamu cigaba da labari taurarinmu sun girmaπŸ’ƒπŸΌ) Agidan Alhaji Mekudi kula da komai yadawo hannun Jawad,duk wasu takardu na kadarorin Alhaji Mekudi sunkoma sunan Jawad,acikin shekaru 37 d'innan arziqinsu yaci uban nada, Jawad yatsaya tsayin daka babu abinda yake face kasuwanci,tun kafin amaida sunan kadarorin izuwa sunansa haka yake aiki baya zama, bayan komai yadawo qarqashin sama bai zauna ba,saima himma daya qara, saida ya kasance Jawad yanada resuna na kamfanin-nikansa sama da guda talatin aduniya,yana zuwa manyan qasashe daban-daban,har yanzu yana nan yanda yake tunda can baya magana,babu abinda yaragu daga miskilancinsa sai qaruwa ma da abun yayi kasancewar tun yana yaro kafin yanemi abu,anriga anyi masa basai yabude baki yayi magana ba,hakan yasa yasake zama miskilin gaske,matsalar sa d'aya bashida kirki a fannin kasuwanci,inde zakai wasa da aikinka to bazaka shirya dashi ba. Manya-manyan 'yan kasuwa da 'yan siyasa sun san Jawad amatsayin shugaban kamfanin jiragen sama,idan aka had'a kud'ad'en dukkanin kasuwancin sa za'a iya cewa yana samun ribar million dubu talatin a kowacce shekara,kasancewar tun yana qarami yatashi da koyon kasuwanci hakan ne yasa yazama me mutuqar basira a fannin kasuwanci, tun zamowarsa mamallakin dukannin company's dinsu daga nan yafara ruguza kishiyoyin kasuwancin sa,kafin abokan kasuwancin sa su farga har ya musu tazara bakajin sunan kamfanin kowa saina Jawad Mekudi,duk yanda d'an kasuwa yakai gayin takarar kasuwanci dashi to lokaci d'aya Jawad zai daqusheka ta hanyar rage farashin kayan kamfanin sa nad'an wasu lokaci,daga nan kuma mutane su dinga tururuwar neman kayan kamfanin sa,hakan yasa sauran manyan qasashen duniya sukasan da Jawad Mekudi. Lokacin dayayi Degree na farko akan kasuwanci yayi project dinsa,lokacin dayayi masters akan kasuwanci yayi project dinsa,haka p.h.d dinsa ma, bayan yagama karatu saida ya rubuta littattafai dadama duka a fannin kasuwanci domin na qasa dashi su amfana da irin salonsa. Yawan ayyukan dayake dasu hakan yasa yana iya kaiwa kusan shekara ko fiye da haka baishigo Nigeria ba. Jawad yahad'u sosai maqura,d'an gayu ne nabugawa a jarida,uwa uba ga kudi,ba qaramin d'aukan hankalin 'yanmata yake ba. Shine matashi na farko dayake d'aya daga cikin masu manyan kamfanin nika acikin Nigeria dama wasu qasashen. *** *** *** Niger Republic Zuwa wannan shekarar damuke ciki ta 2024 Inaas tacika shekara goma sha takwas,tayi Candy shekara d'aya data wuce,tagirma ta zama budurwa me bala'in kyau kamar mamarta Jamila,yawan gashin ta tun tana qarama har yanzu gashi yana nan har gadon bayanta,tanada tsananin kyau me daukar hankali,rana d'ai-d'ai ne ba zakaji sallamar samari a qofar gidansu ba amma Bilkisu tahana ta

Chapter 3 of 7