sunansa, sai dube-dube take tana fad'in "Malam...!!"
Amma shiru kakeji,wasu d'aid'aikun masu tafiya gona sai kallonta suke saboda sunga abun mamaki,basu ta6a tunanin akwai kyakykywar halitta kamarta acikin qaunyensu na Garin Malam ba,wani me Keke yazo wucewa shima zai tafi gona tsabar waigowar dayake yana kallonta har fad'uwa yayi sakamakon cin karo dayayi dawani tsoho.
Tana ganin abunda yafaru tasan cewa itace sila,cikin sauri taja mayafin jikinta ta6oye fuskarta,sannan tajuya takoma gida,d'akinsu tashiga tafara tattare musu kayan Shimfid'arsu,anan idonta yasaauka akan wata farar takarda,gabanta ne yafad'i da ganin takardar cikin sauri tad'auka sannan ta bud'eta,lokaci d'aya taci karo da rubutun mijinta Malam Manu inda ya rubuta mata cewa ( KIYAFEMIN ) jikinta ne yafara rawa,taji numfashinta yana sama kamar zai d'auke,hakan yana nufin kenan Manu yagudu yabarta,daqyar tasamu ta fuzgo numfashinta tareda sakin wata irin gigitacciyar qara,wanda yajawo hankalin maqotanta.
(so sadπ,sorry Mama Bilki)
Littafin ME 'DEBE KEWA na kud'i ne,300 Naira kacalππ»
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034
Amnah El Yaqoubβπ»
π *ME 'DEBE KEWA*π
('yar me gwanjo)
Writing By Amnah El Yaqoub
Dedicated to Bilkisu's name
https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu
3&4
maqotanta sunyi tunanin naquda ce ta taso mata,hakan yasa suka shigo a fujajan,anan suka tarar da bilkisu tana kuka tad'ora hannunta akanta,d'aya daga ciki ce tafara bubbuga bayanta alamar lallashi tace"Balki me gwanjo kiyi haquri,ciwo ba mutuwa bane"
Cikin kuka da baqin cikin halin da tashiga tace"Manu ya gudu yabarni Bintu,bai duba maraicina ba yatafi yabarni da tsohon ciki"
Wadda Bilkisu takira da Bintu saita zabura taja gefe guda jikinta yana rawa,d'ayar maqociyar tata kuwa duka hannunta biyu tasa tarufe bakinta hawaye yana zuba a'idon ta,cikin kuka tafice da gudu tabar gidan taje tafad'awa mijinta halin da'ake ciki.
Kan kace me,labari yaje kunan mai Gari,Bintu tana rungume da Bilkisu tana lallashinta saide itama hawaye take zubar wa tana fad'in"kiyi haquri me gwanjo,insha Allahu muna nan tare dake bazaki tagayyara ba"
Sallama suka jiyo daga qofar gida,Bintu taje taduba,mutumin dayake tsaye yace"kece Balki me gwanjo?"
Bintu ta girgiza kai hawaye yana zarya daga idonta tace"Balki tana ciki"
"kice mata megari yana kiranta,maqocinta yakai masa labari yanzu"
Bintu batace masa komai ba tajuya,takamo hannun Bilkisu suka futo idanun nan nata yayi jajir abunka da farar mace,zama sukai agaban megari yayinda idanun fadawansa yadawo kan Bilkisu,wasu suna mata kallon qurulla wasu suna mata kallon tausayi, maigari yayi gyaran murya yace"Munsamu labarin abinda yafaru,kiyi haquri insha Allahu za'a ga mijinki,haqiqa Sulaimanu bai kyauta ba,kuma dole zai kar6i hukunci mai tsanani daga fada,maqociyarki fatsime tafad'awa mijinta Haruna gashinan a zaune,Haruna yazo fada ya sameni yafad'a min abinda yake faruwa,bamuyi qasa a gwiwa ba mun tashi matashi me hanzari akan Keke, mun turashi Garin Gandun Galadima yaje yanemo Sulaimanu,nasan duk inda Sulaimanu yake,bazai wuce garin Gandun Galadima ba"
Rufe bakin megari keda wuya,dan aikensa yadawo,lokaci d'aya idanun fada yakoma kansa,cikin ladabi matashin yadubi maigari yace"Allah yaqarama lafiya mun bincika cikin Gandun Galadima kaf....babu malam Manu babu dalilin sa,da yiyuwar yayi nisa ranka ya dad'e"
Bilkisu tanajin bayanin wannan matashi kanta yasara,cikinta yayi wata irin juyawa,lokaci daya tasaki qara tafara naquda afadar megari,nan take megari ya kalli Bintu da Fatsime maqotan Bilkisu yace"ku qarasa da'ita cikin gidana ta sauka acan har mugama binciken inda Sulaimanu yake"
Babu musu fatsime da Bintu suka kama Bilkisu datake d'aga qafa daqyar saboda naquda tazo mata gadan-gadan sukai cikin gidan megari da'ita.
