wallahi haka kurum sai mu dinga zama bama wani bawa talauci tsoro ko zai kama gaban sa ki duba ga ki gani irin gidajen alfarmar da nake gani a waya idan baka tashi ka nema ba taya zaka same su..,
dan shiru lantana tayi sannan tace '' amma yumna bakya ganin rabon bawa baya taɓa tsaire masa idan abu rabon ka ne rabon ka ne wallahi zai zo ya same ka har idan kake. rabon bawa shike binsa fiye da aljalinsa..,
tashi yumna tayi ta rangada wata uwar buɗa tare da gyara zaman mayafinta tace '' sadakallahul azeem ina me karatu na gaba..? ashe bansan kin iya wa'azi haka ba kika bar cikin gidan ku da kungurmayen yan daba baki musu ba sun shiryu..? kinga sai anjima sai na zo yi miki sallama..,
bata jira cewar ta ba ta fita ranta a ɓace ganin takalmin da ta saka zai hanata sauri sai ta cire ta riƙe a hannu.
zafin ranar da ake ta sami guri ta zauna tana sauke ajiyar zuciya kamar ance ta dago kanta katuwar bishiyar goba ta gani washe baki tayi ɗamara taci da mayafinta ta fara ƙoƙarin hawa ji tayi ance billahilazi kina hawa sai na wullo dake kin faɗo ƙasa in banda iskanci irin na dan yau me zaki yi da abin da ba'a baki ba wato sata kika zo yi kenan..?,
chak ta tsaya ta sauko kare wa tsohon kallo tayi ta jinjina kanta tace '' baba kaci darajar tsofanka..,
a'a dawo dan girman Allah kar naci darajar tsofana bake bace yar gidam malam nura me sittin ba ai daman ace kece wacce kika fita zakka a cikin ya'yan sa tur da halinki albasa batai halin ruwa ba mahaifinki mutumin kirki
takaici ne ya kama yumna zuciyar ta tamkar ta faso kirjinta amma ba komai akan jikarsa zata rama shi dai yaci darajar tsofanka sa.
zata raga mai daukan takalmin ta tayi ta saka ta fara tafiya ko waiwayen sa batai ba gaban tane ya waɗi ganin malam a kofar gida yana tsaye abakin kofar shiga gidan nasu ga Mamman yana tsugunne a gefe yayi kasa da kansa.
wara hannuwanta tai yi ta buga cinyar ta, tace '' shikkenan wallahi maƙiya sunyi aiki ni nasan za'a rina an saci dan mahaukaciya ni da nace ya fadawa tsofaffi shine ya faɗawa malam, amma dai Allah ya kwashe wa Mamman albarka,bara naje naji da wannan matsalar da ta tun karo ni..,
tamkar wata mumina haka tai kasa da kanta ta ƙarasa tace '' malam zan wuce..,
ran malam aɓace yace '' daman ke nake jira jeki gida ki zauna yanzu zan shigo..,
dafe kirji tayi tamkar bata san me ya faru ba tace '' na shiga uku malam me ya faru kardai ce maka akai nayi wani abu wallahi malam ba hadu da kowa a hanya ba nan gidan lantana kawata naje..,
Kai malam ya girgiza tabbas shi ya yarda da cewa yumna zata iya kashe aure ko daga acting dinta tamkar ba ita ta aikata abin da aka faɗa mai ba wanda be san halin ta ba ya shiga uku dan haka yace '' wani abu nace miki kika fara rantsai rantsai ba ce miki nai ba zo ki shiga cikin gida..,
wani yawu ta hadiya tace '' eh haka ka ce min..,
hanya ya nuna mata ba tare da yace mata komai ba shiga tayi cikin gida a kan turmi ta zauna tana kallon kowa daddai kiris take jira ta fashe yaran gidan kuwa tuni suka kama kansu saboda yumna mala'ikan yara ta dawo..,
shamsiyya ce ta fito ta kalle ta tace '' yaya yumna dan Allah zo ki koya min karatu..,
wata uwar harara ta banga maka domin ita kaf karin jiya bata dauki komai ba domin suna baya suna surutu ana bata labarin wani littafi da yar ajin su ta turo,
ganin tai shiru ƙara ma rairaice murya tayi tace '' dan Allah aunty yumna ki biya min yau za a karɓi hadda..,
dan kwalin da ta chokala ya fadi kasa durkusawa tayi ta dauko shi wani irin bugawa kirjinta ke yi tace '' ke karki takura min bazan koya ba ana dole ne..,
barim gurin shamsiyya tayi ba tare da tace komai ba , shamsiyya na barin gurin ta tashi ta shiga dakin su zarya ta fara tana cije lips din'ta tasan dole malam ya korasu makaranta gashi bata son ta kunyata a idon jama'ar ajin su dole fa ta nemowa kanta mafita tun kafin lokaci ya kure mata jar ubancan lallai yau ana yin ta haka ta faɗa a fili
yumna me ya faru nazeefa ta faɗa tana kallon ta
da sauri ta juyo domin bata san nazeefa na dakin ba tace '' innalillahi wainna ilaihir raji'un wai nazeefa munafurcin naki da son ganin kwakwaf dinki har yayi haka to wallahi jiya dai kina jin malam yayi wa'azi akan illar munafurci ..,
yanzu yumna dan na tambaye ki me akai sai ya zami matsala
a fusace tace '' ubanki akai naci ubanki da uwar akai shegiya kawai ba damar mutun ya huta sai kun kirkiri wahala kun ta kura min..,
haba yumna yanzu iyayen namu kike zagi
buɗe baki za tai da sauri ta rufe domin ido hudu da sukai da malam da ashar zata lailayo ta yi wa nazeefa...
