mu"
Wani irin murmushi yasaki sannan ya qaraso cikin dakin yazauna agabanta,yakama hannyenta yariqe yakai bakinsa yayi kissing hannun nata sannan yace"Mummy aure fa lokaci ne"
Dan qaramin tsaki tasaki tace"Jawad kullum haka kake fada,lokaci yayi Jawad"
Murmushin qarfin hali yayi yace"Mummy aina baku dama,duk lokacin da kuka shirya nima I'm ready"
Lokaci d'aya farinciki ya wanzu a fuskarta,ta kalleshi dakyau tace"Allah yayi maka albarka Jawad,insha Allahu baza muyi ma za6on tumun dare ba"
Murmushi yasaki sannan yatashi yakoma kan gadonta ya kwanta yana qoqarin kunna plasma din dakin.
****
Kamar yanda p.a yasanar dashi, ranar da za'ai taron bude masallaci,hakan yasa ya shirya tsaf suka tafi shida Fu'ad da sauran guards dinsa,gaba daya mota uku suka dauka,waje na musanman aka bar masa acikin masallacin wanda Iya tsaruwa ya tsaru,malamin addini yanata wa'azi akan falala da dunbin ladan da'ake samu idan angina masallaci,Jawad yayi shiru yanajin wa'azin,cikin ransa yana tunanin yanzu duk wannan ladan da'ake magana akai Shima fa ubangiji yabashi ko? sai hakan yasake qarfafa masa gwiwa dangane da taimako,bayan yagama fad'ar falalar gina masallaci saiya gangaro wajan falalar sharar masallaci da ladan da'ake samu idan an tsaftace shi,daga qarshe ganin matasa dayawa a masallacin sai wa'azin nasa ya gangaro kan batun aure wanda yake magana akan matasa wanda Allah yabasu damar aure su daure suyi aure domin rage zinace-zinace adoron duniya,bawai lalle saika samu yanda kakeso sannan ne zakayi aure ba,daga nanfa jikin Oga Jawad yayi sanyi yaji kamar danshi ake wa'azin.(🤭)
Tunani yafara aransa yana tuna dalilan da yasa baiyi aure ba tun tuni,nafarko kasuwancin sa,na biyu baima san soyaiyar ba bare yaga wata wadda zata dauki hankalinsa,na uku be'iya soyaiya ba tayaya zaija hankalin yarinyar? Nahudu ba lalle yasamu irin yarinyar dayake so ba,yanason matarsa ta kasance marar dogon karatu wanda idonta bai bude dayawa ba,yanason mace mai gashi yanda zai kama ya dinga wasa dashi,yanason gashin turawa da larabawa,yana birgeshi sosai,amma Allah bai bashi damar riqewa yayi abinda yakeso dashi ba,saboda shiba manemin mata bane,sannan bayason matarsa tayi aikin gwamnati ra'ayinsa ne wannan kudin daya tara ya'ishesu rayuwa,yasan cewa su Daddy zasu nemo masa mata,kowacce irin yarinya suka kawo masa zai Iya rayuwa da'ita amma ya kasance tanada gashi dakuma sauran abubuwan more rayuwa najikin mace,yasan cewa bazasu Samo masa irin matar dayake so ba wato marar dogon karatu, yasan gogaggiyar 'yar Boko za'a samo masa,babu kuma yanda zaiyi tunda shine yabasu dama su za6a masa,saide yayi haquri ya yarda ya aure ta ahakan,saide da sharadin babu aiki,matar J.mekudi saide tabada umarni bawai wani daga sama yabata ba.
gaba daya sai jikinsa yagama sanyi bayan yasan cewa bafa lalle ne yasamu irin wannan yarinyar ba saide in qasar zai bari,ya lumshe idonsa yana tuna irin tsawon shekarun daya dauka yana faman shan maganin kwantar da sha'awa duk saboda wad'annan dalilan nasa, wazai aura? tanada abunda yakeso?
