Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 10
mace ta haɗa shi , ita da take da aure ma tafi ta komai to halin namiji ba tabbas duk irin son da yake mata zai iya sakawa idonsa toka yace labari ya canza. da taga suna mutunci da taufiq sai hankalinta ya dan kwanta ko kaɗan bata so wato kishiya. Yau ranar Litinin yusrah ta tafi makaranta juhud wajen aiki taufiq ma ya bi juraij asibiti daga ita sai mommy sai masu aiki rasa yadda za a yi tai wa mommy karya ta barta ta fita, dan a kwana kusa take son barin kasar niger ta tafi makka. tana cikin wannan tunani saliha me aikin su ta ajiye mata lemo tace '' gashi nan.., ɗauka tayi ta buɗe ta fara sha ba tare da tace komai ba kwata kwata tunaninta baya kan su yana wani guri can daban hakan da saliha ta gani ya saka ta zauna kusa da ita tace '' yar nan tunanin me kike haka ..?, da sauri ta ɗago saita kan'ta tayi tace '' bakomai bana son magana ne baba saliha kaina ke ciwo.., dafa kan'ta tayi tace '' ayya sannu Allah ya baki lafiya kin faɗawa hajiya..?, yumna tayi kallar tausayi tace '' a'a ban fada mata ba , bana so hankalinta ya tashi .., Baba saliha tace ''gaskiya kinyi kyan kai tunda na lura kamar kwana biyu hajiya na cikin damuwa bara na kawo miki magani ki sha za kiji sauki..,, da sauri ta kalle ta , tace '' a'a barshi nagode nan da anjima insha'Allahu zai saki.., dariya tayi tace '' bakya son Shan magani Allah ya shirye ki.., shiru tayi mata tabar gurin da sauri ta ajiye lemom hannunta ta shiga dakin mommy samun ta , tayi tana danna waya zama tayi a ƙasa tace '' mommy barka da wannan lokaci.., mommy tace '' barka dai yumna ya jikin naki..., ƙasa tayi da kai tace '' na samu sauki.., to masha Allah wasa ta fara da mayafin'ta tace '' mommy Dan Allah ina so naje gidan su wannan kawar tawa yau ba kowa a gidan bana so na fara wani tunanin da zai ƙara kaini da kwanciya asibiti.., murmushi mommy tayi tace '' to ba damuwa amma karki dade kinji..?, tashi tayi tana murna tace '' to.., da saurinta ta fita daki kawai ta shiga ta dauko wayar ta da takalminta sannan ta fita tana fita ta danyi nisa sannan ta kirawo number wannan mutumin sai dai har ta katsai be ɗauka ba ci gaba tayi da tafiya tana kiransa sai da ta zo gab gurin sannan ya ɗaga kiran ta lokacin tai mai kira kusan goma sha , da sauri ta kara a kunne tace '' yallaɓai gani nan ina bakin gate din ku na farko yau nazo a yimin komai da komai.., Mutumin yace '' to masha Allah kin kuwa yi sa'a wannan satin zan mu kai wasu kinga sai a saka har dake a ciki tunda kin dade da yin booking.., wani dadi ne ya kamata tace '' kai amma naji dad'i Nagode Allah ya ƙara arziki..., ba damuwa ki shigo muyi maza muyi abin da za muyi lokaci yana kurewa dan gani nake na za'a ƙara kwana biyar ba za ku tafi... ba ƙaramin dad'i yumna taji ba da wannan zance jin kanta tayi a sama shiga gate din tayi tana rarraba ido can ta gani office din nasa, da sauri ta ƙarasa knocking tayi sai da ya dan jima sannan ya buɗe mata samin wata mace tayi daga, ganin ta yar duniya ce amma ba zata wuce sa'ar ta ba idan ma ta girmeta kaɗan ne sallama tayi ta juyo ta ƙarewa yumna kallo sannan ta amsa cikin fara'a. yumna ma ganin bata ja mata aji ba sai ta saki jikin ta tace '' ina wunin ku ina gajiya.., amsawa sukai da lafiya qalau wannan matar tace '' sunana bintu mukhtar maradi.., murmushi yumna tayi tace '' ni kuma yumna nura Agadez.., kai bintu ta gyaɗa tace '' kin sha hanya.., murmushi kawai yumna tayi ta mai da hankalin'ta kan