YAN ZAMAN MAKKAH
EPISODE 3
Girgiza kai malam yayi yace '' yumna zo..?,
ba musu taje har gaban sa ta tsuguna tace '' malam gani..,
cikin takaicin abin da ta aikata yace '' abin da kikai kinyi dai-dai kenan ki cewa mamman ya turo iyayen sa su karbi kuɗin da ya kawo yumna me kike son zama ne ..? kullum ina miki nasiha amma inda nake nuna miki daban inda kwakwalwar ki take nuna miki dabam
zaro mayan idanuwanta tayi ta dafe kirjinta tace '' na shiga uku shi da bakin sa yake ce maka ma faɗi haka innalillahi wainna ilaihir raji'un malam ni...,
ai kafin ta ƙarasa tuni ya tari numfashin ta yace '' yumna bana son fina da neman magana kamar yadda na saka auren ku watan cika ciki to yanzu wata me kamawa idan kin ga dama ki hadiyi zuciya ki mutu aure ba fashi kaf yan uwanki ba wanda yake neman ya sakani gaba sai ke..,
ƙasa tayi da kan'ta har ya gama fadan sa ya fita nazeefa na zaune tana jin su yana fita, tashi tsaye tayi ta shiga kaiwa da komowa turkashi akwai fa babban aiki a gaban ta ba zai yiwu ba a haifeta a cikin talauci ta tashi a talauci ta girma a cikin sa , a hanyar neman arziki tazo ace mata ba haka ba ina ba zata saɓu ba tafiya makka kamar tayi ta taga ma ne..
Yumna me kike cewa cikin zafin rai tace '' uwar ki da ubanki nake cewa munafuka..,
tana gama fadar haka ta dauki ƙaramar wayar ta , ta fita bata samu kowa ba a kofar gida bata da ko ficika a jikin'ta ina zata sami kudin da zata tafi arlit kama kugu tayi ta lula duniyar tunani ihun kazar Inna hadiza ne ya dawo da ita duniyar da muke ciki,da yake kwai take ta fito kenan daga kwanci kafin ta koma wani farin ciki ne ya mamaye ta a hankali ta soma binta tana sanda cikin ikon Allah ta cafke ta rufe ta tayi da mayafinta, ta fara tafiya da sauri babbar bukatar ta , ta ƙarasa inda zata cikin ikon Allah ta isa mado mado mado bude kofar sa yayi yana sakin hamma da miƙa yace '' yumna lfy kike kirana da rana tsaka..?,
liƙen dakin da ya fito take jin kamar muryar mace tace '' mado kamar bakai kaɗai bane a dakin nan..?,
haɗe rai yayi yace '' karki kawo min maganar banza me kika gani..,
gyara riƙon kazar tayi ta ɗaga kanta sama tace '' anya mado kaima baka bi layin su ilu ba..?,
layin uban ilu nabi wallahi ki kiyaye ni.
murguda baki tayi tace '' idan naki fa..,
zan san yadda zanyi dake
ya faɗa yana hade ransa
kaga bar maganar nan nawa zaka siya kazar nan ..?,
karɓar ta yayi yana juyata yace '' kiwo kika fara ne ..? ai wannan kazar kwanci take yi..,
Uhmmm kwanci take yi zaka siya nawa ..?