Baigama dawowa daga tunanin dayake ba yaji p.a dinsa yana fadin "muje Yalla6ai" cikin sauri yadawo hayyacinsa yaga har angama wa'azin,Fu'ad dake gefensa sai fara'ah yake yana fadin "Yaya yau kasha Addu'ah"
Kai tsaye wajan motarsa yanufa amma mutanan garin suka nuna suna so suje dashi gida yaci abinci kafin yawuce,ganin dukansu tsofaffi ne hakan yasa baiyi musu ba yabisu suka qarasa wani had'ad'd'en gida inda aka tanadar musu abinci kala kala,da naman kaji,da naman sa,saide Jawad baici komai ba saide yadauki gorar ruwa ta faro yasha d'an kadan,yayinda Fu'ad da sauran guards dinsa da p.a suka nutsu suka kwashi girki abun su.
Washegari da safe gaba d'ayansu su hud'un sunacin abinci a dining, Jawad yana sanye cikin qananun kaya nashan is'ka kamar kullum,Mummy datake kusada Jawad itace take bashi abincin da spoon din hannunta,yayinda shima Daddy yake sakawa Fu'ad abaki, abun gwanin sha'awa basai an fada makaba zakasan cewa akwai tsananin Qauna a tsakanin iyayen da yaran nasu.
Daddy yabude wata yar madedeciyar iPad yakamo pictures din 'yanmata tsala-tsala sunsha kyau,jikin nan an matse shi da dinkin zamani,ya kalli Jawad yace"yaran sanatoci ne,da yaran ministoci da 'ya'yan sarauta,akwai guda ukun farko acikin su yaran gamna ne kaduba kagani idan akwai wacce tama sai muje dasu Man Sulaiman da abokaina anemo ma aurenta"
Dam!!! gaban Jawad yafadi,gashi de shine da kansa yabasu za6i su za6o masa matar amma saida yaji gabansa yafadi.
Kafin Jawad yayi magana Mummy tace"haba Alhaji,duk da muna son abun nan aida an barshi yad'an huta tukunna,duka-duka yaushe ne yazo qasar?"
Bata jira amsar da Daddy zai bata ba tamaida kallonta wajan Jawad tace"ci abincinka yarona"
"shekara kusan Arba'in shine kike kira yaro? yanda kike masa kullum kina shagwa6a shi hakanne yasa yake daukar kansa yaro,tunda yazo qasar nan ban ganshi da manyan kaya ba,inda ya ajiye iyali yaga matarsa da qaton ciki kokuma yaga matarsa da Baby dole zai nutsu ya dinga saka manyan kaya yazama cikakken magidanci"
Cewar Daddy.
Jawad yajuyo ya kalli Daddy yanason ya kaucewa maganar yanmatan,sannan yasake juyawa ya kalli Fu'ad yace"shaddar wanne Campany ce takeda kyau?"
Fu'ad da dariya ta kamashi ya kawar dakai yayi murmushi sannan yace"zanyi magana ad'inkama Yaya"
Jawad ya sunkuyar da kansa qasa ransa duk ba dadi,sai yanzu ne yagane kuskuren sa nacewa su nema masa auren, daya sani yayi ta basu haquri har zuwa lokacin dazai samu wata.
Daddy yagane saboda maganar matan dayayi masa ne yasa yaketa hura hanci,kokadan babu damuwa aransa yasake tura masa wayar yace"gasunan duba"
Fuskarsa adaure yadauki wayar cikin sauri far-far yayi scrolling screen din,sannan ya ajiye kansa aqasa yace"basuyi ba"
Daddy ya kalleshi yace"hmm"
Sannan yaci gaba dacin abincinsa.
Mummy tasaki ajiyar zuciya tace"to Jawad mezai hana inyi magana da Uncle dinka Bature Yaya na,sai a nema maka auren Amal?"
duk ransa babu dadi haka ya sassauta muryar sa duk da baisan yarinyar ba, yace"shikkenan Mummy tunda za6inki ce na Amince"
Fu'ad dake zaune yasaki murmushi,yasan Amal sosai yana bibiyarta ashafinta na tik tok, cikin sauri yadauko photon ta yadora a status dinsa yayi kalamai wanda yake nuni da cewa itace yarinyar da yayansa zai aura.
Adede lokacin Yaya Mariya yayar Daddy tana zaune a gidanta tana zuba iko, wayarta a hannunta tana duba saqonni,ganin Fu'ad yayi status da photon mace hakan yaja hankalin ta hartaje tabude tagani,lokaci d'aya ranta ya6aci,idonta ya rufe da masifa, ta wullar da wayar tata can gefe,tafara girgiza qafarta.