Da taimakon 'Dayyaba matar maigari su Bintu da Fatsime suka had'u suka dinga tausar Bilkisu har Allah ya sauketa lafiya,ta haifi d'anta namiji kyakykywa dashi masha Allah,kallo d'aya zaka yiwa yaron kaji yashiga ranka,fari ne tas qato,babu abinda ya dauko na mahaifinsa sai yatsun qafarsa sak irinna Manu,babu rama atareda yaron 6ul6ul dashi kamar ba rainon Gaarin kwaki ba, bayan sun tsaftace su itada yaran haka ta rungume shi a qirjinta tana hawaye,gashi de abinda take fatan haifa Allah yabata,saide babu Manu,baisan me suka haifa ba,baisan awanne hali take ciki ba,baisaniba tana raye kota mutu ta dalilin haihuwar d'ansa,hawayen idonta ta share tazuba wa yaron ido tana kallonsa yayinda yafarka daga baccin dayake shima idonsa cikin nata,wani hawayen ne yasake zubo mata tana kallonsa tana murmushi ga hawaye,Fatsime ce tashigo takawo mata kunun kanwa,suka zauna agabanta suna sake bata haquri dakuma tabbacin insha Allahu za'a ga mijinta.
Sai dare aka kawo mata dahuwar Jan nama umarnin maigari kenan,haka take cin naman amma daqyar take iya had'iyeshi saboda jin wani irin abu aqarqashin wuyanta wanda takeji kamar dutsi ne awajan tsabar damuwa.
Washegari ma tasamu kulawa wajan matar maigari anyi mata wankan jego irinna mutanan da,taci dumaman tuwon dawa dakuma kunun kanwa,babu 6ata lokaci kuwa ruwan nonon ta yake zuwa yaronta yanasha yana qoshi.
Da misalin qarfe goma shad'aya na safe kira yasameta daga maigari,wannan lokacin bayan Fatsime da Bintu maqotanta harda ita kanta 'Dayyaba matar maigari suka nufi fada,yaronta yana rungume a qirjinta ta qanqameshi,bayan sun zazzauna maigari yadubeta yace"Balki saide kiyi haquri,mun tura mutanan mu Garin Galadima jiya ba'a ga Malam Manu ba,munsake tura mutane cikin garin Hadejia da Gaarin Gabas,har zuwa Birniwa,amma babu labarin Mijinki Manu,wasu daga cikin masu zaman fada sunbawa fada shawara asake bincikawa, duk da haka fada batayi qasa a gwiwa ba munsake tashin mutane sun nufi yamma har zuwa garin Gujungu,amma babu Manu, babu Labarinsa"
Lokaci d'aya Bilkisu tafashe da kuka harda shashsheka.
'Daya daga cikin masu zaman fada ya gyara zaman sa ya kalli Bilkisu sannan yakai dubansa wajan Maigari yace"Allah yaqara ma lafiya ai tunda akayi irin wannan nema ba'aga Manu ba to haqiqa yagudu yabi duniya,akwai manema aure dayawa anan,saboda haka kawai karaba wannan auren nasu,saita samu miji kamar de nid'innan sai tayi aurenta"(π²π€)
Cikin tsawa Megari yace"Rufe mana baki Bala"
Yajuya ya kalli Bilkisu yace"Balkisu nasan danginki suna qasar Nijar,zakiyi haquri ki zauna damu har aga mijinki? Ina miki albishir zamu harhad'a miki kud'i kidinga sana'ar saida kayan gwanjo,tunda med'akina tafada min cewa duk garin nan,bayan Tabawa me saida kayan gwanjo babu wanda yakaiki samun nasibi akan saida gwanjo,zaki zauna tare damu?"