mutumin nan tace '' nice wacce mukai waya yanzu.., dariya yayi yace '' na gane ki yanzu za ayi komai.., ba karamin dadi taji ba ai kuwa ba ɓata lokaci yayi mata komai bayan ya gama nasa ya turata office office ta cike takardu tare da saka hannu visa ma anan akai mata abin ka na kudi komai a ranar aka gama yi mata duk wani chuku chuku suka bata set number ta ashe itama wannan tafiya za tayi tare da ita akai musu komai ita da yumna sukai chanzan number sannan sukai sallama yumna ta kamo hannyar gida tun karfe biyu ta fita bata dawo ba , sai biyar tana shiga mommy ta fara yi mata faɗa tace '' haba yumna haka mukai dake wallahi ban ji dad'i ba , yanzun nan malam ya fita daga gidan nan duk da be nuna min wani abu a fuskar sa ba amma nasan ba zai ji dadi ba , tas an kwaso kayan ki, wannan shegiyar matar ta cuce mu wallahi yawo take tana cewa cikin shege kika yi labari duk ya baza gari.., zaman yan bori tayi bawai dan abin ya dame ta ba a'a sai dan kawai sun kyale ta, ta yi tafiyar ta. kuka ta rushe dashi mommy komawa tayi tana lallashin ta tare da bata baki amma ƙememe taki yin shiru ta ci gaba da kukan ta zuciyar'ta fes idan bata nuna ta damuwa ba, ba zata iya zama a kusa da mutane ba zata ƙeɓe kan'ta zuwa na ɗan wani lokaci tasan ba zasu barta ba , ta sarara dan haka wage baki tayi tana ta kuka har da shashsheka rarrashin duniya mommy tayi mata taƙi yin shiru. tamkar zugata tayi ma, sai da tayi me isarta sannan tayi shiru tace '' mommy yanzu wanne kallo mutane za su yi min wallahi mommy bazan iya komawa Agadez ba , mommy Dan Allah ku barni nayi nisa da ku, zuciya ta ko zata samu sukuni bazan iya cire kaina daga cikin wannan zargi ba har abada mutane da abin za su dinga kallo na ranar da aka daura min aure ranar aka sake ni, sauka ƙasa tayi ta haɗa hannuwanta guri ɗaya tace '' mommy Dan girman Allah ku barni nayi nisa da kowa ko hankali na zai kwana dan da ɗan wani lokaci nasan zan dawo dai-dai Wallahi bana son zama a kusa da wanda na sani dan girman Allah ku barni na tafi makka ko na rabin shekara ne sai na dawo lokacin nasan mutane sun riga da sun manta da abin da ya faru nima na manta da shi.., da sauri mommy ta kalle ta cikin mamakin abin da yumna ta faɗi tace.. Ku hanzarta yin payment sauran pages biyu na gama free book 1 Book 2 500 Ne idan ya zama document ya koma 1000 Karku ce ban faɗa muku ba Domin biya 8141785374 Amina alhasan Muhammad opay Ku turo da shedar biya ta wannan number 08141785374 Receipt evidence kawai nake so idan kika turo na saka ki a group bana son wannan tambayar nawa ne bayan kin karanta na baya kinga abin da na saka YAN ZAMAN MAKKAH OUMYASMEEN BOOK 1 Copy is not allowed 🚫 Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku shiga wannan link din sannan ku danna min subscribe Dan Allah. https://youtu.be/cDE5bjYY2HY ___________________ https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c Episode ¹⁵ YUMNA kinsan kuwa me kike faɗa..? anya kuwa lafiyar ki qalau..? karma ki sake malam yaji wannan maganar, dan wannan abin ya faru sai tunanin ki ya gushe kim bawa mutane ma damar su faɗi duk abin da suka ga dama.., kuka ta ƙara rushewa dashi tace '' mommy ke uwa ce nasan zaki san irin radadin da nake ji cikin zuciya ta , mommy bansan ina zan saka kaina ba. kaɗai ci nake so wallahi a yanzu bana kaunar kowa ya raɓe ni mommy ku tausaya min ku fahimce ni nasan abin da kuke gudu, anan ma banyi ba sai a can da bani da kowa garin da ba nawa ba kowa abin da yake ransa shi