ina sauran kwan nata kawo har su na baki 2000fcfah (jaka biyu )
da sauro ta saka hannu ta amshi kayar ta , tace '' ai ba ta sata nace ka bari sai lokacin da na fara sata sai na kawo maka ka siya...,
yanzu yumna harda fadar bakar magana daga cewa jaka biyu
Mado wallahi idan ba naja shidda zaka siya ba wallahi ba zan siyar ba kaga aba ko sasshiya da ita kace haka zaka siya wai har da kwai to na soyawa su baba lami sunci..
kama haɓa yayi yace '' gaskiya ban siya haka ba ..,
karbar abarta tayi tace '' dadin ta bakai kadai bane akwai dubun ka..,
dariya yayi yace '' ya zaki tafi ban baki wani labari ba..,
tsayawa tayi ranta a hade tace '' wanne labari zaka bani..?,
Albishirinki na'ima kawar ki Allah ya darajar ta ta turo da kudi a rushe musu gidan su yanzu haka ma an fara aikin gidan bulu da bulu za'a mai da musu..
zaro idon ta tayi tace '' turkashi ikon Allah ashe kai ma kaji wannan zancen..,
Yumna zancen duniya yana karewa ne ai baya karewa kadai Allah ya azurta mu..
amma nifa ji nayi ana cewa karuwanci suke yi wasu kuma neman mata
da sauri ta toshe kunnuwanta tace '' yanzu ba dama wani yayi arziki sai ace ga abin da yake ti zati zunubi ko da ya kasance gaskiya ni wallahi ka bata min rai wallahi.
Mamman ne ya ƙara so tarar da su yayi, yana musu wani irin kallo irin na tuhuma din nan sannan yace'' masoyiya m kike yi a wannan guri...,
da hallacan rufewa jama'a baki, ni ni yumna yar malam zaka kai karata gurin malam to ka kyauta Allah ya ƙara karfin shedanci da annamimanci mado wannan mutumin da ka gani me taɓa ya'ne da mahaifinta bawan Allah nan bashi da kirki nace mai bana son sa bana son sa ana dole ne yaki..,
dan jim mado yayi sannan yace '' yumna me ya hadaki dashi da har kike wannan kikirarin...,
A fusace tace '' wallahi bana son sa banƙara jin tsanar sa ba sai da ya kai karata gurin malam wato idan munyi aure haka zai dinga kai karata, ko to Allah ya rufa asiri na gano waye shi..,
tafiya tayi ta barsu a tsaye ran Mamman duk aɓace yace '' kana ji abin da yarinyar nan take fada min ko wallahi zan dauki kwakkwaran mataki a kan'ta auren ta kuma dole inyi kona kwana ɗaya ne dole na kwanta da ita..,
dariya mado yayi yace '' daman tun da naga ka likewa yarinyar nan nasan da wata a ƙasa son sha'awa kake mata bawai son gaskiya ba..,
aa wallahi dukka biyun ina yi mata shi wallahi ina jin yumna a jinin jiki na dukkan wani motsi da nake tana cikin ruyina da zuciya ta. tabbas idan taki aure na ita da aure har abada sai dai taga ana yi.
me kake nufi karfa ka cutar da ita ko dan mahaifinta da kake tare da shi ba abin da be maka ba a rayuwa.
dariya yayi ya shafa kansa yace '' ka manta me ake ce wa *DAN KUKA ME JAWA uwarshi jifa*
Allah ya kyauta cewar mado ta faɗa yana shiga dakin sa zama yayi yace '' na barki, kina ta jira ko..,
murmushi tayi tace '' wallahi ba komai amma kamar muryar yar malam naji..,
ita ce taso da ta shigo dakin nan na hata.