Ba tareda tunanin komai ba,Bilkisu tagoge qwallar data taru a'idon ta tace"Zan tafi qasarmu Ranka yadade"
Megari yace"to kiyi haquri kizauna damu idan anyi suna saiki tafi,kafin nan kema kin sake samun qwarin jikinki"
Bata iya amsa masaba tatashi suka koma cikin gidan maigari,domin kuwa idan tace zatayi magana haqiqa kuka ne zai biyo baya.
Zaman Bilkisu agidan maigari babu laifi,tana Samun kulawa kamar tana gidan iyayenta,matar maigari 'Dayyaba cikin kwana shida ta koya mata yanda zata dinga wankan yaronta,Bilkisu tanajin bala'in qaunar d'anta,koda yaushe idon yaron qur akan uwarsa kamar ba haihuwar kwana shida ba,haka itama Bikisun kullum idonta a kansa tanajin wani irin nishad'i idan ta tuna ko bata da kowa to tabbas tana dashi,tasan cewa koda kowa zai gujeta shikam yana tareda ita,ita kanta 'Dayyaba matar maigari jitake kamar ta qwace wannan yaro na Bilkisu,yaron abun sha'awa fari qal dashi kamar Mamansa.
Yauda safe tanayi masa wanka tana masa surutu kamar tana magana dame hankali,bayan tasakashi acikin zani ta lullu6eshi tana qoqarin shafa masa mai ajikinsa ta kalleshi cikin sanyin jiki tace"Babanka yagudu yabarmu,nasan kai bazaka gudu kabar Mama bako?Mama tana sonka,karka gudu kabarta kaji? idan kabarni bazan iya jurewa ba,nima ina tareda kai Babana,yanda Babanka yagudu yabarmu insha Allahu saimun bashi kunya,insha Allahu saika mulki mutane dayawa a duniyar nan,kaine d'ana,d'anda nafiso fiyeda komai a rayuwata...."
tana kaiwa nan ta sunkuya ta sumbaci goshin yaron.
'Dayyaba matar maigari tashare hawayen tausayin Bilkisu,sannan tajuya ahankali tafasa shigowa cikin dakin bayan tagama jin duk maganganun da Bilkisu take yiwa yaronta.
Washegari tacika kwana bakwai da haihuwa,kuma a ranar aka sanyawa yaron Bilkisu suna MUHAMMAD kamar yanda ta buqata,yaro yaci sunan mahaifinta,Megari yasa mutanan gari sukayi karo-karo aka hada mata kudad'e masu yawa aka bata,a ranar kuma aka kira me photo yayiwa yaronta photo yace zaije cikin garin Hadejia ya wanko mata photon gobe zai kawo mata,a ranar taso tafiya amma saboda photon ta tsaya tasake kwana,washegari da safe kuwa me photo yakawo mata,tashirya yaronta tagoyashi,sannan itama ta shirya suka futo.
Ba'iya maqotanta ne suka futo domin yimata rakiya ba,harda matar maigari da sauran 'yan unguwa duk suka futo qwansu da qwarqwatarsu domin yin sallama dame gwanjo,bayan tayi sallama da Megari tasake yimasa godia tajuya ta kalli gidansu,ta tuna irin rayuwar dasukai itada Sulaimanu,taji hawaye yanason taruwa a'idon ta amma ta daure batayi kuka ba,tasake tuna lokacin da iyayenta suke raye,suka damqa amanarta a hannun Manu,ashe Manu talauci zaisa ya gujeta,a wannan lokacin kam saida ta zubar da hawaye,tana kuka mutanan arziqin qauyen suna kuka haka tahau mashin suka tafi.
Bayan sun futo daga Garin Malam, suka wuce Garin Galadima, sannan suka dauki hanya har zuwa cikin garin Hadejia, a Hadeja tahau motar Maigatari,bayan mota tacika,direba yaja Mota sukabi ta hanyar malam madori,tacikin Gumel suka shiga garin Maigatari daga nan suka d'auki hanyar bodar dazata kaisu cikin qasar Niger.
*** *** ***
Lagos Nigeria
Alhaji ALIYU MEKU'DI yana tsaye agaban matarsa tana shirya shi,gefe guda kuma yana qare mata kallo yanajin tsananin qaunarta duba da yanda bata ta6a gajiyawa wajan yimasa hidima tun bayan da'aka d'aura musu aure tsawon wasu shekaru masu yawa.