yake aikatawa.., zama mommy tayi jikin'ta yayi sanyi tausasa muryarta tayi tace '' yumna ki fahimci abin da nake so ki fahimta, zaman ki anan shine rufin asirin ki wallahi bar ganin wa'yanda suke can suna baki sha'awa baki san rayuwar da suke ciki ba kiyi fatan Allah ya azurta ki, ta hanya me kyau ki tsaya kiyi karatu Allah ya fito miki da miji kiyi aure wallahi yumna duk inuwar da kike gani kina hangen ta , to ƙuna ce ba ko wacce inuwa bace inuwa wata zafin ta , yafi na rana akwai dana sani a cikin'ta mara amfani ba zaki gane wannan zancen nawa ba sai nan gaba , wani ma idan kin dawo kallon da zai miki daban har sai kin gwammace kiɗa, da karatu.., share hawayen ta tace '' mommy a tunani na zaki fahimci inda magana ta , ta dosa mommy komai yayi min zafi.., shiru mommy tayi domin abin yumna ya fara bata tsoro ganin haka yumna tashi tayi, ta tafi dakin ta turo kofar tayi ta murza key, zama tayi a kan gado ta zuba ta gumi tabbas idan ba tai musu wuta wuta ba to wallahi ba za su yarda da wannan tafiyar tata ba ɗaukan waya tayi, ta nemi number Na'ima har ta katsai ba'a dauka ba dogon tsaki taja ta ajiye wayar a fili tace '' ke daman tsiyar ki, kenan ai ta kiranki a banza.., kwanciya tayi tana , ta wassafe wassafe a zuciyar ta , limshe idanuwan'ta, tayi tasan yanzu ba za su taɓa fuskanta ta ba , sai lokacin da nasara ta zo mata yanzu kowa kallon bai bai zai mata idan kuma nasara tazo sai a dinga dama nice, sun manta a baya abin da suka ce tabbas me hakuri yana tare da nasara zata shanye komai zata dauki komai tasan wannan duk abin taki ake zuba mata. bacci ne ya dauke ta kiran sallar magariba ne ya tashe ta, tashi tayi ta dauro alwala ta , tayar da sallama bayan ta idar ta ƙara jaraba number Na'ima still bata dauka ba message ta rubuta mata tace '' Assalamu alaiki Na'ima ban yi fushi ba , na kira ki amma ba kiyi picking call din ba na bugo ne na sanar dake nima ina nan tawowa, ki turo min sunan unguwar da kike zan kawo miki ziyara sannan ina godiya da yi min hanyar tafiya makka da kika yi Allah ya bar zuminci.., turawa tayi ta ajiye wayar ji tayi ana knocking din kofar dakin ta banza tayi domin hausawa sunce da zafi zafi ake bugar ƙarfe.., ko da yusrah ta gama bugunta bata buɗe ba sai ta juya ta tafi gurin mommy tace '' mommy taki budewa.., tana faɗar haka ta zauna ajiye chokalin hannunta tayi tace '' to bara naje naga ko lafiya.., Juhud da take operating system din'ta ta ɗago tace '' mommy sai kace wata yarinyar karama ki kyale ta idan ta gaji zata fito ne ita fa bari ba shegiya bace da uban'ta amma zaki damu kanki.., shiru mommy tayi ta bar gurin ƙara zuwa kofar dakin yumna tayi, ta fara bugawa still tai mata shiri hakura tayi ta barta. bayan sallar isha ta kwanta tana addu'ar Allah ya fahimtar da yumna gaskiya. Wasa wasa ƙaramar magana tana ƙoƙarin zama babba yumna har washegari bata fito ba Alhaji ma yayi mata magana taƙi buɗa kofar gashi aranar taufiq zai koma Ingila acan yake karatun sa tafiya su kayi rakiyar sa zuciyoyin su duk ba dad'i. a bangaren yumna kuwa itama ba ƙaramin buguwa tayi ba kwana ɗaya da rabi da tayi ba abinci. bayan tafiyar su fitowa tayi a wahale ta dade a kwance a parlour yawa wata matacciya haka suka shigo suka ganta da sauri mommy ta ɗagata numfashin'ta sai kaiwa yake yana komowa cikin sauri tace '' juraij zo ka duba min yarinyar nan sakin jikin ta tayi hakan da tayi ba ƙaramin daga hankalin su yayi ba , ban da juhud da juraij ko a jikin su mommy taɓa kirjinta tayi