Daddy yayi ajiyar zuciya sannan yace"Alhamdulillah,Allah ya tabbatar da Alkhairi"
Mummy tace"Amin ya Allah Alhaji,nasan shima Jawad zaiji dadin zama da'ita inde anyi auren,zai yaba da kyawawan dabi'un ta,lokaci daya zai sota"
Fuska babu walwala Jawad yace"no Mummy,zan aure ta ne saboda ke,Mummy niban ta6a soyaiya ba,ban'iyaba,abinda nasani kawai shine kasuwanci,babu yarinyar danake tunanin zanso ta"
Mummy tayi ajiyar zuciya ta kalli Jawad tana girgiza kai jikinta duk a sanyaye,taga alama rigima kawai yakeji.
P.a ne yashigo falon bakinsa dauke da sallama ya rissina awajan Jawad yace"yalla6ai,shugaban babban kamfanin taliya na qasar Masar Sheik shamiy,yaji labarin kashigo Africa yaturo maka da saqon gayyatar shan shayi,zan'iya duba jadawalin lokutan dakake free sai a afada masa ranar da zakaje?"
Ba tareda ya kalli P.a ba,cikin 6acin rai yace"Shan shayi ko maganar kasuwanci? P.a bakasan hutu nazo bane?"
Cikin fishi yamiqe yabar dining din yanufi hanyar zuwa dakinsa ransa fal qunci dama ga maganar auren nan da'aka masa.
baiyi nisa da tafiya ba,wayarsa tafara qara,cikin sauri p.a yasake cewa"yalla6ai ana..."
Kafin ya qarasa cewa ana kira,cikin jin haushi yajuyo yace"waye kuma? ko Sheik Shamiy dinne?"
P.a daya lura yau Yalla6ai akusa yake ya sassauta murya yace"daga qasar Niger ne"
Kai tsaye yace"kashe waya"
Daga nan yayi dakinsa bai sake futowa falon ba sai dare,kuma babu wanda ya nemeshi saboda sun San cewa akusa yake,da alama kadan yake jira yace yafasa auren, sukuma suna so yayi auren.
Da daddaren ma ransa babu dadi fuskar nan a murtuke haka yake zaune afalo yayi shiru duk abun duniya yataru yamasa yawa.
p.a yashigo falon yace"yalla6ai ana waya daga Niger,number d'azu ce aka sake kira"
Babu musu Jawad ya kar6a,sannan yad'auka bakinsa d'auke da sallama,daga can 6angaren Alhaji Auwal yace"Jawad nakiraka da safe zan baka Baby itace ta dameni saina kira mata kai batajin dadi ne sai maganar ka take"
Cikin sanyin jiki Jawad yace"Ya Salam nayi busy ne da safe, please Papa bata wayar"
Cikin sanyin jiki Alhaji Auwal yace"Jawad saide kayiwa Baby Addu'ah Allah yamata rasuwa yanzu-yanzun nan,ka fad'awa mahaifinka kace nakira wayarsa bata shiga ba"
Lokaci d'aya Jawad yaji kansa yayi masa wani iri dummm!, Baby tarasu? lokaci daya yafara fadin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,please Papa inaso inzo suturar ta qarfe nawa za'a yi?"
Alhaji Auwal yace"sai gobe dasafe insha Allah kamar qarfe takwas"
Jawad yakashe wayar yadafe kansa yana tuna irin alqawarin dayayi wa yarinyar baicika ba,gashi de baisan taba,bai ta6a ganin taba amma mutuwar ta tadakeshi.
Mummy ta kalleshi tace"waye yarasu?"
Jawad yad'ago kansa yace"jikar Alhaji Auwal ce,abokin Daddy na Niger"
Daddy yace"ayya, to ainima bazan zauna ba,saimu shirya muje goben"
Jawad yace"Daddy zaka Iya ne? jikinka yagama warware wa?"
Daddy yace"a a karka damu, na warke sosai Jawad"
Jawad yayi ajiyar zuciya yabawa p.a wayar sannan yace"ashirya mana tafiya zuwa qasar Niger gobe da sassafe"
P.a ya kar6i wayar sannan yajuya yafita.
****
Washegari sassafe ya shirya cikin shadda milk color harda babbar riga yayi bala'in yin kyau kamar ka saceshi ka gudu,yana sakkowa falo yaci karo da Hajiya Mariya yayar Daddy.