Wani tsadaddan turare ta d'auka mai mutuqar tsada tafara fesa masa ajikin d'anyar shaddar sa wadda kallo d'aya zaka yiwa shaddar kasan cewa ba shaddar yara bace saide manyan attajirai,cikin murmushi ta kalleshi cikeda soyaiya tace"yau ina cikin farinciki mijina abin Alfahri na zai sake bud'e sabon Company aqasar Niger,ina Addu'ah Allah yadawo min dakai lafiya Alhaji,ubangiji Allah yabaka nasara akan wannan sabon company dazaka bud'e,Allah ya kauda ma idon maqiya"
Cikin jin dad'in addu'ar ta yasaka hannunsa yajata jikinsa ya rungume ta,hannayen sa duka biyun suna kan bajajjen hips d'inta,cikin tsantsar soyaiya yace"Amin My Dear,kema Allah yabaki abinda kikeso"
Ahankali tazame jikinta daga nashi,tasaka hannayen ta duka biyun ta riqe fuskarsa dashi sannan tace"Haihuwa....,Fatana na haihu dakai,nima inga 'yata ko d'ana suna amfani da sunan ALIYU MEKU'DI,kyakykywar nasaba,kyakykywan tushe, wannan kad'ai zai zama abun Alfahri agareni"
Murmushi yayi yakai hannunsa ya d'ora akan qugunta,yayinda hannayenta suke kan fuskarsa har yanzu,cikin jin dad'i yace"ZALIHA muci gaba da Addu'ah,Allah yana sane damu"
Qwalla ce tacika idon matar tasa wadda yakira da suna Zaliha...kafin yabata amsa landlines phone d'in dake d'akin irin tada can tafara qara,saida ya sunkuya yayi kissing fuskarta sannan yaje yad'auki wayar.
Tsawon mintuna biyu yana magana a wayar sannan yakashe yadawo wajanta yace"Aminina Alhaji Auwal yakirani,ya fad'amin already angama komai nikadai suke jira,ki kula da kanki Zaliha,banaso kisa damuwa aranki kinji ko?"
Zaliha tatashi tsaye ta fuskanci mijin nata sarqar gwal din dake wuyanta sai walwali take, ahankali kuma cikin kissa tace"idan bakaso nasa damuwa araina to kada ka saurari matan qasar Nijar,ina tsoro kada wata buzuwar ta qwace min mijina....,sannan inaso kabani dama idan kadawo inje in dauko yaro ko yarinya agidan Marayu,ina son Baby Alhaji"
Murmushi yayi sannan yace"inde hakan kikeso zamuje ki za6i duk yaron daya miki Zaliha,please ki kula da kanki banda sa damuwa"
Yana fad'ar haka bai saurari amsar taba yajuya yafice daga falon nasu.
Yana futowa babbar harabar gidan nasa wadda tayi kama data shugaban qasa,guard's d'insa suka taso suka rufa masa baya har zuwa wajanda aka adana motocinsa domin yimasa rakiya Airport,briefcase d'in hannunsa wani guard ya kar6a sannan aka bud'e masa mota yashiga suka futo daga gidan dawani irin gudu.
Adede lokacin SULAIMANU mijin Bilkisu wanda yazo garin tun kwanaki hud'u dasuka wuce, yazo wucewa zai tsallaka titi,lokaci d'aya motar da'akejan Alhaji Aliyu Mekud'i tabigeshi.
Cikin sauri suka ja wani irin birki,Alhaji Mekud'i yabude motar da kansa ya futo yadafa Malam Manu yace"bawan Allah bakaji ciwo bade ko?"
Malam Manu daya gama galabaita duk kamanninsa sun fara sauyawa saboda damuwa dakuma yunwa,ya dubi Alhaji Mekudi yace"Alhaji karka damu,banji ciwo ba"
Alhaji Mekudi yad'aga kansa ya kalli direban sa yace"kadinga driving da nutsuwa mana"
Cikin rawar jiki driver yace"to Alhaji tuba nake,kayi haquri"
Alhaji Mekudi baice komai ba yasake kallon guards dinsa dasuka furfuto daga Mota sai zare ido suke suna gyara bindigar hannunsu yace"ku kaishi gida a bashi abinci da masauqi naga kamar yana cikin damuwa,idan nadawo daga Niger zan ganshi"
Yana fad'ar haka bai saurari amsar su ba yaduba tsadaddan agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yakoma cikin Mota aka rufe masa murfin motar sukaci gaba da tafiya.