numfashin ta sai kaiwa yake yana komowa zama Alhaji yayi yace '' to ku kuyar da mana ku bita da addu'a, Allah ya tsare ya kare ba wayon mu ba ba dabarar mu ba Ubangiji shi yake tsarawa yake kuma ikon sa.., jikin mommy yayi sanyi tace '' Alhaji mu bar wannan maganar za muyi ta , juraij wai ba magana nake maka ba ..? ka mai dani yar iska yawa da dutsai nake magana.., Mommy yarinyar nan ku barta duniya ce ɗaga hankalin da taga kuna yi shi ya saka take wani abin tana nan ma anyi mata wannan sharrin balle ta tsallaka wata ƙasar. cewar Juraij ran mommy ne ya ɓaci da jin wannan maganar juraij dan haka tayi shiru bata ce mai komai ba. runguma ta , tayi, tana yi mata addu'a ko Allah zai saka zata dawo dai-dai. ranar yadda mommy yaga rana haka ta ga dare washegari malam ya zo tun da mommy take mai bayani yayi ƙasa da kan'sa Alhaji na gurin shi daman Juraij yana gurin aiki . Mommy ta ƙara da cewa kawai mu barta sai a tayata da addu'a dan yau ne ka haife shi baka haifi halinsa ba zan yi magana ma da hajiyar mu itama nasan ba zata ki ba , kuma da alama duniyar ce tai mata zafi take ƙoƙarin barin gurin da aka santa duk ranta hankalin'ta ya dawo jikin'ta zata dawo gida zata waiwayo mu, idan muka matsa abin da zai faru yafi na yanzu dan zata iya illata kan'ta idan haka ta faru wa za'a zaga mu ne a ciki.., Alhaji ma yace '' nasan da ciwo dukkan mu ba haka muka so ba amma tun da , tace ita ga abin da ta za barwa kanta shikkenan ga hanya nan Allah ya bata sa'a iya gata muna yi mata ko da ace ba zata zauna a can agadez ba to ga nan, nan ta zauna ta ci gaba da karatunta har Allah ya fito mata da miji tayi auren ta amma ya kanne idanuwan'ta ta toshe kunnuwan'ta, bata tunanin wannan ɓacin rai da ta saka mu zai iya zame mata matsala a rayuwar ta sufa iyaye ba abin wasa bane , ba lallai bane wata ran ta budi ido ta gan mu, a lokacin kuma sai tai ta cizon yatsa tana dama nayi kaza , dan haka kawai kayi hakuri wannan ita ce jarabawar ka , dan kana malami ba wai ana nufin cewa ba za'a jarabe ka ba a gwada imanin ka wannan abin nasan ka sani ƙara tuna maka nake malam..., ajiyar zuciya ya sauke ya ɗago idanuwan'sa yace '' taje na barta.., hamdala su kayi duk da sun san bawai dan yana so ba kawai ba yadda ya iya ne hamdala yumna tayi a ranta duniya zata koma mata sabuwa bayan sallar la'asar sallama yayi musu ya tafi tare da cewa kawai baya bukatar ta ƙara zuwa Agadez ya yafe daga nan tayi tafiyar ta , ko a jikin'ta haka tace '' to malam Allah ya kiyaye hanya.., be ce mata komai ba ya fice daga dakin ranar haka ta wuni cikin jin dad'i farin ciki ba'a magana duniya tayi mata dadi sai shirye shirye take ba ruwanta da haɗa ran da su juhud suke yi mata juraij kuwa yafi kowa yi mata kallon banza abin da tayi ba ƙaramin ɓata mai rai tayi ba murmushi take yi ta wuce ta bashi guri Washe garin da za su tashi tana tsaye a harabar gidan tana shawagi da yake garin yayi limshi alamar ko wanne lokaci ruwa zai iya tsugewa a guje motar sa ta shigo ko dai-dai ta parking din'sa be yi ba ya fito cikin sauri kusan dariya ce ta kusan kubbucewa yumna ganin yana sauri kamar zai tashi sama bin bayan sa tayi da kallo ta taɓe baki tace '' a haka zaka ƙare mijin tace duk ka wani firgice ɗan kadangaren da na saka mata a tsakar daki shi ne take zunduma wannan ihun wallahi kaɗan kuka gani tun da ni zaku tsana akan nace zan je na nemo arziki kamar kowa.., be dade ba ya fito yana kwalawa masu wanki da guga kira cikin badda kama ta karaso kamar bata