Mamaki ya kama Jawad me yakawo Mama gida da sassafen nan,itada sai an dad'e ma kafin a ganta agidan,saide in wani muhinmin abu ne yafaru,cikin sauri ya qarasa wajanta tun kafin yagaida ta tana ganinsa tace"ina uwar taka?"
Jawad yayi saurin yin qasa da idonsa ganin akusa take,tuni ya rissina qasa cikin nutsuwa yad'an motsa lips dinsa sannan yace"Hajiya Mama ina Kwana?"
Hajiya Mariya bata amsa gaisuwar tasaba cikin masifa tace"Uwar taka tana gani da idonta za'a baka wannan yarinyar?"
Tafad'i hakan tana nuna masa photon Amal dake screen d'in wayarta,saide kansa aqasa baima dago ba bare ya kalleta.
Cikin Masifa Hajiya Mariya tasake daga murya tace"yarinyar da batada tarbiya?,kullum tana cikin yin raye-raye a tik tok yara suna nunamin rawar datake tana nunawa duniya jiki shine za'a dauko a liqa maka?"
Shide Jawad yayi shiru baice komai ba,har lokacin kansa yana qasa baice da'ita uffan ba kasancewar yasan halin ta masifaffiya ce.
Adede lokacin Mummy tafuto daga daki itada Daddy wanda yagama shiryawa zasu wuce Niger,Hajiya Mariya ta kalli Mummy tasan sarai tanada nasaba da Amal amma sai tace"da ke kinsan yarinyar ne kokuma asama-sama kika santa da zaku bashi ita?"
Mummy ta sunkuyar da kanta,tarasa a'ina Yaya Mariya taji wannan maganar.
yayinda Hajiya Mariya ta kalli Daddy tace"ban yarda da wannan hadin ba,aje asake bincike akan yarinyar tukunna"
Tajuya ta kalli Jawad dahar yanzu kansa yake qasa ta tsatstsare shi da'ido tace"kokaine kaganota ahakan kaji kagani kana sonta harka kawo ta gida?"
Jawad yayi shiru kansa yana qasa saboda babu ladabi babba yana fada kayi magana,musanman ma ita datake gaba da mahaifin sa,shi baisan dalili ba,amma yarasa meyasa koda yaushe Hajiya Mariya take nunawa kamar tafi kowa sonsa,wani lokacin qiri-qiri zata dinga yin abu kamar tafi Mummy sonsa.
Kafin wani daga cikinsu yasake yin magana p.a yashigo yace"yalla6ai mungama shirya komai kai muke jira,sannan akwai baqin manoman dakace asanar dasu suzo yau zaka gansu sunyi magana zasu taso yanzu"
Sai alokacin Jawad yadago kansa yace"kafad'a musu nadage ranar dazan zauna dasu,saika basu wani lokacin daya dace"
Daddy yayi ajiyar zuciya ya zauna sannan ya kalli Jawad yace"tashi kuje Jawad,kayimin ta'aziyya awajan Alhaji Auwal d'in tunda Yaya tazo zan zauna zamuyi magana da'ita,nina haqura dazuwa"
Babu musu Jawad yamiqe,ya kalli Hajiya Mariya cikin ladabi yad'an motsa lips dinsa sannan yace"Kihuta lafiya Mama"
Daganan yabi p.a suka wuce.
Daddy ya kalli yayar tasa ya sassauta murya yace"yaya zauna muyi magana,abun duk bana zafi bane"
Cikin fishi Hajiya Mariya ta nemi waje ta zauna bayan tagama yiwa Hajiya Zaliha wani irin kallo.
*** *** ***
Yana futowa zuwa Compound guard's dinsa suka fara take masa baya har zuwa wajanda aka a dana motoci domin kaishi Airport,d'aya daga cikin guard yabude masa motar yashiga,Man Sulaiman yaja motar suka tafi,Jawad yayi shiru ya lumshe idonsa yana zaune abaya,kwata-kwata yakasa sakewa ganin wanda yadauko shi,kokadan bayason ganin mutumin yana aiki bare kuma ace shine wanda zaijashi amota,haka nan yake jin qimar mutumin aransa,saide labarin sa da Daddy yabasu na gudun iyalinsa kwata-kwata baima sa dadi ba.