Yayinda d'aya daga cikin guard yayi sauri yakama hannun Malam Manu sukai cikin katafaren gidan Alhaji Mekudi dashi.
(Ina labarin Bilkisu me gwanjo a Hanyar tafiya qasar nijar?π€)
*** *** ***
Bayan sun bar cikin Maigatari suka wuce boda suka fice daga Nigeria gaba d'aya suka shiga cikin qasar Niger, a qasar Niger sun wuce 'Garin Isah',suka wuce 'Katurje',sunyi nisa sosai da barin 'Katurje' acikin daji motarsu ta lalace sakamakon fashewar taya,dole sai futowa sukayi suka nemi wata bishiya suka zazzauna,bayan Bilkisu dawata tsohuwa gaba d'aya motar duk maza ne,hakan yasa itada wannan tsohuwar suka koma gefe,nesa da maza kad'an sukai zaman su suna zancensu kad'an kad'an.
Kafin asamu masu gyara suzo an d'auki tsawon lokaci sosai daga baya aka sabunta musu wata tayar sukaci gaba da tafiya.
Kasancewar bata futo da wuri ba kuma ga yanayin jiran fasinjoji kafin sutaru mota tacika hakan yasa dare yayi musu ahanya,har wasu daga cikin fasinjoji sun kama bacci amma idon Bilkisu biyu,akan idonta suka shiga cikin garin 'Washawa' suka wuce garin,jaririn hannunta ne yafara kuka kamar wanda take mintsininsa,tsohuwar datake gefenta wadda take d'an gyangyadi kad'an-kad'an tabud'e idonta tace"bashi yasha mana"
Cikin sauri Bilkisu tagyara mayafin jikinta tasaka masa nono a bakinsa amma kwata-kwata yaqi kamawa,saima wani sabon kuka dayasake fashewa dashi duk ya gigitata,hawaye ne yacika idonta cikin ranta take tunanin tome yakeso?
haka ta d'auke shi daga kan cinyarta tamaida shi kafad'arta tana jijjigashi amma yaro yaqiyin shiru.
Suna gab da shiga cikin garin 'Dungas' Direban motar yataka wani irin mahaukacin birki sakamakon ganin wasu d'irka d'irkan 'yanfashi agabansa,yana taka birkin mota 'yan fashin suka yiwa motar su Bilkisu qawanya,wani babba daga cikinsu da muryar sa ta 'yan daba marar dad'in ji yace"qananun 'yan'iska kowa yafuto yazube aqasa"
Ya kalli yaransa yace"aje a futo dakomai na guzurin su akawo min shi nan"
Lokaci d'aya mutanan Mota suka fara salati,masu bacci idonsu yabud'e ras, yayinda gaban Bilkisu yayi wata irin bugawa,tasake qanqame Muhammad ajikinta,gaba d'aya ilahirin jikinta yad'auki rawa,batayi qoqarin 6oye kud'in hannunta ba,sai photunan da'aka yiwa Muhammad tayi sauri ta 6oye su acikin bujen siket d'inta naciki wanda yakeda aljihunsa irin wanda mutanan da suke sakawa domin 6oye kud'in su.
Gaba d'aya motar aka futo dasu kan titi, yanda taga suna gabzawa maza bindiga akansu kai yana fashewa da jini hakan ne yasake tsoratata tasake qanqame d'anta suka dunqule waje daya ita da wannan tsohuwar, ga Muhammad sai tsala wani irin kuka yake kamar tana dukansa,maza biyu ne suka shiga cikin motar suka kwashe komai da komai na guzurin matafiya,suka zube shi agaban ogansu.
'Daya daga cikin yaran ne yakalli inda su Bilkisu suka dunqule itada tsohuwa yace"ke dan uwarki ki rufewa yaron nan baki komu tattakaki anan wajan"
Lokaci d'aya itama tafashe da kuka,ganata gana Muhammad,tasaka hannunta tarufe masa baki,numfashin yaro yafara sama-sama kamar zai mutu cikin sauri tabud'e masa bakinsa.
d'an fashin daya ga taqi bin umarninsa cikin 6acin rai ya hasketa dawata fitilarsu me shegen haske,adede lokacin Bilkisu ta sunkuyar da kanta qasa tana jijjiga yaronta,mayafin kanta yad'an zame yayi baya kad'an sakamakon sunkuyar da kannata datayi,hakanne yasa d'an fashin yayi tozali da gashinta wanda yake sheqi da qyalli,yadawo da fitilar kan fuskarta ya haska kyakykywar fuskarta,lokaci d'aya yasaki murmushi yace"oga gawata zazzafa fa..."