san me ya faru ba tace '' yaya lafiya naga hankalin ka a tashe..? ni fa wallahi ban iya zaman gaba, ba.., tamkar ya ɗora mata ashar sai kuma su yaga rashin dacewar haka tunda wanda ya kula ka , ai daraja da dashi sannan kuma tabbas ba kyau zaman gaba yace '' wallahi kadangare ahlam ta gani a kusa da ita , ta kirani ni, tace kamar ta ga wulgawar mutum to sai dai kallo take bata gama tantance mene bane sai taga kadangare yana yawo..., zaro manyan idanuwan'ta tayi ta ɗora hannu aka tace '' innanallahi wainna ilaihir raji'un amma dai ba abin da yayi mata..?, banza yayi mata ganin masu yi musu wanki da guga sun ƙaraso yace "dan Allah mati Ka iya fitar da kadangaren..?," kallon kallo suka shiga tsakanin mati da Haruna dakyar mati ya iya cewa wallahi oga ko son ganin shi, bana son yi ai wannan muguwar halitta ce.. innanallahi wainna ilaihir raji'un amma dai mati wallahi kun bada maza kuna maza kuna tsoran kadangare.. ta faɗa tana kallon juraij domin ta yi haka ne da biyu aikuwa ya gane sarai ita daman ba'a zaman mutunci da ita sai anyi na tsiya juyowa yayi yace '' dan ubanki shige muje ki ɗauke shi.., Zaro manyan idanuwan'ta tayi ta nuna kirjinta tace '' na shiga uku ni, ku, kuna maza baku ɗauke ba sai ni gaskiya ba zan iya ba.., Haɗe rai yayi yace '' shige mu tafi ko na kwarfe ki.., ƙara kallon juraij tayi a karo na biyu tace '' sai kace wata ruwa zaka ce zaka kwarfe ni.., kallon su mati yayi yace '' ku koma bakin aikin ku.., To suka ce masa suka juya suka tafi yumna tana cikin tunani , bata ankara ba taji ana janta tamkar kayan wanki. Ihu ta shiga zab gawa amma ko a jikin sa sai da ya dangana ta da parlour sa fisge hannun ta tayi tace '' wallahi abin da kake baya dacewa kai , ka kasa sai kace ni nayi.., Mari zai zabga mata ƙadan gare yayo kan'su da gudu suka , fita har da ahlam yumna tsayawa tayi tana dariya har da riƙe ciki ganin kamar ba namiji ba ya biyo su a guje nuna shi take tana zabga uwar dariya har da riƙe ciki, biyota yayi ta shiga parlour mommy da gudu. Bayan mommy ta shiga ta ɓoye tana danne dariyar ta mommy tace '' juraij lafiya me ya faru.., leko da kan'ta tayi tace '' mommy gudun kadangare yake.., sai ta ƙara fashewa da dariya har da buga cinya tana cewa namiji da gudun kadangare hhhhh wallahi mommy wannan abu ya ban dariya tare muka dinga gudu dashi yana ƙoƙarin rikoni wai kar mu tafi mu barsa. a fusace Juraij ya zagaya bayan mommy zai fisgota ta dawo gabanta tana cewa wayyo Allah kinga akan na fadi gaskiya shi ne zai dake ni.. Haba juraij sai kace wani yaro ka dinga beye mata Mommy ta faɗa tana danne dariyar ta , duk jarumtar juraij baya son ganin kadangare barin irin babban nan wanda har canza kala yake sabo da girma. juyawa yayi bece komai ba . ajiyar zuciya ta sauke ta zauna akan carpet tana sauke numfashi tuno ahlam tayi da ƙaton ciki tana cewa baby karka gudu ka barni dariya ta ƙara shekewa da ita tace '' su baby manya.., kallon ta mommy tayi tace '' lafiya me ya faru kike magana ke kaɗai..?, ba komai mommy dauke kai tayi tace '' dazu naje gurin mutumin nan da kika bani number sa , nayi bincike na tabbatar da gaskiya.., da sauri ta ɗago cikin mamaki tace '' mommy yaushe kika fita har wajen kenan kinje..?, Eh naje yumna kuma yayi min bayani gaban tane ya faɗi karfa ya faɗa mata gaskiyar duk abin da ya faru da yadda tsarin su yake tace '' mommy me yace miki wanne bayani yayi miki.., gyara zama mommy tayi tace '' yayi min bayani wanda ya gamshe ni saboda yace duk lokacin