Har suka je Airport shide Jawad baisaki jikinsa sosai ba,har saida jirginsu yatashi.
Bayan wani lokaci jirgin su ya sauka a Aeroport International Diori Hamani Niamey Niger Airport,kamar ansan da zuwansa nan da nan 'yan jarida sukai masa caaaa, sai hasken camera ne yake tashi ta ko'ina ana masa photo, yayinda guard's d'insa suke hana mutane tunkarar inda yake,bai saurari yan jaridar ba kasancewar jana'iza ce takawo shi idan yayi wasa kuma bazai samu ba.
Yanajin yanda wasu mutane suke tambayar sa ko zasu iyayin salfie? amma Jawad ko juyowa baiyi ba.
Motocin gidan Alhaji Auwal ne suka zo suka daukeshi zuwa gidan,yana zuwa kuwa babu dadewa akayiwa Baby jana'iza aka kaita gidanta na gaskiya,sannan suka dawo suna kar6ar gaisuwa, manyan mutane wanda sukasan Jawad d'in sai zuwa suke suna gaidashi,shi kuwa yaci wannan babbar riga ya hakimce kamar wani magidanci.
Gidan rasuwar yacika sosai da mutane kai kace shi kansa Alhaji Auwal d'in ne yarasu,ma'aikatan gidan sai futo da katan-katan d'in ruwan gorar DALLOL suke,ana rabawa mutane masu zuwa gaisuwa.
Farouq Abban Inaas shima yana zaune daga can gefe tare da wasu mutanan suna kar6ar gaisuwa,abakin nakusa dashi yaji suna qus-qus suna cewa wannan matashin nakusa da Alhaji Auwal wanda mutane suke zuwa suna gaidashi shine mamallakin kamfanin Mekudi Oil na qasar,shine Babban d'an Alhaji Mekudi abokin Alhaji Auwal.
Abban Inaas yakai dubansa inda su Jawad da Alhaji Auwal suke zaune,yaga yanda manyan mutane suke zuwa gabansa su tsugunna su bashi hannu su gaisa mamaki yasake kamashi,dama wannan matashin yaron shine shugaban kamfanin Mekudi oil? dama tun lokacin da Jawad d'in yazo gidan ya ganshi tareda wasu gabza gabzan muqarrabai dasuke take masa baya anan yasake tabbatar wa koma waye wannan yaron to tabbas wani babban mutumin ne.
Bashida damar zuwa rumfar dasu Jawad d'in suke zaune ta manyan mutane,aida ya matsa kusa ya ganshi sosai a zahiri,ko watarana a tarihi zaice shima yaga me kamfani Mekudi Oil, amma yanzu saide gani daga nesa.
Har dare Jawad yana tareda Alhaji Auwal,yaso sukoma Nigeria a ranar saboda kwata-kwata bayajin dad'in jikinsa tunda yashigo qasar,masifar fad'uwa gabansa yakeyi kamar ana doka masa wani abu a gefen zuciyarsa,hakan yasa yace zai tafi,to amma Alhaji Auwal ya hanashi tafiya,shikuma bazai iya musu dashi ba saboda shima kamar Daddynsa ne.
Washegari yana tashi da safe aka aiko masa da kayan sakawa wata suit ruwan toka mai mutuqar kyau,cikin sauri yake shiryawa yanaso yabar qasar saboda har yanzu bai daina jin wannan fad'uwar gaban irinta jiyaba,yayi Addu'ah yayi Addu'ah amma abu shiru yaqi yadena.
Duk da cikin sauri ya shirya,hakan bai hanashi yin wani irin kyau me masifar daukan hankali ba,iya ruwan tea kawai yasha yamiqe zasu wuce,Alhaji Auwal ya kalleshi dakyau sannan cikin bada umarni yace"Jawad kafin ka wuce ya kamata kashiga kaga kamfaninka na Mekudi Oil kaga abubuwan dasuke faruwa,nadad'e ban kaiwa kamfanin ziyara ba,amma tunda kashigo qasar yanzu,saika shiga kaga meyake wakana,inyaso saika dawo kuyi sallama da sister's dinka saiku wuce okay?"
Ya qarasa zancen yana nuna masa yaransa 'yanmata guda biyu wanda suka ta6a yin waya da Jawad din tun kafin yazo Nigeria.