Ogan su dayake zaune akan wani qaton itace,yadaka mata tsawa yace"Ke!! ajiye yaron nan kizo nan"
Bilkisu ta kalli qasa taga rairayin qasa tayaya zata kwantar da yaronta aqasa?
batayi musu dasu ba tatashi ta nufi inda Ogan yake,saide yaronta yana hannunta saima sake qanqameshi da tayi,sai jan zuciya yaron yake saboda kukan dayasha.
Agabansu ta tsugunna,Ogan ya kalleta yayi wani irin hadiyar yawu, cikin tsananin sha'awa yace"yaronki yana kuka futo da nono kibashi yasha,inkin gama dashi nima kibani"
Yafad'i haka yana kwashewa dawata irin mahaukaciyar dariya,yaransa ma suka fara tayashi.
Hawaye ne yafara zarya a'idon ta,bakinta yafara karkarwa takasa yin magana.
Wannan tsohuwar dasuka taho tare tad'aga murya tace"yaro kayi haquri karka cutar da'ita,ku kar6i duk abinda kuke so a wajanta dan Allah karku cutar da'ita"
Oga yanajin haka yadaga bindigarsa baiyi wata-wata ba ya harbi tsohuwar nan,lokaci d'aya rai yayi halinsa(π)
Bilkisu tana ganin haka tasaki kuka me sauti,shima Muhammad dayake hannunta yaci gaba da kuka,yayinda mazan dasuke qwance aqasa jikinsu yasake d'aukar rawa ganin yanda akai kisan kai awajan amma kamar sun kashe kiyashi.
Muryarta tana rawa tahad'a hannunta biyu waje d'aya tace"dan darajar Allah kuyi haquri,kuyi haquri ku qyalemu mutafi karku kashemu"
Ogansu yayi wata irin dariya yabuga qafarsa aqasa yace"kibamu wani abun,saimu qyale ku kutafi"
Cikin sauri tace"kun qwace mana komai,banida abinda zan baku,dan Allah kuyi haquri"
'Daya daga cikin yaran Ogan nasu dayake zaune akusa dashi da alama shine na hannun daman oga ya kwashe dawata irin dariya yace"kaji fa,wai batada abinda zata bawa oga,baki ji abinda matacciyar tsohuwar can tafad'a ba? mu kar6i komai a wajanki amma kada mu cutar dake,yanzu oga na zai kar6i komai kuwa"
Yana fad'ar haka ya fuzge mayafin jikinta,dogon gashinta ya bayyana,Bilkisu tasake qanqame Muhammad a hannunta na dama,yayinda takai hannunta na hagu tacikashi da rairayin qasar wajan,ogansu baiga abinda tayi ba ya sunkuya yakai hannu zai ta6a gashin kanta tafaki idonsa ta watsa masa wannan rairayin qasar a'idon sa, sannan ta kwasa aguje tafara wani irin mahaukacin gudu kamar wanda tashiga gasar tseren gudu,lokaci d'aya suma yan fashin suka mara mata baya suka bita da mahaukacin gudu.