Dan jim tayi sannan tace '' me zata shigo tayi..?,
waya sani kinsan ta da shegen bin kwakkwafi sai taga abin da ya turewa buzu nadi mado ya fadi haka yana washe baki.
gyara zaman gyalanta tayi tace '' bani kudin na tafi..,
shafa gemunsa yayi yace '' ki bari na dan sha kaɗan sai na ninka miki kudin ki..,
gaskiya ni a'a jiya ma wuni nayi yana min zafi bazan iya ba na hakura da kudin nan kawai siya wanda zaka siya ka bani kudi na su fa'iza da kake taɓa nasu ai kaga yafi nawa kuma sun girme ni..,
Nana ta faɗa tana kara rufe kirjinta da be dade da fara fitowa ba.
kudi ya ciro a aljihunsa yace'' taɓawa zanyi ke baki ga yadda su fa'iza suke fantamawa ba da yumna bata yi baki ga yadda take ba samun canji ba wahala yake mata ..,
tunani ta shiga yi can kuma sai tace '' to amma ni dai wallahi ance ba kyau kaga na hakura basai ka siya ba tafiya zanyi ta faɗa tana tashi tare da dora farantin tallanta a ka.
tab lallai ma yarinyar nan wallahi baki isa ba kin gama tada min komai yanzu kuma kice ga zance.
sauke mata farantin yayi da sauri ta cika ganin yana neman zubar mata da shinkafar tallan'ta kuka ta saka ganin zata tara mai jama'a duk da rana ta kwalle gari yayi shiru amma akwai yan sa ido suna nan suka abinda yake wakana cikin mugunta ya murɗe mata su sannan ya cika ta ko banza dai ai yayi daukan farantin ta tayi ta fita a guje jikin'ta na rawa sai da ta sha kwana sannan ta fara tafiya a hankali a kofar gidab su fa'iza ta tsaya da sauri fa'iza da take soro ta , tashi tace '' yanzun nan yumna ta wuce wai kema kince mata zaki makka aikatau haka ne..?,
eh hakane wallahi ina son zuwa.
kai ta gyaɗa tace '' wanda be ji bari ba , ba yaki gani ba wallahi ke kinji yadda ake fadin rayuwar da bakaken fata suke yi..,
dariya tayi tace '' duk karya ne kinke kin gani da idanuwan'ki dan haka karki dorar da komai tunda ba gani kikai ba..,
ajiyar zuciya ta sauke ganin tana kokarin nuna musu babban kuskuran da za suyi a rayuwar su mafi girma amma idanuwan'su sun makance ita tasan wace na'ima tun tana garin nan yanzu da ba idon iyaye Allah ne kadai yasan me take aikatawa fa'iza tace '' ya naga kin tawo duk a firgice..?,
a gaskiya bazan iya ba ina gurin mado da kika kaini kika ce har waya yake siyawa yan mata to jiya naje abubuwana suna zafi yau kawai sai na kai mai tallan shinkafa tun da yace in dinga kai mai to shine yace min ga zance nace ni ba zanyi ba jiya wallahi kamar na saki fitsari lokacin da yake yi lokacin da na dawo gida duk sunyi tsami dakyar suka dawo dai-dai shine yanzu ya danne ni wai be san zance ba.
jin jina kai fa'iza tayi tace '' kinga mun tsaya a rana ki shigo mana daga ciki...,
shigowa tayi ta ajiye farantin ta tana cewa kai wallahi dakin maman ku ba karamin sanyi ne da shi ba.
dariya fa'iza tayi tace '' haka kowa ma yake cewa..,
nana tace '' wallahi akwai sanyi yadda kika san na kwanta wallahi nayi bacci saidai ina tsoran fadan maman mu yanzu idan ta fara faɗa wallahi har bayan isha barin ta ga ba abin da na siyar mata..,
Allah ya kyauta yanzu dai gobe zaki goma
zaro ido tayi tace '' ina ba inda zani wallahi yanzu ma murde min da yayi zafi suke ba..,
kinga yadda sukai fa ta fadi haka tana daga mata rigar ta dariya fa'iza ta fara yi har da riƙe ciki tace '' kai jama'a shi yanzu mado me zai yi da wannan lemon tsamin wallahi dole yayi miki zafi...,
harararta tayi tace '' ai kinsan da haka kika kai ni..,
sannan kuma son zuciya shike dawainiya dake waya ce miki haka siddan namiji zai dauki kudi ya baki lallai kinyiwa kanki karya.
muguwa wallahi bazan ƙara daukar shawarar ki ba.
cewar nana
Fa'iza tace '' yauwa kamar tafiyar nan ce makka haka kurum idan dai ba fita za kiyi ki nema ba , ba za su baki kudi ba.
ba ance ana bara ba a bakin harami saboda suna tausayawa miskinai
wata harara ta zabga mata tace '' ai kinsan haramin soron ubanki ne dole ki zauna kiyi bara a nan bara na kirawo na'ima kuji me take domin la lura idan ba haka nai muku ba sai kun kai kanku mahalaka ita fa bama a garin makka take ba tana Labanon a gidan wasu arna take aiki..cemin tayi mijin matar yayi itama matar ta lallaɓo tayi.