da mutum ya so dawowa yana iya dawowa sannan a guri me tsabta suke kai mutum wanda addinin sa ko imanin sa ba zai taɓu ba sai dai in mutum ne ya kaucewa dokar da suka shinfida mai amma su aiki suke yi da addini abin yayi min dad'i wallahi har ayoyi da hadisai yake karanto min mutumin masani ne kuma babban mutum wanda yasan kan'sa duk ya nuna min shedar kasar nan tasan da zaman su akwai sa hannun hukuma da dama ya nuna min.., ajiyar zuciya ta sauke tace '' to Allah dai ya dafa mana.., amin ya Allah mommy tace , Bayan sallar isha ta shiga daki ta kwanta bacci me cike da jin dad'i har hango kan'ta take a makka. Washegari da asubar fari ta shirya kayanta ma tas ta haɗa su ta daure su a zanin atamfa wayar ta kuwa soke ta tayi ta saka a kugu mommy ce ta shigo turus tayi ganin ikon Allah lamarin na yumna tamkar wacce aka jefe anya kuwa wannan abin da take yi lafiya qalau take mutum yana cikin gatan sa yace sai yabar cikin gatan sa ya koma wata uwa duniya ta sani sarai ba yadda suka iya da ita shi ya saka suka barta kuma malam ma fushi yake da ita amma ko a jikin ta duk da be buɗa baki ya furta ba fuskarsa ta nuna abin da yake zuciyar sa ajiyar zuciya ta sauke tace '' yumna badai da safe zaku tashi ba..?, cikin farin ciki tace '' a'a ba da safe za mu tashi ba nice dai kawai na shirya domin kinsan jirgi baya jira sai dai a jira shi.., hmmm Allah ya kyauta ta fadi haka zuciyar ta na mata wani irin suya Hajiyar su ma faɗa tayi tace a kyale ta duniya tafi bagaruwa iya jima tas zata koya mata hankali idan dai son abin duniya mutum zai yi to ba shakka zai girbi abin da ya shuka kuma zai halaka tana cikin wannan tunanin ne yumna tace '' mommy wallahi saboda murna bazan iya cin abinci ba Allah ya sani ba ƙaramin farin ciki nake ciki ba ‘‘ O,, Mamman yana nan yana figar talaucin sa ba damuwa idan na dawo zan bashi dan na jari..., da sauri mommy ta kalle ta sai kuma tayi shiru domin bata da bakin magana juyawa tayi ta fita zama tayi a parlour zuciyar ta ba dad'i da ace juraij ya aure ta ba yadda za tayi dole ta zauna, ga maganar abokin sa da yayi mata ma lamarin babu shi domin ya koma gida hutu be kuma ƙara yi mata magana ba , Allah dai ya tsare rayuwar ta mommy mommy mommy da sauri ta ɗago tace '' juhud har kin shirya yau da wuri haka..?, zama juhud tayi tace '' mommy tunanin me kike yi haka..?, ba komai juhud hmmm wallahi nasan ba zai wuce na yarinyar nan ba haka kurum kun dauki son duniya kun ɗora mata kun kasa hanta abin da tayi niya tun da tace sai tayi sai ku zuba mata ido gata ga hanya nan karta tsaya a makka ta , tafi bangon duniya wannan matsalar ita , ta shafa ni wallahi ko san ganinta ba nayi haka kurum ta jefe ki a cikin tunani kina ga ranar da malam ya bar gidan nan idon sa yayi jajir ko wannan hakkin da ta kwasa wallahi Allah ba zai barta ba da sauri ta ɗaga mata hannu tace '' juhud ya ishe ki, tafi bana son kara jin komai daga, gare ki.., tashi tayi jikin ta a sanyaye tace '' mommy Allah ya baki hakuri amma wallahi yarinyar nan.., Cikin ƙara ji ta tari numfashin ta, tace '' nace miki bana son jin komai daga, gare ki, ki tafi inda zaki Allah ya kiyaye hanya.., juyawa tayi tana cewa amin.. dafa kan'ta mommy tayi ta lula duniyar tunani har lokaci yaja bata sani ba a guje yumna ta fito tana cewa mommy mommy mommy. da sauri ta ɗago tace '' yumna me ya faru..?, cikin murna tace '' yanzun nan aka bugo min waya, wai na zo za'a gama haɗawa mu ayi duk wani bincike da ake yi sannan sai

Chapter 9 of 10