Gudun datake ne yasa dogon gashinta yabazu a bayanta, yayinda wani ya rufe mata fuska amma bata damu ba haka taci gaba da gudu ko sanin inda zatasa qafarta batayi,wahalar da Muhammad yaji hakan yasa yaci gaba da kuka,yayinda kukan yaron yasa 'yan fashin suke binta duk inda tayi,dole qanwar naqi,dole Bilkisu tasa hannunta tarufe masa baki ganin kukan nasa shine yasa suke gane inda take,taci gudu sosai harta 6acewa ganinsu,tasamu bayan wata bishiya ta 6uya,adede lokacin suma 'yan fashin sukazo wajan sunata dube-dube,Bilkisu tana ganinsu tasake rufewa Muhammad baki yayinda wahala tasa yaron nan take ya suma(ππ»ββοΈπ₯)
Ta waiga gefenta,cikin sa'ah taga wata hamshaqiyar Mota a adane,da alama motar wasu matafiya ne suka tsaya uzuri,ahankali tafara tafiya tana nufar inda motar take,taku take sid'af sid'af ahankali hartaje wajan motar,duka glasses d'in motar a rufe suke,tana ganin idan tashiga cikin motar tarufe,ba zasuji kukan yaron ba,batasan cewa shikam yaro yariga ya suma ba(π)
Cikin ikon Allah tana bud'ewa motar ta bude alamun ba'a kulle motar ba,tana shiga cikin motar wani irin qamshi me dad'i ya bugeta da wani sanyi-sanyi da motar takeyi alamun ba'a dad'e da kashe esin ciki ba,ahankali ta ajiye Muhammad tasaka hannu zata rufe motar wannan 'yan fashin suka ganta,cikin 6acin rai suka qarasa suka fuzgota,d'ayan yasaka hannunsa ya rufe motar ga Muhammad acikin Mota (ππ»ββοΈ)
Janta sukai can bayan bishiyar data 6uya musu,Mayafin jikinta dayake hannunsu wanda suka fuzge matashi d'azu,dashi sukai amfani suka d'aure mata baki,yayinda mutum biyu suka rirriqe mata hannayenta tabaya,ogansu ya matso cikin zilama yad'ora hannayen sa duka biyu akan qirjinta yafara murzawa,baqin ciki yasa tasaki wani irin kuka gashi sun rufe mata baki,hawaye sai zarya yake a fuskar ta yayinda take girgiza masa kai alamun a'a,tanajin wani irin baqin ciki kamar zata mutu.
Adede wannan lokacin Alhaji ALIYU MEKU'DI,yazo yabud'e motarsa yashiga ya zauna ya kunnata,danjar mota takawo haske alamun mota tatashi,gaban Bilkisu yayi wata irin fad'uwa ganin an kunna motar kuma Muhammad yana ciki,lokaci d'aya ta zaro manyan idonta waje,tafara fuffuzgewa daga hannun su,amma sai suka sake riqeta,hasken wannan fitilar motar shine yasake haskawa har taga number motar,tanaji tana gani mota tafara tafiya,ganin yanda taqi tsayawa waje d'aya sai faman fuzge-fuzge take hakan yasa oga ya wanke fuskarta da wani zazzafan mari,zafin Marin yasa ta sunkuyar da kanta qasa,dogon gashinta ya sakko ya rufe mata fuska,tad'ago kanta da sauri ta kalli motar tagade da gaske fa motar nan tafiya take gakuma d'anta yana cikin Mota,lokaci d'aya tasa qafarta tadaki abunsa(π)
Tsananin azabar dayaji ne yasa ya janye hannunsa daga kan qirjinta yamaida hannun zuwa gabansa ya tsugunna yana runtse ido,ganin Mota tafara nisa yasa Bilkisu ta qwace ta kwasa aguje tabi bayan motar,tacire mayafin dasuka rufe mata baki tayi wulli dashi,tabi bayan motar da mahaukacin gudu tana kuka tana fad'in " d'ana,d'ana yana ciki,Muhammad karka tafi kabarni,...."
Tasake daga murya tace" me Mota ka tsaya!!! "
Amma inaaa,Alhaji mekud'i kokad'an baiji taba,saima gudu daya qarawa motarsa sakamakon lokacin tashin jirgin su yana gab da qurewa gashi ko cikin Nigeria bai shigaba bare yaqarasa jihar kano yagana da wasu baqi sannan yahau jirgin zuwa Lagos,haka Bilkisu tasake bin bayan motar da gudu tana d'agawa Mota hannu tana magana kamar ta6a66iya.
kasancewar gudun mutum dana mota ba d'ayaba,hakan yasa Bilkisu tanaji tana gani,Mota tatafi da d'anta idonta akan Number wannan Mota,lokaci d'aya ta tsugunna awajan tasaki wani irin qarajin kuka me tsoratar wa,adede lokacin kuma 'yan fashin suka sake zuwa zasu kamata, a wannan yanayin zuciyar Bilkisu ta bushe,ta tsinke,bata tsoron koma mezai faru yafaru,wani qaton itace dayake gefenta tad'auka tayi kukan kura ta maka musu shi,sannan tasaki itacen ta gudu,bata hango nisan tafiyar da tayi tana gudu ba,harta qaraso cikin Garin 'Dungas' a wahale,alokacin masallatai suna kiran sallar farko,tana tafiya tana had'a hanya kamar 'yar maye,ga dogon gashin kanta yayi buzu-buzu ya hargitse yana rufe mata fuska kamar na mahaukaciya,saida tazo qofar gidansu idonta ya rufe ruf...tadena ganin komai tazube awajan Sumammiya.