Kansa aqasa cikin nutsuwa da kamewa irin tasa yace"to Papa"
Sannan yamiqe yafice,yana fita yaga motoci guda uku ajere suna jiran futowar sa da alamu Alhaji Auwal yariga yafad'a musu,tun kafin ya qarasa suka bud'e masa mota,sannan yashiga suka fice daga gidan.
suna tafiya ahanya yana kallon Agogon dake d'aure a farar fatar hannunsa wadda tacika da gargasa,yasaki d'an qaramin tsaki gaba d'aya ransa adagule yake saboda yaso yanda yatashi sassafen nan kawai yawuce Nigeria, yajuya gefensa ya kalli window yana ganin yanayin garin gwanin birgewa,duk yanda yake yawon zagaya kamfanin nikan nasu shi bai ta6a tunanin zuwa na Niger ba.
Qarfe bakwai da rabi daidai suka iso kamfanin,aka bude masa ya futo hannunsa guda daya zube cikin aljihun wandonsa yana tafiya yana qarewa kamfanin kallo, yayinda guard's d'in dasuka rakosu suke tafiya cikin sauri suna masa nuni da hanyar dazaibi.
Suna qarasawa ciki aka yi sauri aka kawo masa kujera yazauna yad'ora qafa d'aya kan d'aya,dayawa daga cikin ma'aikatan kamfanin duk basu qaraso ba,fuskarsa ad'aure babu walwala yakalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa sannan yasaki wata is'ka me zafi ya furzar,qarfe bakwai da minti arba'in tayi amma har yanzu de baya ganin ma'aikata suna cincirindon shigowa.
Kamar manager yasan tunanin dayake shima sai gashi yashigo alokacin,ai yana ganin fuskar Jawad lokaci daya jikinsa yad'auki rawa,ya qarasa wajansa yana gaidashi,Jawad ya kalleshi baice dashi komai ba kuma bai amsa gaisuwar tasaba sai agogon hannunsa daya kalla.
Daga nan ma'aikatan kamfanin suka fara shigowa d'aya bayan d'aya,ganin yanda manager yayi tsumu-tsumu agaban Jawad lokaci d'aya suka gane shine de mutumin dasuke jin labari yashigo Niger,shine J.mekudi,mamallakin kamfanin Mekudi Oil.
Duk ma'aikaci ko ma'aikaciyar data shigo haka zasuyi qasa da kansu sum-sum su wuce cikin kunya ganin oga kwata-kwata yakawo musu ziyarar bazata,kuma ya riskesu dayawa daga cikinsu duk sunyi latti.
Jawad ya kalli manager yace"bani bayanan kamfani zan duba"
Cikin sauri manager yakoma yashiga office d'insa yad'auko masa wasu file-file's da wata computer yakawo masa,sannan yasake tsayawa agefe kamar yanda guard's d'insa suka maqale a tsaye.
Kundin shigar da bayanan kamfani yafara dubawa a nutse,adede lokacin aka gabatar masa ruwan gorar DALLOL mai mutuqar sanyi jikin gorar har ra6a yake,tareda wasu lemuka aka ajiye agaban kujerar dayake zaune,saide Jawad kota kan ruwan baibi ba.
Duk wannan buduri da'ake Hajiya madam Inaas 'yarme gwanjo bata qaraso kamfanin ba.
Yadad'e yana ganin yanda ake shigarda bayanan daki-daki abun ya birgeshi,har wajan qarfe takwas dawasu mintuna yakai yana ganin bayanan sannan yad'ago kansa ya kalli manager anan yaga yanda ma'aikata dayawa suke had'a kai suna qus-qus,saide baisan me suke cewa ba ya d'auke kansa daga garesu.
a nasu 6angaren kuwa gulmar sa suke suna yaba irin tsantsar kyan dayake dashi,'yanmatan dasuke aiki a kamfanin sai qasa da murya suke suna fad'in "wallahi ya had'u sosai".