gyara zama tayi dan jin wayar na'ima tana ringing cikin Sa'a aka ɗaga hello na'ima ya kike..?,
Lafiya qalau fa'iza yau kin tuna dani..
cewar na'ima.
kullum kina raina kawata ki warware wannan kullin da kikai yumna da nana suna ƙoƙarin tawowa zasu nemi agent din ki suma yayi musu visa su tafi makka ki fada musu ayyukan da ake yi kinsan dai ke ba'a makka kike ba ko haka kwanaki da jimawa kika ce min..
wani takaici ne ya turake ta , tace '' a gidan uban wa nace miki ba'a Makka nake ba to ina aiki ne da gidan Sarkin makka abdulaziz..
buga cinya nana tayi tace '' fa'iza be kamata idan ke ba zaki ba ki hana wani ya tafi, duk kinbi kin addabi kanki akan munce za mu je Alhamdulilah Magana a bakin me ita tafi dad'i gashi nan tace a gidan sarki ma take aiki duk wani dan bakin ciki sai dai ya mutu..a ko ina ba'a rasa na Allah.
EPISODE 4
Tashi fa'iza tayi tace '' na nuna muku gaskiya kun ki bi ko to wallahi kuje ga Duniya nan zata koya muku hankali..,
dariya nana tayi tace '' ta dai koya miki hankali mu dai tafiya ce ba fashi sai munyi..,
Dariya fa'iza tayi tace '' to Allah ya kaiku lafiya.,
amin ya Allah nana ta faɗa tana fita daga cikin gidan
kai tsaye gidan su yumna ta nufa a hanya suka ci karo da ita riƙe da kaza da sauri nana tace '' yar malam kaza kika siya ne..?,
haɗa rai yumna tayi domin sarai ta san halin nana kuma bata son munafurci da tsaigumi dan yanzu sai taci uban'ta tace '' eh kaza na siya ban isa bane..?,
dafa ta nana tayi tace '' Allah ya wuci zuciyar ki ni bada wata manufa na faɗa ba..,
wani kallo tayi mata tace '' to sai an jima domin sauri nake ina da a bin yi..,
sosa kai Nana tayi tace '' yumna ya maganar tafiyar mu makka.?,
chak yumna tayi ta juyi tace '' tana nan ba fashi ki nemo kudin tafiya ARLIT domin acan agent din na'ima yake da zafi zafi ake bugar karfe gwara muyi da gaske dan naga yan hassada sun soma tu somu a gaba yawa wanda nace zan tafi yawan karuwanci kowa aibata garin nan yake kai Allah isaka ranar lahira muna ɗaya daga cikin yan kallo, domin wallahi Ubangiji bazai bar masu yiwa garin manzo sharri ba.,
farantin ta ta sauke ƙasa tace '' amin ya Allah nima fa abin ya soma ban mamaki har kura ita ce zata cewa kare maye yanzu fa'iza tana nan mene bata yi, naga kwana ki bayan tafiyar ki da kika zo kika tarar damu muna kallon wannan video har kika ce ba kyau to wallahi ce min tayi mu gwada ba kunya ta dinga taɓa min abubuwana har sha tayi.,
zaro ido yumna tayi tace '' ke nana bana son sharri mayya ta zama kome..? me ta taɓa miki..,
kauda kai nana tayi tace '' kema yumna kamar ba wayis ba so kike a dinga fadar abu gatsal ba sakayawa..,
kai yumna ta jinjina daman ta gane kawai so take ta ƙara tantance wa domin tasan wanne kalar ɗiban albarka za tayiwa fa'iza ajiyar zuciya ta sauke tace '' to na fahimta kuma yanzu dai bani da wani lokaci da a yau naso ma na tafi amma abu ne samu ba dan haka zan bari sai gobe, gwara muje ɗiban yan aiki da za ayi a saka mu a sahun gaba kar duk a cike guri me dan malasa.,
daukan farantin ta tayi ta dora aka tace '' wallahi kuwa gwara muma mu samu guri me dan danshi kai Allah ya kai mu ranar da yau zan wayi gari a garin manzo sai naje naga ka'aba wallahi..,
dariya yumna tayi ta limshe ido tace '' amin ya Allah wallahi har na gano ni a makka..,
lah lah lah ba malam ya hanaki wannan maganar tafiyar ba wallahi sai na faɗa mai cewar shamsiyya da sauri yumna ta juyo tace '' kutumar ubancan lallai yau zan ɓalla ƙasusuwan ki wallahi sai na ladabtar dake ko wani kika ga yana Magana ba ki baza ki ƙara saka mai baki ba a cikin zancen sa dan uwar babar ki .,
kafin kace me tuni shamsiyya ta ci kafar kare ta arta a guje da gudu yumna ta bi bayan ta , still bata ajiye kazar nan ba shaf ta manta da ita ma kawai ƙoƙarin kama shamsiyya take wani uban birki ta ja a kofar gidan su ganin wata iriyar mota har daukan ido take tasan dai malam bashi da wasu yan uwa masu kudi
dan haka momy ce ta zo ganin ta farin ciki ne ya kamata ganin faduwa tazo dai-dai da zama da sauri ta shiga cikin gidan nasu ta ajiye kazar inna Hadiza a soro.