(so Sad....πSorry Bilkisu)
(masu karatu karfa ku manta har yanzu labarin 1986 mukeyi shekaru talatin da bakwai dasuka wuce Kenan π€yauwa)
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne, 300 ne kacal
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Tareda turo shedar biya ta wannan number 08033300034
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Amnah El Yaqoubβπ»π *ME 'DEBE KEWA*π
('yar me gwanjo)
Writing By Amnah El Yaqoub
Dedicated to Bilkisu's name
https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu
5&6
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.
Alhaji Aliyu Mekudi,yayi nisa atafiya yaji kamar motsi abayan motarsa,juyawar da zaiyi yayi tozali da jariri wanda ubangiji cikin ikonsa yasa ya farfad'o da kansa sai d'aga qafafu da hannu yake sama irinna jarirai.
Alhaji Mekud'i yataka wani irin birki ya futo daga mota yazo yabud'e gidan baya,idonsa ya sauka akan kyakykywan yaro masha Allah fari tas dashi,gabansa yayi wata irin fad'uwa ganin jaririn kyansa yayi yawa kamar ba d'an Bil Adama ba,yakai hannu zai d'auki yaron hannunsa yafara karkarwa,haka ya daure yad'auki yaron wanda yunwa tasa yasaka d'an yatsansa a bakinsa yanata tsotsa,Alhaji Mekudi yasake kallon jariri yace"innahu min sulaimana wa'innahu bissmillahirrahmanirrahim"
Yayi tunanin ba d'an mutum bane Aljanine.
Yajuya ya kalli gabas da yamma yaga babu kowa,to waye zai saka masa jariri amota idan ba aljannu ba?(π€)
ga yaro kwata-kwata babu inda zakace bahaushe ne saide Balarabe duk yanda akayi yaron aljannu ne.
Cikin sauri ya lalla6a kamar yana tsoron aljannun zasu kamashi yamaida yaron cikin mota yarufe, yakoma yatada mota yajuya baya zaije inda ya ajiye motarsa ko Allah zaisa aljannu suzo su dauki d'ansu,cikin gudu yaja motar yajuya,saide yana zuwa wajan yaga babu kowa,yaduba yasake dubawa babu alamun komai, yabude murfin motar gidan baya yakoma gefe ya yatsaya yana jira masu d'a su dauke d'auke d'ansu, wato aljannu.
Saide tsawon mintuna babu abinda yafaru,saima wasa da Muhammad yakeyi da yatsansa abakin sa idonsa abude kar ko alamun kuka bayayi.
Alhay Mekudi daya gaji da jira yakoma wajan motar yasaka hannunsa ya d'auki Muhammad,yad'aga shi sama sannan yace"ya ubangiji na,haqiqa ni bawankane mai yawan godia agareka,na kasance tsawon wasu shekaru Ina neman haihuwa ubangiji Allah baka bani ba,amma rana irinta yau ya Allah ka azurtani da wannan wanda bansan daga inda yake ba,Allah nagode maka da wannan kyauta dakamin,bazan baka kunyaba wajan yiwa yaron nan tarbiya kamar nine na haifeshi,haqiqa zan riqe amanar wannan yaro kamar yanda kayiwa sauran iyaye umarni su riqe amanar 'ya'yansu"
Ya sauke hannunsa qasa yasaka Muhammad a qirjinsa ya rungume shi,sannan ya zagaya dashi yabude motar yasaka shi a cinyarsa, yaci gaba da driving.
Da yaron a hannunsa ya gana da wasu baqin turawa akano,saida yagama dasu sannan yanufi Airport d'in Malam Aminu.
Lokacin daya qarasa filin jirgin already har jirgin dazaibi yatashi, saida yasake yin booking yajira lokaci yacika, sannan jirgin su yasake tashi zuwa Lagos.(ππ»)
*** *** ***
Niger Republic
Azabure Bilkisu me gwanjo tafarka daga baccin datake,gefenta ta kalla