Jawad yayi ajiyar zuciya bayan yagama kallon manager sannan yad'an motsa lips dinsa yace"komai yayi kyau,yanda ake shigar da bayanan company daki-daki yayi kyau sosai,but waye yake shigar da bayanan? naga yayi qoqari sosai aikinsa yana kyau"
Cikin sauri Ilyasu manager yafara rawar baki yakasa magana,Inaas ce me wannan aikin,gashi har yanzu bata qaraso kamfani ba,daqyar ya'iya kallon Jawad yace"yalla6ai ba... bat bata qaraso ba"
Cikin tsananin mamaki Jawad ya kalli agogon hannunsa yaga qarfe tara saura ,sannan ya kalli manager,kafin yayi magana p.a d'insa dayake tsaye agefensa yabashi waya alamun ana kiransa,Jawad ya kar6i wayar yakara a kunnansa,daga d'ayan 6angaren shugaban kamfanin gidan radio da television ta qasa yafara roqon sa yace"Ranka ya dad'e daga nan ORTN ne,Office de Radio et Television Nationale,gidan radio da television na qasa,munji labarin ka shigo qasar ne idan babu damuwa muna so kabamu minti talatin zamuyi muyi fira dakai".
Kai tsaye Jawad yace"ok ganinan zuwa"
Yakashe wayar yamiqawa p.a,sannan yadawo da kallonsa ga manager yace"mace ce take shigar da bayanan?"
Manager yakasa magana sai kansa daya gyad'a kawai alamun hakane.
Kai tsaye ya kalli assistant manager dayake tsaye agefe yace"bani bayanan takardun ta"
Cikin sauri assistant manager yagabatar wa da Jawad photo copy na takardun Inaas,Jawad yaqarewa takardun kallo,takardun sunyi kyau sosai,saide iya secondary ne, cikin mamaki yadago kansa ya kalli manager yace"S.s.c.e? a kamfanina? meyasa zaku dinga d'aukar irin wad'annan sakarkarun aiki a kamfani babba kamar wannan?,qualification dinta bekai ba,sannan bata zuwa aiki akan lokaci"
Cikin rawar jiki manager yace"kayi haquri Yalla6ai yarinyar ce abun tausayi wallahi,sannan munga tanada sani ne sosai akan tattara bayanai,idan kaduba wasu daga cikin sauran companies zakaga ana iya samun irinsu,basuda dogon karatu amma sunada basira da qwarewa akan aiki"
Jawad ya kalli manager fuskarsa babu walwala yace"magana nake akan kamfanina,menene alaqata da sauran companies dan sun d'auki irinsu? ni d'an kasuwa ne, bazan lamunci wannan ba,afad'a mata na sallameta daga aiki takoma makaranta"(🙆🏻♀️)
(shikkenan tafaru ta qare,d'an aikin kamfanin da muka samu ma an koremu 😣😫😥)
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne.
300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.
Amnah El Yaqoub ✍️💝 *ME 'DEBE KEWA*💝
('yar me gwanjo)
Writing By Amnah El Yaqoub
Dedicated to Bilkisu's name
15&16
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne.
300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.
___
Yana fad' ar haka yamiqe,guad's d'insa suka mara masa baya,yayinda manager da manya-manyan ma'aikatan kamfanin suka masa rakiya zuwa wajan motocinsa,saida sukaga fitar sa sannan sukai shirin juyawa kowa yana ajiyar zuciya, daga nan baki yabud'e aka fara maida zance.
Motocin Jawad suna fita adede lokacin Inaas tazo,ma'aikatan da sukasan ankoreta sai qus-qus suke suna gulmar ta harda masu nunata da hannu, Ilyasu manager ya kalleta yace"Inaas saide kiyi haquri ki koma gida shugaban wannan kamfanin Jawad Mekudi yakawo mana ziyarar bazata,yaga takardun ki yace ya sallameki daga aiki kuma yace afad'a miki ki koma makaranta"
Inaas tazuba wa manager ido tana kallonsa takasa magana,duk tsananin surutun ta bata ta6a tunanin akwai ranar da zatazo afad'a mata magana ta kasa maida martani ba.(😂)
Ahankali tasaki ajiyar zuciya ta kalli manager tace"to nagode"
Daga haka bata sake cewa komai ba tajuya tabar kamfanin,tsabar taqaici aqafa tatako zuwa gida ranta baqiqqirin tana tafe tana tunani ta saqa wannan ta kunce wancen,idan a lami lafiya ne bazatayi wannan doguwar tafiyar aqafa ba,amma yau tashin hankali yahanata ganin nisan tafiyar.