kaza ta azabtu kasa motsi tayi sai ta rakube guri ɗaya gaban yumna ne ya fadi ta dungure ta da kafar ta batai wani motsi ba tasan shamsiyya sarai ta ga kazar inna a hannun ta amma ai ba zata rasa abin da zata fadi ba dan haka ta shiga cikin gidan Inna Hadiza da sauri tace '' yumna ance ke kika daukar min kaza ta..,
zaro idanuwanta tayi tace '' gata can ganin ta nayi yara suna ƙoƙarin kama ta shine na ci ubansu na dauko ta na ajiye miki ita a zaure..,
bata tanka ta ba , ta nufi hanyar zaure ita kuma yumna shiga cikin gidan tayi tana zare ido can ta hango momy a guje ta ƙarasa gurin ta tare da rungume ta cikin farin ciki tace '' mommy dani zaki tafi ko..?,
murmushi tayi tare da gyara mata zama a kan cinyar ta baba lami tace '' yumna baki iya gaisuwa ba ne katuwar ki da ke zaki hau mata kan cinya..?,
Murmushi momy yusra tayi tace '' ah barta bakomai kuruciya ke damun ta.,
taɓe baki baba lami tayi ta ci gaba da aikin iza wutar ta indai yumna ce ba'a ci mata alwashi shege ba bakon mutum ɗaya bane dan haka zata koya mata darasi ne kala kala.
tashi yayi yace '' mommy zan fita waje naga nan ba network zan kira ahlam ne naji ya jikin nata.,
ɗago kai mommy tayi tace '' hmmm har yau ka kasa fahimtar wace ahlam Allah dai ya fahimtar da kai so ya rufe maka ido.
ƙasa cewa komai yayi ya zura wayar sa a aljihu yace '' mommy sai kin fito.
kallon mamaki take mai tace
''juraij baka ga yar uwarka ba ne ko magana bakai mata ba ,
zaro kuɗi yayi a aljihunsa yace'' ungo ki bata ,
ƙin amsa tayi tace '' maganar kudi nayi maka ce wa nayi baku gaisa ba yanzu ko bayan raina ba zaka iya ci gaba da rike amanar da aka bar min ba yumna marainiya ce bata taso ta san daɗin uwa ba taso na riƙe ta amma mahaifinta yaƙi.,
zama yayi a zahiri yarinyar ta bashi tausayi amma da ya tuno zuwan sa da yayi lokacin da mommy ta aiko shi ya zo ga gane mata ya take ita lokacin bata kasar nan yazo ya tarar taci kwalar wani namiji suna bawa hammata iska ta rufe idon ta yasan cewa bata da mutunci,tun daga nan ya gane yarinyar bata da wata isasshiyar tarbiya cikin deep voice din sa yace '' ya karatu ..?,
sosa kai tayi ta ɗauke fuskar'ta, haka kurum taji ta tsani wannan mutumin bata son rainin hankali ita kuma ta lura halin sa ne kamar ma wani gani gani yake mata waishi gashi me kudi to ai itama ta dauki hanyar yin kudin sai ma ran da yazo ya ta rushe musu gidan su tace '' Alhamdulilah an ma bamu hutu.,
oh Allah ya temaka ya faɗa yana ficewa daga dakin zamewa yumna tayi tace '' mommy zan biki..zaki tafi dani.,
kama kumatun ta tayi tace '' yumna me zai yana idan dai malam ya yarda sai na