Su Jawad kuwa suna barin kamfani kai tsaye wajan wani baturen qasar france suka qarasa suka tattauna dashi akan wasu abubuwa,sannan p.a dinsa yatuna masa maganar zuwa gidan television d'in da zasuyi fira dashi,hakan yasa yamiqe,yabawa Baturen hannu suka sake gaisawa sannan yayi masa sallama suka d'auki hanyar gidan television d'in.
sunyi nisa atafiya sosai motar da Jawad yake ciki ta tsaya adede layin gidansu Inaas,driver yayi-yayi ya kunna mota kwata-kwata mota taqi tashi,hakan yasa ya futo yaduba yaga ruwan ciki ne yaqare kuma babu ruwa acikin motar.
Sauran motocin guda biyu suka tsaya kowa ya futo zuwa wajan Jawad,ahankali shima yabud'e ya futo,baisan dalili ba adede lokacin kuma gabansa ya tsananta fad'uwa sosai,ya kalli yanayin unguwar yaji hankalinsa ya kwanta da wajan yanason yad'an sha is'ka kad'an,hakan yasa ya kalli sauran guard's d'in yace"kuyi gaba kawai babu damuwa,ku sanar dasu ina qarasowa,p.a katsaya tare dani"
'Daya daga cikin drivers d'in dasuke jan sauran motocin yace"ranka yadad'e ko zaka shigo nan saimu qarasa dakai duba da yanayin wajan nan akwai sahara dayawa gashi rana tafara futowa"
Jawad yayi murmushi yace"no ba damuwa,aiba wata matsala bace, ruwa ne kawai,zamu taho yanzun nan,kuje kawai"
Babu musu drivers sukaja suka tafi gidan tvn domin isar da saqon Jawad nacewa yana hanya.
Direban dayake Jan motar yabud'e booth d'in motar yad'auki wata gora yace"bari asamo ruwa acan, nasan baza'a rasaba"
Cikin sauri shima p.a yabi bayansa, Jawad yasaki ajiyar zuciya tareda kallon agogon hannunsa yaga sunada sauran lokaci kafin afara shirin,yafara kallon yanayin wajan babu gidaje dayawa sosai amma akwai sahara awajan sosai.
Daga can nesa ya hangota tana tafiya aqasa cikeda wahala dakuma tsantsar gajiya,tun barowarta daga kamfanin bayan taji baqin labari sai yanzu Allah yayi taqaraso gida,baqar laffaya ce ajikinta wadda tasake qawata farar fatarta,tundaga nesa yake qare mata kallo yana kallon d'an qaramin bakinta yanda yake motsi da'alama magana take ita kad'ai duba da yanda take maganar tana watsa hannayenta biyu alamun 6acin rai,tun kafin taqaraso wajansa yashagala a kallon kyakykywar fuskarta,haka yaci gaba da kallonta kamar zai cinye ta,da alama baima san ya lula duniyar kallon nata ba.
Harta qaraso kusa dashi bata daina surutu ba,tagefensa tazo zata wuce tana masifa kota kansa batabiba bare tasan wanda yake tsaye kusa da qofar gidan nasu, haka taci gaba sababi tana fadin"kora daga kamfani aiba kora daga duniya zuwa lahira bace"
Ganin zata wuce shi hakan yasa yad'an motsa lips d'insa,cikin sauri yace"am...kinga,naceba..."
Inaas tajuyo ta kalleshi cikeda masifa dakuma taqaicin ankoreta daga aiki tace"kace me?"
Jawad yadan motsa lips d'insa kamar baison magana saikuma yace"please inason ruwa ne"
Inaas ta kalli idonsa tace"ruwa? anan wajan? to babu"
Mamaki yakama Jawad,yad'an saci kallon dan mitsitsin bakinta yace"kinga driver na yacemin za'a iya samu,but har yanzu kuma ba sudawo ba,kuma babu ruwan gora a motar"
Inaas tasaki ajiyar zuciya ta nuna masa wata hanya tace"idan kabi nan hanyar,saika miqe kasha kwana zaka iya samu anan"
Jawad ya kalleta da mamaki 'yar qarama da'ita sai zaro magana take,yace"okay kuma da kinsani d'in but why zakiqi sanar dani tunda farko?"
Ganin